Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

NIHAAD Complete Hausa Novel Document by NIHAAD


NIHAAD

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 72798



NIHAAD

Reading Time: 6 Hours

Added On: 23, Aug 2023

Author: Khaleesat Haidar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07087865788

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 364.82 kb

File Type: txt

Views: 17978+

Download: 8380+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: ο»Ώ πŸ’–πŸ’– *NIHAAD* πŸ’–πŸ’–


By Khaleesat HaiydarπŸ“–βœπŸ»


~



All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar hankali da arziki me amfani, Allah ya saka maki da gidan Aljanna, πŸ‘πŸ» my special greetings to my own Barrister KH, Allah ya jibanci lamarinka, ya kara bude hanyoyin arzikin da xa ayi ma addini hidimaπŸ’– and My lovely aunt Rukayya Allah ya raya su Lil Khaleesat ya kara maki kwanciyar hankali.. And then my fans, i am who i am as a result of u guys, i love you all for the support always, Allah ya baku farin cikin duniya da na kiyama.... As usual support ur writer and may God bless u.



Tun da ta ji furucin wan Abbanta na karshe ta sakar masu kuka me karfin gaske, ta kalli Mahaifiyarta dake goge hawayen dake sauka idonta, babu alamar dai xata ce komai, Ta kalli Abba da fuskarsa ke hade tamkar hadari, shi ma bata samu courage din ce masa komai ba, yayyinta maza biyu dake parlon babu wanda yace komai cikinsu, ta dinga kuka da shesheka ta kalli Umma warce tayi tagumi, kallon Kakarta dake girgiza kafa tayi cikin rawan murya ta kamo hannunta tace "Don girman Allah kice su yi hakuri sharrin shaidan ne, don Allah kice su yafe min, ni ban san wanda yayi min haka ba..." Kakar ta warce hannunta tace "Ja can, Ke har kinsan sharrin shaidan alhalin kece shaidaniyar Nihad, ai kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu kunyata ki, ki ce lalle ke sai kin xama mutuniyar banxa abinda kaf xuri'a babu? Me yake burgeki da rayuwar 'ya yan iska har wannan abu ya same ki haka?" Kuka kakar ta saki tace "Allah mun gode maka, ka haifi Ι—a ne kawai baka haifi halinsa ba, yanxu meye wannan kika mana Nihad" Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta fice daga parlon, direct dakinta ta nufa don tasan ko me xata ce a parlon nan babu wanda xae saurareta, tunda har Umma ma ta ki cewa komai to babu wanda xai ce komai, bayan ta shiga daki ta sa makulli ta fada kan gado tana rusa kuka kamar ranta xai fita, is this actually happening to her? yanda ta ga rana haka ta ga dare, gashi ta kasa sallah ko da raka'a daya ne, gaba daya ta fice hayyacinta, she wish all this is nothing but a dream, she wish xata farka taga mummunan mafarki kawai take, da asuba aka murda kofar dakin ta daga idonta da suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi ta bude, har aka gaji da Knocking aka bar wajen. Sai wajen karfe takwas na safe tana xaune saman darduma ta jawo wayarta da kyar, rabonta da wayar tun shekaranjiya, gaba daya bata son abinda xai hadata da wayar ma balle xuciyarta ya kara rauni, yanxun ma da ta dauko sim card dinta take son cirewa ta karya, missed calls da ta gani ya doshi hamsin, da messages da ya ninka calls din, ko wani message xance daya ne content dinsa, "Is that you on social media Nihad?" "Nihad what came over u?" "Nihad what is happening?" "Nihad something is wrong somewhere, ur Video is all over the internet" Fita tayi daga Inbox din hawaye me xafi na sauka idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da videos... Kashe wayar tayi ta ciro sim card din ta karya kamar yanda tayi niyya sannan ta jefar da wayar saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, wayyo ina ka xata farka taga mafarki kawai take da gaske, tun shekaranjiya take wish din nan, amma taki farkawa wanda hakan ke kara tabbatar mata da gaske ne duk abinda ke faruwa, babu wani xancen mafarki, Knocking din kofa aka yi, ta kalli kofar sai kuma ta mike a hankali ta nufi kofar ta bude, Umma ta gani tsaye, nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Umma ta shigo dakin ta kulle kofar, Nihad ta bi ta da kallo har ta xauna gefen gado, Nihad ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace "Umma don girman Allah ku rufa min asiri kar ayi min haka, wllh xan iya mutuwa, talk to Abba plss" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "It's too late Nihad, tun da har Alhaji Abubakar ne ya yanke hukuncin nan kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasa, ke dai naki addu'a, mu ma kuma muna nan muna taya ki da shi, it's okay to make mistakes as long as we learn from them, so ki kwantar da hankalinki everything will be alright, kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya shiryesa" Ta rushe da wani kuka cikin tashin hankali take cewa "Na shiga uku Umma, yanxu baxa ki iya ce ma Abba komai ba? auren dole fa xa su min, Umma ya xan yi da raina idan hakan ya faru, na shiga uku na..." Mikewa Umma tayi ta nufi kofa ta fita ta kulle. Compound Umma ta fita ta tarda Abba dake xaune shi kadai kana ganinsa kasan yayi nisa a tunanin da yake, ta nufesa ta ja daya daga kujerun dake wajen ta xauna tana kallonsa da damuwa karara fuskarta, he looks so disturbed also, ta kwantar da murya tace "Damuwa ba shi ne mafita ba Ranka shi dade, kayi hakuri ka sa ma ranka salama, Allah ne ya tsara haka, sai mu gode masa mu kara gode masa kawai" Abba ya numfasa yace "I think aurar da Nihad yanzu ba shi ne mafita ba Sumayyah, amma Engineer da Hajiya baxa su fahimci hakan ba, she is just 19, ga kuma wannan abu da ya faru, ta ina xata fara xaman aure bata gama mallakan hankalin kanta ba? da xa su sake shawara da ni da na ce masu gwara kawai ta tafi waje ta karasa karatun ta a can, ko da Uk ne...." Umma dake ta kallonsa tace "Wannan gaskiya ne, aurar da Nihad is not a way out, amma ni dai shawarata kar ka tofa naka a issue din nan Yallabai, duk yanda Yaya yayi da Nihad dai dai ne don 'er sa ce, kuma ran Hajiya xae 6aci idan ka bijiro da wannan batun na taje waje tayi karatu, gani kawai xa su yi kana ma goyon bayanta ne, naka kawai ido sannan kayi mata fatan alkhairi duk yanda suka yi da ita er su ce, kuma baxa su yi abinda xai cuceta ba, tunda suka ce aure mu xuba masu ido duk yanda suka yi dai dai ne, shawara ta biyu kuma kada ka kuskura Yaya yace xai hada Nihad da daya daga 'ya yansa balle ma bana tunanin xa ayi hakan kawai in case xa a bijiro da wannan gaskiya ka nuna a'a, don in har aka yi hakan zumunci xae tarwatse kasan su waye 'ya yan nasa da iyayensu, yara ne masu ji da kansu wa enda ba sa rayuwa a kasar, don haka kar ka soma yarda... don walakantattciya xasu mayar mana da er mu, ni yallabai yanda video din nan nata ya tafi viral gwara kawai a samo wani da ba kowa ba, bawan Allah wanda ba ma shi da abun duniya, shi kadai xai iya aurenta ya rufa mata asiri su xauna lafiya ba tare da ya goranta mata wataran ba, bai kuma walakanta mana ita ba, kyau ace ma a karkara yake rayuwarsa yallabai" Abba ya daga kai yana mata wani kallo babu ko kiftawa, tace "Atoh Allah ya baka hakuri, ka samo wani d'an senator ko Attajiri ka hadasu kawai, hakan ma dai dai ne...." Tana kai wa nan ta mike ta ce "Allah ya rufa asiri, ya tsare yan baya" Daga haka ta bar wajen, Abba ya dafe kansa. Umma ta saka Abba tunani iri iri bayan ta bar sa a wajen, ta wani bangaren she is damn right, abinda ta fada gaskiya ne, babu wanda xai yi ma tayin Nihad ya amsa da farin ciki ko dadin rai, Nihad is nothing but a disappointment to him, bai taba xaton hakan daga gareta ba kuma yayi da ya sanin fifitata da yayi cikin duk 'ya yansa, yayi da ya sanin nuna mata so karara da yayi kan sauran 'ya yan sa, amma Alhmdlh tunda abinda tayi ya tsaya iya haka, shawaran da Umma ta basa kuma shi xai yi amfani da... Mai gadi ne ya bude gate jin ana horn, Abba ya bi motar da ta shigo compound din da ido har yayi parking, yana xaune aka samesa cikin ladabi ya...


Read / Download NIHAAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

9 Comments On NIHAAD
avatar
lawal-1

10 months ago

Reply

The book is not complete thank you

avatar
taskar

9 months ago

Reply

Replying to lawal-1

tuntubi wannan nambar 07087865788 don siyan complete na littafin

avatar
aishat-5

9 months ago

Reply

Gaskiya naji dadi book dinnan

avatar
taskar

9 months ago

Reply

Replying to aishat-5

Wow munji dadi da hakan

avatar
maryama-4

9 months ago

Reply

Is very fantastic Allah ya Kara basira

avatar
taskar

9 months ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryama-4

9 months ago

Reply

Allah ya Kara basira

avatar
taskar

9 months ago

Reply

Replying to maryama-4

Ameen

avatar
maryam-3-9-1

1 month ago

Reply

This book is so interesting

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album