Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansa ya fahimci hkn shiyasa ya miqe yace" me sunanki" cikin hard'ewar baki tace" bim...bii" yace" daga ina kk fito" tace" gombe" shikan besan ina ne gombe ba dama cewa tayi nigeria wataqila ya fahimci sunan qasa take nufi daga qasashen africa,murmushi yyi yace" koh na tayaki kwashe tuffan ne" saurin girgiza masa kai tayi jikinta na rawa ta soma tattara tuffan data tsinko tana zubawa cikin kwando tana gama ta soma qoqarin daukan kwandonta ta tafi, daukan kwandon yyi ya dora mata akanta yace" bimbii sai anjima" saurin kallonsa tayi tana mamakin jin yadda ya furta sunanta, sauri sauri take ta fice daga lambun shi kuwa yyi folding hannunsa a tsakiyar qirjinsa yana kallonta har ta fice daga lambu, sauri take tamkar zata kife tanayi tana waiwayen bayanta burinta kawai tabar wuraren lambun, ita batason ta shiga idanun wadannan y'an sarautan tana zaman zamanta lfy, kitchen ta wuce takai musu suka juye kayan marmarin suka bata kwandon ta mayar dashi ma'ajiyarsa sannan ta dauki tulu ta nufi qorama de6o ruwa, ranar hk ta yini da fargaba fal cikin ranta tana mamakin dogon zancen da wannan d'an sarki yyi mata, hk ta gama aikinta ta koma 6angarensu na bayi, tana shiga taga su israt ranar sun rigata dawowa, hannunta khulood ta kamo suka zauna dukkaninsu a qasa suka sanya abincinsu a tsakiya suna ci, bimbii gani tayi su uku ne kawai ba lailah ta kallesu tace" ina lailah take" khulood ta nuna ta masa wurin da lailah ke kwance tace" batajin dadi ne" saurin cire hannu bimbii tayi daga abincin ta nufi wurin da lailah ke kwance bisa busassun ciyayin da suka saba kwanciya ta dafata tace" lailah sannu koh" dagowa lailah tayi da kanta tana mata murmushin qarfin hali,hannunta tasa ta ta6a jikin laila tajishi zafi zau, miqewa tayi ta fita ta samu qaramin bowl ta ciko ruwan sanyi a ciki ta shigo dashi, mayafin kanta ta cire ta sakashi cikin ruwan tana matsewa tana sanya mata a jiki sbd jikin nata ya rage zafi, khulood da israt suma duk suka matso inda laila ke kwance, zazza6i ne sosai a jikin lailah, tashi d'aya kuma saita soma yunqurin amai ta fita ta dinga kwarara amai, khulood da israt suka fita da sauri don amsowa laila magani a dakin amsar magani, suna zuwa suka tarar k'ofar wurin a rufe sbd gsky dare yyi sosai, buga k'ofar suka dinga yi amma jahan yaqi bud'ewa don shine babban bawan dake kula da wurin maganin, hk suka gaji suka koma, bimbii na ganinsu ta taso da sauri tana tmbyrsu ko sun amso maganin, duk sukayi shiru tana ganin hk tasan basu amso ba, tace" sun kulle k'ofarsu koh" suka daga mata kai alamar ehh,duk sun zagaye lailah sunyi shiru suna kallonta tana numfashi a hnkli gumi sai keto mata yake,bimbii ta kallesu tace"toh yanzu meye abun yi" khulood tace" kawai muje mu haura katangar wurin mu sato maganin tunda na tabbata jahan na jinmu ya mana banxa sbd rashin imani" israt tace" hkma zamuyi" bimbii tace" toh kuma kar muje su kama mu" khulood tace" insha'Allah ba zasu kama mu ba, ta baya zamu duqa basa rufe kofar ciki a bud'e suke barinta" hk suka fito cikin wannan tsakiyar daren su uku suka soma la6a6awa cikin sand'a har suka qarasa gdn maganin,dayake sun saba da haura bishiya take suka haura katangar gdn magani suka soma tfy cikin sand'a, israt ce ta bud'e kofar a hnkli ta soma shiga bimbii na biye dasu, bincike suka somayi a wurin da magunguna ke jera har suka