Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fito jikinta sai rawa yake, kallonta yyi ya kalli karen sai ya bushe da dariyar mugunta ya nuna mata karen da hannu wai taje ta masa wanka, gaban mugun fad'uwa yake taje ta ciko ruwa a wani kwarmi tazo ta kama karen don taga maheer dab dasu, abun mamaki karen be kuma mata komai ba har ta gama masa wankan, tunda maheer ya shige building d'insa be kuma fitowa ba bare tasa ran ze bata abinci, yunwa takeji sosai ga dare yyi ba wurin kwanciya tana dai raku6e a wannan rumfar gezevon, tsirawa sararin samaniyya idanu tayi hawaye na zarya akan kumatunta, garin da hasken farin wata gashi kuma da yalwar taurari a sararin samaniyya tana takure wuri d'aya cikinta sai qugin yunwa yake,bata ta6a tsammanin a cikin larabawa akwai marasa imani da tausayi irin maheer ba, hk tayi kwanan zaune washegari babu k'arfi a jikinta sbd yunwa amma hk take ta faman 2aikace don tasan dole ne ma tayi ko kuma yana fitowa yaga ba tayi aikinta ba ya had'ata da karensa, maheer tashinsa kenan daga bacci ya kunna sigarinsa yana sha ya fito ya tsaya a barandar gaban building d'insa yana hangawa yaga abunda ba tayi ba ko wanda ya kamata ya qara mata, gani yyi tayi komai tunkan ya tashi ta gyara furanni ta basu ruwa sannan ta baiwa kifi abinci ta share farfajiyar wurin ta wanke masa qaramar motar hawansa tayi fes, komawa yyi ciki ya fito da wani farantin silver ya ajiye a wani wuri ya juye ragowar abincin dayaci ya rage jiya da dare sannan ya kirata ta taso tazo wurin dayake, nuna mata wannan abincin yyi yace ta dauka taje taci ta dawo da farantin wurin ta ajiye, tsugunawa tayi ta dauki farantin abincin ta wuce ta tafi ta soma ci duk da bata saba da cin irin cimmarsu ba amma hk take taci sbd yunwa, tana gamawa ta komar da farantin ta ajiye a wurin, toh tun daga wannan lkcin a wannan farantin yake zuba mata ragowar abincin idan yaci yage ya ajiye mata a wurin tamkar yadda ake zubawa kare ko sauran dabbobi abinci idan sun gani suzo suci hk itama idan taga ya zuba saita zo ta dauka ta tafi taci ta dawo da farantin ta ajiye a wurin wataran ma har abincin ya soma bushewa batasan ya zuba ba sai idan tazo ta duba ta gani ta dauka hkma kuma zataci ko yunwa ta kasheta a banza baida damuwa, yau hadari ne ya had'u sosai a garin ana sanya ran samun ruwan sama a kowanne lkci ita kuwa fargabar sakkowar ruwan take don tasan kwanan tsaye zatayi a wannan rumfar, cikin dare kuwa aka soma sheqa ruwa kamar da bakin kwarya tun ruwan yana feso mata har ya jiqa cikin rumfar gbdy, miqewa tayi ta tsaya a tsaye ta qanqame jikinta don sanyi ne ke shigarta sosai ga kuma ruwan dake fesowa cikin rumfar duk ya jiqa mata jiki,kayan dake jikinta duk ya jiqe shakaf kuma gashi su kadai gareta idan ma jiqewa sukayi hk zasu bushe a jikinta, wani lkcin idan sukayi datti sosai sai ta bari idan dare yyi dare saita tashi ta ciresu ta daura mayafinsu a jikinta ta wankesu ta shanya kafin asuba ta kwashesu ta maida jikinta, hk aketa sharara ruwa har da qanqara bimbii na tsaye qanqame da jikinta tana rawar sanyi sai gab da wayewar gari ruwan ya d'auke, ita kuwa bimbii ruwan daya jiqata ya sanya mata zazza6i sosai, tashi d'aya tana miqewa jiri ze d'ebeta ga tsananin ciwon kai, kuka take tana roqon Allah kar yasa zazza6in nan ya kayar da ita tana fargabar kar maheer ya fito ya tarar bata aiwatar da aikinta ba, jan jikinta ta somayi ta soma bawa furanni ruwa duk da ruwan saman da aka kwana ana sheqawa, jiri ne ya d'ebeta ta fad'i a wurin kanta yana wani irin sarawa, rarrabawa tayi ta koma gefe ta zauna tana maida numfashi tana son taji dama dama kafin ta kuma yunqurin miqewa, maheer ranar be fito da wuri ba sai yana building d'insa yana playing wani game, wanka ya shiga sannan ya shirya ya fito da niyya zuwa gaida mahaifiyarsa, abunda ya bashi mamaki shine yana fitowa ya tarar bimbii batayi ko d'aya daga cikin ayyukanta ba, makwancinta ya nufa ransa a mugun 6ace ya tarar ruwa ya cika wurin bata ciki, fitowa yyi ya duddubawa ya hangota jingine da wata qaramar bishiyar guiba dake qarshen gdn tana yashe a zaune tayi zaman dirshan, qarasowa yyi wurin batare da la'akari da yanayin da take ciki ba yasa hannunsa ya kamo gashin kanta ya watstsaketa da wasu lafiyayyun mari har uku sannan ya jefar da ita kanta ya bugu da bishiyar guiban sannan ya soma zazzage mata ruwan bala'i batare da digon tausayawa ga yanayinta daya ganta ciki ba ya umarceta data tashi ta kama aikinta, shiru ta masa taqi motsawa daga inda take bare yasa ran zatayi abunda ya umatceta, ranta yyi mugun 6aci take taji zuciyarta ta kangare koda kasheta zeyi ta sadaqar bata yin abunda yace, shi kuwa kallonta yake kawai da mugun mamaki don ya saba duk abunda yasata ba musu bare gardama zatayi amma yau dubi taurin kan da take gwada masa, hannu yasa ya cire belt din dake d'aure a k'ugunsa ya soma dukanta dashi tamkar Allah yyi masa wahayi, duk ya farfasa mata jiki amma be fasa dukanta ba ita kuma bata motsa daga inda take ba kuma ba tsillin hawaye ko qiris a idanunta, yana cikin dukan nata yayansa zayeed ya shigo gdn, wurin ya qarasa da sauri don shi kansa yasan zuciyar maheer idan har ransa ya 6aci zai iya aikata komai, jansa ya somayi yana qoqarin fizge belt d'in hannunsa shi kuma yana tirjewa, dakyar ya iya lalla6ashi ya shigar dashi cikin building d'insa yana cika yana batsewa yana kuma huci don ransa ya 6aci sosai gani yake bimbii bata chanchanci ta masa wannan taurin kan ba a matsayinta na qasqatacciyar baiwa kuma baqar fata shiyasa cikin zaqin dayake mata har yana ce mata gorilla family wai duk baqar fata dake africa daga family na gwagwggon biri suke she never deserve to behave like this cox she is nothing but gorilla family......zagi na uwa na uba hk ya dinga sauke mata kwando kwando yyi da larabci yyi da turanci, tun shigarsu ciki tana wurin bata motsa ba don batajin idan ta miqe tsaye k'afafunta zasu iya d'aukar gangar jikinta, sai lkcin taji saukar wasu hawaye masu d'umi a saman quncinta, kallon jikinta tayi taga yadda ya farfashe da duka sai kuma tayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,zayeed ne ya fito ya kalleta shima cike yake da fushi amma yana kallonta ya fahimci bata da lafiya shima dai ba wani daraja bayi baqar fata ke dashi a idanunsa ba amma dai yaji tausayinta kad'an, samo mata magani yyi ya bata ta amsa da godiya shiko batare daya saurari abunda take fad'i ba ya fice daga gdn yyi tafiyarsa, maheer kuwa ranar bak'in ciki kamar ya kasheshi hk ya kwana cike da qunci, washegari kuwa ya fito da sanyin safiya yaga ko batayi aikin nata ba don qiris yake jira da ita ya mata dukan da zata kusa ziyartar lahira sai kuma yyi rashi sa'a don ta gama kowanne da cikin aikin nata duk da rashi jin dad'in jikinta da take amma ba kamar jiya ba don maganin da tasha yyi mata amfani yau taji dama dama ba kamar jiya shiyasa tun safe ta lalla6a ta gama komai ta koma gindin bishiyar guiwa ta zauna, cike da haushi ya koma ciki ya kwanta akan doguwar kujerar dake qaramin parlourn nasa yana fitar da hayaqin sigarin dayake busawa,hoton bimbii ne ke dawo masa lkcin dayake dukanta, idanunta qamas suke babu alamun kuka, zumbur yyi ya miqe ya kuma fita ya tsaya a barandar dake gaban building d'insa yana hangota zaune a gindin bishiyar guiba tana tsefe kalbar dake kanta tana sake kitsa wata,ita kuwa batasan ma ya fito ba tana tsifanta tana rera waqar da take idan ta fita kiwo cikin harshenta na fillanci,juyawa yyi ya koma ciki ya shiga kitchen d'insa ya soma preparing breakfast a cikin kowanne tunaninsa bimbii ce ke fad'o masa ya ayyana mugunta daya dace ya mata,yana gama girkinsa ya zuba a wani plate ya fito wajen inda yake ajiye mata abinci ya juye mata, ita kuwa bimbii daman tun jiya babu abunda taci kuma yanzun ma bakinta babu dandano ko kadan bama ta sha'awar cin komai sai koko da qosai wannan kuwa tasan samunsa wurinta saidai ko a mafarki amma ba'a gaske ba, bata ta6a sanya ran ze zuba mata abinci ganin yadda suka kwashe dashi jiya kawai tana biyowa ta wurin taga ya zuba mata abinci, wucewa tayi bata d'auki abinci ba, shi kuwa duk bayan sakan guda sai ya leqo yaga ko ta dauki abincin daya zuba mata, hk kawai ya samu kansa da son yaga taci abincin amma har dare ya fito yadda ya zuba abinci hk ze gansa, shiru yyi yana tunanin ko fushi tayi sbd abunda ya mata jiya don ya fahimci kamar tana da zucciya, ita kuwa bimbii ta mance ma da batun abinci kawai lalla6a jikinta take don batason ta kuma kwantawa rashin lfy sbd gudun wulaqancin maheer, qunci da tsantsar bauta duk sun sauya bimbii ta koma wata irin miskila bata da fara'a kullum fuskarta a tsuke babu annuri ko kad'an, duk sanda maheer ya fito ze tarar tayi aikinta ta koma gindin bishiya, yauma yana fitowa ya tarar ta gama aikinta, kiranta yyi ta taso tazo juyawa yyi ya shiga cikin building d'insa ita kuwa ta tsaya a inda take don tasan bata da damar shiga wurin, juyowa yyi yaga tana tsaye bata biyoshi ba, saida ya kuma kiranta sannan ta biyo bayansa ta shigo ciki gabanta yana tsananta fad'uwa don batasan me ze mata ba ya kirata cikin wurinsa, parlourn nasa qarami ne amma yana da kyau sosai kuma ya wadatu da kayan more rayuwa, kitchen d'insa babu abunda babu na kayan amfani, kallonta yyi ya soma nuna mata wasu ayyuka da zata din ga masa cikin building din nasa ciki har da girki, itako bimbii binsa kawai take da kallo cike da mamaki toh yaushe ya sauya ra'ayi har ya amince mata ta din ga ta6a abunda zeci har ma da yarje mata ta din ga shigowa bangarensa tana masa 2aikace,tsawan daya mata ne yasa ta dawo cikin hnklinta, saidai itakam bata iya girki irin nasu ba toh me yakeson ta dafa masa ko irin abincinmu na gargajiyar baqar fata, dayake yanzu tana jin larabci sama sama don Allah ya mata kwakwalwa mai kyau da kaifin basirah,cikin harshen nasa ta masa mgn tace"nikam ban iya girki irin naku ba sai irin namu na baqar fata idan kana so kuma sai na mk" harararta yyi ya wuce yabarta a wurin tare da kora mata warning cewa duk aikin daya yanka mata ta tabbatar bata gocewa kowanne ba, washegari tana gama aikin furanni da baiwa kifi abinci ta nufi wurin building nasa, danna masa alarm tayi saida aka dan jima yazo ya bud'e kofar sanye yake cikin kayan bacci da alamu alarm din data danna ne ya tashe shi daga bacci, bece mata komai ba ya matsa gefe ya bata hanya ta shiga, komar da k'ofar yyi ya rufe ya koma bedroom d'insa ya kwanta, ita kuwa ta shiga kitchen d'in nasa ta soma wanke masa kwanuka,gani tayi wasu abubuwan ma dake kitchen din duk sunyi qura, hk ta wanke komai ta fitar da abubuwan da suka lalace a fridge ta gyara komai ta goge floor din yyi tas, tuni wuri yadau haske da annuri, fitowa parlourn tayi ta goge electronics d'in dake parlourn ta kad'e kujeru ta gyarasu sannan ta share ko'ina ta goge, ba tayi gigin girka masa komai ba don itakam bata iya irin girkinsu, har ta gama aikin nata maheer yana baccinsa baida niyyar tashi, bud'e kofa tayi ta fice tunda ta gama aiki nata ta koma gindin bishiyar guiba inda ta saba zama, tunda ta shigo gdn maheer bata ta6a leqa koda k'ofar waje ba kullum tana ciki tana aikatuwa, tana wurin a zaune taga shigowar wata mota qirar mercedez ta shigo farfajiyar gdn, wasu samari ne su wajen biyar dukkaninsu larabawa ne amma suna sanye ne cikin qananan kaya, wurin building maheer suka nufa, shi kuwa tashinsa kenan ya fito parlourn nasa, tsayawa yyi kawai yana bin ko'ina da kallo tamkar ba parlourn nasa ba ganin yadda floor din ke kyalli da d'aukar idanu ga komai a shirye tsaf, shelves na littattafansa a gyare tsaf duk ta kad'e qurar wurin, yana shiga kitchen ya kuma yin turus sbd komai na kitchen tamkar an maidashi sabo hattar oven d'in dake manne da gas d'in girkinsa cikinsa sai sheqi yake, tunda yake masu aikin dake kula da building d'insa be ta6a samun wanda yyi masa wannan aiki mai kyau hk ba, murmushi yyi kawai be damu ba duk da yaga dinning din dake kitchen babu komai wato bata girka masa komai ba amma shi aikin nata kawai ya birgeshi don shi a rayuwarsa yana son tsafta, alarm din dayaji ana danna masa ne yasa ya fito daga kitchen ya nufi wurin k'ofa ya bud'e, friends dinsa ya gani, dariya yyi ya basu hanya suka shigo, duk suka kame akan kujerun dake parlourn shi kuwa ya shiga kitchen ya soma qoqarin had'a musu tea, su kuwa suna parlourn sun kunna waqar Ali bin wasid suna chashewa da ita abinsu,fitowa yyi ya fita, tsayawa yyi a baranda ya kira bimbii dake gindin bishiya, tahowa tayi tazo wurin tana kallonsa, juyawa yyi tabi bayansa, tana shigowa duk suka bita da kallo suna kallon maheer, daya daga cikinsu yace" mah a ina ka samo mai aiki baqar fata kana nufin ita take maka abinci,God forbid" bimbii tana tsaye daga gefensa, murmushi yyi ya kalle friends din nasa yyi yace" oh guys calm down, she is just my cleaner" d'ayan kuwa yana hakimce a kujera tunda suka fara mgn be furta komai ba kawai bin bimbii yake da kallo tun daga sama har qasa,tsayar da idanunsa yyi kan k'ugunta wanda sai mutum ya mugun qura mata idanu ze gano girmansa don doguwar zumbulin rigar dake sanye jikinta ta taimaka wurin asirtashi, sake dire idanunsa yyi kan na shanunta dake tsaye dodar sukam tsinin tsayuwarsu ya fito ta rigar kuma data taka kad'an suke girgixa don ba bra a jikinta, masu yanci suke da arziqin sanya bra,murmushi yyi kawai tare da lumshe idanu ya komar da kansa ya kwantar jikin kujera yasa hannu yana shafa kwantaccen sajen dake gefen fuskarsa,maheer kuwa kallon bimbii yyi yace ta biyoshi kitchen, bin bayansa tayi tana shiga ta tsaya a gefe shi kuma ya soma had'a breafast, duk abunda yake tana kallonsa.......





Littafin nan na siyarwa ne ki siya kiyi karatunki cikin yanci,idan kin shirya siye saiki tura naira#300 ta wannan acct no.0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp 07041195806, idan kina buqatar wani bayanin kuma saiki kira wannan layin 08080611486





Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



4


Bayan ya gama komai akan idonta yace ta tafi, fitowa tayi daga kitchen d'in ta fito parlourn da niyyar fita, daya daga cikin friends nasa dake parlourn mai suna farid yasa hannu ya damqo hannunta yana murmushin qetai, qoqarin fixgewa take ta kasa maheer ya fito da cups na green tea a hannunsa, tsayawa yyi yana kallon farid da mamaki yace" ta maka wani abun ne koh" yace" No, but u said she is ur cleaner so i want her to clean my body" gbdy sauran abokan nasa suka bushe da dariya, shi kuwa farid murmushi kawai yyi, wani cikinsu mai suna jalil ya kalli farid yace" clean ur body as how,just make it clear" dariya yyi ya miqe ya soma 6alle ma6allan rigarsa ya cireta daga jikinsa ya kalli maheer yace" kace mata ina son tayimin wanka" maheer jin abun yyi wani banbarakwai ya kalleshi yace"wanka?" yace"yes,ko ba baiwa bace?" murmushi maheer yyi ya kalli 6angaren da bimbii ke tsaye don farid yyi blocking hanyar fitar, duk sauran abokan nasa suna daga zaune suna jiran maheer ya bawa bimbii umarnin yiwa farid wanka, shi kuma gashi baya son abokan nasa suyi zaton ko yana siding din bimbii ne don hk ya kalleta fuska a tamke yace" kije ki yiwa abokina wanka" kwalalo idanu waje tayi ta soma ja da baya tace" wanka zan yiwa wannan qatoton billah ban iya yiwa babba wanka ba" mgnr duk tana yine cikin harshenta na fillanci don bata gama kwarewa da larabcin ba, basu jin yaren nata amma yanayin yadda tayi ya tabbatar musu da gardama take baza tayi masa wankan ba, miqewa maheer yyi ya nufo inda take yace" yauma gardama zakiyimin" su kuwa sauran duk suna daga zaune suna dariyar qeta tare da qara zuga maheer wai lalle yyi sake baiwarsa bata bin umarninsa, kafin su ankara bimbii ta bud'e k'ofa ta fice da gudu, binta yyi da niyyar sakar mata kare ita kuwa Allah ya bata sa'a ta fice daga gdn gbdy, yana ganinta ta fita ya bita da gudu, ita kuwa tana fita ta miqe hanya tana ta gudu don wlh tsoro taji sosai gani take idan ta tsaya zasu iya keta mata rigar mutunci tunda har abun yakai ga hk, shi kuwa maheer gani yyi har ta masa nisa, komawa yyi gd ya kira masu tsaron hanyar data nufa kansu dakatar da ita baiwa ce take neman gudu, su kuwa sukace mata basu ganta ba, rikicewa yyi sosai lkcin da suka sanar dashi basu ganta ba, fita yyi da kansa yana ta zagayen neman bimbii amma ko mai kama da ita be gani ba, ita kuwa bimbii ba sanin gari tayi ba,tana cikin gudun tayi wata hanya data nufi outcast wato wajen gari,tsayawa tayi tana kalle kalle taga tabbas wurin da take wajen gari ne don ba mutane sosai, tana cikin waige waige ta jiyo qarar takun dawakai tana juyawa taga wasu mahaya dokuna ne su shida suna gwada tseren sukuwa sun nufo inda take gadan gadan tamkar basu ganin komai a gabansu, mugun firgita tayi ta soma qoqarin juyawa da gudu aikuwa tuni sun cimma inda take kafin kace kwabo daya daga cikinsu ya gwabjeta da gefen dokinsa, duk sukayi wucewarsu batare da sun tsaya ganin halin da take ciki ba don faduwa tayi a wurin, daga bayansu ashe akwai wasu dakarun mahaya dawakan dake take musu baya, shugaban wannan dakarun ne ya tsaya ya bada umarni a dauki bimbii dake kwance tamkar bata numfashi,su kuwa wadannan shidan da suka soma wucewa ya'yan sarakuna ne dake taqama da izzar jinin sarauta don kowannesu ya fito ne daga sananniyar masarauta me fada aji cikin daular larabawa, wannan wuri kuma filin tseren sukuwar dokunansu ne da suke fitowa duk qarshen mako don nishad'intar da kansu, hadimansu kuma na take musu baya tare da al'qalan dake fitar da gwanin daya cinye tseren cikinsu, suna isa madakata suka ja tunkan dawakansu suka tsaya, PRINCE AKBAR....shine ya samu nasarar cinye wasan tseren sukuwar dokin, sakkowa yyi da fuskarsa da babu yabo babu fallasa daga kan dokinsa, hadiminsa na hannun damansa ubaid ya kama masa dokinsa, sanye yake da wasu fararen kaya tamkar pakistan kansa sanye da rawani baki da fari, fari ne sol kallo daya zaka masa kasan cikakken balarabe, sajen daya zagaye fuskarsa baki ne ya taimaka wurin tona asirin kyan d'an sarkin,yanayin tafiyarsa da kallonsa kawai zai haska cikakkakiyar izzarsa, haqoransa a jere suke farare tas dasu duk wata halitta dake jikinsa fara ce idan ka cire gashin dake jikinsa da kuma kansa,gashin kansa dogo ne tamkar na mata har rawa yake idan ba rawani akansa,PRINCE AKBAR shi ya buge bimbii ta bashi haushi sosai daya ganta a hanyar sukuwar tseransu, ubaid ne ya matso kusa dashi yace" Your highness wannan alamunta ya nuna baiwa ce dake neman gudu" kallo d'aya yyiwa keken dokin da suka dauko bimbii yace" ku kaita cikin yan'uwanta bayi" abunda yace kenan ya wuce abinsa ya sake hawa dokinsa suka dau hanyar komawa gdn sarautar burham dake tsakiyar babban birnin kuwait........




*Masarautar Burham*🔱🔱

Ginin gdn sarautar burham shi kansa abun kallo ne don gini ne da kwararrun magina suka tsarashi cike da basira, gdn gari guda ne dauke da 6angarori daban daban tare da lambuka na shaqatawa da qoramai wanda ruwansu ke kwaranya, masarautar burham tsohuwar masarauta ce a qasar kuwait mai kafaffen tarihi, akwai arziki da tarin izzah ga jinin sarautar burham, sarki abdallah bin jabal shine mahaifi ga PRINCE AKBAR kuma shine riqe da sarautar wannan daular masarautar burham, sarki abdallah bin jabar mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi irinna larabawan farko ga taurin kan bala'i shiyasa har yau suke kan tsoffi al'adunsu a wannan masarauta, suna da tarin bayi da hadimai,rukunin bayin dake wannan gdn sarauta ya kasu kashi uku kuma dukkaninsu da alamominsu, bayin farko sune na qasa qasa masu kula da share share da gyare gyare da yiwa dawakai wanka, sai na biyu masu kula da bangarorin iyalan wannan gd, kaso na uku kuma sune masu kula da lfy da kuma abincin iyalan wannan gd tare da tsaftace komai nasu, prince akbar shine daya d'a ga sarki abdallah bin jabal sai kuma ya'yan wasu sarakunan dake qasan masarautarsu da suka taso cikin wannan gdn sarauta kuma kowanne cikinsu da 6angarensa da hadimansa tare da gayyar bayi, 6angaren prince akbar yafi kowanne 6angare girma da fad'i, akwai bayi na musamman dake hidimtawa 6angaren nasa sai hadiminsa na hannun damansa ubaid, ubaid yafi kowa sanin halin prince akbar kuma yana mutuqar masa biyayya baya sa6awa umarninsa, gdn sarautar burham sun dau bayi tamkar ba rayuka ba don laifi qanqani bawa ze aikata sarki abdallah ya zartar da hukuncin kisa akansa shiyasa bayin gdn kowa yake taka tsantsan da kaffa kaffa, idan har baka daya daga cikin bayin dake hidimtawa 6angaren sarki ko sarauniyya ko ya'yan sarki to kuwa baka isa ka shiga 6angarensu ba, kowanne rukuni na bayi akwai wanda ke shugabantarsu, idan aka kawo sabbin bayi akwai wacce ke nuna musu ayyukansu suna kiranta ummul shukri, bata da wasa ko kadan gashi ta iya horar da bayi yadda ya kamata a hannunta ubaid ya damqa bimbii,akwai doka sosai a wannan gdn sarauta, kafin a za6i bayi su hidimtawa sarauniyya ko sarki ko ya'yan sarki sai an tabbar da asalin bayin da kuma himmarsu, bayi marasa asali yawancinsu basu aiki a bangaren iyalan gdn suna aiki ne kawai a cikin gdn sarautar,fadar sarki abdallah bin jabal an ginata ne da danyen gwal kowacce kusurwa a fadar daukar ido yake, tsarin wannan gd shine bawa ya tsaya iyakar matsayinsa idan kuwa ya nemi ya qetare kai tsaye hukunci mai tsauri ze hau kansa, kafin su dauki bawa ya soma aiki a wannan masarauta sai ummul shukri ta gwadasu ta kowacce siga shiyasa suke kiranta uwar bayi.........
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




5



*Love is the unsoluble equation to a great mathematician and also a heavy weapon to hold for a great legends and heroes*......🔱🔱



Tana farfad'owa ta ganta kwance bisa busassun ciyayi a yashe tsakiya wani d'aki mai yalwar teburan katako da tsoffin kwabobi, gefenta wasu y'an mata ne su uku kyawawa dasu jinsin larabawa saidai alamu sun nuna tamkar suma suna da tambarin bauta tattare dasu, suna ganin ta farfado suka matso kusa da ita suna mata sannu cikin harshensu na larabci, dayake tana d'an fuskantar larabcin 2kadan sai ta d'aga musu kai kawai ita dai sai qarewa d'akin kallo take tana tunanin yau kuma ina Allah ya jefota, hannun suwa kuma ta fado, d'ayar da taji suna kira da khulood ta miqe ta

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment