Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya a bakin kofa,prince da sumayya suka shiga ciki, saurin qarasawa yyi inda take durqushe riqe da mararta ya tsuguna ya riqo hannunta, sumayya na gefenta itama, kallon prince tayi tace" kamar haihuwa ce ta matso mata" saurin dago da kansa yyi yana kallon sumayya bece komai ba yyi saurin miqewa tsaye ya fita, ubaid yyiwa mgn sannan ya dawo ciki, gbdy gumi sai tsatstsafo masa yake tamkar shine yake labour din, a telephone ubaid ya kira gdn sarautan even kan suna buqatar royal doctor, bada jimawa ba even house suka turo musu da wata likita, baturiya ce ta shigo itama atleast bazata gaza shekaru hamsin ba, shigowa tayi da gudu da qaramin briefcase a hannunta, ubaid na ganin shigowarta yyi mata jagora har dakin da bimbii take ta shiga, prince na ganinta yyi saurin miqewa ya bata wuri, bude briefcase dinta tayi ta fito da handgloves ta saka cikin azama take gudanar da abubuwa, sumayya na taimaka mata prince kuwa, kasa cigaba yyi da kallon yadda bimbii ke shan azabar naquda yyi saurin ficewa daga dakin,ita kuwa bimbii wani irin ninshi take sbd ciwon da takeji bata ta6a jin irinsa ba tunda uwata ta haife sai yau, bayan ciwon naquda ga kuma wani azababben ciwon kai tamkar kanta ze rabe biyu,ita dai gbdy ta sadaqar da rayuwa sbd ta soma jiyo qamshin lahira,Dr.Margaret pushing nata take sosai, itama tana numfasawa da qarfi, prince yana bakin kofa ya harde hannayensa dukka a baya yana jiyo sautin ninshinta, idanunsa ya kada yyi ja shi kadai yasan me yakeji but still he looks very smart, cikin izinin Allah sai ga kan jariri ya fito, hannun doctorn tasa ta ciro jaririn ta miqawa sumayya dake gefe, jaririn kuwa ya charke musu da kuka, prince da ubaid kukan jaririn kawai suka jiyo,murmushi ubaid shi kuwa prince kawai so yake yaji yaya lfyr uwar jaririn, yana son shiga dakin amma yana daurewa, bimbii kuwa tasha wuya ba kadan ba gashi kanta be dena ciwo ba, hknne yasa doctorn tayi mata allurar bacci sbd ta huta, sumayya ce ta fita cike da farin ciki ta yiwa babban prince albishir bimbii ta sauka ta samu yaro namiji, sai lkcin ya shiga dakin wurin gadon da take kwance ya nufa yana kallonta tana bacci, kallo daya ya yiwa fuskarta yasan ta jigata ba kadan ba, doctorn da kanta ta dauki jaririn ta miqa masa tana murmushi, hannu yasa ya amshi jaririn ya tsira masa idanu, yaron fari ne qal gashi dogo masha'Allah, yanayin ga6o6in jaririn ya kalla yasan komai nasa ne, murmushi yyi sosai har fararen haqoransa suka bayyana, bimbii baccinta yyi tsayi sosai har kusan yamma bata farka ba, hkn ne ya tashi hnklin prince ita kuma doctorn sai kwantar masa da hnkli take sai dare ta tashi a razane, tana kallon inda take, fuskar da bazata ta6a mancewa da ita bane ta gani kusa da ita, kallonshi take sosai shima ya qura mata idanu, fashewa tayi da kuka ta dora kanta saman kafadan shi, kallonta yake cike da mamaki, ita kuwa all that past events da suka faru take tunawa ta sake dago da fuskarta tasa hannunta tana shafa face dinshi sannan ta sakko da hannunta daidai wurin da mahaifinsa ya harbe shi da mashi, hannunta ya riqe dukka ya janyota jikinsa ya kwantar da ita tana kuka a hnkli, yace" ki dena kuka baki ganin yanzu kin zama ummi" ya nuna mata babyn dake kwance a gefenta, saurin janye jikinta tayi ta komar dakanta ta kwanta ta rufe idanunta tana son tuna komai da komai ne, prince matsawa yyi kusa da ita yaja duvet ya rufeta, sunkuyawa yyi ya mata peck a kumatu, shiru tayi bata bude idanunta har saida taga ya fita daga dakin ta bude idanunta tana kallon babyn data haifa tana qura masa idanu,kuka take sosai tana tausayawa rayuwarta, tunani take yanzu idan qaddara ta kuma daukarta ta mayar da ita nahiyarta me zata fadawa su baffa da innah, tayi ciki har ta haife kenan bada igiyar aure ba, sosai ta kuma fashewa da kuka, sumayya ce ta shigo dakin ta ganta tana kuka tayi saurin qarasawa wurinta ta zauna kusa da ita tana rarrashinta da kalmomi masu kwantar da zuciya, prince komawa yyi side dinsa ya zauna ya dafe kansa, babban tashin hnklinsa mahaifinsa ne ya rasa ina ze dosa da wannan rayuwar, zuciyarsa fal take da tsantsar tausayin bimbii da babynsa dake tare da ita, har gobe yasan shine silar faruwar komai, tashi yyi da sauri ya koma dakin da bimbii take ya tarar da ita zaune fuskar nan nata babu alamar annuri, hannunsa yasa da niyyar kama mata hannu tayi saurin matsawa gefe ta dago da fuskarta tana kallonshi tace" kaga na haife muku jininku dake tare dani don Allah ku mai dani nahiyata na koma wurin iyayena na gaji da wannan rayuwar mara madafa" durqusawa tayi a gabansa ta daga hannunta alamar roqo tana kuka tace" don Allah ku maida ni nahiyata kar ka komar dani wannan masarautar na mahaifinka" shiru yyi komai ya daqule masa ya kalleta da jajayen idanunsa yace" kina son ki tafi ki barni kenan baki da damuwa, duk tsawon wannan lkcin dana dauka ina jiranki ki dawo gare ni kk dawo batare da kin iya shaida fuskata ba hk na kuma hkr har memory nk ya dawo kk gane ni amma abunda zaki iya fadamin kenan sbd baki dauki soyayyar da nk miki da daraja ba" kallonshi tayi tace" ranka ya dade ba wannan zaka duba ba, wannan son da kk fada tun farko na fada mk ze haifar da mtsl gashi silarta ne har rayuwarka ta shiga garari, mahaifinka dakansa ya harbeka da mashi duk silar wannan soyayya da kk fada don Allah kayi hkr ka taimake ni na koma qasata" wata uwar tsawa ya daka mata wacce ta sanyata shiga taitayinta, ubaid da sumayya dake waje su kansu sun razana da wannan tsawar da prince yyiwa bimbii, yace" kiyi yadda kkso" juyawa yyi ya fice ransa a 6ace sosai, bimbii fashewa tayi da kuka ita dai ta gaji da wannan rayuwar qasarta take son komawa don muguntar larabawan nan ya tsorata ta dayawa, basu dauki kisa a bakin komai ba, laifi qanqani sai su kashe rai batare da shakku ba, fushi sosai prince yyi da ita kusan kwana uku be sake shigowa inda take ba saidai sumayya ta dauki babyn takai masa duk safiyya da maraici, idan ya tuna abunda take fada wai ya maidata qasarta sai gabansa ya yanke ya fadi, tunani yake kar fa ya wayi gari ya rasa bimbii ta gudu tabar shi da dakon sonta, shi gani yake kamar bimbii ba sonshi take ba shine kawai Allah ya jarabta da soyayyarta, qanqame babyn dake hannunsa yyi yana kallonshi, idanunsa yyi ja tausayin kansa yake sosai, rana zafi inuwa quna, ta 6angaren mahaifinsa babu sassauci gata itama tana son ta gudu tabar shi, bimbii kam sai duk taji babu dadi fushin dayake da ita, tana zaune sumayya ta shigo ta sameta, kallonta tayi tace" kije ki bawa prince hkr sbd ranshi ya 6aci sosai dake tana mugun kafiya da zuciya bazai ta6a kallonki ba kar ki bari ya juya miki baya kece kadai macen da Allah ya dora akanshi" shiru tayi kawai tana sauraron sumayya, sai kuma tace"tohm" sumayya tace" ki same shi da dare a bakin teku nan yake zuwa duk dare" kallonta bimbii tayi tace" shikenan"da dare ubaid dakansa yyi mata rakiya har wajen teku, garin da hasken farin wata sosai, tunkan ta qarasa ta hango inuwarsa yana tsaye hannunsa dukka a baya ya qurawa ruwan teku ido, alamu sun nuna tunani yake mai zurfi, a hnkli ta qarasa inda yake ta tsaya a bayansa, shima ya hangi inuwarta kawai juyowa ne beyi ya kalleta ba, ita kuwa shiru tayi ta rasa abun fada, ta jima tana tsaye a wurin, juyowa yyi ya wuce ta da niyyar komawa gd, tana ganin hk tayi saurin qarasa kusa dashi ta sanya hannunta cikin nashi, tsayawa yyi chak ya juyo yana kallonta, cire hannunsa yyi daga cikin nata yyi gaba abinsa, da gudu ta kuma binsa ta rumgumesa ta baya ta qanqamesa da dukka hannayensa tana masa kuka tana bashi hkr, shiru yyi sannan ya juyo ya riqeta sosai a jikinsa duk sukayi shiru,hannunsu ta sarqe dana juna suka soma tfy a hnkli kanta na kafadarsa hannunsu na sarqe har suka qarasa bakin teku suka nemi rairayin suka zauna suna kallon ruwan teku, shiru sukayi saidai zuciyoyinsu na amsar saqonnin juna, muryarsa a hnkli cike da sanyi yace" har yanzu kina son ki tafi ki barni koh?" yanayin yadda yyi mgnr ta fahimci akwai rauni tattare da muryar nasa, dago da idanunta tayi tana kallonshi, daga hannunta tayi ta cusa a gashin kansa tana wargaza masa sumar kanshi, shikam binta kawai yake da kallo, cikin sanyin murya tace" bazan barka ba komai wuya zan kasance tare dakai" tsayar da idanunsa yyi kan fuskarta sai kuma yyi murmushi, nuna mata bakinsa yyi yace" kimin abunda zan so anan" sosai ta gane abunda yake nufi tayi saurin rufe ido ta 6oye fuskarta a saman shoulder dinsa cike da kunya irin nasu na fulani, shi kuwa dariya ta bashi yadan murmusa yace" kina son akbar?" sosai tmbyr tasa ta qara bata kunya, ta6e baki yyi kafin ta ankara sai ji tayi ta kwantar da ita a wurin rairayin shima ya kwanta ya dora kansa a saman qirjinta, dukka kansu na sama suna kallon hasken farin wata da taurarin dake watse a sararin samaniyya,hannunta ya kamo ya hade da nashi, ita kuma tana wasa da sajen fuskarsa da dayan hannunta, wannan yanayin da suke ciki ya kore musu duk wata damuwa ji suke tamkar su kadai ne a duniyar, tmbyrsa take abubuwan da suka faru dashi duk ya fada mata amma sai ya 6oye mata sanya shi a kurku da mahaifinsa yyi gudun kar ya qara mata karayar zucci, har dare ya shiga sosai basu sani ba suna nan kwance wurin, hadarin da suka gani ne yasa suka miqe suka soma tfy suna manne da juna suka nufi orchard house din da suke, kafin su isa ruwa ya tsuge sosai, hnklin prince ya tashi sosai sbd gani yyi bimbii ba wani kwarin jiki ne da ita ba ga danyen jego kar ruwan saman ya sanya mata zazza6i, itama dan qaramin hannunta ta daga wai zata kare masa ruwa amma tsayinta ya gaza kaiwa saman kansa sai dage take, dariya yyi, kallonsu tayi don ita wallah bata saba ganinsa yana dariya ba saidai murmushi,rawanin dake kafadarsa ya cire ya rufa mata amma duk da hk saida ruwa ya jiqasu, tfy suke kamar masu tausayin qasa a hk suka qarasa, dakyar ta iya kwace hannunta a cikin nashi ta shige dakin da take shima ya nufi dakin dayake, washegari, sun tashi ne da shirin komawa gd, bimbii dai gabanta faduwa yake idan taji an ambaci sunan masarautar burham, dukkaninsu suka shiga cikin jirgin ruwa tare da abram, bimbii fuskarta a rufe take kuma batare suke da prince ba tamkar ba tfyrsu daya ba sbd tsaro, sumayya tana rumgume da baby dayake cikin yalwatattun kayan sanyi, abram yana zaune kusa da ubaid, tmbyrshi yyi alaqarsu dasu bimbii, batare shakku ba ubaid ya soma bawa abram lbrin soyayyar dake tsakanin bimbii da prince mai cike da sarqaqiya da tarin qalubale, sosai wannan tsohon bayahude ya tausaya don lbrin nasu ya ta6a masa zuciya,hk har suka qarasa yankin masarautar burham, tunkan jirginsu ya iso dakarun masarautar burham suka iso don tararshi, lkcin da jirginsu ya iso fasinjojin jirgin suka soma fitowa, kamar yadda prince ya shirya tuni sumayya ta wuce da bimbii ta wani 6angare daban babu wanda zeyi tunanin tare suke da prince, bimbii fuskarta na rufe cikin niqab, sumayya tana da wayo shiyasa yaseer ya hadosu da ita, yadda prince ya umarceta ta wuce da bimbii qasarban wani asirtaccen gd ne da babban prince ke zuwa shan iska yana nesa ne sosai da masarautar burham,bimbii cike take da tunani kar wannan sarki mara imani ya ganota cikin yankinsa ya turo a kasheta ita da jaririnta,tuni tsoro da fargaba suka mata dirar mikiya...






Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp a wannan layin..07041195806...





Alkalamin Bintuu ne.....
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer



38


*I want to be with you even beyond for ever*......you are my destiny💕💕



Sun isa masarautar burham inda kai tsaye wasu hadimai suka wuce da abram inda akayi masa masauki,prince kuwa wucewa yyi 6angaren mahaifinsa ya same shi yadda dai yabar shi, sarauniyya na zaune gefensa, sarki abdallah yana daga kwance idanunsa na kallon prince akbar, tabbas prince yana cike da tausayin mahaifinsa bisa halin dayake ciki, baya iya mgn har yanzu kawai saidai yana bin komai da idanu tamkar ba sarki abdallah bin jabal ma'abocin cikar izzah da qarfin mulki ba, prince ya labarta masa yadda abubuwa suka kasance tsakaninsa da sarki abu ansar da kuma haduwarsa da abram, batare daya iya cewa komai ba sai kawai murmushi daya bayyana a saman fuskarsa, hkn ya nuna yaji dadin bayanin da prince yyi masa, sarauniya ta kalli prince tace" tashi kaje ka huta don kana buqatar hutu" miqewa yyi ya rissinar dakansa alamar girmamawa sannan ya juya ya fice daga turakar mahaifin nasa, 6angarensa ya wuce ubaid na take masa baya, suna shiga suka tadda bayin dake 6angaren sun jeru sunyi layi don tarbar babban prince, suna ganin shigowarsu duk suka rissinar dakansu har ya shigesu ya wuce 6angarensa, ubaid ne ya dawo ya tsaya a saman corridorn dake 6angaren ya sanar dasu babban prince ya dawo lfy kuma yana kowa fatan alheri sannan ya umarcesu kowa ya koma bakin aikinsa,yana zaune sanye da wata farar riga ta shiga wanka lenah ta shigo, sanye take da wata doguwar jar riga, hannunta yasha tsiraran awarwaro ya cika mata hannu,bisa al'adarta qafarta daure da sarqar qafa, qarasowa tayi inda yake ta tsaye tare da rissinar dakanta qasa alamar girmamawa sannan ta dago dakanta ta wuce da sauri ta shige dakin wanka ta hada masa ruwan wanka mai dumi a cikin kwarmin wanka tasa sinadaran wanka sannan ta fito ta sake rissinar dakanta qasa tayi gefe ta tsaya, wuce ta yyi ya shige dakin wankan, washegari, tun safe abram da prince suka bayyana a turakar sarki abdallah bin jabal, abram kallon sarki abdallah kawai yyi yaga yanayin yadda jikin nasa yyi, dago idanu yyi ya kalli sarauniya mar'atussaliha dake tsaye gefe yace" ina buqatar ku bani lkcin nan da kwana uku nayi bincike akan gubar" tace" an baka amma ka tabbata kayi bincike maikyau don mu nan bamu son kuskure" sunkuyar dakansa yyi alamar girmamawa ga wannan sarauniya sannan ya fita, sarauniya ta kalli babban prince tace" kana ganin akwai alamun nasara tattare da wannan bayahude, kasan fa mutane abun tsoro ne bani yarda da kowa ya duba mahaifinka sai cikakken amitacce sbd muna da maqiya dayawa masu neman ganin bayan wannan masarauta" murmushi babban prince yyi yace" ranka ya dade wannan bayahude baida wani niyya mara kyau ki duba kwayar idanunsa zaki tabbatar da hkn" murmushi tayi ta shafa kansa cike da qauna tace" madallah da wannan jarumin d'a nawa mai tsananin kaifin basira tabbas ina alfahari dakai" murmushi shima yyi ya miqe tare da rissinar dakansa ya fice, komawa yyi 6angarensa yana son ziyartar qasarban don duba lfyr bimbii da gudan jininsa saidai yana shakkar hkn don ko qaqa baya son wani ya gano bimbii na raye har ta haife cikin dake jikinta sbd tsaro, ubaid ya buqaci gani ya shigo da sauri ya iso wurinsa tare da rissinar dakansa qasa yana sauraron umarni,kallonsa babban prince yyi yace" meye tunaninka da ziyarar da nkson kaiwa qasarban" shiru ubaid yyi yana tunani sannan ya dago dakansa yace" yakai ma'abocin hikima tabbas har yanzu duk wani motsinmu akan idanun masarauta yake kuma ko yaya ka fita ziyartar wani wuri a yanzu zasu iya tunanin wani abu wanda hkn zesa su sanya masu binciken sirri su soma gudanar da bincike" jinjina kai yyi alamar gamsuwa, ubaid yace" duk wani kulawa tana samu ita da gudan jinin burham dake tare da ita, kuma nasa cikakken tsaro daya dace" kallonsa prince yyi yace" madallah da wannan amintaccen hadimi" rissinar dakai ubaid yyi saida prince ya daga masa hannu ya ja da baya sannan ya juya ya fice, jinginar dakansa yyi a kujerar dayake zaune yana tunanin qalubalen dazai fuskanta zuwa gaba kan wannan batu don masarautar burham na da tsauri sosai bisa jagoranci mahaifinsa sarki abdallah bin jabal, yana daga cikin tsaurin wannan masarauta basu amfani da maganin bature komai a gargajiyance suke yinsa suna kan al'adun iyaye da kakanni wato larabawan farko, bimbii tana qarqashin kulawar sumayya tana bata cikakken kulawar data dace, gudan jinin burham kuwa yana cike da kuzari sam be dauko bimbii a komai ba yyi gadon larabawa ne, yau suna kwance cikin dare yaro ya soma kuka sosai yaqi yin shiru, daukansa bimbii tayi tana ta jijjigashi ko zeyi shiru amma yaqi yin shiru kuma yaqi karbar nono yasha, kukan shi sumayya taji tayi hanzarin shigowa dakin a rikice tana tmbyr bimbii abunda ya same shi, bimbii tace" nima gani nayi ya fara kuka yaqi yin shiru" hannu tasa ta amshi jaririn tana kallonshi, jikinsa taji yyi zafi alamun sun nuna zazzafi ne a jikinsa, ruwan dumi ta hada ta sanya shi ciki sannan ta bashi mgnin zazzafi, saida ta jima dashi cikin ruwan dumi sannan ta fito dashi ta goge shi ta sanya masa kaya masu taushi,hkn data masa yasa ya tsagaita da kukan har bacci yyi gaba dashi, washegari, kwana ukun da abram ya diba ya cika, sai yamma abram ya iso akayi masa iso ga sarauniya ita kuma ta wuce dashi turakar da sarki abdallah ke kwance, anan suka tarar da babban prince yana tare da mahaifinsa suna sauraron qarasowar abram, batare da 6ata lkci ba abram ya fito da wasu tsinkaye masu kaifin gske ya ajiye gefe, tare da wani farin ruwa, dago dakan sarki abdallah yyi ya bashi wannan ruwan dake cikin wani gora yasha sosai sannan ya sanya wannan tsinken daya a bakinsa ya fito masa da wani abu kamar dan wuya ya ajiye a cikin wani qoqo hk ya cigaba dayi har ya gama, wata qaramar kwalbar ya fito da ita da wani ruwan magani a ciki ya sake bashi yasha sannan ya goga masa wani mai mai kyalli a dukka sasssan jikinsa, prince da sarauniya kuwa suna daga gefe suna kallon abunda wannan bayahude yake, miqewa yyi ya kalli sarauniya tare da rissinar dakansa qasa yace" ranki ya dade na gama sai mu saurara mu ga yadda jikin nasa ze amshi mgnin, gubar dake jikinsa baquwar guba ce wacce ta fito daga nahiya mai nisa wato nahiyar baqar fata, nayi nasarar gano antidote dinta ne sbd na ta6a krt yanayin wannan guba, idan har jikin nasa yyi maraba da wannan antidote toh daga gobe alamar hkn ze soma bayyana" murmushi sarauniya tayi tace" idan har nasara ta tabbata lfyrsa ta dawo kana da kyakykyawar kyauta ta musamman idan kuma muka ga akasin nasarar tabbas fushi na ze tabbata akan ka" murmushi abram yyi ya sake rissinar dakai sannan yaja da baya ya fice,dukkanin wanda ke wannan masarauta kawai tsumaye yake yaji ya lfyr sarki abdallah bin jabal har tsawon kwana daya da yini jikin sarki abdallah be nuna wata alamar na sauyi ba, cikin izinin ubangiji a washegari sai gashi ya soma miqewa zaune dakansa, wannan cigaban da aka samu a lfyr sarki ba qaramin farin ciki yasanya sarauniyya ba, saidai sarki abdallah da batun auren babban prince da gimbiya qifdiya ya bude baki,hkn yasa prince yyi shiru, cikin kwanaki uku jikin sarki abdallah ya warware ya dawo yadda yake tun farko, sarki abdallah bin jabal yyi farin ciki da wannan lfy daya samu tuni yasa aka kira masa wannan bayahude wato abram har fadarsa, abram na shiga wannan fada ta sarki abdallah bin jabal da aka ginata da danyen gwal ya zube gaban sarki yyi gaisuwa, murmushi sarki abdallah yyi yace" yakai wannan masani ma'abocin kimiyya da tarin sani tabbas nayi farin ciki da wannan ingantaccen magani nk don hk ka fadamin buqatarka gareni kowacce iri ce nayi maka alqawarin cika maka ita batare da wani 6ata lkci ba,zan faranta ranka kamar yadda ka faranta min" fadar sarki abdallah tayi shiru kowa na sauraron jawabin dake fita daga bakin sarki kuma suna sauraron suji buqatar wannan bayahude ga sarki abdallah, prince na tsaye gefen mahaifinsa shima yana sauraro, abram dago dakansa yyi ya kalli sarki abdallah sosai yace" yakai wannan sarki ma'abocin qarfin mulki da magana daya ina da buqata mai qarfi a gareka duk da ina da cikakken sani kan halayyarka ta cika alqawari da tsayawa kan mgn daya amma duk da hkn ina da shakka bansan ko zaka iya cikamin wannan buqata tawa ba don tana da qarfi" wannan zance na abram ya sanyawa kowa tunani shin wanne bayahude kuwa wacce buqata ce dashi hk dayake wannan batu, jikin sarki abdallah yyi sanyi da jin wannan batu na abram don shi tunaninsa wannan bayahude buqatarsa bata wuce dukiya, shi kuwa dukiya kowacce iri yakeso ze iya mallaka mishi batare da yasan yyi wani abu ba don yana da qarfin arziqi, prince shima a nashi 6angare mamakin abram yake yana tmbyr kansa shin wanne bayahude wacce buqata yake da ita a wannan masarauta tasu da har yake fadin tana da qarfi, kallonsa sarki abdallah yyi yace" ka fadi buqatar taka naji kai tsaye" shiru abram yyi yana shakkar fadin wannan buqata tashi kar wannan sarki yasa a masa kisan gilla, daka masa tsawa uxair yyi yace" yakai wannan bayahude ba'a yiwa sarki shiru ka hanxarta fadar buqatarka don sarkinmu ma'abocin alqawari ne da mgn daya kowa ya shaida" ajiyar zuciya abram yyi ya numfasa sosai sannan ya dago dakansa ya kalli sarki abdallah bin jabal dake hakimce a wata kujera ta alfarma mai ruwan zinare yasha alkyabba baqa da rawani mai baqi da fari, duk da sarki abdallah ya cika masa idanu amma hkn ya bude yace" yakai wannan sarki buqatar da nk nema gare ka itace ka yarje auren prince akbar da tsohuwar baiwarsa daka yankewa hukunci kisa sannan kayi aikin gafara a garesu tare da sanya musu albarka su da gudan jininka da yanzu hk wannan baiwa ta zama silar zuwansa duniya".....fadar yanayin rudani da daya bayyana a fuskokin al'ummar dake wannan fada yafi gaban kwatance, prince akbar kuwa mutuwar tsaye yyi, sarki abdallah bin jabal kuwa qurawa abram idanu yyi da fuskarsa da babu alamun annuri, jin zciyarsa yake kamar zata tsago ta fito sbd tsananin 6acin rai, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, prince gabansa mugun faduwa yake duk da tarin jarumtarsa yana masifar shakkar mahaifinsa, wannan yanayi da abram ya gani ne yasa tsoro da tarin rudani hade da firgici ya bayyana a fuskarsa,jikinsa rawa ya somayi sosai, miqewa sarki abdallah yyi yayi ya soma takawa a hnkli masu tsarinsa suka take masa baya yabar cikin wannan fada batare daya furta komai ba,sarkin hukunci yaba dakarun dake fadar umarni su kama abram su wuce dashi dakin horo don koyar dashi darasin harshe.......








Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 a wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,saiki tura screenahrt na payment naki ta whatsapp ta wannan layi......07041195806..........





Alkalamin Bintuu ne......
9/26/20, 7:47 PM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔



Written By Bintuu Seer




39


*I feel a lot about you darling*........My blood circulate in your blood,yeah, our love has an identity, I adore you💕💕



Qaramin kurku suka kai shi kafin sarki ya yanke masa hukunci dakansa, prince kuwa zuciyarsa a hargitse ya koma 6angarensa, ubaid ya kira yace" ka samu amintacciyar baiwa

2 Comments On DAREN GOMA SHA HUDU
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

I want to read the novel

avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Replying to abubakar-sunusi

Click The READ THIS NOVEL button

Please Login or Register in order to submit comment