Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasu tsayayyun dangin a yanzu na rasa kowa nawa a rikicin ta'addanci boko haram".

Sune zantukan da suka sauƙa a dai dai ƙofofin kunnuwana, na kuwa baza kunne cike da son sauraran ragowar zancen, Umma ce ta ɗaura da cewar"Maman Walida ko wani aure da irin nashi matsalar sannan shi mai ɗaki shi yasan inda yake masa yoyo, amma tabbas matsala irin naki tana buƙatar waliyanku su shiga ciki, a yi masa gargaɗi da jan kunne domin tabbas ya aikata ba daidai ba, kuma ya wuce iyakarsa. Wani wajen aka ce namiji ya sanya hannu ya duki matarsa haka siddan babu laifin tsaye balle na zaune, abin baƙin cikin har da yi mata tsirara a kan idon yaranta wa iya zubillah".

Tunin Maman Walida ta kuma ɓarkewa da wani kukan, da nake jiyo sautin sa yana ratsawa har cikin kunyar kaina, kafin tayi nasarar jawo numfashinta da yake maƙalewa a ƙirji tace"Malama bani da wanda zai ɗauka min mataki, bani da iyaye duk sun rasu haka nan ma dangina duk sun ƙare rikicin faɗan boko haram shi ya rabo mu da ƙauyen mu, ya sanya danginmu warwatsuwa iyayena suka rasa rayukan su, ni kaɗai na shigo garin nan da Abban Walida na fara haɗu ya taimake ni, tare da bani wajen zama a cikin gidan su, bayan na sanar dashi da kuma iyayensa labarina da musabbabin barowa ta ƙauyen mu. Ya nuna ra'ayi a kaina har aka ɗaura mana aure dashi a nan ƙofar mai unguwa ba tare da mahaifiyarsa ta so ba, tun satin farko na amarcina a gidan Abban Walida ban ƙara samun farin ciki ba, baƙin ciki da ƙunci suka ƙara samun gurbi zaman daram a cikin raina".

Sosai ta saki kukan daya zo mata a lokacin, sai da ta tsagaita kana ta cigaba da faɗin"Malama wallahi idan naji ana cewar, ana samun farin ciki da walwala gami da kwanciyar hankali a gidan miji. Wallahi gani nake yi kamar ƙarya ne kuma shi mai faɗan kawai ya faɗi son ransa ne, domin ni duk ban taran da wannan jerin ababaɗen a cikin gidan nawa auren ba. Rashin dangi da gata su suka haɗo suka durƙushe min rayuwata, wallahi Malama cikin ƙirjina nawa akwai damuwowi masu tarin yawa da in bake na furtawa su ba bana jin nauyin da ƙirjina yake min ya rago".


Ina iya jiyo tagwayen ajiyan numfashin da Umma ta sauƙe kafin ta kai ga furta"Maman Walida tabbas wannan lokacin za ki ga gatanki, domin kina da Allah sarki da ya haramta zalumci akan kansa, kuma ya sanya ta haramun a tsakanin bayinsa. In sha Allah da zaran Malam ya dawo zan faɗa masa komai sai kuje wajen mai unguwa ayi komai a gabansa, idan ba'a samu sulhuba kuma bai amshi laifinsa ba ko takardarki ne sai ya bak......".

Saurin katse Umma, Maman Walida tayi cikin saurin muryarta dake bayyanar da taci kukan har ta gaji take faɗin"A'a malama ko meye za'a yi banda saki, wallahi in ya sake ni bansan inda zan tafi ba a yanzu bani da wajen zuwa ƙauyen namun ma ba kowa bane ya koma".

Rawar da ƙafafun suka fara yi suna barazanar gaza ɗaukar nauyin gangar jikina, ya sanya ni saurin jansu na fice izuwa namu ɗakin na kuwa yi sa'a babu kowa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".

Shine abinda yayi nasarar fitowa daga bakina, ina ƙara jinjina girman lamarin Maman Walida tun tasowar mu muke mata kallon mahaukaciyar da ta daɗe da rasa hankalinta. Babu irin aikin wahalar da bata yi domin ciyar da kanta, mijinta da ƴaƴanta har ma da iyayen mijin, sai da kuma girma muka gane ba mahaukaciya bace tsabar talauci da ƙangin rayuwa ce ta mayar da ita hakan.


Wayyo MATAN AREWA waye zai taimake mu?, kaf AREWA mun rasa.



MATAN AREWA

©Maimumah Tijjani Iyam

____________________________________


H.W.A

Page 0⃣5⃣


Na daɗe a haka har sai da naji kaina yana sarawa da matuƙar ƙarfi, kafin ya yunƙura dafe da goshina da nake ji tamkar ayi mini ajiyar wani abun mai nauyi a tsakiyar kaina. Sosai lamarin Maman Walida yake nuƙurƙusan rai da ruhina, duk da ba yau ne karo na farko Umma take samun ziyaran irin waɗannan matan ba ko wacce da iriyar nata matsalar.

Amma sai naji wannan ta fi ko wanne riƙe mini zuciyata, Ta ina zan fara kawo gyara a cikin al'ummata?, Wata zuciyar tayi saurin raya mini ta hanyar karatu ne kawai haƙata zata cimma ruwa, Babban burina raina tun ina ƴar ƙanƙanuwa nake da sha'awar zamtowa ƴar jarida, haka nan marubua suke burge ni fiye da yanda kalmomin da baki kan iya furtawa.


Ƙarƙarfan ajiyan zuciya mai matuƙar sauti, na sauƙe wata zuciyar tana cewa dani yaudaran kaina kawai nake yi.

Miƙewa nayi na fito waje na wanke fuskana da nufin ko zanji sauƙi sarawan da kan nawan yake mini. Idona sam na gaza kawar dashi daga ƙofar ɗakin Umma, kana nan zuciyata take kwaɗaita mini son sauraran ragowar zancen Maman Walida.


Miƙewa nayi zan koma ɗaki sallamar yaya Majid suka a kunnena.

Amsawa nayi, sannan na gaishe shi ya amsa. Yace na kawo masa abincinsa ɗakinsa, ɗakin girkin na nufa da zummar ɗauko masa naga babu kwanon abincinsa.
Girkin Ummansu Anty Kubra ce, don haka na ɗauki hanyar ɗakinta bakina ɗauke da gajerar sallama, sai da nayi baki uku ina shirin yin na huɗun aka amsa.

Gaishe ta nayi, ta amsa mini cikin halin ko in kula, kana nace"Umma daman abincin yaya Majid ne yace a kai masa, kuma naga kamar kin manta baki zuba masa ba".

"Ba mantawa nayi ba, abincin ne bai isa ba shiyasa na zubawa ƙananan yaran".

Tana gama faɗin hakan ta sakin labulen ta koma ɗakin, yanda muka yi da ita naje na sanarwa yaya Majid, bai wani damu ba domin ko ƙananan yaran gidan mu sun san halin Umman su Anty Kubra.
Sashin Hajiya Babba na nufa, kamar kullum na iske ta tana sallar walaha, yiwa kaina mazauni nayi gefe da ita kaɗan har ta iddar da sallan.

"Takwara kece, har kun taso kenan?".

"E wallahi Hajiya mun taso".

Daga haka nayi shuru ina wasa da yatsu hannuna, na rasa yanda zan fara fuskantar Hajiya da wannan zancen, sosai naji yayi mini nauyi akan harshena, domin nima kaina nasan nazo da sabon abu a cikin ahalin namun.

Ban sani ba ko fahimtar yanayina, ne ya sanya ta cewa dani"Lafiya kuwa?, ko wani abun kike son faɗa?".

"Hajiya wata magana ce ta kawo ni".

"Ina jinki Na'imatu".

Gyara zama nayi, ina lanƙwashe ƙafafuna waje guda kana nace"Hajiya sauƙar mu sai matsowa take yi, kamar yanda iyayen mu suka zarta za'a haɗa walimar sauƙar da bikinmu, gashi ni kuma har yanzu Allah bai fito mini da miji ba. Shine nace ko za ki yiwa su Abba magana ko makaranta ne na kom...".

Ƙarƙarewa zancen tayi, ta maƙale mini a hanyar maƙoshina, sakamakon kare ni da ido da tayi. Ƙasa nayi da ƙwayoyin idona ina sauraran lugudan dukan tara taran da ƙirjina yake yi, ɓal ɓal ɓal.

"Na'ima".

Cikin rawar murya nace"Na na na'am".

Sai da ta sauƙe numfashi"Na'ima kin zo da baƙun lamari mai girma, zuwa yanzu bana ce da ke komai ba. Amma tabbas za ki fuskanci ƙalubale shawarata gare ki shi ne, ki nutsu ki fidda miji kafin wa'adin da iyayenku suka ɗebar muku ke da ƴan uwanki ya cika, domin tabbas babu abinda zai dakatar da auren nan".

Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe, duk yanda naso dauriya da ƙarfin hali gami da son ƙarfafa kaina, ta hanyar matse ruwar ƙwallar da suka wadaci kurmin idaniyata. Lamarin faskara yayi sai da ƙwallar suka fara gudu gefen da gefen fuskana.


"Ke macece Na'ima aure shine abinda yafi dacewa dake, karatu na ƴaƴa maza ne domin sune suƙe riƙe da iyali kuma muke ƙarƙashin kulawar su, ki zamto macen ƙwarai ga mijinta abar alfahari ga ƴaƴanta".

Sosai naji bakina yayi mini nauyi, ta yanda naji ko kalma ɗaya bazan iya furta mata ba, kaina kawai nayi nasarar ɗaga mata.

"Ke kuwa meya kai ko wannan mummunan tunanin uwata?, kiyi auren ki shine babban gatan da za'ayi miki yanzu, ƴan mata nawa ne da suka riƙi boko yanzu kuma suke dana sani sun sama bokon, amma sun rasa mazajen aure, suna nan a gidaden iyayen su cike da nadama".

Furcin Goggo Jummai kenan da take tsaye daga bakin ƙofar ɗakin, kafin ta ƙarisa shigowa.


Na tabbata na cigaba da zama a wajen kuka ne zai ɓalle mini, don haka nayi hanzarin miƙewa na fice daga ɗakin, cikin muryata da take rawa nace"Hajiya ina zuwa zan dawo anjima".

Ban jirayi ta cewar ta ba, na fice da sauri izuwa sashin mu kaina tsaye na nufi ɗakin mu. Ban damu da mutanen da na iske a tsakar gidan ba, balle ƙananun maganar da suke yi suna raka ni da kallon tuhuma.

Ɗaƙin mu na faɗa na zube akan katifar mu, kafin na sake wani kuka mai ƙarfin gaske da duk ɗakin ya amsa. Sosai nake rero kukan har izuwa lokacin da Anty Zakiyya ta shigo ɗakin tamkar an jefo ta.


A kiɗime ta nufo ni haɗi da faɗin"Ke ke Na'ima lafiyarki, meye ya faru, meya same ki?".
A jere tayi mini tambayar wata na bin wata, maimakon na bata amsa sai ma tsananta ƙarfin kukan nawan da nayi. Ba ta gaji ba ta cigaba da jero mini tambayoyin.

Jin sheshsheƙar kukan da ta fara yi ya sanya ni, tashi zaune ina share fuskana kafin na kamo hannunta cikin nawa"Ya isa haka Anty".

"To menene?".

Sai dana daidaita nutsuwata kafin nace"Anty Zakiyya yaya zanyi da raina?, dan Allah ki sanar dani abunda zanyi naji sanyi a sashin ruhina, damuwa ya cunkushe mini raina na rasa wanda zan fara warwarewa".


"Ina jinki menene yanzu ya faru?".

Sai da na zuƙe majinar kukan daya zo mini, kafin nace"Su Abba sunce walimar sauƙar mu da bikin mu za'a haɗa, har yanzu ni babu wani saurayin da nake kulawa balle har magana mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu, a kai ga maganar ƙulla alaƙar auratayya a tsakani. Makaranta nake son na koma amma duk wanda na tunkara rashin yiyuwar abun yake nuna mini, hatta Umma da Hajiya Babba, ban sama goyan bayansu ba. Yanzu ma Hajiya Babba ta ƙara jaddada mini akan lalle na fidda miji kafin wa'adin da su Abba suka ɗeba mana ya cika".

Daga ni har ita kukan muke yi, babu mai lallashin wani sai da muka yi, muka gaji don kan mu. Kafin ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata haɗi da cewar"Na'ima ko nima yanzu abinda suka faɗa miki, shi zan ƙara maimata miki. Duk wanda yazo miki da nufin aure to ki gabatar dashi ga su Abba ayi magana a wuce wajen, shin ni ban ishe ki ishara ba Na'ima?. Wallahi ko maƙiyina bana masa fatan jinkirin aure mussamman idan ƙaddara ta sanya ka faɗo a cikin gidan yawa".


"Anty Zakiyya dukkanin jinkiri alkhairi ne ga wanda yayi imani daga Allah ne, ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah domin shine wanda ya tsarawa kowa ƙaddararsa tun kafin a san da samuwar ruhin mu a bayan ƙasa, don haka ya daina damun ki dududu nawa shekarun ki suke, idan ana wani abun sai kace wacce ta shekara ɗari a gida ba tare da aure ba haba".
Taƙaitaccen murmushi tayi"Na'ima kenan, ke dai yanzu ki mayar da hankali akan wannan maganar da muka yi, idan Allah ya fito miki da miji kinga ko karatun ne ma kya yi cikin ɗakin mijinki. A wannan lokacin yardarsa kawai kike nema".

Musgutawa nayi kawai, ba tare dana iya cewa da ita komai ba, sai can nace"Maman Walida ta tafi kuwa?".
Ita ma sai da ta sauƙe ajiyar zuciya kana tace"Ta tafi tare da Umma Abba da kuma Baba basu ma dawo ba".

Har na yunƙura da zummar cewa wani abun, sai kuma wani tunanin ya shigo mini na kawar da zancen. Mun tattauna sosai da Anty Zakiyya, har naji ɗan sauƙi daga ƙonar da raina yake ya tsirka mini.

Umma bata dawo ba sai yamma lilis, da alama a gajiye take aihun, ban sama damar tunkarar ta da zancen Mama Walida ba, don ta kwanta da wuri. Daren daren rabi da kwatansa ban runtsa ba, su Balkisu sai faman haɗa zance suke yi zasu turawa samarin su wasiƙa.

Kasancewar duk cikin mu babu mai waya, a aƙidar gidan mu babu wacce ake bari ta riƙe waya sai dai in a ɗakin mijinta in yayi ra'ayin saya mata to.

Washe garin ranar gidan mu ya tashi ciki hidiman tarban iyayen saurayin Salma, Abdallah da iyayensa zasu zo yau.
Zo kaga harbin iska da habaici wajen Ummansu, haka nan ma Salma sai wani kici kici take da fuska. Abinci da ababen sha aka yi musu domin tarar su, zuwa ƙarfe goma sha ɗaya suka iso falon su Abba aka kai su.

Tunin sauran matan gidanmu da ƴaƴansu, suka firfito domin ba wa idanunsu abinci, ƴaƴansu kuwa ko wacce burin ta da abinda suka zo dashi.

Har jikin motocinsu su Abba suka yi musu rakiya, sannan suka dawo ciki. Basu yiwa kowa maganar ba illa zarcewa sashin Hajiya Babba da suka yi.



Bayan sallan magrib ina zaune a ɗakin mu ina tilawar karatuna, su Balkisu suna gefe suna hirar su, ta kullum da take tusa mini takaici, Nurain ya shigo yace su Abba suna neman su.

Kallon kallo muka shiga aikawa junan mu kafin, muka miƙe muka fice izuwa sashin su Abba.
Abba, Baba, da kuma Baba ƙarami muka tarar a falon, cikin ladabi duk muka gaishe su suka amsa.

Kafin Baba yayi gyaran murya kana yace"Yau iyayen Abdallah sun zo, kamar yanda suka bamu lokaci sun cika wannan alƙawarin. Balkisu da Abasiya suma iyayen ku mata sun sanar damu cewar naku zasu turo sati mai kamawa, Na'ima kece kawai bamu ji wani magana mai ƙarfi ba a kanki shin kina da tsayayye?".

Dam dam shine saurin da ƙirjina ya bada, tunin duk jikina ya ɗauki rawa. Sai da ya ƙara maimaita tambayar a karo na biyu kafin na aro jarumta na azawa kaina nace"Baba bani da tsayayye a halin yanzu sai da..".

"Dakata har yanzu kina da saura lokaci, kiyi amfani da wannan ki fidda miji domin ba zamu saɓa ba a kan maganar aurar daku a tare da ƴan uwanki, idan kuma ba za ki fitar ba zamu bada ke ga duk wanda muka ji hankalin mu ya nutsu da nagartarsa".

Wasu hawaye masu ƙarfi ne suka ɓalle mini jiyo maganar da Abasiya ta ɓarke dashi.

"Baba akwai wani malami a islamiyyar mu ta safe, kowa ya fahimci yana son Na'ima ita ce dai kawai bata bashi dama ba".

MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 0⃣6⃣



Ɗago kaina na kafe Abasiya da kallo, da sam ta ƙi yarda mu haɗa ido da ita. Jin sautin muryar Abba sun sauƙa a ƙofofin kunnuwana ya sanya ni kawar da idanuna daga kan Abasiya.

"Na'ima".

Cikin harɗewar harshe nace"Na'am Abba".
"Haka ne zancen Abasiya?".

Take wani zuffa ya fara tsatstsafo mini daga dukkan mafitar gashin dake jikina.
"Ke nake sauraro".

"E haka ne Abba, amma dai bai furta hakan gare ni ba, kawai dai hashashen su Abasiya".

Shuru ya ratsa ilahirin falon, kafin Baba ƙarami yace"zamu yi magana zamu neme ku".

Kamar kazar da aka jefa da gishiri haka na miƙe, tamkar wacce aka zarewa laka a jiki. Ɗakin mu muka nufa dai dai sannan masallacin dake kusa da gidan mu aka ƙwala ƙiran sallan isha'i. Sai da nayi salla na je ɗakin Umman mu duk abinda ya faru duk na fayyace mata.
Sai da na ƙare zancen na kai aya, kafin ta kallo ni gami da cewar"Na'ima ki karɓa duk hukuncin da suka yanke, ba zasu taɓa yi miki mummunan zaɓi ba, don haka ki taushi zuciyarki kiyi biyayya ga dukkan hukuncin da zasy zartar a kanki inji Mamana?".

Kaina na ɗaga mata ina matse ruwar ƙwallar da suka wadaci idaniyata, a ƙoƙarin hana ta gano hakan, banyi zaman mintuna ashirin ba nayi mata sai da safe kafin na leƙa ɗakin su Anty Zakiyya ita ma kuma yiwa juna sai da safe.

Juyi kawai nake yi akan katifar namun domin na ƙudurce a raina cewar ko meye zai je ya dawo, ba zan taɓa tanka wa Abasiya akan abinda tayi ba. In ma da wani nufin ta aikata hakan a gare ni, to bazan taɓa bata damar cimma manufarta a kaina ba.

Ƙiran sallan asubahin farko kuwa kamar a ƙofofin kunnuwana aka ƙwala ta, ko da nayi sallan kwanciyata nayi a bisa katifar mu, don sam bana da niyyar zuwa islamiyyar.

"Ke Na'ima amma dai kinsa ke muke jira ko?, aikin banza kawai ke zai wulaƙanci da shegen jin kan tsiya".

Ko ɗaga kai banyi nayi mata kallon arziki ba, balle har ta sanya rai ga samun amsa daga gare ni, mirginawa nayi na kwanta ruf da jiki tare da lumshe idaniyana.

Dogon tsakin ta tsirkar mini, tayi ficewarta tare bankaɗo ƙofar ɗakin da matuƙar ƙarfi. Ko a jikina, ban san meya faru ba cikin su babu wacce ta ƙara zuwa da zummar yi mini magana.

Ban fito ko ƙofar ɗakin ba, har sai da haske ya fara kawar da duhun asubahin da ya lulluɓe garin, na tashi na share mana ɗakin.

Sannan na fito nayi wanke wanke, na nufi ɗakin Umma na iske ba ta nan tana sashin Hajiya Babba, don haka na gyara ɗakin kana na leƙa ɗakin su Anty Zakiyya na tarar tana bacci.

Hakan ya sanya ni komawa ɗakin mu, na fara tilawar karatuna sai dana haɗa izifi biyar, sannan Salma tayi sallama bata jira amsawa ta ba. Ta faɗo ɗakin tana jifa na da kallon uku saura kwata, ban mayar da hankalina a kanta ba, har sai da Balkisu ta shiga.

"Na'ima Na'ima".

Da kallo nake alamta mata menene. Cike da zaƙuwa take cewar"Na'ima malam Yusuf ne gashi can a ƙofar gida, yazo wajen ki".



Wani kallo na watsa mata sam na gaza furta mata koda kalma ɗaya ce, ɗauke kaina kawai nayi daga gare ta raina yana mini matuƙar ɗaci, na rasa gano dalilin su Balkisu wajen mutumin nan.

Shigowar yaya Majid bakinsa tamkar gonar auduga, yana cewar"Na'ima kina da baƙo a waje".
Yana gama furzar da zance ya saki labulen ɗakin ya fice, ba don raina yaso ba na zara hijabi na. Na fice bayan na gama wurgawa su Balkisu harara.

Tsaye da yaya Majid na iske su, ganin fitowa ta ya sanya yaya komawa cikin gida, a nutse na ƙarisa inda yake tsaye da siririyar sallama a bakina ya amsa idanunsa suna kaina, kaina a ƙasa na gaishe shi ya amsa shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe.


Har izuwa lokacin da yayi gyaran murya yace"yau ba ki je islamiyya ba, shine na tambaya ƴan uwanki suka shaida mini suma ba ki sanar dasu dalilin rashin zuwan takin, nace bari n biyo sawu lafiya dai ko?".

"Lafiya ƙalau kawai bana jin daɗin jikina ne".

"To Alhamdulillah daman kullum hakan ake fata, Allah ya ƙara lafiya".

"Amin".

Na amsa dashi cike da ƙosawa da sauraronsa, ban sani ba ko dan ban saɓa tsayiwa da saurayi bane, ya haifar mini da rawar jikin da nake fama dashi oho, don gabaɗaya jikina ya ɗauki mazari.

Ban sani ba ko lura yayi da hakan, ya sanya shi furta"To ni zan koma sai kuma wani lokacin ko?".

"To nagode Malama".

Laulausan murmurshin da ya jefo ni dashi, ya sanya ni yi masa kallon ido cikin ido ya ƙara sako mini wata kafin ya juya ya ɗauki hanyar tafiya.
Sai da na sauƙe numfashi kana na juya zan shige gida, nayi kiciɓus da yaya Majid a zaure yace zuwa anjima nazo na same shi yana son magana dani.
Da to na amsa dashi, na bashi hanya ya fice ni kuma na shige ciki, sashin Hajiya Babba na wuce na iske ta zaune tana jan carbi, kusa da ita nayi wa kaina mazauni raina cunkushe da tunani marasa adadi, sam na gaza gano manufar murmushin nan ta Malam Yusuf.

Tunin naji kaina yana juyawa, ban san Hajiya Babba na mini magana ba sai da taɓo ni na dawo figigi daga tunanin dana fara zurmawa cikinsa.

"Na'am Hajiya magana kike yi?".
Sai da ta ƙare mini kallo, mai kama da na tuhuma kana tace"Tunanin meye kike yi?".


"Babu komai".

Na faɗa ina ƙoƙarin dasa ƙirƙirarriyar murmushi akan fuskana, bata ce da ni komai ba, ganin hakan ya sanya ni miƙewa na gyare mata ɗakinta tsaf sannan na wanke banɗaki.


Sai da na gama na fito, zan wuce sashin mu na tarar da baƙin a sashin su Abba, sai da na shigo cikin gida nake jin tsegumi wai iyayen mijin Anty Kubra ne, ɗakin Ummata na nufa na gaishe ta, kallon da Anty Zakiyya take mini ya hanani sakat sai ƙunshe dariyar dake son kuɓuce mata take yi.

"Ina kika shiga ne, tun bayan sallan asubahi ban ganki ba?".

"Umma ina sashin Hajiya Babba".

Wani kallon Anty Zakiyya ta kuma yi mini, nayi mata alama da ido akan lafiya kuwa tace dani"Ke dai ki faɗi gaskiya yarinya".
Kallon rashin fahimta na bita dashi"to kenan yanzu ba gaskiyan na faɗa ba?".
Ɗage mini kafaɗa tayi alamar bata sani ba, kana ta zauna kusa da Umma tace"Umma yarinyar nan baƙo tayi ɗazu,wai malamin islamiyyar su haka naji yaya Majid yana faɗa don dashi suka fara zantawa".

"Na'ima haka ne zancen Zakiyya?".

Nan take naji yawun bakina ya tsaya cak, tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya ƙafe, a sanyaye cike da kunyar Umma nace"E haka ne".

"To da yazo me kuka tattauna dashi?".

"Umma kawai yazo ganin lafiya ne, yau banje islamiyya ba shine kawai fa".


Na ƙare zancen ƙarshen kamar zan fashe da kuka, murmushi na hango fal a shimfiɗe a bisa fuskar Ummata bata kuma cewa dani ko kanzil ba, hakan nan na gaza gano manufa da maƙasudin wannan annurin fuskar natan.

Shigowar Nurain ya katse mini karatun wasiƙar jakin da nake yi a raina, yana faɗin wai nazo muci abinci inji su Salma. Miƙewa nayi muka fita a jere dashi har ɗakin mu na zauna zaman cin abincin, ko kaɗan naƙi ba wa kowacce daga cikin su fuskar da har zata yi mini wani maganar banzan, har muka kammala cin abincin.



Ɗakin yaya Majid na wuce, kowacce mata tayi cirko cirko tare da ƴaƴanta sun kafa tare da tsarewa, da son jin ƙwaƙwaf akan zuwan iyayen Habibu mijin Anty Kubra.
Da sallama na tura ƙofar ɗakin, ya bani iznin shiga yana zaune kan katifarsa dake yashe a ƙasa a cikin ɗakin, na zauna kusa dashi. Sai da ya rufe takardar dake hannunsa ya ajiye ta gefe guda, kana ya fuskanto ni da kyau yace dani"Na'ima ince dai Malam Yusuf ya sanar dake dalilin wannan zuwan nasan?".
Dam-dam shine sautin da ƙirjina ya bata, kafin nayi nasarar fizgo numfahsina da yake maƙale mini a ƙirji nace"A'a ya dai ce yazo ne ya duba ko lafiya yau banje islamiyya ba".

Sai da yayi nisa yace"To ya sanar dani cewar yana sonki, kuma idan an bashi dama yana son ya gabatar da kansa ga su Abba, a shirye yake sai a haɗa bikin da na su Salma".
Banje dashi komai ba, don zantukansa ya gama shayar dani giyar mamakin da har yanzun mayenta ya ƙi saki na.

"Don haka ki bashi dama, za kuma a gudanar da binkici a kansa matuƙar an same shi da kyawawan halayya kinga kawai sai ya turo iyayensa".
Na ƙare zancen ƙarshen kamar zan fashe da kuka, murmushi na hango fal a shimfiɗe a bisa fuskar Ummata bata kuma cewa dani ko kanzil ba, hakan nan na gaza gano manufa da maƙasudin wannan annurin fuskar natan.

Shigowar Nurain ya katse mini karatun wasiƙar jakin da nake yi a raina, yana faɗin wai nazo muci abinci inji su Salma. Miƙewa nayi muka fita a jere dashi har ɗakin mu na zauna zaman cin abincin, ko kaɗan naƙi ba wa kowacce daga cikin su fuskar da har zata yi mini wani maganar banzan, har muka kammala cin abincin.

Sanƙarewa nayi a wajen, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya gagare ni, sai can nace"Yaya Majid amma nifa bai furta hakan a gare ni ba, sai nake ga kamar anyi sauri".

"Haba Na'ima menene abin sauri, ince dai ba ki manta a cikin satin ukun da ya rage yau kun cinye kwana biyar, Na'ima ki amshe Malam Yusuf hannu biyu biyu".

Sai da ya numfasa kamin ya ɗaura da faɗin"Na'ima a yanzu maza ne kawai suke auran waɗanda suks so, saɓanin MATAN AREWA da suna aura wanda yazo musu ne, kuma ya shirya yin auran don haka ki amshi malam Yusuf".


MATAN

Please Login or Register in order to submit comment