Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batayi ba balle tabar wajen sannan yad'an d'aga muryarsa tayanda zata iya jiyosa yace

"Eh ummanah lafiya klw nake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah gobe ana gama d'aurin aure zamu kamo hanya nida amaryata, kiyi farinciki sosai domin dady mutumen kirkine, yayimun gata da babbar 'yarsa alokacin da k'aramar 'yar tasa taso ta tozartar da rayuwata" sosai Billy taji d'acin kalaman da taji kunnuwana najiyo mata daga bakinsa amma sai tabasar tare da barin wajen tana nanata kalmar _hazbunallaha wani'imala wakeel_,

Gaba d'aya duk abunda kefaruwa daga yaya Mahmud harsu Basmah da Batool da kuma au mom babu wanda ya sani kuma dady sunbar maganar atsakaninsu akan cewa sai gobe tayi idan and'aura auren kowa zai san da maganar,

Yinin ranar kuma gaba d'aya Ummi fushi tadingayi da Billy akan maganar da tayi mata d'azu batare datasan cewa tuni mafarkin da tace idan shi Billy keyi ya kusa zama gaskiya.

Shikuwa yaya Mahmud yana can wajen faraaha da kullum cikin k'orafi take yimasa akan baya attending programs d'in duk da tayi on time don haka tana son ganinsa kafin lokacin waima yayi don atare za'ayita da tasu Batool, hakan yasa yaje don ya nuna mata cewa tabbas shid'in natane kuma zai iya bata lokacinsa aduk sanda ta buk'ata.

K'arfe 5:00pm na marece aka gabatar da waleema cikin kwanciyar hankali wacce Billy da kanta taje taciro wata abaya acikin kayan lefen da yaya mahmud yakawo mata bayan sun shirya za'a wuce takaiwa yayya Basmah had'e da cewa

"Yayya ga wannan kisa gaskiya yau shiga kala d'aya zamuyi dake mungaji da warewar da kikeyi acikinmu bayan mudake 'yan uwane" murmushi basma tayi had'e da cewa

"Ikon Allah, kufa amarene ku akeyiwa walima to mezai kaini yin shiga d'aya daku?"

"Pls yayya don Allah kikarb'a daga yaufa shikenan gobe rabuwa zamuyi"

"Eyyeee lallai sisto na fahimci kinyi nisa a so, har kin matsu murabu kiganki agidan yaya Mahmud ko?" Basmah tafad'a tare da lak'amo hannunta wajen wuyan Billy tana dariya saboda yanda taga tab'ata rai tad'an turo baki, hakan yasa Basmah takarb'i abayar bayan tagama shiryawa tsaf ta aza asama, jitayi nan take gabanta yafara fad'uwa wanda bata san meye dalilin hakan ba, cikin wannan yanayin sukaje wajen walimar da tasamu hallarar manya manyan malamai mata awajen, inda malama Jidda alk'ali tagabatar da nasiharta mai taken YARDA DA QADDARA itace tabbatuwar imanin musulmin k'warai, tana gamawa itama malama Afrah tagabatar da tata mai cike da nuna muhimmanci akan rik'o da zumunta acikin al'ummah sannan malama tak'arshe malama Asma'ul husnah itama takarb'a tayi masu nasiha akan biyayyar aure agidan miji bisa tarbar hak'uri da juriya, sosai amaren ke kuka wanda nan take itama Basmah ganin kukan da sukeyi yasa itama ta tayasu wanda kowanensu akwai dalilin daya sashi kuka akan nasihohin, bayan ankammala cikin natsuwa akabi duk wud'anda suka samu damar halartar walimar da wata k'atuwar leda da aka rubutawa _JAZAKUMULLAHU BIKHAIR FOR ATTENDING OUR MARRIAGE WALIMAT_ dake d'auke da alk'ur'ani hizib sittin dardumar sallah, tazbaha, hisnil Muslim, kaskon turare da kuma turaren wuta acikin wata kwalba mai kyau, kasancewar akwai alk'ur'ani acikin ledar yasa ba'ayi wata hayaniya ba wajen rabawa kuma manya kad'ai aka bawa, sannan kowa yatafi gida jiki duk yayi sanyi saboda nasihohin da suka karb'a awajen k'wararrin malaman daban daban,

Aranar kam Billy tayi kuka kukan da ita kad'ai tasan dalilinsa sai kuma mahaifinta da kuma Mahmud pilot, duk wanda yaga yanda take kuka lokacin da aka taso wajen walimar saida ya tausaya mata, shikanshi yaya Mahmud pilot yayi kuka kamar ba gobe, ji yakeyi tamkar kada safiyar gobe tawaye saboda itace ranar da zata haramta masa Billynsa har abada matuk'ar 'yar uwarta na agidansa kuma amatsayin matarsa daga k'arshe ya d'auro arwala tare da rok'on Allah yabashi hakurin rashin Billy kuma ya bashi ikon rik'e Basmah bisa gaskiya da amana batare da soyayyar Billy tayi tasirin da zatasa ya taushe mata hak'k'ok'anta dake kansa ba, Umma kuwa tuni ta shedawa alhaji mahaifin Mahmoud abunda kefaruwa Wanda nan danan ya kira dady yasake tambayarsa ko meye gaskiyar al'amarin, sosai yaji badad'i cikin zuciyarsa kuma ransa yab'aci sosai amma daga baya da yaji yanda dady kebasa hak'uri cike da nuna damuwa sai shima yayi fatan Allah yasa hakan shiyafi zama alkhairi, tun safe har dare Umma bata minti goma bata kira Mahmoud ba don taji ko yana lafiya, ta kirasa babu adadi wanda daga k'arshe yafahimci cewa ya amshi k'addararsa ayanda tazo masa kuma ya hak'ura da ita.

Basmah kuwa yanda tayi bacci a wahalce jiya kuma ta wuni a wahalce tana b'oye ciwon hakama daren yau ta kwana awahalce, amma duk da haka bata bari kowa yafahimci yanayin da take cikiba.

Da shire shire yau aka tashi sosai agidajen ahalin guda hud'u, gidan dady, garin borno gidansu Mahmud, gidansu faraaha da kuma gidansu dr. Ahmad don gudanar da shagulgulan bikin d'aurin auren nasu yanda yakamata, sosai yau mamy kecikin farinciki ganin yanda 'yan uwan mijinta da abokanan arzik'i suka taru agidan don taya d'anta tilo farinciki da murnar aurensa, Dr Ahmad kuwa baki yakasa rufuwa yau za'a kawo masa fatimarsa agidan sa kuma amatsayin matarsa, kallon Muhib sake faman tsula kula ahannun wata mak'wabciyarsu da mamy taba tashi tarik'e masa yace

"Shiii..Muhib today is a happiest day, bai kamata ace kana kuka ba saboda ur in-law is coming to dis house in d next few hour's" yana yimasa wasa da glass d'in hannunsa daya ciro daga idanunsa.

Shiru Muhib yayi yana kallon yanda yake jujjuya glass d'in a fuskarsa tamkar yana jin abunda yake cewa.

Yau dai bakin alk'alami ya bushe domin da misalin k'arfe 1:00pm aka d'aura auren yaya Mahmud da amaryarsa faraah bisa zunzurutun kud'i har naira dubu d'ari, lak'adan ba ajalan ba d'aurin auren daya samu halartar manya manyan 'yan kasuwa daga k'asashen duniya daban daban abokanan kasuwancin dady, dattijai da sarakuna, manya manyan k'usoshi acikin gwamnati duk sun samu hallara wannan bukin, wanda alhaji kabiru da kansa ya ansarwa d'an d'an d'an uwansa auren faraha, murmushi dady yayi mai had'e da kuka tare da d'aga idanuwansa sama lokacin da aka gama d'aurin auren yana godewa Allah daya nuna masa wannan rana daya samu kusanci da soyayyar da d'an uwansa yayiwa d'ansa waliccin aure.

Ana gamawa kuma aka nufi anguwar nasarawa family house d'insu dady inda kusan sama ga kashi tara bisa goma da suka halarci d'aurin auren faraaha suka sake garzayawa can harda iyayen nata don shedar aurensu dr Ahmad, kasancewar dama k'arfe biyu daidai za'a d'aura auren nasu yasa ana isa ba'awani tsaya b'ata lokaciba aka shiga sigar d'aurin aure tsakanin alhaji bukar da kuma iyayen Mahmoud filot da suka samu isowa tun k'arfe sha biyu narana kusan mota biyar, inda dama tuni sun dad'e da amsar k'addarar data kutso cikin auren, nan take suka fara nemawa d'insu Mahmoud auren Basmah ahannun alhaji bukar kuma yabasu bisa yanda addini yatanadar kowanensu farinciki na kwance afuskarsa, hatta Mahmoud pilot ya danne damuwarsa yayin da mutane suka fara kallon kallo da tambayar kansu taya hakan tafaru, yaya mahmud kuwa kusan mutuwar zaune yayi yana tambayar kansa shin da gaskene abunda yaji ko kuma mafarki yakeyi, kai hardai aka kammala d'aurin auren Batool da dr.Ahmad kawunan mutane na ad'aure munkasa fahimtar wannan sark'ak'iya da akayi, ana kammala d'aurin auren aka fara fir fitowa mutane da take away na abinci da ferfesun nama dasu drinks, garar swan water ana rarrabawa da yake wasu irin manya manya rumfunane au alhaji kabiru sukasa aka kakkafa abakin k'ofar gidan yayinda dama antanadi securities d'in da zasu kula da tsarin auren har zuwa lokacin daza akammalawa,

Kasa hak'uri yaya Mahmoud dake sanye cikin babbar riga farar shadda yayi har awatse taron saida yaje yajawo hannun Mahmoud pilot dake can gefen da aka tanadarwa iyayensa da abokanan sa da sukazo tundaga borno d'aurin auren, cikin rud'ewa yana d'aga hannun Babar rigarsa ya aza akan kafad'a yace

"'Dan uwa anya kaji wajen d'aurin aurennan sunan wacce aka ambata kuwa, wai kodai su dady sun mantane?" Cikin halin rashin damuwa da ko inkula da abun Mahmud pilot yace

"Eh mana najiya, ba nida 'yar uwata Basmah aka d'aura ba?"

"Wai mekake fad'i kana nufin da saninka kenan akayi? Bilkisu fa?" Saida Mahmud pilot yayi wani irin murmushin da yafi kuka ciwo sannan yace

"Ba ita bace Allah yatsaro zan aura, kasan matar mutum kabarinsa, to Allah baiyi cewa Bilkisu zata zamo matata ba saidai Basmah" cike da damuwa yaya Mahmud ya shafo hancinta zuwa bakinsa yayinda idanuwansa suka kad'a sukayi jawur yace

"Look amma aikai Bilkisu kake so, daidai da rana d'aya baka tab'a cewa kana son Basmah ba, donme za'ayi maka haka?" B'ata rai Mahmoud pilot yayi yana kallonsa had'e da cewa

"Kai yaushe nafad'a maka cewa bana son Basmah, dukansu 'YAN UWANA NE kuma ina sonsu ina k'aunarsu kuma rashin auren Bilkisu bazai canza komai tsakanina dasu ba don haka Allah yatsaro cewa Basmah itace matata saboda haka kacire wannan mugun tunanin aranka kaje kakula da bak'in ka kaji ko" yak'are maganar had'e da d'aga hannu yana nunasa, Wasu hawayene suka zubo a idanuwansa lokaci d'aya ya rungume Mahmoud pilot yace

"Tabbas kai d'an uwane na K'warai, wlh inajin rad'ad'i da zafin faruwar wannan abun don nasan jurewa kawai kakeyi amma bak'aramin abubane ka hak'ura da soyayyar Billy don kana sonta sosai, kawai bayanda zakayine don anfi k'arfin kane" sai alokacin Mahmoud pilot yasamu damar zubar da hawayen nasa da tun d'azu yake k'ok'arin dannewa zuwansu, hugging d'insa shima yayi sosai kamar zai tsaga jikinsa yashige tanaci gaba da kukan, ahankali yaya Mahmud da shima hawayen yakeyi yadinga bubbuga bayansa alamun rarrashi har saida yayi ku kansa mai isarsa sannan yad'ago daga jikin d'an uwan nasa had'e da cewa

"Tabbas naso Billy arayuwata tayanda nake tunanin idan narasata bazan sake moruwa aduniyaba, ahiyasa Allahn daya bani rayuwar yajarabceni da kanta tace bazata aurenba saboda bazata samu farinciki agidana ba, kaga kuwa dole duk son da nakeyi mata inbarta kuma in amshi sauyin da Allah yayimun da hannu biyu, koba komai abunda yayi Billy shiyayi Basmah don haka nayi imani da wannan qaddarar so da Allah yayimun kuma Alhamdulillah" yana gama fad'ar haka yayi murmushi tare da barin wajen.

Har ga Allah kokad'an yaya Mahmoud baiji dad'in fasa auren Billy da Mahmoud pilot ba, amma shiwaye da bazai amshi wannan qaddarar ba tunda har wanda akayita akansa ya amince da ita, tunaninsa d'aya shine meyasa Billy ta aikata haka, meyasa Billy tarusa farincikinta da kanta?, shin kodai mom d'in sace taje tafad'i halin da Basmah keciki?, haka yadinga jerowa kansa tambayoyin da bayada mai bashi amsarsu awannan lokacin, ganin haka yasa jiki bak'wari yaje aka k'arasa tarbon bak'i dashi, ancire Ansha tare da fatar Allah yazaunar da wud'annan amare da angwaye lafiya kuma yabasu zuri'a masu albarka, multicolours d'in shaddodi masu tsada da agogayyen hannu dady yadinga rabawa duk wud'anda zasu tafi bayan kammala d'aurin auren har zuwa lokacin da taron yawatse.

Bayan ankammala taron d'aurin auren su dady sun dawo gida Basmah da duk tad'an fad'a tana zaune itada su Billy sunsha kwalliyar yinin buki sai k'arfin hali take famanyi tana tsokanarsu tana cewa

"Yau dai kunzama, kun zama d'auko hula, kun zama d'auko riga, kun zama d'auko wand.." Kafin ta iyar sukaji irin masu kirarinnan acan k'ofar gida suna fad'in

"Ina kike uwar amarya Basmah uwar amarya Batool yau kifito ranar murna ce da farinciki and'aura auren 'ya'yanki, kifito kiyi mana alkhairi yau kike uwar ango Mahmudu farin d'a mai farar aniya yayan amarya Basmah da Batool, ubangiji Allah yazaunar lafiya yabada zuria masu albarka, gaban Billy ne yayi wata irin muguwar fad'uwa da sauri ta rintse idanuwanta had'e da karanto " hazbunallaha wani'imal wakeel" shikenan yau shikenan tafaru tak'are duk wani mafarkinta da burinta akan yayan nata yak'are, kallonta Basmah tayi tana dariya had'e da cewa

"Kai sister tsofaffincan sunrud'e, kinji abunda suke cewa kuwa?" Tak'are maganar had'e da dafa Batool tana kallonta, murmushi itama tayi don gaba d'aya jikinta yamutu yana bata kamar akwai wani abun, mik'ewa Basmah tayi cikin k'arfin hali jin basu dena kiran sunanta amatsayin amarya ba tad'auki hijab d'inta tare da d'aukar rafar 'yan naira ashirin ashirin tanufi wajen masu ik'irarin dake cikin harabar gate, tana zuwa tamik'a masu had'e da cewa

"Batool da Bilkisu ne amaren ba Basmah ba don haka kugyara" tana rufe baki motar su Mahmoud pilot da yaya Mahmoud tashigo, bayansu kuma motocin mutanen borno ne da suka d'aurin aure sukazo su d'auki amaryarsu anjima kad'an suwuce" da sauri yaya Mahmoud yafito cikin motar had'e da jan hannunta da k'arfi suka wuce cikin gida, yayinda sukuma masumasu kirarin ganin tajik'esu da rafar kud'i yasa suka koma kirarinsu yanda tafad'a, fitowa Mahmoud pilot dake zaune tunda suka shigo yana kallonta har zuwa lokacinda yaya Mahmoud yaja hannunta suka shige yayi tare da dafa wanda kefaman bushes bushe suna kirari yace

"Malan auren Basmah da Mahmoud, Batool da dr Ahmad zakace ba Bilkisu ba kaji ko?" Kallon kallon suka shiga yima junansu cikin rashin fahimta suna kallonsa kafin suce

"Amma yanzu kuma wata tafito tace ba Basmah ba Bilkisu ce sunan d'ayar amarya"

"A'a itace Basmah amaryar nikuma nine angon ko baku ji yanda aka fad'a wajen d'aurin auren bane" yafad'a tare da shigewarsa...



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____86💎


Suna shiga cikin gida yaya Mahmoud ya d'aga hannu kamar zai mareta had'e da nunata da hannun yace

"Meke damunki? Meya kaiki fitowa awannan lokacin?"

"Ya kyauta naje yimasu, kuma bakaji shiren da sukeyi ba wai Basmah amarya" tak'are maganar tare da turo baki, tsaki yaja sannan yajuya tare da sake juyowa yana kallonta yace

"Ofcouse ba waibane, ke yanzu amarya ce domin dake aka d'aura auren"

"Kaji yaya da wani zance, sai kace shi auren wasar k'asace da za'a tsaroshi da wanda za'ayi daga k'arshe kuma ace amfasa"

"Keep joke aside Basmah, Billy tace bazata auri Mahmoud ba shiyasa dady yace a d'aura auren dake, believe me Basmah ba wasa nakeyi ba, keyanzu matar aurece bai halarta kije wajen waniba har saida izinin mijinki" yafad'a tare da rik'e mata kafad'u ganin yanda take yimasa wani kallo tanaja da baya,

"Bazai yuyu ba yaya wlh Billy nasonsa, kada kuayarda da zancenta domin nida kaina natabbatar da irin soyayyar da takeyi masa" itama tafad'a tanaja da baya da baya,

"What ever dai Basmah anriga da angama yanzu kece matarsa" wani irin kuka tafashe dashi don tatabbatar da cewa yayan nata bawasa yakeyiba lura da yanda marok'an tun farko suka shigo auna kiran sunanta amatsayin amarya, toshe baki tayi hawaye na tsiyaya a idanuwanta tace

"No.." Tare da barin wajen aguje, k'ok'arin rik'ota yayi sanin batada cikakkiyar lafiya yaji andafo kafad'arsa, juyowa da zaiyi yaga dady tsaye abayansa fuskarsa ba walwala yace

"Barta, amma wayasa kafad'a mata?, tun d'azu saurin da nakeyi kenan in dawo gida inkirata insanarda ita komai tayanda zata fahimceni, yanzu kaga shikenan inba Allah yaso ba birkice mana zatayi tunda batada isashshiyar lafiya"

"Afuwan dady nakasa controlling kaina saboda yanda abun yazo abazata shiyasa nafad'a mata, farko ma nazata da saninta komai yafaru, amma dady meyasa zakayi haka wlh Billy tana son Mahmud sosai, kawai k'ilan wata 'yar matsalace tafaru tsakaninsu shiyasa fushin zuciya yasa ta aikata haka amma..." Saurin dakatar dashi dady yayi tahanyar d'aga masa hannu kawai sannan yabar wajen, dafe kai Mahmoud yayi tare da cewa

"Meyasa kika aikata haka my sister, tabbas nasan bazakiyi hakaba sai kinada wani babban dalili, ya Allah kazamo mata gata kuma majib'incin al'amurranta, Allah kada kawofantar da ita bisa wannan abu da tayi" hango Mahmud yayi zaune a guiding yayi tagumi babu abunda yake tunawa sai irin rayuwar soyayyar da sukayi awurin tare da yanayin murmushin da take yimasa da dariya idan suna wajen, d'aga kansa yayi sama had'e da cewa

"Qadarallahu wama sha'a fa'ala" sannan yasauko da kansa had'e da furzar da wata iska mai zafi abakinsa idanuwansa na tsiyayar da hawaye, jiyayi ansa hannu anagoge masa k'walla, d'ago idonsa da zaiyi yaga yaya Mahmoud tsaye agabansa shima hawayen tausayin 'yan uwan nasa gaba d'ayansu yakeyi,

"Kayi hak'uri d'an uwana, kuma kada ka k'ullaci my sister arai, wlh natabbata tanada babban dalilin da yasa ta aikata hakan, tana matuk'ar k'aunarka Allah ne yashiryo haka atsakaninku saboda wani dalili nasa da bamu saniba, pls d'an uwana don Allah kayi mata uzuri kuma kayafe mata" yak'are maganar tare da had'e hannuwansa waje d'aya har yana zancen duk'awa agabansa, da sauri Mahmud pilot ya d'agosa had'e da kallonsa sannan ya rungumesa.

"Karka damu d'an uwa duk da naji zafin abunda tayimun hakan baisa narik'eta araiba, ina mai yimata fatar Allah yabata wanda takeso itama kuma yabasa ikon kula da ita kamar yanda nayi buri, sannan yasota fiye da yanda nake sonta"

Lokacin da labari yakai kunnen Ummi cewa bada Billy aka d'aura auren ba fad'uwa tayi asume saida akayita yayyafa mata ruwa sannan tafarfad'o saboda tsabar yanda hankalinta yatashi, "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, allahumma ajirni fi musibati wa'ahlifni khairan minha" tadinga nanatawa afili sannan taci gaba da cewa "Shikenan Bilkisu burin ki yacika, gaba d'aya wannan kuskuren nawane da nad'auki cewa maganarki da wasa kuma amatsayin mafarki, har kikaje kika aikata wannan babban kuskure batare dana hanaki ba, amma ina rok'on Allah da yasa hakan shiyafi zama alkhairi tsakanin ke dashi"

Anan wata tazo masu da zancen cewa ai da 'yar uwarta Basmah aka d'aura auren don tsabar munafucci, duk abunda annan momyce ta aikatashi don ganin 'yar tata batada mashinshini shine tasan yawa Billy tsanar d'an uwanta don d'ai ya auri 'yarta, nan dai aka dinga gulmace gulmace da tsogumukka ana zagin mom,

"Alhamdulillah, Allah nagode maka daka sanya cewa alhaji yanada wata 'yar da zata share masa hawaye batare da muntozarta a idanun duniyaba, Basmah Allah yayi maki albarka kuma yazaunar dake lafiya agidan ki yabaki 'ya'yan da zasu yimaki biyayya kamar yanda kika yiwa mahaifinki" sukaji Ummi nafad'a cikin farinciki duk da tanajin wani irin mugun rad'ad'i azuciyarta nafasa auren 'yarta amma saita samu quwwar data iya dannesa saboda sunan Allah data ambata had'e da mik'ewa tsaye tajuyo tana kallon matar data kawo gulmar har 'yan uwanta suka biye mata ana zagin mom tace

"Ke kuma kiji tsoron Allah, kuma kije kinemi gafarar hajiya hussaina don kinyi mata k'azafi kuma Allah zai tambayeki kuma yabi mata hakk'inta" sannan tajuya ga 'yan uwanta da sukayi tsurutsuru da idanuwa suna kallonta cike da mamakin anya ko ita tahaifi Bilkisu da har aureta zaifasu tadalilin makircin kiahiyarta kuma tayi tsaye tana yimaka Allah godiya akan haka tare da musa zagin nasu tace

"Ku 'YAN UWANA NE bai kamata ace kuzaku had'a wutar da zata ruru agidana ba harta tarwatsamun farincikina, kusa tutar babu tacimmin gani cikin damuwar abunda yafaru ga 'yatah sannan ga bak'ar fitina da gaba da bak'in ciki da zai dinga ruruwa acikin zuciyata, nuna mom Jidda tayi sannan taci gaba da cewa ke shedace akan fad'an da kikaji inayi jiya da safe har kikazo kina tambayata nace maki da 'yarki Bilkisu nakeyi kika cemun Allah yasawak'e, to ba'akan komai bane illa akan wannan matsalar Allah shine sheda sai kuma ni da iyayenta maza dana tabbatar sutajewa da wannan maganar suka goya mata baya da kanta tace batason auren nan, idan akayi matashi bazata tab'a samun farinciki agidan saba wanda bansan meye dalilinta na aikata hakanba amma zaku kama kuyita zagin wud'anda basuji suka ganiba akan wannan maganar, gaskiya banji dad'iba kuma kunyi kuskure, nan gaba yakamata kudinga tantance magana kafin kuhau yin sharhi akanta" tana gama fad'ar haka tabar wajen had'e da maimaita hazbunallaha wani'imal wakeel saboda tasamu sauk'in rad'ad'in da zuciyarta keyimata,

Sukuma gaba d'aya nan rake kunya takamasu, jikinsu yayi sanyi tare da fad'in "to Allah kayafe mana"

Yayinda mom dake k'ok'arin shigowa palourn wajen kiran Ummi da dady yakirata awaya yace tayi lokacin daya taso zaizo gida akan suhad'u a parlounsa don fayyace masu abunda kefaruwa, wanda kawai tazone bisa umurninsa badon ranta yasoba, sai gashi tajiyewa kunnuwanta abunda idan wanine yafad'a mata nan take zata k'aryatasa, tayi sauri juyawa da sauri tabar wajen idonta cike da k'walla tare da nadamar abubuwan da tayiwa Ummin abaya jin yanda take k'ok'arin wanketa akan zargin da ake yimata, tabbas yau tayarda Ummi tafita ako ina kuma tad'arata aduk inda za'a shiga, ko kad'an bata tab'a tsammanin cewa kyawawan halayenta sunkai haka ba, yanzune tafahimci dalilin dayasa tayi mata zarra kuma take tsallake duk wani makirci da tuggu da take k'ulla mata saboda kyakkyawar zuciyartane, part d'inta takoma duk jikinta amace sannan tatura Batool taje tafad'o mata sak'on dady,

Ana hakanne saiga Basmah tashigo aguje tana kuka tashiga d'akinsu tare da fad'awa kan gado, wanda nan take taji zuciyarta nabuga mata da sauri da sauri, bayanta mom tabiyo hankalinta atashe tana fad'in

"Basmah, Basmah lafiya kike kuwa" tare da shigowa d'akin ta d'agota daga kwance da take "Basmah nikuma yafaru haka kike kuka bayan kinsan halin da kike ciki" cikin kuka tace "Nashiga uku mom abunda nake gudu shiya faru, mom wai don me matsaloli ke bibiyar rayuwarmu nida 'yan uwana?"

"Basmah kinsani aduhu, kiyimun bayani mekuma yake faruwa ayanzu"

"Mom an..d'au..ra aurena da wanda k'anwata ke matuk'ar k'auna aranta, taya zan iya rayuwa dashi bayan ita yake so? Innalillahi wa inna'ilaihirrajiun wannan wane irin son kaine nayi haka, naci amanar 'yar uwata da kaina natabbata bazan tab'a yafewa kaina ba"

"Yishiru mana Basmah wai duk wannan bayani ina yanufa ne?"

"Mom and'aura aurena da yaya mah.mu.." ai kafin ta iyar kawai tasome, Billy dake tsaye jikin k'ofar itama tabiyosu lokacin da taga 'yar uwar tata tashigo tana kuka tayi saurin juyawa zatabar wajen saboda tausayinta akan kalaman da taji suna fitowa daga bakinta sai ga dady ya shigo, saurin shigewa d'akin mom tayi har saida yashige d'akin nasu Batool sannan tafita tanufi part d'insu cike da tsarguwar kanta saboda 'yan buki da suka zubomata idanuwa suna kallo wasu har da nunata ana suruttai.

Daidai lokacin da tasumà mom na jijjigata ne dady yashiga d'akin, a firgice ya k'arasa wajen had'e da d'an bubbuga kuncinta yana kiran sunanta wanda anan take yagane cewa suma tayi, tura mom yayi takawo masa ruwa ya yayyafa mata wanda saida tayi kusan minti biyar yana shafa mata ruwa afuska sannan shed'arta tadawo, ahankali tabud'e idanuwanta suka sauka akan fuskar mahaifin nata tayi saurin fad'awa ajikinsa tana kuka.

Shafa kanta yadingayi cikin sigar lallashi yake yimata magana

"Kiyi hak'uri Basmah, nasan ba'a kyauta makiba ganin cewa and'aura maki aure bada sanin kiba kuma da wanda kike tunanin zai zama miji ga 'yar uwarki, amma amatsayina na mahaifinki da kike da hak'k'i akaina nayi hakanne don inada tabbaci akan zakiyi mun biyayya kuma zakibi zab'in da nayi maki don bazan tab'a cutar da keba, Basmah yazanyi daidai lokacin dana tara duniya nace suzo au sheda auren 'ya'yana guda uku idan har aka samu akasin haka alokacin da suka hallara, shin kina tunanin akwai sauran kima da darajata a idanuwan wud'anda nayiwa alk'awarin basu auren 'yata, nakarb'ar maau sadaki da lefe kuma nace nafasa, shin ashe girma da mutuncina basu zube ba a idanuwansu dama duniya? tsoron hakan yasa lokacin da 'yar uwarki tafad'amun cewa bata son aurenta da d'an d'an 'yar uwata bisa wani dalili nata da take ganin kamar na tauye mata hak'k'inta nayi tunanin musanya masa ke da ita, cike da yak'inin cewa bazaki tab'a bani kunya ba ko kuma watsamun k'asa a idanuwa ba, amma idan har kina ganin kema natauye maki hak'k'i shikenan sai inje inrok'esa ya sawwak'e maki tun kafin ranar nadamar yin hakan tazomun" da tuni jikinta yayi sanyi jin kalaman mahaifinta ta d'ago kai had'e da kallonsa har lokacin idonta na hawaye tace

"Dady amma 'yar uwata fa?, nasani tana matuk'ar son yaya Mahmud kamar yanda yake sonta"

"Kenan ke bakya buk'atar kasancewa dashi amatsayin matarsa tunda 'yar uwarki yake so? Shikenan nafahimta, zance ya sawwake maki inyaso zanje insamo masa matar da zata sosa tunda duka 'yan uwansa basa buk'atar kasancewar su atare dashi"

"Ba haka nake nufi ba dady, kawai ina tausayin 'YAN UWANA NE akan halin da zasu shiga saboda yanda suke son junansu, amma dady idan wannan zab'in da kayimun yayi maka zanzauna dashi duk da cewa har inmutu bazan tab'a dena kallon kaina amatsayin

Please Login or Register in order to submit comment