Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magunguna daga jakar dake rataye a kafadarsa, wuraren harbin mashin ya soma zubawa garin maganin, 6angaren sarki abdallah kuwa jira kawai su dawo masa da kan bimbii da kuma dansa prince akbar,shi yana son ya hukunta prince dakansa bisa laifin daya yyi, sai dare suka koma ga sarki abdallah ba bimbii ba prince akbar, hkn ba qaramin 6ata masa rai yyi ba yasa a rufe dukkanin dakarin, sarauniya mar'atussaliha kuwa kuka sosai take ta kasa cin abinci ba yadda ummu nana batayi da ita ba kawai ita danta take son gani, gimbiya hindu ita ta labarta masa abunda ya faru, miqewa tayi tsaye da sauri ta fice ta nufi 6angaren sarki abdallah bin jabal, tana shiga ta zube a gabansa tana kuka sosai tana roqonsa don girman Allah yasa a nemo mata danta, kallonta kawai yyi ya tashi yabarta a wurin, durgushewa tayi tana kuka kamar ranta ze fita, prince akbar shi kadai ne dansu yanzu gashi silar wannan baiwa ta rasa danta gudan jininta.........







Littafin nan na kudi ne, idan kin idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct.....0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turomin da screesht ta whatsapp da wannan layin 07041195806......





Alkalamin Bintuu ne.....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



28


*You are the only one I can hear*.....You are the only one I can feel cox you are are the reason of my living💕💕



Bimbii kuwa tunda ta fada wannan dogon rami bata kuma sanin inda kanta yake, dulmiyewa tayi cikin wannan ruwan dake kwaranya tamkar na 6ul6ula, ruwan zuba yake shaaaa daga jikin wani dutse gashi fari tas dashi, karfin ruwan ne ya janyeta ta fada wani qaton ruwa wanda yyi iyakar yankin burham da yankin dilham, wannan ruwa shi ya raba tsakanin yankunan guda biyu,qananan jiragen ruwa da manyan kwale kwale masu safarar bayin zuwa yankunan qasashen larabawa 2daban suna ratsawa ta wannan dogon kogi, igiyar ruwa ce tayi tfy mai nisan gaske da ita takaita ga6ar wannan kogi cikin izinin ubangiji wani mutuqin kwale kwale mai suna abeed ya hangi gangar jikinta a yashe gefen wannan kogi igiyar ruwa ta watso ta ga6a, cikin sauri ya nufi wurin don tabbatarwa kansa yana zuwa kuwa ya ganta kwance babu alamun ruhi tattare da gangar jikinta, sunkuyawa yyi yakai hannunsa daidai wurin bugawar numfashinta yaji shiru, duk da hk be hkr ba yasa hannu ya dinga dannan cikinta ruwa ya soma fita mata ta hanci ta baki har saidai ruwan data sha ya fita, jikinta yyi sanyi tamkar qanqara hkn ya tabbatar masa cewa ta jima a cikin ruwa, yatsunsa biyu ya kuma pointing kan qahon zuccinta sai lkcin yaji dif dif alamun akwai sauran ruhi tattare da gangar jikin nata, daukanta yyi yasata cikin kwale kwalensa ya shige ya soma tuqa kwale kwalen nasa har suka fita asalin ga6ar da yake da 2hadar jama'a, duk wanda ya gansa sai yyi zaton baiwarsa ce ta kasa har jaje ake masa hk ya samu ya wuce da bimbii, abeed mutumin dilham ne kuma masunci ne yana zaune shi da iyalinsa a wani qaramin gdn katako kusa da wannan kogi, matar shi daya da d'ansa daya dan kimanin shekaru ashirin sunan shi farhan, matar shi saudat ta tausaya mutuqa da taga halin da bimbii ke ciki, hk suka din ga bata taimakon daya dace kasancewarsu masunta, saudat ta dumamawa bimbii jikinta sosai yadda jikin nata ya dauki dumi sosai, kallon daya ta yiwa bimbii ta fahimci tana dauke da juna biyu, hk suka cigaba da bata duk wani taimako kusan sati guda kenan amma bimbii bata ta6a koda motsi ba bare su sanya mata ran samun lfy, dansu farham a lkcin yana high schl ne ajin qarshe, ba wasu mawadata bane talakawa ne saidai sun fi qarfin cikinsu, bimbii saida tayi sati uku chur tana kwance tamkar mutum mutumi amma basu gjy da kula da ita ba, yau da dare saudat tana kasa mata jiki kawai taga yatsun qafarta sun motsa, murza idanunta tayi ta kuma kallon kafarta taga tabbas motsi take da yatsun qafarta, kwalawa danta farhan kira tayi suka shigo cikin dakin da gudu shi da abeed, nuna musu yatsun kafar bimbii tayi su ga tana motsasu, murna sosai suka somayi tamkar wata jininsu,washegari, da sanyin safiyya saudat ta shigo dakin da bimbii ke kwance sai ganinta tayi idanunta bude tana 2kalle dasu, matsowa tayi da gudu ta zauna kusa da ita ta riqo hannayenta tana mata sannu, ita kuwa kawai binta take da idanu tamkar wata kurma,6angaren prince akbar kuwa shikam be dauki wani tsawon lkci ba, kwanan shi biyar kwance abbas yana bashi magungunan da suka tsuge dafin mashin daya soke shi, a kwana na biyar ya bude idanunsa, ubaid da abbas ba qaramin dadi sukaji ba na ganin prince ya farka, suna dai cikin wannan kogon dutsen dashi sbd sarki abdallah bin jabal har yau be hkr da nemansu ba, prince akbar ya zamto wanted ga masarautar burham,mtslr shine har yanzu suna cikin yankin masarautar burham basu da hnyr da zasu iya ficewa daga yankin masarautar burham sbd nemansu ake ruwa a jallo, prince akbar ya farfado kuma yana cigaba da amsar magani wurin dattijo abbas saidai tunda ya farfado har yau be tankawa kowa ba, da tunanin bimbii ya farka ita kawai yakeson gani a halin da yake ciki, d'an sarki mai cikakken izzah wanda ya saba kwana bisa tattausa yau shine ya samu kansa cikin wannan kogon dutse amma shi duk ba wannan ne ya dame shi ba,babbar damuwarsa shine shin bimbii tana raye ko tana mace, idan har bimbii bata raye toh shikam be ga amfanin tasa rayuwar ba sbd itace mahadin ruhinsa itace bugawar numfashinsa, wadannan irin tunani su suka zame masa sana'a, ubaid ya fara damuwa da yanayin da yake ganin prince ciki sai yake ganin kodai ya samu wata mtslr ne, dattijo abbas yace ya kyale prince ya kadaice da zuciyarshi, prince akbar ko gama samun sauqi beyi ba ya fito daga wannan kogo, ubaid ya kalleshi ya rissinar dakansa qasa yace" ranka ya dade dakarin masarauta sun bazu ko'ina nemanka kawai suke idan kayi wani wuri yanzu zasu iya ganinka" kallon prince yyi sannan ya dauke kansa ya juya sai can yace" gudu yana ga raggo ne amma namiji baya gudu a fagen fama koda hkn na nufin ajalinsa" yana gama fadar hk ya kama dokin dake daure yahau ya sakar masa linzami yabar wurin, kai tsaye wurin ramin daya tura bimbii ya nufa, yana qarasawa wurin ya sauka daga kan dokin ya nufi wurin ramin ya leqa qasan ramin ya tabbatar da tsayinsa batare da wani shakka ba ya soma shirin afkawa cikin dogon ramin shima ya isa duniyar da bimbii take, murya da yaji bayansa ne yasa shi juyawa, ubaid ne yace" ranka ya dade kafin ka aikata hkn ya kamata kasan halin da sarauniya take ciki tun ranar daka bar masarauta ta kwanta babu lfy kuma jikinta ya tsananta tana da burin sake ganinka kar ka kashe kanka batare daka gana da mahaifiyarka ba" kalaman ubaid sunyi tasiri mutuqa sun sanya ya soma begen ganin mahaifiyarsa duk da laifinta gare shi amma uwa ai uwa ce" jiki a sanyaye ya koma ya haye dokinsa kawai bisa mamakin ubaid sai kawai gani yyi babban prince ya dauki hanyar masarautar burham, tun daga nesa dakarin dake tsaron kofa suka hango shi batare da wani 6ata lkci ba suka bude masa kofar wannan gdn sarauta ya shige da dokinsa, duk wanda yaga prince sai ya cika da mamaki, tuni wannan albishir yakai kunnen sarauniya sannan yakai ga sarki abdallah bin jabal, umarni ya bayar a rufe kowacce kofa ta wannan masarauta sannan ya sake bada umarni a kama prince a miqashi kurkun qasa, prince yana sauka daga dokinsa yaga dakarin tsaron wannan gd sun tsagayeshi ta ko'ina dukkaninsu riqe da makamai, sarauniya bata da masaniyyar wannan umarni da sarki abdallah ya bayar saida ummu nana ta shigo ta shaida mata, prince kuwa fuskar nan tashi tamkar hadari ya kalli wadannan dakaru yace" duk wanda yakeson uwarsa ta haifi wani ya cigaba da tsayuwa anan" dukda sun san jarimtarshi amma basu kauce ba don suna mtuqar shakkar mahaifinsa sarki abdallah bin jabal, prince wata qaramar wuqa ya ciro daga jikin dokin dake gabansa ya nufi shiga cikinsu, kai tsaye yaji muryar mahaifiyarsa daga bayanshi tace" idan har nina haifeka kar ka kuma aikata wannan abu,bani son ka kuma zare takobinka bisa umarnin mahaifinka kabi umarnin shi" juyawa yyi a hnkli ya hango an turota a wheel chair, sauke wuqar dake hannunsa yyi ya qarasa inda take a hnkli ya tsuguna gabanta ya dora kansa bisa cinyarta ya rufe idanunsa, hawaye take sosai tasa hannunta tana shafa kansa, daidai lkcin sarki abdallah bin jabal shi da tawagarsa suka qaraso wurin, fuskarshi babu digon afuwa, dago dakai prince akbar yyi ya juya sukayi ido hudu da mahaifin nasa, dauke kai sarki abdallah yyi ya kalli dakarun dake wurin yace" ku miqashi kurku" kafin ya rufe baki sun matso wurin da prince yake suka kama shi, saurin cire musu hannu yyi daga jikinshi ya kalli mahaifin nasa yace" zan tafi dakai na" wucewa yyi gaba suka bishi a baya, sarauniya ta fashe da kuka ta kalli sarki abdallah tace" don Allah kayi masa aikin gafara" be kalleta ba bare ta sanya ran ze bata amsa ya juya abunshi yan fadansa suka take masa baya, ummu nana ta tura wheel chair din da sarauniya ke kai ta koma da ita 6angarenta tana kuka, ita kanta tasan sarki abdallah ba qaramin kafiya ne dashi da taurin kai ba shima kuma dan nasa hk yake ai gado ba karambani bane, bude masa kofar kurku sukayi ya shige ya zauna abinsa suka maida kofa suka rufe, bimbii kuwa tana samun kulawa yadda ya kamata daga wurin saudat da danta farhan saidai babban tashin hnklin shine bimbii tayi losing memory nata, 2kwata bata iya tuna komai ta manta duk abunda ya faru da ita ta mance ita wace ce,komai koya mata ake hatta mgn da yadda ake cin abinci dama komai, farhan yana mutuqar qoqari wurin kula da bimbii da koya mata abubuwa, shidai abu guda ne ya tsole masa idanu game da bimbii shine wannan jikin dake jikinta ya tsani yaji ance bimbii tana da ciki, sudai sun tsinci bimbii basu san ko tana da aure bane ko bata da aure sudai kawai sun ganta da ciki kuma gashi tayi losing memory nata bata iya tuna komai bare su nemi ta sanar dasu wace ce ita, yau da gobe jikinta ya warware saidai komai nata cikin sanyi take yinsa, bata son mgn shiru shiru, farhan shi kullum mamaki yake wai bimbii yar qarama da ita amma tana da ciki don shi gani yake ya girmi bimbii, tun bimbii bata mgn har ya dage ya soma sanyata mgn, hk yake shiriricewa kullum gabanta yana bata labarai na ban dariya, ya maida bimbii tamkar wata qawarshi itama saita dauke shi aboki kuma dan'uwanta don ita duk zatonta saudat itace ta haifeta, farhan kuma qaninta ne saidai ita mamakinta meyesa ita bata kaisu hasken fata ba, tana yawan yiwa farhan wannan tmbya shi kuma sai ya shashatar da zancen, a kwana a tashi cikin bimbii kullum qara girma yake, tmbyr saudat tayi wai meyesa cikinta ke girma hk, murmushi kawai saudat tayi tace" kar ki damu wataran zaki haifa mn baby ne" shiru tayi bata kuma cewa komai ba,hk rayuwa ta cigaba da tfy, shaquwa sosai ta shiga tsakanin bimbii da farhan sun zama tamkar abokai,wata rana sun je bakin teku kallon ruwa, farhan ya kalli bimbii yace" ki bani wannan zoben na hannunki yana min kyau" kallon zoben bimbii tayi wanda ita bata ce ga yadda akayi zoben ya shiga hannunta ba tace" zoben nan yana min kyau a hannu bani cireshi don ma kaji" dariya yyi yace" toh shikenan ai" prince akbar kuwa tunda sarki abdallah ya sanya shi cikin kurku ya dauke masa kai, kuma yace ayi treating nasa equal da sauran prisoners, babban damuwa prince bimbii ce, shi kansa yana mamakin irin son da yake yiwa bimbii, duk daren duniya sai yyi mafarkinta, hali yake ciki na quncin zuciya da damuwa, tun yana daurewa har abu ya soma cin qarfinsa sai wayar gari akayi prince na aman jini, sarauniya kam kullum tana hanyar wannan kurku kuma kusan duk ranar duniya saita neman wa prince gafara wurin mahaifinsa amma ya kafe kai da fata sai prince ya gane kurensa kafin ya fito dashi kuma sai ya fito duniya ya qaryata soyayyarsa ga wannan baiwa sannan ya nesanta kansa da cikin dake jikinta idan yyi hk kawai shine ze iya yafe masa, wannan abu kuwa shine abu mafi tsauri ga prince akbar, bazai ta6a qaryata soyayyar bimbii ba hkma cikin dake jikinta duk kuwa da cewa besan ko tana raye ko bata raye ba........







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screesht na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806....





Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




29


*Only one person fill my heart*.....You are the reason of my breathing,I love you so much dear💕💕




Yau bimbii na kwance ita kadai a daki sbd tun safe take jin jikinta wani iri babu dadi amma tana ta daurewa batason ummu farhan ta gane halin da take ciki, ummu farhan ce ta shigo dakin hannunsa riqe da wani qaramin cup da zuma a ciki, bimbii na ganinta tayi saurin miqewa zaune, murmushi ummu farhan tayi ta miqa mata qaramin cup din dake hannunta tace" ki shanye zuma ce tana cike da sirrika na magunguna 2kala musamman wurin mace mai juna biyu" murmushi bimbii tayi tasa hannu ta amshi cup din ta soma shan zumar har ta shanye, da dare lkcin cin abincin dare duk suna zazzaune kan wata qatuwar darduma duk sun harde kafafunsu suna cin abinci, farhan ya kalli mahaifinsa abeed yace" abu itama andal akaita mkrt mn" dago dakai abeed yyi ya kalli 6angaren da bimbii ke zaune yace" andal wai kina son mkrt" murmushi bimbii tayi tace" ehh abu ina so" kallonta farhan yyi ya kalli cikinta daya dan turo sosai ya ta6e baki ya cigaba da cin abincinsa, ummu farhan ta kalli abeed tace" amma dai ba yanzu ba saita haihu tukunna" farhan ya dago ya kalli bimbii yace" nikam ban ta6a ganin yarinya qarama kamar ki da ciki ba" iyayen nasa ne sukayi saurin kallonshi tare da harararsa sai yyi saurin sunkuyar dakansa qasa, shima kawai zancen ne ya kubce masa sbd ya tsani ganin wannan ciki a jikin bimbii da suke kira da andal, bimbii kuwa tsuru tayi tana son tuna wani abu amma kwakwalwarta ta toshe duk wata kafa ta tuna mata abunda ya faru da ita a baya, ummu farhan ce ta dafata da murmushi a saman fuskarta tace" andal ko bacci kkji ne" daga mata kai tayi alamar ehh, kamo hannunta tayi suka miqe suka nufi dakin kwanan bimbii, gyara mata wurin kwanciya tayi tace" ki kwanta saida safe" kallonta bimbii tayi tace" Allah ya bamu alheri" murmushi tayi ta sunkuya ta shafa kan bimbii tace" ameen summa ameen"bimbii cikin dare ta tashi zaune, bayanta taji ya riqe qam ga wani irin ciwo da mararta take mata duk ta hada gumi, hk ta din ga fama har asuba tayi ta soma jin motsin abeed da farhan zasu fita masallaci, tana cikin wannan hali ummu farhan ta shigo dakin, cikin sauri ta qarasa wurin da bimbii ke durqushe riqe da mararta, tace" andal mene ke damunki,kiyimin mgn" bimbii ba bakin mgn sai idanu kawai take bin ummu farhan dashi, ummu farhan kam tasan ba haihuwa bane sbd cikin nata bekai mizanin haihuwa ba saidai idan wani ciwon ne daban, ruwan zaitun da zuma ta bata ta sha, suna cikin hk su abeed suka dawo, farhan ne ya shigo dakin ya tarar da abunda ke faruwa, shigowa yyi cikin dakin a rude yana kiran suna bimbii, tana jinsa amma ba bakin amsawa, juyawa yyi ya fita da sauri ya sanarwa mahaifinsa, abeed ya shigo shima cikin dakin, farhan ya kalli mahaifinsa yace" ina ganin kawai mu wuce da ita asibiti" kada kai abeed yyi alamar hk za'ayi, cikin wannan safiyya farhan da abeed suka fita, suna fita suka tarar da wani tsoho yana jan keken dokinsa, alfarma abeed ya roqeshi kan ya amince ya fitar dasu bakin babban hanya ko zasu samu abun hawa zuwa asibiti,wannan majanyin keken doki kuwa ya amince suka fito da bimbii suka sanyata ciki tare ummu farhan mai keken dokin yaja suka tafi, sunyi tfy mai nisan gaske kafin suka isa bakin hanyar motoci ke wucewa, dakatawa sukayi har su abeed suka qaraso sannan suka tsayar da wata mota suka shige, daidai king faisal specialist hospital motar tasu ta tsaya suka fito dukkaninsu har da bimbii, suna shiga hospital din wadanda ke yawo da gadon daukar marasa lfy suka dauki bimbii suka shige da ita,wata nurse ta wuce da gudu zuwa office din doctorn dake kula da wannan 6angare ta sanar masa an kawo wata patient mai juna biyu dake buqatar taimakon gaggawa, doctorn be dago kai ya kalleta ba saida ya gama danne dannensa a laptop din dake gabansa sannan ya dago dakansa yace" kije gani nan zuwa" juyawa tayi ta fita sbd idan da sabo duk sun saba da halin DR.MAHEER mugun dan I dnt care akan patients, hknlinsa kwance ya miqe ya fita daga office din nasa, farhan da abeed na ganin fitowarsa suka nufo shi da sauri, be sauraresu ba yyi wucewarsa cikin dakin da bimbii ke kwance,qarasawa yyi bakin gadon da take yana kallon ruwan drift din dake shiga jikinta sannan ya maida dubansa ga saman fuskarta......wani irin bugawa gabansa yyi da karfi ya qurawa fuskar bimbii idanu, tabbas shidai yasan bazai ta6a mance wannan fuskar ba cikin rayuwarsa, fuskar da kullum take masa gixo ba dare babu rana, mamaki yyi mutuqa na ganin ciki a jikinta, juyawa yyi ya kalli nurse din dake gefensa ya nuna cikin dake jikin bimbii yace" meye wannan a jikinta" nurse din kallonsa tayi cike da mamaki sai kuma ta kalli cikin bimbii dayake nunawa da hannu tace" tana da ciki ne doctorn" cikin tsantsar rudewa yace" what!" nurse din sai abun ya soma bata tsoro ta soma kallon Dr.maheer da tarin mamakin wannan action din nasa, yace" waye ya kawota" tace" wadanda suka kawota suna waje" juyawa yyi da sauri ya fita yana fita farhan yyi saurin shan gabansa yace" yy jikin nata" tsayawa yyi yana qarewa farhan kallo tun daga sama har qasa sannan yace" kaine ka kawota?" cikin sauri yace" ehh, nine" Dr.maheer yace" kai waye nata?" kai tsaye yace" mata ta ce" wani irin kallo maheer ya masa sai kuma ya juyar dakai yana wani irin murmushi mai ciwo, cike da axama ya juya ya chakumi kwalar rigar farhan da idanunsa da suka kala sukayi jazir, ummu farhan da abeed dake gefensu sukayi saurin qarasowa wurin suna mamakin abunda ya hada Dr.maheer da farhan, maheer da idanunsa suka juye sbd tsantsar bala'en kishi ya kalli kwayar idanun farhan yace" kasan wacce ita a wuri na kk fadamin wannan iskancin nk" farhan da idanunsa suka firfito sbd tsaurin shaqar da maheer ya masa yace" kaima kasan wacce ita a wuri na" hknne yasa maheer yyi jifa dashi gefe daya, yace" wlh,wlh bazan kyaleka ba saika fuskanci hukunci" wucewa yyi a mugun fusace ya wuce office dinsa yasa key, nurses din dake tsatstsaye da sauran ma'aikatan asibitin kowa ya cika da mamakin wannan abu, Dr.maheer kuwa kifa kansa yyi kawai a saman table din dake gabansa ya fashe da kuka tamkar wani qaramin yaro, meyesa bimbii tayi masa hk, meyesa bimbii ta bawa waninsa dama har ya ratsa gonar da ba tashi ba, shikam ko a ido ya raina shekarun farhan amma wai wannan danyen yaron bimbii ta baiwa kanta yyi mata wannan danyen aiki, tsananin so tare da tsantsar qiyayyar bimbii su sukayi tarayya cikin zuciyarsa, shi kansa ya rasa wanne ne yafi rinjaye, miqewa yyi a hnkli ya dauki handkerchief dinsa ya goge hawayen fuskarsa sannan ya dauki farar rigarsa ta likitoci yasa ya bude office dinsa ya fita, dakin da bimbii take ya shiga ya tarar da nurses sun zagayeta don bleeding take sosai, suna ganin shigowarsa suka bashi wuri, kai tsaye ya soma gudanar da aikinsa akanta batare daya kuma kallon fuskarta ba, cikin izinin Allah ya samu nasarar tsaida jinin dake zuba sannan ya mata allurar bacci mai nauyi, yana gama aikinsa ya fito daga dakin ko kallon inda su farhan suke beyi ba saida abeed ya miqe da sauri yasha gabansa yace" kayi hkr abunda yaro na ya mk don Allah ka dubamin diyata dakyau" kallon mamaki maheer ya masa sai kuma yyi murmushi yace" ka ta6a ganin inda mutum yyi wasa da rayuwarshi?" dukkaninsu kallonsa sukayi don basu fuskanci me yake nufi da hk ba, be sake kallonsu ba ya koma office dinsa, farhan dogarewa yyi daidai bakin dakin da bimbii take har lkcin da nurse ta basu damar shiga su ganta, cikin sauri duk suka miqe suka shige dakin, samunta sukayi tana bacci, farhan ya zauna gefenta yana kallon fuskarta yana hararar cikin dake jikinta don gani yake duk wannan cikin ne ke wahal da ita,ummu farhan riqo hannun bimbii tayi tana mata addu'ar samun lfy, ranar Dr.maheer a asibiti ya kwana ya kasa tfy gida, bini bini ze leqa dakin da bimbii ke kwance, idanunsa kuwa sunyi jajir sbd kukan daya sha, kishi ne kawai ke wahal dashi mutuqar ya bude idanu yaga bimbii dauke da jikin waninsa sai zuciyarsa tayi daci,6angaren masarautar burham kuwa har yanzu sarki abdallah bin jabal na nan kan bakansa, wannan abu dake faruwa shine ya bawa prince nasaar damar samun shiga sosai wurin sarki abdallah, prince nasaar ya samu cikakken iko da fada aji cikin wannan masarauta ta burham, hkn shine ya bashi damar fito da abunda ya jima a qasan ruhinsa wato daukar fansa kan sarki abdallah bin jabal, prince nasaar da ne ga sarki hamxa mai sarautar birnin al' bait, sarki abdallah bin jabal shine silar rusa wannan kyakykawan birni ya dawo dashi qarqashin mulkinsa, qarfi da shahara da masarautar burham ke dashi idanun duniya yasa batare da wani jayayya ba sarki hamxa ya miqa wuya ga sarki abdallah bin jabal inda birninsa ya dawo qarqashin inuwar masarautar burham, sarki abdallah dakansa ya nemi sarki hamxa ya bashi riqon prince nasaar tun yana qarami sbd yana son masarautarsa ta qulla zumunta ta musamman da masarautar al'bait, wannan shahara da daukaka da masarautar burham ta samu ya mugun tsolewa masarautu da dama idanu burinsu su durqusar da wannan izzah ta sarki abdallah bin jabal, prince nasaar babban burinsa shine masarautar burham ta dawo qarqashin izzah da sarautar birnin mahaifinsa, wannan kudiri nasa yasa shi cigaba son cigaba da kasancewa cikin wannan masarauta yana aikawa da sirrin wannan masarauta birnin al'bait saidai har wayau masarautarsu batayi tsayin da zata iya hada kafada da masarautar burham ba, prince akbar ya kasance babbar garkuwa ga wannan masarauta ta burham sbd tsantsar jarimtarsa hadi da sharp intelligency nasa, rufe prince akbar da sarki abdallah yyi ya baiwa tarin maqiyansa na ruguza masarautar burham ne batare daya fahimci hkn ba,prince nasaar ya samu yarda da amincewar sarki abdallah sosai, prince akbar yasa bimbii cikin qalbinsa, zuciya da gangar jikinsa bimbii suke buqata, yau tsawon watanni hudu kenan yana rufe amma bimbii bata ta6a 6acewa cikin tunaninsa ba,yau da dare yana zaune ya kalmashe kafafunsa ya jingina da jikin qarfen kurkun, idanunsa a lumshe suke yana tuna duk wani kyakykyawan memory nasa da bimbii,muryar mahaifiyarsa yaji tana masa mgn tace" ina son kayi yadda mahaifinka keso ka mance da wannan baiwar, cikin jikinta ba nk bane daman ai, ka

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment