Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin kurku kuwa azeez jira yake qarafan nan suyi jajir ya soma manna mata a jiki har saita magantu, ita kuwa fuskar nan nata tayi jajir saboda kwanciyar jini, idanunta sun kumbura har sun soma hadewa kamar zasu rufe, jikinta kuwa duk ya farfashe ko a hk suka kyaleta sai tayi jinya maikyan gaske, azeez tsugunawa yyi gabanta ya ciro daya daga cikin qarafan dake wutan yyi jajir tamkar zuga zugi yasa hannunsa yaye mata doguwar rigar dake jikinta yana shirin yin sama da ita ya manna mata qarfe a tsakanin cinyoyinta, tana ganin hk ta rufe idanunta rufe tana shirin taji saukar qarfe amma sai taji akasin hk don kunnenta ne ya jiyo mata sautim muryar da har yau bata mancewa, hancinta kuma ya jiyo mata qamshinsa,wata irin tsawa mai tsananin rikitarwa ya kwasawa azeez dake shirin sauke wannan jan qarfen wutan a tsakanin cinyoyin bimbii, hkn ne ya dakatar da azeez ya jiyo yyi ido hudu da prince, mamakine ya cikashi ya tsaya kawai yana kallon prince akbar, takowa yyi har tsakiyar dakin yasa hannu daya daya shaqo wuyan azeez take rawanin dake kime a kansa ya fadi qasa, duk da tsantsar jarimtar azeez amma kasa kwacewa yyi a hannun prince akbar, dagashi yyi sama da hannu daya, hannunshi daya harde a bayansa fuskar nan tasa tamau ya cillar dashi gefe guda take ya fadi kan wannan qarfen wutan dake yashe gefe yyi wata qara sbd zafin wannan qarfe daya janye fatar jikinsa sauran hadiman kurkun dake wannan daki kuwa duk sunyi 2tsuru suna kallon prince daya dawo musu tamkar wani namijin zaki, ita kanta bimbii duk da halin da take ciki be hanata mamakin yanayi na tsantsar fushi data ga prince ciki ba, qarasawa yyi inda take ya tsuguna 2kwata be dago da kansa ya kalleta ba sbd bayason ganin halin da fuskarta ke ciki, kunce mata hannayenta yyi da qafafunta ya dauketa chak ya juya ya fice da ita hk suka din ga bi ta wadannan dogayen corridorn sbd shi kanshi wannan kurku a jikin dutse aka ginashi, hk suka din ga ratsawa har suka fito wajen kurkun wurin da dawakansu ke daure ya fara dorata saman dokin sannan shima yahau suka zabiri dawakan nasu suka bar wurin da gudu, sosai suke gudu bisa dawakansa cikin jeji ubaid na biye da dokinsu har suka iso wani kyakykyawan kauye, kai tsaye kofar wani gida suka tsaya,prince ya rufe kusan rabin fuskarsa da rawanin dake kansa sbd baya son wani ya shaida shi don wannnan qauye shima mai suna jandun yana cikin yankin masarautarsu ne, wani tsoho ne ya fito sanye da wata akyabba da qaton rawani yana dogara sandarsa a rankwafe yake tfy sbd da tsufa, gemunsa fari ne gashi dogo sosai, dakatawa yyi yana kallonsu, prince dauke yake da bimbii a hannunsa, murmushi yyi wannan tsoho don sai yanzu ya gane prince daya kalli idanunsa sosai sbd fuskarsa rabi rufe take,nuna musu hanya yyi suka shige cikin gdn,ginin gdn dai gini ne irin nasu na larabawa na zamanin baya, ginin jajir irin na jar qasa, cikin wani daki suka shiga mai yalwa sosai ya nunawa princewa wata shimfida ya kwantar da bimbii data jima da shiga coma, wata dattijuwa ta shigo riqe da faranti da qananan cups ta ajiye gaban prince, itace naiha matar wannan tsoho, shi wannan tsoho ya fito ne daga yankin dilham, Allah yyi masa baiwa ta sanin magani sosai, prince akbar shine ya taba ceto rayuwar wannan dattijo mai suna abbas daga tarkon sarkin yankin dilham sarki najash ya bashi mafaka shi da matarsa cikin wannnan dan qauye.....





Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki sanya #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank sai turomin da screesht na payment ta wannan layi..07041195806 da ita nk whatsapp...





Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔


Written By Bintuu Seer




26



*I'm here to hold you tight dear,if you feel like cry do it on my shoulder*.......I' m here for you my love💕💕




Tunkan su mishi bayanin komai, matarshi naiha ta sake shigowa dakin dauke da wani qaramin bowl mai dan fadi da ruwa a ciki ta wuce inda bimbii ke kwance, sunkuyawa tayi kusa da bimbii ta soma sanya wasu ganye cikin ruwan bowl din nan tana fito da ganyen ta matse tana daddanna mata a jiki musamman wuraren dake da rauni, saida ta gama sannan ta fito da wani garin magani tana shafe mata dukkanin jikinta dashi, su kuwa su prince akbar basu iya hangen abunda take mata har ta gama, ubaid tuni daman ya fice yana farfajiyar tsakar gdn yana jiran fitowar princce akbar, dattijo abbas shima miqewa yyi shi da prince suka nufi wurin da bimbii ke kwance, kallonta kawai abbas yyi yace" amma tana da ciki sbd alamun hkn ya bayyana tattare da ita" shi kansa prince gabansa yyi mugun faduwa na jin wannan zance, dago idanunsa yyi ya qura mata idanu, kallonsa abbas yyi yace" dole tana buqatar hutu da cikakken kulawa" murmushi prince yyi kawai, dattijo abbas ya juya ya fita shi kuma ya nemi gefenta ya zauna tare da riqo hannunta dukka yana kallon zoben azurfan daya sanya mata har yanzu yana nan bata cireshi ba, ganin hawaye yyi na fita daga idanunta dukda kasancewar idanun nata a rufe suke tana bacci, qura mata idanu yyi sosai sai kuma ya kwantar dakansa gefenta ya dauki hannun nata ya cusa cikin gashin kansa yadda take masa kenan idan tana son sanya shi bacci, ji yyi duk duniya babu wacce yake tsananin tausayi irin bimbii sai ya soma ganin laifinsa na rashi bawa abunda yafi so fiye da komai cikakken kulawan daya dace, shigowar naiha ne yasa ya dago dakansa da sauri yaja gefe amma still hannunsa na riqe da nata, murmushi naiha tayi tace" ina son gyarata ne" kallonta prince yyi sai ya maida kansa ya kalli bimbii daidai lkcin bimbii ta bude idanunta a hnkli ta saukesu bisa fuskarsa, hannunta ta kalla ta gansa cikin nasa sai ta dago idanunta ta zuba ma fuskarshi idanu shima ita yake kallo duk sun qure juna da idanu, naiha dake tsaye gefe binsu kawai take da kallo tana karantar saqon idaniyansu, murmushi tayi kawai don tabbas yanayin kallon dake kwayar idon kowanne cikinsu ya bata tabbacin dukkaninsu sunyi nitso cikin kogin soyayya hade da kewar junansu, juyawa tayi ta fice ta basu wuri, bimbii rufe idanunta tayi tana kuka, matsawa yyi kusa da inda take kwance yasa hannu yana share mata hawayen dake fita daga idanunta, cikin sanyin murya yace" kiyi hkr ki yafe min kinji" shiru tayi amma still idanunta na rufe yace" don Allah ki bude idanunki ki kalleni qila ki yadda da abunda zan fada miki" qin bude idanunta tayi yyi, hannunsa yasa ya soma tattaro dogon gashin kanta dake baje yasa wani dogon kyalle ya daure mata wuri daya, duk da hk bata bude idanunta ba, hannunsa yakai kan kirjinta tana jin saukar hannunsa wurin tayi saurin bude idanunta tana son ture hannunsa daga wurin amma jikinta ba qarfi tana cikin zafin ciwo, shima da gangan yyi hkn sbd ta bude idanu ta kalleshi aikuwa yyi nasarar sarqe idanunsa da nata, ta jima tana kallonsa sannan ta juyar dakanta, naiha ce ta shigo prince ya miqe ya fice, a farfajiyar tsakar gdn ya tarar da dattijo abbas yana hada wasu magunguna suna hira da ubaid,suna ganin fitowarsa ubaid yyi saurin tashi daga inda yake ya tsaya qam, dattijo abbas ya fito da wata qaramar kwalbar magani ya miqawa babban prince yace" ranka ya dade gashi ka riqe wannan yana maganin duk wani zugin ciwo" hannu yasa ya amshi mgnin ya daga masa hannu alamar ya gode, rakasu yyi suka fita waje suka haye dawakansu suka zaburesu suka dauki hanyar barin wannan qauye, 6angaren sarainiyya kuwa wannan mummunan labari yakai kunnenta, kwatanta rudewar da tayi ba'a mgn, tasan tabbas tunda hk ta faru dole sarki abdallah bin jabal ya samu labari, sarki abdallah bin jabal kuwa ya samu labarin zuwan prince akbar babban kurku abunda ya daure masa kai shine wai prince ya fitar da wata baiwa da aka sameta da ciki, toh meye hadin babban prince da baiwa kuma? miqewa yyi tsaye ya bada umarnin ayi masa bincike kan wacce wannan baiwa kuma wanne laifi tayi aka kaita wannan wuri,batare wani 6ata lkci ba bincike ya kammala, cikin binciken sun tabbatar masa wannan baiwa dai tsohuwar babbar baiwar prince akbar ce kuma hadima a 6angaren sarauniyya amma basu gano laifin da tayi aka kaita wannan wuri ba saidai ta tafi wurin ne bisa umarnin sarauniyya mar'atussaliha, sarki abdallah bin jabal ya dago fuskarsa da tayi ja sbd tsantsar 6acin rai yace" babbar baiwa ga prince kuma take dauke da ciki?toh cikin waye?" miqewa yyi kawai ya shige cikin gd, sarauniya kuwa tana 6angarenta sai faman zirya take don tabbas ta rasa mafita, saqon kiran sarki ne ya tarar da ita, sanye take daman da wata doguwar riga da mayafi ta fito ummu nana ta mata rakiya har kofar shiga 6angaren sarki tana shiga ta tarar dashi zaune a wata kujera, neman qasan carpet tayi ta zauna tare da sunkuyar dakanta qasa, be mata mgn ba sai ya dauki lkci sannan yace" meye laifin baiwar da kk bada umarnin a kaita babban kurku?" dago dakanta tayi ta kalleshi tace" ranka ya dade wannan baiwa a 6angare na take kuma an sameta da laifin ciki" yace" kurkun qasa shine kurkun da ake miqa duk baiwar da aka samu da ciki amma ita wannan meyesa aka kaita babban kurku?" shiru sarauniyya tayi saida ya daka mata tsawa tukunna yace" ina mgn kin min shiru, cikin waye a jikin wannan baiwa?" sarauniyya jikinta har rawa yake ta daga idanunta ta kalli sarki abdallah da idanunsa kawai sun tabbatar mata da rashin wargi, tace" nima binciken da nk kenan" girgixa kansa yyi ya daga mata hannu ta miqe jiki a mugun sanyaye ta fita, tuni sarki abdallah ya bada umarni cikin wannan daren yake son su nemo duk inda prince akbar yakai wannan baiwa su kaita kurkun qasa kafin washegari, isowar prince akbar kenan shi da ubaid labarin abunda ke faruwa ya taddasu, wannan zance na cikin jikin bimbii gbdy ya zama wani zance dake masifar tashe cikin wannan gdn sarauta, duk inda taron bayi suka hadu toh wannan zance suke gutsurawa junansu cikin hk har zancen yakai kunnen su israt, wannan abun sun jishi tamkar al'amara, mafi yawan mutane cewa suke bimbii a wani wurin tayo cikinta don tabbas ba wanda ya shaida ta fito wankin budurci, gimbiya hindu har ma da prince nasaar dukkaninsu sun aminta cewa cikin jikin bimbii bana prince akbar bane,prince yasan sarai halin mahaifin nasa bazai tanka masa ba har sai ya samo inda bimbii inda take, kiran ubaid yyi yace" komawa zamuyi qauye jandu don tabbas yankin burham ne kuma zasu iya gano inda bimbii take" ubaid yace" ranka ya dade yanzu duk wani motsinka dama duk wanda ke wannan 6angare yana kan idanun masarauta, yanzu hk gbdy saman 6angaren nan zagaye yake da dakarin sama masu masu" shiru prince yyi amma hnklinshi ba'a kwance yake ba, 6angaren bimbii kuwa tana samun duk wata kulawa daga wurin wadannan dattijai sun dauketa kamar wata diyarsu don daman basu ta6a samun magaji ba, bimbii ta samu ingantattun magunguna bacci mai dadi yyi gaba da ita, wadanda aka sanya binciko inda bimbii take kuwa tuni suka yiwa kauyen jandu tsinke cikin shigar bad da kama ta yadda babu wanda ze ganesu suka soma kewaye cikin qauyen bawai sun tabbatar wannan qauyen bimbii take ba, sun shiga qauyuka da dama bincike suke sbd ance prince yyi gabas ne lkcin daya dauki wannan baiwa kuma bisa doki yake, prince baya shiga cikin gari bisa doki kuma idan har gabas yyi toh tabbas wani qauyen ya kaita dake maqobtaka da masarautar burham,cikin masu farautar bimbii har da mutanen prince nasaar, suma burinsu su riga dakarun sarki abdallah bin jabal samo inda bimbii take ya basu umarni mutuqar sun ganta su dauketa su miqata qasar spain ta jirgin ruwa,cikin izinin ubangiji mutanen prince nasaar suka riga isa inda bimbii take suka dauketa suka qarasa da ita port suka sanyata cikin jirgin ruwa saidai kafin wannan jirgi ya tashi har dakarin sarki abdallah bin jabbal sun bayyana a wurin,bayin prince nasaar kuwa suna ganin hk suka sulale suka bar port din don basu so wadancan dakaru su shaida fuskokinsu, su kuwa dakarin babban burinsu su chafke bimbii kuma cikin ikon Allah sukayi nasarar kamata, 6angaren masarautar burham kuwa sarki abdallah bin jabal ya sanya taro na musamman wanda ze gudana a filin kofar fadarsa, washegari filin wurin ya cika maqil da jama'a, sarki abdallah bin jabal yana can saman matattakala bisa kujera ta alfarma gefensa kuma prince akbar ne sai sauran princes din da ragowar masu fada aji cikin wannan masarauta ta burham, ta can daya gefe kuma sarauniya mar'atussaliha ce tasha kaya na alfarma ita da yan fadanta duk suna zazzaune a kujerun girma idan suka hanga qasa matattakar al'umma ne birjik kowa na sauraro, wurin tsaro ne ta ko'ina,sarki abdallah bin jabal dakansa ya miqe ya soma jawabi, jawabinsa na farko shine yace" yau ranar farin ciki ce hade da baqin ciki dukka,yau itace ranar da masarautar burham zata qulla yarjejeniyar aure tsakaninta da masarautar abu ansar, wannan yarjejeniya ta aure zan qulla tane tsakanin da prince akbar da princess mariyatul qifdiya" prince akbar dake gefe sunkuyar dakansa yyi, zuciyarsa cike da mamakin wannan abu, prince nasaar kuwa sai wani murmushi yake, fuskokin kowa wurin dauke take da annuri musamman sarauniya mar'atussaliha, sarki abdallah ya tsuke fuska sannan ya koma ya zauna prince andal ya miqe ya dora bisa jawabin sarki abdallah yace" sannan yau din kuma wannan masarauta ta zartas da hukuncin kisa kan wata tsohuwar baiwa dan sarki da aka samu da ciki wanda kowa yasan girman wannan laifi cikin wannan masarauta ta burham" sai lkcin prince akbar yyi hanxarin dago da fuskarsa inda ya hango manyan dakaru majiya qarfin sun fara hawo da bimbii kan matattakalar, tsayar da ita akayi gbdy duk sun daddaureta, sarki abdallah ya bada umarni sarkin kisa ya sare kan bimbii...........






Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, union bank, saiki turomin da screesht ta whatsapp ta wannan layi....07041195806.....






Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



27



*My heart is paining*....I can't stop the tears💕💕



Sarkin kisa ra'iz wani gabjejen qaton mutum ne mai yalwar girman jiki da fad'I ga wani jibgegen rawani akansa, hannunsa rige da wata takobi tsirararta ya soma haurawa matattakalar inda bimbii ke daure, bimbii gbdy ta jigatu bakinta sai fitar da jini yake ga gashin kanta daya hargitse ya rufe mata fuska, jira kawai take su gaggauta fille mata kai ko zata huta da wannan mawuyacin halin da take ciki, ra'iz ya qarasa hawa wurin ya daga takobinsa sama da niyyar fille kan bimbii yaji an daka masa wata razananniyar tsawa, dakatawa yyi ya waiga sai ganin prince akbar yyi tsaye a bayansa, sauke takobin yyi qasa, hkn yyi daidai da miqewar sarauniya daga kujerarta ta dakawa prince tsawa akan ya hanzarta barin wurin, sarki abdallah kuwa yana daga zaune yana kallon abunda ke faruwa,murmushi sarki abdallah yyi ya kalli prince nasaar dake gefensa yace" ka sanar da sarkin kisa yana bisa umarni ne kar ya tsaya 6ata lkci" miqewa prince nasaar yyi shima jikinsa a mutuqar sanyaye ya daga murya sosai yace" sarkin kisa ya harzarta aiwatar da umarni batare da 6ata lkci ba" wannan zance na shiga kunnen sarkin kisa ra'iz ya kuma daga takobinsa da niyyar cika umarnin sarki abdallah bin jabal, cikin tsananin zafin nama prince akbar ya chafe takobin nasa yyi wulli da ita gefen daman bimbii tuni takobin ta tsinke daurin da akayi mata ta 6angaren dama, qara chafe takobin yyi ya kuma cillata gefen hagunta tuni daurin ya warware dukka ya riqeta yyi gefe da ita, wurin yyi tsit sbd kowa ya cika tsantsar mamakin wannan abu da prince keyi bisa umarnin mahaifinsa, sarki abdallah bin jabal miqewa yyi cike da mamaki shima amma sai ya 6oye hkn a fuskarshi ya kalli shugaban dakarin dake tsaye a wurinl yace" su kama prince maxa su miqashi kurku tare da azabtar dashi pita kuma wannan baiwa su kawo masa kanta yanzu gabanshi"wannan umarni da sarki abdallah bin jabal ya bayar yyi masifar gigita sarauniya mar'atussaliha saidai ko kusa bata da damar mgn musamman a wannan yanayi da ran sarki abdallah ke tafasa,batare da wani 6ata lkci ba dakarun dake wurin duk suka zare makamansu sukayi kan prince akbar, shi kuwa yana tsaye yana ganin hk kawai yaja bimbii zuwa bayansa, kallo daya zaka masa kasan ya shirya tararsu, suna qarasowa suka afkan kansa da hannu guda kawai yake 6arar dasu dayan hannun nashi riqe da bimbii, cike da azama da mugun zafin nama yake uwar watsi dasu tamkar wani gawurtaccen zaki ta tsakiyarsu yake bi idan ya watsar dasu sun zube qasa, wuri gbdy ya hautsine da artabu tsakanin dakarin sarki abdallah bin jabal da prince akbar shi daya kawai ya gagaresu, ba kashesu yakeyi ba kawai raunata su yakeyi ya wuce burinsa kawai ya samu doki ya haye su bar wurin amma ina abu ya gagare sbd dakarin nan kamar qaruwa suke, gumurxu sosai ake bugawa a wannan wuri, bimbii bata ta6a sanin prince namijin gaske bane a filin fama sai yau ta tabbatar da hkn, gwaninta kawai yake nuna ta tsantsar jarumta duk yawansu ko kwarzane babu wanda yyi masa kuma a hkn yake kare bimbii daga harinsu, fararen kayan dake jikinsa gbdy sun 6aci da jini, fada yake cikin tsananin zafin nama da gocciya tamkar wani hatsabibi, yadda prince akbar ke fada da nuna bajinta be kasance ya basu mamaki ba don duk wanda ya kwana ya hantse a masarautar burham yasan wane ne prince akbar a filin fama shiyasa shi kansa sarki abdallah bin jabal ke mugun alfahari dashi, ganin hk ne yasa sarki abdallah bin jabal miqawa hadiminsa uxair hannu ya miqa masa wani mashi mai tsinin gaske, daga mashin yyi dakansa yyi saitin prince akbar, shi kuwa yana cikin fada da wadannan dakaru batare daya ankara ba kawai yaji harbin mashi a bayansa, mashin yana dauke da guba sosai, daga kansa yyi ya hango mahaifinsa riqe da wani mashin yana saitinsa, batare daya zare mashin dake jikinshi ba yyi kukan kura yyi watsi da dakarin dake gabansa yaja hannun bimbii da gudu suka hau kan wani doki, dakyar yahau dokin cike da dauriya sbd wannan harbin mashin, suna bisa dokin wani harbin ya kuma samunsa, hk ya cije yaja dokin da mugun gudu suka bar wurin a guje, sarki abdallah ya bada umarnin su bisu, yana kan dokin amma qarfinsa ya soma qarewa sbd harbin mashin dake jikinsa, zuciyarsa ce kawai ke tfy dasu bisa dokin, hannu yasa ya cire mashin dake tsire a bayansa, bimbii juyowa tayi tana kallonshi taga halin dayake ciki amma duk da hk yana qara daurewa yana jan dokin, gudu suke amma dakarin sarki abdallah na biye dasu, wata hanya suka miqa cikin jeji suna gudu saida suka je qarshen hanyar suka tarar ba hanya sai wani qatoton rami mai zurfi da fadi, qasan ramin qananan bishiyoyi ne tare ruwa dake kwaranya tamkar qorama, dokin nasu yaja ya tsaya gaban wannan qaton rami mai tsayin gaske, sauka sukayi daga kan dokin duk suka tsaya sukayi cirko cirko, gashi tabbas wadannan dakaru sun kusa cimmusu, bimbii a wannan lkci ta dena tausayin kanta prince take tausayawa yanayin yadda ta ganshi, matsowa kusa dashi tayi ta riqeshi ya durgusa a wurin yasa hannu ya zare dayan mashin dake cake a gefen cikinsa, tabbas shi kansa lkcin yasan abu ne mawuyaci ya rayu domin wannan mashi na mahaifinsa yana da gubar gaske, saidai babban burinsa shine ya tsirar da bimbii ita da abunda ke cikinta, sautin sawun dawakai suka jiyo hkn ya tabbatar musu dakarin dake biye dasu ne, dago dakansa yyi ya kalli bimbii yace" ki gafarce ni don Allah ki yafemin" riqo hannunta yyi yace" ina son ki rayu komai wuya sannan kar ki mance dani cikin rayuwarki, kin ji, ina sonki dayawa na sadaukar miki da rayuwata gbdynta" kuka bimbii take sosai tana rufe masa baki da hannunta tace" bani son ka sadaukarmin da rayuwarka na fison mu rayu tare ko mu mutu tare, bazan rayu babu kai ba, wlh bazan iya ba" kuka sosai take ta kwantar dakansa a kirjinta, daidai lkcin dakarin sarki abdallah bin jabal suka qaraso wurin, batare da 6ata lkci ba suka sakko daga kan dawakansu suka nufo wurin, prince yana ganin hk yasan tabbas wlh kashe bimbii zasuyi, miqewa yyi duk da jirin dake dibansa. yana ja da baya, bimbii kuwa tana bayansa tana kuka, gani yyi wasu daga cikinsu na bisa dawakai sun saita bimbii da mashi, ita kanta bimbii bata ankara ba sai ji tayi kawai prince yasa hannu cikin azama ya hankadata cikin wannan dogon rami, su kansu dakarin dake wurin basuyi zaton hk ba, ihu take har ta fada qasan wannan rami cikin ruwan dake kwaranya,shi kuwa prince tsayawa yyi yana kallonsu sai kuma kawai ya sunkuya ya dauki takobinsa ya afka musu tamkar ba rauni a jikinsa, prince nasaar daya biyo bayansu yana qarasowa yaga wannan artabu tsakanin dakarin nan da prince, murmushi yyi yasa hannu ya ciro kibiyoyi ya soma masa dashi, burin daman kawai ya kashe shi, aikuwa kibiyoyin suka same shi dukka a gadon baya, sakin takobin dake hannunsa yyi kawai ya durqushe a wurin yyi zaman ruku'u, daga wata kibiyar yyi da niyyar qara masa yaji an riqe ta baya, juyawa yyi a fusace yaci karo da gimbiya hindu bisa doki ta rufe rabin fuskarta da baqin kyalle, tace" waye yace ka kashe shi" sauke hannunsa yyi ya maida kibiyoyin, shi kuwa prince hannunsa kawai yake miqawa saitin ramin da bimbii ta fada har numfashin shi ya tsaya chak, gimbiya hindu ta sakko daga kan dokinta ta nufo inda yake ta soma jijjigashi tana hawaye sosai, kamar daga sama suka soma suka ganin wani irin hayaqi yana gauraye ko'ina cikin dajin, zumbur gimbiya hindu ta miqe tana waiwaye hkma sauran dakarun dake wurin, prince nasaar shima 2kalle ya somayi basu ga kowa ba, wasa wasa wannan hayaqin ya cika wurin sosai ko tafin hannunsu basu iya gani, a hnkli kuma hayaqin ya soma washewa suka kai dubansu wurin da prince yake kwance suka ga wayam, abun yyi mugun daure musu kai da basu mamaki basu ji motsin komai ba kuma basu ga kowa ba amma sun nemi gangar jikin prince akbar sama ko qasa sun rasa, ba kowa ne da wannan aikin ba sai ubaid babban hadimi ga prince,shine ya sanya wannan hayaqin sannan kuma ya lalla6a ya dauke prince batare da sun ankara ba, nesa da wurin sosai ya ajiye dokinsa, hk ya dauki prince ya haye dokinsa yabar wurin, prince nasaar yasa dakarun duk su bazama cikin wannan jeji don nemo gawar prince akbar don miqata ga sarki abdallah bin jabal, batare da 6ata lkci ba suka watsu cikin wannan jeji suna neman prince akbar, shi kuwa ubaid be tsaya ba saida ya tabbatar ya fice daga yankin masarautar burham, wani kogon dutse ya shige da prince anan ya tarar da dattijo abbas, ajiye prince yyi dattijo abbas ya matso kusa da inda prince akbar ke kwance yakai hannunsa ya dora saitin zuciyarshi yaji babu alamun numfashi tattare dashi, kansa ya dora wurin sai lkcin ya jiyo bugawar zuciyar tasa a hnkli, dago da kansa yyi,ubaid yace"meke faruwa dashi ya mutu ne" girgixa kansa yyi yace" da sauran numfashi a tare dashi" ajiyar zuciya ubaid yyi yana kallon fuskar prince da kwance, dattijo abbas ya fito da wasu

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment