Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya gujewa ƙaddararsa.
Ƙiran wayansa a kai a kai da ake jeranta yi, ya sanya mu tashi muka koma cikin asibitin. Zazzaɓi mai zafi ya rufe ni a daddafe nayi sallan zuhr na haɗa da na asr domin lokacinsa ya gabato. Bayan sallan magrib aka yiwa Hanan sutura aka kai ta izuwa makwancinta har izuwa lokacin mahaifiyarta bata tashi ba domin ƙarfin allurar dake aiki a jikinta.
Sai asubahi ta farka, hannayenta ta fara motsawa kafin wangale marafan idanunta da suka kumbura sumtim tamkar ƙwayoyin idanun zasu faɗo ƙasa.
Anti Zuwaira da wata ƴar uwansu da tare tun maraici suke ta yi mata nasiha tare da nusar da ita yarda da ƙaddara mai kyawu ko kishiyar hakan yana daga cikin cikar imanin mutum wanda dukkan mumunin ƙwarai ya kamata a same shi da hakan, ko da aka sanar da ita rasuwar Hanan ɗin idonta ɗaya ne ya zirar da hawaye kafin ta yunƙura ta tashi zaune daga kwanciyar da take. Idonta ƙaf ta kallo Anti Sadiya cikin nushashewar murya ta ce"Na sani damar rasuwa zata yi, naji a jikina shikenan hankalinsa ya kwanta yayi min sanadiyar rasuwar ta, ku tashi mu tafi gida bazan iya zama cikin asibitin nan ba ba zan iya ba".
Yanda ta ƙare zancen ƙarshen cikin matuƙar ɗaga murya, ya sanya Anti Zuwaira umarta ta da na je wajen likita na karɓo mata sallamar da ta buƙata, da rawar jikina shaidawa likitan komai domin su yaya Yusuf basa asibitin suna can wajen karɓan gaisuwa. Tare dashi muka dawo ɗakin ya shaida mana cewar ba zasu sallame ta ba domin har yanzun lafiya bai wadace ta mussamman zuciyarta da ta kumbura akwai buƙata zamanta a asibitin tana karɓan kulawa da shawarwarin likitoti har izuwa sanda komai zai dai dai.
Yanda ta kuma birkicewa ya sanya shi dole rubuta mana sallaman, tare wasu magungun sai dai ya labarta mana cewar tana zuwa asibiti domin binciken lafiyarta. Waya nayi wa yaya Yusuf na sanar dashi ya ce muje gidan Anti Binta a can ake mata suke. Sai da muka fito daga asibitin maman Hanan ta dake akan ba zata koma gidan yaya Auwal ba daga nan sai gidan su, a wanna karon ta sama goyan bayan ƴan uwanta domin na lura duk suma a fusace suke game da lamarin aihun. Hakan suka tari adaidata suka wuce suka barni a wajen tsaye kamar wacce aka sassaƙa, jan ƙafafuna nayi nima na nemi abin hawa ya kai ni unguwar Anti Binta gabana yana tsananta bugu.
Cincirundon ƴan-uwansu na nisa da na kusa na tarar a gidan, duk na bisu da gaisuwa yanda naga Anti Binta bata tambayen ni ina maman Hanan ba hakan ya ƙara tabbatar mini da hashashen zuciyata na cewar tasan komai. Wata zuciyar ta kimtsa mini ko ma yaya za'a yi baza ta sani ba.
Nan na kwana, washe gari sai ga matan gidanmu sun zo bisa jagorancin yaya Yusuf, Umma ke faɗa mini jiya da su Abba aka yi jana'iza basu daɗe ba suka tafi, jikina ya ƙara yin sanyi laƙwas yayin da na gani kuma naji yanda duk suke karkata laifin ga maman Hanan, tare da wanke yaya Auwal watau ita ce karkatacciyar bishiyar kuka mai daɗin hawa?. Sai da aka yi sadakan bakwai yammacin ranar yaya Yusuf ya ce na shirya zamu koma gidanmu, sai a lokacin na sama damar ganin autansu Mahmud wanda naji ance tun washe garin ranar rasuwar yazo. Mun gaisa dashi tare da jajantawa juna abinda ya faru sannan yayi mana rakiya gida

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________

Page 2⃣3⃣

Wani abu ne naji ya zarge mini ƙalbi da naga ƙofar maman Hanan da aka bugawa kwaɗo jikina duk ya mutu na wuce ɗakina na ajiye kayana sannan na fito nayi wanka tare da ɗaura alwalan magrib nazo na gabatar da sallan na daɗe ina addu'ar nemawa maman Hanan sauƙi da sausaucin halin da take cikin domin nasan duk inda take tayi hannun riga da kwanciyar hankali balle samun cikakken nutsuwa. Ƙirjina ya buga da ƙarfi tare da bada sautin ɗas ina runtse idanuna, ina tinanin dalilin wanda ya aikatawa Hanan wannan rashin imanin ba tare da tunanin cewar akwai ranar da zai koma ga mahaliccinsa ba har yayi masa hisabi bisa aiyukan da ya shuka a nan gidan duniya lokacin da yake raye. Jin gidan yayi mini shuru sosai babu motsin maman Hanan haka nan yaya Yusuf da yaya Auwal suna can, Mahmud kuwa tunda ya rako ni shima juyawa yayi tsoro sosai ya yi mini mamaya.
Miƙewa nayi na ɗauko wayata da na kashe ta tun kwanakin da suka gabata na kunnata, jikina na rawa na shiga lalumar lambar maman Hanan domin kawar da ƙishiriwar raina da yake ƙawata mini kwaɗaituwa da son jin halin da take ciki. Shigowar ƙiran Salma ya dakatar dani
kafin na ɗauka wayar ta mutu bayan ta nuno mini gargaɗi na gama zuƙe cajina. Wuf na fice daga ɗakin na jawo ƙofar na fito bayan shima ƙofar gidan na danna masa makulli na faɗa gidan maman Anwar don ba zan iya zaman gidan ba.

Sallamar da na shiga da ita bisa harshena ta amsa, na zauna saman tabarmar da na tarar da ita zaune a kai kana na gaishe ta ta amsa tana ƙura mini idanuna haɗi da cewar"Na'ima yaushe kuka dawo gidan?".

"Ɗazu muka dawo".

Sai da ta musguta tana ba wa wata matashiyar budurwar da na gani a tsakar gidan umarnin kawo mini ruwa, na hutar da ita ta hanyar faɗin alhamdulillah. Sam na kasa nutsuwa da zaman gidan sai dai dole ce ta saka hakan, domin ba zan fara gangancin saɓan ƙafata na koma gida ba sai yaya Yusuf ya dawo zancen da ta ɗaura dashi suka katse mini hanzari daga saƙa da warwaran da zuciyata take ƙulla mini.
"Maman Hanan kuma ashe gidan su ta koma?, naje har sau biyu nayi mata ta'aziyya".

"E wallahi tana gidansu".

Riƙe haɓa tayi"Lamarin nan sam bai yi daɗi ba ko kaɗan, Allah dai ya kawo daidaituwa in da rabon akwai sauran zama a tsakanin su Allah ya kawo sanadin da zata koma ɗakinta, domin ko zuwana na ƙarshen nan ta furta min ba zata komo gidan Auwal ba ta gama zama dashi har abada gwara ta ƙare rayuwarta gaban iyayenta ko da kuwa babu sauran maza a duniya sai shi".
Tagwayen ajiyan numfahsi na fesa, ina ƙara lanƙwashe ƙafafuna wajen guda kafin nayi ƙarfin halin faɗin"Haka dai ta ce amma muna fatan gyaruwan lamarin tun ƙaddara ce ta riga fata duk babu wanda yayi tinanin faruwar hakan".

"Ai dama haka ne in Allah ya ƙaddaro abu babu mai canja faruwarsa, sai daga baya ayi ta tinane tinanen daman kaza aka yi da kaza bai faru ba, Allah dai kawai ya sa mu dace".

"Amin".

Muka haɗe baki tare da budurwan wajen faɗi, da hakan ya sanya ni na cira kaina na bita da kallo daga ita sai ɗaurin ƙirji ta zage ƙarfinta yana wanki da hasken fililla da ya haske filin tsakar gidan. Wani mamakin ya cika ni domin a yanda maman Hanan ta sanar dani ba ta da ƴa mace gabaɗaya ƴaƴanta uku ne duk maza, ban bari nayi nisa da tunanin ba domin bana cikin sukunin yin hakan. A anan nayi sallan isha'i kafin wani yaro ya shigo ya ce ana yaya Yusuf ya mini magana, sallama nayi wa maman Anwar na fice.

Ƙofar gidan na iske yaya Yusuf ya yi riƙo da ƙugunsa, a sanyaye na isa gare shi bakina ɗauke da siririyar sallama. Shima ciki ciki ya amsa sallamar tawan na zara ɗan makulli na buɗe gidan muka shiga kai tsaye muka wuce ɗakin. Ƙululu cikina ya bada sautin sakamakon tinanin da ya faɗo mini cikin kunyata tamkar faɗuwar aradu tinawan da nayi cewar banyi girki ba. Jin sautin muryar yaya Yusuf sun baƙunci ƙofofin kunnuwana ya sanya ni figigi na dawo daga wannan tinanin

"Zauna mana tinanin meye kike yi?".

Murmushin dole na ƙirƙiro kafin na ce"Girki zan ɗaura ne, tsoro ya hana ni zama cikin gidan ɗazu gashi wayata ta ɗauke babu caji shiyasa na shiga makwabta ban ƙira ka na sanar maka ba". Shima murmushin ya maido mini dashi haɗi da faɗin"kar ki damu, girki kuma sai dai in kina jin yunwa don ni bana sha'awar ma cin abincin".
Zama nayi kusa dashi ina sauƙe wani gwauruwar ajiyar numfashin da ta tokare mini maƙoshi, sai da na fuskanto shi sosai ina karantar yanayin fuskarsa da ya jinginar da kansa jikin kujerar zaman mutum biyu da yake zaune kai, ya lumshe idanunsa har wani ƴar rama ya yi cikin kwanaki bakwai ɗin nan. Tausasa amon muryata nayi cikin sanyi nake cewar"Haba mijina duk wannan damuwar ta mecece?, dubi yanda ka koma cikin ƙasa da kwanaki bakwai?, dan Allah ko dan lafiyarta ka sausata ma kanka wannan tinanin". Wasu mini idanunsa ya yi, na ɗage masa nawa guda ina faɗaɗa zancen nawan"E lafiyata duk abinda zai shafi lafiyarka ai tamkar nawa ya taɓa".
Caraf naji hannayensa cikin nawa kafin ya jawo ni na faɗa ƙirjinsa lamau na kwantar da kai daga ni har shi cikin mu babu wanda ya ce uffan, illar sauƙar numfashi da fitarwa da muke yi a tare.
Haka muka zauna har zuwa wasu mintoti, muka yi shirin kwanciya bayan na tirsasa masa zuƙar ruwan shayi mai kaurin da na haɗa masa. Sai da muka jira dawowar yaya Auwal na jiyo muryar Mahmud da nake kyautata zaton cewar tare suka taho da yaya Auwal, kenan shima nan zai dawo da zama?.

Dawowar yaya Yusuf daga rufe gidan da ya fita yi, ya sani kawar da zancen muka kwanta. Da ƙyar na iya tashi wayewar safiyar ranar sakamakon wani ciwon kai da na jiki da ya sauƙar mini da rashin kuzari a jikina ta yanda ko ƴatsar hannuna bana ƙaunar ɗagawa. Da taimakon yaya Yusuf nayi wanka nasha shayin da ya haɗa mini kana na kura magani. Dole na fito nayi dukkan aikin gida kamar yanda ya kallafa bisa kaina duk yanda yaya Yusuf yaso na koma nayi kwanciyata zai haɗa mana abin kari ƙiyawa nayi, domin ko ba komai yaya Auwal da Mahmud suna cikin gidan sai zuciyata take ayyano mini rashin dacewar haka su fito su iske shi yana aikace aikacen cikin gida.

A daddafe na kammala girka mana dafa dukan tafiyar hausa, yaya Yusuf na biye dani tamkar inuwa domin ranar ko islamiyyar safe bai je ba, haka nan na lura bashi da niyyar zuwa ta bokon duk kuwa saboda raguwar nan ya ɗauki hutu amma yau ne cikar wa'adin ƙarewar hutun kamar yanda ya furta mini. A haka na tusa abincin duk da bana jin ɗanɗanonsa bisa harshena sai don kasawa da tsarewar da yaya Yusuf ya yi mini akan lalle sai naci, sai hantsi ya fito suka fita tare dasu yaya Auwal izuwa gidan Anti Binta domin yin sallama da waɗanda suka zo ta'aziyyar dasu koma.
Ina kwance tunani barkatai suna ziyartar cunkushashshen curin ƙaramar ƙwaƙwalwatar dake cikin ƙoƙon kaina naji yo rurin da wayata da ban daɗe da kunna ta ba ta tsala alamar tana neman agaji. Mirginawa nayi kafin na jawo wayar ba tare da na duba mai ƙiran ba na ɗaga tare da karawa a kunnena.
Muryar Salma cikin kuka da suka yiwa kunnuwana dirar mikiya suka sanya baccin idona wartsakewa saf, na tashi zaune a ƙoƙarin furzo mata tambayoyin da suke cike da bakina na datse harshena.
Muryarta ta kuma dukan zuciyarta, cikin tsanata kukan da take yi ta furta"Na'ima gani yanzu a hanyar zuwa gid..".

Ba ta sama damar ƙarisawa ba sakamakon wani kukan da ya turniƙe ta, tamkar kazar da aka jefa da gishiri haka nan duk jikina yayi la'asar. Na shiga kokawa da numfashina da yake carkewa a iya ƙirjina kafin na sama zarafin faɗin"Lafiya Salma?, ke da waye zaku zo ɗin?, ina Abdallahn naji ki kina kuka?".

A jere na jefa mata dukkan tambayoyin lokaci guda, ba tare da samar mata da watar da zata amsa ta farkon ba balle na biyu.

"Dogon zance ne Na'ima, nayi ta ƙiran wayanki bakya ɗagawa tun kafin na taho yanzu dai zan sauƙa a gidanki".

Iya abinda kunnuwana suka jiyo mini bakinta ya furta kenan, kafin na daina jin komai sai faman faɗin"Hello hello hello Salma kina jina?". Na ke yi kafin daga bisani naji ta datse ƙiran, haka na dinga ƙira amma bata ɗagawa bugun ƙarshe da nayi nayi wayar a kashe. Tunin naji ƴaƴan hancin cikina sun murɗa, ƙirjina ya shiga lugudan dukan tara tara sau tara tamkar zai fito waje ya daka rawar disko. Dukkan raguwar kuzarin da yayi saura ga gangar jikina ya hau na nema nutsuwata na rasa, a haka har nayi sallan zuhr na haɗa wuta na tafasa mana doya fara nayi ƴar miyar tomatur da albasa marar wahala da ɗaukar lokaci, dai dai ina kashe garwashin wayata ta soma ruri zumbur na shige ɗaki na ɗauko ta, Yaya Yusuf ne na ɗaga ina saisaita nutsuwata.

"Qurratul aynun ya jikin nakin?".

"Da sauƙi sosai yaya".

"Alhamdulillah, dan Allah ki kula min da kanki kuma ki tabbatar kin ci abinci sannan kin sha magani, nima ba wani daɗewa zanyi ba zan dawo".
"To in sha Allah, Allah ya tsare mini kai cikin tsarewarsa ya kuma dawo mini da kai cikin aminci, ya kauda idon duk wata macen daga gare ka".

Na ƙare zancen ƙarshen ina sausauta muryata, ban yi zaton yaji ba sai ji nayi ya dara kana amsa mini cikin faɗin"Amin amin, kar ki damu domin ko sun kalla ma ni bazan zan suna yi ba duk inda nake ke kike mini gizo a idaniya".
Murmushi nayi ƙasa ƙasa kana muka yi sallama tare da datse ƙiran, alƙawarin da nayi wa yaya Yusuf akan zanci abinci shi ya sanya ni zubo doyar na tisa ta a gabana sam bana cin sha'awar cin komai.
Na ƙyar naci yanka uku ana huɗun, naji sallamar Salma sun ratsa masarrafan ji na, kafin na miƙe har ta faɗo ɗakin. Muƙut na haɗiye doyar ina jin tana sukan maƙoshina tamkar wacce ta haɗiyi ƙarangiya.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

__________________________________________


Page 2⃣4⃣

Fit na fice daga ainihin hayyacina, har mazari jikina yake yi nake duban ta duk ta rame ta lalace tamkar kazar mayu da wasu haƙwaran da suka yo gaba a bakinta yangau kamar wacce tayi karo da mota. Duk fuskarta ta kumbure idanunta sunyi luƙu luƙu, kamar zasu faɗo ƙas.

"Salma lafiyarki kuwa?, ke da waye kike tafe?, menene ya faru?. Ki sanar dani kin barni cikin duhu".

Ganin bata da niyyar amsa mini ko guda cikin jerin gwalon tambayoyin da na watsa mata, sai ma tsananta ƙafin sautin kukan natan da tayi da ya karaɗe dukkan kusurwan ɗakin bai ɗaya, kamo hannunta nayi na zaunar da ita kafin na fice a hanzarce na ɗebo mata ruwa na kawo mata da kaina na kafa mata a bakinta ta ɗan zuƙa kafin ta ture kofin tana janye bakinta.
Ajiye kofin nayi gefe guda ina mai ƙara fuskantar ta da kyau na ce"Yi maza Salma ki sanar dani, abinda ya faru wallahi zuciyata harbawa take da sauri sauri a dalilin saƙon tozali dake cikin wannan halin da idanuwana suka aika mata". Rinannun idanunta da tsabar kuka har wani ƙanƙancewa suka yi suka ƙara zurmawa ciki ta kafe ni dasu, kafin ta kuma tuntsirewa da wani sabon kukan tana faɗowa jikina. Ban iya lallashin ta ba domin nima hawayen nake shara sai da muka yi muka gajiya don kawunan mu kafin nayi ƙarfin halin ɗago ta daga jikinta tare da tallafo haɓarta na furta"Sanar dani menene, domin bana son ki ba wa zuciyata gaskata hashashenta na saƙa mini rabuwa kuka yi da Abdallah".

Sai da ta fesar da zazzafan numfashi ta bakinta da naji ɗuminsa bisa kuncina kana ta ce"Abdallah ne Na'ima, ya cuce ni ya zalunci ni ya bar min tabo cikin zuciyata wayyo Allahna ina zan nufa da wannan abun?".
Sosai ta ƙara firgitani gami da ruɗewa na cakumo ta na riƙe gam"Meye Abdallahn yayi miki?, yana ina shi Abdallahn?, sannan menene dalilin wannan zuwan nakin?".


"Nima ban san inda yake ba, ban sani ba gidan iyayensa ya kai ni tahuwar nan ma da nayi basu sani ba domin babu iznin su".

"Ina ya tafi?, menene dalilin kai ki gidan iyayensa bayan naji an ce ya yi ginin yayin bikinmu?".
Duk na gama hautsinewa , ina ganin tamkar bakinta ba zai yi gaggawan samar mini da amsar tambayoyin da suke bakina ba cikin sauri, ji nake kamar ta buɗe mini zuciyarta na hango komai. Sai da ta zuƙe majinar kukan da suka taho mata kana ta ce dani"Haka ne yayi gini sai dai gidan gadonsu ne ya gina shi da ƴan-uwansa aka wara masa nashi ɓangaren, wanda muka sauƙa a ciki da muka koma garin. Kwanan mu goma da komawa na fara fahimtar sauye-sauye daga Abdallah ko baccin kirki baya samu yayi domin duk duhun dare na farka zan iske shi zaune ya zagba tagumi iwa wanda aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da uba, na tambaye shi yafi sau shurin masaƙi amma a duk lokacin da na jefa masa tambayar ko na nuna masa damuwata game da hakan, kalmar babu komai ita ce take fitowa daga bakinsa".
Sai da ta numfasa kana ta ɗaura da"Haka muka cigaba da zama wataran ya dawo ba tare da motarsa ba, da na tambaye shi dalili sai ya kada baki ya ce dani ya sayar da ita buƙata ce ta taso masa ta ujila gaba baya ya umarci ni akan na shirya zamu je gaida iyayensa sai da muka je ya ce zan zauna nayi kwan biyu da yamma ya haɗo mini kayana ya kawo mini. Kwanana biyu tare da iyayensa wata yammaci ya turo mini saƙon cikin waya".

Daga hakan ta dakata, sai da taci kuka son rayinta hakan ta ɗaura daga inda ta dakarata"Na'ima kar kiyi mamakin abinda za ki ji bakina ya furta domin babu kuskure cikinsa. Duk abubuwan da Abdallah yayi yayin bikinmu duk aro kuɗi yayi kama daga kan lefe da ma komai gabaɗaya. Cikin saƙon yake shaida mini cewar wanda ya ranci kuɗi wanda zai iya kaiwa kimanin miliyan goma sun matsa masa, har suna yi masa barazanar maka shi a kuto inda bai mayar musu da kuɗin su ba, dalilin hakan ya sanya shi sayar da motarsa gidanmu ma ya sayar da nashi ɓangaren. Ba zai iya zama ba don haka shi ya shiga duniya na cigaba da zama da iyayensa har izuwa lokacin da Allah zai nufe shi da samu wannan kuɗaɗen ya dawo gida. Wai alƙawari ya ɗaukarwa kansa cewar komai rintsi komai wuya sai ya aure ni kuma ya cika burinsa tunda na zamto matarsa".
Ƙara fashewa tayi da wani azababben kukan da suka ni na runtse idanuna da suka yi da suka yi mini nauyin gaske. Da ƙyar na iya haɗiye wani miyau mai ɗan karen ɗacin da naci ɗacin ya wanzu a dukkan kusurwan bakina. Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wasu mintotin da ba zasu gaza goma ba kafin na iya cira kaina haɗi da cewar"Menene dalilinki to na dawowa gida?, kin sanar da iyayensa hakan?".

"Ba zan iya wannan zaman ba, shiyasa zuciyata ta bani shawaran zuwa na sanar da nawa iyayen. Iyayensa kuma duk sun sani domin wani lokacin ma su suke tausa na a duk lokacin da na yunƙuro da nufin zuwa gida ko tahowata yanzu ma basu da masaniya domin zagawa nayi kawai na zarce tasha na hawo mota da kuɗin wayata da na sayar cikin tashar".

"Tirƙashi wannan shine ana wata ga wata!. Lalle Abdallah ya ratsa yardar da yaƙinin da nake dashi a kansa, meyasa bai yi haƙuri da abinda Allah ya wadata shi dashi ba?, ya aure ki a hakan meyasa yazo miki ta wannan fuskar?".
Sai da ta sanya hannayenta ta tare ruwar ƙwallar da suka wadaci kurmin idaniyata kana ta sama zarafin cewa dani"Tambayoyin da nima kaina na gaza cimmawa kenan, meyasa Abdallah zai min hakan shin sanda zuciyarsa take kimtsa masa wannan lamarin meyasa bata yi min adalci ba?. Ta hanyar tinanin halin da zan iya faɗawa anya Na'ima yasan yanda nake son shi kuwa?, kayan lefena duk iyayensa sun sayar dasu a cewar su zasu rage bashi da ya ciwo haka nan ma kayan ɗakina duk sun sayar dasu su riƙe kuɗin, ban san meyasa ba ko Ummata na kasa sanar da ita sau da yawa nasha ƙiranta a waya da nufin sanar da ita komai sai naji tamkar an riƙe min maƙoshi. Ke ma nasha ƙiran wayarki bakya amsawa daga baya kuma a kashe, ke kaɗai zuciyata ta nutsu da na tunkare ki tare da neman shawararki tun gabannin tahowata Na'ima wallahi ina cikin matuƙar tashin hankalin da bansan yanda zan furta shi da kalmomin da bakin kan iya furtawa ba, meyasa Abdallah zai yi min haka meyasa zai tafi ya barni ni ba aurarriya ba ni ba sakakkiya ba".

Jinjina kaina kawai naji domin ji nayi na rasa abin faɗi kan lamarin saboda ya girmewa kwanyata, tsoro da fargaba da tausayin al'ummar yankina da suka ɗauki aure tamkar wasar yara suka ƙara shige mini can ƙololuwar raina. Lallashinta na fara yi har dai na yi nasara ta tsagaita kukan da take yi tamkar ranta zai fita, hakan yayi dai dai da ƙiran sallan asr na zuba mata ruwa a buta ta fito tayi alwala sannan nima nayi, koda ta idda sallar raguwar doyan nan na ɗebo mata ta nuna mini sam ba zata iya cin komai ba, da ƙyar da suɗin goshi na samu taci yanka biyu ta kwanta saboda zazzaɓin ta sanar dani ya rufe ta.
Zama nayi jugum ina nazarce nazarce cikin raina ni kaɗai, na saƙa wannan na ware wannan kafin na kai ga sauƙe wata ƙatuwar ajiyar zuciya.
Wai meye al'ummata suka ɗauki aure ne?, meye suka me da ita wasar yara koko karkatacciyar bishiya mai daɗin hawa?, da saka hau ta a sanda kaso kuma ka sulo izuwa ƙasa yayin da kayi niyya. Anya maza sun san ainihin manufar addini da ya wajabta aure ga dukkan mai hankali matuƙar yana da hali domin kaucewa faɗawa haɗarin zina?, Da yawan samari gani suke su sauƙe sha'awarsu tare da matayensu da addini ta halalta musu shine kawai ma'anar aure, auren kawai ake yi kara zube tare da haifan ƴaƴan da za'a kasa ɗaukar nauyinsu balle har a gina su bisa kyakykyawan tubalin tarbiyyar da zasu zamto ababen alfahari tsakanin al'umma. Su waye suke da haƙƙin gyara wannan ɓarnar da ta zamto tamkar da ta faro daga teku maganinta Allah, da take ƙoƙarin cinye MATAN AREWA domin ruwan yazo musu har wuya suna linƙaya a cikin sa. Matan ne ko matan ko kuma iyayen koko malamai suke da haƙƙin kawo gyaran game da wannan lamarin?.

Zancen zucin kenan da nayi nisan kiwo cikinsa, har kunnuwana suka kumurce daga jiyo sallamar yaya Yusuf. Sai da Salma ta taɓo ni na dawo a firgice.
"Ana sallama kamar malam Yusuf ne ko?".

"E shine".
Na faɗa ina miƙewa na fice daga ɗakin, na iske shi a falo sannu da zuwa nayi masa ya amsa mini kamar kullum fuskarsa yalwace da wannan murmushin da ya saba shigo mini da ita cikin gida yana tambayata yaya jikin nawan?.
Da kalmar "Alhamdulillahi" Na amsa masa ina miƙewa naje na kawo masa ruwa na zuba masa tare da miƙa masa ya karɓa sai da ya kurɓa ɗaya ya ce"Naga kaman gidan da baƙuwa shiyasa na dakata daga nan".
Sai da nayi nisa kana na ce"E Salma ce tana ciki".

"Ah Lalle kice mutanen kugu ne yau a gidan namun, tare suka zo da maigidan natan kenan?". Sauƙe numfashi da na sama damar faɗin"A'a ita kaɗai tazo".
Ban sani ba ko yanayin da nayo maganar ce ta sanya shi saurin jefo mini tambayar"To lafiya kuwa, naga kema duk yanayinki ya sauya?".

Ban ɓoye masa komai ba duk na zayyanu masa, domin ko bai tambaya ba nima ina da tawa niyyar faɗa mishi. Musgutawa yayi yan haɗe hannayensa waje guda kana ya ce"Tabbas Abdallah bai kyauta mata ba, kuma tayi kyan kai da ta garzayo domin sanar da iyayenta halin da ake ciki, domin shi ice tun yana ɗanye ake lanƙwasha shi idan ya bushe sai dai ya karye, zan fita masallaci yanzu idan na dawo ma ƙarisa zancen daman nima akwai zancen yaya Auwal da maman Hanan da nake mu tattauna a kai".
Fatan

Please Login or Register in order to submit comment