Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHIM INA MAI FARINCIKIN SAKE HA'DUWATA DAKU MASOYANA ACIKIN WANNAN SABON LITTAFI NAWA MAI SUNA A SAMA๐Ÿ‘† TARE DA ROK'ON UBANGIJINA DAYA BANI IKON KAMMALASA CIKIN K'OSHIN LAFIYA DA AMINCI, WANNAN LITTAFI HAKK'IN MALLAKA TANE BAN YARDA WANI/WATA A SARRAFASHI TA WATA SIGA DABAN BA, YIN HAKAN KUSKURE NE KUMA LAIFINE, LABARIN DAKE CIKI GASKIYANE YAFARU KUMA YAKAN CIGABA DA FARUWA ACIKIN AL'UMMA DON HAKA IDAN YA DACE DA HALINKI SAI KIYI GAGGAWAR CHANZAWA FATANA SHINE DANI DA KE 'YAR UWA MUTARU MUGYARA DON KYAUTATA GOBEN RAYUWARMU A CIKIN ZAMANTAKEWAR AURATAYYA...INA KIKE QAWAR ARZIKI *SAINAH ABUBAKAR (UMMU MINAL)* DUKKANI WANNAN LITTAFIN DON FARINCIKIN KINE, INA ROK'ON ALLAH DAYA HA'DAKI DA ALKHAIRANSA ADUK INDA KIKA SHIGA๐Ÿ‘ INA SO KISANI BILLY S FARI NA K'AUNARKI HAR ZUWA LUMFASHINTA NA K'ARSHE, *MOM HAFSAT RANO, YA HAJJA CE, MOM HAFSAT XOXO AND MY LITTLE PRINCESS SALMAH ABALI* INA SO KUSANI DUK WANI ALK'ALAMI NAWA DA ZAN 'DORA WAJEN RUBUTU CIKE YAKE DA ALFAHARI DAKU TARE DA TSANTSAR K'AUNARKU FISABILILLAH!, BURINA ARAYUWA SHINE ALLAH YABAKU FARINCIKI MAI 'DOREWA ACIKIN RAYUWARKU HAR IZUWA AL-JANNAH FIDDAUSI๐Ÿ‘


๐Ÿ’ŽPage______1๐Ÿ’Ž


Wata 'yar kyakkawar yarinya ce mai yanayi da k'irar mutanen Japanis, wankan tarwad'a ce da baxa ta wuce 'yar kimanin shekara goma sha hud'u 14 da haihuwa ba. Ita na hango zaune akan matattakalar da zata sadaka da babban falon gidansu dake nan k'asa, ta buga uban tagumi hawaye na zubar mata a idanunta biyu, in ban da tunani da kukan bak'in ciki ba abunda take yi.

"Billy..!Billy..!!...Billy..!!!"

Ta jiyo muryar yayan tah mahmud yana kiranta, kyakkyawan saurayi ne d'an kimanin shekara 27 dake tafe daga abayanta yana kiran sunanta cike da shauk'in dake nuna tsantsar k'auna, shak'uwar dake tsakaninsa da ita, tsananin k'unci da bak'in ciki da suka tarar mata a zuciya yasa ta kasa amsa kiran yayan nata da take matuk'ar k'auna. Mahmud ya kasan ce shine babban d'ah acikin familyn alhaji Bashir mai furniture, yana da k'anne guda biyar uku mata biyu maza Batool, Bilkisu, Basmah, Bilal da kuma Bassam.

A hankali ya k'araso wajen ta tare da dafa shoulder d'inta fuskarsa cike da damuwar yanayin da ya ganeta a ciki yace.

"Sister me yake faruwa dake ne kika zo nan kina kuka, ko wani abun ne aka yi maki? fad'amun don ku 'YAN UWANA NE! bana son abunda zai tab'a mani ku"

Kallonsa Bilkisu tayi tare da kallon gefe gefensu taga babu kowa, turo labenta na k'asa tayi tana neman sake fashe masa da wani sabon kukan, da sauri Mahmud yasa yatsansa akan labbanta,

"Shiiiiii....bana son kukan nan sister, fad'amin waye ya tab'a min ke?" ya Karashe maganar yana mai goge mata hawayen dake neman gurbin zama a fuskarta.

"Yaya don Allah kafad'a mun wane laifi na yiwa small mom da ta tsaneni, ko ince ta tsane mu a rayuwar ta please yaya fad'amun me yasa take yi mana haka..?!"

"Ke Billy!..ba dai d'an na wane kika zaunar kina fad'a masa cewa na tsaneku ba, saboda iya makirci har kina fitar da wasu k'walla tsabar munafurci ko?"

Muryar small mom ce suka jiyo fitowar ta kenan daga bedroom rik'e da hannun bilal ta turo k'eyarsa tare da hankad'a shi har sai da ya fad'i k'asa tana fad'in haka,

Da sauri Mahmud ya k'araso wajen ya d'auke bilal dake k'asa yana kuka ya rungume sa a jikinsa ransa a b'ace yana kallon mahaifiyar tasa kamar zaiyi kuka, Bilkisu na ganin haka ta ruga aguje wajen mahaifiyarta don ta sanar mata,

"Haba mom..! fisabilillahi meye haka kika yi? yanzu d'an wannan yaro me yayi maki da kike neman saukar masa da b'acin rai shima?"

Mahmud ya k'arashe maganar had'e da kallon bilal da yayi lamo (kwance) a jikinsa yana shasshekar kuka, cike da masifa small mom take cewa...

"Banda iskancin yaron nan taya za'a yi yaje har k'uryar d'aki na ya watsarmin da kayan dake kan madubi na, gashi duk sun farfashe don tsabar k'eta da muguntar da aka koya masa shima.."

"Yanzu mom bilal d'in da iya karsa shekara uku yasan wata k'eta da mugunta?" kallon bassam dake gefen small mom yana dariya yayi tare da d'aukesa mari kawau!

"Hey.. stupid boy dariya ma kake yi min don ubanka? wallahi mom yanzu haka wannan shed'anin yaron ne yayi maki b'arnar kika yi zaton Bilal ne"

"Kai Mahmud bana son sharri da yarfe, bassam d'in ne zai fasa mani kaya? In banda kana shashasha taya zaka yiwa d'an uwanka sharri kaso bare kuma kafifita shi akansa?

"A'a mom sumafa 'YAN UWANA NE don me ba zan so suba?, idan har kince sharri na yiwa Bassam dake da shekara biyar ba zai iya yi maki b'arna ba taya zakice Bilal ne yayi mom? don Allah mom kidena yin irin wud'annan abubuwan bana so, Bilkisu da Bilal 'YAN UWANA NE ko kad'an bana farin ciki da abunda zai cutar mani dasu"

Yana rufe baki sai ga Ummi ta fito tare da Bilkisu biye da ita, murmushin k'arfin hali ta yiwa Mahmud ba tare da takalli inda mom d'insa take tsaye ba ta karb'i Bilal, cike da takaicin abunda mom tayi Mahmud yace

"Ummi kiyi hak'u...." Be k'arasa ba Ummi hak'uri ba yaji k'arar Bilkisu dake gefen ta, juyowar da zai yi kenan ya hango Batool rik'e da gashin kanta billy tana ja tama fad'in.

"Munafuka meye na zuwa ki wani kirawo Ummi sai kace kashesa aka yi? wallahi mom yarinyar nan taji bak'in hali, yanzu haka ma ita ta turasa ya fasa maki kwalab'en turare dake kan mirror, nikam ban san ya aka yi wud'annan mutanan suka zamo jinin muba, na tsanesu mom don nikam ba 'YAN UWANA NE ba...!"

A fusace Mahmud yayo kanta "Batool dama ba kida hankali? jinin namu kike cewa haka? to idanke ba 'yan uwanki bane ni 'YAN UWANA NE kuma don ubanki yau sai kin fad'amun ko 'yan uwan waye a gidan nan"

Belt d'insa ya cire tare da yowa kanta, sanin halinsa yasa ta saki Bilkisu ta ruga aguje tana ihu yana binta, ganin da gaske ya keyi yasa ta shiga k'eta ihu tana fad'in,

"Wayyo yaya don Allah karka dukeni da zafi wlh, mom kiceceni, wayyo na bani wlh yaya 'YAN UWANA NE su...!, YAN UWANA NE...!! su yaya, wlh na tuba suma 'YAN UWANA NE....!!!

Mahmud babban yaron Alhaji Bashir Mai funitures mutunen da yayi suna wajen rik'ongaskiya da amana yanada mata biyu da yara shidda ukku maza ukku mata yana matuk'ar kula da iyalansa yanda yakamata babu wani abu da zasu nema surasa indae aduniya ne haka kuma yana kwatanta adalci atsakanin matansa da 'ya'yansa yanda yakamata, Amma kash har yanzu abuguda ke damunsa, shine yanda matarsa kuma amaryarsa bata son a zauna lafiya wanda yayi iya k'ok'arinsa yasan ko meye dalilinta yagagara, lokutta da dama yakan tambayeta meyasa takeyin hakan sai tace masa Bakomai, Hajia Aisha itace uwar gidansa mace mai hakuri, juriya da kuma K'ana'a abu mafi burgewa atare da ita shine gaskiya macece kaifi d'aya Nata son munafurci arayuwarta shiyasa alhaji bashir KE matuk'ar k'aunarta aransa Sunyi aurena da ita bisa zab'in iyaye kuma sae Allah yasa akadace da suna k'aunar junansu sosae, Bayan sunyi aurena da shekara bakwae Hajia Aisha ko b'atan wata bata tab'ayi ba balle asa ran haihuwa mahaifin alhaji bashir ya auro masa 'yar amininsa mai suna hussaina, haka alhaji bashir yayiwa mahaifinsa biyayya yazauna da hussaina bisa amana badon yana Sontaba, Hajia hussaina macece mai son mulkar duk wani wanda take tare dashi kasancewar mahaifinta sarkine yana mulkar wani gari acan cikin birnin kano, ko kad'an tatsani taga fifikon wani akanta tanada matuk'ar izza daji dakai wanda sune suke
taimakonta wajen walak'anta natare da ita harma dana nesa, in kaga tana son mutum to tabbas yana bintane yana yimata yanda take so abunda Hajia Aisha Kenan takasa d'aukar mata shiyasa zamansu yakasa dai daita duk da kuwa mijin nasu na iya k'ok'arinsa.

Wata tara cikin na goma da kawo Hajia hussaina ta haifawa alhaji bashir 'yarsa kyakkyawa sosae Hajia Aisha tanuna farincikinta afili duk da ana kyararta akan yarinyar hakan besa tayi fushi ba takoma gefenta, Kwatsam ranar suna Alhaji bashir ya rad'awa 'yarsa sunan hajia Aisha sbd tausayinta da yakeji na bata haifa ba kuma yayi hakan ne saboda ya faranta mata kamar yanda take k'ok'arin faranta masa acikin dukkanin alamurransa,

Haka kuwa akayi Hajia Aisha tayi farincikinki sosai tare da yiwa mijin nata godiya tana kuka don tsabar jin dad'i,

Lokacin da Hajia hussaina taji sunan 'yarta ba k'aramin bakin ciki tayiba duk da soyayyar da akeyiwa Yarinyar hakan bai hanata fatar inama bata haifeta ba, kwanaki biyu da suna yarinyar ta koma sanadiyar Typoid data yimata mugun kamu, a maimakon Hajia hussaina tadamu sai tanuna ita k'arama da yarinyar takoma duk da ko tanajin radadin rashin 'yar tata azuciya, sosai Aisha tayi kukan rashin takwarar tata tare da fatar Allah yabasu wata mai albarka haka ta fannin alhaji bashir ya damu matuk'a da rashin yarinyar saboda son da yake yimata daga karshe dai duk suka tattara suka barwa Allah ikonsa, Bayan shekara d'aya hussaina tasake haifo yarinya kamarta sak da alhaji bashir amma cikin ikon Allah ko minti goma batayi aduniya ba itama tarasu, wannan karon kam Hajia hussaina tafi kowa shiga tashin hankali tayi kuka sosai rungume da yarinyar bayan tarasu halin d'ah da mahaifi saida akayi dagaske sannan akarabata da gawar yarinyar, bayan wash kwanaki Hajia hussaina ta fara b'ullowa da makircin wai Hajia Aisha ke kashe mata yara don ita bata haihuwa haka tabi dangin alhaji tana cewa ai asirine Hajia Aisha keyimata yaranta namutuwa don ita bata haihuwa, nan take Aisha tafara samun matsaloli da dangin mijinta ciki Kuwa hadda mahaifiyarsa dake matukar sonta, k'aunarsa k'waya d'aya kad'ai takejin sanyinta wato hafsat itama saboda jininsu ya had'u da ita tun kafin akawo Hajia hussaina tariga tasan halinta kuma tasan mezata iyayi da wanda bazata iya ba shiyasa bata shiri da Hajia hussaina ko kad'an,

Alhaji bashir najin suruttan dake yawo acikin danginsa wai Aisha nakashe masa 'ya'ya saboda ita bata haihuwa amma daidae da rana d'aya betab'a bari sukayi tasiri azuciyar saba, wannan abun ya matuk'ar k'onawa hussaina rae don haka tafara kukan wai Hajia Aisha tarigata shanye alhaji baya ganin laifinta dole itama ta tashi tsaye, wannan karon wata goma hussaina tayi bayan haihuwarta tasake haifo santalelen jaririnta kyakkyawa kamar ba ita ta haifeshi ba, kowa farinciki a fuskarsa baya misaltuwa Anata fad'in alhaji yasamu magaji, Aisha kuwa duk yanda taso taga yaron ta d'aukesa aka hanata acewarsu wai umurnin mahaifiyar alhaji ne tace kada abari ta d'auki yaron, ran alhaji ya matuk'ar b'aci akan wannan abun da akayi mata don haka ya riko hannunta suka bar d'akin tunda Aisha take bata tab'a kukan rashin haihuwaba sai yau...kuka maitsanani da ban tausayi tafashe dashi tana cewa

" _Ya rabbhi habli minasswaliheen_"

Cike da tausayawa ya rungumota

"Amin.... Aisha kiyi hakuri komai yanada lokaci insha Allah kema naki nazuwa"

Anan taci gaba da KIMANTA Tana tambayarsa metayi da Hajia tahana tadauki dansa jininsa shidae hakuri kawae yadinga bata tare da kalaman da zasu kwantar masa da zuciya aransa kuma yana jin rad'ad'in zafin kukan da Aisha keyi da kuma abunda akayi mata tun daga ranar yad'au alkawarin ko dukiyarsa zata k'are tun daga nan k'asar har zuwa k'asashen waje sae yakai Aisha an nema mata maganin matsalar data hanata haihuwa itama tahaihu, haka akaci gaba
da hidimar biki Aisha bata tab'a d'aukar jaririnta ba, ga wani irin maseefar son yaron da Allah ya azo mata ana gobe suna saega hafsat kanwar alhaji ta iso wajen buki da yake acan borno tayi aure har da yaranta biyu shiyasa bata samu isowa da wuriba.

Nan yayan nata ya zayyana mata abunda hajiya tace da yake shima bayada abokin kaiwa kukansa ko shawara sai ita kasancewar tanada hankali da tsinkaya gashi itace auta ad'akinsu.

Cikin b'acin rai tace "haba yaya wlh kabani mamaki yanzu don sunce haka Saeka biye masu tanaji tana gani jininka yayi mata wahalar d'auka da gani to wlh tun daga hussaenar har zuwa munafukan dake tare da ita basu isaba" Cike DA isa tabar falon nasa tanufi d'akin hussaina ko kallon wud'anda ke wurin batayi ba ta d'auko jaririn
tafitowarta dashi Tana hucin tab'ani inka isa, Kai tsaye tashiga dashi d'akin Hajia Aisha dake kwance akan gado tunanin duniya duk yabi ya isheta ta kwantar dashi dai dai fuskarta had'e da cewa

"Ga d'anki nan nakawo maki kigani kuma kid'aukesa injini babu wanda zai hana"

Rungumesa Aisha tayi cike da soyayya tana tofa masa addu'o'in kariya fuskarta d'auke da farincikinki tamkar ance yazama nata, man hafsat tayita bata hak'uri da fad'an tacirewa kanta damuwa komai yanada lokaci, sosae Aisha taji dad'i tayi mata godiya, alhajine ya shigo d'akin yana kallon yanda Aisha tayi kyau da jaririn a hannunta yace

"Masha Allah kema Allah ya kawo maki naki rabo mai albarka"

Duk suka amsa da amin

Anan hafsat tacewa yayanta ta rad'awa yaron suna mahmud sae kuma akaci sa'a da sunan mahaifin Aisha kenan shiyasa takarajin son yaron aranta har take kiransa da babana.

Tunda aka haifi mahmud hussaina bata sake haihuwar saida ya shekara goma da wata biyar sannan hussaina ta samu ciki ta hafo 'yarta har lokacin Aisha na shiru bata haihuba sun karad'e duk wasu kwararrin asibitotan dake k'asarnan amma ba'a dace ba, Ranar suna aka rad'awa yarinya Basmah.

Ba'ajimah da haihuwar basmah ba wajen aikinsu Alhaji aka turashi k'asar Egypt yayo couse d'in shekara biyu hakan yasa yafara tafiya da Aisha shima saida akayi daru da hussaina kafin ta amince ai kuwa suna isa Alhaji yamaida hankali sosae wajen kai Aisha asibitota ana duba lafiyarta, duk da haka dae ba'a dace ba har shekarar ta k'are bayan sun dawo kuma saega hussaina tafara laulayi lokacin basmah nada shekara d'aya da wata biyu da haihuwarta don haka tacireta ga nono,

Alhaji yaso barin hussaena gida ya komawarsa shikad'ai tunda cikin nabata wahala ga kuma k'aramar yarinya agabanta abun zai zame masu lalura idan yatafi da ita don haka sai yayi tunanin yabarta gida, Aishace ta nuna masa illar da abun zai haifar k'ara yatafi da ita inyaso itama ya kaita asibiti har tasamu lpy nan yake tambayarta to ya zayayi jinyarta ga basmah da batayi wani wayo ba, Murmushi tayi tace idanka amince itama momynsu ta amince to kubar babanah da basmah awurina insha Allah zankula maka dasu kafin kudawo, koda alhaji yafad'awa hussaina cewar za'abar mahmud da basmah hannun Aisha k'in amincewa tayi saeda yanuna mata idan har bata amince ba toshi ba inda zaije da ita tazauna gida saboda bazae iya kwasar yara yaje dasu wata qasaba gashi ita da zata kula dasu batada isassar lpy sannan ta amince badon ranta yaso ba.

Bayan tafiyarsu hussaina qaddara Egypt Aisha ta rungumi yaran hannu biyu kamar ita ta haifesu suna samun kula da tarbiya awajenta sosai, watansu biyu da tafiya kwasam Aisha tafara ciwo tana zuwa asibiti aka tabbatar mata da cewa tana d'auke da juna biyu d'an kimanin wata hud'u sai taji abun kamar a mafarki saboda lokacin shekararta goma sha tara da wata bakwai kenan bata haihuba, saida Aisha taje kusan asibiti biyar saboda ta gasgata cewa tanada ciki ana tabbatar mata da cewa tanada juna biyu sannan tayadda, tayi farinciki sosae don har da kuka tayi sannan tayita yiwa Allah godiya da ni'imar da yayi mata, hafsat tafara yiwa albishir ita kuma tace takama bakinta karta fad'awa kowa sai dae idan yafito agansa hatta yayan nata cewa tayi kar tafad'a masa sae inya zo mata nan da three months yaga kyakkyawar tarba, haka kuwa akayi saeda yazo yaganewa idonsa, tsabar farinciki har d'aukarta yayi kamar k'aramar yarinya yana dariya tare da yiwa Allah godiya daya nuna masa wannan ranar, Lokacin da labari yaje kunnen hussaina ba k'aramar tsanar Aisha tak'araji aran taba, itadai Aisha tazame mata qadan garen bakin tulu gashi dama hausawa nacewa _hasada ga mai rabo taki ce_

Bayan wata biyu hussaina tahaihu tahaifi 'yarta da aka rad'awa suna Batool bayan sati uku itama Aisha ta haifo santaleliyar 'yarta da akasha buki bidiri taci suna Bilkisu, daga lokacin hussaina tasake dage damtse wajen karfafa k'iyayyar da take yiwa Aisha da ganin cewa sai taraba Aisha da alhaji, amma da yake Aisha ta rik'e Allah sosai babu abunda yafaru da ita,

Bayan haihuwar Batool da Bilkisu saeda hussaina tayi haihuwa uku yaran basa zuwa da rai kafin tasake samun wani cikin lokacin su Bilkisu nada shekara takwas da haihuwa tahaifi d'anta aka rad'a masa suna Bassam,

Bassam nada shekara uku da haihuwa sukuma su Bilkisu nada shekara goma sha d'aya Aisha tasamu ciki ta haifi d'anta Bilal ganin yanzu Aisha nada yara biyu ita kuma hud'u yasa hussaina tafara k'orawa Aisha jawabi da hantarar yaranta Amma Aisha bata tab'a tanka mata ba sai dai tayita haushinta inta gaji tabari, yanzu kam alhaji bashir yatara familynsa gwanin ban sha'awa yayinda Hajia Aisha wato Ummi uwar gidansa kenan take da 'ya'ya biyu Bilkisu da Bilal ita kuma Hajia hussaina small mom kenan wato amarya take da yara hud'u, Mahmud, Basmah, Batool da kuma Bassam.
Mahmud shine babba yanada shekara 27 sai Basmah dake bimasa tanada 16years sai Batool da Bilkisu 14-15years sai Bassam 7years Bilal kuma 3years.

_Back to the story_































Mr's huss@inโœ๐Ÿป

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWA NANE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage______2๐Ÿ’Ž


Kafin batool ta rufe baki taji saukar belt ajikinta, cikin wata irin kasalalliyar murya ta samu damar yin ihun da yasa small mom rugowa aguje ta ture Mahmud gefe tana fad'in

"Amma wannan yaro baka san ciwon kanka ba wallahi! Yanzu akan waccan munafukar yarinyar kake nema kajiwa 'yar uwarka ciwo?, to Wallahi tunda naga rashin hankalin naka na nema ya wuce gona da iri saina sab'a maka rai, shashasha da baisan inda keyi masa ciwo ba" Cikin dak'ilalliyar murya dake nuna k'ololuwar b'acin rai mahmud yace.

"Amma mom kinajin maganganun da take fad'a fa, ko kad'an basu dace ba, don me zata yi hakan?"

Sake da baki small mom ke kallonsa kafin ta jefa masa wata irin muguwar harara tare da sakar Masa dakkuwa tana cewa,

"Ungo nan marar kunyar yaro, Anya mahmud nina haifeka kuwa? Anya ba musayarka akayo mani a asibiti ba? har wani tambayana kake don me take yin hakan, to don ubanka take yi, nace don ubanka take yi kaji ko? Meye abun b'acin rai da har zaka kaiwa 'yar uwarka duka?, idan kace su 'yan uwanka ne ita d'in meye taka da zaka nemi ka illata min ita akan wud'an can zuri'ar da basu gaji arzik'i ba sai dai suci banza..."

Da k'arfi mahmud dake duk'e da kansa k'asa ya d'ago yana kallon gefen dasu Ummi ke tsaye saboda yanda take nauyin maganar da mom d'insa kefad'a don ya san da gangan small mom ta fad'i haka saboda kawai a b'atawa ummi rai, Cikin Sa'a yaga ummi bata wajen, tunda ummi taga small mom ta fara fad'a taja hannun Billy har Lokacin bilal na sab'e akafad'arta ta bar falon, wata irin ajiyar zuciya mahmud yayi tare da cewa.

"Alhamdulillah" sannan ya jefawa batool dake tsaye a abayan small mom tana shafar shoulder d'inta tana hawaye na belt d'in daya shimfid'a mata a jiki yace,

"kuma kitabbatar kinkai mini abuna d'akina, pls mom kiyi hakuri kidena fad'ar irin wud'annan kalaman saboda samu da rashi duk na Allah, wannan abun da kike yi babu kyau tamkar training ne kike yiwa wannan dak'ik'iyar yarinyar" Mahmud ne ya sake fad'ar haka Bayan ya maida kallonsa ga mom da tun d'azu ta k'ara hasala da kalamansa, azuciye ta d'auko belt d'insa daya jefawa Batool dan ta kai masa a d'akinsa ta nufo wurinsa dashi,

"Kai yaron nan bari nayi maganinka tunda naga kana nema karenani sannan banza da wofi tun kafin kazo duniya nake shan wa'azi"

Da gudu mahmud ya bar falon yana dariyar kalaman mom d'insa a zuciyarsa kuma yana rok'on Allah daya sauya mata rayuwa ta gane cewa sumafa su bilkisu 'yan uwansu ne bai kamata ta dinga neman raba masu kai ba saboda zafin kishi, da wannan tunanin ya nufi part d'in Ummi, Zaune ya tarar da ita tana yiwa su Bilkisu fad'a akan sudena zuwa suna yiwa small mom abunda zaisa ta dinga dukansu ko kuma ta hantaresu, cikin sheshshekar kuka Billy tace

"Ummi Bafa abunda muke yi mata kawae dai ita ta tsane mune bata sonmu bata son murab'i 'yan uwanmu shi yasa take mana haka"

"Kashh! sister ba haka bane, kawae baki fahimci mom bane kamar yanda itama wani dalili yasa ta kasa fahimtar matsayinku awurinmu" Mahmud ne ya fad'i haka tare da dafa kafad'ar Billy,

"Ummi don Allah kuyi hakuri, kufahimci mom d'ina kuma kuyi mata uzuri, wlh ni kaina bana son abunda take yi" ya k'arasa maganar tare da zaunawa gefen da ummi take ya rok'i hannun Bilkisu yana cewa,

"Plz sister ...ku 'YAN UWANA NE kada kurik'i mom d'ina amatsayin mai laifi ku d'auka tana yin kuskure ne wit time zata gyara insha Allah" yatsansa yasa ya gogewa Bilkisu hawayen da suka zubo mata "smile my Billy japanis" dariya ce takuccewa Billy ta d'an kai masa Duka cikin

Please Login or Register in order to submit comment