Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔


Written By Bintuu Seer



1


This is historical adventure story which occurred during the era of slave trade in one of the biggest and prestigious kingdom in middle east........




K'atoton jirgin ruwa ne irin gari gudan nan yana tafe a saman tekun atlantic ocean cikin tsakiyar daren goma sha hud'u,duniyar tamu gauraye take da hasken farin wata yana hasken ruwan teku,idan mai hange ya qure dubansa gabas da yamma, kudu da arewa babu abunda zaka hango sai ruwan tekun bahar maliya wanda baida iyaka,tamkar gbdy duniyar tamu ruwa ne sbd girman ruwan teku,jirgin ya fito ne daga nahiyarmu ta africa zuwa qasashen sahara.....



A cikin wannan jirgi kowa yana sabgogin gabansa tamkar ba a saman teku suke ba, yawancin fasinjojin wannan jirgi larabawa ne da turawa wanda suke zuwa qasashenmu na baqar fata kwasar al'umma su kaisu qasarsu su maishesu bayi, yanzun ma hknne don kuwa kusan dukkanin baqar fatar daka gani cikin wannan jirgi toh yana daya daga cikin kamammun bayin da suka kamo a qasashenmu na africa,wasu y'an mata na gano cure wuri guda daka gani dukkaninsu sun fito ne daga mabambamtan qasashe don kowacce cikinsu yanayin shigar jikinta ya bayyana hkn, wasu yan fillo na gano sanye cikin shigarsu ta saqi daga ganinsu fulanin ruga su biyar ne kowacce ba baya bace a fagen kyan halitta saida daga qarshen duk na rauna kyawun halittarsu lkcin da idanu na suka sauka bisa kan d'ayan cikinsu dake takure wuri guda ta sanya fuskarta tsakanin cinyoyinta nayi nasarar tozali da kyakykyawar fuskarta wannan yar fillo ne lkcin da wani bature dake gefensu yasa hannu ya dago dakanta ya busa mata hayaqin sigarin dayake busawa,lalle tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan kyakykyawar halitta, tana da dara dara idanu farare tas tamkar madara, bakinta dan mitsitsi ga le6enta pink tamkar ta sanya jan baki, hancinta dodar yake, kanta babu dankwali hkn ya bani daman ganin tsawon gashin kanta, gashin ra6e yake gida biyu rayi kalba, tsawon kalbar ta sauka har duwawunta ga gashin sai kyalli yake don baqine qirin irinna fulanin usul,billah Allah yyi ruwan tsallar madarar kyau a wurin, tsantsar kyau ne kawai daga rabbil izzati babu alqus.....


Jikinta rawa yake,haqoranta na had'uwa da juna ta qara qudundune jikinta a cikin wani kwali dake gefenta don dukkaninsu a yashe suke a qasan jirgin, babbar cikunsu ta matso kusa da ita tana ta6a jikinta tace" bimbii zazza6i kk,jikinki da zafi sosai" tana mata mgn ne da harshen fillanci,shiru ta mata batace komai ba, baturen dake kula dasu ne yazo wurin yana kallonsu sai kuma ya d'ora hannunsa a jikin bimbii yaji da zafi sosai yace"noo" watsa musu harara yyi yana huci don shi abunda ya tsana ya samu mara cikakken lfy a cikin bayinsa,gani yake tamkar asara zeyi kafin ya isa dasu wurin da saidawa,kuma ma ba kowa ne yake siyan bawa mara isashshiyar lfy ba, dafe kansa yyi ya koma ya zauna ya cigaba da busar sigarinsa, wani balarabe dake gefe guda shima tafe yake da nasa bayin ya kalli baturen yace" ita wannan bata da lfy ne" mgn yake masa cikin British English irinna na qasar birtaniyya, d'ago da kansa yyi ya kalli balaraben yace" ehh" tasowa balaraben yyi yazo wurin yana kallonsu sai yyi murmushi ya kalli baturen yace" idan kana so sai muyi musanye na baka bawa mai lfy ka bani ita" tuni baturen ya miqe ya kalli balaraben yana dariya yace" nunamin bayinka sai na za6a dakaina" murmushi balaraben yyi ya nuna masa tawagar bayinsa wadanda kusan dukkaninsu zaratan samari ne majiya qarfi saidai mafi yawancinsu qabilu ne" kallonsu ya dingayi har idanunsa suka sauka kan wani murd'add'en basamuden mutum mai ji da qarfi ya dafashi yace" muyi musanyan da wannan" hk balaraben yasa d'aya daga cikin masu kula masa da bayin ya kunce wannan mutumi ya damqawa wannan bature shi kuma ya taso qeyar bimbii ya kawo masa cikin jerin bayinsa, tana kuka sauran yan'uwanta suna kuka hk don dole suka rabu ita ta koma cikin jerin tawagar bayin wannan balarabe......


A jerin bayin nasa su biyar ne kawai mata kuma kowacce yarenta daban ba wanda yake jin yaren wani, sauran duk maza, tunda ta koma wannan tawagar ta koma tamkar kurma, basa iya mgn da junansu don basu jin yaren juna, zazza6in dake jikinta ya soma tsananta sai rawar d'ari take gashi babu abun rufa hk dai ta takure wuri d'aya, wani saurayi ne d'an qabilar igbo fari sol dashi ya matso kusa da ita ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya rufa mata, jin a rufe ne yasa d'ago dakanta tayi tana kallonsa sai kuma ta komar da kanta kan guiwowinta, mgn yyiwa daya daga cikin masu kula dasu ya miqo masa ruwan sha a wata kwarya ya ta6ata ta d'ago da sauri ta matsa daga kusa dashi don su babban zunubi ne a rugansu namiji ya ta6a mace shiyasa tayi saurin matsawa,miqa mata kwaryan ruwan yyi ta miqa hannunta ta amsa ta soma sha sannan ta miqa masa cikin harshen fillanci tace ta gode.........................





*Wannan novel na siyarwa ne karki soma karanta free pages idan kinsan baki da halin siyan sauran pages wannan shawara ce........Ga wacce ta shirya siye zaki tura #300 ta wannan detail din


acct no: 0100790419

Bank:Union bank

Name: Alhaji shahida Nasir


Idan kin tura saiki turomin da screensht na payment naki ta wannan layin


07041195806





Alk'alamin Bintuu ne👌ðŸ»
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



2


Kwanaki sun shud'e anyi dare dayawa duk sun shud'e amma sukam suna doron ruwan teku suna tfy rabonsu da doron qasa sun jima, duk cikin wad'annan bayi babu wanda yasan qasar da suka nufa abunda suka sani kawai an kamosu daga qasashensu an sakosu cikin jirgi a matsayin kamammun bayi,tunda bimbii ta soma zazza6i wannan saurayin d'an kabilar igbo shike kula da ita yana tausayin bimbii sosai sbd gsky tana da qarancin shekaru, sanyi na ratsa dukkanin sassan jikinsu amma saidai su takure wuri d'aya don babu abun rufa, shi kuwa wannan saurayin daga shi sai wata yar qaramar riga don ya cire rigan dake da kauri a jikinsa ya rufawa bimbii, jirgin nasu ne ya soma tangal tangal tamkar ze kifa kowa cikin wannan jirginsa cikinsa ya d'uri ruwa sbd tsoro, riqe hannun bimbii yyi qam don yaga gbdy ta rikice cikin ikon Allah jirgin ya koma yadda yake normal, kowa ya soma ajiyar zuciya, bimbii a hnkli ta janye hannunta, kallonsa tayi taga alamun shima dai yana jin sanyi amma ya gwammace ya rufa mata jacket dinsa, hannu tasa ta cire rigan daya rufa mata ta rufa masa, kallonta yyi yana qoqarin cire rigan tayi saurin dakatar dashi da hannunta cikin harshen fillanci tace" bana jin sanyi ka sanya kawai" be fahimci mai take fad'I ba amma ya fuskanci abunda takeson yyi, murmushi yyi mata yace"nagode" saurin dago da kanta tayi tana qare masa kallo don tabbas idan har ba kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba kamar hausa taji yyi,tana jin hausa itama 2kad'an don tana fita kasuwa tallan nono, tace" kana jin hausa ne" murmushi ya kuma mata a karo na biyu yace" ehh,amma ni igbo ne daga Abia nk" tace" me sunanka" yace" obinnah" yace"ke me sunanki" tace" bimbii" ya qara nanata sunan nata yace" daga ina kk" tace" ruganmu tana kudu da qauyen lamirde cikin garin gombe" kad'a mata kai yyi alamun ya gamsu, daga shi har ita babu wanda hausar tasa ke fita daidai duk tata suke a hausar amma hk suke dan mgn, bimbii bata da yawan zance amma saita samu kanta da sakewa dashi, cikin tsakiyar daren goma sha hudu jirginsu ya samu isa matattarar tsayawar jiragen ruwa wato Brandford port dake Amsterdam,tunda suka fito daga jirgin nan suke 2kalle kana ganinsu kaga k'auyawa, dole kam suyi k'auyanci don kaf nahiyarmu ta africa ba irin wannan port din, turawan dake kai kawo a wannan port kuwa kallonsu suke tamkar kashi sbd tsabar racism, dukkaninsu babu wanda ze iya fad'ar sunan qasar da suke amma yanayin kalar fatar mutanen qasar ya tabbatar musu qasa masu jan kunne ce wato lardin turawa suke, falmata d'aya da cikin yan'uwan bimbii da aka rabasu tun a jirgi ta saci jiki daga cikin tasu tawagar ta shigo cikin tawagar su bimbii, riqo hannun bimbii tayi tana kuka tace" bimbii zamu rabu gbdy kin ga zasu kuma shigar damu wani jirgin bamu san inda zasu kaimu ba, mudai tamu qaddarar kenan sun rabamu da danginmu sun shigo damu duniya,bimbii ki kula da kanki sannan ki saukar da kanki kiyi duk abunda suka sanyaki don basu da imani zasu iya kashe mutum" kuka suke sosai suna qanqame da juna har lkcin da baturan dake jagorantar tawagarsu ya ankara babu mace daya cikin yan matan nan, suna rumgume da juna suna kuka suka ji an finciko falmata batare da 6ata lkci ba ya sauke mata tagwayen mari a fuska sannan ya jata ya koma da ita cikin tawagarsu, had'esu turawan sukayi suka zargesu da igiya sannan suka tasa qeyarsu suka shige wani jirgin dasu,suna tfy suna waiwayen yar'uwarsu itako bimbii kuka take sosai tana kallonsu har suka shige jirgin,obinnah dake kusa da ita ne ya soma rarrashinta, itama tana cikin alhinin rabuwa da yan'uwanta wani daga cikin masu kula dasu yazo yace ta biyoshi, batasan meze mata ba ita dai kawai batare da gardama ba ta miqe tabi bayansa, obinnah dake gefenta yyi saurin miqewa ze rakata mutumin ya daka masa tsawa dole ya koma ya zauna ita kuwa tabi bayansa suka qarasa wurin wani tsohon jirgin ruwa dake gefen port din, nuna mata kofar jirgin yyi yace ta shiga, shiga tayi shima yabi bayanta, suna shiga gabanta ya yanke ya fad'I don lura tayi jirgin abandon one ne ba kowa cikinsa sai tarin shirgi, bata qarasa rikicewa ba saida taga ya soma zame wandon dake jikinsa, take jikinta ya soma rawa tamkar mazari ta soma ja da baya cike da tsantsar rudewa, murmushi yyi lkcin daya gama zame dukkanin tufafin dake jikinsa ya kalleta yaga yadda ta rufe idanunta ruf sai makyarkyata jikinta yake ta durqushe a wurin tare da daga hannayenta dukka ta soma masa mgn da harshen fillanci tace" ka yiwa Allah ka yiwa annabinsa ka kyaleni karka ketamin haddi niba kafira bace" cikin kuka take roqonsa duk fuskarta tayi 2sha6e da hawaye, shi kuwa tumuqin arne besan ma abunda take fad'I ba don ba jin yarenta yake ba, shima baqar fata ne amma yyi kala da irin mutanen kenya din nan baqine qirin tamkar gawayi asalin african man, matsowa kusa da ita tana ja da baya har takai qarshen jirgin yana biye da ita da murmushin qeta a fuskarsa, hannu yasa yana shirin kamota aka doko kofar jirgin, wannan asalin balaraben ne daya amsheta daga wurin baturen nan, kallon mutumin yyi ransa a mugun 6ace ya soma zaqinsa cikin harshen turanci yace" kai wawa ne so kk kamin asara, kasan dalilin dayasa na amsheta sbd daka ganinta kasan danyar budurwa ce kuma kudin virgins ko wurin saidawa daban yake, shine dan kai dan iskane kk neman mini asara daman all those africans are bunch of animals,bauta ita tafi dacewa daku" hk balaraben nan ya din ga masifa, shi kuwa sai qoqarin sanya wandonsa yake,bimbii kuwa na daga gefe sai ajiyar zuciya take, qeyarta dan balaraben ya tasa ya komar da ita cikin tawagar sauran bayin, obinnah na ganinta ya soma tmbyrta ko sun mata wani abunne ta kada masa kai alamar basu mata komai ba,suna nan yashe a gefen ruwa tamkar ba mutane ba sanyi sai busasu yake sai wurin asuba suka ga tsayawar wani jirgi, yana sauke fasinjojin cikinsa ya soma deban wasu fasinjojin, hk akazo aka tasa qeyarsu suka shige wannan jirgi,kwanansu biyu suna tfy kafin suka soma shiga lardin larabawa, jirginsu ya tsaya ne qasar KUWAIT..... Abdullah bin faisal International port, tun saukarsu daga jirgi wasu zungura zunguran motoci suka soma dibansu kai tsaye kasuwar cinikin bayi aka wuce dasu, yadda ake cin kasuwa saida tumakai ko dawakai hk ake cin kasuwar saida bayi, manya manya keji akeyi ake zuba bayin ciki, suma hk aka zubasu cikin keji, farashin bayin hawan hawa ne wani kudinsa yafi na wani, manya masu kudi da jinin sarauta da masu mulki sukan siye bayin dayawa sukaisu muhallinsu suna musu kowacce kalar bauta amma yawanci jinin sarauta basu daukan baqar fata sai larabawa kalar fatarsu, masu ma'aikatu da gonaki suke siyen baqar fata sukaisu suna musu aiki amma masu daukar boyi boyin gd ma sunyi son larabawa kalar fatarsu suna mugun kyamar baqar fata musumman na africa,bimbii an hadata keji daya ne da wasu yan'mata amma dukkaninsu larabawa ne sukansu kallonta suke suna mamakin wai daman a qasashen baqar fata ma akwai mata masu kyau kamar bimbii, gani sukayi gashin kanta yafi nasu tsawo gata duk cikinsu ta fisu kyau da cikakken diri irinna mata saidai kawai su nuna mata hasken fata, mutanen sai 2zirga suke suna siyen bayin da suka musu,kowanne bawa so yake a siyesa ko Allah zesa yyi dace da mutanen kwarai su masa riqon arziqi,wata balarabiya itama tazo duba bayi kallon daya zaka mata kasan ba daga gdn talauci take ba, balaraben dake dasu bimbii ne yyi saurin tararta ya kawota wurin kejin dasu bimbii suke wai ta duba koda wacce tayi mata, kallonsu take daya bayan daya tana duddubasu tamkar wacce zata siyi akuya, idanunta ne ya tsaya kan bimbii ta nuna bimbii da hannu tace" wannan baqar fata ce koh" balaraben yace" ehh,amma tana da cikakken lfy ba zaki samu mtsl da ita ba" sake kallon bimbii tayi tace masa ya fito da bimbii aikuwa ya bude kejin ya fito da bimbii, batare da bata lokaci ba tayi cinikinta ta biya suka bata certificates of ownership na bimbii har wurin motarta balaraben ya rakata ya budewa bimbii boot din mota ta shiga aka rufeta sannan matar ta shige gdn baya drivernta yaja motar suka wuce, bimbii na bayan boot din motar tamkar akuya tana rakube har suka iso gdnsu sannan aka budeta ta fito, gdn qaramin bungalor ne mai kyau da tsari ga furanni ta ko'ina kunsan larabawa da son hutawa, tsagaya matar ta somayi da bimbii tana nuna mata ayyukan da yake nata ciki har da baiwa wadannan furannin ruwa da kula dasu, duk aikin nata na wajene be danganci cikin bedroms,kitchen ko cikin parlourn ba don wannan aiki daya shafi cimmarsu ko kula da wurin kwanansu basu amincewa da baqi yyi musu ba suna da kyankyamin baqin mutum sosai duk wannan ayyukan na cikin gd balarabiya yar'uwarsu suke dauka, wani qaramin daki aka baiwa bimbii, kullum bimbii tunkan kowa ya tashi take tashi tayi dukkanin aikin da matar nan ta yanka mata, batasan sunan wannan balarabiya ba amma taji ma'aikatan gdn na kiranta ennah, tana da tsauri sosai batason wasa ko sakaci da aiki, tana yara biyu dukkaninsu maza ne amma kowanne da gdnsa basu zaune tare da ita, bawai iyali ne dasu ba amma kowa yana zaune shi kadai a gdnsa saidai duk weekend suzo su gaishe su yini sai dare suke tfy, ennah tana son wadannan yaran nata sosai da zayeed da maheer, maheer shine qarami atleast bazai gaza shekaru ashirin da uku ba sai zayeed mai shekaru ashirin da shida, yau weekend tun sanyin safiya bimbii ta gama aikinta, zuwan bimbii gdn yasa furanni dake gdn suka soma kyau da fitar da kyawawan furanni masu kala sannan tana yankesu tana saitasu tana cire ciyayin dake fitowa qasansu suna hanasu girma, kullum ennah na kallon yadda bimbii ke gyaran furannin ta windown dakinta, ita kanta ta yaba da aikin bimbii, kullum tana aikinta tana waqarta cikin harshen fillanci,tun tazo gdn bata taba shiga cikin wannan bungalor na masu gdn ba, ranar wata asabar maheer ya shigo gdn, tsayawa yyi yana kallon yadda bimbii ke gyaran furanni fuskarsa sam babu annuri don shi be ta6a tsammani ennah zata kawo musu baqar fata gd ba, qarasa yyi inda bimbii ke aikinta yasa hannu ya janyo mayafin dake rufe da gashin kanta ya janyo dogon gashin kanta, cike da tsoro ta dago a idanunta tana kallonshi tace" malam lfy me na mk" cikin harshen fillanci take masa mgn aikuwa ya watsa mata mari saida shatar hannunsa suka fito a fuskarta ya bala'i cikin harshen larabci wai uban waye ya kawo musu baqar fata gdnsu, muryarsa ennah taji tayi saurin fitowa ta qaraso wurin,kamashi tayi suka shige bungalor ita kuwa bimbii hawayene ya cika mata idanu kawai ganin yadda ake wulaqanta bil'adama toh shi baqar fata ba Allah ne ya halicceshi ba, itama bimbii indai a kalar fata ne tana da haske idan anan africa ne zamu iya kiranta da fara amma su kallo daya suke mata suke gane ba balarabiya bace duk da tsantsar kyawun halittarta.....




Washegari ennah ta kirata tace ta shirya zata koma gdn danta don ta bar mashi ita ta din ga masa hidima, gaban bimbii ne ya fad'i tayi shiru kawai don babu yadda ta iya a qasar da bata da kowa bata da komai sai Allah,ranar da yamma maheer yaxo ya tafi da ita gdnsa, gani tayi ai shi kadai yake zama a gdn nasa dake Najb ushakhair steet, gdn nasa qaramin flat ne mai kyau, kallonta yyi cike da tsana ya nuna mata rumfa da aka kewaye don shaqatawa yace"na miki alfarma ki din ga kwana anan idan kin tashi ki gyara furanni ki share duk gdnnan sannan ki din ga bawa kifi abinci ya nuna mata wani qarami fond dayake kiwon kifi,iya aikin daya nuna mata kaf ba wanda ze shigar da ita cikin flat dinsa, shigewa yyi ciki abinsa yabarta a wurin tare tabbatar mata da cewa daga yau aikinta xe fara, wata jemammiyar doguwar riga ce a jikinta da wani tattararren mayafi da take rufe kanta dashi, hk ta tsuguna ta soma cire matattun ciyayin dake qasan furannin tana tarawa a gefe, cike da kuzari da himma take aiwatar da aikinta babu kasala don ta qaddara she only want to survive amma tasan ita gd ko sake haduwa da danginta har abada don ta bar gd kuma nahiyarta da nisa bata ta6a sanya ran wataran zata tsinci kanta a qasarta ba hk dai take rayuwa cikin qangin bauta..........



*This book is seriously for sale dnt ever start reading the free pages if you know u can't afford the remaining pages,for those who want to purchase the continuation of the story these are the details for transaction*...... #300 naira for this acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank.....send the screenshrt of ur payment through whatsapp....07041195806...for more information call....08080611486



Alkalamin bintuu ne.....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



3


Ta gama nome busassun ciyayin dake farfajiyar gdn sannan sauyawa kifin dayake kiwo ruwa ta basu abinci sai gumi take ga yunwa dake neman kayar da ita, wannan rumfar gezevo din daya nuna mata a matsayin wurin kwananta ta nufa ta zauna tana ajiyar numfashi, gyangyadi ne ya soma daukarta ta batare data ankara ba taji saukar ruwa a tsakiyar kanta, bud'e idanunta tayi da sauri ta saukesu akan maheer yana tsaye akanta riqe da tiyon da ake baiwa furanni ruwa yana mata wanka da ruwan, kallon tsana yyi mata yace" daman bawa har yana da sukunin baccin yamma koh kin manta matsayinki ne" bata fahimtar larabcin dayake amma tana fahimtar tsantsar wulaqancinsa, miqewa tayi ya nuna mata wani karensa dake keji yace" ta fito dashi ta masa wanka" yanayin yadda yake mata alama da hannunsa yasa ta fahimci abunda yake nufi, miqa mata makullin kejin da karen yake yyi ta amsa ta nufi kejin da karen yake tana qoqarin bud'e kejin shi kuwa karen sai haushi yake kamar zeci babu tunkan ta bud'eshi aikuwa tana bud'eshi ya rarumota yana qoqarin cizonta ita kuwa sai ihu take tana neman taimako tana tureshi da iyakar k'arfinta, tun abunda ke faruwa maheer na tsaye daga gefe yana kallonsu yana murmushin mugunta, turmusheta karen yyi a qasa duk yaji mata ciwo da faratansa ita kuwa kuka take sosai tana ture karen ta matsawa duk ta cire takalman k'afarta tana jifan karen dashi,kamo rigarta yyi da haqoransa ya shirin cizonta maheer yyi masa mgn da harshen larabci sakinta yyi ya koma gefe yana haushi 2kad'an yana kallonta ita kuwa duk ta jigata hk ta miqe a razane ta soma qoqarin ficewa daga farfajiyar gdn da gudu ta fice waje don ta mugun tsorata da karen, kallonta maheer yyi sannan yyiwa karen nasa alama da idanu,wani irin tsalle karen yyi yasha gabanta ya gurnanin haushi, juyowa tayi da gudu ta koma ciki ta shige wannan rumfar gezevon, karen be biyota ba ya kyaleta ya tsaya wuri guda, maheer matsawa yyi wurin karen ya tsuguna yana shafashi don ya gama birgeshi yau din nan, kallon bimbii yyi dake raku6e tana kuka yace" matsa tashi ki fito kiyi masa wanka" bata ma ji abunda yake fad'i saida ya daka mata tsawa amma duk da hk taqi fitowa daga inda take kawai kallon karen nan take, nuna karen yyi inda take ba shiri

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment