Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bishi har zaure?, wanna wacce irin mayitaccen soyayya ce?. Irin haka ai sai ki fita fit daga zuciyarsa, shi ɗa namiji bai cika son haka ba, ban hana ki nunawa mijinki soyayya ba amma gaskiya na lura daga ke har shi zumuɗinku yayi yawa sai kace a kanku aka fara aure, ko kune tattabu iyayen soyayya sai haka".
Tunin jikina yayi sanyi, ta wani gefen kunya ta hana ni sakat wani ɓangaren zuciyata ta antaya tinani ko ta ga munyi wani abun ne da ta fassara shi da rashin kunya?. Ban cimma amsar tambayoyina ba amon muryata ta koma dukan kunnuwana.

"Ke ce daman ban sama damar sanar dake ba, amma ita Habiba ta san komai bana ɗaukar rashin kunyar ƴaƴan zamani mussamman naku ke da Yusuf da soyayya take fisgar ku, don haka ku kiyaye".

A ladabce na ƙanƙan da murya na ce"In sha Allahu za'a kiyaye Allah ya huci zuciyarki".

"Amin".
Ta amsa a daƙile, kafin ta ɓarke da tambayar shin kuna yi girki kamar yanda ta tsara duk muka amsa mata da e, nan ta wuni har sai da tayi sallan asr kana ta tafi duk wani motsinmu tana ankare dashi, da ta ga abinda bai kwanta mata a rai ba sai tayi magana kansa.

Bayan tafiyarta ina alwalan sallan magrib da ya gabato, Maman Hanan ta ce dani"Sai haƙuri Na'ima halin Anty Binta sai dai haƙuri, domin komai kika yi bakya yi mata gwaninta ba balle har ta furta miki kalmar yabo. Haka take ba'a burge ta, ai ke tayi sauƙi ma lokacinki domin ni sanda nake amarya ko amarci bata barni naci da Abban Hanan ba kullum safiyar duniya tana gidan nan".

Murmushi kawai nayi sakar mata"To Allah ya kyauta".
Ta amsa mini da"Amin". Ban san dalilin zuciyata na ba sam ban ga laifin Anty Binta ba akan abinda tayi, sai ma wani ɓangaren zuciyata da take ayyana mini cewar soyayyar ƴan-uwanta ne ke sanya ta aikata hakan.

Salla na shiga ɗaki nayi, nan Maman Hanan ta iske ni muka kafa hira nan nake sanar da ita burina da nake dashi na zamowa marubuciya kuma ƴar jarida. Ta bani kwarin gwiwa sosai, sai dai kuma ta tabbatar mini da cewar ko da na sama amincewar Yaya, Anty Binta ba zata taɓa laminta hakan ba balle har ya kai ga afkuwa.


*MATAN AREWA*

*_©Maimunah Tijjani Iyam_*
____________________________

Page 1⃣4⃣

Duk na zaƙu da son jin muryar Abbana, Maman Hanan har dariya take yi mini, da zokalar sai kace auta ko ƴar fari. Ban bi ta kanta ba na shiga dannawa lambar Abbana ƙira bugu biyu ya ɗaga ƙira tare da sahihiyar sallama a bakinsa.
A nutse na amsa sallama gami da cewar"Ina wuni Abba an wuni lafiya?".

"Lafiya ƙalau Na'ima ya mijin nakin?".

Tsaf ya ɗauki muryata duk da kasancewar kuwa ba shi da layin nawan, hasalima basu san nayi salula ba.

"Lafiya ƙalau Abba, ya gida da kowa da kowa Hajiya Babba da su Baba".
Duk da bana ganin shi gabana, amma muryarsa ma kaɗai ta isa fallasar da tsantsan farin cikin dake ransa.
"Lafiya ƙalau Mamana ina fata babu wata matsalar?".
"Babu komai Abba lafiya ƙalau, daman shine ya saya mini waya har da layi nace bari na ƙira ku na shaida muku".

Sai da yayi nisa kafin yace"Masha Allah, Allah ya saka masa da alƙhairi ke kuma ya ba ki ikon yi masa biyayya dai-dai gwargwado sai ki bi waya a hankali na sanki da zumuɗi".
Sai da na sheƙa dariya kafin na ce"Amin amin Abba".
Mun yi hira sosai dashi, yake shaida mini baya gida balle ya haɗa ni da Umma da Hajiya Babba. Ina kashe ƙiran na dannawa ƙiran yaya Majid har ya katse bai ƙira ba, ina shirin ƙira a karo na biyu ƙiransa ya shigo wayata, ko ruri ban bari tayi ba nayi caraf na ɗaga. Sallamar da nayi ya amsa kana na gaishe shi.
"Yaya Majid nayi kewarku sosai wallahi, kowa yazo mini amma banda kai".
Na ƙare zancen ina turo baki kamar ina gabansa, sai da ya dara yace"Nima zan zo, amma ba yanzu ba sai kin shekara har kin haihu kana nazo". Rufe fuskana nayi cike da kunyar zancensa"Haba yaya Majid haihuwa kuma?, ni da nake son komawa makaranta nayi yaya kenan?. Ai sai dai na ɗauki ɗaya karatu ko reno domin taura biyu a baki basa taunuwa".

"Na'ima ai shi aure sam baya hana karatu, kamar yanda karatu baya hana aure, ko yanzu mijinki ya amince miki za ki yi ko lokacin mu a NCE department ɗin mu akwai matan aure da yawa wasu ma har da ƴaƴansu, amma hakan bai dakatar dasu daga neman ilmi ba".
Ƙarƙarfan ajiyar zuciya na sauƙe da ta bani damar haɗiye wani abun da ya tokare mini maƙoshi, kafin na sama sararin faɗin"Daman maganar da nake son muyi kenan, wallahi Yaya Majid ina son karatu ina son komawa makaranta, ina son cimma burina na zamtowa ƴar jarida kuma marubuciya. Sai dai a duk sanda na yunƙuro sai zuciyata take ayyana mini cewar lokaci ya ƙure min...". Taran numfashina yayi ba tare da na dire daga zancen da na ɗauko tiriyan tiriyan ba.

"Na'ima kamar yanda nasha faɗa miki, matuƙar kina da rabo a karatu za ki yi domin bawa baya tsallake rabonsa duk inda yake ke dai kawai ki dage da addu'a kuma ki sama lokacin da ya dace kuyi mana da mijinki yanda zai fahimce ki, idan ya amince babu abinda zamu ce sai hamdala ga ubangiji idan kuma ya nuna baya so sai kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara".
Kalamansa na ƙarshe suka daki zuciyata, har sai da na runtse idanuna ba tare da na buɗe su ba na soma cewar"zan yi mishi maganar in sha Allah ka taya ni da addu'a Allah ya bani nasara". Kamar abinda yake jira kenan yace dani"Amin amin in sha Allah ma za'a dace, domin na taɓa yi masa maganar kafin bikinku kamar yanda nayi miki alƙawari ya kuma nuna mini babu damuwa. Ban sani ba ko a lokacin giyar soyayya ce take ɗibar shi shiyasa ya bani tabbacin babu damuwa, kinsan wasu daga cikin mu a lokacin da suke biɗe da son mallakar yarinya babu abinda ba za suyi ba don ganin sun mallake ta, haka nan dukkan tsaurin alƙawari su kan iya ɗaukar ta ko babu gammo, sai an aura kuma su nuna sam basu san zance ba mussamman mu da ba yarjejeniya muka ƙulla dashi akan zai barki ki yi karatu ba".
Sosai naji jikina yayi sanyi laƙwas, na jawo ƙafana na langwashe shi na buɗe baki da zummar furta wani kalmar rurin wayan ya ƙare, tisa ta gaba nayi tallafe da kuncina ina kallonta duk da kuwa hankali da tunanina sam basa gare ta. Ɗago kan da zanyi idanuna suka sauƙa akan fuskar Yaya dake tsaye bakin ƙofar ya naɗe hannayensa dukka biyu a ƙirji yana kallona da na jigamunsa. Da alama ya ɗau lokaci tsaye a wajen, ni na fara janye idanuna kafin na tashi na isa gare shi ina yi masa sannu da dawowa tare da tambayar yaushe ya shigo?.

Sai da ya sakar mini gajeran murmushi ya ce"Na daɗe da shigowa, kawai hankalinki ya tafi kan waya ne shiyasa ba ki ji shigowata ba balle ki lura da ni". Kunya naji na duƙar da kai, ya riƙo ni na taimaka masa wajen ɓalle maɓallan hannu da wuyar rigarsa sannan na haɗa masa ruwan wanka ya shiga yayi a gurguce ya shirya saboda har an fara ƙiran sallan magrib ya fita.
Sallan nima nayi na daɗe kan sallana ina miƙa kokena ga maƙagin rayuwata, mai ikon juya tsanani zuwa sauƙi duhu zuwa bayyanannan haske. Ya juya lamuran rayuwata izuwa mafi zammantowa alkhairi a gare ni, a raunane na shafa addu'ar na zare hijabin kaina na fito na kamawa Maman Hanan wasu aiyukan kafin isha'i mun kammala abincin dare. Na ɗauro alwala zan shiga ɗaki sallamar wata maƙwabciyarmu suka dakatar da ni washe baki tayi tana yi mini kirarin da bata gajiyawa da yinsa shiga goma fita goma.

"Amarya mai tuwon damin, Amarya bakya lafiya ko da kuwa kin kwantar da ɗan gida kin yanka ta Malam Yusufu".

Taƙaitaccen murmushi nayi haɗi da gaishe ta, ta amsa tana nufar ɗakin Maman Hanan, don tun zuwa gidan babu garin Allahn da zai waye bata niƙo gari tazo wajen Maman Hanan ba. Ko da wasa basa zance a gabana fahimtar hakan da nayi ya sanya ni da mun gaishe nake tashi na basu wajen gudun kar na takura su.
Ina sallan ta ɗago labulu tayi mini sallama, ko da na iddar kallon ƙofar nayi haka nan naji zuciyata bata gamsu da ita ba ko in ce jininmu bai zo ɗaya ba. Tare da yaya Auwal Yaya suka dawo muka yi abincin tare kamar yanda muka saba, kafin muka yi musu sallama muka wuce ɗaki.
Tun ina wanka a banɗaki nake saƙa da warwaran yanda zan tunkari Yaya da maganar, har na fito na gama shirin kwanciyana a hankali na saci kallonsa yana zaun saman gado yana duba littattafan ɗalibansa da ya basu aikin gida. Ba tare da ya ɗago ba yace dani"Zo ki zauna".
Banyi musu ba na zauna kusa dashi ya ture takardun gefe guda yana fuskanto ni sosai har ina jiyo sauƙar numfashinsa. Ɗaga mini gira yayi"ina jinki menene kike son sanar dani?, don yanayinki ya nuna bakinki yana ɗauke da magana".

Ras! naji gabana ya faɗi, na ɗan yi jim kafin na aro jarumta na yafawa kaina na soma cewar"Yaaya daman wani alfarma nake son roƙo a wajenka".

"Na'ima kin wuce roƙon alfarma a wajena, sai dai ki bada umarni faɗi ko menene ina tabbatar miki indai bai fi ƙarfina ba har kin samu".
Musgutawa nayi kamin na ɗaura da"Yaaya daman magana ce akan karatuna, kasan na kammala ƙaramar sakandiri shine nake son ɗaurawa izuwa gaba idan na sama yarjewa da goyan bayan ka".

Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe, har sai da na sha jinin jikina zuciyata ta buga da ƙarfi shikenan ta faru ta ƙare!. Sai da yayi gyara murya yana gyara zamansa yace"Hakan burinki, kuma kin tabbatar zai sanya ki cikin farin ciki?".
A harzance na ɗaga masa kaina. Da hakan ya bashi damar ɗaurawa da cewar"Matuƙar hakan shine burinki tun gabanni haɗuwarmu dake, bazan miki katanga da tabbatar da mafarkin rayuwarki ba. Ni Yusuf mijin Na'ima nayi mata izni da kuma yarje mata ta ɗaura da karatunta har sai ta cimma burinta, ba kuma hakan yana nufin bana kishinta bane illa iyaka na yarda da ita na kuma san wacece na auro na ajiye a cikin gidana, kasancewar ki mace kuma marar aure mai iyali bashi zai sanya ki cire rai ga cimma muradin zuciyarki ba naji duk tattaunawanku na ɗazu da Yaya Majid kuma ya taɓa sanar dani hakan. Ina so yanzu ki samu ƙwarin gwiwar tunkarar mafarkin rayuwarki har sai kin tabbatar dashi a zahiri ba mafarki ba".

Farin ciki, daɗi, murna da annashuwa na gaza ware takamammen wanda ya ziyarci ruhina a wannan lokacin. Ban san yanda aka yi kunyata tayi ƙaura daga gangar jikina na wucen gadi ba, don ji nayi na ƙanƙame Yaaya tsaf a jikina tamkar wani zai ƙwace mini shi.
Jin muryarsa kamar mai raɗa yana cewa"A sausauta min, na sama damar zuƙar numfashi".
Na janye jikina a kunyace, yana mini dariyar da ya sani sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna nake faɗin"Haƙiƙa Yaaya babu wasu kalaman da zasu iya kwantanta yawan farin cikin da nake ciki a yau. Nagode Allah ya saka maka da alkhairi duniya da lahira yanda ka sanya ni farin ciki Allah ya bani ikon zamtowa mace ta gari a gare ka".
Tunda na fara yake bina da kallo, murmushi ya gaza barin fuskarsa har na dasa aya ya amsa mini cikin faɗin"Amin amin ya Allah tawan, kamar yanda kika roƙi alfarma a gare ni nima zan roƙe ki da ki tsare mini mutuncin kanki a ko ina kika shiga".
Tun kafin ya rufe bakinsa na tare shi da"in sha Allah ba zan taɓa butulce maka ba, sannan nayi alƙawarin riƙe maka mutumcin kaina da kuma na igiyoyin auren dake bisa kaina".
Kansa ya jinjina cike da gamsuwa da zantukan nawan, sannan yace"Gobe zamu je gidan Anty Binta sai na sanar da ita komai, da kuma su Abba suma ya kamata su sani kafin komai ya kankama".

"Allah ya kaimu".

"Amin ya Allah".

Ya amsa dashi yana ɗage mini ido ɗaya"Ba'a sanar da ni shin menene burin abar alfaharin nawan ba".
Sheƙewa nayi da dariya sai da na tsagaita nace"banda burin da ya wuce zama marubuciya kuma ƴar jarida".

"Kyakykyawan buri Allah ya taimaka".

"Amin".

Ban taɓa ganin daren da yayi mini tsawon kamar wannan ba, ban sani ba ko don tsantsan zaƙuwar da nayi gari ya waye ne oho. Ban sama bacci kirki ba domin tsantsan murnar da nayi nitso a cikinsa ya hana ni hakan, banda burin da ya wuce gari ya waye muna rayayyu kuma lafiyayyu na zama yarda iyayena suma da Anty Binta da nake fata..

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 1⃣5⃣


Tun da nayi sallan asubahi ban komar da haƙarƙarina na kwanta ba, na gama dukkan aikace aikace na kasancewar ranar ƙarshen mako ce watau asabar babu makarantar boko islamiyyar safe kawai Yaaya yaje. Duk abinda nake yi murmushi kawai yake yi yana bi na da kalaman da suka ƙawata birnin zuciyata maƙil da farin ciki marar iyaka"Na'ima Allah ya cika miki burinki".
Sai da na rausayar da kai na amsa da"Amin amin". Muna gama karin kumallo muka shirya, nayi Maman Hanan sallama muka fice a mashin ɗinsa. Sai da muka yi tafiya mai ɗan tsawo kasancewar tsakaninmu da gidan Anty Binta akwai tafiya, a ƙofar gidan ya ajiye mashin ɗin muka shiga ɗauke da sallama a bakunan mu.
Ita kaɗai muka iske a gidan tana sauraron radio, ganin mu ya sanya ta ƙara yalwata annurin fuskarta tana baje mana tabarman da take kai ta yanda zai ishe mu, sai da muka zazzauna kana duk muka haɗe baki wajen gaishe ta, ta amsa mana ɗaiɗai ta yunƙura ta miƙe ta kawo mana ruwan sha.

"Anty ke kaɗai a gidan, ina sauran yaran fa?".

"Husna ta shiga maƙwabta kitsi Amiru kuwa ya tafi shago, Abbansu kuwa kasan ba mazauni bane".

Kansa ya jinjina, ta ƙare mana kallon tsaf kafin tace"Ki shiga ɗaki ki ajiye hijabin naki da jakan ki fito mana ko bakya jin zafin nan ne?, ko da yake ma yanzu da ragowar sanyin safiya".
Saurin taran ta Yaaya Yusuf yayi cikin faɗin"A'a Anty ai ba wuni zamu yi ba, daga nan ma gidan su zamu je daman wata magana ce take tafe damu".
Sai da ta ɓantari guntun goron da ta sinco daga gefen zaninta, ta furta cike da mamaki"To in ce lafiya?, ba wata matsalar kuka samu ba tsakanin ku?".

"Lafiya ƙalau babu wata matsalar tsakaninmu, daman magana ce jiya muka tattauna da Na'ima. Kafin aurenmu ta kammala karatunta na ƙaramar sakandiri ba ta sama ɗaurawa izuwa na gaba ba, har aka yi bikin shine naga dacewar ta cigaba da karatunta don na lura tana da sha'awar hakan ita ma. Ni dai na amince mata shine nazo mu tattauna kan batun naji naki ra'ayin, kamar yanda iyayenmu suka bar miki amanar mu tare da nusar damu yi miki biyayya akan komai matuƙar bai saɓawa hayan Allah, kuma mu kasance masu neman shawaranki akan dukkan lamuran rayuwarmu shine dalilin kawo maganar nan gabanki".
Taɓe baki tayi tana masa wani irin kallon da na gaza hango ma'anarsa kana ta ɗan murmusha kafin ta ce"To ai Yusuf ban da abinka, wannan ba neman shawarata kake yi ba hukunci ne ka gama zartarwa shine yanzu kake sanar da ni".
Duƙar da kai yayi cikin bata cikakken girmanta yake faɗin"A'a Anty sanin kan ki ne ba zamu taɓa zartar da wani hukunci ba sai da shawararki da kuma saninki, ko da na yanke shawaran naki yana iya ruguje nawan".
Sai da ta numfasa tana kawar da idanunta daga gefe ta furta"Ku dai amanar iyayenmu ne a gare ni, kuma kullum cikin ƙoƙarin sauƙe wannan amanar nake Yusuf duk abinda nake yi akan ku kama daga yin ruwa da tsaki a lamuran gidadenku so da ƙauna ne ya haifar dashi, kuma ina gani na isa da ku ne shiyasa. Amma gaskiya wannan batun nakan mai girma ne komawar matar aure makaranta gaskiyar zance babu tsari cikin wannan lamarin kuma bai yi kama da abinda hankali zai ɗauka ba".

Katse ta Yaaya Yusuf ya soma yi, tayi saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu alamar bata son sauraran komai daga gare shi, shuru yayi nikam kamar wacce ruwa ya cinye tunda na zauna na kasa ƙwaƙwƙwaran motsi balle tofa wani abun.

"Yusuf in dai ka yarda har yanzu amana tace ku, to gaskiya ban amince game da komarwa Na'ima makaranta ba kuma bana son a ƙara tado da maganar na gama da ita na rufe ta anan na burne, in ba lalacewa ba meye abin burgewa a cikin lamarin nan mace mai aure da iyalinta ta zari hanyar makaranta kullum tana tafe tana cuɗanya da garadan maza. Ina abin burgewa a cikin boko ga mace da har zaka yiwa matarka ta aure halaliyarka sha'awar ta tsunguma cikinsa?".

Ƙululu cikina ya bada sauti, kafin bugun ƙirjina ya fara hawa da sauƙa tamkar farashin man fetur a gidaden mai. Wani kuka ya taho mini da nayi azamar toshe bakina a ƙoƙarin hana sautinsa bayyana.
A sanyaye Yaaya Yusuf yake cewar"Anty Binta ba wai ina ƙoƙarin kaucewa shawararki bane, amma shi karatu a zamanin yanzu da muke tsinci kanmu a ciki, ya zamto kamar wajibi ga ɗiya mace ko ta fuskan kula da gidan aurenta da tarbiyan ƴaƴanta tabbas zai an ci karo da bambamce bambamce da wacce ba ta da ilmi. Sannan ba ko wacce mace bace take ballagazar da kanta wai don tayi boko wallahi da yawansu sun fi wanda basu yin sa suke ƙunshe cikin gida kamewa da tsare mutumcin kansu. Dan Allah Anty ki fahimce ni akan wannan lamarin".
Sai ta ƙare masa tanadin kallo tsaf!, tana ta ja wani tsakin mai dogon zango haɗi da cewar"Lalle Yusuf dole ka zauna gabana kana tsaro min wannan zantukan daki-daki wani bayan wani duk akan mace?, watau kaji daɗin aure ko ba shakka. Duk karatun bokon da zata yi ince dai ƙarshen abun a nan duniya zata tafi ta bar shi, ko zai amfane ta lahira?, Tunda yarinyar nan tana da ilmin addini dai-dai wadaida har hadda littafi mai tsarki gare ta to ni banga abinda zaku tada hankali sai ta koma boko ba".
Sai da ta ƙaurara amon muryarta ta ɗaura da"Yusuf ka nutsu kayi dogon tunani, nadamar da zaka tarar a gaba nake hango maka, tun wuri gwara ayi wa tufka hanci".

Duk shuru muka yi, kafin ta juyo kaina"Ko ke kike son komawa makarantar, kika matsa masa har ya tiso ki gaba kuka zo nan kuke ɓoye min?".

Sosai wani zuffa mai maiƙo ya karyo mini saman goshi, cikin rawar harshe da ƙoƙarin danne kukan da ke son ɓalle mini nace"Anty daman daman dam....".
Ban ƙarisa ba Yaaya Yusuf yayi caraf ya amshe zancen"Anty ko kusa ba ita ta taso da maganar ba, hasalima ni nake sha'awar matata ta ƙaro karatu".

Sai da ta kalle shi, nima ta ƙare mini tanadin kallo kafin ta murmusa gami da faɗin"Ba shakka Allah sarki soyayya to ni dai na gama magana, ra'ayi ya rage naka in kaso kaje kayi gaman kanka ni dai nadama nake guje maka, ke kuma in ma kece kik kitsa masa tun wuri ki dawo hayyacinki don ko a garin gaɓagaɓa a yi hakan ba".
Duk da ban ɗago kaina ba, amma jikina yana bani tabbacin idanun Yaaya Yusuf suna kaina yake cewar"Zamu tattauna da yaya Auwal in sha Allahu za ki ji yanda muka yi".

"To Allah ya kyauta, amma ni Binta ina na taɓa jin wanga lamari duk tsawon rayuwata a duniya mutum da hankalinsa ya gindine aurensa ya kama boko ilmin nasara".

Daga ni har shi babu wanda yace ko kanzil, bamu ƙara mintuna goma masu kyau ba muka miƙe muka yi mata sallama muka tafi sai ƙara jaddada masa hatsari da rashin yiyuwar abun take yi har muka hau mashin muka nufi gidanmu.
Duk iya ƙoƙarina nayi shi don ganin na danne ɓallewa kukan dake nuƙurƙusan rai da ruhina, amma abin yaci tura dai dai kwanan da ya karya na shiga layinmu babu shiri na tuntsure da kukan da nima kaina ban so fitowar sa ba a wannan lokacin, don har raina na son danne shi.

Tsayawa yayi ya sauƙa ya kashe mashin ɗin, a kallo ɗaya da nayi wa fuskarsa na lura shima duk jikinsa a sanyaye yake kamar an jefi kaza da ruwan gishiri.
"Na'ima dan Allah ki daina wannan kukan, domin kuwa bashi bane mafita gare mu. Ki tausaya min ki daina domin bazan iya jurar ganin zubar hawayenki ba amanarki iyayenki suka bani don haka ni nake da haƙƙin samar miki da duk wani abunda zai faranta miki, kuma na miki alƙawarin matuƙar muna tare sai kin cika burinki a karatu da iznin sarkin da ya sanya mace ta gari ta zamto sanyin idaniya mijinta, goge fuskar ya isa haka".

Ya ƙare zancen yana miƙo mini farin handkerchief da ya zaro daga aljihunsa, sosai maganganunsa suka ratsa ni sai dai bakina yayi mini nauyin da bazan iya cewa dashi komai ba, karɓa nayi kamar yanda ya buƙata na goge fuskana sannan ya hau kuma ƙarisa ƙofar gidanmu. Hindatu auran Hajiya muke fara haɗuwa da ita, a ƙofar gida zata shige ganin mu ya sanya ta nufar mu tana yi mana sannu da zuwa sosai na saki fuskana gare ta. Muka shiga ciki sai da na fara biyawa ɗakin Yaya Majid ya fita wajen wajen Yaaya Yusuf, kamar yanda na bar gidan haka na iske shi kowacce mace tana zaune ƙofar ɗakinta da ƴaƴanta zagaye da ita Ummata ce kawai ban hango ba don ita tun da can ba ta tsirawa kanta wannan ɗabi'ar ba. Da Anty Zakiyya nayi tozali tana wanki, ganin ta ya sanya ragowar sallamar da na fara maƙalewa a maƙoshina nufar ta nayi muka rungume juna cike da kewa.
Sai da na bi dukkan matan gidan na gaishe su, suka amsa fuska babu yabo babu fasalla kafin Anty Zakiyya ta ja hannuna izuwa ɗakin Umma har da kuka na sanya mata don tabbatar da yawan kewarta da nayi. Ban sanar dasu komai ba don sam na gaza samun ta inda zan fara. Hirar mu muke yi sosai da Anty Zakiyya Umma ta ƙara tilasta mini nace ɗakin kowacce na gaisheta bayan wanda nayi na farko, hakan nayi sannanna zarce sashin Hajiya Babba nan na iske Yaya Majid da Yaaya Yusuf, cikin son kaka da jika muka gaisa da Hajiya Babba kafin na maƙalƙale mata a jiki Yaya Majid yayi wa Yaaya Yusuf jagoranci har sashin mu yaje ya gaisa matan gidan da Ummanmu.
Nan muka yi sallan zuhr, har su Abba suka dawo muka gaisa kafin muka fara haramar tafiya, har na sanya hijabina bayan Ummata ta gama ɗaura mini wani nasihar yaya Majid ya aiko Nurain wai na jira tukunna Yaayan suna tattauna da su Abba.
Kasancewar a tsakar gida ya sanar da ni hakan, ya sanya matan gidan kallon junansu kafin wani ƙusƙus ya fara yaɗuwa wai ko ƙarata ya kawo na aikata wani laifin. Ban basu hankalina ba muka cigaba da hira da Anty Zakiyya da su Habiba da suke tsoma baki lokaci zuwa lokaci, har sai lokacin da Daada tayi wata maganar da ta baƙanta zuciyata.

"Na'ima ke kuwa daga ke har mijinki nakin kuka niƙo gari kuka zo hannu rabbana, ko ɗan tsabara a ƙannan nakin ba ki riƙo ba".
Shuru nayi kawai don sosai zancen suka dake zuciyata tare da baƙanta ruhina, Anty Zakiyya ce ta amsa mata da cewar"Daada ba daga gida suke bane shiyasa basu yi wannan shirin ba, amma ai akwai gaba zuwa kuma yanzu ta fara ai".

Taɓe baki tayi kawai ta kawar da kanta gefe, muka cigaba da hirar mu nan Anty Zakiyya take shaida mini zancen da ya faranta ruhina ainun cewar sun haɗu da wani saurayi ranar bikinmu, bata san daga rukunin wani ango yake ba. Amma ya nuna ra'ayi a kanta. Har gaisawa suke a wayan Yaya Majid. Sosai nayi murna tare da fatan Allah ya tabbatar da

Please Login or Register in order to submit comment