Join Our WhatsApp Group

DARE DA RANA Complete Hausa Novel Document by DARE DA RANA


DARE DA RANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23907



DARE DA RANA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 125.22 kb

File Type: txt

Views: 1097+

Download: 230+

Last download: 2 days ago

Description/Story: DARE DA RANA
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Nazir Adam Salih
DARE
Uku Ga Watan Maris Alif Dubu Daya Da Tari Tara Da Chasa'in Daidai.
3-March-1990
.
KASHI NA FARKO
"Da mota, mata, da mai mita, zama dasu sai haƙuri Jamilu
Samarin biyu suka bushe da dariya, wanda ke maganar wani dogon saurayi ne baƙi mai dogon gemu, yana sanye da doguwar jallabiyya da rawani gami da dogon carbi mai kwandala-kwandalan 'ya'ya yana jansu da kyar kamar kwallon goruba. Sunan saurayin
USTAZU ABUBAKAR, abin da ya kawo shi kuwa shi ne, taya abokinshi JAMILU murnar Bikin aurenshi da aka daura jiya, to amma shi Ustazun bai samu damar Zuwa ba.
Saurayin da akewa bikin auren, wato ANGO Jamilu wankan tarwada ne mai matsakaicin tsayi da dara-daran idanu, haka nan duk Lokacin da ka dubi fuskarsa sai ka ga kamar zai yi dariya, sanye yake da babbar riga da 'yar cikinta da wandonta na shudiyar shadda 'yar ubansu, hular dake kansa dara ce baka wacce tayi dai dai da bakaken takalman da ke sanye a kafafunsa suna daukar idanu kamar madubi.
Duk wannan abin dake faruwa a wata fankadediyar farfajiyar wani gida ne ma'abocin shuke-shuke na itatuwan ƙawa da furanni, daga can ƙuryar farfajiyar gidan kuma ƙaton gini ne irin na mutanen kasar Sin, wanda duk kusan inda ka duba a jikin ginin daukar idanu yake yi a cikin dan abin da ya rage na daga hasken yammacin ranar, a nan ne ake sa ran in anjima kadan misalin karfe takwas zuwa tara na daren ranar za a kawo amaryar Jamilu wato RUKAYYA ta tare a ciki.
.
Ba samarin biyu bane kawai a farfajiyar gidan, domin duk inda ka duba a farfajiyar gidan samari ne da 'yan mata ana ta al'amura nan da can, wasu ka hangesu a gindin bishiya su biyu suna tattaunawa, wasu a tsaye, wasu kuma a farfajiyar. Wannan hada-hada ta kawayen amarya ce da abokan ango, suna ta kokarin shigar da kansu ko ta wane hali, domin tuni wasu sun lashi tokobin anan suma zasu samu matan da zasu aura.
.
Wadannan shagulgula dake faruwa a tsakanin samari da 'yan matan amarya, su suka sa Ustaz Abubakar ya kirawo ango Jamilu gefe guda yake yi masa nasiha.
"Allah..kuwa Jamilu. Zama da mata da mota da mai mita sai hakuri...."
Ustaz Abubakar ya ci gaba da magana, sa'ar da suka daina dariyar.
"in tayi maka laifi sai ka yi mata nasiha, ka fada mata abin da Allah da Manzon sa suka ce, ba wai ka hau ta da fada ba."
"To, na gode Ustaz, in sha Allahu zan kula da duk abin da ka ce."
Ango Jamilu ya ce yana dubansa cikin murmushi, sannan sai ya ce a cikin zuciyarsa.
"DA KASAN TAƁARGAZAR DANA TAFKA da sai ka kai gobe kana yimin wa'azi, da wani gemunka kamar burushin wanke kwalba."
"Yauwa Jamilu, don haka nake son yi ma nasiha, domin kana dauka. To Alhamdulillah, ni zan koma, domin wannan kade-kaden diskon naku duk ya fara rudani...in banda abinka maimakon ka tara Mallamai ayi maka saukar Alkur'ani mai tsarki sai kuma ka tara samari da 'yan mata ana ta irin wannan raye-rayen banzan?"
Ustaz Abubakar ya ce, lokacin da yake kallon samari da 'yanmatan dake farfajiyar gidan suna dansewa abinsu, jikinsu na bin yanayin kidan zamanin dake ratsowa ta cikin ɓoyayyun sifiqun dake cikin shuke-shuken furannin da suke gidan.
"In da don wannan ne ma ai da sauƙ, don ma baka san mugun ta'annatin da na yi ba ne."
Jamilu ango ya ce a cikin zuciyarsa.
"Dubi fa don Allah..."
Ustaz Abubakar ya ci gaba.
"kana ganin yadda maza da mata ke cudanya....Am...Wa'iyazubillahi, dubi wata yarinya can zaune akan cinyar wani. Tab! Duniya tazo karshe. Ni zan tafi Jamilu, wannan ba gurin zuwa na bane, kai dai Allah Ya baka zaman lafiya da amaryarka. Su kuma Allah Ya shirye su."
Samarin biyu suka gaisa da juna, sannan Jamilu ya rako shi har zuwa kofar gidan, sa'anan suka rabu cikin raha.
.
Jamilu ya juyo zuwa cikin gidan zuciyarsa cike da tunane-tunane, lokaci-lokaci duk sa'ar da ya tuna sai gabansa ya fadi ras! Wannan abu duk shi ya hana shi walwala sosai, gashi dai duk taron bikin nan don shi ake yi amma a banza, su suke jiye masa dadin bikin, amma shi akwai abin dake addabar zuciyarsa.
Duk da yake dai ITA CE TA AMINCE amma har yanzu yana jimantawa, domin kuwa a wasikar da ya aika mata ya so ayi abin ne cikin gaggawa amma taki gashi kuma yau kusan wata guda kenan amma shiru.
.
Jamilu yasan cewar kowanne kwana daya da akayi a cikin watan abin hadari yake kara zama, to amma yaya zai yi da ita. Tunda ta ce ya yi jiranta har sai ta shirya.
A dai-dai lokacin da ya kai farfajiyar gidan, sai babbar ƙawar amarya BADURA ta baro inda suke tare da sauran kawaye, ta tari ango Jamilu tana murmushi.
"Ango Jamilu meke damunka ne, ni duk naga kamar ranka a ɓace yake, kai da ake tsammanin zaka fi kowa walwala, sai kuma ka yi jugum?"
Jamilu ya yi mata murmushin karfin hali, domin kuwa ji yayi tambayar tata ta sake tuno masa da abin, shi kuma duk lokacin da ya tuno da abin sai yaji kamar ana buga masa guduma akan sa. Musamman ma idan ya tuna da irin barazanar da ta yi masa a daren da ya gabata.
"ke fa halinki kenan Badura. Ba kya rabuwa da surkulle, in ban da abinki me kuma ya kawo zancen bata rai ?
Badura tayi 'yar dariya ta ce
"Haba Jamilu, saidai kawai ka ce ko abubuwan biki ne suka yi maka yawa, amma ai kowa ya sanka ya san ba haka kake ba, kai da kullum kake cikin fara'a?"
"Gaskiyar ki Badura, Wallahi duk bikin nan ne ya ruda ni."
Jamilu yayi mata karya. Sannan don gudun kada ta ci gaba da yi masa tambayar, sai ya yi sauri ya ci gaba da cewa.
"Karfe nawa zamu tafi daukar amarya ne."
Badura ta harare shi tana murmushi.
"Af har ka fara matsuwa ne? duk abinka dai ai ka bari duhun dare ya shigo."
Ta dubi agogon dake ƙyalƙyali a hannunta sannan ta ci gaba da cewa.
"Nan da karfe takwas na dare za mu tafi, ina fatan dai kun tanadi motocin daukar amarya?"
Jamilu ya sake yin murmushin yake ya ce.
"Shi ne dama dalilin da ya sa na tambayeki, ba wai zumudi ba ne, domin a yanzu haka muna da motoci ashirin a hannu, kuma ban da su muna sa ran zuwan wasu abokanmu guda uku duk da motocinsu, a cikin su ma har da mutuminki."
Badura ta harare shi.
"Wani mutum ne nawa kuma?"
"Ah, kin manta dashi ma kenan? To SANI ALIYU nake nufi, wanda na ce zan bashi kyautarki."
Badura ta murguda baki gami da tafa hannu.
"Allah Ya kiyaye, wannan gurgun mai kafa daya da rabi, ala suturi buƙui, kafa kamar lawurje, ina shi ina ni? Kai ka ga Jamilu wallahi ka fita hanyata...in ka yi wasa sai mu ƙi kawo maka amarya yau."
Jamilu ya fashe da dariyar karfin hali.
"Ayi hakuri manyan kawaye , aure dai ai an riga an dau..........
Tunaninsa ya katse...ƙirjinsa na bugawa sa'ar da ya tuna da kalaman LARAI lokacin da take cewa.
"BANCE KADA KAYI BA TO AMMA FA KASANI DOLE NIMA SAIKA AURE NI
.
Badura ta dubeshi cikin mamaki sa'ar da ta ga subucewar murmushin da ke a fuskarsa "lafiya ?" Jamilu ya gyada kai gami da murmushin karfin hali.
"lafiya lau, tunanin yadda zan zauna da amaryata Rukayya nake yi."
Ya dada sheƙa mata ƙarya a karo na biyu.
**** **** ****
Karfe takwas da 'yan mintuna na dare, amma farfajiyar gidan kamar rana, wannan yana da nasaba ne da ɗaruruwan kwayayen lantarkin da aka mammaqalasu a jikin bishiyu da furanni 'yan qanana masu tsananin haske tarwai dasu kamar taurari.
.
Amaryar Jamilu Ruqayya ta bayyana, sama da motocin samari da 'yanmata talatin ne suka rakota, hudu daga cikin motocin iyayen mata ne a ciki.
.
Har yanzu ko'ina in ka duba samari da 'yanmata ne rakuɓe a guri-guri suna tadi, yayin da kuma can cikin gidan, dakin amarya cike yake da kawayenta da kuma tsofaffi, wasu na zolayarta wasu kuma na yi mata nasiha.
Ba'a dade ba iyaye mata da suka rako amarya Rukayya suka fito, sannan aka kwashe su a motoci aka mayar dasu. Sannu a hankali samari da 'yanmata suka fara watsewa, kafin karfe tara gidan yayi shiru kamar ba shi ba, duk an gama watsewa daga ango Jamilu sai manyan abokansa guda biyar wadanda tun suna yara suke tare.
Abokan guda biyar suka tasa shi a gaba domin zuwa sayen bakin amarya irin na al'ada.
Tun kafin su shiga kawataccen tangamemen falon amarya, kamshin turare iri-iri ya fara bugun hancinsu, wani turaren na jikin amaryane, yayin da wasu kuma kamshin turarukan daga jikin kawayen amarya yake tashi.
Suka shiga cikin dakin da sallama. Manyan kawayen amarya uku suka amsa musu cikin farin ciki da kissa, gami da girmama manyan abokan ango.
.
Abin gwanin ban sha'awa, domin duk manya-manyan kujerun da suka yiwa dakin kuri, amaren basu damu da su zauna akai ba, maimakon haka ma sai duk suka zauna a tsakar dakin shaqatawar, kan lallausan kilishi mai numfashi suka sa amarya Rukayya a tsakiya, wacce ta sha ado dan uban su mai suna fada qauyanci. Tana zaune abinta tamkar wata a cikin taurari. A sarauce kuwa kamar gimbiya a cikin kuyangi.
Tsawon mintuna talatin aka yi ana musayar kalamai, tsakanin qawayen amarya da abokan ango, kamar dai yadda aka saba a al'ada.
Abokan ango suka miqe, sannan sai Nasir Ishaq abokin ango na hannun dama, ya dubi su Badura qawayen amarya ya ce.
.
"ku ai sai ku mu mayar da ku gida ko?"
Nan da nan suka miqe cikin fara'a. Badura tana tsokanar amarya Rukayya.
"to amarsu ta ango, mu zamu tafi mu barki da shi, dama na san Allah Allah yake yi mu tafi."
Aka fashe da dariya. Sannan ango Jamilu ya sako su a gaba su duka domin ya yi masu rakiya.
.
'Yanmata da samarin suka ratso ta wani qaton dakin shaqatawa na biyu, wanda shi ne zai kai su har farfajiyar gidan, suna tafe suna tadi abin gwanin ban sha'awa da faranta xuciyoyi.
Kai bama su ba hatta ango Jamilu dake fama da fargaba a xuciyarsa wacce ke qunshe da mummunan sirri a lokacin sai ya ji ransa fari tas! Musamman ma sa'ar da suka yi ido biyu da amaryarsa Rukayya. Sa'ar da ta dube shi da murmushin Allah kashe ni don dadi. A dan wannan lokacin ango Jamilu sam ya manta ma da tashin hakalin dake gabansa.
A daidai lokacin da suka zo tsakiyar dakin shaqatawar ne, to wayar tarho din ta dauki ruri wur! wur!! Gabadaya samari da 'yanmatan suka yi shiru lokaci guda, sannan suka dubi ango Jamilu.
Jamilu ya ji gabansa ya fadi ras! Shi kansa bai san dalilin faduwar gaban nasa ba....to amma sai wata zuciyar ta ce dashi.
"kai marar gaskiya, amaryarka ce Rukayya."
Tunanin cewar a cikin dakin da suka baro amaryarsa kuma akwai kan tarho a cikin dakin, shi ya sa shi ajiyar zuciya, tabbas Rukayya ce.
.
"Ku yi gaba, gani nan zuwa, mutuniyar ce.".
Jamilu ya ce dasu yana kashe musu idanu. Samari da 'yanmatan suka fashe da dariya, sannan suka fice daga dakin zuwa farfajiyar gidan kowa na fadin albarkacin bakinsa.
Jamilu ya zauna akan kujera, sannan cikin murmushi sai ya dauki kan wayar ya tausasa murya ya ce.
"Hello, Darling Rukayya ce?"
"Ba ita ba ce..Jamilu ni ce!"
Ya ji kamar duniyarce ta ruguxo masa a tsakiyar gadon baya. Nan da nan wani zazzafan gumi ya fara sartu akan fuskarsa har zuwa gadon baya, duk duniya ya san babu mai irin wannan murya sai mace daya..macen da ya so a da, a yanzu kuma ya tsana fiye da kowacce mace a duniya.
"LARAI!....ke ce?"
Jamilu ya tambaya a cikin kaduwa, lokaci guda kuma ya dubi agogo karfe tara har da minti biyar, menene dalilin bugo masa waya kuma a yanzu ?"
"Ni ce Jamilu..ya ya amaryar taka?"
Jamilu ya katseta ransa a bace.
"kin ga Larai, fadi abin da ki ke so, tare muke da baƙi."
"Af, Allah Ya baka hakuri mai amarya, wato Jamilu abin ma tsakanina da kai har da tsawa?"
"Larai me ki ke so ne?"
Jamilu ya yi saurin katse ta a karo na biyu, shiru na dan lokaci a can bangaren. Daga baya kuma ta ce
"Jamilu yanzu nake son MUJE A ZUBAR DA CIKIN DA KAYI MIN!"
.
Jamilu ya ji kamar an soke shi da kibiya, nan da nan ya karaya.
"Haba Larai...daren farko kenan fa...ni da amarya ta...kuma..."
Ka cika son kanka da yawa Jamilu, wato kai ka fi son farin cikinka ko? Ni ka gama dani, in naso in mutu ko? To Wallahi bari ka ji. Yanzu-yanzun nan nayi niyyar tafiya...."
Ki yi min hakuri don Allah zuwa gobe, tunda ko likitan da na fadawa bai san da zuwanmu yau ba, kuma ina da baki.
"Ina jiranka a nan KANTI SAUKI nan da minti ashirin. Cikin a jikina ya ke ba a jikinka ba. Amma yanzu lokaci yayi da zai fara komawa kanka...idan baka iso nan da minti ashirin ba to ka same ni a gidan iyayenka don kuwa a can zan haife musu shi."
.
Jamilu yayi shiru, ya ƙanƙame kan tarhon har sai da hannunsa ya fara gumi, sannan ya fahimci cewa kan talfon din dake hannunsa gawa ce.
"Larai...!"
Jamilu ya kira sunanta, shiru bai ji ta amsa ba, ya saki kan tarhon ya fadi qasa, jiki na rawa ya nufi farfajiyar gidan. Sannan murya na rawa ya ce da Badura.
"ke ki tsaya Rukayya tana son magana da ke, idan kun gama ganawar ko mota ta sai na baki, ki tafi kya dawo min da ita gobe."
Lokacin da hakan ke faruwa tuni sauran sun shige cikin motoci biyun dake a farfajiyar gidan, ba a dade ba suka fice daga cikin gidan suna dagaw juna hannu.
Jamilu da Badura suka shigo cikin falon, Badura ta dubi fuskar Jamilu wacce ke diga kamar ledar ruwan sanyi ta ce.
"lafiya kuwa?"
Jamilu ya girgiza kai.
"ina fa lafiya? Baba ce...


Read / Download DARE DA RANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album