Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alkhairi.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

_________________________________________

Page 1⃣6⃣


"Na'imatu ya naga fuskar nakin duk a kumbure alamar kinsha kuka kin ƙoshi, in ce lafiya lumi ko?".

Furcin Umman su Salma kenan da suka sauƙa a masarrafar ji na, sunkuyar da kaina ƙas nayi kafin na ce da ita"Umma babu komai lafiya ƙalau daren jiya ne ban sama ishashshan bacci ba, saboda ciwon kan da ya matsa mini".

"Ai de kuwa naga alamar hakan, to Allah yayi mana mai kyau".
"Amin".
Na amsa dashi can ƙasan maƙoshina, Anty Zakiyya tana taya ni amsawa.Dai-dai sa'ilin da Umma ta fito daga ɗakinta ta kallo ni haɗi da cewar"Na'ima har yanzu basu fito ba?".

"E".
Ina rufe bakina, yaya Majid yana isowa inda muke ya shaida mini sun gama yana jira na a waje sallama muka yi da Umma da Anty Zakiyya da tayi mini rakiya zaure sannan muka baro gidan. Mun iso gida ana ƙiran sallan asr don haka Yaaya Yusuf ya ajiye ni shi kuma ya wuce masallaci.
Shau babu kowa a filin tsakar gidan, haka nan duk sallan da nake rangaɗawa da dushashshiyar muryata ba'a amsa ta ba, ganin hakan ya sanya ni tinanin ko Maman Hanan ta shiga makwabta ne. Har na zaro ɗan makulli zan tsura na buɗe ƙofar ɗakina kukan da Hanan take rerowa daga cikin banɗaki suka dakatar da ni ajiye jakata nayi na nufi banɗaki. Can ƙu'iya na hange ta fuskarta jiƙe lijif da hawaye, cikin sauri na isa gare ta haɗi da faɗin"Ke Hanan menene?, me kike yi a nan?".
Bata ce dani uffan ba domin ajiyar zuciyar da take sauƙewa a kai a kai, ya ƙi bata damar furta mini ko kalma ɗaya. Ganin hakan ya sanya ni riƙo hannunta muka fice na wanke mata fuskarta sannan na bata ruwa tasha idanuna tar akan ƙofar mamanta da aka ja shi aka rufe. Ɗakina na buɗe bayan nayo alwala na shige da ita kafin na ajiye jakana da ɗauko sallaya har Hanan tayi bacci, taɓo wuyarta nayi naji zafi gau alamar zazzaɓi mai ƙarfi ya sauƙar mata jiki.

Tagwayen ajiyan numfashi na saka, kafin na miƙe na gabatar da sallan asr. Na fito ganin ba'a sanyawa ƙofar makulli ta waje ba ya sani fara rangaɗa sallama shuru babu amsa na fara dukan ƙofar a hankali na ɗauki mintuna a haka kafin na jiyo motsi daga ciki hakan ya tabbatar mini da hashashena akan cewar tana cikin ɗakin. Sai dai meye take yi haka da ya hana ta jin sallamana balle shigowata cikin gidan, har ya toshe mata kunnuwa daga jin kukan Hanan.
Ja da baya nayi jin ana tunkaro ƙofar za'a buɗe, kanta kawai ta leƙo ba tare da ta buɗe ƙofar gabaɗaya ba balle na sama damar ganin abinda ke wakana ciki.

"Na'ima har kin dawo?".

"E wallahi Anty na dawo tun ɗazu, banji motsinki ba shiyasa nace bari nazo naga ko shin lafiya ga Hanan can ma a ɗakina zazzaɓi ya rufe ta".
Na ƙarishe zancen ina bin ta da kallon, da yake bani damar karantar yanayinta. Tun daga kallo ɗaya da nayi mata na tabbatar da cewar wata matsalar domin sam bata a ciki cikakken nutsuwa ko maganar da take yi fizgo shi take yi. Dai da ta gyara ɗaurin ƙirjin dake neman warwarewa daga jikinta kana ta furta mini cewar"Wallahi kin ganni nan tun bayar tafiyarku, nake fama da ciwon kai ga rashin kuzari ban iya taɓuka komai ba, nan na kwanta Hanan ta dame ni da rigima shine na shigo ɗaki na rufe".
Kaina na jinjina ina ƙaƙalo murmushin da ya tsaya iya kan leɓɓana na sakar mata, ba tare da na samu nutsuwar zuciya akan zancenta ba nayi mata yaya jikin ta amsa mini da kalmar alhamdulillah.

