Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita da sauri ba jimawa sai gata sun shigo da wata tsohuwar balarabiyya, tana tafe tana dogara sandarta, doguwar riga ce ruwa k'wai a jikinta ta yane kanta da mayafi amma hkn be hana gashin kanta dayake fari fat da furfura leqowa ba,wuyanta da wata katuwar sarqa,kunnuwanta kuma da wasu manya yan kunne sai yatsun hannunta kusan dukka da manya zobuna na azurfa, fuskarta a tamke ba alamun fara'a tana shigowa sauran y'an matan bayin nan suka rissinar da dakansu qasa alamar girmamawa ga uwar bayi ummul shukri, bimbii kuwa kallon tsohuwar kawai take,itako uwar bayi ummul shukri sandarta ta sanya ta d'ago da ha6ar bimbii tana qarewa fuskarta kallo musamman cikin idanunta don mafi yawan larabawa suna karantar sirri zucciyar mutum ne ta cikin k'wayar idaniyansa shiyasa uwar bayi ummul shukri ta qure bimbii da idanu tana karantar sirrin zucciyarta ta k'wayar idanunta, bimbii kuwa sai tayi sauri yin qasa da idanunta kamar yadda taga sauran yan matan bayin sun mata, tana ganin bimbii ta rissinar da idanunta qasa sai tayi wani d'an murmushi na gefen baki ta d'auke sandarta daga ha6arta ta kalli khulood tace" ki bata abinci" tana fadar hk ta dogara sandarta ta fice daga dakin bayin,khulood ta tashi da sauri ta fita don kawowa bimbii abinci itama israt ta tashi ta kawo mata ruwan sha cikin wani kofin tasa daidai lkcin khulood itama ta shigo da wani qaramin kwanon tasa da abinci a ciki,duk suka sanya mata a gaba, bimbii kuwa daman da yunwa ta tashi don hk batare da wani kunya ba ta wanke hannunta da ruwan da suka kawo mata, ta soma cin abincin duk da a ido ta raina yawan abinci suna kallonta ta gama cin abinci tasha ruwa tayi hamdala,khulood ta kalleta da murmushi tace ta tashi su fita ummul shukri na son ganinsu, ba musu ta miqe tabi bayansu suka dinga wuce kusurwowi har suka shiga kusurwar da ummul shukri take, zaune take bisa kujera tana riqe da sandarta suka durqusar da guiwowinsu dukka a gabanta tare da rissinar da kawunansu qasa suna jiran umarninta, itama yadda taga sunyi hk tayi, ummul shukri ta kalle bimbii ta soma mata mgn cikin harshen larabci tace" kin san inda kk yanzu?" girgixa kai bimbii tayi alamar aa, tace" kina gdn sarautar burham,kina cikin jerin maqasqatan bayin masarautar burham"nuna mata su khulood tayi da hannu tace"rukunin aiki iri d'aya zasu nuna miki naki aiki ciki" rissinar dakanta tayi alamar ta amsa yadda dai taga sunayi, sallamarsu tayi suka miqe suka fice, bimbii sai bin wannan gdn sarauta take da kallo don tsarin ginin masarautar ya birgeta sosai, gani tayi bayin gdn sai kai kawo suke,matan kusan dukkaninsu da mayafi a saman kansu,mazan kuma yawancinsu da rawani a kansu,ko'ina na gdn zagaye yake da furanni masu kwantar da zucciya, gdn kusurwa kusurwa ne, kowacce kusurwa an mata yanayi kamar kofar masallaci sanda sanda, israt da khulood na gaba, laila da bimbii na biye dasu,fita sukayi daga wannan 6angaren suka wuce wani wuri suka dauki kwanduna, lailah ta dauki kwando daya ta bawa bimbii ta amsa ta riqe suka sake ficewa daga wannan 6angaren sai tfy suke har suka fara fita daga inda gine gine suke suka soma shiga jeji jeji kuma fa duk a cikin gdn suke, bimbii dai sai binsu take, wani lambu mai cike da bishiyoyi na kayan marmari suka shiga, khulood ta hau bishiyar zaitun, israt tahau bishiyar tuffa suna tsinkowa suna jefo musu su kuma suna tattarawa suna zubawa a kwandunansu, saida suka cika kowanne kwando sannan su khulood da israt suka sakko kowacce ta dauki kwandonta ta dora a saman kanta suka fice daga lambun suka nufi cikin gd, suna cikin tfy wasu samari suma bayi ne suka tare musu hanya,abunda ya baiwa bimbii mamaki shine ashe kowacce cikinsu tana tafe da qaramar wuqarta a cikin jikinta sai gani tayi duk sun sauke kwandunansu sun sanya hannu cikin fatarinsu sun fito da qananan wuqaqensu sun tsatstsaya suna sauraron su ga me zasuyi musu su soma yankarsu, bimbii kuwa ta qame a tsaye da kwandonta a saman kanta cike da mamaki, su kuwa suna ganin yan matan sun fito da wuqa sai suka wuce abinsu saida suka ga sunyi nisa suka maida wuqaqensu cikin jikinsu suka sunkuya suka dau kwandunansu suka cigaba da tfy,su mazan larabawan wannan yankin Allah ya zuba musu son jikin mace ba wuya suke yiwa yan mata fyade shiyasa yan matansu ke yawo da wuqa sbd tsaro, bimbii dai tana ganin abun mamaki cikin wannan gd sbd ita daman tunda ta shigo qasar kuwait tana qunshe ne a wuri daya batasan al'adunsu ba sai yanzu da Allah ya jefota gdn sarautar burham, wani qaton kitchen suka shiga, kitchen bayi ne ciki keta hidima, shugabar bayin dake wannan babban kitchen din mai suna jahan ita ta amshi kwandunan nasu ta jujjuye kayan marmarin a cikin wasu manyan kwanduna dake kitchen din ta basu kwandunansu, duk bayin dake hidima cikin kitchen din sai bin bimbii suke da kallo tamkar sun ga wata sabuwar halitta,lallah ce taja hannun bimbii suka fice daga kitchen din,maida kwandunan sukayi suka koma wani 6angaren suka fito da wasu manyan barguna suka nufi wata qatuwar qorama dake dake tsakiyar gdn suka dauko wasu manyan abubuwan wanki da akayisu da katako suka soma dirzar wankin wannan manyar barguna sai yamma liqis suka kammala ayyukansu suka koma 6angarensu,su hud'u ne a dakin nasu,khulood,lailah, israt sai yanzu da aka kawo musu bimbii, dukkaninsu akan wannan busassun ciyayin suke kwana tamkar shine suka maida katifarsu saidai su shimfida mayafansu akan ciyayin su kwanta, ita bimbii ranar kam bacci tayi mai dadi don kuwa gani take ta samu cigaba tunda har ta samu damar kwanciya cikin daki ba'a rumfa ba kuma har ta samu albarkar kwanciya a ciyawa ba'a dandamalin k'asa ba wannan kadai cigaba ne a wurinta bata damu da tiqar aikin da suke ba don daman tasan ta ita baiwa ce kuma tana cikin qangin bauta,kwanan farin ciki tayi ga qawaye ta samu da basu nuna mata zangwama ko kadan sun dau kansu tamkar yan'uwa hk suke rayuwarsu tamkar jini daya kuma kusan dukkaninsu sun fito ne daga qasashe mabambanta saidai su duk daga qasashen larabawa suke masu makwabtaka da qasar kuwait ita kadai ce baqar fata daga africa, washegari da sanyin safiya duk suka tashi, tunkan su fita ummul shukri ta shigo ta kama tsintsiyar qafar bimbii ta sanya mata wata qaramar sarka irin wacce wasu matan ke sanyawa a qafa sbd ado su kuma wannan sarqar qafan itace alamar dake nuni da rukunin bayin da suke shiyasa taga suma su khulood kowacce da wannan sarqar a qafarta ita da ta dauka sbd ado suka sanya ashe shine tambarin rukunin bayin da suke,kallon qafar tayi taga sarqar ta mata kyau, miqewa tayi suka fice, ranar kwaryoyi suka dauka suka tafi tatsar nonon raqumi,kowacce saida ta cika kwaryarta da nonon sannan suka dauko suka taho kai tsaye wannan babban kitchen suka kai nonon aka juye a charkoki, daga nan suka wuce kowacce ta dauki tulunta suka tafi babbar qorama don debo ruwa, saida suka ciccika duk wasu abubuwan tara ruwa na 6angarori 2daban sai yamma liqis ranar ma suka koma 6angarensu, bayan sun gama cin abinci suna shirin kwanciya lailah ta fito da wata sabuwar wuqa yar qarama ta miqawa bimbii tace" ki riqe wannan kema sbd akwai hadari ki din ga yawo babu abun kare kai kin ga kema budurwa ce saiki sanya budurcinki cikin hadari" amsar wuqar bimbii tayi mata gdy sannan ta sanya wuqar qasan wurin kwananta......



***

6angaren maheer kuwa tunda bimbii ta gudu ya rasa kansa,shi kansa ya rasa abunda ke damunsa tun yana qoqarin 6oye damuwarsa har mutane suka soma fahimta, yau tun safe yana tsaye a barandar dake gaban building dinsa ya qurawa gindin bishiyar guiban da bimbii ke zama lkcin tana gdn,gani yake tamkar ze ganta zaune, har yayansa zayeed ya shigo gdn be sani yyi nisa cikin tunani saida ya dafashi tukun ya ankara da shigowarshi, zayeed kallo daya yyi masa yasan akwai abunda ke damunsa,ya lura da maheer tun sa'adda baiwarsa ta 6ace ya shiga damuwa ya kasa dawowa daidai har yanzu, dafa kafadarsa yyi ya soma masa mgn cikin taushin murya yace" maheer are you in love with that african lady" saurin dago dakai maheer yyi yana kallon yayan nasa da mamaki a shimfide a fuskarsa yace" what are you saying?" murmushi zayeed yyi yace" if not,why are worrying about her disappeared" kallonsa maheer yyi yace" cox she my slave" dariya zayeed yyi sai kuma yace" ok, i will bring another slave for you" haushi mgnr ta bashi ya tashi daga wurin ya shige cikin building nasa ransa a 6ace, zayeed kuwa bai bishi don yasanshi da shegiyar zuciyar tsiya ya cigaba da wasa da kare,maheer kuwa yana shiga ya kwanta a couch din dake parlourn nasa ya rufe idanunsa yana hango lkcin da bimbii ta 6acewa ganinsa bai ta6a zaton be zata dawo ba don shi la'akari yake ai bata da inda zataje dole ma ta dawo wurinsa saida yaga yau kusan kwana uku kenan ba bimbii ba alamun dawowarta, zuciyarsa tana tsananta bugawa idan yana tunani bimbii,gashi shi ko sunanta ma be sani ba, idan ya tashi baida aiki sai tunanin bimbii,tunda bimbii ta gudu bacci yake gagarar idanunsa,yauma dare yyi sosai ya fito ya tafi cikin rumfar gezevon da bimbii ke kwana ciki ya zauna ciki ya qurawa sama idanu yana kallon hasken farin wata tare da taurarin dake sararin samaniyya,a hnkli ya furta 'I lost my star,pls my black african lady come back to me" sai ga maheer uban marasa mutunci yana kuka da hawayensa,be ta6a sanin ashe son bimbii ya illata masa zuciya ba saida ta gudu tabarshi, dora kansa yyi akan cinyoyinsa yana kuka har sauti, ruwa aka soma kamar da bakin k'warya amma maheer na cikin wannan rumfar yana kuka da hawayensa, ji yake ya tsani friends din nan nasa da suka zama silar gudun bimbii shi kansa ji yake ya tsani kansa idan ya tuno rashin mutuncin daya din ga shukawa bimbii,sai yanzu ya fahimci lalle kowanne mutum yana da baiwa, wani baiwarsa a 6oye take Allah kadai shi yasan irin baiwar daya axirta kowanne bawa nashi dashi, duk irin yanayin da muka ga mutum karmu rainashi wataqila warakarmu tana tattare dashi,maheer ranar a rumfar ya kwana yadda ruwa ke jiqa bimbii hk ruwan saman ya jiqash amma shi duk ba wannan ne damuwarshi,zaman wurin kadai ya sanya masa nutsuwa don gani yake kamar zega bimbii, washegari ya nufi wurin dayake sanya mata abinci yyi zaman dirshan gaban plate din yana cin abinci daya zuba mata don dukda yasan bata nan amma kullum ranar duniya baya fashin zuba abinci a wannan plate gani yake kamar ze dawo yaga anci abincin, cikin mako guda maheer ya gama zaucewa da soyayyar bimbii,wata irin zafaffiyar soyayya yake yiwa bimbii wacce ke wahalar da ruhi da gangar jikinsa, soyayyar dake sanyashi kuka duk dare duniya,hmm, alhaki ai kamar dan kwuikuyo yake, bibiya yake.....





Masha'Allah, anan na kawo qarshen free pages na wannan littafi duk mai buqatar cigaban wannan qasaitaccen labari sai ya biya naira #300 kacal ta wannan acct no.0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, sai turon da screenshrt ta wannan layi through whatsapp....07041195806 ga mai buqatar qarin bayani saiki nemi wannan layi....08080611486...



Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HU'DU*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



6


*One Goodbye is enough to melt a heart* he missed her like crazy...💕


Washegeri da sanyi safiya suka tashi kamar yadda suka saba saidai yau ayyukansu yana dayawa sbd yau itace ranar zagayowar haihuwar PRINCE AKBAR... Princess hindu ita ta shirya qasaitaccen birthday partyn wanda ze gudana a lambun sarauniyya mar'atussaliha, bayi da barorin wannan gd na sarauta sai kai komo suke wajen shirya inda taron ze gudana, su bimbii kuwa su aikinsu a wannan wuri shine su rissina d'iyan saraki suna bi takansu tamkar sun sami gada sbd tsa6ar izzah da daukar bawa ba a bakin koman komai ba, dukkanin wadannan ya'yan sarakuna sun hallara shima kansa prince akbar ya iso cikin wata alkyabba golden da rawaninsa ruwan k'wai sai irqa baqi daya dora a saman kansa, princess hindu ita ta iso a qarshe cikin wani keken doki yasha ado, bayinta na biye da ita, dage keken dokin sukayi ta sakko, takan bayi itama ta wuce har ta isa wurin zamanta dake kusa da prince akbar, bimbii kawai baiwa idanunta abinci take tana 2kalle don taga wata al'ada ce ta daban, princess hindu idan mgnr tsantsar kyawu ake toh tabbas zata iya cin gasar sarauniyyar kyau don bayan izzar da take taqama dashi na jinin sarauta ga kuma na kyawu da cikar asali, tasha ado na kwala kwalai,wata doguwar rigace a jikinta irinta d'iyan saraki kalar sararin samaniyya, 2ciye suka soma da 2shaye suna raha da barkwanci a tsakaninsu jinin sarauta, prince akbar yana daga zaune fuskar nan tashi dai ba yabo ba fallasa, wata baiwa na hango tsaye a bayansa amma ita sanye take da kaya masu kyau tamkar ba baiwa ba, kallon israt bimbii tayi tace" waccar ta dake bayan prince wacce ita?" tace"itace lenah babbar baiwa a 6angaren prince akbar, ita ke kula da duk wani ci da shanshi da kula da wurin kwanciyarsa kai har ma ta tayashi kwana ta raya masa dare idan yana da buqatar hkn" jinjina kai bimbii tayi tana cin tuffan dake hannunta tana qara kallon lenah, tana da kyau itama ko hassadun iza hassada ze furta hkn, bimbii ta kuma kallon israt tace" kince har da tayashi kwana idan da buqatar hkn toh kuma ai ba matarsa bace" dariya lailah tayi don tana bayansu tana jin hirar tasu tace" su al'adarsu shine d'an sarki da sarkin shi kansa idan sun ga baiwa ta musu sukam maidata ta zama kwarkwararsu amma da kyakykyawan sharad'i kar baiwar ta yadda ta fad'a soyayyarsu bare har ki nuna feeling dinki garesu sannan kuma ba haihuwa tsakaninku dasu don basu hada jini da bayi, hukuncin kisa shi yake tabbata ga duk baiwar data qetare wannan sharad'i ko kuma daurin rai da rai har qarshen rayuwarta, mafi yawan bayi suna son su kasance a wannan matsayi sbd tamkar an y'antasu ne kuma duk abunda suke so zasu samu,zakici maikyau ki saka mai kyau ki fita ki tafi duk inda kkso sbd kina da y'anci, zakiji dadin rayuwa idan kk samu kanki a wannan matsayi saidai karki sake ki karya sharadin nan" jinjina kai bimbii tayi tace" yoo idan bakai kai ba meye hadin zomo da kura ai ramin kura sai y'ayanta,bawa ai sai ya tsaya iyakar matsayinsa" murmushi israt tayi tace" kin ga ni kuma wlh kullum addu'ata Allah yasa shekara mai zuwa idan na shiga gasa na samu" harararta khulood tayi tace" waye ya fada miki rukunin bayin da muke ciki suna samun damar shiga gasar, rukunin bayi na biyu dana uku suke da damar shiga wannan gasa" bimbii tace" au kafin ma ka samu matsayin kasance baiwar prince din sai anyi gasa" sukace mata" ehh mn, sai an gwadaku kafin a fitar, duk shekara yake sauya baiwa" bimbii tace"tirqashi!" fitowar wasu jerin yan matan bayi ne ya janye hnklinsu daga hirar da suke,yan matan su sha biyu ne suka fito don nishadintar da wurin da waqoqi, sanye suke da skirt mai baza ta qasa da wata qaramar riga iyaka cibiya,rawa suka fara tare da girgixa jikinsu sannan zabiyar cikinsu ta soma rera wak'a mai dadi, wurin yyi shiru kowa na sauraron baitocin dake fita cikin wannan wak'e nata, baitoci ne da suka shafi rabuwar masoya, baitocin nata sun samu ta6a zuciyar masoya dayawa dake wannan wuri, bimbii sunkuyar dakanta tayi tana murza wani zobe dake yatsanta na tsakiya tana kuka da hawaye don ta tuna ranar da lamid'o ya bata wannan zobe da kuma rabuwarsu dashi ta qarshe itace ranar da wad'annan turawa suka kamasu lkcin sun dawo daga tallan nono suna sauri su koma gd don magriba ta kawo jiki Allah ya hadasu da wadannan turawan akan hanyarsu ta komawa rugarsu suka kamesu suka sanyasu cikin mota, kullum tunaninta shine wanne halin innanta yadikko zata shiga silar 6acewarta,wanne hali baffi da lamid'o zasu shiga silar 6acewa, tabbas tasan rayuka dayawa suna cikin wani hali dalilin 6acewarta, kuka take sosai saida su khulood suka rumgumota suna bata hkr, idanun gimbiya hindu ne ya tsaya akansu lkcin suna rumgume da bimbii suna bata hkr, nunawa babbar baiwarta su tayi da idanunta tace"wadan can bayin dake bayan bishiya me suke" kallon wurin zulham tayi tace"ranki ya jima suna rarrashin yar uwarsu ne" tace"aikin da suka zo yi wurin nan kenan, basu san murnar zagayowar babban prince muke ba shine suka ware kansu daga cikin yan'uwansu bayi suka koma gefe, toh kije ki tahomin dasu nan gabana naji me suke tattaunawa" cikin sauri zulham ta nufo wurinsu tace" gimbiya na son ganinsu gabanta" dukkaninsu gaban ya fadi suna tunanin ko laifi sukayi, itako bimbii ko d'ar bataji ba tunda dai tasan babu abunda tayi, hk ta sakosu a gaba ta kawosu gaban gimbiya hindu duk suka durqusar da guiwowinsu gabanta tare da rissinar dakansu qasa, lkcin ne idanun kowa dake wurin yazo kansu har shima prince akbar ya kallesu sau daya ya dauke kansa ya cigaba da shan ruwan inibin dake gabansa, daya bayan daya gimbiya hindu ke binsu da kallo ta tsaida idanunta kan bimbii tana qare mata kallo, tace" kece kk janye hnklinsu daga kan aikinsu koh" shiru bimbii tayi su kuwa su khulood sai suka sake rissinar dakansu suka hada baki sukace" mun tuba ranki ya dade" kallonsu tayi ta yatsine fuska tace" su tashi su bata wuri amma bimbii kuwa ta tsaya saita musu rawa da wak'a na abunda yasata kuka" kallon zulham tayi tace" ta sanar da mai gabatarwa ya gabatar da bimbii a matsayin mai rawa ta gaba" aikuwa hk akayi, duk wurin bimbii suke kallo itako gabanta sai faduwa yake, bata iya waqar larabci ko guda ba sai na harshenta na fillaci, kama hannunta zulham tayi ta fice da ita suka shiga wani wuri ta sauya mata kaya ta saka mata rigar nan iya ci6i da skirt mai baza ta qasa ta taje mata gashin kanta ya sakko mata har duwawu gashi da cikowa kuma baqin qirin dashi, bimbii kallon kanta tayi ta kalli zulham tace" hk zan fita gaban mutane kuma ni ban iya wak'a cikin harshen larabci ba" tamkar tana mgn da dutse don zulham aikinta kawai take ba sauraronta ba, tana shiryata ta kamo hannunta suka fito lkcin yan matan dake wak'e sun bar wurin bimbii ake jira, idanun kowa nakan bimbii sbd yadda kayan nan dake jikinta ya fito da asirin dirin dake tattare da ita sannan suna mamakin tsawo da cikar gashinta kasancewarta baqar fata amma ta zarta dayansu tsawon gashi da tsantsar diri irinna mata, itako bimbii tsayawa tayi a wurin ta kasa komai sai kallonta suke suna jiran suji ta fara rero baitoci, a hnkli ta soma juya qugunta tana girgixa tamkar macijiya wata irin rawa take wacce take sabuwa a wurinsu, basu ta6a ganin salon rawan ba, cikin zazzaqar muryarta me amsa amo ta soma rero baitocinta cikin harshenta na fillanci tana juya qugu cikin wani salo rawa irin nasu na d'iyan fillo,rawar ce ta dauko hnklin kowa kanta, prince akbar dago da kansa yyi yana kallonta tashi daya yaji rawar da take da kuma wak'en da take cikin harshen nata ya sanyashi nishadi sosai har wani lumshe idanu yake, hk suma sauran yaran sarakunan dake wurin musamman prince nasaar daya qurawa bimbii idanu yana kallon zubin tsarin halittarta, kunsan dai san larabawa da mugun qulaficin jikin mace, gimbiya hindu kuwa gbdy haushin kanta tayi na kuskuren sanya bimbii rawa, kishi sosai taji tanayi data ga yadda rawar da bimbii take ta dauke hnklin ya'yan sarakunan dake wurin, miqewa tayi zumbur ta buga teburin dake gabanta cike da tsantsar masifa ta dakawa bimbii tsawa kan tabar wurin, duk ya'yan sarakunan suka jiyo suna kallonta prince nasaar yace" no, ta cigaba rawan nata ya birgemu" tace" wlh idan bimbii ta cigaba ita zata bar wurin" dage kafa bimbii tayi alamar ta gama rawan ta taho kanta a qasa ta soma qetarawa ta gaban prince akbar ta wuce shi kuma yana satar kallonta ta gefen ido sai wanda ya lura sosai ne ze fahimci ita yake kallo,ita kuwa bimbii shigewa tayi taje ta sauya kayan dake jikinta ta mayar da nata na asali, har aka gama taron gimbiya hindu tacewa baiwarta zulham kar ta sake tabar bimbii ta kuma dawo wurin taron, bimbii ta gama sauya kaya zulham tace" ki wuce ki koma 6angarenku karki kuma dawowa wurin taron nan" bimbii kuwa dadi taji don daman kunya takeji ta koma wurin,kai tsaye 6angarensu ta koma tana jiran dawowar su lailah, sai dab da magriba su lailah suka dawo suna shigowa duk suka taho da gudu suka rumgumeta, israt tace" gsky kin iya rawa zaki koyami nima" murmushi bimbii tayi kawai,ranar basu yi bacci da wuri ba sai faman jarraba yadda bimbii ke rawa suke ita kuma sai dariya take musu, israt tafi kowa zaqewa don ita a rayuwa tana son rawa da wak'a,bimbii na koya musu irin rawarta suma suna koya mata irin nasu hk suka 6ata darensu sun qi kwantawa da wuri duk da kasancewar gobe ayyukansu yana dayawa, aikuwa suna kwanciya bacci mai nauyi yyi gaba dasu, washegari ummul shukri taga dukkaninsu babu wacce ta fito kan aikinta, dogaro sandarta tayi ta shigo dakin nasu ta tarar dasu sai sharar bacci suke ba wacce ta tashi a cikinsu, juyawa tayi ta fice ba tashesu ba, suna tsaka da sharar baccinsu sukaji saukar ruwan sanyi a jikinsu gbdy an musu wanka dashi kafin su gama sanin abun yi sun soma jin saukar dorina a jikinsu, miqewa sukayi da mugun gudu suka fita, ita kuwa ummul shukri tana tsaye da dorina a hannunta ranta yyi mugun 6ace don batason sakaci da aiki.....





Littafin nan na kudi ne ki biya ki karanta cikin yanci ba satar faga ba, idan kin shirya siye ga transaction details nan, #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp through wannan layin 07041195806, idan kuma da buqatar bayani ga layin kira nan 08080611486....



Alkalamin Bintuu ne...
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



7


*We are far apart from the thousand miles of journey only the destiny links us together*.......never,never leave me my luvv💕



Raba musu aiki ummul shukri tayi ranar kowacce tayi 6angaren da aikin nata yake,bimbii tsinko kayan marmari ne nata takai babban kitchen,israt da lailah kuma wanki ne nasu, khulood kuma tatso nonon raqumi, kowanne cikinsu yyi hanyarsa, bimbii zuwa tayi ta dauki kwando ta tafi lambu, tana shiga ta haye bishiya tana tsinko tuffa tana jefowa qasa tana yar waqarta cike da nishad'i, tana cillo na qarshe sai kawai gani tayi mutum ya chafe, prince nasaar ne fuskarsa dauke da murmushi yana kallonta, ita kuwa bimbii tsa6ar mamaki ne ya hanata sakkowa daga bishiyar saida ya mata alamar ta sakko da hannu sannan ta sakko,dole bimbii tayi mamakin ganinsa don ta karanci akwai izzah da cikakkiyar qasaita irinta sarauta ga jinin sarautar burham, tayi duba da yadda suka dauki bayi ba a bakin komai ba, idan har sunanka bawa kana dauke da tambarin bauta toh suna maka kallon qasqanci ne tare da nuna izzarsu akanka toh mamakinta shine me ya kawo wannan d'an sarki gareta, tashi guda tsoro da fargaba suka mata qawanya sai kallonshi take tamkar taga wani baqon mutum, tunawa tayi bata gaishe shi ba, saurin duqawa tayi akan guiwowinta tare da rissinar dakanta qasa yadda taga bayin wannan gida nayi, murmushinsa ya fad'ad'a ya tsuguna kusa da ita yana qarewa kyakykyawar fuskarta kallo, ita kuwa jikinta har rawa yake ta qosa tabar wurin, shima

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment