Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mgn tace" ni...baiwa..c..e, shu..ga..ba ce ta turon gareka" be kuma furta komai ba saida kallonta dayake tun daga sama har qasa, ja yyi da baya ya koma kujerar dayake ya zauna ya kwantar dakansa jikin kujerar ya rufe idanunsa sbd dokawa da zuciyarshi take 2akai,ita kuma tayi saurin qarasowa gabansa ta durqushe qasa bisa guiwowinta, batare daya bude idanunsa ya kalleta ba yace" me sunanki?" cikin sauri ta amsa masa tace" suna na andal" bude idanunsa yyi ya kalleta sosai sai kuma ya rufe saida ya jima sannan ya sake mgn yace" waye da cikin jikinki?" cikin tsantsar rudu ta dago da fuskarta tana kallonshi taga idanunsa na rufe sai ta sunkuya ta kalli cikin dake tare da ita, cikin sanyin murya tace" nima ban sani ba kawai ganin cikin nayi a jikina" cikin sauri ya bude idanunsa yana kallonta yace" me kkce?" shiru tayi bata sake mgn ba don yanayin yadda yyi yasa taji tsoron sake maimaita abunda ta fada, tashi yyi zaune sosai ya zuba mata idanu sai kuma ya miqe abinsa ya qarasa hadadden gadon dake can gefe ya kwanta sannan ya dago ya kalleta yaga tana inda yabarta bata da niyyar tashi yace" hk shugabar ta koyar dake aikinki" saurin tashi tayi ta qaraso wurin gadon ta tsaya batare data hau kan gadon ba, murmushin yaqe yyi wanda a zahiri ji yake tamkar ya rushe da kuka, ga zuciyarsa ta gaza dena bugawa da qarfi kawai dauriyya yake yace" ina buqatar ki sanya ni bacci" shiru tayi sai kuma ta hau gadon cikin sanyin jiki yana ganin tahau yyi matashi da cinyarta ji yake tamkar ya rumgumeta a jikinsa ko bugawar da zuciyarsa keyi ze ragu, saidai kawai ya daure, ita kuwa sakoko tayi tana kallon gashi kansa,ba zato taji.muryarsa yace" idan ina jin bacci sai an bani labarai masu dadi nk bacci,ki bani labarinki sai nayi bacci sbd kin min kama da wata wacce na sani" kallonshi take da mamaki sai kuma ta kalli gyararren sumar kansa dake kwance a saman kafadarsa, ji tayi gbdy ya birgeta, cikin sanyin murya ta soma bashi lbrinta iyakar wanda ta sani har da lbrin gidansu farhan da zaman a gdn maheer har kawo wannan lkci, kwance yake a saman cinyarta idanunsa a sama yana kallonta ya harde hannayensa saman qirjinsa ya qura mata idanu a hnkli yace" kuma baki da buqatar sanin me wannan cikin na jikinki" yasa hannu saman cikin nata yana dannawa a hnkli, shiru tayi sai kuma tace" in Allah yaso wataran zan tuna lbr na" murmushi yyi yace" kiyi qoqarin tunawa sbd qila mai cikin yana jiran abinshi" shiru tayi tana mamakin wannan dan sarki daya sake yake mgn da ita hk kuma ya bada interest nasa yana sauraren lbrinta, cikinsu babu wanda ya sake mgn, shi babban prince duk cikin lbrin data bashi babu wanda ya 6ata masa rai yaji bala'in kishinsa irin maheer, be sanshi ba amma yaji tsanarsa sosai cikin ranshi, lumshe idanusa yyi yana jinsa tamkar wani sabon mutum yau gashi ga rayuwarsa suna numfashi a muhalli guda abu kamar cikin mafarki, ita kuwa bimbii hannunta na cikin sumar kansa tana son sanyashi bacci, tunda ya rufe idanunsa be kuma budewa ba, idanun nasa na rufe ya daga mata hannu alamar ta tafi, ji tayi sam batasan sauka sbd qamshin dake fita daga jikinsa yana mata dadi sosai amma dole ta sauka ta nufi hanyar fita, tana fita yyi saurin tashi zaune yana kallon hanyar data bi, zumbur yyi ya miqe ya soma zirya, bimbii kuwa tana fita ubaid ya bita da kallo,saidai be samu nasarar ganin fuskarta ba amma ya hangi cikin dake jikinta, hknne ya bashi tabbaci dalilin dayasa babban prince ya koreta kenan, wani hadimi ne ya sanar dashi prince na son ganinshi ya shiga da sauri,batare da bata lkci ba prince ya bashi umarnin abunda ze aikata.....


**


6angaren maheer kuwa hauka tuburan ya gwada musu lkcin daya dawo gida ya tarar ba bimbii ba alamunta cikin gdn, a guje ya fito tamkar mahaukaci yahau motarsa yyi gdn ennah, tana zaune tana krt wata jarida taji shigowarsa ya afko ciki kamar an jefo shi kallonta yyi yace" ina kk kaita ina kk kaimin ita?" kallonshi tayi cike da rashin fahimta tace" me kk fada" kallonta yyi a tsorace yace" ban ganta ba ina kk kaita nasa kece kk dauke min ita" miqewa tayi tana kallonsa tace" au taji gargadin da na mata kenan ta nemi hanyarta hkn yyi kyau" kallonta ya tsaya yi yace" ina take?" tace" wannan kai zan tmby" kallonshi tayi kawai sai taga yana hawaye yace" do you want me to live?" kallonshi ta tsaya tanayi cike da mamaki don batayi zaton abun nashi yyi tsananin hk ba tace" what do you mean maheer" wani murmushi yyi ya kuma kallonta batare data ankara ba yyi saurin daukar qaramar wuqar yanka lemo dake gefenta ya soma ja da baya yace" I told you my life is useless without her, do you know how much I suffered when I lost her? a rikice take kallon wuqar dake hannunsa tace" no, maheer dnt do this u are a muslim" murmushi yyi be sake cewa komai ba ya chaka wuqar a qirjinsa, wani irin ihu ta kurma a guje tayi kansa tana kiran sunan shi, shi kuwa sulalewa yyi qasa cikin jini...........



pls manage it pls....






Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, union bank saiki turo da screenshrt na payment naki a whatsapp ta wannan layi...07041195806....






Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi๐ŸŒท: *DAREN GOMA SHA HUD'U*๐Ÿช”๐Ÿช”



Written By Bintuu Seer




35


*To me you are the princess*........you are my queen,you build a perfect kingdom in my heart.....so, you are the star๐Ÿ’•๐Ÿ’•




Bimbii na komawa turakar jira kuwa yan mata wannan turaka suka soma tuntsira mata dariya don su tunaninsu babban prince ya koreta ne, wata daga cikinsu mai suna veesha tayi saurin miqewa tayi wani irin juyi da rausaya tana karkada jikinta cike da salo, sauran yan mata suka dauki tafi da shewa, murmushi veesha tayi tace" ku duba fa ku gani da mata irinmu wadanda suka kware wurin iya sarrafa jiki da kissar dauke hnkli kowanne taurarren namiji amma wai duk a wuce mu dauki wannan mai tutsetsen cikin,hhhh" zeena tace" kedai yi shiru kawai ai daman sanya idanu nayi naga yadda abun ze kaya, ke kin ga haduwar wannan dan sarkin kuwa, tayaya ne ma ze sauke buqatarsa kan ragowar wani ga danyun yan mata irinmu masu cikakken budurci ga kuma salon hillata" tafawa sukayi suna sheqa dariya ita kuwa bimbii tana zaune gefe tayi tsuru tana kallonsu, ganin suna watsa mata baqar mgn yasa ta miqe ta wuce dakin kwananta,2kwata kasa rintsawa tayi burinta kawai ta sake shaqar qamshin jikin babban prince,miqewa tayi ta soma shinshina jikin kayanta ko ya kama qamshin nasa, hk ta din yi tamkar wacce ta samu aiki, shigowa wasu yan mata biyu da suke kwana daki daya ne yasa tayi saurin komawa ta kwanta amma a zahiri hoton fuskarsa ne yake mata gixo, hannu tasa ta daki kanta dashi tace" na shiga uku me nake yi hk" zuciyarta ta gargadeta kan ita fa qanqantacciyar baiwa ta tsaya matsayinta kar ta sake takai kanta inda Allah be kaita ba, hk dai ta din ga fama tana qoqarin manta fuskarshi dake mata yawo har ta samu bacci ya soma daukarta,washegari, suwaiba taje ta sanar da gimbiya mariyatul qifdiya wannan kyakykyawan lbri hkn yyi mutuqar sanyayawa gimbiya mariyatu zuciya, musamman aka shiryata cikin wasu kayan na alfarma don ganawa da masoyinta rabin rayuwarta, babban prince yana tare da sarki abu ansar a dakin ganawar sirrinsa, sarki abu ansar ya kalli prince akbar yace" tabbas maqiya sunyi amfani da baquwar guba ne wacce take sabuwa qirqira da har yau masana basu gano laqonta wurin cutar da mahaifinka sai zan tura ka ga wani bawan Allah tsohon masani ne kuma bayahude daya jima yana qirqirar gubobi masu tsananin cutarwa ga lfyr bil'adam, yasan sirrin kowacce irin guba, wannan bayahude yana rayuwa ne a wani tsibiri can arewacin spain da ake kira oldest Inland na tabbata wannan bayahude bazai rasa sani game da abunda ze daqusar da wannan guba dake jikin mahaifinka ba" shiru prince akbar yyi sai kuma ya dago ya kalli sarki abu ansar yace" yakai wannan sarki ma'abocin sani tabbas da yarda wannan raina ke hannunsa bazan koma ga mahaifina ba har sai da mgnin matsalarsa" murmushi sarki abu ansar yyi yace" madallah da d'a nagari kuma kyakykyawan jarimi a fagen fama" rissinar dakai prince yyi alamar girmamawa ga sarki abu ansar" hannun prince akbar sarki abu ansar ya riqe suka fito, babbar hadima ga sarauniya ita ta yiwa babban prince jagora har wani babban lambu mai cike da kyawawan furanni da tsuntsaye masu dadin kuka, wata kyawawan kujeru aka tana don zaman shi, bayan fitar ta bada jimawa ya soma jiyo wani sassayyan qamshi mai kwantar da hnkli, daga kansa yyi yana kallon 6angaren da qamshin ke tahowa, gimbiya mariyatul qifdiya ce sanye da wata doguwar riga mai ruwan kwai, tayi ado na awarwaron zinare ga sarqa ga abun wuya, tasha kyau na ban mamaki, kallo daya za'a mata a fahimci diyar girma ce kuma jinin sarauta, tfy take dai dai cike da qasaita da kuma izzah har ta qaraso wurin dayake daya daga cikin hadiman dake take mata baya ta gyara mata zaman kujerar dake gefensa ta zauna, juyawa hadiman sukayi suka fice daga lambun ya rage daga ita sai babban prince, duk sunyi shiru don kowanne cikinsu yana taqama da izzah da kuma qasaita gdn sarautar daya fito, gimbiya khamriyya da kanta ta jaddadawa gimbiya mariyatu akanta 6oye soyayyarta ga prince akbar ta martaba izzar gdn sarautar abu ansar, ta bari shi ya soma sauke izzarsa gareta ya fallasa mata sirrin zuciyarshi, prince sau daya ya kalleta duk da kuwa tsantsar kyawunta irin na larabawan usul,sun jima a hk babu mai niyyar mgn cikinsu, gimbiya mariyatu kam taji ana ambatar cikakken izzah irin na wannan dan sarki amma bata ta6a zaton yakai hk ba, miqewa taga yyi ya soma takunsa mai cike da qasaita ya fice daga wannan lambu yabarta zaune tamkar an dasata, kuka ta fashe dashi tana dana sanin daukar shawarar yayarta kan ta nuna masa cikar izzarta gashi nan ya fita ya barta da izzar nata, shi kuwa prince akbar duk duniya mace daya ce zata iya gwada masa izza tasha kuma ita din ba kowan kowa bace face qasqantacciyar baiwa amma ita Allah ya dora bisa kansa ko durqusawa gabanta ze iya yi sbd ta gama da qarfin izzarsa, hadimansa na ganin fitowarsa suka take masa baya, ubaid na daga hannun damansa, bimbii ta tashi da kasala ranar sai bin jiki take babu abunda takeson ji sai qamshin jikin prince, fitowa tayi tana kwashe shanya tana zubawa cikin wani kwandon saqi, tana shiga 6angarensu ta hango dukkanin yan matan dake turakar jira sun fito farfajiya wurin sunyi jeri tana shigowa duk suka bita da kallo,ramlatul aswat ta gani tare da suwaiba sai kuma wasu qattan bayi, kallonta ramlatul aswat tayi a wulaqance cikin fada tace" ke daman gudandiyar baiwa ce daga gdn yasser bin walid amma har kk shigo wannan masarauta ta abu ansar" wani hadimi dayake cikin hadiman da suka siyo bimbii yace" tabbas bamu san gudaddiyar baiwa bace daga gdn yasser da bamu siyenta" ramlatul aswat ta galla masa harara sannan ta kalli bimbii take sauraronsu don bata gane abunda suke fada ba, turata cikin hadiman gdn yasseer bin walid ramlatul aswat tayi tace" ka baiwarku nan amma ku bawa nana hkr kar wannan zance yakai kunnen sarauniyya" hadiman gdn yasser suka ja bimbii suka fita da ita har suka fice daga masarautar abu ansar da ita, yasser bin walid shararren attajiri ne mai qarfin arziqi da yalwar bayi, sarakuna suna ganin darajarsa sosai sbd qarfin arziqinsa, yasser bin walid abokin kasuwancin prince akbar ne kuma shine ya tura ubaid wurinsa kan ya masa wannan alfarmar batare da bata lkci ba ya aika hadimansa gdn sarautar burham don aiwatar da wannan aiki, yasser ya damqa bimbii ga ubaid sai lkcin ubaid yaga bimbii shi kansa ya cika da mamakin ganinta, kamar yadda prince ya umarci ubaid hk ya aiwatar yasa bimbii cikin wani babban jirgin ruwa mai zuwa spain tare da wata amintacciyar hadima mai suna sumayya da yasser ya hadasu da ita don kula da lfyr bimbii har su isa qasar spain, sumayya mace ce mai mutuqar jarimta tamkar na maxa gata da hikima hk ta din ga kula da bimbii har jirginsu ya isa qasar spain suka wuce masaukinsu, ubaid ya isa ya sanar da babban prince jirginsu bimbii ya tashi zuwa spain, suma da yamma tawaga guda sarki abu ansar yasa suka yi masa rakiya har ya shiga jirgin ruwa tare da ubaid, sauran hadimansa kuwa suka koma ga masarautar burham suka sanar da tfyr babban prince spain don ganawa da tsohon bayahude abram dake oldest Inland, bimbii tunda jirginsu ya tsaya a port na tsayawa jiragen ruwa dake qasar spain ta fito sai kalle kalle take, gani tayi ta dena ganin masu rawani sai turawa nasarar asarar duniya, qasar spain ta mata kyau ko'ina hasken fitilu dayake da dare suka qarasa, sun sauka ne a wani orchard house mai kyau, qaramin gini ne irin na turawa amma ya tsaru sosai, ko'ina ta gefe bishiyoyin fruit ne da shuke shuke, tsarin wurin kawai akwai kwanciyar hnkli, bimbii ranar bacci tayi mai rai da lfy sbd peaceful environment din data samu kanta ciki, cikin kwana uku ubaid da babban prince suka iso qasar spain, suma a wannan orchard house suka sauka sbd tsarin wurin yana yiwa prince dadi idan ya shiga spain a wannan wuri yake rayuwarsa, nesa kadan da wannan orchard house teku ne,bimbii dai kam batasan dalilin zuwanta wannan waje ba ita dai kawai gata nan ne batasan ina rayuwarta ta dosa ba,da dare sumayya ta sanar da ita wanda ya siyeta ya iso yana buqatar takai masa abun sha, ba musu bimbii ta tashi ta hada lemon zaitun da zuma ta zuba a kyakykawan mazubi ta din ga qetare corridor har ta isa bakin dakin da prince yake,ta6a kofar tayi taji ta a bude tayi sallama ta shiga, bedroom ne mai girman gaske, komai na wannan bedroom fari ne da dark blue, everything is so cool, qamshin da take maita ta soma shaqa, prince kuwa yana kwance a tafkeken gadon dake dakin yana duba wani littafi yaji ta turo kofa, ita bata lura dashi ba kawai kallon dakin take sai data waiga wurin da wannan tafkeken gadon yake ta hango shi kwance ya tsareta da idanu,gabanta ne ya yanke ya fadi ta tsira masa idanu cike da tarin mamaki da al'ajabin ganinsa a wannan wuri, shafa idanunta ta somayi tana son tabbatarwa wannan dan sarkin ne kuwa.....


***

6angaren maheer kuwa tuni ennah ta kira faisal suka nufi hospital dashi, hnklinta duk a tashe sbd tana da masifar son yaranta,maheer yyiwa kansa rauni sosai, bayan hk likitoci sun tabbatar musu jininsa yahau dayawa a kowanne irin lkci zuciyarsa zata iya bugawa, ennah kuka take sosai sai lkcin take nadamar dauke masa bimbii da tayi har kasuwar saida bayin data kai bimbii ta koma amma wannan balaraba ya fada mata shi wlh ya saida ita dole hk ta dawo hospital din da maheer ke kwance cike da tarin dana sani, zama tayi ta tsura masa idanu, shi kuwa yana kwance duk an sanya masa oxygen a hanci da bakinsa, numfashinsa na fita a hnkli, tunani take wai wanne irin so kuwa maheer yake yiwa wannan baiwa hk, she can't imagine this kind of sacrifices until she witnessed it on her son......







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screenshrt na payment nk ta whatsapp ta wannan layi..07041195806.....





Alkalamin Bintuu ne.....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi๐ŸŒท: *DAREN GOMA SHA HUD'U*๐Ÿช”๐Ÿช”



Written By Bintuu Seer



36


*I LOVE YOU*๐Ÿ’•๐Ÿ’•I MISS YOU๐Ÿ’•๐Ÿ’•



Duk abunda take idonsa na kanta yana qare mata kallo, dauke kansa yyi daga kallonta ya cigaba da karanta littafin dake hannunsa, hknne itama ya bata damar takawa a hnkli ta qarasa wurin qaramin stool din dake gefen gadon dayake kwance ta ajiye farantin hannunta ta dauki cup ta soma tsiyaya masa drink, daukan cup din tayi ta matsa daidai wurin dayake kwance ta rissinar dakanta qasa tare da miqa masa cup din dake hannunta, daga idanunsa yyi kawai yana kallonta, tashi yyi zaune ya ajiye littafin dake hannunsa ya amshi cup din dake hannunta ya soma sipping drink na zaitun din, miqa mata cup din yyi ta mayar dashi kan faranti ta ajiye sai kuma ta dauki farantin da niyyar ficewa dashi don ta soma gjy da wannan kallon qurallah da wannan dan sarki ke binta dashi, rissinar dakanta tayi alamun girmamawa sannan ta juya da niyyar fita saidai taku daya zuwa biyu tayi taji charaff an damqe mata hannu, kafin ta dawo cikin tunaninta ya rumgumeta ta baya hannunsa nakan qugunta ya dora kansa akan dokin wuyanta yana sauke numfashi a hnkli, ita kuwa bimbii mutuwar tsaye tayi zuciyarta na wani irin tsere da mugun speed, saukar numfashinsa kawai take iya ji, jikinta sai rawa yake kamar mazari, shi kansa yaji rawar da jikinta yake yi, murmushi yyi ya janye hannunsa daga qugunta ya juyo da ita suna fuskantar juna, tsirawa juna ido sukayi, bece mata uffan ba amma tana iya karantar saqonsa da cikin kwayar idonsa, zallar madarar sonta kawai take hange cikin kwayar idonsa shi kuwa babu abunda yake gani cikin idonta sai tarin tsoro da rudu, hannunsa yakai wurin idanunta yyi kamar ze tsole mata idanu tayi saurin blinking eyes nata, janye jikinta ta soma qoqarin yi amma ta kasa don namijin gaske ne yake riqe da ita, raurau tayi da idanunta da niyyar fashe masa da kuka, rufe idanunsa yyi don baya son ganin hawayenta kuma baida niyyar fasa abunda yyi niyya, matsar da fuskarsa yyi sosai ya hade da nata ya dora dogon hancinsa kan nata, bimbii kuwa qirjinta kamar ze faso sbd tsoro, bata gama sallamawa da lamarinsa ba saida taji ya hade bakinsu wuri guda,numfashinta ne ya soma fizga shi kuwa gently yake kissing nata dukkaninsu idanunsa a lumshe kowanne cikinsu zuciyarsa na bugawa da qarfi, a hnkli ya tsare bakinsa daga cikin nata amma be dauke fuskarsa dake manne da nata ba kuma be bude idanunsa ba, itama idanunta na rufe, saida suka jima a hk sannan ya janyota ta fada qirjinsa yasa hannunsa around her, kuka take masa, idanunsa shima sunyi jajir he wish to be with her this night but he can't until she gain her memory back, bimbii tana kuka tana qara manna fuskarta a qirjinsa tana shaqar qamshinsa sbd abunda take so kenan, ya jima yana rumgume da ita yana shinshinar qamshin da gashinta ke fitarwa yana tunanin abunda ze iya raba shi da ita, mahaifinsa ne ya shigo cikin tunaninsa take yaji gabansa ya yake ya fadi, idan har ya rasa bimbii baya jin rayuwarsa zata dore sbd kowanne sashi na jikinsa qaunarta ne hatta jinin dake circulating a cikin jikinsa, sonta shine bugawar zuciyarsa, hannunsa yasa ya dago da fuskarta data jiqe da ruwan hawaye ya tsura mata idanu, qasa tayi da kanta don kallon nasa na sanya mata mutuwar jiki, hannu yasa a aljihu ya fito da wani farin handkchiep nasa yasa hannu ya dago da ha6arta ya soma goge mata hawayen da yyi spoiling beautiful face dinta, gani tayi ya durgusa a gabanta ya dora kansa kan cikin dake jikinta yana jin motsin abunda dake cikin, hannu tasa ta tureshi yyi saurin miqewa yyi yana murmushi ya kanne mata ido daya tare da dage mata kafada kamar wani qaramin yaro, komawa yyi ya kwanta abinsa ya daga mata hannu alamar ya sallameta, kamar jira take tayi hanyar kofa da sauri kamar zata ci tuntu6e ta murda handle na kofar ta fice, murmushi yyi kawai daya ga ta fita ya lumshe idanunsa, ita kuwa bimbii tana fita tasa gudu ta qarasa dakin da take tana sauke numfashi tare da kallon kofa tamkar wacce tayi gamo, sumayya dake bayanta riqe da cup na black tea tace" mene ya tsorataki hk na ganki duk a rikice" inda inda ta somayi kamar wata munafika don gani take kamar sumayya tasan abunda ya faru da ita, sumayya na ganin hk ta wuce tare da basar da tmbyr data mata, zuma ta sanya a black tea din dake cikin cup din hannunta ta miqa mata, amsar cup din tayi tana shan tea din a hnkli har ta shanye, bathroom ta shiga tayi wanka da warm water sannan ta fito ta sanya wasu kayan bacci masu taushi tabi lfyr gado, mood nasu na dazu kawai take tunawa ya kasa 6ace mata a cikin brain nata, hannunta tasa ta shafa lips dinta daya sha kissing, yanayinsa take tunawa da cool love nasa mai tsayawa a rai, mafi yawan soyayyarsa a kwayar idonsa take be cika yawan mgn ba, murmushi ne ya su6uce mata ta rufe fuskarta da small pillow din dake gefenta, da wannan tunanin bacci 6arawo yyi gaba da ita, washegari, bata samu ganin prince ba sbd da sassafe suka fice shi da ubaid suka nufi oldest Inland, cikin nasara suka gane inda wannan tsohon bayahude yake, abram yana rayuwa ne shi daya a wani gdn katako, suna tsayawa da mota ubaid yyi saurin budewa babban prince kofar mota ya fito, hk suka taka suka qarasa wannan gdn katakon, ubaid yasa hannu ya buga kofar katakon a hnkli, saida aka dauki time abram ya bude kofar ya tsaya yana kallonsu, tsoho ne sosai, gashin gemunsa dogo kuma fari sol, sanye yake da wata hula iyakarta tsakiyar kansa irin wacce jews ke sanyawa, kansa duk saiqo, kallonsu yake da mamaki kuma yaqi basu hanya su shiga ciki yace" arab men to my house, what's are you up to...?" ubaid yace" this is not abram house" they are speaking with pure british english, yana ji sun ambaci sunan shi ya basu hanya suka shiga ciki, ko'ina cikin gdn kwalabe ne dauke da chemical samples, ta gefe guda kuma shelter ne na manya tsoffi littattafan manya scientists da suka shude, yanayin tsarin gdn kawai ya tabbatar musu gd ne na masana kimiyya da binciken qurulla, coffee ya kawo musu yana turiri suka soma sipping sannan prince ya soma masa bayanin abunda ya kawosu gare shi, shiru yyi na wasu daqiqai sai kuma yace" ina son ganin mahaifin nk don na duba yanayin gubar dake circulating a jikinsa" gdy sosai babban prince yyi masa bai ta6a tsammanin wannan bayahude zeyi saurin amincewa dasu ba cox most of jews basu da trust ga larabawa.......




Pls don Allah kuyi manage da wannan page din, bani jin dadi ne naso yau nayi muku dogo typing amma jiki da jini sai gdyr Allah.....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi๐ŸŒท: *DAREN GOMA SHA HUD'U*๐Ÿช”๐Ÿช”



Written By Bintuu Seer



37


*Your love is a special chemistry and also the most concentrated pure love to my heart*.......I love everything about you๐Ÿ’•๐Ÿ’•



Sun shirya komawa masarautar burham da abram don ya duba sarki abdallah bin jabal dakansa ya fahimci irin gubar dake jikinsa,6angaren bimbii kuwa tana zaune ita da sumayya suna hira taji mararta tayi wani irin murdewa, skipping tayi ta runtse idanunta tare da riqe mararta, cikin sauri sumayya ta matso kusa da ita ta riqeta tana mata sannu, abu kamar wasa ciwo ya soma cigaba, fita sumayya tayi da hanzari ta nufi wurin ubaid ta sanar dashi abunda yake faruwa, shiga yyi ya sanar da prince, cikin hanzari ya fito suka nufi dakin da bimbii take, ubaid ya

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment