Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji bayin kitchen din na qus qus ita dai bata tasu take ba ta, honey tea ta masa ta sanya ginger kadan ta dora a faranti na alfarma ta nufi 6angaren nasa, tana shiga ta tarar dashi yana rubutu batasan rubutun me yake ba dai ta ajiye masa honey tea din a gabansa, ajiye abun rubutun yyi ya dago da idanunsa yana kallonta saurin dauke kai tayi tare da rissinar da fuskarta sannan ta soma tsiyaya masa honey tea din a qaramin cup ta dago da fuskarta tana miqa masa cup din, abunda ya bata mamaki shine ba cup din da take miqa masa yake kallo ba ita yake kallo kuma wani irin kallo yake mata wanda ta kasa tantance ma'anarsa don bata saba ganin irin kallon cikin kwayar idanun jama'a ba, riqe cup din tayi ta sunkuyar dakanta qasa, hannunsa yasa ya amshi cup din ya soma sipping a hnkli tare da lumshe idanunsa, ajiye cp din yyi ya tashi ya tafi gaban manya manyan windows dake rufe da wasu kofofin glass ya tsaya tare da kalmashe hannayensa ta baya ya qurawa glasses din windown idanu, bimbii kallonsa tayi kawai ta fahimci kamar akwai abunda ke damunsa, cikin qarfin hali ya taho wurin dayake tsaye cikin sanyin murya tace" koh akwai abunda yarima yake buqata ne" bece mata komai ba kuma juyo ya kalleta ba, ganin hkne yasa ta koma ta dauki farantin ta fita dashi, tana fita ya juyo yana kallon kofar, komawa yyi ya zauna ya lumshe idanunsa yana fitar da wata zafaffiyar ajiyar zuciya, hk abu ya cigaba da tfy tun bimbii tana tsarguwa idan prince akbar ya qureta da idanu har ta saba da kallon nasa ta dau hkn ko shima duk yana daga cikin al'adarsu wato kallon qurilla, prince nasaar shima ya takurawa bimbii har ta soma shakkar zuwa qorama don baya gjy da zuwa wurin musamman sbd ita, bimbii yanzu wannan shegen tsoron nata ya soma raguwa ta soma zama jarumar mata, prince nasaar baya ta6a samun sakin fuska a wurin bimbii shi kuwa baya zuciya don har ga Allah son bimbii yake irin sosai din nan, sai ya shafe kusan awanni yana jiran fitowar bimbii bakin qorama wanki, israt da khulood kuwa saida bimbii ta samar musu da alfarma suka dawo 6angaren prince da bauta suka shiga jerin bayin dake aiki a kitchen, musamman bimbii tace su dawo dakinta da kwana hk suke kwana su uku kamar yadda suka saba,khulood ita ta din ga koyar da bimbii girke girke irin nasu na larabawa daban daban yanzu ta kware sosai a fagen girki, israt kuma ita take koya mata waqoqi iri daban daban, suna taimaka mata sosai, yau suka tashi cikin tsantsar rudani sbd samun labari da sukayi za'a jefe yan matan bayin da sukayi ciki, hanyar 6angaren prince bimbii tayi da gudu bayin dake tsaron kofar suka qi bude mata kofa suka sanar da ita prince baya buqatar ganin kowa, shi kuwa yana tare ne da hadiminsa ubaid suna tattaunawar sirri, bimbii kuwa hk ta din ga jira amma shiru babu alamun zasu bude mata kofar, juyawa tayi ta koma ta nufi bakin qorama, bata jima da zuwa wurin ba prince nasaar ya bayyana shima, tana ganinsa ta miqe kamar zataci tuntu6e ta nufi wurinsa shima abun ya bashi mamaki ya bita da kallo, kallonsa tayi ta sunkuya bisa guiwowinta a gabansa tace" don Allah ka taimakamin ka cetomin yar uwa tana cikin yan matan da za'a jefe yau" shiru yyi sai kuma ya kalleta da murmushi yace" wannan alfarma tana da wahalar gaske sbd sarki abdallah dakansa ne yasa hannu a jefesu babu wanda ya isa ya dakatar da hk duk cikin masarautan nan amma...." sai kuma yyi shiru tace" amma me?" yace" zan iya sanyawa a saceta akaita masarautarmu saidai wannan tamkar qunar bakin wake ne da tarar aradu da fadin kai don idan har aka samu mtsl toh gsky nikaina ina cikin mtsl amma karki damu zan iya yin komai sbd ke sbd na yarda da ingancin soyayyar da nk miki" kallonsa tayi da mugun mamaki ta nuna kanta tace" so kuma?" daga mata kai yyi alamar ehh, tace"don Allah ka dena fadar hk bani so" yace" baki sona kenan" tace" Aa, amma tsakanimu akwai bambanci mai karfi wanda yyi mn iyaka kayi hkr" murmushi yyi yace"bana mgn biyu kuma duk abunda nakeso babu makawa sai na same shi komai wuya ki fahimci hkn" bimbii sake baki tayi tana kallonshi tana waiwaye kar wani ya ganta tare da dan sarkin, takawa yyi ya wuce ya haye dokinsa yabarta a wurin,ranar ta makara sosai na zuwa 6angaren prince shi kuwa yana kallon kofa yaga shigowarta amma shiru sai yanzu taxo ta tarar ya bada umarni kar bayin dake tsaron kofarsa su barta ta shigo,qememe suka hanata shiga hk ta juya ta koma dakinsu ta tarar dasu israt sunyi jugum jugum ita ta zauna gefensu tayi shiru, tmbyrta israt tayi koda wani kyakykyawan labari, shiru tayi sannan ta zayyana musu yadda sukayi da prince nasaar, shiru sukayi don tabbas sun san wannan matakin yana da girma, kallon bimbii khulood tayi tace"kuma shi da kansa ya sanar dake ze miki wannan alfarma, gsky yaudararki yake don kuwa wannan abu mataki ne mai tsauri mai cike da kasada" duk abunda suke zantawa lenah na la6e tana jinsu, cikin sauri ta nufi 6angaren prince akbar jikinta har rawa yake, bata samu ganin prince ba sai ubaid ta samu ta zayyane masa abunda taji su bimbii na zantawa,batare da wani 6ata lkci ba ubaid ya shiga 6angaren prince ya tarar dashi a zaune, sunkuyawa yyi daidai kunnensa ya rada masa abunda lenah ta sanar dashi, shiru yyi sannan ya miqe dakansa ranar ya nufi 6angaren prince nasaar, cike da mamaki prince nasaar ya kalli babban prince don yasn ba qaramar mgn bace ta kawo shida kansa har 6angarensa, baiwarsa ce ta kawo musu green tea duk suka zauna a wasu kujeru suna fuskantar juna, prince akbar ya kalli prince nasaar yace" ina son ka janye kudirinka da kk dashi na shirin sace daya daga cikin bayin da aka zartas musu da hukuncin jefawa don ba zaka samu nasara ba kuma yin hkn tamkar hada masarautu biyu fada ne" cike da mamaki prince nasaar ya dago dakai yana kallon prince akbar, mamaki yake a ina yaji wannan sirrin dayasan duk duniya bimbii ce kawai ta sani toh ko ita ta sanar da babban prince wannan zancen, murmushi prince akbar yyi masa yace"ina baka shawara kar ka sake kayi wannan kuskuren don ba riba cikinsa kuma zaka sanya rayuka dayawa cikin qunci" har prince akbar ya gama jawabinsa be furta komai sai daga qarshe kawai yyi murmushin yaqe yace" zan so naji a ina prince yaji wannan labari na qanxon kurege duk da nasan cewa kai mutum mai taka tsantsan" murmushi prince akbar yyi tare da miqewa yace" ni zan wuce fata dai kayi aiki da hange don qaramar mgn kan iya zama babba" hk prince akbar yabar prince nasaar cike da tunani, washegari bimbii ta shiga kitchen ta shirya abun sha ta nufi 6angaren prince tana zuwa kofa ta bude mata ta shige, yana ganinta yyi saurin dauke kansa ya cigaba da abunda yake batare daya ba shigowar nata wani muhimmaci ba......





Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screesht na payment naki ta whatsapp da wannan layi..07041195806....idan kuma da buqatar kira ga layin kira nan..08080611486



Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



14


*You break my heart*.......


Ita kanta jikinta yyi sanyi yanayin yadda taga yyi mata, qarasa tayi ta ajiye farantin dake hannunta tare da rissinar dakanta qasa, saida ya gama duk abunda yake sannan ya dago idanunsa yana kallonta ba zato taji muryarsa yace" jiya ina kkje" shiru tayi sai kuma tace" na tafi wanki qorama" tsayar da kwayar idonsa yyi akan fuskarta yace" sai kuma kk tsaya a ina" tsoro ne ya soma shigarta muryarta har rawa take tace" ba....bu...k..o.ina" tayi mgnr ne a daburce kuma cikin qinqina, murmushi yyi yana qare mata kallo ita kuma kanta na qasa, miqewa yyi ya nufi wurin windows din daya soma tsayawa hannayensa dukka yyi folding nasa a baya, batare daya juyo ba yace"me ya hadaki da prince nasaar" innalillahi wa'inna ilaihir rajuna.....abunda ta furta kenan kuma a bayyane sbd razana da tayi ta marairaice fuska kamar zatayi kuka gashi dai ba damar musawa sai ta sunkuya bisa guiwowinta tare da rissinar dakanta qasa alamar dake nuni data amsa laifinta, juyawa yyi ya koma ya zauna ta taso da sauri ta soma tsiyaya masa herbal tea din data hada masa, yace" kar ki sake sanya kanki cikin abunda be shafe ki ba" rissinar dakanta tayi tare da miqa masa cup na tea din sannan ta koma bayansa ta tsaya ta sanya hannunta a kafadarsa ta soma daddana masa jiki tana masa tausa, murmushi yyi sbd yasan abunda yasa tayi hkn sbd tasan tayi laifi ne, bece mata uffan ba ya cigaba da sipping tea nasa, daga mata hannu yyi alamar ya isa hk ta tafi, sum sum ta wuce ya bita da kallon wutsiyar ido, komawa tayi dakinta ta zauna tayi shiru gashi su khulood basu nan, tunanin abunda prince ya fada mata yanzu, gani tayi kamar yana da masaniya game da plan dinsu da prince nasaar shiyasa yake mata mgn cikin shagu6e, dafe kanta tayi kawai cike da tsantsar fargaba, shigowar wata baiwa ce ta sanyata dago da kanta, kallon bimbii baiwar tayi tace" prince nasaar yana da buqatar ganinki, kallon baiwar baiwar tayi sosai sannan ta miqe tabi bayanta, tfy sukayi mai tazara sannan suka shiga 6angaren prince nasaar, lambunsa ta wuce da bimbii sannan ta juya ta koma bakin aikinta, bimbii koh ta qarasa ciki, ganinsa tayi zauna akan wani farin dutse fuskarsa babu yabo ba fallasa, rissinar dakanta tayi alamar girmamawa ga prince din,yace" kece kk fadawa prince akbar plan din dana shirya na sace wannan baiwar" shiru bimbii tayi cike da mamaki sai kuma tace" Aa,bani bace" yace" amma kin sanar da wani koh" tace" ehh,munyi mgnr da yan'uwana amma tabbas nasan sukam basu sanar da kowa" yace"meyesa kk fadawa wani bayan na fada miki wannan mataki yana da tsauri kuma rashin nasara babban barazana ne" tace" an samu mtsl koh" shiru yyi yana nazarinta sai kuma yace" prince akbar yazo ya same ni akan wannan mgn kuma yace na dakata idan kuma ba hk ba za'a samu matsl" shiru bimbii tayi kamar zatayi kuka tace" babu komai" yace" zaki iya tfy" a hnkli kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta juya ta soma tfy har ta fice daga lambun ta nufi sashinsu, tana shiga ta tarar su israt sun dawo, zama kusa dasu tace" bansan ya zamuyi ba an samu mtsl" dukkaninsu suka dago kai a razane don sunyi tunanin koh wurin aiwatar da plan din ne aka samu mtsl, bimbii ta kallesu sosai ta sanar dasu abunda ya faru, duk aukayi shiru suna tunanin waye kuwa ya sanar da prince wannan mgn, bimbii tace" ba abun mamaki bane don prince ya samu labari don yana da tsatstsauran tsaro da kuma tsananin taka tsantsan" israt tace" amma duk da hk alamu sun nuna akwai wadanda suke mn la6e" bimbii tayi shiru tana nazari kan mgnr israt, tace" toh yanzu meye mafita" duk sukayi shiru, suna cikin mgn sukaji sanarwa kowa ya fito wurin jifan bayi, dukka suka miqe a zabure suka fita, wani shararren fili ne me dauke da rairayi sosai nan aka fito da yan matan su ashirin da biyu wasu daga cikinsu sun haife cikin dake jikinsu wasu kuma basu haife ba, sai lkcin bimbii ta ta6a tozali da sarkin abdallah bin jabal dake zaune a wata kujera ta alfarma a can saman wata matattakala cikin wani tanti, farin balarabe ne tas yana da yalwar dogon farin gemu ga hancinsa dogo dodar amma ya manyanta sosai hannunsa riqe da sandar sarauta, sanye yake cikin wata alkyabba dark brown da jan rawani mai adon fari da ja, gefen hannunsa na dama prince akbar ne sanye yake shima cikin farar jallabiya da rawaninsa baqi da fari dayan 6angaren hagunsa kuma ragowar ya'yan sarakuna ne sai ministocinsa da y'an majalissar zartarwa, bayi kuma na tsaye cirko cirko daga qasa suna jiran ganin abunda za'a aiwatar kan wadannan yan matan, wasu manya manyan bayi majiya qarfi suka kukkunce yan mata suka soma haurawa dasu saman wani gini suka kuma daddaure a jikin wani qarfe, bimbii idanunta ne ya saukan akan lailah wacce hawaye ya gama 6atawa fuska tana daure ita jikin qarfen, fashewa bimbiii tayi da kuka suma su khulood duk kukan suke, sai yanzu bimbii ta tabbatar da zalinci a wannan masarauta tayi Allah tirrr da wannan al'ada tasu, prince akbar ne ya miqe dakansa ya nufi inda aka daure yan matan ya kallesu daya bayan daya sannan ya bada dama a soma jifansu, murmushi sarki abdallah bin jabal yyi lkcin da aka soma aikawa yan mata da saqonnin duwatsu, jifansu ake ta ko'ina, bimbii rufe idonta tayi qam tare da qanqame jikinta tamkar ita ake jifa, bayan an gama jefesu ne aka sakko da gawarwakinsu qasa abun gwanin tausayi, batare da bata lkci ba sarkin abdallah bin jabal ya tashi yyi jawabin gargadi ga duk wanda ya kuma aikata wannan abu sannan suka soma sakkowa daga matattakalan sai darewa ake ana basu hanya suka wuce zuwa fada, bimbii kafafunta kasa daukarta tayi ta zube bisa rairayin tana kukan zucci don tayi na filin har ta qoshi, rashin amfaninta kawai take gani tunda gashi ta kasa ceto rayuwar lailah, dakyar su khulood suka jata suka koma 6angarensu, bimbii tunda ta shiga dakin bata fito ba har dare sai da daren ta fito takaiwa prince dinner, tunda ta shiga ta ganshi zaune yana ta rubuce rubucensa ta ajiye masa dinner din wata kusurwa mai yalwar shimfidadden centre carpet da ado, kunsan mafi yawan larabawa sun fi son cin abinci a zaune bisa shimfida,tunda ta shigo ya lura sam babu annuri a fuskarta tayi mugun tsare gd, be kuma kallonta ba ya cigaba da gudanar da abunda yake, bayan ya gama ne tayi abunda ya kamata na al'adar wankansa ya fito cikin shigar bacci sannan ta tsaya har yaci abinci sannan ya bata umarnin tfy, tana komawa 6angaren nasu taga su khulood na jiranta don ta sanar dasu cikin dare zasu ruwan da aka watsa gawarwakin su lailah su mata kallon qarshe,dare nayi sosai suka saci jiki suka nufi wannan ruwa dayake nesa sosai daga wannan gd na sarauta amma duk cikin masarautan ne, gawarwakin na nan basu gama wucewa ba, tattare rigunansu sukayi suka soma shiga cikin ruwan suna lali6e ko Allah ze basu sa'ar gano gawar layla, khulood ce ta soma ganin gawar ta kirasu suka zo wurin da sauri, bimbii ta ta6a gawar, dago fuskarta tayi da sauri tace" kamar tana da sauran numfashi" israt ta dora kanta taji kamar alamun zuciyarta na buga a hnkli, kallonsu tayi tace" tabbas akwai alamun numfashi tattare da ita yanzu meye abunyi, shiru sukayi suna tunanin ina ya dace su dosa da gawar laylan tunda sunji kamar tana numfashi,jan gawar suka somayi suka kaita bakin wata bishiya, dukkaninsu sunayi suna 2kalle gudun kar wani ya gansu,bimbii tace" tana buqatar taimakonmu ina ya dace mu kaita inda ba za'a kamamu ba" suna kan shawara sukaji sawun dawakai sun nufo wurin da suke,take gabansu ya fara dokawa tara tara.......






Littafin na kudi ne gamai buqata za'a tura #300 kacal ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, sai a tura screesht ta whatsapp ta wannan layin...07041195806.......




Alkalamin Bintuu ne...
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



15


*I never care about the difference betwee us*....my only concern is you to accept me as your companion💕



Wasu ne daga cikin dakarun dake tsaron gdn sarautar, suna kewayawa ne ta ko'ina cikin wannan masarauta don tabbatar da tsaro, tun kan su qaraso wurin da suke, khulood ta kallesu tace" muna cikin rikici fa idan suka ganmu"neman wurin 6uya suka somayi amma duk wurin babu wurin da zasu iya 6uya,israt ta kallesu a rikice tace" mu haye bishiya kawai" aikuwa kafin ta rufe baki sai ganinsu tayi sun rigata hayewa bishiyar dayake bishiyar tana da yalwar ganye kuma ga duhu, hkn yyi daidai da qarasowar dakarun wurin, ganin gawar layla da sukayi ne a gindin wannan bishiya yasa duk suka ja limzamin dawakansu suka tsaya, babban cikinsu ne ya fara sakkowa daga saman dokinsa sannan sauran ma duk suka sakko, duba gawar sukayi cike da mamaki don tabbas sun gane gawar na daga cikin gawarwakin yan matan da aka jefe yau, abunda ya basu mamaki shine wanda ya jawo gawar daga cikin kogi ya kawota wurin bishiyar nan, 2waige suka soma ko zasu gano wata alama dake nuna da wani a yankin wurin amma basu ga komai ba kuma basu ji motsin komai ba, babban cikin nasu ne ya gano alamar sawun kafar su bimbii dayake wurin rairayi ne, bin sawun ya somayi har ya gano daidai wurin da sawun kafar tasu ya tsaya, su bimbii kuwa dake maqale akan bishiya tuni cikinsu ya duri ruwa,israt kan rufe idanunta tayi kawai tana addu'ar Allah ya fisshesu ya rufa musu asiri kar su gano su,babban cikin nasu ya kalli sauran yace" su duba kan bishiya" israt tana jin hk ta saki fitsari a wando, bimbii da khulood kuwa sun sadaqar kawai mutuwarsu tazo,duk sunyi 2tsuro a maqale akan bishiya suka ga dakarun nan sun soma qoqarin hawowa bishiyar, daidai lkcin wani mahayin doki ya bayyana, takun sawun dokin nasa ne ya janye hnklinsu daga hawa bishiya duk suka juya suna kallonsa sanye yake da baqin kyalle ya rufe rabin fuskarsa, wucesu yyi da gudu bisa dokin nasa,hkn da suka gani ne ya janye hnklinsu suka haye dawakansu suka rufa masa baya,hknne yaba su bimbii damar sakkowa daga kan bishiya duk da hk zuciyarsu tana tsananta bugawa, sake ta6a gawar layla sukayi suka ji 2kwata ta dena numfashi alamar rai yyi halinsa, dukkaninsu kuka suke suna tfy suna waiwayen gawar layla babu halin su mata suttura hk suka bar wurin cike da taka tsantsan kar a gane takun sawunsu har Allah ya basu sa'ar komawa 6angarensu, suna shiga daki suka rufe da sakata suka hau gadonsu da gudu suka ja bargo suka rufa dashi zuciyarsu na cigaba da bugawa 2tara don gani suke kamar basu tsira ba, aikuwa basu jima ba sukaji ana buga musu kofa kamar za'a 6alla, bimbii ta rada musu kar ku sake koma waye ku bari a gane alamun tsoro ko rashin gsky a fuskokinku ku aro jarumta idan har kuna son tsira,raggo baya zama gwani damu mutu ragwaye gwara mun mutu jarumai, wadannan kalmomi su suka sanya wata sabuwar jarumta ta shigesu tashi guda, bude kofar sukayi fuskarsu da alamun nuna bacci, masu tsaron farfajiyar gdn ne suke bi daki daki na bayi don tabbatar da kowa yana cikin dakinsa a kwance, suna ganinsu suka wuce zuwa daki na gaba hk suka din ga zagaye cikin wannan dare, su bimbii kuwa rufe kofarsu suka sakeyi suna sauke ajiyar zuciya don da bayin sun zo kafin su dawo suka ga basu nan toh asirinsu ya gama tonuwa kenan sbd sai sun bincika su ga inda sukaje da wannan dare, komawa sukayi suka kwanta amma cikinsu babu wanda ya iya rintsawa don zuciyar har yanzu tana cike da fargabar abunda ze faru gobe,6angaren dakarun da suka bi bayan wannan mahayin dokin kuwa basu samu damar qarasawa wurinsa ba ma bare su iya kintata siffarsa sbd kwarewarsa wurin iya gudu da doki tashi daya ya 6ace musu suka rasa inda yyi babu irin duban da basu masa ba, dole suka koma wurin bishiyar nan suka ga ba gawar da suka bari a gindin bishiya, hkn ya basu mugun mamaki, kogin da aka watsa gawarwakin nan suka nufa suka tarar ruwa yyi gaba da kusan dukkan gawarwakin yan matan sai kadan kuma cikin kadan din da sukayi saura babu mai kama ma da wannan gawa da suka gani a bakin bishiya, so suke su gano asalin gawar sbd su bincika makusantan ta amma basu ga gawar ba, hk suka juya suka bar wurin amma sun sanar da dukkanin sauran dakaru masu tsaron masarautar su sanya idanu sosai kan kowanne lungu da saqo na masarautar, washegari su bimbii suka tashi suka shirya kowacce ta nufi wurin aikinta, sun 6oye duk wani tsoro nasu, bimbii sanye take cikin wata farar doguwar riga mai ado da kyalkyali, gashin kanta kuwa yasha gyara na musamman, kunnuwanta sanye da wasu manyan yan kunne masu kyau,hannunta kuma da wasu awarwaro, kitchen ta shiga ta hada abinci kala, bayin dake aiki a kitchen sai kallonta suke a yatsine, bimbii tana aiki ne cike da tsantsar takan tsan tsan, bata matsawa konan da can saita gama shirya komai sbd tsaro da kuma gudun kaidi da makirci na gdn sarauta, wani qaton basket ta dauka mai kyau ta soma sanya mazuban dake dauke da abincin a ciki ta dauka ta nufi 6angaren prince dashi, tana zuwa kofa ta bude ta danna kai ciki, yana zaune a wata royal chair yana rubuta wata wasiqa yana gama rubutun wasiqar ya dauki hatimin gdn sarautar burham ya danna a jikin wasiqar sannan ya rufe takardar ya sanyata cikin wani qaramin akwati, dago da kyakyawan idanunsa yyi yana qare mata kallo, ita kuwa tayi saurin yin qasa da kanta alamar girmamawa gareshi sannan ta wuce inda yake cin abinci ta soma jera masa abincin data shigo dashi shi kuwa rakata yyi da kallo kawai, bayam ta gama ne ta dawo wurin dayake tace"komai ya kammala" bece mata uffan ba ya tashi daga inda yake ya nufi wurin shimfidar alfarmar da abincin ke jera ya zauna, wurin itama taje ta soma zuzzuba masa abinci a qananan plate yana bin kowanne yana ci 2kadan, bayan ta gama bashi abinci ya koma ya kwanta akan gadonsa yace"tazo ta masa tausa" kwanciya yyi ruf da ciki ita kuma tana tausa masa baya, cikinsu babu mai mgn sai qarar awarwaron hannunta, muryarshi taji yace" ina sake ja miki kunne da ki guji sanya kanki a fitina idan kuma ba hk ba wataran zakiyi nadama mara amfani" saurin kallon fuskarsa tayi taga idanunsa a rufe suke yake wannan mgn, cike da jarumta ta 6oye tsoronta tace" zan cigaba da kiyayewa ranka ya dade" shiru yyi be kuma cewa komai ba ita kuma zuciyarta cike take da tunanin wannan mgnr ta prince, shi baya furta mgn kai tsaye saidai yyi shagu6e yabarka cikin tunani, tayi nisa cikin tunanin mgnrsa har ta dakata da tausan da take masa batare data ankara ba, shi kuwa yana ji ta dakata da tausan da take masa yasan tunanin abunda ya fada mata yanzu take, hannunsa yasa ta baya ya riqo hannayenta ya murzasu da karfi,saurin kallonsa tayi taga idanunsa a lumshe suke kuma yaqi sakin hannun nata, qoqarin janye hannun nata take a hnkli cikin dabara da hikima ya bude idanunsa ya saukesu akan fuskarta, yanayin yadda taga idanun nasa yasa tasha jinin jikinta tayi saurin sunkuyar dakanta qasa,ya jima yana mata wannan kallon qurullan da har yanzu ita ta kasa gane ma'anar kallon sai ta dauki hkn a matsayin al'adar prince akbar,yace" ki shirya zaki rakani wani wuri" rissinar dakanta tayi alamar amsa umarnin nasa,sakin hannunta yyi ya mata alama data tafi, sauka tayi daga kan tafkeken gadon nasa ta sake masa shara shara curtain din dake kame ta koma can wani gefe ta durqusa kan guiwowinta tana jiran fitowarsa, ya jima a kwance kuma ba bacci yake ba idanunsa biyu,babban hadiminsa ubaid ne ya shigo ta sanar dashi bazai samu ganin prince yanzu ba

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment