Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafin ciwon kan yasa kakula niba" tana gama fad'ar haka tawuce bedroom d'inta hawaye na zubar mata a idanuwa,

Zaune dady yayi wajen tare da buga tagumi yace "Tirk'ashi! yaufa nataro ruwa, saida meamah dasu Ummie suka yita bani shawara akan bekamata na d'auka da zafiba amma nak'iji, ai yau ga irinta nan, wannan fushin da tayi nasan babu mai bata hak'uri taji idan ba mutanen rano online ba" haka yazauna shikad'ai yana faman suruttansa yakasa zuwa ya fuskanceta saboda tsabar nauyin abunda yayi mata balle yasamu yabata hak'uri ta hak'ura, gyara zamansa yayi tare da jawo wayarsa yana lallatsawa har aka kusa kiran magrib saiga su Bassam da Bilal da kuma Billy sun dawo daga gidan yaya Mahmoud da shima yake biye dasu abaya, da gudu sukaje suka haye jikin dady suna yimasa oyoyo, cikin fara'a dady ke shafa kanunsu yana fad'in "oyoyo yaran dady andawo?"

"Eh dady aunty faraaha mai mutunci dady ta siya mana chaculate da sweet hadda Ball" Bilal yafad'a tare da rik'o wuyan dady yana dariya

"Iyeee gayu, to injin dai lafiya kuka baro auntyn taku?"

"Eh dady kuma tayi mana abinci mai dad'i mukaci kuma taba aunty Billy wani abu aleda" Bassam yafad'a shima yana lak'ame ajikin dady, murmushin jin dad'in hakan dady yayi kafin yace

"Iyyeee lallai agaida aunty faraaha Allah yayi mata albarka gaba d'aya suka amsa da "amin"

Juyowa yayi yana kallon Billy da sai yanzu suka iso ita da yaya mahmud tare da amsa sallamarsu cikin girmamawa suka k'arasa cikin parloun had'e da gaishesa, bayan ya amsa Billy tamik'e zata wuce d'akinta dady yayi saurin cewa

"Bilkisu" wani irin fad'uwa gabanta yayi tare da juyowa tace "na'am dady"

"Zonan mana" yafad'a cikin sigar rarrashi da alamar sakkowa daga fushin da yakeyi da ita, dawowa tayi cikin palourn tazauna kanta na duk'e ak'asa, alama yayi mata data dawo kusa dashi ta zauna sannan yacewa su Bassam suje su d'auro arwala ankusa kiran sallah, bayan sun fita dady yafara k'warara masu labarin abunda dr yafad'a masa akan 'yar uwarsu da kuma abunda ya isko mom nafad'awa Ummi sannan yajuyo yana kallon Billy yace

"Hak'ik'a ke 'yace tagari da zanyi alfahari da ita duniya da lahira, kinnuna mun cewa kobana duniya zakibi 'yan uwanki kuma kisoau fiye da yanda nake buk'ata, kiyi hak'uri bisa abubuwan dana yimaki, yanzune nafahimci dalilinki na cewa bazaki samu farincikiba idan kika auresa, duk da dai cewa kinyi laifi wajen rashin sanar mani da gaskiyar hak'ik'anin dalilin da yasa kikace bazaki auri d'an uwanki ba hakan bazai hana inrok'eki yafuwar hukunci dana yimaki bisa rashin fahimtar ki, kiyafemun Billy ubangiji Allah yayi maki albarka kuma kema yabaki 'ya'yayen da zakiyi alfahari dasu kamar yanda nima nake alfahari dake, yanzu kije kiyi tunani idan kina buk'atar cigaba da karatu sai inda ayimaki replacement da takardar gurbin karatun da aka nemowa Basmah kinji ko?"

"Eh dady, ngd Allah yak'ara girma" tafad'a hawaye nazuba a idanuwanta, abu biyu ya sakata kuka, nafarko halin da taji 'yar uwarta keciki, na biyu kuma yanda Allah yakawo mata k'arshen fushin da dady keyi da ita, ahankali ta d'ago kanta tana kallonsa tace

"Dady kakira yayya kaji tana lafiya kuwa?, wlh bana tunanin koda akwai matsalar dake damunta zata fad'a don tanada matuk'ar zurfin ciki"

Mahmud da gaba d'aya jikinsa ya mutu jin abunda dady yafad'a yana kallon irin jarumta da sadaukarwar da Billy tayiwa 'yar uwarsu baisan lokacinda tafurta cewa

"Billy bana tantama cewa insha Allah ke 'yar aljanna ce, bantab'a ganin wanda zaiyi irin sadaukarwar da kikayi ba kuma yakama bakinsa yarufe duk da matsalolin da yaketa fuskanta da damuwa ba sai ke, Allah narok'eka kada kisake bani damar yin rayuwa aduniya idan babuke 'yar uwata" idonsa na kawowa cike da k'walla tunawa da yanayin da tashiga cikin lokacin don ko yanzuka kalleta zakaga yanda tafad'a, duk da tab'angarenta ita batada wata damuwa irin sosai d'innan don ta dad'e da fawwalawa Allah dukkanin al'amurranta kewar 'yan uwanta kad'ai kedamunta.

Mik'ewa tayi jin ankira sallah tawuce d'akinta sukuma sukayi arwala tare da wucewa masallaci.

Tana gama sallah tanufi d'akin Ummi, zaune ta iskota saman sallaya tagama sallah, gefenta tazauna tana mummurza zoben hannunta kafin tad'ago kai tace

"Ina wuni Ummi" juyowa Ummi tayi had'e da cewa

"Lpy klw, agaisheki mai gayya mai aiki, yau naji duk abubuwan da kikayi wud'anda amatsayina na mahaifiyarki ban cancanci ace najisu daga wajenki ba"

"Don Allah Ummi kiyi hak'uri nayi kuskure, tutuni nayi tir da halina na rashin sanar dake abunda kefaruwa har najawowa kaina shiga cikin fushin ki" tashi tayi tadawo gabanta tare da durk'usawa akan guiwowinta tace

"Umminah kiyimun duk hukunci daya dace dani bisa b'acin rai da bak'in cikin danasa kika shiga a idanun mutane matuk'ar hakan zaisa kidena fushi dani kuma kiyafemun, Ummi nayi hakanne saboda a kullum ke kike fad'a mana muso 'yan uwanmu, kuma muso masu duk abunda muke so fiye da muke sonsa, sannan kika horemu akan kame baki ga yawan fad'ar alkhairin da kayi domin zai iya tafiyar da ladarmu, shiyasa saboda son da nake yiwa 'yar uwata nabar mata wanda zan aura kuma bak'i fad'ar haka saboda kada kimanta ta tab'a ko kuma in rasa k'afar yin hakan" cike da tausayi Ummi ta rungumeta had'e da cewa

"Hakane Bilkisu amma ita uwa abokiyar shawarace bai kamata kib'oyemun ba, kinsan bazan tab'a cewa a'a ba don nima Basmah 'yata ce amma zan d'ora ki hanyoyi mafi sauk'i da zakabi ki sadaukarwa da 'yar uwarki Mahmud batare da kin wahala ba, kuma kinsa mun fuskanci damuwa dani har ke, kidena fad'ar kin sani cikin bak'inciki a gaban mutane Bilkisu, domin farinciki da alfaharin zamowarki 'yatah kawai kika sani, kawai naji badad'i ne ganin har laifinki ya shafeni, shiyasa nake shareki don kiji irin d'acin da nakeji akan shiriyar da dadynki keyimun amma ko kad'an bafushi nakeyi dake ba"

"Ummi natuba kiyi hak'uri kiyafemun hakan bazata koma faruwa ba"

"Shikenan Bilkisu Allah yayi maki albarka, kije kitchen doughnut nanan dana had'a kifara soyawa kafin in ida azkar d'ina, ina fatar kema kinyi ko?"

"Eh Umminah" Billy tafad'a cikin wani courage dajin dad'in ganin yau she's free from any sorrow and annoyed

Bayanta Ummi tabi cike da mamakin yanda gaba d'aya wannan abun bai dami zuciyarta ba balle har ya illatata, godiya tayiwa Allah da wannan baiwa da ni'ima daya yimata nasamu 'yar da tasan daraja da kimar 'yan uwanta da kuma rayuwa sannan taci gaba da azkar d'inta zuciyarta cike da farinciki marar misaltuwa.

Batool kam yanzu anriga da anzama jerin matan aure kuma 'yan gida domin kullum cikin samun kulawa da riritawa take awajen mamy, haka shima dr Ahmad don har yau bai koma wajen aikinsa ba, duk yanda zatayi tayi akan yakoma amma yace ina ba inda zaije sai anyi sati biyu, gashi indai yana cikin gidan babu abunda yafi buk'ata irin yagansa tare da fatimarsa yana tayata aikace aikace shima yana aikinsa ajikinta na 'yan....., zallar shagwab'a take yimasa son rai shikuma yana biye mata, ita kuwa mamy intun safe har zuwa magrib zai kai babu abunda yadameta tana d'aki ita da yaronta Muhib da yayi matuk'ar wayo, sosai Batool ke girmamata tare da bata kulawa don tana gama had'in breakfast d'inta da taimakon dr.Ahmad zata silalikkewarta k'asa tabarosa sama tazo ta gyarawa mamy bedroom d'inta da palour sannan ta karb'ar mata Muhib ta hau sama dashi tayo masa wanka tagyarosa tsaf yana k'amshi sosai sannan takawowa mamy shi,

Yauma kamar haka tana yiwa Muhib wanka taga dr. Sai faman cika yakeyi yana batsewa, yana jejjefa kayans nawasa da tazo masa dasu abakin k'ofar toilet d'in, juyowa tayi takallesa tana murmushi had'e da cewa

"My angel meye haka kakeyi?, kana faman yimasa jifa da kaya, koda yake kaine saya idan ka lalata kasiya masa wasu" irin 'yar k'aramar Ball d'innan ya d'auko ya d'an jefeta da ita adaidai waist d'inta had'e da cewa

"Wato ke tama kayan wayarsa kikeyi ko? to Allah bazan yarda da wannan wayon da Muhib keyimun ba nima yau bazan yarda ba sai kinyimun wanka, ido ta k'walalo waje tubarkallah daidai lokacin tafito rik'e da Muhib tak'are masa wankan tana neman towel d'in da zata nad'esa dashi don ta tsane masa jiki tana dariya tace

"Tab wai wayaga bursili, ina ni ina yimaka wanka dubeka fa?"

"Aww haka kikace?, wato nima ne bursili ko?" Wajen yanufo tare da tad'ar d'uwawun Muhib da take gogewa jiki yanda bazai ji zafiba, ai kuwa Muhib yazata abun wasane ya b'angale masa da dariya sannan ita kuma yace mata

"Ki maimaita abunda kikace ko kema ki karb'i naki hukuncin" sanin abunda zai iya biyo bayanta yasa tace

"Haba my Angel, ai da wasa nakeyi, bari nakaiwa mamy yaron nan sai kaima inyi maka naka kaji ko?" tak'are maganar had'e da yin kiss a 'yan yatsunta ta d'ora masa akan lips d'insa, shima hakan yayi mata tare da cewa ina sonki milkheart d'ita.

Hmmm tsabar rigimar dr. Sai dai da tagama gyare Muhib tsaf sannan ya karb'esa ya kaiwa mamy yadawo suka farantawa juna sosai tare da samun nishad'i, kamar yanda ya buk'ata haka tayi masa tanata nishi yanata yimata dariya saboda yanda tagaji, taimaka mata yayi itama tayo wankan sannan suka fito tana mitar gaba d'aya jikinta ciwo yakeyi, bayan sun shirya tsaf cikin k'ananan kayansu suka dawo palour ya zauna akan 3seater ita kuma takwanta tare dayin matashi da cinyoyinta, soyayya sukeyiwa juna mai cike da tsafta da yarda da kuma kulawa duk da dai hakan bai hana wataran sud'an sab'awa juna wanda nan take kowanensu zai fahimci kuskurensa kuma sai yagyara don gudun sake faruwar hakan"

Mom kuwa tunda tafita takoma part d'inta take kukan jin yanayin da akace 'yarta na ciki, gashi tayi kiran wayarta har tagaji amma bata d'aga ba, lokacin ita kuma Basmah tashiga kitchen don tace yau ita zata d'ora masu abinci da kanta saboda tahutar da Ummansu da kullum saita aiko masu da abincin da zasuci, hakama dady yayita kiran wayar Basmah amma bai samu.

Ana hakane yaya Mahmoud yashigo ya iske mom cikin wannan damuwar, lallaahinta yayi tayi har saida yaga tasaki sannan yake tambayarta cewa "mom ya akayi kika gano cewa saboda Basmah Billy tak'i auren d'an uwa wanda gaba d'aya wlh ni mom tunanina bai tab'a bani haka ba"

"Nima ban saniba son, Basmah ce da kanta tasanar dani haka d'azu da mukayi waya"

"Allah sarki Bilkisu, duk inda d'an uwa ke kaiwa takai, wani zubin har mamakin irin firar da Allah yayi mata nakeyi, yanda tayi wannan sadaukarwar don farincikin 'yar uwarta itama Allah yakawo mata wanda zai sanyata farinciki, kingani mom abunda nake nuna maki ada idan nace 'YAN UWANA NE sai kice a'a ba 'yan uwanmu bane su, yanzu don Allah idan ba d'an uwaba kuma nagartacce wazai iyayin hakan? Akoda yaushe kamata yayi ace idanau iyaye sunada matsala atsakaninsu to kada susa 'ya'ya aciki domin su 'YAN UWANE dabai kamata ace sun sanya masu gaba da tsanar junansu azuciya ba, wlh mom badon kyakkyawar zuciyar Ummi ba da take nunawa 'ya'yanta damu dasu duk abu d'ayane kada sutab'a bari wani abu yarabasu damu da natabbata saidai Basmah ta mutu Billy bazata tab'a barmata d'an uwaba don itama tana sonsa"

"Hakane son ai nagano kuskurene tunkan insan da faruwar haka kuma nayi nadama, kuci gaba da k'aunar junanku ubangiji Allah yatsare mana ku"

"Amin mom bari inje ingaida Ummi sai in wuce, saida safe"


"To masha Allah ya iyalin naka lafiya take ko?"

"Eh mom tacema in gaisheki sosai, kinga namanta"

"Ina amsawa, Allah yayi maku albarka, inkaje ka gaiahemun da ita sosai"

"Zataji insha Allah" yana fita yanufi part d'in Ummi, yasamu tana yiwa Billy tsifar kai.

"A'a'ah Ummi yau tsifar dare kukeyi kuma?" Yafad'a tare da kamo tsoron Billy d'aya yana cigaba da cewa "Ummi najifa kamar anacewa bakyau rage gashi takeyi, Billy idan bak'yason gashin bari nayi cutting d'insa daga nan sai inkaiwa auntynki tak'ara dama gata guidus"

"Tab..aikuwa kamar kayi akunnenta don saina fad'a mata" dariya Ummi tayi had'e da cewa

"To kanwa uwar gami, dako kinyi abun kunya kai gulmar yayanki ga auntynki" sannan takallesa had'e da cewa

"Sannu da zuwa babana ya 'yatah take tana lafiya?"

"Lafiya klw Ummi tana gaisheku"

"Muna amsawa, yau tasha rigimammin bak'i duk sun wahalar mani da ita, ga kuma abun arzik'i data had'osu dashi, Allah dai yayi maku albarka yasa agama lafiya"

"Amin mom, ya akaji da abubuwan da suka faru?"

"To Babanah aikomai yawuce, Allah dai yaba 'yar uwarku lafiya"

"Ai yanzu naje muke maganar da mom tana k'ara yimun bayanin ashe Basmah takirata d'azu tana kuka tayi mata bayanin komai saboda taji ance har yanzu bakudena fushi da my sister ba, shine hankalinta yatashi tace mom tazo tafad'a maku ko kuma ita tazo da kanta tafad'a kowama yaji"

"Allah sarki, ni yanzu condition d'in da take ciki shiyafi damuna babana, wlh jinake kamar inje indubo halin da take ciki"

"To Ummi muyi mata addu'a in sha Allah zata samu lafiya, ai tunda matsalar tunani da damuwa ke haifar da ita natabbata yanzu zata samu sauk'i koda kashi sittin bisa d'ari ne"

"Allah yasa haka?"

"Amin ya Allah, ummi ni zan wuce saida safe, my sister Allah kidena tsifar dare ko kema ki koma gui.." bai k'yar ba ummi tace

"Kama bakinka babana tunda kana da redio maijini akusa da kai, haka kurum tafitineni da marecennan wai gobe gidan Batool zataje tanaso tayo mata kitso, to kannata ne da d'an banzar yawa shiyasa nafara tun yanzu kafin gobe da safe don kada yahanamu aiki"

"To Ummi, saida safe"

"Agaida mani da 'yata inkaje, kafad'a mata nace sannunta da k'ok'ari angode"

"Yaya gudnigth" Billy tafad'a tare da rakasa zuwa bakin k'ofa

"Yawwa our mighty baby sweet dream kinji" sannan ya buga motarsa yayi gida, yana isa yatarar da faraaharsa zaune agaban wasu littafanta tana 'yan dube dube aciki, saye da wani d'an k'aramin mini skirt pitch colour sai wata armless shirt brown tad'an bud'e k'asa kad'an ajikinta, baki k'ofa ya tsaya yana kallon yanda tayi kyau abinta kafin yace

"My faraah am backkk..." Faraaha da batasan dashi awurin tsayeba tad'ago kai tana kallonsa had'e da tasowa cikin murna tana bud'e hannuwa tana fad'in "oyoyo all I have, you are wlcm sweet me" dariya yayi tare da bud'e hannuwa shima yana jiran isowarta sai ji yayi an sakar masa kiss akumatu saboda yanda ya shafa'a da kallonta har ta iso wajen tamaida hannuwanta baya sannan tayi masa kiss bai sani ba, dariya tayi masa had'e da juyawa tana k'ok'arin barin wajen yayi saurin d'auketa ta baya yana fad'in "lallaima yarinyar nan ni kika shammata haka ko?, tab zaki gane kuwa don bazan yarda da wannan wayon ba" bai direta ko inaba sai kan gado tanata faman wutsil wutsil da k'afafuwa tana dariya, ganin haka yasa yafara yimata cakulkuli yana fad'in "zaki k'ara?" Dak'yar tasamu cikin dariyar tace

"A'a" tashi yayi zaune tare da duk'awa akan guiwowinsa saman gadon yasake bud'e hannuwansa kamar yanda yayi d'azu yana fad'in "so am waiting for my welcoming hug" cikeda gajiyar da tayi itama tayi kamar yanda yayi sannan tayi hugging nasa had'e da yimasa romancing kiss, wanda nan take yafara jin yana neman fita hayyacinsa, hannu yakai da niyar jawota ajikinsa sosai tayi saurin jabaya had'e da fad'awa kwance saman gadon fuskarta na kallon ceiling tana dariya, shima hakanan yayi kamar yanda take kwance agefenta tare da juyowa fuskokinsu na kallon juna yace

"Ina sonki my faraah!"

"Nima ina sonka fiyema da sonda kake yimun mijina" nandai kalamai suka antayar dasu duniyar da tazamo sabuwar shiga a tsakaninsu har suke tunanin cewa babu wasu taurari da suka fisu haskawa aciki,

Bayan sun fito wanka suna shan 'yan ruwan tea yaya Mahmud ya kalleta had'e da cewa

"My faraah wai wud'ancan littafan dana isko kintara kinsa agabanki namiye?"

Dafa hannunsa tayi had'e da cewa "sweet me dis week fa zankoma wajen aiki, kuma coliques d'ina nawajen aiki sun kirani sunce akwai seminar d'in da zamuyi nan cikin asibiti don k'arawa juna sani, shine nake d'an biyar littafaina, kasan aikinmu dole sai mutum yanayi yana sake dudduba karatun daya yo a school don gudun wasu abubuwan su kucce masa"

"Ok ..gud matata Allah yakaimu kuma ya taimaka"

"Amin mijina" tafad'a sannan taci gaba da kurb'ar tea d'in dake gabanta, ganin tayi yaya Mahmoud yafara dariya sosai har yana rik'e ciki, tabishi da kallo sake da baki kafin can ya tsaya da dariyar sa yace

"My faraah don Allah kitashi kiyimun tafiyar nan da kikayi ta guragu ranar da muka had'u amatsayin zab'insu jaddi, 'yar harararsa tayi itama tana dariya tare da shafo hancinta da yayi zufa tace

"ita kake so nayi?"

"Eh"

"Shikenan anything for you my husband ni matarka ce babu wata kunya da zanji" mik'ewa tayi ta jefa k'afarta sai kuma ta kwashe da dariya yana tanata kafin ya juya yamaza ya d'auko wani abu acikin wardrobe yana fad'in

"Pls my faraah kiyimun ita nake sha'awar gani yau saboda gobe tafiya nake son yi, inba haka ba kuwa idan naje na gano wata 'yar gurguwa acan Allah sai in aurikketa tayita yimun ina gani, juyowa tayi tab'alla masa harara, shikuma ya d'aga mata kafad'i had'e da mere baki alamar I don care d'innan.

'Bata fuska tayi tare da botsewa tana jefa k'afar tana danne dariyar dake taho mata har ta isa bakin gado yana biye da ita shima yana dariya, tana juyowa tagan haurun da shima yasaka aranar abakinsa yana faman dariya, gaba d'aya suka fad'a kan gadon atare yajawota ajikinsa bayan yacire haurun ya ajiye akan bedside locker yace

"Thank you my faraah, haka nake son mu kasance happy family akoda yaushe har lokacin da muka tara 'ya'yan mu, ina so bisa taimakonki mu gina gidanmu a matsayin Happy home kinji ko?" Ya k'are maganar tare da kissing forehead d'inta sannan ya kashe masu wutar d'akin had'e da cewa "I luv you"itama tace

"I luv you too".

Tunda sassafe faraaha tatashi bayan tayi sallar asuba tahad'a masa breakfast yaci sannan tayi had'a masa lunch shima a lunch box tare da kayansa kala biyu ajikka saboda yafad'a mata yau zaije borno yadubo Basmah da jiki, tana kammalawa suka shiga wanka atare bayan sun fito tana 'yan kukanta akan saita bisa yace

"my faraah kiyi hak'uri in sha Allah nafad'a maki gobe zan dawo kinji ko, ina so indubo 'yar uwata insan halin da take ciki shiyasa amma badon haka ba nida nake ango mezai kaini tafiya wani waje, zance naturo maki Billy ta tagaji kwana idan tsoro kikaji, ko kuma kitafiyarki gidansu papi kafin indawo gobe" dak'yar yasamu yashawo kanta tayarda zataje gidan papi don basuda nisa had'e da cewa

"Shikenan ubangiji Allah ya tsare hanya kuma ya saukeka lafiya, yakareka daga dukkanin sharrin k'arfe dana mugun mutum da aljan kuma yadawo mani dakai lpy"


"Yawwa my faraah amin ya Allah matata, ngde maki sosai da wannan addu'ar Allah yayi maki albarka" k'arfe takwashe nayi ya d'auri niyar kama hanyar zuwa borno tare da shiga motarsa tana maiyi masa bye bye tare da cewa ya gaida mata da Basmah sosai bayan tahad'a mata wani sak'o ga leda tace yakai mata sannan yawuce....


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭
_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____92💎


Kai tsaye asibiti yafara biyawa kafin ya wuce wajen family dr d'insu ya rok'esa akan ya had'asa da likitan dake kula da rashin lafiyar Basmah duk da dai ya sanshi amma saboda yana sauri yasan idan shi yaje ya had'asu zaifi saurarensa cikin lokaci, haka kuwa akayi har office dr jamil yaje yayi masa magana yabashi dama suka shiga, nan yaya Mahmud yasake gabatar masa da kansa sannan ya rok'esa daya sake yimasa bayanin da yayiwa dady akan rashin lafiyar Basmah, kasancewar ya wayesa kuma ga dr. Jamil atare daahi yasa yayi masa bayani dalla dalla yanda zai iya fahimta, nan yayi masa godiya sosai tare da fad'a masa dalilin ciwon na Basmah kuma ya sheda masa cewa yanzu haka wanda ta aura shid'in ne wanda takeso, murmushi dr yayi kafin yace

"I think yanzu everything will be right, tunda dama rashin samun sane ya haifar mata da damuwa har tashiga cikin matsala amma yanzu kuwa tunda gata ga wanda take so ina tsammanin za'a d'an samu sauyi ko kad'anne don bazance zata warke ba saboda yanda ciwon yayi mata tsanani, amma muna fatar zata samu sauk'i koda ba gaba d'aya bane in sha Allah matuk'ar za'ayi k'ok'arin kula da Shan maganunnukkanta bisa k'a'ida tare da yawaita zuwa wurin likita ana duba lafiyarta akai akai"

Godiya yaya Mahmud yayi masa sosai sannan sukayi sallama bayan sunyi musayar lambobin wayoyinsu,

Yana fitowa assibiti yakama hanyar zuwa garin maiduguri lokacin har tara tayi na safe,

Kusan awa biyar yayi akan titi yana faman tafiya kafin ya isa, faraaha kuwa tayi kiran wayoyinsa har tagaji amma bata samuba saboda gaba d'aya kashesu yayi don gudun kada su d'aukar masa hankali yana driven, hakan yasa dole tahak'ura tafara tattara abunda zatayi amfani dashi ta tafiyarta gidan papi tana kumbure kumbure ita ala tilas taji haushi,

Ab'angarensa kuwa yana isa kai tsaye gidansu ummah yafara wucewa, bakinsa d'auke da sallama ya shiga cikin cikin palourn lokacin ummah tafito nafitowa daga kitchen rik'e da plate d'in abinci tana k'walawa junior kira.

"Ah lale marhaban da baban bak'o, Mahmud kaine yanzu atafe?" K'arasowa cikin palourn yayi yana murmushi had'e da cewa

"Eh Ummah mun sameku lafiya?"

"Lafiya klw, saukar yaushe haka yaronah"

"Yanzunnan ummah" Yana rufe baki yaji anfad'o masa ajiki ana fad'in "oyoyo yayan kd"

"A'a junior daga ina kafito haka banga shigowar kaba saidai naganka anan" yaya Mahmud yafad'a tare da mik'a masa hannu suka gaisa yana kallon ummah dake faman harararsa sannan yace

"Ina nan bayan kujera nab'uya ummanah zata yimun d'ure, yaya don Allah kace kada tabani bana sonci nak'oshi"

"Au! dama ashe kana jina inata faman kiranka shine ka k'yaleni?, Maza zonan kazauna kaci abinci kafin yanzunnan in sab'a maka, jimun yaro so kakene yunwa tayi maka illa" umma tafad'a tana mik'o masa plate d'in abinci dake hannunta. Kallon yaya Mahmud yayi ya tab'e baki zaiyi kuka yayi saurin cewa

"A'ah yaron dady, idan kayi kuka bazan baka abunda nazo maka dashi ba kaji ko?"

Abincin yakarb'a hannun Ummah tare da d'orasa saman cinyarsa yasa spoon yana basa abincin abaki, da wayo da wayo yayita tura masashi har saida ya canye plate d'in tas sannan ya zuge zip d'in jikkarsa daya zo da ita yaciro masa jirgin wasa da k'atuwar ledar chocolate ya mik'a masa yana fad'in

"Kadinga cin abinci sosai ni kuma zandinga kawo maka irin wud'annan aduk lokacin da zanzo kaji ko" cike da jin dad'i junior ke tsalle Yana fad'in "Thank you yaya, Ummah kinga kayana kuma bazan sammaki ba,

"Dallah ja can, kazo ka wahalshemun da yaro daga isowarsa, fad'amun yanzu waya cinye abincin tunda kace bazaka ciba kak'oshi" wucewa yayi abunsa yana b'allar ledar chocolate d'in takalli yaya Mahmud sannan taci gaba da cewa

"Duk kai ke sangarta k'annen nan naka shiyasa sukuma sukeyita wahalsheka"

"Ummah meye abun wahalshewa anan? To idan banyi masuba ummah wazanyiwa? 'YAN UWANA NE fa.." bata tsaya jiran tajira ya ida fad'aba don tasan ta tsuniyar gitso bata wuce k'ok'i taje tad'auko ruwa masu sanyi a fridge tare da cup takawo masa agabansa ta aje tana cewa

"Sannu da hanya ga ruwa kasha ka kwaso rana, gashi baka fad'awa ummar taka zuwanka ba balle tayi maka tarba ta musamman" gorar ruwan yad'auka yana murmushi ya aza abaki saboda k'ishirwar da yakeji da zafin ranar dake bugunsa bai sauke taba saida ya shanyesu tas sannan ya ajiye gorar had'e da cewa,

"Afuwa ummanmu, wlh babu wanda yasan da zancen tafiyar nan inba 'yarki ba, yanzu nake cewa bari inkira dady infad'a masa cewa gani nan tare dake nazo gaisheku"

"Anya Mahmud wannan tafiyar tawace kuwa?" Sosa 'yar k'eyar kansa yayi kafin yace

"Sosai kuwa ummah ai duk tafiyar da zatasa ind'auko k'afafuwa inzo har garin borno to don kine za'ayi saboda kece dalili"

"To ai shikenan tunda kace haka, yanzu kaje kawatso ruwa saika fito kaci abinci kahuta, bari naje nakawo maka makullan d'akin d'an uwan naka"

"Ummah d'akin dai junior, aishi mun yayesa"

"Rufamun asiri kada yajika, ai yace shikam bai yarda da hakaba, yanzu haka d'akinnanan kamar yanda kasanshi, hatta kayansa na sawa da wasu abubuwa duk sunanan, shiyasa duk bayan kwana biyu dole sai nasa anje angyaro masa d'akin, gudun kada datti yataru aciki" dariya yaya Mahmud yayi

Please Login or Register in order to submit comment