Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kwance,komawa yyi bakin kofa ya tsay yana jiran lkcin tashinsa, yana jinsu amma akwai abunda ke damunsa ne kuma yake tunani akai shiyasa yakeson kadaici, saida ya dade a kwance sannnan ya tashi ya shirya cikin wasu fararen kaya hatta rawanin kan nasa shims fari ne sol, ubaid ne ya shigo ya tsaya a wurin kujerar da prince yake ya rissinar dakansa sannan ya dago yace" komai ya tafi yadda ya kamata" ita tana tsaye daga gefe abunda taji ubaid ya fada kenan, prince ya daga masa hannun alamar shikenan, sake rissinar dakansa yyi sannan ya juya ya fita ya tsaya a bakin kofa yana jiran fitowar prince, daukar wani qaramin box yyi mai kalar ja ya miqa mata, sunkuyawa tayi ta amsa box din, bece mata komai ba ya miqe yyi hanyar waje shima tabi bayansa da sauri, a keken doki aka daukesu suka tafi wurin taron, sarki abdullah bin jabal ne dakansa ya shirya wannan qasaitaccen taro wadanda ya samu halarta wasu daga cikin manyan sarakuna na wannan nahiya, taro ne na cikarsa shekaru hamsin da tara akan mulki, masarautar burham kuma tana da shekaru dari uku da sittin da uku da kafuwa, wurin taron ya qayatu da shiri na alfarma ga kuma jini na sarauta masu ji da kansu da taqama da cikakkiyar izzah ta sarauta duk suna hakimce bisa kujeru na alfarma, ko'ina ka hanga hasken farar fata kk gani suna mgn da yaren alfarma wato harshen larabci, bimbii dai tana bayan prince akbar dayake wani babban jigo a taron, ubaid kuma yana daga gefensa na dama hk suka rakasa mazauninsa ya zauna, wurin bimbii taga bayi dayawa wadanda suke baqar fata maza da mata amma yawancinsu qasqantattun bayi ne, gimbiya hindu na daga gefe tare take itama da wasu ya'yan sarakuna,ganin bimbii a bayan prince yasa abun ya bata haushi ta kuma shirya yadda zata toxarta bimbii a taron kowa ya shaida, kade kade ne ya soma tashi a wurin irin nasu na larabawa, prince akbar kuwa duk sakan daya sai ya waiga yaga ko bimbii na nan, ubaid yana lura dashi yyi mamaki sosai na ganin yadda babban prince ya damu da lamarin bimbii, yana lura da yadda yake yawan kallon bimbii hkn tamkar wanin baqon hali ne cikin halayyar prince din don yadda ya sani prince akbar yana da cikakkiyar izzar da baya yiwa abu kallo biyu musamman mace, macen ma baiwarsa, baiwar ma wacce suke kira mara asali jinsin baqar fata, taro yyi taro sai shagali ake da kuma shan shayi irin nasu na al'adar larabawa, gimbiya hindu ce ta tashi ta nufi wurin sarki abdallah bin jabal tadan rissinar dakanta kusa dashi tace" Allah yaja zamaninka sarkin masu adalci baqinmu na da buqatar babbawar baiwa ga prince akbar ta fito ta nishadintar dasu da waqoqi masu dadi don kwararriya ce a wannan fannin" murmushi sarki abdallah yyi ya juya ya kalli badakaren dake bayansa yace" ya sanar ana buqatar babbar baiwar ga prince akbar ta fito ta nishadintar da taron da salonta" batare da 6ata lkci ba wannan badakaren ma'abocin babbar murya ya soma shela cikin muryarsa data karade wurin,prince akbar yana jin wannan sanarwa ransa yyi masifar 6aci sbd bimbii babbar baiwarsa ce dole saida izininshi zata aiwatar da wani abu amma ganin daya yyi babban bawan mahaifinsa ne yake wannan sanarwa yasan umarni ne daga wurin sarki abdallah dakansa,shiru yyi don ba yadda ya iya, bimbii ko gabanta ne ya yanke ya fadi tana tsoron fita gaban wadannan bunqasassu masu fama da izzar mulki, wasu bayi ne suka xo suka mata jagora ta tafi dakin sauya kaya, kayan da suka bata ta sanya wasu shara shara duk qaurun kafafunta a bude suke ga cikin nata shima a wangale dakyar suka janyota ta fito don dagewa tayi bata fita hk, prince akbar na daga idanu ya hango wannan shiga dake jikin bimbii take ransa ya qara 6aci ya daure fuskarsa tamau,prince nasaar na gefe yana karantar yanayin prince din har lkcin da bimbii ta hau stage, tsayawa tayi sai kalle kalle take kafin zaqaqqiyar muryarta ta soma rero wasu baitoci.....




Littafin nan na siyarwa ne, kan naira #300 kacal, zaki tura ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screesht na payment ta whatsapp ta wannan layi....07041195806....




Alkalamin Bintuu ne....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



16

*The more I see you, my heart beat faster than I Imagine*.....so,you are my heart beat....💕



Idanun kowa a wurin yana kanta, lkcin ta soma rero baitocin dake cikin waqenta cikin karyayyen harshenta na diyan fillo dake fitar da luqqa na larabci mai dadin mutuqar dadin sauraro, waqa daya ta dauka cikin waqoqin larabcin da israt ta koya mata har da irin salon rawar waqar, rawan da ciki ake ana karkad'a k'ugu, toh abunku da masu ma'adanan kadawa gaba da baya tuni ta janye hnklin kowa na wurin da salon rawarta, k'ugunta take k'adawa cike da tsantsar k'warewa tana rero baitocinta da muryarta data gama kared'e wurin sbd zaqi, dayawa a wurin sun koma tamkar mutum mutumi sun zuba mata na mujiya, gimbiya hindu ranar ma hk ta din ga cika tana batsewa don ba hk taso ba, ita tunaninta bimbii waqar fillanci zatayi sbd ta toxarta ta a wurin a aibata harshenta tare da kalar fatarta, sai ga bimbii ta bata mamaki tayi waqenta cikin harshen larabci, juyi take sosai skirt din data saka mai batsa ne ta kasa yana hurawa, duk inda ake neman cika na mace toh bimbii ta qetare wurin, tana zuwa qarshen waqar ta sunkuya da qafa daya tare rissinar dakanta qasa ta musu hk da hannuðŸ™wurin ya dauki tafi sosai, shikanshi sarki abdallah murmushi yyi irin nasu na manya, prince akbar kuwa gbdy ransa a dagule yake ji yyi zaman wurin duk ya gundureshi, bimbii koh dawowa tayi bayansa ta tsaya bayan taje ta sauya kayan dake jikinta, prince nasaar shima takaicine ya ishe shi yadda yaga bimbii ta koma bayan prince akbar ta tsaya, wata baiwa ce wacce ke cikin bayin dake rarraba abun sha a wurin ta kawo ruwan inibi ta sunkuya tare da ajiyewa a gaban prince akbar sannan ta dauka ta tsiyaya masa a qaramin cup ta rissinar dakanta qasa tare da miqa masa cup din da hannu biyu, bimbii tayi sauri ta zagayo wurin ta zata amshi cup daga hannun baiwan nan, gani tayi baiwar taqi bata cup din sai miqawa prince take dakanta, kallon baiwar prince akbar yyi yace" ki bata itace keda haqqin bani abu naci" jiki a sanyaye baiwar ta miqawa bimbii cup din dake hannunta bimbii ta dan diga ruwan inibin a farcen dake babban yatsanta, duk suka tsaya suna mata kallon mamaki,yatsan nata ne yyi duhu sosai, juyawa tayi ta miqawa baiwar ruwan inibin data kawo tace" babban prince baya shan ruwa inibi" kallonta prince akbar yyi sannan ya kalli wannan baiwa dake tsaye sai kawai ya miqa mata hannu ta miqo masa cup din data tsiyaya ruwan inibi yakai bakinsa da niyyar sha, bimbii kuwa sai kallonshi take taga tabbas sha zeyi sai tayi saurin sanya hannunta ta amshi cup din daga hannunsa takai bakinta,gimbiya hindu dake kallonsu miqe tayi da sauri cike da tsan tsar mamaki, baiwa ta amshi abu daga hannu prince takai bakinta, hknne ya dauko hnklin mutane, prince akbar kuwa tsayawa yyi kawai yana kallon bimbii data shanye ruwan inibin dake cup din tas, kafin ta sauke cup din, ubaid ya dauketa da wasu kyawawan mari lafiyayyu guda uku,tana matsayin baiwa har ta samu yancin da zata amshi cup a hannun prince takai bakinta, wata irin fizga ubaid yakai mata ya durqusar da ita a qasa bisa guiwowinta, shi kuwa prince bece uffan ba kawai kallon bimbii yake, ita kuwa bimbii abunda yasa tayi hk shine tun tana rawa bisa stage idanunta yakai kan dan sarkin dulham wanda ake kira da prince amir shima ya bayyana a wannan taron, lkcin da baiwar takai masa nasa ta ajiye ta nufo wurin prince da dayan na hannunta ashe ita kanta baiwar bata ankara ba sa'adda prince amir ya musanya mata farantin da jug din da ruwan inibin da zata kaiwa prince akbar yake ya tura mata nashi wanda ta fara ajiyewa, ita kuma bimbii ganin hkn yasa tasan tabbas babu qamshin gsky kan lamarin, diga ruwan inibin da tayi a saman farcenta har yyi duhu shine ya tabbatar mata da akwai guba mai qarfi a cikin wannan abu don tun tana yarinya Allah yyi mata wannan baiwar, idan har akwai abu na cutarwa a abunda zataci idan ta sanya bisa farcenta tana ganewa, idan farcen nata yyi duhu toh abincin da akwai abun cutarwa a cikinsa,wannan dalili ne yasa ta hana prince shan ruwan inibi data ga kuma ya amsa ze sha shine ta amsa ta shanye ita,aikuwa tana wurin a durqushe kan guiwowinta idanunta suka soma gani dishi dishi, tsintsiyar hannunta tashi daya ta soma sauya launi zuwa kalar ja, basu ankara ba sai ganinta sukayi ta zube a wurin, zumbur prince ya miqe daga inda yake zauna ya nufo wurin da bimbii ke kwance ya tsuguna yakai hannunsa ze riqo tsintsiyar hannunta daya ga tayi jajir yana son tantance qarfin gubar dake jikinta, ubaid yyi saurin riqe masa hannu yace" ranka ya dade kar ka ta6a, guba ce mai qarfu zata iya shiga jikinka"sarki abdallah bin jabal kuwa dayake suna da dan tazara tsakaninsa da wurin da ya'yan sarakunan ke jera besan abunda ke faruwa ba saida hadiminsa ya matso kusa dashi ya rada masa abunda ke faruwa, saurin tashi yyi ransa a mutuqar 6ace, baiwar kuwa data kawo wannan ruwan inibi tashi daya jikinta ya soma rawa, ita dai har ga Allah tasan bata zuba komai a ruwan inibin ba toh waye ya mata hk, sarki abdallah bin jabal dakansa ya taso ya iso wurin yana kallon bimbii dake kwance ya kalli hannunta daya suntume tashi daya hkma wurin maqogwaronta, kallon hadimin dake bayansa kawai yyi shi kuma ya sunkuya da hanzari ze dauki bimbii ya fice da ita, prince yyi saurin dakatar dashi shi ya sunkuya da niyyar daukanta, tsawar da mahaifinsa sarki abdallah ya daka masa ne yasa shi janye hannunsa, akan idanunsa wannan hadimi ya sunkuya ya dauki bimbii ya fita da ita, ita kuwa wannan baiwa sarki abdallah ya bada umarnin tfy da ita dakin azabtarwa har saita bayyana wanda ya sanyata aikata wannan gangacin kan magajin masarautar burham, bimbii wani dogon daki aka kaita suna binciken irin gubar don bata magani, 6angaren wurin taro kuwa cigaba sukayi da taronsu batare da nuna kulawa ga abunda ya faru da bimbii ba sbd ita din baiwa ce, sarki abdallah yana da mugun ra'ayin riqau babu wanda ya isa yasa shi janye abunda yyi niyya shiyasa suka cigaba da gudanar da wannan taro tamkar babu abunda ya faru, prince kuwa kasa zama a wurin yyi ya sulale shi da hadiminsa ubaid suka bar wurin taron,suna fita ya kalli ubaid yace" kaje ka bincika inda suka kaita" rissinar dakai ubaid yyi alamar ya amsa umarni sannan yyiwa prince rakiya har 6angarensa sannan ya koma don binciko wurin da akai kai bimbii,prince kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye saikai komo yake da hannayensa a baya yana tunanin halin da bimbii ke ciki, zama yyi a wata kujera ya bude wani akwati ya fito da wata qaramar kwalba ta antidote na irin gubar dake jikin bimbii ya dora saman table din dake gabansa, bimbii kuwa gubar dake jikinta ba'a son ta jima a jikinta idan ta jima a jikin mutum tana illata dukkanin garkuwar jiki ne,sun bata magani amma har yanzu jikin nata beyi respond ga maganin ba, 6angaren prince kuwa ubaid ya kawo masa labaran dukkanin abunda ke faruwa da bimbii, cikin dare ya fice shima ya nufi sashin da bimbii, masu tsaron wurin suna ganin prince suka rissinar dakai tare da bashi hanya ya shige ciki, bimbii ya gani kwance bisa wani dogon gadon katako an lullu6a mata wani mayafi, hannun nata ya kalla da wuyanta yaga wurin ya qara yin jajir, batare daya sanya wata safar hannu ba ya kamo hannun nata yana kallo, kallon bayin dake kula da ita yyi yace su fita su bashi wuri, cikin sauri suka juya suka fice, handkchief dinsa fari sol yasa ya daure mata hannunta sannan ya fito da wannan qaramar kwalba ta antidote na wannan gubar ya bude bakinta ya tsiyaya mata ya jijjigata sosai har antidote din ya wuce zuwa maqogwaronta, qara riqo hannun nata yyi yana kallon wurin yaga ko mgnin zeyi respond har be ga wata alama data nuna jinkinta ya amshi mgnin ba, qura mata idanu yyi cike da sanyin ciki yasa hannunsa ya cire dukkanin awarwaron dake hannunta yasa a aljihunsa, gumi duk ya jiqa masa fuska sai qare mata kallo yake yana dana sanin gardaman daya mata da hkn be afku ba, 6angaren su israt da khulood kuwa sun sami labarin abunda ya faru da bimbii ranar dukkaninsu kasa bacci sukayi, sunyi kuka sunyi kuka har sun gaji, israt ta kalli khulood tace" shikenan mu kuma hk rayuwarmu zata cigaba da kasance kenan ,dubi abunda ya faru da layla yanzu kuma ga wata masifar ta kuma faruwa da bimbii duk a silar bauta" khulood ta kalleta tace" muma idan har muka cigaba da wanzuwa a wannan masarauta wlh qarshenmu bazai kyau ba, gwara mu cire tsoro kawai mu nemarwa kanmu hanyar gudu" kallonta israt tayi tace" abunda ya kamata kenan amma gwara musan halin da bimbii ke ciki tukun" khulood tace" hknne" prince akbar kuwa be bar dakin da bimbii take ba sai gab da asuba, saidai ya gargadi bayin dake tsaron wurin da wadanda suke aikin cikin wurin kar yaji kar ya gani, wato baya son wani ya fahimci a wurin ya kwana tare da bimbii, sukam mamaki ne ya cikasu na ganin duk girma da cikar izza na prince akbar yazo ya kwana tare da baiwarsa sannan ya nuna damuwa sosai kan halin da take ciki amma duk cikinsu babu wanda yasan ya bata antidote din nan, basu kawo komai ba saidai suna ganin yana nuna kulawar ne gareta don nuna halaccinsa ga sadaukarwar da tayi dominsa, sarki abdallah bin jabal kuwa baida masaniyya cewa prince yaje ganin wannan baiwa dakansa, wannan baiwa kuwa data kawo ruwan inibi tana nan ta azabtuwa amma har yanzu bata furta komai game da gubar da suke zargin ta zubawa prince a ruwan inibi............





Pls don Allah kuyimin afuwa kuyi hkr da wannan ba yawa...





Littafin nan na kudi ne kan naira dari uku kacal zaki samu damar karantashi, #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon screenshrt na payment naki ta wannan layin...07041195806.....




Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



17


*Every second my heart beat just cox of you*........I really care about you💕


Washegarin ranar an tashi ne da ruwan sama sosai kamar da bakin k'warya shi kuwa yana tsaye a dogon corridorn dake gaban 6angarensa sanye da wata farar rigar iyaka guiwa da wando shima fari, takalmin qafarsa irin mai laushin nan ne half cover, kansa babu rawani hknne ya bawa gashin kansa damar sakko masa har kafarsa, iskar daminan dake kad'awa sai hura gashin nasa take yana rawa, hannunsa dukka suna hard'e a bayansa yana kallon iskar dake kad'a ganye bishiyu da furanni da kuma ruwan dake sauka, yanayin tsayuwarsa kawai ze tabbatar mk da yana tunanin wani abu ne, ubaid ne yazo ya tsaya a gefensa tare da rissinar dakansa qasa sannan yace"binciken ya nuna gubar an hadata ne da dafin wasu kunamai da bamu da irinsu a wannan yanki namu yawanci an fi samu irin kunaman a yankin masarautar dulham suna amfani da dafin kunaman wurin hada abuwawa dayawa ciki har da irin wannan gubar"shiru prince yyi batare daya juyo ya kalli ubaid ba sai can yace" na bata maganin kashe qarfin gubar" yana fadar hk ya juya ya soma takunsa cike da izza ya koma cikin 6angarensa, zama yyi akan wata kujera ya bud'e wani babban littafi mai dauke da tsohuwar kimiyya ta larabawa game da ilimin sanin 2kala dafin kunama da maciji yana wani nazari, lenah ce tsohuwar baiwarsa ta shigo hannunta riqe da wani faranti azurfa sai daukar idanu yake da qananan cups a saman faranti, tfy take tamkar zata karye sbd da rangwada na salon jan hnkli, le6enta jajir da jan baki ga gashin girarta tayi sama zara zara a gyare, wuyan qafarta da wata sarqa mai kwalliya, hancinta ma da dan kunne dan mitsitsi, ajiye masa farantin tayi ta risssinar dakanta qasa sannan ta sunkuya ta soma tsiyaya masa black ginger tea din data kawo masa, shi kuwa tamkar besan ta shigo ba ya cigaba da karatunsa, qara rissinar dakanta tayi ta miqa masa cup din dake hannunta tana murmushi, sai lkcin ya dago dakansa ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa ya sanya hannu ya amshi cup din ya ajiye a saman table din, daga mata hannun yyi alamar dake nuni da baya buqatar komai wannan lkci ya maida kansa ya cigaba da abunda yake, ubaid ne ya shiga kai tsaye ya wuce inda prince ke zaune tare da rissinar dakansa qasa ya ajiye masa wata farar takarda akan table din dake gabansa, a hknli yasa hannu ya dauki takarda ya soma karantawa, takardar tana dauke da sanya hannun mahaifinsa sarki abdallah yana umartarsa yyi shirin raka sarki najash bin akhir wato sarkin dake mulkin masarautar dulham tare da dansa prince amir da sauran tawagarsu da suka zo taya masarautar murnar cika shekaru dari uku da sittin da kafuwa,zasu rakasu bakin bodar da zata fitar dasu daga yankin masarautar burham don tabbatarwa sun fita daga yankin burham lfy, qara kallon takardar yyi sosai sannan ya ajiye ya kalli ubaid yace" kun bincika sosai babu wata alama dake nuni da sanya hannunsu a sanya guban nan" ubaid yace" babu alamar data nuna hkn" shiru prince akbar yyi sannan ya fito da hatiminsa yasa hannu a takardar sannan ya miqawa ubaid ya rissinar dakansa sannan ya amshi takardar ya fita, miqewa tsaye prince akbar yyi ya nufi wurin 2sharan curtains din dake sake sun rufe window ya tsaya yana kallon farfajiya waje hannunsa dukka a baya, 6angaren bimbii kuwa cikin izinin Allah sai gashi ta bud'e idanunta, le6enta ya bushe sai bin ko'ina na dakin take da kallo, lkcin herbalists din dake kula da ita ta shigo ta tarar ta bude idanu, matsowa tayi kusa da ita tana mata sannu, daga mata kai kawai tayi sannan ta mayar da idanunta ta rufe, sunyi mamakin bude idon nata sbd daren jiya maganin da suka bata sam be nuna ya dauki jikin nata, su basu san cewa prince ne ya bata antidote nasa ba kuma shine ya mata aiki don ya kashe qarfin gubar kaso sittin cikin dari,prince akbar kam beso wannan rakiya da mahaifin nasa yasashi yyi ba, yana cike da tausayin bimbii yana ganin idan ya tafi yabarta hk kwance cikin ciwo tamkar be kyautawa sadaukarwar da tayi. dominsa bane amma babu yadda ya iya hk ya soma shiri, daren ranar yaso yaje duba bimbii amma hkn be samu ba don tfyr dare zasuyi, cikin daren suka dauki hanya dukkaninsu bisa dawakansu tare da rakiyar manyan dakarin tsaro,kwanansu daya da yini guda suka isa boda dasu sarki najash, prince amir kuwa babu abunda daya hadashi da prince akbar ko a hanya, dalili kuwa shine sarki abdallah shine sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa, shekaru ashirin da suka gabata sarki abdallah yakai harin bazata yankin dulham inda ta qarfin tsiya yacisu a yaqi ya kwashe matansu ya maishesu bayi sannan ya kama mahaifiyar prince amir ya kawota masarautarsa ya maidata kwarkwararsa, qarshen ita kuma baqin cikin hkn yyi ajalinta, wannan shine yasanya har ranar yau gabar dake tsakanin masarautun tana nan saidai kowa cikinsu ta bayan fage yake neman durqusar da daya musamman ma masarautar dulham, sarki najash da dansa prince amir sun shirya zuwa wannan taron ne kawai don cimma manufarsu,prince amir ya rantse sai ya qunsawa sarki abdallah irin baqin cikin daya qunsa musu suma hknne yasa ya shirya poisoning din prince akbar dayake magajin masarautar burham sbd yasan mutuwar prince akbar itace hanya mafi sauqi ta ganin bayan sarki abdallah don duk wani buri nashi yana kan babban prince,rashin samun nasarar hknne yake cin ransa har yanzu, bimbii kuwa cikin hukuncin Allah sun samu sun zuqe ragowar guban dake jikinta, tana soma dawowa cikin hayyacinta suka ce ta koma bakin aikinta, hk ta dawo dakinta bata tarar dasu israt ba ta hau gado ta kwanta, khulood da israt kuwa suna bakin qorama suna shan wanki har kusan yamma sannan suka nufo dawowa, suna shiga tamkar gixo suka ga bimbii kwance bisa gado, cikin saurin suka qarasa bakin gadon suna kallonta tana bacci, zama sukayi kusa da ita israt na mata fifita ita kuma tana bacci, sai wurin yamma ta farka ta gansu zagaye da ita, murmushi tayi musu tare da hadasu ta rumgumesu suma suka qara rumgumeta suna jajanta mata abunda ya faru, cikin dauriyya ta sauka tayi wanka ta shirya ta nufi babban kitchen su khulood na biye da ita, tana shiga duk bayin dake cikin kitchen din suka bita da kallon mamaki don basu da masaniyyar samun sauqinta tunda ance gubar mutuwa tasha, ta6e baki sukayi, dayar cikinsu ta kalli bimbii tace"daman baki mutu ba don mun ji ance gubar mutuwa kk sha" israt tayi zagal tace" gata nan bata mutu ba don mutuwar ba yar aiken uban wani bace balle ya turata ta kashe" kallon israt sukayi gbdynsu sannan suka sheqe da dariya, dayar cikinsu tace"toh kema kawai ki maida fatarki kalar nata mn saiku saje" khuood tayi dariya tace" wasu idan ana mgnr siffa maikyau su daina sanya baki wlh don farar fatar ce kawai gadararsu amma ba qira da zubin zati irin na mata ba" shiru sukayi basu sake mgn ba suka cigaba da aikinsu, israt da khulood na daga gefen bimbii ta gama jera kayan marmari a farantai masu mutuqar kyawu ta nufi 6angaren prince batasan cewa yyi tfy ba, kan hanyarta ta hadu da lenah ta fito daga 6angaren prince, shigewa zatayi ta wuce abinta, lenah ta bita da kallon mamaki sai tayi saurin shan gabanta tana huce don haushi taji na ganin bimbii ta samu lfy sbd ita aka bawa aikin bimbii ta cigaba da hidimtawa prince kafin bimbii ta samu lfy, kallon rainin ta yiwa bimbii tace"uban me ya tashi kafadunki baki mutu ba" kai tsaye batare da wani shakku ba bimbii ta bata amsa tace" ubanki mn" wata irin zabura tayi ta nufo kan bimbii da niyyar bata mari taji an riqe hannunta, juyawa tayi a fusace sai tayi toxali da ummu sumayya tace" haba lenah meyesa kk hk ko kin mance dokar wannan 6angaren ne, kina son a sauya miki 6angaren aiki ne" shiru tayi sai huci take tana kallon bimbii sannan tayi gaba da sauri tabar wurin, ummu sumayya ta kalli bimbii tace"idan 6angaren prince kk nufa toh baya nan yyi tfy" turus bimbii tayi ta kasa gaba ta kasa baya, ita kuwa ummu sumayya ta wuce tabarta a wurin, babban abunda ya bawa bimbii mamaki shine wato su wadannan mutane basu dauki bawa mutum ba shiyasa dukka da abunda ya faru da ita tayi ne don kare prince matsayinta na baiwar dake kula da hidimarsa amma yaci ace ko sau daya yaje ya duba halin da take ciki, amma sbd kasancewarta baiwa be damu kota mutu kota rayu ba tfy ma yyi abinsa yabarta cikin mugun yanayi, neman wani tudu tayi ta zauna tana tunanin gd, mahaifinta da innanta yadda suke nuna mata gata tamkar zasu maidata ciki, idan kuwa bata da lfy sun shiga damuwa kenan amma nan kuwa wasu ma ftn mutuwa suke mata, shiru tayi tare da zabga tagumi, tunowa da tayi dasu khulood shine yasa ta

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment