Join Our WhatsApp Group

ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA Complete Hausa Novel Document by ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA


ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 133669



ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 28, Jun 2023

Author: Ayusher Muhammad ,

Ebook Compiler : Umar Dalha

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 753.54 kb

File Type: txt

Views: 1645+

Download: 1247+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)

*ZUCIYA*
_kowa da irin tasa_

© *NA AYUSHER MUHD*

1⃣
Duk yanda yaso ya taka burki abun ya gagara gashi a kan gada yake sannan ga motoci na wucewa, cikin rikicewa ya zuro da hannunsa ta window yanawa mutane alamar su matsa akwai matsala, wasu sun fahimceshi wasu kuwa basusan ma me yake nufi ba, wani yaro ya gani ya taho gadan gadan yana kokarin tsallake titi horn ya shiga yima yaran hakan yasa yaran ya kalli motar sai dai kasancewar yarone karami kawai sai duk ya daburce ya rasa ina zai nufa tsoro yasa shi ya karkata kan motar wanda tsautsayi yasa ya afka cikin kokin jikake tim mota ta fada ciki nan fa mutane suka taru dan neman yanda za'ai sai dai inaa mota tuni ta tafi can kasan koki, rukicewa yai ganin motar ta cika taf da ruwa, shi kanshi duk ruwa ya fara cikamai baki nan ya fara kokarin fitowa ta glass din motar wanda yai sa'a a bud'e yake, dakyar ya fito sai dai yana fitowa yaji ya bugi wani abu wanda baisan menene ba ga ruwa ya shakka dayawa wanda yasa ya suma.....



_A Rigar Datti_

Nafi ta d'ago ta kalli mahaifinta wanda yasata a gaba yana zabga mata masifa cikin yarensu na fulani tace " Baffa kayi hakuri wlh ni bansan ya akai kajin nan suka faracin geron nan ba."
Wanda ta kira da Baffa wato mahaifinta cikin tsananin masifa yace " kedai wannan yarinya baki da mutunci dan tsabar wulakanci da asarar abinci har kaza ta samu matsayin cimin gero na? Wanda nine nake wahalar neman kayana bake ba bakuma waccan balagazazziyar uwar taki ba wacce ta d'au kaninki ko kunya ta saida saniya ta ta had'a ta tafi wai saudiya yin takaranci ba? Ni dai wannan masifa ta faru ne tunda na auri waccan tambad'ad'iyar uwar taki wacce ban tambatar da tsatson ta ba."

Nafi ta share kwallar ta tace " Baffa kayi hakuri nasan inna taba kyau...."
"Gafaracan ni munafuka yimin shiru ai kinji a sara nayi mamakin da zata gudu menene dalilinta na barinki tadau namiji yanzu da alama na fara fahimta."
Ya maida numfashi sannan ya cigaba " kidahumar banza kidahumar wofi to wallahi a hir d'inki da min almubazaranci."
Yana kainan yai waje a fusace, hawaye ta share sannan ta mike ta d'au kwarya ta tafi garken shannun baffa dan yin tatsa.
Tana yi tana 'yan wakenta na fulani, kasan zuciyarta kuwa takaicin tafiyar uwarta da kaninta take sun barta ita kadai a wannan rigar tasu ko tausayinta basayi.
Kasancewar Mahaifinta mutum ne mai bala'in gaske in nace bala'i to fa lalai ina nufin bala'i baya ganin mutuncin komai a rayuwarsa banda na dukiyarsa ko da wasa wani ya tab'amai dabba to fa lalai ya shiga uku, saboda tsabar masifarsar ne yasa ya bar cikin mutane ya dawo can gefen kogi ya dasa nasa gidan wanda ake kira da rigar Datti.

*Dattin* sunan mahaifin Nafi kenan, Mahaifiyar Nafi ba karamin hakuri tai da Datti ba, auren soyayya sukai sai dai kasancewar ita ba bafulatana bace (Kad'o suke kiran hausawa.)ta samu kalubale da dama gun danginsa, har sukazo suka hakura saboda tsantsar mutuncin ta wanda ya ninka na d'an nasu.


