Join Our WhatsApp Group

DAREN GOMA SHA HUDU Complete Hausa Novel Document by DAREN GOMA SHA HUDU


DAREN GOMA SHA HUDU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 71319



DAREN GOMA SHA HUDU

Reading Time: 5 Hours

Added On: 30, Aug 2023

Author: Bintu Seer ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07041195806

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 391.16 kb

File Type: txt

Views: 1492+

Download: 886+

Last download: 2 days ago

Description/Story:
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔


Written By Bintuu Seer



1


This is historical adventure story which occurred during the era of slave trade in one of the biggest and prestigious kingdom in middle east........




K'atoton jirgin ruwa ne irin gari gudan nan yana tafe a saman tekun atlantic ocean cikin tsakiyar daren goma sha hud'u,duniyar tamu gauraye take da hasken farin wata yana hasken ruwan teku,idan mai hange ya qure dubansa gabas da yamma, kudu da arewa babu abunda zaka hango sai ruwan tekun bahar maliya wanda baida iyaka,tamkar gbdy duniyar tamu ruwa ne sbd girman ruwan teku,jirgin ya fito ne daga nahiyarmu ta africa zuwa qasashen sahara.....



A cikin wannan jirgi kowa yana sabgogin gabansa tamkar ba a saman teku suke ba, yawancin fasinjojin wannan jirgi larabawa ne da turawa wanda suke zuwa qasashenmu na baqar fata kwasar al'umma su kaisu qasarsu su maishesu bayi, yanzun ma hknne don kuwa kusan dukkanin baqar fatar daka gani cikin wannan jirgi toh yana daya daga cikin kamammun bayin da suka kamo a qasashenmu na africa,wasu y'an mata na gano cure wuri guda daka gani dukkaninsu sun fito ne daga mabambamtan qasashe don kowacce cikinsu yanayin shigar jikinta ya bayyana hkn, wasu yan fillo na gano sanye cikin shigarsu ta saqi daga ganinsu fulanin ruga su biyar ne kowacce ba baya bace a fagen kyan halitta saida daga qarshen duk na rauna kyawun halittarsu lkcin da idanu na suka sauka bisa kan d'ayan cikinsu dake takure wuri guda ta sanya fuskarta tsakanin cinyoyinta nayi nasarar tozali da kyakykyawar fuskarta wannan yar fillo ne lkcin da wani bature dake gefensu yasa hannu ya dago dakanta ya busa mata hayaqin sigarin dayake busawa,lalle tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan kyakykyawar halitta, tana da dara dara idanu farare tas tamkar madara, bakinta dan mitsitsi ga le6enta pink tamkar ta sanya jan baki, hancinta dodar yake, kanta babu dankwali hkn ya bani daman ganin tsawon gashin kanta, gashin ra6e yake gida biyu rayi kalba, tsawon kalbar ta sauka har duwawunta ga gashin sai kyalli yake don baqine qirin irinna fulanin usul,billah Allah yyi ruwan tsallar madarar kyau a wurin, tsantsar kyau ne kawai daga rabbil izzati babu alqus.....


Jikinta rawa yake,haqoranta na had'uwa da juna ta qara qudundune jikinta a cikin wani kwali dake gefenta don dukkaninsu a yashe suke a qasan jirgin, babbar cikunsu ta matso kusa da ita tana ta6a jikinta tace" bimbii zazza6i kk,jikinki da zafi sosai" tana mata mgn ne da harshen fillanci,shiru ta mata batace komai ba, baturen dake kula dasu ne yazo wurin yana kallonsu sai kuma ya d'ora hannunsa a jikin bimbii yaji da zafi sosai yace"noo" watsa musu harara yyi yana huci don shi abunda ya tsana ya samu mara cikakken lfy a cikin bayinsa,gani yake tamkar asara zeyi kafin ya isa dasu wurin da saidawa,kuma ma ba kowa ne yake siyan bawa mara isashshiyar lfy ba, dafe kansa yyi ya koma ya zauna ya cigaba da busar sigarinsa, wani balarabe dake gefe guda shima tafe yake da nasa bayin ya kalli baturen yace" ita wannan bata da lfy ne" mgn yake masa cikin British English irinna na qasar birtaniyya, d'ago da kansa yyi ya kalli balaraben yace" ehh" tasowa balaraben yyi yazo wurin yana kallonsu sai yyi murmushi ya kalli baturen yace" idan kana so sai muyi musanye na baka bawa mai lfy ka bani ita" tuni baturen ya miqe ya kalli balaraben yana dariya yace" nunamin bayinka sai na za6a dakaina" murmushi balaraben yyi ya nuna masa tawagar bayinsa wadanda kusan dukkaninsu zaratan samari ne majiya qarfi saidai mafi yawancinsu qabilu ne" kallonsu ya dingayi har idanunsa suka sauka kan wani murd'add'en basamuden mutum mai ji da qarfi ya dafashi yace" muyi musanyan da wannan" hk balaraben yasa d'aya daga cikin masu kula masa da bayin ya kunce wannan mutumi ya damqawa wannan bature shi kuma ya taso qeyar bimbii ya kawo masa cikin jerin bayinsa, tana kuka sauran yan'uwanta suna kuka hk don dole suka rabu ita ta koma cikin jerin tawagar bayin wannan balarabe......


A jerin bayin nasa su biyar ne kawai mata kuma kowacce yarenta daban ba wanda yake jin yaren wani, sauran duk maza, tunda ta koma wannan tawagar ta koma tamkar kurma, basa iya mgn da junansu don basu jin yaren juna, zazza6in dake jikinta ya soma tsananta sai rawar d'ari take gashi babu abun rufa hk dai ta takure wuri d'aya, wani saurayi ne d'an qabilar igbo fari sol dashi ya matso kusa da ita ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya rufa mata, jin a rufe ne yasa d'ago dakanta tayi tana kallonsa sai kuma ta komar da kanta kan guiwowinta, mgn yyiwa daya daga cikin masu kula dasu ya miqo masa ruwan sha a wata kwarya ya ta6ata ta d'ago da sauri ta matsa daga kusa dashi don su babban zunubi ne a rugansu namiji ya ta6a mace shiyasa tayi saurin matsawa,miqa mata kwaryan ruwan yyi ta miqa hannunta ta amsa ta soma sha sannan ta miqa masa cikin harshen fillanci tace ta gode.........................





*Wannan novel na siyarwa ne karki soma karanta free pages idan kinsan baki da halin siyan sauran pages wannan shawara ce........Ga wacce ta shirya siye zaki tura #300 ta wannan detail din


acct no: 0100790419

Bank:Union bank

Name: Alhaji shahida Nasir


Idan kin tura saiki turomin da screensht na payment naki ta wannan layin


07041195806





Alk'alamin Bintuu ne👌ðŸ»
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



2


Kwanaki sun shud'e anyi dare dayawa duk sun shud'e amma sukam suna doron ruwan teku suna tfy rabonsu da doron qasa sun jima, duk cikin wad'annan bayi babu wanda yasan qasar da suka nufa abunda suka sani kawai an kamosu daga qasashensu an sakosu cikin jirgi a matsayin kamammun bayi,tunda bimbii ta soma zazza6i wannan saurayin d'an kabilar igbo shike kula da ita yana tausayin bimbii sosai sbd gsky tana da qarancin shekaru, sanyi na ratsa dukkanin sassan jikinsu amma saidai su takure wuri d'aya don babu abun rufa, shi kuwa wannan saurayin daga shi sai wata yar qaramar riga don ya cire rigan dake da kauri a jikinsa ya rufawa bimbii, jirgin nasu ne ya soma tangal tangal tamkar ze kifa kowa cikin wannan jirginsa cikinsa ya d'uri ruwa sbd tsoro, riqe hannun bimbii yyi qam don yaga gbdy ta rikice cikin ikon Allah jirgin ya koma yadda yake normal, kowa ya soma ajiyar zuciya, bimbii a hnkli ta janye hannunta, kallonsa tayi taga alamun shima dai yana jin sanyi amma ya gwammace ya rufa mata jacket dinsa, hannu tasa ta cire rigan daya rufa mata ta rufa masa, kallonta yyi yana qoqarin cire rigan tayi saurin dakatar dashi da hannunta cikin harshen fillanci tace" bana jin sanyi ka sanya kawai" be fahimci mai take fad'I ba amma ya fuskanci abunda takeson yyi, murmushi yyi mata yace"nagode" saurin dago da kanta tayi tana qare masa kallo don tabbas idan har ba kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba kamar hausa taji yyi,tana jin hausa itama 2kad'an don tana fita kasuwa tallan nono, tace" kana jin hausa ne" murmushi ya kuma mata a karo na biyu yace" ehh,amma ni igbo ne daga Abia nk" tace" me sunanka" yace" obinnah" yace"ke me sunanki" tace" bimbii" ya qara nanata sunan nata yace" daga ina kk" tace" ruganmu tana kudu da qauyen lamirde cikin garin gombe" kad'a mata kai yyi alamun ya gamsu, daga shi har ita babu wanda hausar tasa ke fita daidai duk tata suke a hausar amma hk suke dan mgn, bimbii bata da yawan zance amma saita samu kanta da sakewa dashi, cikin tsakiyar daren goma sha hudu jirginsu ya samu isa matattarar tsayawar jiragen ruwa wato Brandford port dake Amsterdam,tunda suka fito daga jirgin nan suke 2kalle kana ganinsu kaga k'auyawa, dole kam suyi k'auyanci don kaf nahiyarmu ta africa ba irin wannan port din, turawan dake kai kawo a wannan port kuwa kallonsu suke tamkar kashi sbd tsabar racism, dukkaninsu babu wanda ze iya fad'ar sunan qasar da suke amma yanayin kalar fatar mutanen qasar ya tabbatar musu qasa masu jan kunne ce wato lardin turawa suke, falmata d'aya da cikin yan'uwan bimbii da aka rabasu tun a jirgi ta saci jiki daga cikin tasu tawagar ta shigo cikin tawagar su bimbii, riqo hannun bimbii tayi tana kuka tace" bimbii zamu rabu gbdy kin ga zasu kuma shigar damu wani jirgin bamu san inda zasu kaimu ba, mudai tamu qaddarar kenan sun rabamu da danginmu sun shigo damu duniya,bimbii ki kula da kanki sannan ki saukar da kanki kiyi duk abunda suka sanyaki don basu da imani zasu iya kashe mutum" kuka suke sosai suna qanqame da juna har lkcin da baturan dake jagorantar tawagarsu ya ankara babu mace daya cikin yan matan nan, suna rumgume da juna suna kuka suka ji an finciko falmata batare da 6ata lkci ba ya sauke mata tagwayen mari a fuska sannan ya jata ya koma da ita cikin tawagarsu, had'esu turawan sukayi suka zargesu da igiya sannan suka tasa qeyarsu suka shige wani jirgin dasu,suna tfy suna waiwayen yar'uwarsu itako bimbii kuka take sosai tana kallonsu har suka shige jirgin,obinnah dake kusa da ita ne ya soma rarrashinta, itama tana cikin alhinin rabuwa da yan'uwanta wani daga cikin masu kula dasu yazo yace ta biyoshi, batasan meze mata ba ita dai kawai batare da gardama ba ta miqe tabi bayansa, obinnah dake gefenta yyi saurin miqewa ze rakata mutumin ya daka masa tsawa dole ya koma ya zauna ita kuwa tabi bayansa suka qarasa wurin wani tsohon jirgin ruwa dake gefen port din, nuna mata kofar jirgin yyi yace ta shiga, shiga tayi shima yabi bayanta, suna shiga gabanta ya yanke ya fad'I don lura tayi jirgin abandon one ne ba kowa cikinsa sai tarin shirgi, bata qarasa rikicewa ba saida taga ya soma zame wandon dake jikinsa, take jikinta ya soma rawa tamkar mazari ta soma ja da baya cike da tsantsar rudewa, murmushi yyi lkcin daya gama zame dukkanin tufafin dake jikinsa ya kalleta yaga yadda ta rufe idanunta ruf sai makyarkyata jikinta yake ta durqushe a wurin tare da daga hannayenta dukka ta soma masa mgn da harshen fillanci tace" ka yiwa Allah ka yiwa annabinsa ka kyaleni karka ketamin haddi niba kafira bace" cikin kuka take roqonsa duk fuskarta tayi 2sha6e da hawaye, shi kuwa tumuqin arne besan ma abunda take fad'I ba don ba jin yarenta yake ba, shima baqar fata ne amma yyi kala da irin mutanen kenya din nan baqine qirin tamkar gawayi asalin african man, matsowa kusa da ita tana ja da baya har takai qarshen jirgin yana biye da ita da murmushin qeta a fuskarsa, hannu yasa yana shirin kamota aka doko kofar jirgin, wannan asalin balaraben ne daya amsheta daga wurin baturen nan, kallon mutumin yyi ransa a mugun 6ace ya soma zaqinsa cikin harshen turanci yace" kai wawa ne so kk kamin asara, kasan dalilin dayasa na amsheta sbd daka ganinta kasan danyar budurwa ce kuma kudin virgins ko wurin saidawa daban yake, shine dan kai dan iskane kk neman mini asara daman all those africans are bunch of animals,bauta ita tafi dacewa daku" hk balaraben nan ya din ga masifa, shi kuwa sai qoqarin sanya wandonsa yake,bimbii kuwa na daga gefe sai ajiyar zuciya take, qeyarta dan balaraben ya tasa ya komar da ita cikin tawagar sauran bayin, obinnah na ganinta ya soma tmbyrta ko sun mata wani abunne ta kada masa kai alamar basu mata komai ba,suna nan yashe a gefen ruwa tamkar ba mutane ba sanyi sai busasu yake sai wurin asuba suka ga tsayawar wani jirgi, yana sauke fasinjojin cikinsa ya soma deban wasu fasinjojin, hk akazo aka tasa qeyarsu suka shige wannan jirgi,kwanansu biyu suna tfy kafin suka soma shiga lardin larabawa, jirginsu ya tsaya ne qasar KUWAIT..... Abdullah bin faisal International port, tun saukarsu daga jirgi wasu zungura zunguran motoci suka soma dibansu kai tsaye kasuwar cinikin bayi aka wuce dasu, yadda ake cin kasuwa saida tumakai ko dawakai hk ake cin kasuwar saida bayi, manya manya keji akeyi ake zuba bayin ciki, suma hk aka zubasu cikin keji, farashin bayin hawan hawa ne wani kudinsa yafi na wani, manya masu kudi da jinin sarauta da masu mulki sukan siye bayin dayawa sukaisu muhallinsu suna musu kowacce kalar bauta amma yawanci jinin sarauta basu daukan baqar fata sai larabawa kalar fatarsu, masu ma'aikatu da gonaki suke siyen baqar fata sukaisu suna musu aiki amma masu daukar boyi boyin gd ma sunyi son larabawa kalar fatarsu suna mugun kyamar baqar fata musumman na africa,bimbii an hadata keji daya ne da wasu yan'mata amma dukkaninsu larabawa ne sukansu kallonta suke suna mamakin wai daman a qasashen baqar fata ma akwai mata masu kyau kamar bimbii, gani sukayi gashin kanta yafi nasu tsawo gata duk cikinsu ta fisu kyau da cikakken diri irinna mata saidai kawai su nuna mata hasken fata, mutanen sai 2zirga suke suna siyen bayin da suka musu,kowanne bawa so yake a siyesa ko Allah zesa yyi dace da mutanen kwarai su masa riqon arziqi,wata balarabiya itama tazo duba bayi kallon daya zaka mata kasan ba daga gdn talauci take ba, balaraben dake dasu bimbii ne yyi saurin tararta ya kawota wurin kejin dasu bimbii suke wai ta duba koda wacce tayi mata, kallonsu take daya bayan daya tana duddubasu tamkar wacce zata siyi akuya, idanunta ne ya tsaya kan bimbii ta nuna bimbii da hannu tace" wannan baqar fata ce koh" balaraben yace" ehh,amma tana da cikakken lfy ba zaki samu mtsl da ita ba" sake kallon bimbii tayi tace masa ya fito da bimbii aikuwa ya bude kejin ya fito da bimbii, batare da bata lokaci ba tayi cinikinta ta biya suka bata certificates of ownership na bimbii har wurin motarta balaraben ya rakata ya budewa bimbii boot din mota ta shiga aka rufeta sannan matar ta shige gdn baya drivernta yaja motar suka wuce, bimbii na bayan boot din motar tamkar akuya tana rakube har suka iso gdnsu sannan aka budeta ta fito, gdn qaramin bungalor ne mai kyau da tsari ga furanni ta ko'ina kunsan larabawa da son hutawa, tsagaya matar ta somayi da bimbii tana nuna mata ayyukan da yake nata ciki har da baiwa wadannan furannin ruwa da kula dasu, duk aikin nata na wajene be danganci cikin bedroms,kitchen ko cikin parlourn ba don wannan aiki daya shafi cimmarsu ko kula da wurin kwanansu basu amincewa da baqi yyi musu ba suna da kyankyamin baqin mutum sosai...


Read / Download DAREN GOMA SHA HUDU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

2 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

2 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album