Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

stupid slave you are exchanging word with your mother" bimbii kuwa jikinta na rawa sbd tsorata da tayi ta soma qoqarin fita ta gudu, charaff, maheer ya riqe mata hannu, kallon ennah yyi yace" I just want to marry her" wata irin zabura ennah tayi tana masa wani irin kallo irin wanda ake yiwa masu ta6in kwakwalwa, tunani ta somayi anya maheer be samu matsl a brain nasa ba kuwa, murmushi tayi kawai ta juya ta fice daga gdn gbdy ta shige mota driver nata yaja suka nufi gd, tun a mota zuciyarta ke kai kawo da tunani barkatai game da bimbii,tana isa gd ta kira faisal tayi masa bayanin kan abunda ya faru, shiru yyi sai can yace" kinsan rigimar maheer amma ina ganin kawai abunda yafi ki dauki yarinyar ki mayar da ita kasuwar saida bayi inda kk siyota ki musanyo da wata amma kar ki kuma kawo mn baqar fata" murmushi tayi tace" hkn ya kamata nayi kam" maheer kuwa dakyar ya rarrashi bimbii yyi ta bata hkr kan kar ta damu babu inda zata mutuqar yana raye, washegari, ya shiga kitchen ya hada breakfast ya kawo mata har dakinta, tana daga kwance tana faman tunani taga ya bude kofa ya shigo, saurin miqewa zaune tayi tana kallonsa, wani qaramin stool ya jawo ya ajiye mata honey tea din daya kawo mata da wani abu kamar samosa a small plate, yace" ga breakfast ki tashi kici sai kiyi wanka ki kwanta ni zan tafi hospital" daga masa kai kawai tayi ya juya ya fita daga dakin, qaramin briefcase dinsa ya dauka ya fice wajen building din ya hau qaramar motarsa ya nufi hospital, bimbii kuwa a hnkli ta sanya hannu ta dauki cup na tea din tana sipping cike da sanyin ciki ga cikinta sai motsi yake mata, hannunta ta dora kan cikin nata tana shafawa, hawaye ya soma sauka saman kumatunta ba komai ne yasata kuka ba sai rashin sanin waye da wannan cikin dake cikinta wanda akanshi kowa sai tsangwamarta yake, gani take kawai ita tamkar rayuwa take mara alqibla don batasan komai game da rayuwarta ba, sautin qarar bude kofan da taji ne yasata kallon kofar shigowa dakinta, shiru bata ga kowa ya shigo ba, tashi tayi da sauri ta nufi kofar ta dan bude don leqawa aikuwa idanunta ya nuna mata ennah, faisal ne yasa wani key ya bude kofofin shigowa building din gbdy don maheer ya rufe ko'ina, qoqarin rufe kofarta take ta sanya key faisal yyi saurin turowa, kallonta suka tsaya yi cike da mamaki wato har ma daki ne da ita na musamman cikin building din maheer,ennah tace" ki fito mu tafi" kallonsu ta tsaya yi saida faisal yyi mata tsawa sannan ta fito, hk suka tasata a gaba har bakin motarsu, cikin sauri driver ya bude mata butt ba musu ta shiga ya rufe butt din, ennah da faisal suka shige bayan mota suka zauna drivern yaja suka fice daga gdn, kai tsaye kasuwar saida bayi suka wuce da ita, yawanci masu cinikin bayin sun qi siyenta sbd basu son mai ciki sun fi son suna siyen bawa su siyar dashi amma ita idan sun siyeta saidai suyita wahala da ita masu siye basu son mai ciki, ennah da taga kowa yaqi siyen bimbii sai kawai ta kalli wani daga cikin masu saida bayin tace" toh gata na baka ita kyauta" washe baki balaraben mutumin ya somayi yana dariya cike da jin dadi ya mata gdy sosai, ennah ta siya wani bawan suka shige motarsu suka tafi, bimbii kuwa balaraben ya sanya gefe cikin bayin da basu da kasuwa don be sanya cikin kejin siyar da bayi ba kar masu siye su qi qarasowa wurinsa idan suka hangi mai ciki cikin bayinsa, wasu manyan hadimai ne daga masarautar abu ansar suka shigo wannan kasuwa don siyen bayi, masu cinikin bayi kuwa suna ganinsu suka soma zuwa wurinsu da gudu suna nuna musu bayinsu don tun daga ganinsu sun san daga gdn sarauta suke kuma sun san sarakai bayi dayawa suke siye basu siyen dai dai, su kuwa wadanda manyan hadiman gdn sarauta sai wani shan qamshi suke suna tfy suna kalle kallen kejin da bayi ke ciki, tsayawa sukayi wurin kejin wannan balarabe da bimbii ke wurinsa, kallonsa sukayi suka ce suna son siyen dukka bayin dake wurinsa, jikinsa na rawa ya shiga rumfarsa ya soma rubuta musu certificate na mallakar bayin da suka siya ya fito ya miqa musu, har zasu wuce dayan ya kalli bayin dake gefe yace" wadannan bana saidawa bane" da gudu balaraben yace" suma na saidawa ne ranka ya dade" yace" toh meyesa baka hada dasu ba" shafa dogon gemunsa yyi yace" su wadannan suna da yar matsala ne shiyasa" nuna bimbii yyi da yatsa yace" waccer ita ciki gare ta sauran kuma basu da cikakken lfy" murmushi daya daga cikin hadiman yyi yace" bamu son marasa lfy amma ita mai cikin tana da cikakken lfy ne?" cikin sauri balaraben yace" ita tana da cikakken lfy kawai cikin ne mtslrta" yace" ka hada mn da ita" da gudu ya shiga cikin rumfarsa ya rubuta musu certificate na mallakar bimbii ya kawo musu, hk suka din ga bi keji keji suna siyen bayi suka hada bayi dayawa suka kwashesu cikin wata doguwar mota suka nufi masarautar abu ansar, sarki abu ansar aminin sarki abdallah bin jabal ne sosai kuma shima masarautarsa tana da qarfi sosai, yana da ya'ya mata guda biyu, gimbiya khamriyya da gimbiya mariyatul kifdiyya wacce itace akayi yarjejeniyyar aure tsakaninta da prince akbar, dukkanin wadannan gimbiyoyi kyawawa ne na gaban kwatance, gimbiya mariyatul qifdiya itace qarama, sarki abu ansar ya dora buri sosai kan wadannan yara nasa yana mutuqar son su baya son 6acin ransu ko kadan, lkcin da manyan hadiman wannan masarauta ta abu ansar suka iso da bayi, tuni uwar bayi ramlatul asuwat tayi jawabi ga wadannan sabbi bayi ta sanar dasu duk wasu dokoki na wannan gd, tana gamawa ta rarrabasu 6angarori daban daban na wannan gdn sarauta tare da basu ayyuka daya dace da kowanne, kallon bimbii tayi ta ganta da ciki tace" ke zan kai ki turakar jira sbd anan baki da aiki amma can qila wani ya buqaci mai yaron ciki" kallonta bimbii kawai take don ita bata fuskanci ina ne turakar jira ba, turakar jira wuri ne da ake ajiye mata masu kyawun jiki da siffa mai kyau dake iya daukar hnklin maza sbd da tarar manyan baqi, idan aka kai mace wannan wuri bata da aiki saidai gyaran jikinta da kula dakanta da kwalliya da sutura mai kyau, toh idan akayi wasu manyan baqi a wannan masarauta akan zo turakar jira a za6i mata a kai musu don su debe musu kewa, suyi musu tausa su kwana dasu idan suna buqata, duk macen dake turakar jira toh amfaninta kenan a wannan masarauta, batare da wani 6ata lkci ba ramlatul aswat ta miqa bimbii hannun suwaiba wacce itace mai kula da matan dake turakar jira, suwaibah kallon bimbii tayi da murmushi a fuskarta tace" tabbas zaki samu wurin zama a wannan turaka sbd kina da siffa mai kyawun gaske duk da kasancewarki baqar fata" ita dai bimbii bata fahimci kwata kwata me suwaiba take nufi har ta kira wata baiwa tace" kije ki gyara wannan sabuwa ce tana buqatar a koya mata dabarun jan hnkli da kula da jiki,amma yanxu ki shiga da ita ki soma gyarata tukunna" kama hannun bimbii tayi suka shige ciki, dogon gashin bimbii ta soma wankewa tayi masa tas sannan ta hada sinadaran wanka ta kalli bimbii dake tsaye tamkar wawuya tace" ki shiga kiyi wanka da wadannan sinadarai" ba musu bimbii ta shige dakin wanka, tana wanka tana ganin datti sosai na fita sbd wadannan sinadaran wanka basu barin datti a fata, tana fitowa wannan baiwa mai suna rabi'at ta zaunar da ita ta soma shafeta da kayan gyara, tuni fatarta ta soma sheqi da daukar idanu tamkar ba baiwa ba, gashin kanta shima ya kwanta har tsakiyar gadon bayanta, sai kyalli yake,ita dai bimbii sai kallon ikon Allah take gani tayi sai gyarata ake tamkar wata amarya, kayan mai kyau rabi'at ta bata ta sanya ta nannade mata gashnta yyi tudu tamkar a cuci sannan ta yafeta da wani mayafi mai shara shara, turare kuwa an mata 6arinshi, maida ita tayi dakin da suwaiba take, tana ganinta tayi murmushi tace"masha'Allah" basu sanya bimbii cikin jerin masu tarar baqi ba sai ta kware sosai wurin iya hillata da kissa da sauran dabaru na janye hnklin maza kafin su sanyata cikin jerin matan dake tarar manyan baqi, daki na musamman aka kaita inda ta ga dukkanin mata dake dakin sunyi ado na kece raini suna zazzaune, wata hamshaqiyar mace zaune tana koyar dasu salon tfy da rausaya da iya juya jiki har ma da yadda zasuyi taku a gaban namiji, tashin kowacce take cikinsu daya bayan daya suna gwada yadda zasuyi taku da karkada jikinsu don su janye hnkli, bimbii sakwato tayi tana ganin abubuwan mamaki, lalle kuwa cikin akwai salon rayuwa 2kala sai wanda idanunka suka iya gani da wanda kunnuwanka ya ta6a ji, ita dai bimbii gata ta shigo duniya tana diban darasi 2iri mai amfani da mara amfani, yau dai ga bimbii Allah ya jefota masarautar abu ansar kuma a turakar jira,6angaren masarautar burham kuwa jikin sarki abdallah bin jabal dai toh har yanzu dai cigaban kadan aka samu da taimakon wannan antidote da prince akbar ya bashi yanxu yana iya motsa jikinsa, prince tunda yake be ta6a tsintar kansa cikin halin rayuwa irin wannan ba, ga mahaifinsa babu lfy ga bimbii besan tana raye ko a mace ba, yau shi kadai yana tsaye bakin wannan glass window din dayake tsayuwa hannunsa dukka a bayansa, sanye yake da wasu fararen pakistan, gashin kansa yyi luf luf don yana shan gyara, fuskarsa ta dan fada hkn ya baiwa dogon hancinsa damar fitowa dodar tamkar biro,sajensa kwance gefen fuskarsa, kallon waje yake tamkar mai tuna wani abu hannunsa na dama riqe da wadannan awarwarayen na bimbii, lenah ce ta shigo hannunta riqe da wani qaramin faranti mai kyan gaske ta ajiye saman wani table, takowa tayi a hnkli wurin dayake tsaye ta tsaya a bayansa tare da rissinar dakanta qasa tace" ranka ya dade ka kwantar da hnklinka insha'Allah jikin sarki mai daraja zeyi sauqi bada jimawa ba" shiru ya mata kuma be jiyo ya kalleta ba, idanunta ne yakai kan hannunsa na dama inda ta ga yana riqe da wasu awarwaraye, mamaki sosai ya cikata take tunanin ko wannan awarwaron wacce prince yake riqe dashi, cigaba tayi da tsayuwa har ya juyo ya wuceta ya koma kan wata kujera ya zauna ya janyo alqalami da farar takarda yana rubutu, tahowa tayi wurin ta soma tsiyaya masa herbal tea din data kawo masa, hannun biyu tasa tare da rissinar dakanta qasa tana miqa masa cup din, dago da kansa yyi ya kalleta sannab yasa hannu ya amshi cup din ya ajiye ya daga mata hannu, hkn yasa ta dauki farantin data kawo ta juya ta nufi hanyar fita jikinta a sanyaye, ubaid ne ya shigo ciki da sauri ya tsaya tare da rissinar dakansa qasa yace" ranka ya dade muna da baqi daga masarautar abu ansar" .....







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,idan kin tura saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp a wannan layin...07041195806....






Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



33


*I still love you, I still miss you*.........I just want to see you back,pls come back I'm still waiting for you💕💕



Baqi ne daga masarautar abu ansar sun iso ne bisa wakilcin ammar bin jabir don duba jikin sarki abdallah bin jabal,sun samu tarar girma sosai cikin masarautar burham, sarki abdallah kam yanzu jikin nasa babu laifi tunda yana iya miqewa zaune saidai baya iya furta komai,masarautu da dama sun ji dadin wannan cuta da sarki abdallah bin jabal ya kwanta, 6angaren da sarki abdallah ke jinya kuwa ko quda be isa ya ratsa ta wurin ba sbd tsatstsauran matakan tsaro, iyalanshi kawai keda damar shiga su duba shi shiyasa har yanzu babu wanda ze iya bada tabbacin ya jikin sarki abdallah yake ana samun cigaba ko ba'a samu game da lalurar data tadda shi, yau da dare sarki abdallah bin jabal ya daga idanu ya kalli prince akbar dake zaune gefensa yana son furta masa wata kalma amma babu bakin mgn, miqa hannunsa yyi yana buqatar a bashi takarda da alqalamin rubutu, prince ne ya dauki alqalamin da takarda ya miqa masa don ya fahimci abunda yake nufi, amsar takardar yyi ya soma rubutu a hnkli,yana gamawa ya ajiye alqalamin ya miqawa prince akbar farar takarda, amsar takardar yyi yana duba abunda ta qunsa, umartar prince akbar yyi kan yabi wadannan baqi da suka zo daga masarautar abu ansar don ganawa da sarki abu ansar da kuma yarsa gimbiya mariyatul qifdiya, saurin dago idanunsa yyi yana kallon mahaifin nasa cike da mamaki, sarauniya dake zaune gefe ta amshi wannan takarda dake hannun prince akbar ta duba, saurin dago idanunta tayi ta kalli sarki abdallah bin jabal tace" ranka ya dade, yanzu lfyrka itace mafarin farko a gare mu ba batun aure ba don Allah ka kyale wannan mgn har Allah ya tashi kafadunka,tayaya prince ze tafi nesa hk alhalin kaima da kanka kana buqatarshi kusa dakai" kau da kansa yyi gefe alamar hkn dai yakeson ayi, kun dai san taurin kai irin na sarki abdallah sam a tsarinshi baya zance biyu, washegari prince akbar tare da rakiyar babban hadiminsa ubaid da kuma wadannan manya baqi da suka zo suka dugumxuma suka nufi masarautar abu ansar, tun kan su isa sarki abu ansar yasan da zuwan prince akbar don hk ya shirya liyafar girma don tarar wannan dan sarki ma'abocin daraja da qarfin izzah,sun qawata wannan masarauta da kayan ado, jan carpet aka shimfida dogo inda takan wannan carpet prince ya taka har ya samu isa cikin fadar sarki abu ansar, yana zaune bisa kujerar mulkinsa fuskarsa da yalwataccen murmushi dakansa ya miqe ya riqo hannayen prince akbar ya zaunar dashi a kujerar da aka tanada domin shi,sarki abu ansar yyiwa prince akbar dayake tamkar surikinsa barka da ziyartar wannnan masarauta, bayan wannan jawabi na sarki abu ansar sai liyafar da aka shiryawa prince akbar ta soma gudana, gimbiya mariyatul qifdiya kuwa tunda ta samu lbrin zuwan prince take ta murna har farin cikin nata ya kasa 6oyuwa, gimbiya khamriyya tayi ruwa tayi maqarbiya wurin kimtsa tilon qanwarta tata sbd ta fahimci mariyatul qifdiya bata da masoyin data mallakawa ruhinta kamar prince akbar, gimbiya mariyatul qifdiya tayi kwalliya na ruwan zinare hannu,wuya har ma da qafa, sanye take cikin wata lafiyayyen jar doguwar riga da mayafinta data yane kanta dashi,riga ce irin wacce yaran sarakai da manyan attajirai ke iya sakawa,gbdy ta zaqu ta gana da masoyinta prince akbar, shi kuwa babban prince ana qare wannan liyafa sarki abu ansar yasa aka kaisa royal louge na wannan masarautar,6angare ne na musamman suka tanada sbd baqi jinin sarauta, wurin yyi kyau sosai don an qawata wurin tun daga farfajiyar 6angaren idanun mutum zasu soma lumewa kan kyakyawan furanni masu mutuqar daukar hnkli tare da kukan tsuntsaye ta ko'ina,babban hadimin sarki abu ansar jamal tare da wasu hadiman suka yiwa prince akbar rakiya zuwa wannan royal louge, ubaid na biye da prince akbar har ya shiga cikin wurin shi kuma ubaid da sauran wadannan hadimai suka tsatstsaya a bakin kofa don tsaronsa, prince na shiga ya samu komai tsaftsaf, zama yyi bakin wani gado na alfarma yyi shiru, 6angaren turakar jira kuwa inda bimbii take lbrin isowar wannan dan sarki ya iso ga suwaibah don hk ta tashi ta shiga inda yan mata suke don za6o mai cikakken dirin halitta da kaifin basirah ta kasance da wannan dan sarki don hidimta masa, yan matan duk suna zazzaune kowacce tayi ado na a kalleta, kallonsu take daya bayan daya, idanunta ne ya sauka kan bimbii, tace" ke tashi na ganki" miqewa bimbii tayi a hnkli ta tsaya suwaibah na qare mata kallo tun daga sama har qasa, kallon buqasassun hips dinta tayi daya fito sosai ga albarkatun fulaninta tsaye qam tamkar danyar budurwa duk da cikin dake cikinta, kowacce a cikin yan matan burinta a za6eta don tarar wannan dan sarki amma sai suwaiba ta nuna bimbii tace" maxa ki biyo baya na" mamaki ne ya cika kowa wurin sbd kowa yasan ba'a tarar jinin sarauta da baiwar da ba virgin ba wato danyar budurwa toh don me shugaba zata za6i bimbii wacce take da yaron ciki,suwaiba kuwa sam bata duba hk ba abunda kawai tayi la'akari dashi shine bimbii tafi dukkaninsu cikar dirin halitta ta cikakkun matan girma burin kowanne da namiji duk da kasancewarta baqar fata kuma mai yaron ciki, kai tsaye dakin gyara ta wuce da ita ta shiryata dakanta cikin wasu sexy dress masu mutuqar janye hnkli ta taje mata gashin kanta ya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta sannan ta dauko wata abaya fara sol ta sanya mata ya rufe wannan shiga dake jikinta,gashin idanunta kuwa shima yasha gyara yyi baqi qirin hasken kwayar idanunta kawai ake iya gani ga lips nata yasha pink lipatick sai glowing yake, murmushi suwaiba tayi yadda taga bimbii tayi masifar kyau na gasken gaske, hamshaqiya ramlatu ce ta shigo ta kalli bimbii sai kuma ta kalli suwaibah tace" shugaba wannan wa zata tara hk" murmushi suwaiba tayi tace" zata tari dan sarki prince akbar na gimbiya mariyatul qifdiya ma'abocin cikakkiyar izzah" hamshaqiya ramlatu tayi saurin kallon suwaiba cike da mamaki tace" amma baki gani wannan ba budurwa bace sannan cikin darasin jan hnkli da ake koyar dasu sam bata da fahimta gashi tana dauke da yaron ciki shugaba karki saba doka kinsan cikakkiyar izzah irin ta jinin masarautar burham tayaya zaki tari wannan dan sarkinsu da baiwar daba budurwa ba qarewa ma tana dauke da juna biyu wannan tamkar gangaci ne kk shirin aikatawa" dafata suwaibah tayi tace" sam babu gangaci cikin wannan hikima tawa baki da sani cewa prince akbar shine masoyi kuma miji ga gimbiya mariyatul qifdiya,itace ta umarceni kar na sake na tura virgin din baiwa ga masoyinta" shiru hamshaqiya ramlatu tayi tana tunani, tabbas ba komai ne yasa gimbiya mariyatu tayi hk ba sai tsantsar kishi irin nata bata son suwaiba ta tura danyar budurwa ga prince akbar don tasan idan ma yana da tunanin mace ta debe masa kewa yaga an tura masa baiwa mai yaron ciki tasan babu ta yadda za'ayi ya sauke buqatarsa kan wannan baiwa sbd yana da cikakkiyar izzah bazai ta6a kusantar macen da take a bude ba, kuma dakyar ne be koreta ba, ita kuma gimbiya mariyatu hk take so sbd tana da kishi akansa sosai, lkcin da gimbiya mariyatul qifdiya ta nemi ganin suwaiba ta sanar da ita buqatarta, murmushi suwaibah tayi tace" ranki ya dade kar damu don yanzu hkma ina da wata baiwa cikin yan matana dake dauke da yaron ciki kuma gata bata da wata dabara na janye hnklin namiji ita zan tura masa"wannan batu na suwaibah ba qaramin sanya gimbiya mariyatu qifdiya farin ciki yyi ba har saida ta yiwa suwaiba kyautar zoben gwal,bayan an gama shirya bimbii suka fito suwaiba ta kama hannun bimbii ta sanyata cikin keken doki wasu hadimai hudu suka soma jan keken dokin suka wuce da ita royal louge don tarar wannan dan sarki, suna isa ta sakko daga keken dokin fuskarta rufe da mayafi, babbar baiwar dake kula da wannan 6angare mai suna aslamiyya ita ta miqawa bimbii wani kyakykyawan kwando dan qarami mai dauke da kayan marmari ta nufi hnyr shiga cikin wannan 6angare, masu tsaron dake kula da wurin suka bata hanya cikinsu har da ubaid, sam be ganeta ba domin fuskarta a rufe take da mayafi ya bata hanya ta shige,tfy take a hnkli bawai da niyyar yanga ba ko jan hnkli ba saidai kawai ita daman hk Allah ya mata wannan baiwa, idan tana tfy tamkar tarwada duk wasu ma'adanai na jikinta juyawa suke suna tsole idon masu budadden ido suna musu kwalele,cikin wannan irin salon tfy ta samu shiga wannan louge, tsarin wurin yyi mata kyau sosai, bata bude mayafin data rufe fuskarta dashi ba amma tana ganin komai a hk, prince kuwa yana zaune bisa wata kujera fitowarsa kenan daga wanka don be aminta wata baiwa ta taimaka masa wurin wanka ba koh a gida babbar baiwar kadai keda wannan yancin bare a masarautar daba tashi ba, aslamiyya ita ta fara shiga wurinsa kafin bimbii ta iso ta hada masa ruwan wanka a kwarmin wanka ta sanya sinadaran wanka tana gama wannan aiki ya daga mata hannu alamar ta tafi baya buqatar komai bayan hk, yana daga zaune yaji motsin shigowa amma be waiga ba har ta tako inda yake zaune ta tsaya a bayansa,ta bude fuskarta ta dora kyawawan hannayenta wanda ke sanye da awarwaraye masu kyan gaske ta dora bisa kafadarsa ta soma masa tausa...........






Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, idan kin tura saiki turo da screenhrt na payment dinki ta whatsapp a wannan layin...07041195806........






Alkalamin Bintuu ne.......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



34


*My heart is bursting,my heart is beating more and more*......the time I set eyes on you I was totally confused💕💕




A hnkli take masa tausan tamkar tana tausayin jikinsa, yanayin yadda take masa tausan yasa shi lumshe idanunsa yana tuna wacce take masa irin wannan tausan wato bimbii, ji yake tamkar itace ke masa tausan sbd exactly yadda take masa hk wannan baiwar take masa, so yake ya dago da kansa yaga wannan baiwa saidai izzah irin tasu ta jinin sarauta na yawo a jikinsa, daga mata hannu yyi alamar tausan ya isa hk, gabansa ta dawo ta tsaya tare da rissinar dakanta qasa sannan ta dago dakanta ta dauki tuffa daga cikin qaramin kwandon data shiga dashi na kayan marmari ta sanya wata kyakykyawar qaramar wuqa ta yanka tuffan ta sake rissinar dakanta tana miqa masa slice na tuffan,shi kuwa babbar prince yana tozali da fuskarta numfashinsa ya dauke na wasu sakanni kafin ya dawo hnklinsa, zuciyarsa bugawa ta somayi da qarfi tamkar zata fasa kirjinsa ta fito ya qureta da idanu ko qiftawa baya yi cike da tsantsar mamaki, ita kuwa bimbii kanta na sunkuye tana riqe da tuffan da take miqa masa jin shirun yyi yawa ne yasa ta dago dakanta tana kallonshi, kallon daya qureta dashi ne yasa taji gabanta ya fadi, miqewa yyi a hnkli yasa hannunsa ya dago da ha6arta yana kallon cikin qwayar idonta cike da tarin rudani, gani yake tamkar gixo take masa ko kuma mafarki yake, ita kuwa bimbii rawa jikinta ya soma tamkar mazari sbd daman taji tattaunawar shugaba suwaiba da hamshaqiya ramlatu kan zuwanta tarar wannan dan sarki matsayinta na mai yaron ciki sai take gani kamar ganin cikin dake jikinta ne yasa wannan dan sarki yi mata hk, sauke hannunsa yyi yana cigaba da kallonta, gani yyi a tsorace take dashi hkn ya nuna tamkar bata gane shi bane,gabansa ne yaji ya yanke ya fadi, maida kallonsa yyi kan qaramin cikinta daya turo sosai ya jima yana kallon cikin sannab ya dago da jajayen idanunsa da tashi daya suka sauya launi, idanunsa ne suka sake bata tsoro tayi saurin ja da baya, a hnkli ya soma takawa har ya isa inda take tsaye ya matsa jikinta sosai tamkar ze hade jikinsu, ita kuwa bimbii ji take tamkar ta saki fitsari a wando sbd tsabar tsorata da tayi dashi, cikin wata irin murya mai cike da rudani yace" me kk nufi? baki gane ni ba?" mgn ta soma cike da qinqina tamkar me koyon

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment