Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

furta hkn gaban kowa, mahaifinka yana yin hkne duk don ya kare muhibba da daraja na wannan masarauta, ina son ka bashi hadin kai" shiru prince akbar yyi sai kuma ya bude idanunsa ya kalli mahaifiyarsa dake hawaye tana kallonsa yace" ranki ya dade idan har na furta hkn nayi qarya, cikin dake jikin wannan baiwa nawa ne bana wani bane sbd me zan qaryata hkn,kar ki damu dani ko halin da nk ciki a yanzu koda na fita daga nan ba lalle rayuwa tayi tsawo ba nima, nafi son nima na tafi na bar wannan duniya mai cike da rudani" kuka sosai sarauniya take tace" kafi fifita soyayyar mace fiye da soyayyar mahaifiyarka yarima" kallonta yyi sosai yace" soyayyarki ta daban ce cikin ruhina baki da mahadi nan duniya ranki ya dade" murmushi tayi hade da kuka a hade ta zauna dakanta take bashi abinci a baki cike da qauna,hmmm,uwa uwace Allah kabarmu da iyayenmu ka bamu ikon faranta musu, soyayyar uwa soyayya ce da babu alqus so ne na haqiqatan, idan mutanen duniya dukka sun gujeka uwarka tana nan tare dakai.............







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, saiki turon da screesht ta wannan layi a whatsapp...07041195806......







Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




30



*Without you in my life there is no happiness*.....how long can I wait for you my love💕💕



Cikin dare ta farka ta bude idanu ta ganta kwance bisa gadon asibiti, dakin babu kowa sai ita kadai, qoqarin miqewa take zaune taji duk jikinta yyi tsami tamkar wacce ta shekara tana jinya, ciza le6enta tayi ta miqe zaune dakyar, kofar dakin taga an turo ta waiga da sauri ta gano ummu farhan, tana ganinta zaune ta qaraso da yalwar fara'a a fuskarta tana mata sannu da jiki,daga kai kawai bimbii tayi,kamar yadda ta saba mata cup ta dauka ta zuba mata zuma a ciki ta bata ta shanye, shigowar Dr.maheer cikin dakin ne yasa su kallon kofa, tsayawa yyi chak yana qarewa bimbii kallo da take zaune riqe da cup a hannunta sannan ya soma takowa a hnkli ya qaraso wurin gadon da take, kallon dayake mata ne yasa ta dago da kanta ta kalleshi suka hada idanu, sam ita bata gane shi ba amma mamakinta shine meye yasa hk kawai shi wannan mutum ze tsareta da idanu hk, Dr.maheer kuwa tsabar mamakin bimbii ne ya qamar dashi a wurin ganin yadda ta nuna 2kwata bata ma gane shi ba, kallonta yyi sosai ya nuna mata cikin dake jikinta yace" wannan meye a jikinki" ummu farhan kallon maheer tayi galala sai kuma ta mayar da dubanta kan bimbii data sunkuyar dakanta tana kallon cikin dake jikinta, yace" daman hk kk ban sani ba, sai yanzu na fahimci abunda yasa ki gudu wato sbd baki samun abunda kk buqata koh" dukkaninsu kallon maheer suke da tarin mamaki musamman bimbii da ko kusa bata fuskanci inda zancen Dr.maheer yasa gaba ba, kallon ummu farhan bimbii tayi ta nuna maheer da hannu tace" ummu wannan waye shi" murmushi ummu farhan tayi tace" shine likitan daya duba ki" murmushi bimbii tayi tace" toh meye yake fada hk" dafata ummu farhan tayi tace" ki bar wannan mgn zamuyi anjima" wannan abu ba qaramin fusata Dr.maheer yyi ba yace" kin manta dani koh sbd kin samu tsinannen daya la'anta rayuwarki,uhumm" miqewa ummu farhan tayi cike da fushi tace" ya isheka hk mn, baka ganin halin da yarinya ke ciki ne kk takura mata da wasu zantuttuka nk" bimbii ta kalleta tace" ummu wai meye ke faruwa ne dani" daidai lkcin abeed da maheer suka shigo suka tarar da abunda ke faruwa, farhan ya kalli Dr.maheer yace" wai kai waye ne kk takura mn" murmushi Dr.maheer yyi ya fizgo hannu bimbii ya cire mata drift din dake hannunta tunda ya riga ya qare sannan ya dago dakansa ya kalli farhan yace" nine mamallakinta gbdy" abeed ya kalli Dr.maheer yana son mgn kuma sai yyi shiru can dai ya dago dakansa yace" doctor ita wannan da kk gani tana da matslr lose of memory bazata gane abunda kk fada ba yanzu" saurin kallon bimbii maheer yyi cike da mamaki, farhan kuwa haushi ne ya cika shi, ita kuwa bimbii kallon kowa take a wurin galalau tamkar wata sakarya sbd bata fuskanci abunda yake faruwa ba, juyawa abeed yyi ya fice daga dakin Dr.maheer yabi bayansa, office din Dr.maheer suka shiga ya nuna masa wurin zama ya zauna, 2tiryan abeed ya labartawa Dr.maheer yanayin daya tsinci bimbii, shiru yyi ya kasa mgn, dago dakansa yyi yace" kaima bakasan waye da cikin jikinta ba kenan" kada kai abeed yyi alamar ehh, gbdy kansa ya kulle ya rasa abunda ke masa dadi, miqewa yyi ya fice daga office din shima abeed ya miqe yabi bayansa, batare da wani 6ata lkci ba Dr.maheer ya nufi neurologists dept ya samu Dr.waaz suka tattauna, washegari aka sanya bimbii cikin wani na'urar don't bincika mtslr dake faruwa da kwakwalwarta, abunda suka gani kawai shine ta samu temporary lose of memory amma with time insha'Allah all past events ze din ga dawo mata cikin brain nata, cikinta dake jikinta kuma yana da watanni shida da kwanaki, lkcin daya ga result din shiru yyi sbd shi sai yanzu ne yarda tayi losing memory, kwananta uku sukayi discharge nata amma 2qiri Dr.maheer ya nunawa abeed wlh bimbii wurinshi zata koma tunda ita din property dinsa ce yana da certificate na mallakarta, farhan da umminsa suka doge kan basu san wannan zance ba, Dr.maheer yace" idan kunki bani ita da arziki toh hukuma zata bani ita" abeed mutum ne mara son hargitsi tashi daya ya damqawa Dr.maheer bimbii, farhan baqin ciki kamar ze kashe shi, ranar qin yiwa kowa mgn yyi, bimbii kam bata san abunda ke faruwa ba sai wayar gari tayi ta nemi wannan iyali ta rasa sun tafi sun barta a asibitin ko sallama abeed be bari sun mata ba sbd kar hnklinta ya tashi ko kuma taqi amincewa, Dr.maheer ya shigo dakin dakansa ya sanar mata tfyrsu sannan ya shaida mata duk abunda ya faru, yace" yanzu gida na zaki koma da zama" wani irin kallo ta masa mai kama da harara sai kuma ta fashe da kuka tace" kai wanne irin mutum ne hk kawai zaka rabani da dan'uwana da iyayena" murmushi yyi yace" su waye iyayen nk? uhum, ko ban furta miki ba kina kallon launin fatarki da nasu kinsan basu ne iyayenki ba ai suma tsintarki sukayi da cikin da basu san daga inda kk samo shi ba,kona arziqi kona tsiya nafi gani ma dai na tsiyan ne" qura masa idanu tayi kawai tana sauraron baqaqen maganganun dake fita daga bakinsa kan cikin dake jikinta da ita kanta batasan a ina ta same shi ba, murmushin rainin hnkli ya mata daya ga tana kallonshi ya noqe kafadarsa tare da ta6e baki, badan ta so ba hk ta tashi tabi bayan Dr.maheer suka fita daga dakin suka fice compound na hospital din sai 2waige take ko zata gano ummu farhan ko farhan amma bata ga ko masu kama dasu ba, bude mata mota Dr.maheer yyi ta doge taqi shiga saida ya matso da niyyar daukanta ya cusata ciki tayi saurin shiga motar,farhan kuwa yana la6e daidai gate din fita daga hospital din yana kallon fitowarsu, hawayen dayake 6oyewa suka soma sauka kan quncinsa yana kallo har suka fice daga hospital din, tana ta 2kalle ta jikin glass din motars, har suka qaraso wani wurin inda ta hango tarin mahaya dawakai suna wucewa, wannan abun yaso tuna mata da wani abu amma ta kasa tunawa dole ta hkr, suna shiga farfajiyar gdn yyi parking yar motar shi gefe sannan ya fita ya bude mata ta fito, sai kallon gdn take har suka shiga building din maheer,two bedroom flat ne don hk ya bata daki daya, zama tayi a dan qaramin parlourn nasa sai qarewa ko'ina kallo take, shi kuwa ya shige bedroom nasa sai can ya fito sanye da three quater baqi da wata shirt ya shiga kitchen dakansa ya hada mata black tea da honey meast ya kawo gabanta ya ajiye, sannan ya tafi ya gyara mata bedroom din nata, ni kuwa nace lalle yaushe maheer ya zama bawan baqar fata,dakyar bimbii ta yarda tasha black tea, nuna mata dakinta yyi ta tashi ta shiga, dakin madaidaci mai kyau, ita gabanta har yanzu be bar faduwa ba sbd ta lura tunda ta shigo wannan gd bata ga matar gdn ba, tashi tayi da sauri ta sanya key ta rufe kofar sannan ta koma ta kwanta, maheer kuwa yazo ya buga ya buga taqi budewa so yake ta fito tayi dinner amma qirmishishi taqi bude kofar kuma tana jinsa sarai hk ya hkr ya koma yyi dinner dinsa shi kadai, bimbii kuwa kwanciya tayi ta matsantawa kanta da tunani don tana son tuna abubuwa amma kwakwalwarta tamkar ta toshe hk har kanta ya soma sara mata, hk bimbii ta cigaba da rayuwa a gdn maheer shi kuwa yana qoqari wurin bata kulawa yana ture damuwarsa kan cikin dake jikinta, ennah mahaifiyar maheer har yanzu batasan maheer ya gano baiwarsa ba don be sanar da ita ba hkma yayansa, masarautar burham kuwa tsantsar makirci ne yake kai kawo a cikinta, sarki abdallah yaqi sakin prince akbar duk kuwa da iyakar qoqarin neman afuwa da sarauniya keyi a madadinsa kullum ba dare ba rana amma sarki abdallah bin jabal shegen taurin kai ne dashi tamkar na kafiran farko, sarki abdallah yana zaune a dakin ganawar sirri shi da prince nasaar suna tattauna kan yadda zasu buda harkar kasuwanci tsakanin masarautar burham da manyan qasashe na turai, sarki abdallah bin jabal yana daya daga cikin manyan merchants na duniya dake fita da danyen gold a kasuwar duniya, shiyasa ya tara arxiki na ban mamaki, prince nasaar ya fito da wani qaramin akwati ya ajiye a gabansa yace" takardar yarjejrniyar kasuwanci ne tsakanin wannan masarauta da qasar japan" saurin daukan qaramin akwatin sarki abdallah bin jabal yyi ya bude, wata farar takarda ya gani a ciki kai tsaya yasa hannunsa ya fito da takardar ya soma warwarewa, prince nasaar yana kallonsa har ya gama warware farar takardar, hannunsa ne daya riqe takarda ya soma rawa sosai sbd qarfin gubar dake tattare da wannan takardar, dago idanunsa yyi yana kallon yana son yin mgn amma ya kasa,shi kuwa prince nasaar sai zabga murmushin qeta yake yana kallon sarki abdallah dake jan jiki,abunda ya shirya ya tafi daidai, mirqinewa sarki abdallah yyi daga kujerar dayake yana qoqarin nuna prince nasaar da hannu, prince nassar ficewa yyi daga 6angaren yana fita ya tura babbar hadimar sarki abdallah ciki kan sarki na buqatar ganinta tana shiga ta tarar da sarki abdallah cikin wannan yanayin, da gudu ta fito tana sanar da masu tsaron lfyrsa, arresting dinta sukayi kan itace tayi poisoning dinsa, wannan lbri tuni yakai kunnen sarauniyya mar'atussaliha, a gigice ta iso 6angaren ta tarar da gubar ta soma shiga jikinsa sosai,prince nasaar kuwa batare da wani bincike ba yasa takobinsa ya cire kan wannan hadima kan ita tayi poisoning din sarki, sarki abdallah kuwa ba bakin mgn balle ya furta abunda ke bakinsa yana son yin mgn amma ya kasa sai kallon nasaar yake, miqewa sarauniya tayi ta umarci kowa ya fita aka barta daga ita sai uxair sai kuma sarki, prince nasaar yaso ya tsaya amma sarauniya ta nuna shima ya fita dole ya juya ya fice,kallon uxair sarauniya tayi tace" ina son ka haxarta kai tsaye kaje a fito da prince mahaifinsa na son ganinsa" rissinar dakai uxair yyi alamar ya amsa umarninta sannan ya fita, kallon qaramin akwatin dake gefen sarki abdallah tayi ta qurawa akwatin idanu, prince nasaar kuwa tuni ya sanar da prince amir cewa aiki ya kammala, zaki ya kwanta dama wato sarki abdallah kenan, zaki ya kwanta dama shi kuwa dan zaki yana rufe, wannan itace kyakykywan dama da zasu iya amfani da ita wurin murqushe wannan masarauta ta burham, dayake a shirye suke tsaf tuni suka zagaye wannan masarauta da dakarunsu masu qarfin kayan yaqi, prince nasaar dakansa yasa a cinnawa wannan gdn kurku da prince akbar ke ciki wuta sbd so yake ya 6atar da tarihin sarki abdallah bin jabal da dukkanin ahlinsa, sarki najash wato mahaifin prince amir ya riga ya alqawarta ma sarki hamxa idan har ya taimaka musu suka ga bayan masarautar burham toh zasu samu cikakken dama wurin gauraya da manyan qasashen duniya musamman qasashen jar fata wurin kasuwanci, suna ganin kamar masarauta burham ita ta babbanke komai sbd tana da qarfi, su" 2kwata ba'a damawa dasu a kasuwar duniya........







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karatun littafin zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419, alhaji shahida nasir,union bank,saiki turon da screenshrt na payment dinki a whatsapp ta wannan layin...07041195806......







Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



31


*I miss you like crazy*....I will keep up waiting until the end of my last breath💕💕




Idanunsa na lumshe ya jingina da jikin qarfen kurkun yaji ana bude wurin dayake, dago idanunsa yyi sukayi idanu hudu da uxair babban hadimin mahaifinsa, kallon prince yyi ya rissinar dakai sannan ya qara bude masa kofar fita yace" yakai wannan dan sarki mahaifinka na son ganawa dakai" shiru prince akbar yyi sannan ya miqe suka fito, fitarsu kenan suka ga wuta ta kama wannan gdn kurku sai kururuwar mutane ake jiyo daga cikin wannan kurku, cike da mamaki prince ya kalli uxair yace" wannan ne dalilin dayasa kk fito dani sbd ku kashe bayin Allah marasa gata" girgixa masa kai uxair yyi yace" yakai wannan dan sarki wannan sharrin abokan gaba ne yanzu hk sun sanyawa mahaifinka guba yana cikin wani hali sannan gbdy masarauta a zagaye take da dakarunsu kowanne lkci zasu iya cimmu a yaqi" kallon prince yyi yace" yakai wannan hadimi ma'abocin kwarjini ina son ka dakata anan ka bada taimako wurin kashe wannan wuta" batare daya jira amsar uxair ba yyi wani irin tsalle ya haye dokin daya gani gabansa ya sakar masa linzami yyi hanyar da zata sadashi da masarautar burham, tun tahowarsa bisa doki kwararrun maharba mashi suke saitinsa, suna la6e ne bisa kan manyan tsaunika saitinsa kawai suke da mashi, abunku da jarimin gaske jikinsa ne kawai ya bashi tamkar akwai masu harinsa, cikin tsantsar hikima da zafin nama ya juya kan dokin dayake kai suka bar kan miqaqqiyar hanya suka fada cikin jeji, su kuwa maharan suna ganin hk suka tabbatar ya fahimci ana harinsa ne yasa yyi musu hk, dayake jejin na da duhu da sarqaqiya tuni ya soma shiga wannan sarqaqiya har ya samu damar 6ace masu ya fice daga wannan jeji, saidai tun daga nesa ya hango qatuwar kofar masarautar burham a rufe, wasu manya dakaru sun zagaye kofar ta waje suna son fasa kofar su afka ciki, qara gudun dokin yyi ya tunkari wannan rundunar mayaqan, ba jira kawai ya janyo wani bisa doki yyi wulli dashi ya amshe takobin hannunsa ya daga takobin sama tsirararta kafi kace kwabo kawai ya soma shayar da wannan takobi dake hannunsa jinin abokan gaba, wata irin bajinta yake nunawa tamkar wani ifiritin aljani hk yake fada ba gjywa, dakarin masarautar burham dake saman qanuwar masarautar suna hangen artabun dake wakana tsakanin wadannan dakaru da babban prince, fada yake cike da sadaukarwa batare da shakkar mutuwa ba domin zuciyarsa ta bushe qamas baya tsoron mutuwa ko kadan, daga idon da zeyi ne ya hango prince amir dakansa ya saitinshi da mashi, yana harbo mashin ya damqo wani daga cikin mutanensu ya tare mashin dashi,gbdy jikinsa ya 6aci da jini sai lkcin masu tsaron babbar kofar shiga masarautar burham suka wangale kofar dakarin sarki abdallah suka soma fitowa sanye da shigar yaqi saidai lkcin prince akbar shi kadai kawai ya riga yaci qarfin yaqin, abun mamaki prince nasaar na cikin dakarin masarautar burham domin har yanzu babu wanda ya fahimci fuska biyu ne dashi, tsayawa yyi yana kallon yadda prince yyi musu 6arna, tsoronshi daya kar suyi failing plan dinsu sbd idan har aka samu mtsl tabbas daga shi har mahaifinsa suna cikin mtsl don sun san masarautar burham saita dauki fansa akansu, shiga cikin wannan filin artabu ya somayi sai yyi kamar yana yaqar dayan 6angaren, prince akbar kuwa yana tsaka da fatattakar wannan dakaru ya hango fitowar dakarin mahaifinsa sanye da shigar yaqi, juyawa yyi ya cigaba da 6arar da maxa abinsa, prince nasaar cikin hk ya samu qarasowa kusa da prince akbar, prince ya ganshi amma ya dauka a 6angarensu yake don hk ya juya ya cigaba da fadansa, ba zato kawai yaji saukar takobin prince nasaar a qirjinsa, juyawa yyi yana kallon prince nasaar da mamaki yaga ya sake daga takobinsa da niyyar yanke kansa cikin zafin nama ya bige dokin da prince nasaar yake kai ya fadi qasa yasa sawun dokinsa ya takeshi ya wuce abinsa, takobin daya sara masa bata samu damar ratsa shi sosai ba don hk ya cigaba da wasa da jinin abokan gaba, cikin qanqanin lkci suka musu kyakykywar 6arna, tsirarun dakarinsu sarki najash suka soma ja da baya suna neman gudu, prince amir kuwa ya dade da arcewa tunda yaga 6arnar da ake musu daman shi ba wani jarimi bane a filin fama barshi dai da iya hada tuggu, lkcin da prince yaga abokan gaba sun soma arcewa sai yaja gefe ya sauke takobinsa qasa sai digar da jini take ya nufi wurin da abokan gaban suka kafe tutarsu ya tugeta ya jefar, salute kawai dakarin masarautar burham suke masa cike da girmawa, hk suka soma shiga cikin babbar kofar masarautar burham cike da murnar samun nasara akan abokan gaba, tun daga kofa yan mata ne jere sunyi ado suna rera waqar yabo da jinjina ga jarimai mazan fama wadanda suka sadaukar da rayuwarsu sbd kare mutunci masarautarsu, suna rera waqar ne cikin harshen larabci hannunsu dauke da furanni suna watsa musu suna daga musu hannu alamar barkansu da dawowa lfy, prince kuwa fuskar nan tashi tamkar hadari sai bin dokinshi suke suna zuba masa fure suna masa baitoci da jinjinar ban girma bisa namijin jarumtarsa, cikin waqar tasu suna danganta shi da zaki dan zaki, jarimtar gadonsa ce ba haure ba, hk dai suka din ga binsa da baitocin yabo har ya isa cikin gdn sarautar burham, nan ma ya samu tarar girma ga dukkanin bayi da masu tsaron wannan gida hk suka raka shi da baitoci, sarauniya na 6angaren sarki abdallah wannan lbr na isowar danta ya taddata, ummu nana ta sanar da ita prince akbar shine yyi uwar watsi da maqiya ya kuma cire musu tuta, wannan kyakykywan labari yasanya xuciyar sarauniya tayi haske duk da alhinin da take ciki na ganin sarki abdallah bin jabal kwance rai a hannun Allah, tana zaune gefen sarki abdallah prince ya nemi iso take ta bashi damar shigowa, cikin sauri ta tashi ta rumgume shi tana kuka sai kuma ta soma duba jikinsa ko ya samu rauni, murmushi yyi ya riqe mata hannunta suka qarasa inda sarki abdallah bin jabal ke kwance, kallon mahaifin nasa yyi sosai yana nazarin symptoms na poison din dake jikinshi, hannu yasa cikin aljihunsa ya fito da wata qaramar kwalba ta antidote din daya ta6a baiwa bimbii ya bude bakin mahaifin nasa ya tsiyaya masa, wannan antidote shima dattijo abbas ne ya ta6a bashi lkcin daya ceto rayuwarsa a hannun sarki najash, antidote din yana kashe qarfin kowanne irin guba, sarauniya ta kalleshi tace"ka gafarci mahaifinka bisa kuskurensa gare ka yakai wannan jarimin dan sarki" riqo hannayenta yyi yace" komai laifinsa gare ni mahaifina ne shi dole ranki ya dade" murmushi tayi kawai,prince ya jima a 6angaren mahaifinsa suna tattaunawa da sarauniya kafin ya dawo 6angarensa, komai na 6angaren nasa yana nan yadda yake sannan bayin dake hidimtawa 6angaren kowa yana kan aikinsa,lenah itace daman mai kula da makwancin prince 6ata wasa da aikinta, ubaid yana shima yana kan aikinsa, prince yana shiga ya bada izini baya buqatar ganawa da kowa, lenah ce kawai ta samu damar shiga ciki, batare da 6ata lkci ba tayi masa gyaran fuska ta wanke masa qafa, ta rage masa tsawon suman kansa data sauko masa har baya tamkar gashin mata ta maida shi ya dawo kafadarsa,tuni sumar tasa ta soma walwali da sheqi tana daukar idanu, duk abunda take gani yake kamar bimbii ce take masa hidima,6angaren gidan maheer kuwa bimbii bata masa aikin fari bare na baqi komai shine yakeyi dakansa, idan ya dafa abinci tunkan yaci ze kawo mata nata ya zauna ya sata gaba har sai taci sannan zeci nashi, wani lkci idan ya zauna yana kallonta sai ya qurawa cikin jikinta idanu ya tunanin uban waye da wannan ciki, ji yake tamkar idan ya hadu da wanda yyi cikin nan ze iya kashe shi sbd baqin kishin dayake ji idan ya kalli cikin amma a hk dole yake daurewa yake hidimta mata sbd qarfin so daya rinjayi qarfin qiyayya, kullum idan ya shirya fita aiki sai ya ajiye mata komai kusa da ita tamkar wacce bata iya motsi sannan baya fita sai ya tabbatar ya rufe duk wata kofar fita ta gdn, gani yake kamar idan yabar kofa bude bimbii zata sake guduwa ta fice daga rayuwarsa ta barshi da dawainiyya da dakon soyayyarta, idan ya dawo sai ya dubata ya tabbatar ita da abunda ke cikinta suna cikin qoshin lfy, fatar jikinta tuni ta murje tayi kyau da santsi sbd cima da take samu mai kyau da gina jiki,duk bala'I bata bari maheer ya matso kusa da ita tuni zata matsa nesa dashi, wannan abu yana masa ciwo amma Allah ya dorata akansa yadda komai takeso shi yake tamkar wani bawanta,ranar wata laraba ennah mahaifiyarsa ta kawo masa ziyarar bazata, lkcin data ga bimbii abun ya mugun bata mamaki da daure mata kai musamman data ganta da ciki, kallon Dr.maheer tayi tace" a ina ka samota" sosa qeya ya somayi yace" a asibitinmu mn" wata uwar harara ta doka masa tace" shine baka fadamin ba yaushe ka soma 6oyemin abu" murmushi yyi yace" sorrryy" cikin wasa ya furta hkn ya soma riqe mata hannu, fizgewa tayi cikin fushi ta kalleshi tace" wannan cikin dake jikinta na uban waye?! ko kana nufin kacemin a hk ga gano ka kuma amince ta dawo gdnka sbd kai daqiqi ne" kalaman mahaifiyar tashi sun masa tsauri sosai tuni ya tamke fuska, sam shi be saba ganin ennah na masa fada ba ta shagwa6a shi dayawa, batare data kula da hade ran daya yyi ba ta dokawa bimbii tsawa tace" ke cikin uban waye a jikinki" bimbii kuwa jikinta rawa yake ta tsorata da matar kawai kallonta take ta kasa mgn, ennah ta nunawa bimbii hanyar fita tace" ina son ki fita ki kama gabanki ko waiwaye wannan gdn kar ki kuma yi" saurin kallonta maheer yyi yace" what are talking, did you mean ta tafi ta barni kenan" murmushi yyi yace" idan ta tafi nima zan bita mu tafi tare cox she is my life" galala ennah tayi tana kallon abun mamaki..............







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419, alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screenshrt ta whatsapp through wannan layin....07041195806.......









Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




32


*Come back to me my love*......I can't hold back my tears, I can't forget your beautiful face,I'm missing everything about you my sweetheart💕💕



Ennah ta daka masa wata rikitacciyar tsawa tace" are you in your right sense? kai makaho ne baka ga abunda ke tare da ita bane, maheer mai ke faruwa dakai ne, just cox of this

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment