Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk suka kalli juna a rikice, miqewa israt tayi da sauri tayi hanyar waje cike da rudani, khulood ma ta miqe da sauri tabi bayanta, saurin riqo hannu israt tayi da taga ta nufi 6angaren prince sbd ta lura bata cikin hnklinta, juyowa israt tayi a fusace ta fizge hannun daga riqon da khulood tayi mata sai kuma ta tsaya chak ta juyo ta kalli khulood tace" khulood wannan abu baki tunanin akwai sarqaqiya cikinsa sbd nasan bimbii ba zata ta6a tunanin gudu ba, anya babban prince baida hannu a wannan abu kuwa sbd na lura kamar ya takura mata dayawa" khuloo ta jata suka samu wani wuri suka zauna, kallonta israt tayi tace" nikam a yadda nk gani kamar akwai wani 6oyayyen al'amari tsakanin babban prince da kuma bimbii kamar hkn shine ze sata tayi yunqurin gudu" israt tayi ajiyar zuciya sannan tace" tabbas wannan hasashe naki hkne duk da bani da masaniya amma akwai abunda ke tsakanin prince da bimbii sbd ina yawan ganin damuwa tattare da ita, bani son matsa mata da tmby ne kawai" khulood tace" mu tayata da addu'a kawai kar su samu damar kamata" jinjina kai israt tayi alamun nuna gamsuwa da abunda khulood ta fada, 6angaren prince kuwa fitowarsa daga wanka kenan yana sanye da wasu kaya masu mutuqar taushi, zama yyi a wata kujera lenah ta matso ta soma tsiyaya mata ginger tea, daukan cup din tayi ta miqa masa da hannu biyu tare da rissinar dakanta qasa, amsar cup din yyi ya soma sipping a hnkli yana tunanin bimbii, zagayawa tayi ta bayanahi ta soma masa tausa a hnkli, ubaid ne ya shigo da sauri ya tsaye gaban prince tare da rissinar dakansa qasa, kallon ubaid yyi yasan yana tafe da wani labari mai muhimmanci sbd fuskarsa ta nuna hkn, dagawa lenah hannu yyi ta dakata da masa tausan ta sunkuyar dakanta qasa sannan sum sum ta wuce ta fice, ubaid ne ya matso da fuskarsa daidai kunnen prince ya rada masa wani abu, wata irin zabura prince yyi ya miqe tsaye tare da dire qaramin cup din dake hannunsa saman small table din dake gabansa, shi kansa ubaid cika yyi da mamakin yanayin da prince ya nuna,batare daya sake kallon inda ubaid yake ba yyi hanyar waje da sauri ya fice, ubaid ya rufa masa baya, hk suka isa 6angaren sarauniya mar'atussali, saida suka din qetare kusurwa kusurwa suka samu shiga cikin fadarta, ubaid yaja ya tsaya a kofa shi kuwa ko neman iso beyi ba ya afka ciki, bayi ne jere ta 6angaren dama da hagunta wasu cikinsu na mata fifita, ita kuma tayi ado na manya gwalagwalai tunda daga wuyanta har kunnuwanta da kuma hannayenta, batayi mamakin ganinsa ba don daman abunda take jira kenan guduwar bimbii yakai kunnensa, qarewa suturar dake jikinsa kallo take sbd gani tayi kayan bacci ne ma sanye jikinsa hkn ya kuma tabbatar mata da gskyr abunda ta gani cikin kwayar idanunsa, dagawa bayin dake tsatstsaye tayi hannu suka soma ficewa,zuba masa idanu tayi tana sauraron abunda ya kawoshi gareta,neman wurin yyi kan kyakykyawan turkish center carpet din dake malale ta cikin wata kusurwa ya harde kafafunsa, tasowa tayi itama a hnkli ta soma sakkowa daga tudun da kujerar alfarma da take zaune akai ta shiga wannan kusurwa ta zauna bisa wata lumshashshiya kujera mara tudu tana kallon prince, kallon shima yyi sannan ya soma mgn yace" ranki ya dade wani labari nakeji na guduwar baiwar dana bar miki shin wannan zance gskya ne" murmushi tayi sannan tace" tabbas hk abun yake saidai dakaran tsaro na nan suna bincike kan guduwar nata sbd an jima ba'a samu wani bawa da laifin gudu ba" shiru yyi batare daya kuma furta komai ba, tunani kawai yake abunda yasanya bimbii gudu tabarshi da dakon so, nutsawa cikin tunani yyi sai yake zaton ko furta mata kalmo so da yyine ya tsorata ta yasa ta gudu daga masarautar,dafashi sarauniyya tayi fuskarta dauke da murmushi tace" yakai wannan prince ka sanar da mahaifiyarka ma'anar wannan damuwa data bayyana qarara a fuskarka dalilin guduwar wannan qasqantacciyar baiwa" dago da idanunsa yyi da bbu komai cikinsu sai tsananin tashin hnkli ya qure mahaifiyar tasa da idanu, ita kanta ta tsorata dashi batayi tunanin soyayyar baiwar ta masa wannan illar ba, kunsan tsakanin uwa da d'a take wani tausayinsa ya shigeta, bece mata uffan ba ya miqe ta dago idanunta tana kallonsa har ya fice, ubaid na ganin fitowar tasa ya rufa masa baya don shi ko kallon inda ubaid ke tsaye beyi ba ya wuce abinsa, yana komawa 6angaren nasa ya janyo farin dokinsa ya haye ya zabureshi da mugun gudu shima ubaid yahau nasa ya rufa masa baya, ba ko'ina suka tosa ba sai filin sukuwar dokin da suka tsinci bimbii, tsayawa yyi yana kallon hanyoyin da suka rabu gida biyu, kallon hanyar da tayi damansa yyi batare da wata shakka ba ya dunfari hanyar bisa dokinsa mai tsalelen gudu,hk yyita zabga gudu bisa kan namijin dokinsa babban hadiminsa na take masa baya har suka soma shiga cikin gari, hknne yasa yaja linzamin dokinsa ya tsaya yana qarewa ko'ina kallo, juwaya kawai yyi dakan dokinsa ya koma baya, suna zuwa daidai inda ya ta6a bangaje bimbii da doki ya tsayar dakan dokin nasa sannan ya diro yana qarewa wurin kallo, ranar sai tsakar dare suka koma masarauta ya shige 6angarensa yace" kar abar kowa ya shigo masa baida buqatar ganin kowa" take masu tsaron kofar suka rufe kofar shiga 6angaren nasa, yana shiga ya nemi kan wata kujera ya zauna tare da jinginar dakansa cike da tsantsar damuwa da rudani, wata qaramar locker dake manne da table din dake gabansa yaja ya sanya hannu ya fito da wani qaramin akwati mai kyan gaske ya bude akwatin ya fito da wadannan awarwarayen daya ta6a ciresu daga hannun bimbii yana qare musu kallo tare da jujjuyasu a hannunsa, ranar dai prince kwanan zaune yyi don be bawa bacci lasisin saceshi......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *A bitter sweet love affair with so much struggling and challenges* I'm waiting for you like crazy,pls come back to me my life.....💕💕




Sati biyu kenan da 6acewar bimbii daga masarautar burham dayawa sun mance da batunta idan aka dauke prince akbar da duk wayewar garin duniya sai ya fita neman bimbii ya gama zaga gari ya dawo babu labari, daga qarshe kawai ya soma bin duk wata kasuwa ta saida bayi, duk kasuwar daya shiga hk zaka ga masu cinikin bayi na binsa da gudu suna masa tallan bayi ko za'a samu irin wadanda yakeso, idan ya qarewa bayin kallo be ga wacce yake nema ba sai yyi gaba abinshi, babban hadiminsa ubaid na take masa baya domin idan zeyi irin wannan fitar ta sirri baya fitowa da sauran masu tsaron lfyrshi, ubaid shine na hannun damansa ya bashi daman sanin dukkanin sirrinshi sbd ya yarda dashi dari bisa dari dashi kadai yake fitowa, ubaid yana mutuqar tausayin prince yadda yaga ya zurfafa kan soyayyar wannan baiwa wanda tabbas yasan hkn na iya kawo fitina ba qarama ba cikin gdn sarautar burham, ranar ma hk suka koma gd babu wani kyakykyawan labari, bayan yyi wanka ya zauna ya zurfafa tunani kan wannan abu daya faru, nasarar gudu ga bawan dake masarautar burham ba abu ne mai sauqi ba sbd tsatstsauran matakan tsaro ta kowacce kofa,idan kuwa hkne taya bimbii har ta samu nasarar tserewa batare da kowa daga cikin dakarin dake tsaron kofa sun ankara ba,sunkuyar dakansa yyi yana tunani sosai don gani yake kamar da akwai lauje ciki nad'I cikin wannan abu, kiran ubaid yyi dake bakin kofa a dogare, shigowa yyi da sauri ya iso gabansa tare da rissinar dakansa qasa, dago idanunsa yyi da suke jaji dasu tamkar yyi kuka ya kalli ubaid yace" kaje kayimin bincike na musamman kan yadda abun ya faru" ko be nemi qarin haske ba yasan me prince ke nufi, rissinar dakansa yyi alamar amsar umarni, daga masa hannu prince yyi sannan ya fice don aiwatar da abunda aka umarce shi, yana ganin ya fita ya maida kansa ya kwantar jikin kujera dayake zaune,lenah ce ta shigo hannunta riqe da qaramin basket na kayan marmari taje kan table dake gabansa ta ajiye, ta fito da yar qaramar wuqa ta dauki tuffa daya tayi slicing dinta gida hudu tana daukan slice daya daga cikin yankan tana miqa masa idan yaci saita qara masa wani,slices biyu kawai yaci ya daga mata hannu alamar ya isa hk, daukan basket din tayi ta fita dashi sannan ta dawo taci uwar kwalliya tamkar wacce zata gasar sarauniyar kyau, sanye take cikin wata abaya fara sol ta rufe ko'ina na cikinta amma bakinta yadau jan janbaki sai daukar idanu yake abunku da farar fata, gashi ta tsayar da eye lashes na idanunta hkn yasa gashin idanun nata yyi duhu, kafarta bbu takalmi don daman ba'a shiga 6angaren nasa da takalmi, tunda ta shiga yake kallonta amma a zahiri gixo take masa sai yake mata kallo da bimbii, ita kuma ganin yana kallonta sai tayi zaton ta yaudaro hnklinsa kanta ne, murmushi tayi ta wuce kan royal bed nasa ta hau ta zauna tana jiran ya gama abunda yake ya hawo ita kuma ta soma mishi tausa daga nan ta qure basira da hikimarta ko Allah ze bata sa'a prince ya amshi budurcinta daren yau, prince kuwa ya jima yana 2karancensa sannan ya taso ya nufo gadon yahau, yanayin kwanciyar da yyi kawai ya nuna mata baya buqatar komai daga gareta, duk bayin dake masa hidima sun san alamomin mgnrsa koda be furta komai ba idan yyi wata alamar suna gane abunda yake nufi, idan yana son tausa ze kwanta ya juyo bayansa idan kuma ba hk ba toh tsakanin biyu za'ayi daya ko ki tafi ko kuma dai yana buqatar wani abun daban, itama yanzu tana ganin ya kwanta fuskarsa na kallon sama taja gefe sai kuma taga ya daga mata hannu, jikinta a mugun sanyaye ta sakko daga gadon ta sake masa curtains din dake kame gefe gefen kusurwar sannan ta juya a hnkli ta soma tfy har ta fice, 6angaren bimbii kuwa Izuwa yanzu ta gama jigatuwa, abinci sau guda kawai ake basu ga ciwo dake cinta a hnkli amma cikin masu tsaron wannan kurku babu wanda ya kalleta bare tasa ran zasu bata magani, qishirwa kawai ze iya kar mutum cikin wannan wuri don kusan kullum ma sai an fitar da fursunonin da suka mace a dakunansu, su kuwa masu tsaron wannan kurku zuciyarsu a bushe da rashin imani, hk zasu fito da gawarwakin mutanen da wahala ta kashesu su zubasu cikin keken doki aje a watsasu a babban kogi ruwa ya tafi dasu, dayake zuciyar tasu babu ko digon imani basu dauki ran mutum bakin komai ba, bimbii zazza6ine sosai yake wujijjigata kwana biyu amma babu yasan tanayi iyakarsu da furnoni shine duk safiyya su miqa musu abinci a wani qaramin akushi sai ruwa a wani cup na katako, hk zasu dauka suna ci tamkar mayu, bimbii tayi duhu ta lalace sai dogon hanci da manyan idanu da kuma dogon suman kanta daya hargitse ya sake fallasa tsantsar wahalar da take fuskanta, ruwan hawaye ya qare mata kawai kukan zucci take fama dashi da tafasar ruhi, burinta a yanzu shine mutuwa ta kawo mata ziyarar gaggawa, Allah kuma yasa qarshen wahalarta kenan, cikin dare ciwo ya tsananta mata sai murqususu take tana kakari sbd azaba ga gumi dake fama keto mata ta ko'ina, jan jikinta ta somayi har ta qarasa bakin kofa ta miqe zaune a hnkli tana buga kofar da hannunta ko zasu jiyota amma babu wanda ya jiyota har dan qarfin da yyi saura jikinta yyi qasa ta koma ta kwanta kawai, sai safiyya suka bude don ajiye mata abinci suka tarar da ita cikin wani irin yanayi na tsananin ciwo, fito da ita sukayi suka kaita wani babban daki da suka jibge masara lfy, daya daga cikin masu kula da marasa lfyn ana shigo da bimbii ta kalleta sannan ta koma tsaya bisa kanta, wasu yan 2kalle tayi kawai a jikin bimbii ta dago dakanta ta kalli wadanda suka shigo da ita tace" wannan sabuwa ce koh?" daga mata kai sukayi alamar ehh, tace"tana da aure ne?" duk suka kalli bimbii dake kwance a qasa gefe guda tana fama da ciwon dake dawainiyya da ita,dayan yace" gsky bamu sani ba ko tana da aure ko bata dashi" wani yace" ni ban san lkcin ma da aka kawota bare laifin data aikata" kallonta matar tayi tace" kina da shigar ciki shine ke wahal dake" bimbii na daga kwance a qasa ba lfy amma tana ji matar ta ambaci kalmar ciki tayi wani irin zabura ta miqe zaune ta kalleta tace" ciki?ciki kkce ina dashi?toh cikin uban wa?" tsabar rudewa yasata jero wadannan tmbyoyi tamkar wata zautacciya, matar bata kuma kallon inda take ba ta kalli wadanda suka shigo da ita cikin wurin tace" gsky bana jin tana da aure" cikin sauri suka juya suka fita, bimbii kuwa tana daga zaune ta dawo kamar wata mutum mutumi tunaninta ya tsaya chak, gbdy kwakwalwarta ta dakata da duty sbd tsabar dimaucewa da tayi, su kuwa wadanda da suka fita kai tsaye 6angaren azeez sukayi suka sanar dashi cewa an samu wata mai dauke da ciki cikin fursunoni mata amma basu tabbatar ko tana da aure ko bata da aure ba tinda su basu san lkcin da aka kawota ba ma,miqewa azeez yyi da hanzarinsa suka nufi wannan dakin da ake ajiye fursunoni marasa lfy, nuna masa inda bimbii ke zaune sukayi, qare bimbii kallo yyi tuni ya ganeta, mamaki ne sosai ya kamashi dalili kuwa yasan dai bimbii babbar baiwa ce ga prince akbar kuma kowa shaida ne prince akbar be ta6a kusantar kowacce daga cikin bayinsa sbd babu wacce har aka samu ta fito wankin budurci, idan kuwa hkne toh daga ina babbar baiwa guda ga dan sarki kuma jinin masarautar burham ta samo ciki,wannan lalle al'amari ne mai girman gaske don kowa tabbas kowanne cikakkiyar budurwa yake za6e kuma bayanshi babu mahalukin daya isa ya ratsa gonarshi ko ya kusanci baiwa ko karya kusanceta ita dai ta haramta ga kowa mutuqar ta taka wannan matsayi,yana gama wannan tunani ya juya ya fice batare daya furta uffan ba sbd duk wurin babu wanda yasan wacce bimbii ko kuma daga inda ta fito sbd abun sirri ne, shiyasa yana fita be tsaya ko'ina ba sai fadar sarauniya mar'atussaliha don sanar mata da wannan al'amari mai girman gaske, ummu nana ce tayi masa iso ya shiga yana shiga ya rissinar dakai gabanta yyi shiru yana shirin ta bashi umarnin yin mgn,ita kanta tayi mamakin ganin batare data nemi ganinshi ba hkn yasa ta soma tunanin ko wani ya fidda sirrinta ne, ummu nana ce ta sanar dashi sarauniyya ta bashi damar mgn, sai lkcin ya dago dakansa ya kalleta yace" ran wannan sarauniya ya dade nazo miki da wani babbar al'amari" kada masa kai tayi alamar tana sauraronsa, sake rissinar dakansa yyi yace" wannan baiwa da hukuncin daurinta yake kai tsaye daga fadarki an sameta da zaunannen ciki tare da ita" zumbur sarauniyya ta miqe tsaye tana nuna shi da yatsa a mutuqar fusace tace" wannan kuma qarya kk mutumin banza kawai, babbar baiwa ga babban prince a ina zata samu ciki, kowa ya shaida tun aka za6eta bata fito wankin budurci bare ace ya kusanceta koda ya kusanceta tayi ciki tabbas tana hukunci mai girma bare bai ma kusanceta toh idan kuwa a wani wurin ta samo ciki nayi rantsuwar da girman Allah saita gwammace mutuwarta da azabar da zata dandana don wannan tozarci ne ga jinin sarautar burham"...........







Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turon da screenshrt ta wannan layi ...07041195806......






Alkalamin Bintuu ne...
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



25



*My days of deepest sorrow and pain*........heart full of fear💕💕



Dukkaninsu kowa yyi shiru ya sunkuyar dakansa qasa, sarauniyya ta kuma kallon azeez cike da tsantsar 6acin rai tace" ka koma ka sanyata cikin dakin ukuba har sai ta bayyana wannan ciki dake jikinta na waye? amma kar kuyi sake wannan sirrin ya fita har wani yaji" rissinar dakai azeez yyi da sauri sannan yaja da baya ya fita, miqewa tayi ta soma zarya ta kasa zaune ta kasa tsaya tana mutuqar shakkar wannan zance yakai ga kunnen sarki abdallah bin jabal, ummu nana dake tsaye gefenta ta dago dakanta tace" ranki ya dade ki bani dama na dauki yarinyar nan kawai na damqata ga masu cinikin bayin dake tfy habasha su maisheta nahiyarta" saurin kallonta sarauniyya tayi sannan tayi shiru sai can ta dago dakanta tace" wannan shawarar ba mai amsuwa bace yanzu sai na gama binciken mamallakin cikin dake cikinta bana fatan ta kasance da wani abu mai kama da jininmu a tare da ita"kada kai ummu nana tayi alamar gamsuwa da mgnr sarauniya mar'atussaliha, azeez yana komawa yasa aka dauki bimbii batare da sun duba halin da take ciki ba yyi umarni a shigar da ita dakin azaba, batare da 6ata lkci ba suka shigar da ita wannan baqin daki suka dorata kan wata kujera aka daddaure mata hannuwa da kafafu, wata shafadediyar bulala suka soma tsula mata, saukar bulalar sau daya kawai ya dauke ganinta na wasu daqiqai kafin ta dawo hayyacinta sun sake zabga mata wata, azeez na gefe yana kallonta sannan yace" ki fadamin cikin dake jikinki na waye" kallonsa tayi da idanunta da suka kumbura sannan ta dauke kanta, kunsan bimbii idan ta sanya taurin kai ko za'a kasheta bata mgn, hk tayi musu shiru su kuwa basu fasa tsala mata wannan mugur bulala mai tfy da fatar jikin mutum ba, kallonta azeez yyi yace" wannan itace tmby ta qarshe dazan kuma miki wannan cikin dake jikinki na waye daga ina kk samo shi, idan baki bani amsa ba toh sai mu gwada miki azabarmu ta gaba" wuta taga sun kunna a wasu dindinan ginin qasa suka sanya wasu qarafa su jajir, kallonta yyi ya nuna mata wadannan qarafa yace" yanzu zaki ji saukar su a jikinki hkn yasa ki bude baki kiyi mgn"sunkuyar dakanta tayi qasa tana jiran su soma aiwatarwa ta rantse ko zasu kasheta basu sanin waye mamallakin cikin dake jikinta, 6angaren ubaid kuwa tunda prince akbar ya bashi umarnin bincike kan guduwar bimbii be dire binciken nasa ko'ina ba sai 6angaren sarauniya sbd hk kawai jikinsa yake bashi kamar dasa hannun sarauniya kan wannan lamarin qila hkne ma yasa ta amshi bimbii a matsayin baiwarta, duk yadda yyi saida yyi yasa israt da khulood suka koma 6angaren sarauniya da hidima sbd yana da alfarma shima a matsayinsa na babban hadimi ga babban prince be samu mtsl ba ummu nana ta karbesu ta hannun ummul shukri sam ita batasan dangantakarsu da bimbii ba, ubaid ya umarcesu su sanya idanu sosai kan dukkanin shige da ficen dake wakana a fadar sarauniyya mar'atussaliha, fitowar israt kenan daga babban kitchen taga shigowar azeez ummu nana tayi masa iso ya shiga don ganawa da sarauniyya, saurin ajiye kwandon tayi ta waiga hagu da damanta taga babu wanda ke ganinta ta lalla6a ta nufi wurin kofar shiga fadar sarauniyya ta tsaya da can nesa ta hango kuyangin bayin dake tsaye bakin kofar shiga fada, dakewa tayi ta qarasa wurin ta shiga cikin jerinsu tare da sunkuyar dakanta qasa, dayan dake qarshe ta wurin kofa tana ganin israt sai tayi zaton tana cikin masu zuwan rana waton bayin dake amsar dutynsu da rana, fita tayi daga jeri ta tafi sbd tana da uxiri mai qarfi, hkn yyiwa israt dadi sosai, wayancewa tayi ta mannu da kofa sosai tayi qasa kamar tana gyara doguwar rigar dake jikinta, karaff, ta jiyo sautin sarauniyya tana fadar wasu zantuttuka masu kama da al'mara,umarnin da saurauniya ta bawa azeez shine kalmar qarshe data iya jiyowa tayi saurin miqewa ta tsaya qam tare da sunkuyar dakanta qasa yadda taga bayin dake kofar sunyi, daidai lkcin taga fitowar azeez, tana tsaye duk ta qagu ta rasa yadda zata fice daga cikin jerin bayin don daman su uku ne kuma idan suka ga ta fita hk zasu zargi wani abu tattare da ita, tana nan tsaye har ummu nana ta fito kallonsu tayi tace" toh kuje yanzu wasu zasu zo" ita sam bata gane israt ba sbd daman su uku ne kuma ukun ta gansu, sauran suka kalli israt amma ganin da sukayi ummu nana batayi mgn game da israt din ba sai suka juya suka soma tfy daya bayan daya kamar yadda al'adar aikin ta nuna musu,israt kuwa qasa tayi da kanta har suka wuce sauran ita kadai saida ta tabbatar sun wuce kuma ummu nana ta koma ciki itama ta janye jiki ta wuce bata tsaya ko'ina ba sai 6angaren prince, hango ubaid tayi dogare a kofar shiga 6angaren prince, tun shigowarta ya ganota be bari ta qaraso ba ya janye jiki yabi ta wata kofa suka hadu, cikin saurin ta damqa masa takardar dake hannunta bata tsaya wata mgn dashi ba sbd tsaro ta juya ta koma bakin aikinta, shima sanya takardar yyi cikin aljihunsa yyi tfyrsa, saida ya samu wuri mafi sirri ya ciro takardar ya duba, abunda ya gani cikin takardar ne yasa shi sake kallon takardar batare da wani 6ata lkci ba ya nufi komawa 6angaren prince, yana shiga lenah ya gani ta sanar dashi prince bazai samu ganinshi ba yana kwance, kallonta yyi yace" kije dai ki fada masa mgnr tana da muhimmaci" kallonsa tayi tare da murmushi tace" ya kk mgn kamar wani baqo ga dokar wannan 6angare, ni kaina bani da daman iya masa ida baida buqatar hkn" shiru ubaid yyi yana sake duba yanayi yaga lkci na neman kwacewa yasan su waye hadiman babban kurku basu da tausayi bare imani tsaf zasu soma gana mata azaba kamar yadda sarauniya ta bada umarni, qara kallon lenah yyi yace" don Allah ki taimaka ki sanar dashi" haushin ya bata ta harareshi tayi juyawarta ta kyaleshi wurin,juyawa yyi da hanxari don yasan komai nacinsa be isa yaga prince yanzu ba, wurin wata bishiyar magarya ya tsaya ya ciro wani uzir ya hura da qarfi, sai ga wata kyakykyawar tsuntsuwa ta taso da gudu daga gabas ta nufo inda yake ta sauka a kafadarsa, saman wannan bishiyar magarya anan shekar wannan tsuntsuwa yake, sautin wannan uzir ne ke kiranta idan har ba tayi nisa ba,wannan tsuntsuwa ta prince akbar ce tana da tarin baiwa da fiqira daya banbanta ta da sauran tsuntsaye ba inda bata shiga a 6angaren prince akbar sannan duk inda ya aikata bata kuskuren isar da saqo, tasan ubaid sosai don shine kawai da prince ke kiranta da qarar uzir, daukanta ubaid yyi ya qulla mata saqon wata qaramar takarda a kafafunta sannan ya dagata sama ya kalli kudu da ita saitin 6angaren prince akbar ya saketa ta tashi firrrrrr, wannan tsuntsuwa bata tsaya ko'ina ba sai 6angaren prince akbar tasauka har tsakiyar gadon kwanansa daga gefensa, idanunsa na rufe hannunsa dafe da saitin zuciyarshi numfashinsa na sauka a hnkli, kansa ne ke tsananta ciwo,kukan wannan tsuntsuwa tasa yaji kusa dashi, bude idanunsa yyi a hnkli ya kalli gefen nasa ya hangota tana kada masa fika fikanta, tashi yyi zaune yana murmushi yasa hannunsa ya dauketa yana shafata, kafarta ya kalla yaga wata qaramar takarda a daure,hannunsa yasa ya cire takarda yana cirewa ta tashi firrrrr ta fice abinta don ta isar da saqonta, warware takardar yyi ya soma karantawa,be qarasa gama karanta abunda ke takardar ba ya sakko daga gadonsa da mugun sauri ya fice, ubaid kuwa na tsaye daga kofa yana ganin fitowarsa ya rufa masa baya, dokinsa ya hau ransa baqinqirin tamkar garwashin wuta, a wani irin sukawane ya dauki hanyar wannan babban kurku ubaid shima yana yana take masa baya, hk suka din ga qetawa ta cikin duwatsu da shuri har suka fara hango ganuwar kurkun, a

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment