Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RAI BIYU Complete Hausa Novel Document by RAI BIYU


RAI BIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 145556



RAI BIYU

Reading Time: 12 Hours

Added On: 05, Sep 2024

Author: Khadeeja Candy ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : ‪+234 803 588 3279

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 746.1 kb

File Type: txt

Views: 1019+

Download: 2278+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: [11/10/2019, 1‪+234 803 588 3279‬: *RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy

This Novel Is Free. But After This Free Book, Comes Payed one.

1⃣


“Bana son na yi aure a gidan da za'a saka min gadon dubu ɗari biyu da hansin su riƙa girmamani suna ganin girman da ganin mahaifina yana da rufin asiri, na fi son na yi aure gidan da za'a saka min gadon miliyan uku su dinga ganin mahaifina talaka ne suna raina min wayo. Ma'ana dai har yanzu ina kan bakana na auren mai kuɗi fiye da talaka!”

Na yi dariya ina sauraren zance ko burin Jidda da ta saba nanata min a duk lokacin da muke zancen aure da ita.

“Ƙawata ba za ki taɓa ganewa ba, kin fiye maida zancena shirme Wallahi Nawwara rayuwar nan ɗa muke sam bata dace da mu ba”

Dariya na sake yi a karo na biyu kana na dube ta irin duban na nake mata a duk lokacin da nake son ta ɗauki zance na muhimmancin.

“Kina da yawan buri Jidda kamar yadda nima nake da shi, sai dai duk da haka na ki be kai nawa ba, gwargwadon rufin asiri Jidda kuna da shi, amman kina tsawwalawa rayuwarki akan son aure mai kuɗi, ba ko wane kuɗi ba ne na halak, ba ko wane mai kuɗi ba ne bane mutumen arziki, da da yawanzu basa darajanta talaka basa ganin girman iyayen matansu, basa kunyar taka kowa saboda suna ganin suna da kuɗi.

Wasu masu kuɗin maneman mata ne Jidda, ke da kike matarsu sai su wulaƙantaki musamman idan suka sa ke ɗin ba kowa bace, nafi sha'awar auren takala ɗan'uwana mai ilmi da ganin ƙimata, mutumen da zai taimake ni na gyara lahira ta, kuma na inganta rayuwar yaro na, ya mutunta iyayena ko da bayan raina, ni iya wannan ya wadatar da ni matuƙar yaƙar yana da halin da zai iya ciyar da ni”

Jidda ta dafani a lokacin da ta lura da hawayen da ya sauko daga idona ba tare da sani ba har sai da ta yi min magana.

“Share hawayenki Nawwara, nasan abunda kike ji, amman rayuwar nan da muke ciki ne bata da daɗi, ka tashi cikin talauci ka girma a haka kai ma kana son sauyin rayuwa, kana son ka taimaki iyayenka, karatu nan ma fa Nawwara ba zai yiyu ba idan babu kuɗi, idan baka da kuɗi kai ba kowa ba ne, yadda aka ga dama haka ake takaka, babu mai son takala sai Allah”

Na yi murmushi ita kuma ta amsa kiran da Mahaifiyarta take mata ta tashi. Na san yadda ƙawata take ji haƙiƙa rayuwar talauci babu daɗi, sai dai ni har yanzu rayuwar masu kuɗi bata burgeni saboda nasan yadda take, ba ko wace ƴar takala ce ke auren mai kuɗi ta jidaɗin rayuwaba, ko da kuwa ya aje mata banki ne a cikin ɗakinta.

“Kin gani ko kullum baƙin tuwon dawa sai na masara babu wani sauyi, ni Wallahi rayuwar nan ta isheni, ni ina tausayin rayuwar yarana idan nayi aure zasu tashi suna cin tuwon dawa duk suyi baƙi, ke Wallahi Nawwara da kwana ɗari da talaka ƙara kwana ɗaya da mai kuɗi”

Jidda ce take wannan maganar, yayinda take dire kwanon samira mai ɗauke da ƙatowar mulmular tuwon dawa da miyar kuka, agabana.

‘Allah sarki rayuwa ku har kun samu tuwon dawa’

Na faɗa a raina, a fili kuma sai na ce.

“Aifa sai ki yi mitarki kuma ki ci tuwonki dan ni dai a ƙoshe na ke”

Jidda ta wara ido tana min kallonta na iskanci wanda ta saba min a duk lokacin da aljannun rashin mutunci suka hau kanta.

“Maman Nura, Maman Nura yi sauri ki zo”

Nayi saurin kai hannu ina rufe mata baki jin tana kiran mahaifiyarta, nasan wata ƙulalliya zata ƙulla min.

“Jid”

Ban yi furucin ba sai ga Maman Nura a cikin ɗakin wato mahaifiyar Jidda.

“Maman Nura tace gida zata je da shi”

Jidda ta faɗa sai Maman Nura ta ce

“To bari a ƙara mata”

Da sauri na ce.

“Wallahi ƙarya take min Mama, ban ce ba”

Juyowa ta yi ta watsa min wata uwar harara kamar zata zo ta fanɗareni da mari, kana ta nuna ni da yatsanta.

“Kin gani Nawwara wannan halin naki yana ɓata min rai, kina rage ƙima idona, ko abu kika tarar a gidan nan ba zaki ɗauka ki kai gida ba, ni da Mamanki ba ɗaya ba ne ko? Allah wata rana sai na ƙwaɗa miki mari idan kina min irin wannan iskanci, fitsarriya”

Ta juya a fusace ta fice. Ni ko na kaiwa Jidda duka.

“Kin haɗa ni da ita kin jidaɗi”

“Ai nasan idan ba haka na yi miki ba, ba za ki co shi ba, marar mutunci, ni idan naga abu a gidanku tambaya nake ba ɗauka nakr na tsire ba”

Na girgiza kai ganin yadda take magana da tsire baki.

“Allah ya shiryaki Jidda”

“Amin Wallahi, idan Allah be shirya ni ba ai na shiga tara bama uku ba, Jidda ai sai Nawwara”

Bayan Maman Nura ta ƙaro min tuwon na taso Jidda ta rakoni ƙofar gida, a lokacin ana kiran sallah magariba. A bakin ƙofar gidansu ta karɓe tuwon.

“Kawo zan bawa Nura ya kai miki, kinga su idi can ƴan sa ido, ko Sallah ba zasu tashi su yi ba”

Ta taimaka min matuƙa, domin nima kaina ina jin kunyar fitowa da kwano a wani gida saboda ƴan sa'idon unguwa masu zaman kashe wando, zaman ƙirga atamfarki da kuma inda zaki je ki dawo. Sallama nayi mata tare da sai da safe sannan na kama hanya, bayan nayi nisa sai na hango Nura tare ɗauke da kwanon tuwon, sauri na ƙara dan bana son ya cin ma, nasan halin Nura zai iya cin min a hanya ya ce karɓi tuwonki.

Lokacin da na shiga gida har sai da na ɗan tsaya a bakin ƙofa jiransa, tuƙuna ya ƙaraso na karɓi tuwon yana mita ya juya ya koma, ni kuma na shiga gida ina doka sallama.

“Amin wa'alaikissalam Nawwara”

Ya faɗa yana aje butar da yayi alwala, sannan ya ɗauki tsohon rediyonsa da ke aje ya miƙa min.

“Shiga da wannan ɗaki”

“Tau Baba, Allah ya tsare”

“Amin, Amin”

Ya faɗa yana kallon kwanon tuwon da ke hannuna, kamin yasa kai ya fice.

A ɗaki na samu Inna ita da Habiba da Sakina, da mai sunan mama, wato Jamila da muke kira da Ummi.

“Wai Allah na”

Na faɗa ina ƙoƙarin zama kusa da Inna.

“Nawwara kin dawo?”

“Eh ga tuwon dawa Maman Nura ta haɗo ni da shi”

“Tau Allah ya saka mata da alheri, zuba ki ci tun safe rabonki da abinci Nawwara”

Na tada kai na kalli Inna.

“Ai ni matuƙar zaku ci, ko ban cin ba bana jin komai, amman idan na ci ku kuna jin yunwa hankalina ba zai kwanta ba, Habiba zuba ma Baba da Inna sai ku cinye sauran”

Inna ta ce

“Sai fa kin ci, ai ƙara su ma ɗazu Babanku ya samo naira hansi na basu suka siyo garin kwaki suka saka gishiri suka ci”

“Habiba zuba min kaɗan, ina Noor wai?”

Na tambaya ganin baya cikin ɗakin.

“Na aike shi ya samomin batir gurin Hajara wai mu samu na haskawa a fitila anjima”

Cewar Inna, ni kuma na amsa da

“Okay”

Tare da unƙurin tashi na cire hijab domin alwala. Ko kamin na yi alwala na gama, har sun cinye tuwon abun ka da masu jin yunwa.
Bayan na gama Sallah Magariba Habiba ta miƙo min ɗan tuwo can laƙe ga kwano.

“Gashi nan ke da Noor”

Karɓa nayi na aje a gabana. Sai ga Baba ya shigo yana faɗin.

“Bari naje gidan ciyaman na jirashi, ko Allah zai na samu wani abu, sai mu karya da safe”

Wani abu naji ya zo ya tsaya min a zuciya, wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da Babanmu zai je yawon maula. Ina jin lokacin da Inna ta ce

“Allah ya tsare”

Habiba kuma ta ce


“Baba ga tuwon dawa”

“Ina aka samo tuwo?”

“Nawwara ce ta samo gidansu Maman Nura”

“Ku cinye, sai na dawo”

“Allah ya bada sa'a”

Da Amin ya amsa, sannan ya fice. Ni ko na aje carɓin da ke hannuna, na miƙe tsaye ina amsa sallamar Noor.

“Momy a ci abinci gidan Maman Hajara, tace na faɗawa Mama Habiba ta zo ta ɗauki tuwo, Momy har da kifi a miyarsu”

Duk dariya muka sa masa, daman Noor be iya cin daɗi ba, komai ya ci sai ya bada labari. Yasa hannunsa aljihu ya ciro batir ɗin ya miƙawa Inna, sai ya sake saka ɗayan hannunsa a aljihu ya fiddo kifi ɗan tsito ya miƙa min.

“Momy ungo na rage miki, ci ki ji”

Kai na girgiza masa.

“Cinye abun ka nima zan je can na ci”

“Yarinya ya ƙare ai”

“Ni ce yarinya?”

Na tambaya ina nuna kai na, sai ya sa dariya yana tsalle. Haka rayuwarsa take ba duk abu ne yake damunsa ba, ko da bai fahimcin inda duniyar ta dosa ba ne oho.



______________________________________

As i said bayan ZAGON K'ASA zan yi RAI BIYU kuma free. 😍

How do you like my surprise 🤔
*RAI BIYU...♥️🖤*


Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RAI BIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album