samo maganin zazza6i suka juya zasu fita, sai kawai jin muryar jahan sukayi yace" duk wanda ke cikin wurin nan ya tsaya karya fita" duk suka kalli juna cike da tsantsar tsoro, bimbii tayi saurin turasu waje tace" su suyi gaba zata biyo bayansu don tasan tabbas idan ya shigo be ga kowa ba kasancewar yaji motsin mutum a wurin ze ankarar da bayin dake tsaron wurin ne shiyasa ita ta tsaya tace su tafi, suna tfy suna waiwayen k'ofar suka sake haure katangar suka fice amma sai suka qi tfy suka tsaya jiran fitowar bimbii, bimbii kuwa tana ciki jahan ya bud'e kofar ya shigo, kallonta yake cike da mamaki yace" me ya kawoki nan wurin" tace" magani nazo amsarwa yar uwata tana fama da zafin zazza6i kuma nayi bugu ba'a bude ba" murmushin mugunta yace" shine kk shigo satar maganin, alamu sun nuna bakisan hukuncin sata a wannan masarautar bane koh" bimbii tace" toh kaimin aikin gafara" dariya yyi sosai yana qare mata kallo, yace" zan miki aikin gafara amma da kyakykyawan sharadi,kin amince" tace"fadi sharadin naka naji" dariya yyi a karo na biyu ya soma kusanto inda take ita kuma tana matsawa har ya cimma mata yace" sharadin nawa shine ki aminta dani wannan daren ki de6emin kewa" hannunsa yakai saman qirjinta, saurin buge masa hannu tayi tace" idan wannan ne sharadin naka toh bana buqatar gafararka gareni" dariyar mugunta yyi yana tauna asuwakin dake hannunsa, kallon qafarta yyi yaga sarqar kafan nan ya gane rukunin bayin da take, nuna mata kofar fita yyi yace" ga hanya nan zaki iya tafiya" a hnkli ta soma takawa tana kallonsa shi kuma yana mata dariyar qeta har ta fice ta haura ta katangar da suka hawo ta dire, ga mamakin sai ganin su khulood tayi a raku6e suna jiran fitowarta suna ganinta suka rumgumeta suna tmbyrta abunda ya faru, tace" babu komai,muyi saurin barin wurin nan kar wasu su ganmu" hk suka din ga la6a6awa suka koma 6angarensu, suka tarar da lailah sai murqususu take sbd zafin ciwo, cikin sauri suka hada maganin suka bata tasha, gumi sai keto mata yake a hk ta samu bacci, kallon bimbii khulood tayi tace"ki fada mn abunda ya faru a gdn magani, jahan ya ganki ne" daga mata kai tayi tana neman basar da zancen amma suka matsa dole ta sanar dasu yadda suka qare da jahan din, shiru taga sunyi tace" qalau dinku kuwa" israt tace" bimbii jahan mugun mutum ne besan arxiki ba cikin rayuwarsa tunda kkyi hk dashi toh wlh da abunda ze biyo baya gobe sbd basu daukan irin hk da sauqi cikin wannan masarautar" bimbii tayi murmushi tace" karku damu da wannan kudai ko mene ma ya biyo baya karku sake ku sanya kanku ciki" khulood tace" abunda bazai yuwu ba kenan, tunda har tare muka shiga toh koma meye ya biyo baya tare zamu tareshi" girgixa musu kai bimbii tayi tace" idan mukayi hk toh zamu 6ata biyu ne daya be kyaru ba, kun ga muna da mara lfy wa kk tsammanin ze kula da ita idan dukkaninmu muka tafi amsar hukunci, karku damu kudai kuyi yadda nace abun zezo mana da sauqi" shiru sukayi basu furta komai ba har suka kwanta bacci zuciyoyinsu cike da tunanin qarfin hali da tsantsar jarumta irinna bimbii, washegari da sanyi safiyya suka tashi, laila ma tadan ji dadin jikin nata, suna shirin fita kenan ummul shukri ta shigo 6angaren nasu ranta a mutuqar 6ace tana zuwa ta kalli bimbii tace" ke ki fita farfajiya ki amshi hukuncinki na shiga sata gdn magani" bimbii ta miqe ta fita batare data furta komai ba, wasu manya manya bayi ta gani su biyar riqe da wasu zabga zabgan bulalai, suna ganinta suka nuna mata kan wani itace dogo wai tahau ta kwanta ta juya bayanta, bata musu gardama ba tahau ta juya musu baya suka soma zabga mata wadannan manyan bulalan na hannun, lkcin ummul shukri ta fito riqe da sandarta tana kallon yadda suke hukunta bimbii, israt da khulood kuwa gani sukayi sam basu iya kyale bimbii ta amshi hukunci ita kadai ba suka dawo da gudu duk suka zo wurin suka durqushe da kafafunsu, ummul shukri ta tmbyeshi mene ya kawosu wurin sukace" muma mun zo amsar hukunci ne don tare muka shiga gdn maganin da ita" wata uwar tsawa uwar bayi ummul shukri ta daka musu tsawa tace" su 6ace su bata wuri,dole suna ji suna gani bimbii ta amshi hukuncinsu, bulala tamanin suka mata"duk jikinta ya farfashe jini ne kawai ke fita ya 6ata rigar dake jikinta amma abun mamaki ko digon hawaye basu gani ba a idanun bimbii, hk suka tasa qeyarta tana tangadi suka tafi da ita kurkun da ake kulle bayin da sukayi sata wai sai tayi sati biyu kafin ta fito, suna shiga da ita suka watsata cikin kurkun suka fito abinsu" tunda suka watsata bata dago da kanta ba sbd radadi da ciwo da jikin yake mata, tana kwance saman busassun ciyayin dake qasan wurin sai lkcin wasu hawaye masu d'umi suka soma sakko saman kuncinta, tabbas rashin yanci beyi ba, kafin dare ko'ina na jikinta ya suntume ya kumbura gashinta duk ya rufe mata fuska babu dankwali a kanta, idanunta sunyi jajir sun kumbura sbd tsa6ar kuka data tayi wannan dare,ga ciwo na cinta amma babu magani, Allah shi kadai shine gatanta don bata da wani gata kasancewarta qasqantacciyar baiwa mara galihu, 6angaren su israt da khulood kuwa ranar ko abinci kasa cinsa sukayi suna tunanin yar'uwarsu bimbii ga lailah kuma a kwance jiki ya kuma rikicewa, daren ranar ummul shukri ta shigo 6angaren nasu ta taddasu 2jugum, kallon yanayin lailah kawai tayi tasa hannu ta dago da ita tana qare mata kallo take ta hade fuska ta kalli tsakiyar idanun lailah tace" kina da juna biyu lailah, waye yyi miki ciki lailah" wannan kalma da uwar bayi ummul shukri ke furta ita ta razanar dasu israt dake gefe suka soma kuka, lailah kuwa duk da zafin zazza6in da take fama dashi kalaman ummul shukri sunyi masifar fadar mata da gaba, ta kalli uwar bayi ummul shukri tace" ciki? ciki ne dani" kafin ta rufe baki ummul shukri ta zabga mata mari har uku a fuska tace" kinsan hukuncin wannan abun kunya da kk aikata kuwa?" lailah kuwa kuka take sosai har da sheshsheqa tana roqon uwar bayi ummul shukri ta rufa mata asiri ta mata aikin gafara,ummul shukri bata kuma cewa komai ba ta miqe ta fita, tana fita su israt da khulood suka taho wurinta da gudu suna tmbyrta abunda ke faruwa da ita, lailah kuwa kuka kawai take tana tausayin kanta da rayuwarta,israt ta riqo hannunta tace" lailah me kk 6oye mn baki daukemu yan'uwa ba kenan" kuka take sosai ta kasa furta komai,khulood tayi shiru tana tunanin wani abu,a hnkli ta dago kanta cike da rudani da tsantsar fargaba hadi da tsoro ta kalli lailah suka hada idanu tace" lailah,lailah meyesa kkyi hk,lailah abunda nk tunani shine,kicemin aa lailah" sai kawai ta fashe da kuka ta soma jijjiga laila tana cewa tace mata aa, kallon khulood israt tayi cike da mamaki tace" akwai abunda kk 6oyemin,akwai abunda ya faru ban sani bane" miqewa tayi ta soma turesu tana kuka tana cewa baku yarda dani bane kuke 6oye min abu.......






Littafin nan na kudi ne ki biya kiyi karatu na yanci bana satar fage ba,naira dari uku kacal ta siya miki qarashen labarin DAREN GOMA SHA HUDU....zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, sai turomin da screeshrt na payment naki ta whatsapp...07041195806, idan da buqata wani qarin bayani ga layin kira nan..08080611486





Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




8


*My luv to you is beyond words but looks into my eyes you will believe the real magic of your pure luv in it*........I give you my heart dear...💕


Janyo hannunta lailah tayi duk ta hadasu ta rumgume, kuka suke sosai sai can khulood tace" bazan ta6a gafartawa kaina ba lailah idan har wani mugun abu ya faru dake" rufe mata baki lailah tayi tace" ki daina fadar hk a rayuwa kowa da qaddararsa kuma babu wanda ya isa ya goce mata, qaddararmu shine mun zo lkcin da masu mulki da sarauta suke da qarfin izzah tare da murqushe wanda baida y'anci, dole mubi rayuwar yadda tazo mn" khulood tace" meye amfanin abunda kkyi lailah da kin bari mun amshi hukuncinmu a lkcin da duk hk bata faru dake ba" shiru lailah tayi tana tunanin abubuwan da suka faru kwanakin baya wanda shine silar shigarta wannan hali yanzu, khulood da lailah sun ta6a yunqurin guduwa kwanakin baya Allah bai basu sa'a ba aka kamasu don basu da shaidar fita,yawanci yantattun bayi suke da damar fita ko'ina su kuma bayi na qasa qasa saidai idan suna da shaida fita tare dasa hannun wani sananne cikin masarautan, bawan daya kamasu shine raqas babban bawa dake kula da babbar kofar fita daga masarautar,hukuncin bawan da aka kama da yunqurin gudu shine kisa ko kuma akaisa baqin kurkun qasa,kurkun qasa kurku ne da suka tanada a qarqashin qasa suke ajiye masu babban laifi tare da azabtar dasu, lkcin da raqas yaga su lailah da khulood na yunqurin gudu ya kamasu, ba kalar roqon da basu masa ba yyi kunnen uwar shegu dasu yace" wlh sai ya kaisu gaban hukuma sun amshi hukunci daidai da laifinsu amma daga qarshe sai ya nemi lailah ta amince ta kwana tare dashi shi kuma sai ya rufa musu asiri, lailah tayi qememe taqi amincewa da hkn, yace toh su tafi gobe su tsumayi sammaci, hk suka dawo 6angarensu cike da tsoron abunda ze biyo baya, lailah ba kanta take tausayawa ba khulood dake jin tausayi gani take idan bata amince da buqatar raqas ba toh fa daga ita har khulood basu tsira, lkcin da suka dawo israt ta tmbysu ina sukaje sai suka 6oye mata basu fada mata abunda sukayi ba, lailah koh saida ta bari bacci ya kwashe ta tashi ta fice ta tafi wurin raqas, shi kuwa yana ganinta yyi murmushi yace" kinyi tunani maikyau da kk dawo don kuwa da rayuwarku ta shiga garari" lailah bata ta6a tunanin samun shigar ciki ba akan wannan dare kawai, sai wurin asuba ta sato jiki ta dawo lkcin khulood na zaune don ta tashi bata ga lailah ba kuma tabbas zuciyarta ta bata lailah komawa tayi wurin raqas, tana zaune lailah ta shigo idanunta jajir ga dukkan kuka tasha, ganin khulood zaune ne yasa ta soma goge fuskarta, khulood ta zuba mata idanu tace" lailah ina kkje" shiru lailah ta mata itako khulood qara kallon lailah take sosai taga tfyrta ta sauya, miqewa tayi zumbur ta nufo inda lailah take tace" lailah komaqa kkyi wurinsa kk miqa masa budurcin naki" rufe mata baki lailah tayi tace" kiyi shiru kar israt taji hnklinta ya tashi, khulood bamu da wata mafita sai wannan tunda ya bamu za6i" khulood kasa mgn tayi sai durqushewa da tayi a wurin tana kuka sosai, wannan shine abunda ya faru dasu kwanakin baya, hk khulood sanar da israt abunda ya faru, dukkaninsu kuka suke sosai suna tausayawa lailah don ba makawa hukuncin jefewa ne ya rataya akanta,washegari dukkaninsu ba wacce hnklinta yake a kwance kowacce cikin fargaba da tashin hnkli take amma duk da hk saida suka tafi kurku don ganin halin da bimbii take ciki har da lailah, 2qiri bayin dake tsaron wurin suka hanasu ganinta hk suka koma bakin ayyukansu, bimbii kuwa yunwa qishin ruwa ga radadin ciwo duk sun galaibartar da ita, kwanan bimbii biyu prince nasaar yaga baya ganinta sbd yasan duk wurin zuwanta, sanya wani hadiminsa yyi bincike akanta, batare da wani 6ata lkci ba ya binciko masa inda bimbii take,dakansa yaje kurkun yasa a fito da ita, jiki na rawa suka fito da bimbii bata ma gane abunda ke faruwa, wata baiwarsa yasa mai suna salma ta tafi da bimbii ta kula da raunin dake jikinta, hk kuwa akayi salma ta tafi da bimbii wani 6angare na daban ta bata ruwa tayi wanka taci abinci ta bata wurin kwana,tunda bimbii tazo qasar sai ranar ta ta6a kwana a abu mai laushi, salma mace ce mai kirki hk ta din ga kula da bimbii tana shafa mata magani a raunin dake jikinta sbd kar ya bar mata ta6o ita mace ce,6angaren su khulood kuwa basu da masaniya kan sakin bimbii da akayi gashi kullum suna cikin tashin hnkli da tsammani don har yanzu uwar bayi ummul shukri bata kuma furta komai ba kan mgnr lailah, satin bimbii biyu ta murmure sosai don bata aikin fari bare na baqi kawai kula take samu saidai kewar qawayenta da take wato su lailah dukda kasancewar suna cikin gdn sarautan amma da akwai ta tazara sosai tsakanin 6angare zuwa 6angare, bimbii har yanzu batasan waye silar fitowarta daga kurku ba ita dai kawai ta samu kanta a hannun salma kuma itama salman bata fada mata wanda yasanya a fito da ita daga kurku ba, sati biyun na cika salma ta rakata zuwa 6angaresu, su israt kuwa tun safe suka tafi kurku suna zaton ranar za'a saketa amma har suka gama tsayuwarsu basu ga an bude kofar kurkun ba hk suka dawo jikinsu a sanyaye saidai mezai faru? suna dawowa daga ayyukansu ummul shukri ta shigo ta sanar da laila ta fito, duk suka biyo bayan laila suka fito, gabansu ne ya fadi lkcin da suka ga bayin dake aiki a kurkun qasa sun gane sune sbd kalar kayan dake jikinsu, suna ganin fitowarsu suka tmbyi ummul shukri wacce daga cikinsu ta nuna musu lailah,basu wani 6ata lkci ba suka tasa qeyar lailah suka tafi da ita,khulood da israt kuka suke sosai suna riqe lailah amma hk suka hankad'asu gefe suka wuce da ita,suna ji suna gani aka tafi da laila babu suka iya, toh suna cikin wannan jimamin ne suka ga shigowar bimbii, salma bata biyo bimbii ba tana kawota bakin 6angaren nasu ta juya, cike da mamaki duk suka miqe suna kallonta don kyau ma ta qara musu da gudu suka taho suka rumgumeta suna kuka, murmushi tayi musu ta duba bata ga lailah ba tace"ina lailah take, jikin nata da sauqi koh" gani tayi duk sun mata shiru, gabanta ne ya fadi don idan har ta tmbyi su lailah abu taga sunyi shiru sun sunkuyar da kawunansu toh amsar ce babu dadi, tace"wani abu ya faru ne" khulood tace" sun tafi da ita" tace" su waye" jan hannunta israt tayi suka koma suka zauna sannan suka zayyane mata abubuwan da suka faru, bimbii tayi shiru hawaye na fita daga idanunta,juya musu baya tayi ta kwanta bata kuma furta komai ba sbd zuciyarta quna take da tafasa, suna son tmbyrta abunda ya faru da ita amma sun fahimci sam bata mood nason mgn, bimbii kuwa wata irin tsanar wannan masarauta ce ta darsu cikin ranta,gani tayi abun yyi yawa su gbdy basu dauki rayuka a bakin komai ba,alwashi taci koda zata rasa ranta sai ta kubutar da lailah daga wannan hukunci na zalinci da suke son aiwatarwa akanta, washegari sunyi mamaki sosai da suka ga bimbii ta saki ranta ita kuma tayi hkne don ta sanyasu suma su saki ransu suyi ayyukansu yadda ya kamata kar suje suyi kuskure suma hukunci yahau kansu, yau bimbii ita daya ta dauki tulu ta tafi babbar qorama debo ruwa,tana zuwa ta tsuguna zata fara deban ruwanta ta hango wata tsuntsuwa mai kyau da daukar hnkli a jikin wata bishiya aikuwa sai ta ajiye tulunta ta soma lalla6awa da niyyar kama tsuntsuwar,tashi tsuntsuwar tayi ta sauya wuri, ita kuwa bimbii sai binta take wai ita zata kamata suna cikin hk har sukayi nisa da wurin qoramar data tabar tulun ruwanta, tsuntsuwar har bakin wani lambu takaita sannan ta tashi firrrrr ta6ar wurin,bimbii kallon tsuntsuwar take har ta qurewa ganinta, tsak tayi ta juya zata koma inda ta baro tulunta, hango yalwar bishiyoyi tayi a cikin wannan lambu kuma alamu sun nuna lambu yana cike da yalwar kayan marmari, kofar shiga lambu ta gani a bude, batare da wani tunani ba ta shiga lambun ta haye wata bishiyar tuffa tana tsinka tana ci, kishingida tayi abinta akan bishiyar tana cin tuffanta hnklinta kwance...
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



9

*Your love become my oxygen I can't live without you*......I'm infected with a serious virus on earth and you are the only doctor that can cure it......




Wani qasaitaccen k'amshi taji yana tashi ya had'e da ni'imatacciyar iskar dake kad'awa cikin wannan lambu, tashi tayi zaune ta leqa qasan bishiyar don ganin abunda ya haddasa wannan qamshi, abunda ta gani ne yyi mugun kad'a y'ay'an hancinta, PRINCE AKBAK!!.ne shida hadiminsa na hannun dama wato ubaid, tun shigowarsu suka ganta bisa bishiya abun yyi mugun basu mamaki, baiwa cikin lambu babban prince, ita kuwa bimbii tsabar tsorata kasa had'iye tuffan dake bakinta tayi ta sake baki tana kallonsu tamkar wata doluwa, prince akbar kuwa ko kallon bishiyar da take be sakeyi ba yyi gaba abinsa cikin qasaitaccen takunsa da yake bayyana tsantsar izzarsa da kuma isar matsayinsa, ubaid ya gama sanin halin babban prince, idan yana son bashi umarni da ido kawai idan ya kalleshi yana sanin me yake nufi take ze aiwatar, shi prince mgnr ce take masa mutuk'ar wahala tamkar d'an kurma hk yake sai tayi masifar kamawa yake bud'e bakinsa yyi mgn, wata irin tsawa ubaid ya doka mata wanda sauran qiris ya rage ta saki fitsari a wando ba shiri ta diro daga saman bishiya ta kife akan guiwowinta, kallonta ubaid yyi cike da qasqanci yace" wace ce ke? yanayinki kawai ya tabbatar min kedin qasqantacciyar baiwa ce amma ki rasa ina ya dace ki sauke raininki sai a lambun babban prince" kuka bimbii ta soma masa tace" don Allah kuyi hkr wallah ni bansan lambunsa bane" ubaid tsayawa yyi kawai yana kallonta don tabbas shi kansa ya yaba da k'arfin halinta, fuskarsa a murtuke yace" kije ki jira a waje" miqewa tayi sum sum tana d'an waiwayen baya musamman qaramar k'ofa dake cikin lambu da taga prince akbar ya shiga ya barsu a wurin,ubaid kuwa yana ganin ta fice yabi bayan prince cikin k'ofar shima sai gashi ya fito wani babban fili, prince ya hango yana gwada saitin harbin mashi, sauri yyi ya qarasa gefensa ya tsaya yana miqa masa masun dake hannunsa shi kuma yana amsa yana harbawa daidai saitin wata bishiya, bimbii kuwa tana wajen lambun tana jiran fitowar ubaid amma shiru shiru babu shi babu alamarsa har gari ya soma lumshewa,rana na dab da faduwa suka fito daga lambun tasha jira har ta gaji bacci ya dauketa a wurin, sai lkcin prince ya kalleta sosai tana baccinta a wurin, tsayar da idanunsa yyi sosai akanta abun har ya bawa ubaid mamaki don be ta6a ganin prince ya qurawa abu idanu hk ba, bud'e idanunta tayi a hnkli taga inuwar mutum tsaye akanta, k'afarsa kawai ta kalla tun kafin ta dago da kanta tasan mutum ne da hutu ya gama ratsashi,k'afarsa sanye take cikin wani farin takalmi half cover shoe, tunda take bata ta6a ganin mutum mai kyawun k'afa irin prince akbar ba, kafar nan tasa luwui luwui tamkar tumatir gata jajir da ita kamar ka matsa jini ya fito, jallabiya ce fara sol a jikinsa sai rawanin daya rufa a kafadarsa dayake ja da fari, gashin kansa baqin qirin ya sauka har kafadarsa yana rawa tamkar na mata,idanunsa tamkar yasa tozali gasu a lumshe kamar yanzu ya tashi daga bacci,sassayan k'amshinsa ne ya cika hancinta,dago da fuskarta tayi suka hada idanu take taji gabanta ya tsananta bugawa, yana ganin ta dago da idanunta yyi saurin dauke kansa akanta ya haye dokinsa shima dokin nasa fari, alamu sun nuna prince din yana qaunar farin abu, kallon ubaid kawai yyi shima ya haye dokinsa suka barta a wurin batare da sun ce mata komai ba, bin sawun dawakansu tayi da kallo har suka qurewa ganinta, tashi tayi tana karkad'e qasar dake jikinta ta soma tfy har ta isa inda ta ajiye tulunta yana nan inda tabarshi ta cika ruwanta ta dora aka ta nufi cikin gd,tunkan ta qarasa ta hango uwar bayi ummul shukri da tsumangiyanta

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment