Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda zai hana sa fita yaje shi. Ya daina yarda dani na lura shima wani kallo yake min na rashin yarda akan Husna yana tinanin kamar zan cutar da ita.

Ya daina sauran damuwata ya daina jin matsalata ya daina zama muyi hira dashi, ya daina nuna mini kulawa. Ya daina bani lokacinsa ya daina sauƙe haƙƙina dake kansa ya daina kula ni, ya daina zama inuwa ɗaya dani inda ina falo to yana ɗaki in ko ina ɗaki yana falo tare da Husna domin yanzu ita ya ba wa matsayina na matarsa, da ita yake hira da ita yake dariya da ita yake nishaɗi.

Ban san meyasa ba sam na gaza sanar da kowa, ko nayi yunƙuri sanar da Ummata sai naji tamkar an ɗaure mini maƙoshi ala dole na canja ma'udu'in maganar in ba haka ba kuwa na dunga kame kame kenan. A haka har muka gama frist term nayo ta biyu a ajinmu class rep ɗin mu yazo na ɗaya, Maryam da Hafsa duk suma suna cikin goman farko. Har muka gama sss one babu abunda ya sauya zani wanda a lokacin aurenmu shekara ɗaya da watannin huɗu.

Abasiya ta haihu ba rai, shima bai bar ni naje mata ko barka ba. Naci kuka har na godewa rabbi sai ƙiran yaya Majid nayi nayi masa abinda ban taya yi ba a kaf rayuwata watau ƙarya. Na ce masa bani da lafiya ne ba zan sama zuwa ba. Bilkisu ma tayi ɓari da tayi jinya kamar ba zata rayu ba da ƙyar da suɗin goshi ya barni naje naje duba su gabaɗaya.

Kowa yayi mamakin baƙi da ramar da nayi abun ba daɗin gani da ido balle suffantawa da laffuzan baki. Kawar da maganar nayi da cewar makaranta ce duk ta saka haka. Duk tambayar da hajiya Babba ta jani sashinta tayi mini har da haɗa ni da girman Allah naji tsoronsa na faɗa mata abinda yake damuwa, amma na kasa sanar da ita na ce ba komai don dole ta ƙyale ni da addu'ar Allah yasa ba komai ɗin kamar yanda na ce.

Ummata kawai na faɗawa, jikina har tsuma yake yi tsabar kukan da nake yi. Ita ma idanunta suka kaɗa suka yi jajir ta tsare ni da tambayar menene dalilin da tun farko ban zo na sanar dasu.

"Umma wallahi na kasa sanar da kowa, da farko nayi tinanin komai zai wuce tunda bai taɓa yi mini irin hakan sai daga ƙarshe naga abin yafi ƙarfi na".

Na furta ina ƙara tuntsire da wani matsanancin kuka, rarrashina tayi ta sanar dasu Abba suka ƙira ni domin ji ta bakina. Sannan aka ƙira yaya Yusuf sosai gabana ya faɗi jin sallamar da ya shigo da ita don tsoro babu abinda nake tsoro kamar shi hakan nan babu abinda nake fargaban ji kamar muryarsa. A ladabce ya gaida iyayena kafin Baba ya irge masa duka abinda na sanar dasu, wani mamaki ya mamaye ni da ya hana ni kwakwaran motsi. Domin tuburan nunawa yayi babu wata matsala a tsakaninmu har da rantsuwar sa ganin hakan ya sanya su Abba yi mini nasiha sosai wai sheɗan ne ke son shiga tsakanin mu. Ummata ce kawai ta fahimci raɗaɗin zuciyata ta dunga tausa ta bayan mun komo ɗaka ta kuma bani wasu addu'o'i ta ce nayi riƙo dasu.

Tunda muka koma gida yake sauƙe mini kwando kwandon masifar wai na kai ƙarar sa gidan mu, abinda ya kuma yi mini ciwo har Anty Binta ya ƙira ya zayyana ta, ta cikn wayar ta hau sauƙe mini nata har da faɗin wai inna gaji da zama dashi na fito na faɗa kowa ya kama gabansa. Haƙuri na bashi maganar ta mutu.


Naci kuka har sai da naji kaina yana juyawa kafin na tsagaita ba don naji sauƙin sanyi daga wutar dake tashi a ƙasan raina ba, sai don lafiya saboda sosai kaina yake sarawa tamkar zai rabe gida biyu. Alwala nayi nazo na data salla raka'a biyu ta nafila sannan na fara yin addu'o'in da Ummata ta bani tun daga ranar.

Ina zaune jangwaf a falo ga tvn dake aiki da na tsurawa ido ba ko kiftawa sai dai a zahiri hankalina ba gashi yake ba. Tunin nayi niso cikin duniyar tinanin da na zurfa cikinsa Husna ta zaune a gefe tana ƴar waƙar Ado gwanja na cas, dai dai sanda ta iso baitin nan da yake faɗin"Sunyi abin ya sha musu kai cas".

Na ɗago idona sakamakon sallamar yaya Yusuf da suka ratso kunnuwana, sannu da zuwa nayi masa da ya yi mini banza. Yan washe fararen haƙwaransa ga Husna da take masa sannu da dawowan ita ma kusa da ita ya zauna ni kuwa tamkar bai san da wanzuwa na a falon ba. Suna ta taɗin na wasu mutanen daban da ban ma san su ba sai dai nafi tinanin ko dangin su ne na nisa da ban san su ba.

Ganin da gaske bashi da niyyar kulawa ni balle cewa dani wani abun ya sani faɗin"A kawo maka abinci?".

"Naci abinci".

Cikin sauri Husna take faɗin"kawu bari na daba maka wata shinkafan da na gani jiya a talabijin ana girkawa". Da mamakina naji ya amsa bata da"To shalelen kawu ina fatan dai ba zai ɗau lokaci ba?, don na gaji kwanciya nafi buƙatar nayi yanzu haka".
Kanta ta ɗaga masa alamar ba zai ɗau lokaci, ta miƙe ta fice izuwa madafan wani kallo na bi shi dashi raina a cunkushe kamar ba shi bane yanzu nayi masa tayin abinci ya ce ya ƙoshi ba. Idanuna har sun rufe tsabar baƙin ciki nake faɗin"Amma yanzu na maka tayin abinci kake ka ƙoshi". Ba tare da ya kalle ni ba ya furto mini kalamar da suka sanya idanuna wartsakewa tas.

"E nakin ne kawai bana buƙatar ci don ba wani yarda dake nayi ba yanzu balle kuma abinda kika girka".

Hawayen idona suka zuba a hankali jikina ya ɗauki rawa, ban iya cewa dashi komai ba illa kalmar hasbunallahu wa ni'imal wakin da nake maimaitawa a zuciyana. Na ja sanƙararrun ƙafafuna na wuce duk yanda naso zubda ƙwalla hakan ya gagare ni, ina jin ɓuruntun Husna a kitchen ɗina amma bani da ikon dakatar da ita, ina jin hirar da suke yi ƙasa ƙasa daga falon har izuwa sanda bacci ya sace ni. Wayewar garin ranar na tashi da matsanancin ciwon kai komai caka caka a kitchen ɗin na tarar dashi wani ɓacin ran ya kuma zarge mini rai, na haɗiye da ƙyar duk don son a zauna lafiya. Yanda nake jin jikina bana jin ko makaranta zan iya fita don haka ina gama aikin na kwanta ya yi shirinsa zai fice kamar bai ganni ba, nima bance dashi komai ba kawai na bishi da ido har ya fice ya dawo da baya da faɗin"Ba za ki yi shirin makarantar bane?".

"Bani da lafiya".

Na faɗa hawaye suna ciko mini idaniya, tsaki ya saka ya yi ficewarsa sanda zai dawo da dare ya taho mini da paracetamol guda huɗu ya jefa mini tsabar takaici ya hana ni ko kallon maganin balle shan sa, washe gari yaya Auwal ya yi mini sallamar zai tafi kano saro wasu kayan, haka na shafe kwana goma cikin jinya a rana na sha ɗaya da hantsi Abasiyya, Balkisu da Salma suka zo mini murna kamar na kwarara ruwa a ƙasa nasha don na daɗe ban ga wani nawa ba.

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

__________________________________

Page 3⃣1⃣


Ruwa na kawo musu na dire shi a gaban su kafin na fara tsiyaya musu a ƙanana kufunan da haɗo dashi, ina kallo Balkisu cikin zolaya nake faɗin"gawa taƙi rami". Suka bushe da dariya kusan a tare kafin suka ɗauki ruwa suka ɗan sha suka ajiye.

"Ya gidan shuru ina facalan nakin fa Na'ima?".

Na ɗan yi murmushi ina kallon Abasiyya da tayi maganar kafin na ce"Ai maman Hanan ta yi kusan wata shida bata nan, tana gidan su tun bayan rasuwar Hanan".

Cike da damuwa Salma take faɗin"Allah sarki Allah ya jiƙanta lokacin naji mutuwar yarinyar nan wallahi don rashin imani irin na al'umma ƙaramar yarinyar nan da bata komai a ketawa haddi".

Na sauƙe ajiyan zuciya a wahale, ina ganin hoton Hanan ɗin a cikin idona furcin Abasiyya ya katse ni"To ita kuma meye dalilin tafiyar banda abin ta".

"Ke Abasiyya wallahi ko ni ce ban ga abinda zai hana ni tafiya ba, haba ai shima bai kyauta ba".

Salma ta kuma faɗi a karo na biyu, taɓe baki Abasiyya tayi haɗi da faɗin"Cabɗi wallahi in ni ce ba inda zani ina nan daram mai jego ta sama katifa, Na'imar ma abin tuhuma ce anya ba sa hannunki a tafiyarta".

Wani kallo na wurga mata idanuna suna haɗawa tare da canja launi cikin harɗewan harshe nake faɗin"kamar yaya da sa hannuna a tafiyarta?, meye ta tare mini a cikin gidan da zan kore ta?, to ma na kore ta a wani dalilin bayan ba zamana take yi ba nima ba zaman ta nake yi ba, kowa a ƙarƙashin mijinsa yake".

"Dan Allah Abasiyya ki daina irin wannan maganar, wai har yanzu an gaya miki ana irin wannan kishin da iyayenmu suka yi a da ne. Wallahi yanzu duk wacce kika gani cikin ɗakin mijinta to matsalarta ma kaɗai ya ishe ta ba sai ta tsaya sanya ido a wata ba wai ita facala ai ko kishiya ce ni wallahi bakya gabana balle kuma matsalarki".

Furcin Balkisu kenan ƙwalla suna ciko mata kurmin idaniya, nayi mata kallon tsanaki kafin na ce"maganarki tana kan hanya Balkisu don ko nima nan da tawa matsalar da ita kaɗai ta ishe ni ba sai na tsaya ƙarawa kaina matsalolin wasu ba wallahi".

"Na'ima ke kam ai ko ba ki fito kin faɗa ba wallahi ko makaho ya shafa fuskarki yasan kina cikin damuwa, sanda kika zo gida fa duba su Abasiyya bayan tafiyar ba ki ga yanda aka kafa gandarki ba tana ta yi dake wai kin rame kinyi baƙi kamar mai cutar sida".

Duk da furcin Salman sun taɓa mini zuciya amma ƙarfin hali kawai nayi na sarka mata murmushi ina jin wani ciwo a raina, shuru ya ɗan ratsa ɗakin na wucen gadi kafin Balkisu ta katse shurun ta hanyar faɗin" ni wallahi har fargaban komawa gidan Aminu nake ji, da ina da yanda zan yi wallahi ba zan koma ba amma babu yanda na iya ko na ce zaman gidanmu ma zanyi baƙin ciki ne zai kashe ni a banza. Gwara na koma na mutu a ɗaki ko banzan nasan a dalilin bautar Allah da raya sunan ma'aiki na rasa raina".

Ta ƙare sakin hawayen da suka ciko idonta, duk muka riɗime da ganin irin kukan da take yi muna rige rigen tambayarta abinda ke damunta. Bata tanka mana sai da ta ci kukan mai isharta kafin ta soma faɗin" Ashe daman haka aure yake shiyasa tun kafin a ɗaura iyayenmu suka nanata mana kalmar nan ta haƙuri, tun bayan wata uku da aurenmu da Aminu na faɗa shan ruwan baƙin cikin da ya nakasa min dukkan sassan jikina. Nayi zato kamar yanda nake gani a fina finai da nake kuma ji a littattafan hausa ana nuna irin farin ciki da murnar da duk ma'aurata suke yi ya yin da Allah a azurta su da samun ƙaru. Ashe duk abin ba haka bane domin ni a gare ni lamarin bai zo min da sauƙi kamar yanda nake tsammani ba. Naga ɓacin rai a tattare da Aminu ya yin da nake sanar dashi ina ɗauke da juna biyu bai nuna farin ciki ba wanda koda da cikin na shigo gidansa kwatankwancin takaicin da zai yi kenan. Ya buaci da na amince a zubar da cikin a cewarsa bai shirya kula da ƴaƴa ba yanzu yafi son sai munci amarcin mu sosai kafin mu fara haihuwa, duk yanda naso nusar dashi illar haka da son fahimtar dashi hakan tamkar butulwa Allah zamu yi bisa kyautar da ya bamu amma kamar wanda aka liƙawa gayan tuwo a idanu da kunnuwana, Ya saka mini wasu ƙwayoyi a cikin shayi ba tare da sani na ba nasha jini ya ɓalle min, kafin muje asibiti jini cikin ya fita. Ya yi ta lallashina tare da roƙo na akan har na faɗawa kuwa hatta Ummata".

Daga haka ta tsagaita saboda kukan ya fara cin ƙarfinta, Salma ta yi saurin miƙo mata kofin ruwan tasha tana sauƙe ajiyar zuciya kafin ta ɗaura"Na amince ban sanarwa kowa ba shi ya yi jinyata har na warke, na banta da komai bayan wani lokaci wani cikin ya ƙara bayyana a cikina. Banyi niyyar sanar dashi ba saboda gudun kar ya raba ni dashi ta ƙarfin tsiya kamar yanda ya faru a farko. Amma sai da hakan ya bayyana saboda laulayin gaske da cikin yazo min dashi koda ya fahimta ya nuna min ƙudurinsa nazo zubda shi naƙi amincewa. Tun daga lokacin ya daina kula ni ya kuma fara min horo da yunwa baya bari na fita haka nan baya barin kowa yazo inda nake, ya kuma ƙwace wayata balle na ƙira gida a kawo min agaji, yunwa da rashin kulawa da kuma tashin kwanciyar hankali ya sanya cikin faɗuwa da kansa sai da ya tabbatar da cikin ya fita ya kwashe ni izuwa asibit tare da ƙiran gidan ya shaida musu cewar nayi ɓari, koa likitoti suka ce akwai yunwa a tare ni shafe idonsa ya yi da toka ba kunya yake faɗin wai tunda na sama cikin bana son cikin abinci sai ya yi dani kafin nasha ruwan shayi".


Sosai dukkanin mu jikkunan mu suka yi sanyi laƙwas, hawaye suka fareti saman fuskana na ce"Aminun?".

Kafin ta sama damar amsa mini Abasiyya tayi carab ta karɓe zancen da faɗin"innalillahi wa inna ilaihir raji'un caɗjijam!, lalle Aminu shi da nake yiwa kallon salihi. Amma wallahi tun farko ma ke kika bashi fuska ai ni ko kashe ni zaka yi wallahi tallahi sai na sanar da iyayena akan meye wannan baƙin muguntan hakan. Wannan ai rashin tausayi da rashin sanin darajan mace ne don Allah ma ya sani ba za'a yi min irin wannan cin kashin na zauna na zuba ido ba, in ko ka ce baka shirya kulawa da ƴaƴa ba to duk nacinka sai dai mu raba shimfiɗa ina dalili. Ni sanda nayi ɓari irin tashin hankalin da Sagir ya shiga har yaso ya fini shiga ruɗu balle kuma da kansa ya yi ƙoƙarin kawar da cikin".

Kallo ɗaya na yiwa Abasiyya don nasan maganganunta na ƙarshe zance ne kawai, don ta nuna kamar tafi kowa jin daɗin gidan miji a tsakanin mu. Tagwayen ajiyan zuciya na sauƙe kafin na furta"Balkisu tabbas kema kina ganin rayuwa, wannan shine haƙurin da ake nusar damu shi duk wacce kika gani a ɗakin aure to da nata matsalar domin shi mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo. Hakan ko wani aure da nashi ƙalubale sai dai na wani yafi na wani nima nan cikin matsala nake domin sam bana jin daɗin zaman gidan nan yaya Yusuf ya canja tamkar bashi ba". Na ƙare zancen da guntun ƙwalla a idona.

"Duk ku kukan daɗi kuke yi, tunda ko ba komai kunsa kuna ganin mijin kusa da ku saɓanin ni da ban san makomar nawa auren ba".

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! tabbas MATAN AREWA suna ganin rayuwa labarin Balkisu ya taɓa zuciyata aihun wai kayi auren amma ka ce baka shirya kula da yara ba?, har ka iya yin sanadin rayuwar kyautar yaƴan da Allah ya baka tun suna ciki, wayan abinda gobe zata haifar wataƙil wanda ka salwantar ɗin su kaɗai Allah ya rubuta maka zaka samu, haihuwar da ba kowa Allah yake yiwa kyautar su ba wasu suna can suna neman haihuwar tsawon shekaru amma Allah bai nufa ba kai kuma da aka baka har ka butulce masa ta hanyar nuna masa baka buƙata a lokacin da ya baka. Mun tattauna sosai a tsakanin mu kafin na miƙe da nufin ɗaura mana girki sai a sannan na lura da Husna bata cikin gidan ban ɗagawa kaina hankali ba don nasan tana fita makwabta daman, Salma ta fito na bata albasa da attaruhu ta jajjaga mana shinfaka da wake da miya na mana, sai da muka yi sallan zuhr kana na zubo mana a tire muka ci muna ta faɗo matsalolin da suke ci mana tuwo a ƙwarya sai da suka yi sallan asr sannan suka fara haramar tafiya na sanyo hijabina zan raka su suka yi kiciɓus da Husna wujiga wujiga da alamar ta kwaso uwar yunwa tamkar bata ga mutane ba a wajen tayi wucewar ciki.

Abasiyya ta bita da kallo tana riƙe haɓa haɗi da faɗin"Too Na'ima ita kuma wannan fa?".

"Ƴar yayar su ce take taya ni zama".

Na faɗa cikin yaƙe tsaki ta tsirka kafin ta ce"shine ta gan mu zata wuce tana yatsina fuska kamar taga gashi?, ni wallahi in nice ba zan ɗauki wannan rainin wayon ba yayar miji ki dunga zuba mana isa da mallaka ko uwarsa iyakaci. Nifa ko sanda mahaifiyar Sagir ta tsiri aikin sanya mana ido tsefe idona nayi na mata rashin mutumci wai sai dai ya zaɓa ko ni ko ita ko ta tsine masa yo inta tsine masan ma meye asarana, ai ita zata yi asara".

Murmushi na saka cike da mamaki bunƙasar rashin ta idon Abasiyya kafin ta furta"A'a ke dai in ta tsine masan ai kema abin sai ya shafe ki don zaman gidan ma ba zai miki daɗi ba".

"Gaya mata dai ni wallahi zaman nan da muka yi muka tattauna har naji sanyi a raina. Ina ma MATAN AREWA zasu hankalta su daina zaman daban nan su haɗu suna tattauna damuwarsu yafi wannan zaman gulma da tsegumin nan da suke yi".

Murmushi nayi muka tafa da Salma kafin na ce"gaskiya ne kam amma damuwar da baau wuce zarafi ba wanda zaka iya sanar da na kusa da kai, kar kisa MATAN AREWA su ji wannan zancen nakin su fara baje sirrikan gidan aurensu a daba".

Duk dariya muka saka na raka su har bakin titi sannan na dawo cike da kewar su, Abasiyya da Balkisu duk gobe zasu koma gidajensu.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

___________________________________

Page 3⃣2⃣

Koda na dawo na iske Husna zaune a tsakar gidan ta baje kan tabarma tana harare harare, ban bi ta kanta ba nayi wucewa ta ɗaki na cire hijabina sannan na tattare inda muka ɓata dasu Abasiyya na fito na haɗa wanke wanke nayi na share filin tsakar gidan kana na shiga wanka sai da na ɗauro alawa kana na fito saboda sallan magrib da ta gabato. Sai da nayi sallan na jawo wayata tare da danna lambobin cin bashin layin mtn na ci bashin naira ɗari na ƙira Balkisu ina musu ban gajiya tare da fatan sun isa gida lafiya mun taɓa hira sosai har sai da naji an fara mini gargaɗin kuɗina ya kusa ƙarewa sannan na katse ƙiran.

Ciwon kai ya rufe ni nan kan sallayan na kwanta riƙe da goshina, da nake jin kaina yana sara mini tamkar zai tsage izuwa gida biyu. Bansan sanda bacci ya sace ni ba sai jin muryar yaya Yusuf nayi a tsakiyar kaina yana ƙwala mini ƙiran mafarauta, figigi na tashi zaune ina faɗin"wash". Saboda sarawan da kaina ya yi mini a karo na barkatai.

"Baccin me kike haka?, kin bar yarinyar da yunwa ko girki ba ki yi ba".

A zafafe ya yi maganar tamkar zai rufe ni da duka dishi dishi idanuna suke hango mini shi yana tsaye a kaina cikin ƙarfin hali na furta"amma tun kafin ka fita da safe na shaida maka bani da lafiya ko?".

"Ƙarya ne domin sanda ƴan uwanta suka zo, zagewa tayi tayi musu girki".

Naji muryan Husna ta katse ni wani kallo na fita dashi duk da idanuna basa gano mini ita da kyau ya juya ya kalle ta"su waye suka zo?".

"Ban san su ba amma dai ƴan uwanta ne, naji ta ƙira ɗayan da sunan Balkisu har waje tayi musu rakiya".

Ta amsa masa cike da tsiwa zan yi magana ya tari numfashina da cewar"shine za ki fita ba tare da iznina ba?, ko kin manta duk takun da kika yi mala'iku suna rubuta miki zunubi ne Na'ima?".

Take naji wani kuzarin da ban san ina dashi ba a wannan lokacin ya rufe ni, na miƙe cikin ƙololuwar ɓacin ran da bana ganin komai a idanuna sai gilmawan baƙin duhu da wani irin sauri nake furta"na raka su Yusuf na raka su, ince matsayin su Abasiyya ne baka sani ba a waje na ko?. To har yaushe na sanya ka a idona da zan nemi izninka yaushe kake da lokacin da zaka saurare ni balle mu fahimci ju...".

Ban ƙarisa naji ya ɗauke da wani gigitaccen marin da ya bata sautin tas, na dafe kuncina cikin zubda ƙwalla idanuna suka wartsake ina kallonsa tar na ƙara taku uku nazo dab dashi na ɗaga kaina ina jefa ƙwayoyin idona cikin nasa haɗi da faɗin"ni ka mara Yusuf?, ni ka mara ba komai na gode".

Ina gama faɗin haka na wuce ɗaki ina danne kukan dake shirin kufce mini, ina shiga na danna makulli na faɗa kan gado ina sakin wani kuka mai cin rai, ban san ya ya suka ƙare ba ni dai na rufe ɗakina don bana buƙatar ganin fuskokin su naci kuka har na godewa rabbana.

Washe gari haka na kuma tashi da wani matsanancin ciwon kai, dole na shirya na tafi makaranta don zaman gidan ma ba daɗi yake mini ba, na ɗan ji sanyi a raina ina ji tamkar nayi tsuntsuwa na wuce wani wajen kar na koma gidan.

Muna darasin ƙarshen na fita da saurin saboda aman da yake taso mini, sosai nake kwaranyar da aman tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina, Hafsat da Maryam da suka biyo baya na suka rufu a kaina suna ta jere mini sannu wani na bin wani, da taimakon su na wanke fuskana na koma ajin na kwanta. Ko da aka tashi su suka ɗauka mini jakata har izuwa baƙin ƙofar ofishin yaya Yusuf. Wani irin jiri suna kwasa ta na shiga ofishin turus na tsaya ƙafafuna suna rawa cike da son tabbatar da abinda idanuna suke hango mini.

Yaya Yusuf da idanuna suka gano mini da mace zaune a gabansa sun zubawa juna ido. Da alama sunyi nisa cikin yanayin da suke da har ya mankantar dasu shigowa ta ofishin.

Ƙarar zubewan da nayi akan gwiwoyina wataƙil shi ya jawo hankalunan su izuwa gare ni, kafin ya taso da sauri ya nufo ni da faɗin"ke Na'ima lafiyarki?".

Ban iya cewa dashi komai domin Allah ya sani ko ƙaunar kallonsa bana son yi a wannan lokacin balle muryarsa, cikin ƙarfin hali na cije lebbena na miƙe da ƙyar ina jin wani ƙarƙafan jiri yana walagigi da ni ficewa nayi daga ofishin ina haɗa hanya kamar ƴar maye na fito har bakin gate. Lu nayi baya zan faɗi naji ni faɗa cikin mutum saɓanin zarcewa ƙasa da nayi tinani.

"Anty Na'ima lafiya kuwa?, ina malam Yusuf ɗin baku tafi ba?".

Sama sama nake jin muryar Hafsat cikin kunnuwana, na damƙe hannunta gam cikin nawa da ƙyar na furta"sani a abin hawa Hafsat gida nake son zuwa".

"Ina malam Yusuf ɗin?".

Ban kula ba illa riƙe kaina da nayi da hannu bibiyu, a adaidatan su suka kai ni gidan da taimakon kwatancen da nayi musu suka sauƙe ni ko godiya na kasa mata saboda nauyin da bakina ya yi. Da ƙyar naja ƙafafuna na shiga ɗaki tsabar tashin hankalin da nake a ciki na kasa ma kukan a bayyane sai na zuci nake yi.

Har aka yi ƙiran sallan asr na kasa motsawa banji motsin Husna ba ban damu ba balle na ƙarawa kaina wani damuwa akan wanda nake cikinsa a yanzu don ba sabon lamari bane daman ta saba ficewarta sai sanda tayi niyya ta waigo gidan da ta cika cikinta zata ƙara ficewa.

Ganin yamma tana kawo kai ya sani jan jikina da rarrafe na shiga banɗakin dake cikin ɗakin nayo alwala ban yi yunƙuri watsa ruwa a jikina ba don yanda naji sanyin ruwan ya ratsa ni har cikin kwanyata. A zaune nayi sallan asr na zauna har aka yi magrib nayi sai a lokacin naji sallamar Husna tana ta ɓuruntu a kitchen. Isha'i ma a zaune

Please Login or Register in order to submit comment