Ba zan tsaya jin wani abu ba, nayi komawata ɗaki sam na gaza samun nutsuwa da halin da naga Maman Hanan a ciki wani irin nauyin bacci ne haka da ya hana ta jin komai?. Ganin bani da amsar tambayar ya sanya ni miƙewa na cire kayan jikina na ɗaura zani na ɗauki sosona na fito ruwa na ɗiba na shiga banɗaki na watso ruwa a jikina sannan na fito.
Tabbas idanuna fitar mutum suka hango ficewarsa daga cikin gidan, cikin sauri na dawo da baya a ƙoƙarin tabbatar da abinda idanuna suka gano mini, jin ƙarar an tura ƙofar gidan a hankali ya tabbatar mini da abinda idon ganina ya gano mini. Matuƙar tsoro ne ya tanke raina, nayi azaman shigewa ɗaki kamar zan kife akan hancina na dafe ƙahon zuciyata da ƙirjina yake dakan lugudan dukan tara tara sau tara, jawo numashi nayi mai ƙarfi na fesar a ƙoƙarin samawar kaina nutsuwa. Tsawon daƙiƙu biyu ina saye a wajen kafin naja ƙafafuna da naji sunyi mini sanyi laƙwas na zauna tare da jawo robar mai na fara murzawa a fatana kafin na miƙe na ciro dogowar rigata mai sauƙi nauyi na zara.
Rurin da wayata ta soma yi, ya sanya ni kai dubana gare ta. Ganin lambar Yaaya Yusuf ta bayyana cikin screen ɗin wayar da yayi saving da *ZAUJI* da kansa ya sanya ni saurin ɗaga ƙira ina karawa a kunnena.
Sai da na sausauta amon muryata nayi sallama ya amsa, yana ɗaura da"Ina fatan dai kukan nan ya tafi ko?".
Sai da na ɗaga kaina kana na ce"Babu shi Yaaya, tunda kayi mini hani dashi na daina".
Cike da jin daɗin furucin nawan ya furta mini"Masha Allah yayi Albarka, kar ki ji ni shuru n wuce islamiyyar yamma ne sai zuwa dare zan dawo".
Cike da kulawa nake faɗin"Amma Yaaya baka ci abinci ba fa tun safe, inda hali dai ka dawo gida kaci abinci ko ka aiko a karɓa maka".
Ina iya jiyo murmushin da ya saka ƙasa-ƙasa kana ya shiga cewan"Karki damu Na'ima zan nema wani abun kawai naci kafin na dawo ɗin". Shagwaɓe fuska nayi kamar ina gabansa har da ɗan buga ƙafata nake faɗin"A'a ni dai gaskiya Yaaya ban yarda, ƙarfe biyar ana tashi ka dawo gida kaci abinci".

"To shikenan Gimbiya yanda kike so hakan za'ayi, shikenan ko kuma da wani abunda kike so ayi?".
Murmushin jin daɗi da ya bata wani ɗan sauti na saka cikin faɗin"Babu wani abunda ya rage, Allah ya dawo da kai lafiya cikin aminci, in kaci abincin kaje islamiyyar dare ban isa Anty Binta ta ga ka rame ta hukume ni akan ban kiwa ta ka da kyau ba". Sosai ya saki dariya mai ƙarfi, sai da yayi iya jinsa ya tsagaita don kansa yace"Amin ƙurratu aynun madalla na gode da addu'a, watau ma kiwona kike yi kenan?".

"Ƙwarai kuwa".

"To shikenan sai na dawo ɗin".
Da haka muka yi sallama, sai da na katse ƙiran na mance da ban tambaye shi abinda zan dafa masa ba duk da kuwa haɗa girki muke yi amma kowacce in ita ke da girki zaɓin mijinta take girkawa. Saƙo na tura masa akan abinda yake son ci, ya dawo mini da amsar cewar ya bani zaɓi na dafa ko menene matuƙar ni na sarrafa shi ya tabbatar zai burge shi.
Fitowa nayi na haɗa garwashi ya ruru, na fara haɗin girka masa miyar ɗanyen zogale don na lura yana matuƙar jin daɗinta, ina yanka albasa Maman Hanan ta fito miƙa tayi hamma kana ta iso gare ni. Ta zauna akan tabarmar da nake zaune a kai sannu da fitowa nayi mata ba tare da na ko kalle ta ba, jawo tiran zogalen tayi gabanta ta fara tsincewa haɗe da faɗin"Yau kuma Yusuf miyar zogale yake sha'awa kenan?".
Kaina na ɗaga mata ta kuma cewar"hmm kina ji da mijin nan Na'ima, ni tun yaushe na wasar da tambayar Abban Hanan abunda za'a dafa ko kuma abinda yake biɗar ci, duk abinda naga zan iya dafawa shi nake girkawa ko yaci ko ya bari wannan ruwansa".

"Anty kenan hakan kuma yana da muhimmanci ai tambayar ra'ayin mutum, in ya baka zaɓi sai kayi gaman kanka".
Taɓe baki tayi"Ga wanda mijin ya damu da hakan kenan ba, wani ma buƙatarki bai biya miki ba balle ya kula da wannan ke dai ayi sha'ani kawai, kema lokaci ne wataran ko da kuɗi aka haɗa ki ba za ki yi ba".

Cak na dakata daga yankan albasan, ire iren zantukan nan suna ƙara dulmiyar mini da tunanina, nayi wa rayuwar aurena tanadin da sai dai wani ikon ubanjigin ya kawo rabuwa. Maganar da ta ɗaua dashi suka dawo dani daga karatun wasiƙar jaki.

"Ina Hanan take banji motsinta ba?".
"Tana kwance a ɗaki, ta sama bacci ne".

"Masha Allah, bari ta tashi ta sha magani ban san sanda ta shigo gidan ba domin gidan Maman Mus'ab na tura ta da ta dame ni shiyasa ma na rufe ɗakin".

"Ayya".

Shuru ya ɗan ratsa kana ta katse shurun ta hanyar furta"Yaya kula kaya da Anty Binta?". Sai da na numfasa kana na zayyanu mata dukkan abinda ya wakana. Ita ma numfashin ta furzar ta ce"Daman na sanar dake hakan Na'ima, baza ta taɓa amincewa in dain wannan matar ce. Lokacin farkon samun matsalana da Abban Hanan a kan ƙaurace min da yayi tafi kowa bin bayan ɗan uwanta sam bata ga laifin shi ba, balle ƙoƙarin ɗaura shi a turban gaskiya. Wani lokacin ɗabi'unta kamar da jinsin mace ba, don haka kar ma ki ɓatawa kan ki lokaci tare da wahalar da kanki ta hanyar azawa zuciyarki dakon abinda ba zai yiyu ba. Ba zata taɓa amincewa ba shi kuma Yusuf ba zai taɓa aikata abinda ba ta lamince masa a kai ba, don haka kiyi haƙuri kawai ki rungumi rayuwa a yanda tazo miki".

Take naji jikina gabaɗaya yayi laƙwas kamar wacce aka zarewa laka a jiki, haka muka kammala girkin tare. Sai da aka yi sallan Magrib Yaaya Yusuf ya dawo kasancewar Abban Hanan bai dawo daga kasuwa ba na zuba mana muka ci tare dashi, don ni bama yunwar nake ji sosai ba kasancewar naci abinci a gida. Mun gamawa ya fita masallaci nima sallan nayi na watso ruwa nayi shirin kwanciya hijabi na ɗaura a kai na shiga na tambayi jikin Hanan da sauƙi sosai domin tunin ta ware sai da safe nayi mata zam fita ta dakatar da ni da "Yusuf ya shigo kenan?". Kaina na ɗaga mata ina ficewa wani ɓangaren raina cike da tausayin zaman auren Maman Hanan domin Abban Hanan baya dawowa gida sai dare ya tsala haka nan farar safiya ya fice kasuwa, sam baya samun lokacin iyalinsa balle na jin damuwar su.
Na iske Yaaya Yusuf yana karatun al-ƙur'ani, zama nayi gefensa na jona shi muka cigaba dayi. Mun ɗaɗe muna yi kana muka yi haramar kwanciya.

"In sha Allah da asuba zamu yi magana da yaya Auwal, da yardan Allah zamu shawo kan Anty Binta".
Iska na fesar nace"Yaaya dukkan alamo sun nuna babu nasara cikin wannan lamarin".
Saurin tarar numfashina yayi"Kar ki sare in sha Allah matuƙar ina numfashi zan tsaya miki wajen ganin tabbatuwar mafarkinki, musamman yau da muka tattauna da su Abba suma sun nuna goyan bayan su sosai akan hakan kuma sun ji daɗi".
Tabbas nayi zarra cikin mata, da samun arzikin miji kamar yaaya Yusuf, godiya na shiga yi masa har da ƴar guntuwar ƙwallata.


MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam

__________________________________________


Page 1⃣7⃣



Rabi da rabi baccina na daren ranar ya kasance, na zaƙu garin Allah ya waye ji matsayar zancen nan. Ƙiran assalatun farko kuwa tamkar a kunnena ladanin ya tsala shi tar na buɗe idona ko da na tashi na iske Yaaya Yusuf zaune bisa sallaya yana wurudi, bisa al'ada ko yaushe nayi sammakon tashi tabbas zan iske shi yana wurudi ko yana nafila.
Musayar kallo muka yiwa junanmu, kafin na sauƙa na zaune kusan shi ina gaishe shi, sai da ya yalwata annurin dake dashe bisa fuskarsa kana ya amsa mini yana dafa kaina tare da karanto mini addu'ar da ta zamto abinda yake fara yi mini ko wacce safiya, tare muka shige banɗaki muka yo alwala nazo na tada sallah shi kuma Yaaya Yusuf ya fice masallaci. Na daɗe saman sallaya ina addu'ar samun mafita ga bahaguwar rayuwata, mafitar da zata zamto mini maslaha akan komai ya juya ƙuncin ruhina zuwa ga dawwamamman farin cikin marar yankewa. Sai da naji ƙafafuna sunyi sanyi laƙwas na shafa addu'ar ina yunƙurawa na miƙe tsaye tare da zare hijabin dake bisa kaina, haka nan na since kaina da zaba tagumi hannuwa bibiyu ƙirjina yana gudun famfalaƙin da ya haifar mini da runtse idanuna da matuƙar ƙarfi.
Lokaci bayan lokaci nake kai dubana izuwa ga agogon dake maƙale jikin bangon ɗakin, ina duba lokaci don nasan sai takwas in an tashi daga islamiyyar safe Yaaya Yusuf zai dawo, ban san dalili ba sai naga yau gabaɗaya lokacin baya gudu haka nan juyin agogon sam bana ganin saurinsa. Ganin zaman ba zai tsinana mini komai ba ya tilasta mini miƙewa na fito waje na iske Maman Hanan har ta share gidan tsaf, tana shirya Hanan cikin shirin tafiya makaranta na zauna kan tabarmar da na iske malale a wajen na gaishe ta, sai da ta kalle ni sosai kana ta ce"lafiya kuwa kamar bakya jin daɗi?".
Sai da na numfasa na sama zarafin cewa"Lafiya ƙalau Anty".
"Uhmm Na'ima kenan, tabbas akwai wani abun sai dai kin ɓoye min".
Jin hakan ya sanya ni feɗe mata biri har wutsiyarsa, shuru ta ɗan yi dai-dai nan ta kammala shirya Hanan yaran makwabtan mu suka shigo suka tafi tare, don yau Yaaya Yusuf yayi lattin dawowa har takwas ta gota. Rungume ni Hanan tayi domin wannan ne hanyar da muke sallama da ita ko yaushe idan zata fice.

"Na'ima kenan har yanzu kina nan kafe akan wannan ƙudurin nakin, to Allah ya saki sa'a ya basu nasarar shawo hankalin Anty Binta".
Muryata a karye na amsa da"Amin ya Allah na gode".
Tare muka yi karin kumallo sannan na haɗa wanke-wanke nayi, ina wanke ƙafafuna Maman Hanan ta fito saɓe da hijabi a kafaɗa tana faɗin"Na'ima zan shiga gidan Maman Anwar yanzu zan dawo".

Gajeran murmushi nayi haɗi da cewar"Anty na lura akwai aminci sosai tsakaninku da Maman Anwar ɗin nan, ba garin Allahn da zai waye bata zo gidan nan ba kema baki je mata ba".

"Na'ima kenan ke dai kawai ayi sha'ani, amma tsayawa faɗin irin amincin dake tsakaninmu da Maman Anwar ma ɓata lokaci ne. Duk yanda kike tinani ta wuce hakan a gare ni domin tayi min abinda har ƙasa ta rufe min idaniya bazan mance da halalcinta gare ni, ta share min hawaye a lokacin da ko ƴan-uwan da muka fito ciki ɗaya dasu uwa ɗaya uba ɗaya suka gaza fahimta ƙuncin da zuciyata take ciki, ke dai sai na dawo kawai".
Ta faɗa cikin sausauta amon muryarta kafin ta fice fu kamar iska ba tare da ta bani damar cewa komai ba. Da kallo na bi ta raina cike da juyayin maganganunta duk me hakan yake nufi, meye kuma Maman Anwar ɗin ta aikata mata da har take ikirarin ko ƴan uwan jininta basu yi mata ba.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciya na sauƙe kafin na miƙe zan shige ɗaki, sallamar da aka rankaɗa da suka sauƙa a masarrafan jina suka dakatar dani baki sake na zura a guje na rungume Balkisu da Abasiya da suke tsaye tare da Asma'u.
Sam bakina ya gaza rufu na ja hannayensu izuwa ɗaki na kawo ruwa kallon sha'awa na bi Abasiya dashi domin tayi bul bul abinda ga wani haske da sheƙin da fatarta take fitarwa baki sake nake faɗin"Abasiya wannan kyau haka, kin ganki kuwa? ko dai Aminu yayi ajiye ne?". Fashewa muka yi da dariya ni da Balkisu har da tafa hannu fari Abasiya tayi da iya idanu kana ta ce"Ba wani sirrin da ya ɗara kwanciyar hankali da kuma soyayyar mijina, ga cima mai kyau naci mai kyau nasha mai kyau meya wuce haka kuwa".
Murmushi nayi taƙaitacce ina sunkuyar da kaina ƙasa, sai naji maganganunta sunyi mini kamar da ba'a take yi mini don haka na kawar da zancen ta hanyar faɗin"Abasiya kenan Allah ya kyauta, Ya Salma fa kuna magana da ita?, tunda tazo tayi mini sallama shikenan".

"Lalala Salma in gaya miki tana can kudu da Abdallah, rannan da naje gida ta ƙira Ummansu har mun gaisa na karɓa lambarta".

"Allah sarki Salma nima zan karɓa lambarta in sha Allah, karɓi ki sanya mini".

Na miƙawa Balkisu wayata ta sanya mini lambar, sosai muke hirar mu na yaushe gamo cikin raha da kewar juna, annuri da dariya ya ƙi yankewa daga fuskana har sai izuwa lokacin da Abasiya tayi wata maganar da ta daki kwakwalwata ta kuma munana ƙalbina, na nema dukkan annurin nan na rasa kamar anyi kuka an ɗauke.

"Na'ima ina ita facalan nakin?, naga tun zuwan mu bamu ganta ba. Hmm yanzu haka kike haƙurin zama da facala wanda kaidinta yafi na kishiya yo wallahi ni da in zauna da facala gwara Aminu ya auro min kishiyoyi uku rigis lokaci guda mu zauna tare. Cabɗijam ina zan zabari wannan wahalar".

Taune leɓɓana nayi kafin na furta"Abasiya kenan ni wallahi duk babu wannan cikin zamana da Maman Hanan, dan Allah kar ki sake zuwar mini da makamanciyar wannan zance. Yanzu idan da tana cikin gidan nan taji wannan zancen me kike tinanin zai faru?, gaskiya bana son irin hakan".

"Gaskiya kam Abasiya kiyi wa bakinki linzami, in taji wannan zancen ai sai ki haddasa musu rigima cikin zaman su". Furcin Balkisi kenan na ɗauke kaina gefe ban jiyo ba sai da tayi wata zancen.
"Ƴar uwa yanzu daga gida muke nake jin wani zance, wai Malam Yusuf yaje sun tattauna da su Abba akan maganar komawarki makaranta. Gaskiya naji miki daɗi wallahi burinki zai cika koda mu bamu sama damar yi ba ke in kinyi kamar mu dukka ne muka yi, wataƙil ta sanadiyarki ma su Abba su fahimci muhimmancin karatu ga ɗiya mace har sauran ƙannen mu na gida suma su sama damar yi".
"Haka ne Balkisu, amma har yanzun akwai sauran rina a kaba domin akwai wata babbar ƴaƴar su wacce bata amince ba kuma basa gudanar da wani abun ba tare da amincewarta".
Dafa kafaɗata Balkisu tayi tare da sausauta murya ta shiga faɗin"Na'ima in sha Allahu ina ji a jikina sai kin cika wannan burin nakin, duk wata nasarar da za ki ai ƙara ɗaga kimar gidanmu za ki yi. Nima da ina da irin kwakwalwarki ai da na roƙi da Aminu na koma amma ina".
Murmushin dole na sakar mata, ina hange Abasiya da ta yi mana kunnen uwar shegu tamkar bata jiyo abunda muke faɗi, daga bisani ma ta shiga latsa wayarta.
Mun ɗau lokaci muna hirarmu har aka yi ƙiran sallan zuhr na ɗaura mann girki muka ci, har yanzun Maman Hanan bata dawo ba tare da Hanan yaaya Yusuf suka dawo suka gaisa da su Abasiya, Balkisu sai tsiya take masa wai ya mayar dani matar kulle ko gidajen su ban je ba tun bayan biki. Murmushi kawai yayi musu tare da alƙawarin cewar duk zanje musu.
Wanke Hanan nayi na sauya mata kaya, taci abinci sannan nayi mata shirin islamiyya, Abasiya sai faman tsaki take tsirgar mini tana faɗin"Ke dai Na'ima wallahi rayuwarki ta shiga uku, ke ba ki haifa ba amma an barki da reno ko amarci ba ki gama ci ba an barki da renon ɗiyar wasu ke kika ga za ki iya aikin wahalar da ba sannu balle madalla".

Murmushi kawai nake sakar mata, har na gama shirya Hanan ta wuce islamiyya har wannan lokacin mamanta bata dawo ba, har su Abasiya suka tafi na gyare gidan tsaf nayo alwalan sallan asr Maman Hanan ta dawo sannu da zuwa nayi mata nayi shigewa ta ɗaki nayi salla.
Sai da aka yi sallan magrib Yaaya Yusuf ya dawo, tunin na haɗa masa ruwan wanka na kai masa ya shiga yayi sannan na ciyar dashi abinci. Kallo ni yayi yace"Ba ki tambaye ni yaya muka yi da yaya Auwal ba?".
Sai da na sauƙe numfasi na ce"Yaaya kenan so nake ka huta sannan na taso maka da zancen".

"Na sama shi mun tattauna akan batun, kuma ya bani dukkan goyan baya akan hakan. Mun sama ƙanin mahaifinmu da maganar shima kuma ya amince ya kuma tunkari Anty Binta da zance har yayi nasarar shawo kanta, yanzu dai a taƙaice ta aminc....".
Ban bari ya ƙare zancen ba na bi na ƙananneye shi ina jero masa kalaman godiya. Ban dakatar dani ba sai da na tsagaita don kaina kana ya ɗaura da"Har wajen su Abba ma naje kuma alhamdulillah suma sun amince, kar kiso kiga murnar da yaya Majid yayi, sunce gobe na kai ki".
Sosai naji jikina yayi sanyi, lura da hakan ya sa shi tabbatar mana da cewar babu komai. Gama bashi abincin nayi a gurguje ya fice masallacin sallan isha'i. Da murnata na fito ina shaidawa Maman Hanan, sosai na ke iya hango tsantsar murna ita ma cikin idanunta har rungume ni tayi, tana yi mini fatan alkhairi hakan ya ƙara tabbatar mini da cewar tabbas nayi sa'ar samun facala saɓanin yanda ƴan uwana suke tunani tare da yi wa dukkan facala kuɗin goro. Na raya daren ranar da sallan dare sosai tare da addu'ar Allah ya sa na fara wannan karatu cikin sa'a da nasara.
Wayewar safiyar ranar muka yi waya da Salma, taji daɗin ƙiran da nayo mata sosai na shaida mata komai sosai tayi mini fatan alkhairi. Sallamar Anty Binta da suka yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya ya sani sakin wayar ba tare da na katse ƙiran ba, saboda matsananciyar bugun da ƙirjina yake yi tamkar zai faso nama da fatana ta fito waje.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un". Na furta cikin sarƙafewa harshe ina jawo numfashina da yake cushewa da matuƙar ƙarfi.


MATAN AREWA

©Maimunah TIjjani Iyam

_________________________________________

Page 1⃣8⃣


Tun kafin na fito naji wasu zuffa mai maiƙo ya jiƙa mini goshina. Ajiyar wayan nayi na fito da hanzarina tana tsaye a tsakar gidan Maman Hanan tana shimfiɗa mata tabarma sai da ba rusuna na gaida ta ƙara yatsine fuska tamkar wacce taga ɗanyen kashi sakin yau, bata ce da ni uffan ba ta wuce tayi zamanta bisa tabarman da Maman Hanan ta shimfiɗa. Banyi ƙasa a gwiwa ba na kuma jan ƙafafuna na zauna na buɗe baki da zummar ƙara yi mata wata gaisuwar da sannu da zuwa ta dakatar dani ta hanyar ɗaga mini hannunta alamar bata son jin komai daga gare ni kafin ta shiga faɗin"Ba gaisuwarki ce ta kawo ni cikin gidan nan ba, abinda ya kawo ni shi zanyi nayi ficewa ta na bar muku gidanku tunda yazo kowa ba ganin kimata yake yi ba balle ayi mini kallon mai gashi".
Bugun da ƙirjina yake ni ya tsananta wanda nima kaina na gaza gano dalilin harbawan natan. Zancen da Anty Binta ta ɗaura dashi a harsale shi ya dawo dani daga karatun wasiƙar jakin da na dulmiya.

"Auwal da Yusuf sun nuna min iyaka ta akan su, sun nuna min ban isa ga gidansu ba balle ku iyalansu".
Tsagaitawa tayi na wucen gadi, na ɗago kaina cikin sanyin jiki muka haɗa ido da Maman Hanan kafin muryar Anty Binta ta katsar damu"Yau kimanin shekaru goma sha biyu da rasuwar iyayenmu tun Mahmud bashi da wayo nake riƙe da ƙannena har aurena na farko ya sama matsala domin su amma ban karaya na yatsar da amanar su da iyayenmu suka damƙa min ba, basu taɓa yi min musu ba balle bijirewa umarnina ko kara na ajiye basa tsallake ta balle suyi yunƙuri keta hukuncina. Sai yanzu har zamu yi musayar yawo tsakanina da Yusuf da Auwal har da kai ƙarata gaba, duk akan ki Na'ima kin cuce ni kin tarwatsa min kan ƴan-uwa duk domin cimma muradin ranki wanda ko a addinance nasan bani da laifi don na hana ki komawa boko kamar yanda kike so, sha'awar samun rabauta nayi miki ta hanyar inganta miki gidan aurenki amma kika saka ƙafa kika shure. Burinki ya cika tunda Yusuf ya haɗa ni da wanda babu yanda na iya dashi kije kiyi bokon amma ki sani dukkan abinda ya taso sanadin wannan karatun wallahi ba zan ɗauka ba, haka nan Yusuf ko da amincewarsa ko babu zama a tsakanin ku zai zo ƙarshe".
Dirsham nayi zaman ƴar bori take jikina ya ɗauki rawa ba kaɗan ba kalamanta suka daki kwakwalwata, ban iya cewa

Please Login or Register in order to submit comment