Duk yawan shanu da kaji da zabi irin na datti ko da wasa bazakaga an yi abinci mai mutunci agidanba bare har akai da zancen yanka kaxa, koda kuwa ciwo zai kama ta, ya gwammace ya d'au dabbar dabatada lafiya ya fita ya siyar, girkinsu dai baya wuce abin gero ko dawa dan ko shinkafa ba bari yake a ci ba.
Iya tsananin hakuri Matarsa tayi dashi ganin bazai tab'a canzawa ba haushi ya kamata ta d'au saniyarsa ta saida ta kuma dauke karamin danta kanin nafi ta gudu dashi Saudiya inda 'yar uwarta take da zama tana kasuwanci (Takaru).

Samari da dama suna san Nafi dan in taje Talla cikin gari abin shawa duk da ba kaya dayawa gareta ba sai dai zakaga kayanta kullum tsaf tsaf gata ba laifi tanada kyau.
Duk yanda samari suka kai ga santa babu mai iya tunkarar ta dan kowa na tsoron hada zuri'a da Datti acewarsu duk wanda ya aureta sai dai yai kayan daki da kansa sannan har cikin gidansa Datti zai dinga zuwa yana zazzaga masifa.

Nafi kam haka nan take zaune da mahaifinta a rana duk shiga da fitar da zaiyi da masifar dazai mata.


******
Ajiyar zuciya Nafi tai a sanda ta gama yin tatsar, ta mike ta dau bokitin tai cikin gida.

Tana ajiyewa a ciki ta dau wani bokitin dan d'eboma dabobi ruwa da kuka daura sanwar dare.

Tad'anyi tafiya kadan ta isa babban kogi wanda ke bayan gidansu kadan, kallan katon kogin tai yau sam ba kowa ko fulanuwa masu kiwo da suke tsayawa ba dabobinsu ruwa yau basanan, tadanyi tsaki kadan cikin yaransu na filo tace " yau dai da alama banida sa'a ko mutanen da muke 'yar hira dasu wani sa'in ban tarar ba." Takarasa maganar tareda gangarawa kasan Kogin.

Zama tai adan bakin kogin tasa kafafuwanta acikin ruwar tanadan bubugasu kadan waka take dan yi tana murmushi ita kadai, rayuwarsu da mahaufiyarta da kaninta Gaddafi take tunowa.

Ganin rana na neman faduwa yasa ta mike tadau d'an karamin kokonta ta shiga deban ruwan tana zubawa a bokiti, ta dau bokitinta da niyyar tafiya daga d'an gefe inda ruwa ke korowa taga kamar takalmi, mamaki ya kamata can kuma tadan girgiza kai kadan tace " Oh ni Nafi yanzu kila wani bafulatanin ne ya manta da Takalminsa, ba mamaki gobe yazo yai ta neman inda yake."

Karasawa tai kusa da takalmin tana cewa " bari ni in dauka tunda akusa nake sai in ajiye gobe na fito in rataye musus ko a bishiya ne."

Mamakinta ya tsaya ca a sanda tasa hannu dan ciro takalmi sannan a daidai lokacin ruwa ya koro sannan ya koma hakan ya bata damar ganin ashe kafa ce ta mutum kwance a cikin ruwa.
Da sauri ta saki ta kalmin sannan ta kurma wanu ihu mai kara wanda ruwan sai daya amsa, sai dai abin haushi babu kowa agun, idanunta a runtse suke tam ta had'a hannayenta biyu alamar roko tana cewa " Yahkuri Aljanin ruwa wallahi Allah bansan kai bane kake hutawa, natuba kwai ka yafemin wallahi ba ruwana ba kuma zan sake ba."

Tana gama rokonta na shirme ta dan bud'e ido daya cikin tsananin tsoro sai dai yananan a yanda ta barshi, baya ta danyi tana cewa " Kayi hakuri dan Allag ka koma makwancinka in ma fatalwa ne ni wallahi ba ruwana da kai."

Nan ma tad'an sake kyalla ido kadan, sai dai yananan a inda yake, dabarace ta fado mata akan lale ta mike ta falfala da gudu hakan zai fi mata sauki, juyawa tai ta ga lalai fa ba kowa ai kuwa da wayau ta tattare zaninta ta juya tai baya a guje kai kace Zaki ne ya biyota ko bokitin ruwan bata tuna dashi ba.

Gida ta nufa da uban gudunta, tana shiga ta shiga yin haki na tsabar tsoro, Datti dake tsaye a tsakar gida ya kalleta cikin takaici yace " To dabba da alama kema bakida maraba da tinkiya meye hakan kuma?"

A tsorace ta daidaita tsayuwarta tace " Baffa aljani na....."

Yace kiga abinda yafi aljani ma makaryaciyar banza da wofi dan tsabar iskanci dama ba ruwa kika tafi debowa ba? Ai kin sani sarai dabobbi ba ruwa a gunsu."

Sai a lokacin ta tuna da abinda ta fita yi cikin sanyin jiki ta fita, tana tafi tana dan share kwallarta aganinta ya kamata mahaifinta yaji a wani hali take ciki.

Da komawarta idanunta suka sake dira kan wannan mutumin, har ta dau ruwanta zata tafi wata zuciyar tace "Yanzu Nafi in mutum ne fa ya fada ruwa?"
Da sauri ta kara kallan gun, tsoro ne fal a ranta, addu'a ta shiga yi tana takawa a hankali idanunta kuma a rufe wai ita a dole so take inta isa idanun nata na rufe zata zare mai takalma ta gani ko da kafafu.

Haka tai ta tafiya idanu a rufe jitai ta yi tuntube kafarta ta harde saboda tsoro jikake tim ta fada kan wani abu, bata San sanda ta bud'e idanunta ba cikin tsoro ta kalli inda ta fada, itadai tasan lalai akan abu ta fada hakan yasa ta kallin kasa, ganinta kwance akan mutum yasa ta kara calla wani kara mai sauti......

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_kowa da irin tasa_

© *NA AYUSHER MUHD*

2⃣


Kanta ta sake cusawa kan mutumin duk ta rikice, can ta tuna inda tasa kanta hakan yasa ta mike da sauri, jikinta na rawa, sai dai a wannan lokacin tsoronta yadan ragu ba kamar da ba.

Hannu tasa ta zare takalmi mai saucikin dake kafarsa, sannan ta zare safar kafa ta gani kamar ta mutum sai kuma tausayin wanda ke kwance ya kamata, hannunsa ta kamo ta shiga kokarin jawoshi daga cikin ruwan, da kyar da nishi ta samu tadan jawoshi kadan, nan fa ta shiga kokarin murgunashi, nan ma da kyar da numfarfashi ta samu ta juyashi, tsugunawa tai a gabansa tana kallanshi.

Tsoro ta fara ji kardai ya mutu? Nan tasa hannunta a sai tin hancinsa ta dan dade kadan jin baya numfashi yasa tsoro ya kara kamata, idanunta suka fara tara kwalla, hannunta tasa a saitin zuciyarsa, dariya ce ta bayanna a fuskarta a lokacin dataji bugun zuciyarsa.

Ta rufe fuskarta alamar kunya tace " Da ranta wallahi." Ta sake yin dariya tace " Wlh da ranta Allah da gaske."
Ta sake dariya.

Fuskarta ta zuro daf da tashi tana kallo, ba fari bane sannan kuma ba baki bane yanada kyau, hancinsa dogone, ta d'an yi murmushi sannan ta kalli kayansa tace " Kad'o ne wannan kam, sannan da alama bama dan nan garin bane daga birni yake." Baki tad'an turo kadan ganin ita kadai take maganarta sannan ta shiga tunanin yanda zatai ta dawo da numfashinsa.

Hannu tasa ta shiga danna mai kirji tana san ruwan daya shakka ya futo, sai dai ina, ya shaka da yawa duk yanda ta zake tana dannawa ba alamar motsi a tattare dashi.

Idanunta ne suka ciciko, ta kalleshi tace " Dan Birni ya zanyi?"

Ga ba kowa a gun, ta kafeshi da ido tana kallo jitake kamar tai ihu, tunawa tai sanda wasu fulanuwa suka ciro wani yaro daya fada ruwa kwanaki, tana kallo bayan sun danna mai kirji bai farfado ba sai wanda ya danna mai kirjin yasa bakinsa a nasa ya huramai iska alokacin mutane sukai ta ce masa dan iska, babar yaran tazo ta kwace danta itama tana masifa.

A hankali ta matso itama da shirin kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace " Dan Birni ba iskanci zan maka ba kawai iska zan hurama, kaji? inka warke xan baka hakuri."

Nan ta sa bakinta cikin nasa ta shiga huramai iska iyakar karfinta, sai datai tayi sannan can sai yadanyi tari sai ga ruwa dayawa ya zubo daga bakinsa, idanunsa ya bude a hankali ya kalleta, ta kifkiftamai ido tace " Hannu? Kin ganni?"

Gani tai ya maida idanunsa ya rufe, sai dai yanzu numfashinsa na fita sai dai dad'an sauri yake fita, tai shiru tace " ya zanyi? Bacci yake? Ga dare nayi?"
Jijigashi ta shiga yi tana cewa " Karkiyi bacci anan dan Allah kiyi hakuri ki tashi."

Sam bataga alamar motsi a tattare dashi ba, ga gari ya fara rufewa, da sauri ta mike ta suri bokitin ruwanta ta nufi gida, tana shiga ta waiga taga bataga Baffa ba, ajiye ruwan tai ta karasa gun dabobbi ta dauko baro ta fito da sauri.

Inda ta barshi anan yake babu alamun ya motsa, nan fa ta shiga kokarin d'orashi akan baron, sai dai ina.....sam ta kasa.
Duk wani karfi datake tunanin tanadashi ta sake akan mutumin sai dai daga ta dagoshi sai su fad'i tare, saboda rinjayarta dayake yi, duk su biyon sunyu butu butu dasu da jikakkiyar kasa, banda numfashin wahala ba abinda takeyi, ga duhu ya kawo kai, nan ta cigaba da gwadawa, dakyar da sid'in goshin wahala ta samu ta d'aurashi, tana daurashi hannunta ya kume ajikin baron.

Kara tad'anyi saboda zafin dataji, sai dai tsoron rafin ta keyi dan duhu ya fara rufewa, da sauri ta shiga tura baron, sai dai dakyar shima take turawa kasancewar ba siminti bane ko kwalta a gun, iya wahala Nafi taji a wannan lokacin, har ta samu ta isa gida, tai sa'a baffa na kewaye (ban d'aki ) hakan yasa ta tura baron zuwa d'akinta tasani sarai mahaifinta ko wani ne zai mutu bazai taba yanda a kawoshi gidanshi ba koda kuwa dan uwansa ne bare wannan dabatasan inda ya fito ba.

Can gefen dakinta ta sa tabirmar datake kwanciya a kai ta shimfida zannuwa guda uku sannan ta shiga kokarin saukeshi, wannan karan batasha wahala sosai ba sai dai shi yadan kumu da bango garin saukeshi.

Nan tasamai pillow ta kwantar dashi, itama nan ta zube ta kwanta dan tasha bakar wahala.

Batai minti 3 a kwance ba taji muryar Baffa yana kwalla mata kira " Ke Nafi kina inane?"
Dasauri ta mike ta kara jan labulen dakinta tai waje tace " ganinan Baffa."
Yai tsaki yace " Bakida hankali ne zaki d'ebo ruwa baki zubama dabobin ba shinr zaki dangwarar anan? Ko ni kike jira in kai musu?"

Kallan ruwan tai tadan yi kasa dakai tace " cikinane yadan murdamin kadan shiyasa......"
"Ciki? Zancen banza kenan, dan cikinki ya murd'a sai ki barmin dabobi da kishi ruwa? Sannan ba madai kina nufin bokiti dayan nan kadai kika d'ebo ba ko?"

Idanu tadan kifta na mara gaskiya, Datti ya shiga tafa hannu na mamaki yace " Lalai zance kwal ubanki kuwa a gidan nan, banza wacce mahaifiyarta ta gudu da kayan sata, sannan da auranta ta tafi yawan karuwanci."

Idanun Nafi ne suka ciciko tai saurin yin kasa da idanunta a hankali tace " kayi hakuri Baffa wlh ba h......"

"Billahilazi kika b'atamin rai goben nan sai in nemi wani can in aura miki, ni dama na gaji da ciyar dake abincin da bakisan darajarsa ba."
Yanakainan yai waje a zuciye.
Tsugunnawa tai agun ta shiga wani...


Read / Download ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

7 months ago

Reply

Inaso sosai

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album