Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Bazan manta dake ba Aunty nah *AISHA MATAZU* gaisuwa mai yawa da fatar alkhairi agareki bisa yanda kike bibiyar wannan littafi d'aya bayan d'aya, ngd sosai Allah yabar tare, am really appreciate it🀝❀_

_*INNAKA MAYYITUNN WA ANTUNN MAYYITUN*_βŒβœ–

_*INNAKA MAYYITUNN WA INNAHUM MAYYITUN*_ βœ”πŸ’―
_Apage d'in d'aya gabata hannuna yayi kuskuren rubuta wannan ayaπŸ‘†dake sama, don haka nafarkon kuskurene na biyun shine daidai Ina fatar Allah kayafe mana kurakuranm kabamu ikon gyarawa_

πŸ’ŽPage_____100πŸ’Ž


Ba family d'in alhaji Bashar mai furniture d'ai ba mutuwar Basmah ta tab'a hatta ilahirin al'ummar dake duniyar da suke ciki mutuwarta ta girgiza, kasancewar dady mutumne mai kyakkywar mu'amala da kowa yasa tako ina mutane tururuwa sukeyi wajen gaisuwar 'yar tasa, iya rashi kam sunyisa amma gaba d'aya sun tattara sun barwa Allah daya basu ita sun bita da dad'ad'an addu'o'i domin sune tsantsar soyayyar da zasu nuna agareta.

Sosai sunanta da aka mayarwa jaririyar da ummi tahaifa ya tab'awa kowa zuciya, baran ma Ummi da gaba d'aya sai abun yadawo mata sabo tunawa da shekarun baya da Basmah tayi zama hannunta lokacin da aka samu cikin Batool kafin ayayeta sai aka barmata sukuma mom da dady suka bar k'asar, gaba d'aya kamannin babyn sak ita alokacin haka sunan ma d'aya, ai nan take kukanta ya tsananta tanaji inama Allah zai sake bata damar rayuwa mai tsayi tare da wannan Basmah d'in har zuwa girmanta da gaba d'aya ta tarbiyantar da ita a yanda tsarin rayuwar Basmah take saboda ta dinga d'ebe masu kewar d'abiunta.

Ko kad'an dady bayada sha'awar zaman makokin da akeyi, shiyasa yana fitowa bayan angaggaisa wud'an da basu samu damar yin jana'iza ba sukayi masa gaisuwa sannan ya mik'e yayi godiya sosai bisa kulawa da lamurransa da 'yan uwa musulmi sukayi daga k'arshe yace

"Allah shine yabamu wannan 'ya kuma yakarb'i abussa, zaman da zamuyi anan bazai dawo mana da itaba, don haka kowa zai iya tafiya wajen al'amurransa, koba komai yin haka a shari'ance kuskurene, saboda haka babu amfani ga wannan zaman illa muyi mata addu'a Allah yajik'anta kuma ya gafarta mata, Mungode Mungode Allah yabar tare, yajik'an wud'anda suka rigamu gidan gaskiya" duk mutanen dake wajen suka amsa da "amin" tare da mik'ewa suna saka takalummansu d'aya bayan d'aya suna mik'a masa hannu sannan duk suka watse, wajen ya rage daga dady sai 'yan uwansa da Mahmud da mahaifinsa sai kuma yaya Mahmud da dr Ahmad, suma cewa dady yayi kowa yaje ga harkar gabansa saboda zaman bayada alkhairi wani zubinma tak'urawa ne, haka kuwa akayi kowa ya tafiyarsa dady da Mahmud da kuma yaya Mahmud kad'ai yarage suma d'in saida aka nuna masa cewa bai kamata wajen yazama ba kowaba saboda masu zuwa gaisuwa sannan ya amince suka zauna amma shi shigewarsa yayi cikin gida duk wanda yazo sai yasa ashiga dashi su gaisa yafito yatafiyarsa, hakama cikin gida yasa Umma ta sallami duk matan da sukazo gida ya rage daga su mom sai ita dasu Batool.,

Basmah kam tayi mutane sosai don har akayi sati mutane nashiga wajen gaisuwa kuma hakan bai hana satin na zagayowa ba dady ya yankawa little Basmah dabbar sunanta tare dasa akayimata aski kamar yanda musulunci ya tanada, saidai babu wani taro ko shagali da akayi saboda yanayi da alhinin da suke ciki, hatta naman acan family house d'insu dady aka aika dashi matan yannensa suka gyara, little Billy kuwa tuni akayi shawarar had'awa Ummi ita tashayar dasu su biyu wato little Billy da little Basmah, sosai suke samun kula wajenta duk da kasancewar bawata cikakkiyar lafiya ke gareta ba hakan baisa tarasa ruwan mono sosai ba, wani zubin har isarta yakeyi sai tayi masu da gaske sukesha saboda sun k'oshi,

Mahmud gaba d'aya ya susunce kamar wani marar amfani, sosai yaji mutuwar matarsa duk dako bawani dogon zama da ahak'uwa sukayi da itaba, yaso ace ambari Umma taje masa da 'yarsa sai adinga bata madara kodon yadinga ganinta yanajin sanyi amma anriga da anfi k'arfinsa dole yahak'ura, ranar da zai koma borno kuwa haka mutuwarta ta koma masa sabuwa, kuka yayi sosai little na ahannunsa sannan yayi mata addu'a tare da fatar Allah yajik'an mahaifiyarta, Batool kuwa har asibiti saida takwanta daga k'arshe dai anata yimata addu'o'i sannan aka samu takoma Batool d'inta ta da, amma gaba d'aya kuzarinta da walwalarta yaragu ba kamar da ba.

Koda Mahmud ya koma gida kasa zama yayi cikin gidansu ya tattara inasa inasa yakoma gida gaba d'aya, tabbas rashin mata ko miji wata fitinace arayuwa koda kuwa basa son juna balle shida bazaice baya son Basmah aransa ba, yanayin zaman da yayi da ita da irin hak'uri da kulawar da take basa uwa uba soyayyar da takeyi masa su suka taru waje d'aya sukayi tasiri azuciyarsa har yafara k'aunarta, abinci ma wannan sai Umma tayi dagaske da kuma rarrashi da ban magana yakeci,

Bayan rasuwarta da wata d'aya wajen aikinsa suka buk'aci daya tattaro masu inasu inasu idan bazai iya aikin ba yabasu sun sallameshi, hakan yasa yagyara yatafi yabasu hak'uri sannan yak'uduri watsar da komai aransa ya amshi rubutaccen al'amarin da Allah ya wanzar akansa yaci gaba da aikinsa acan reshen kamfaninsu na India da suka turasa wanda dama dak'yar yasamu ya kuccike lokacin daya dawo har Yana zancen zai rok'esu da suyi masa transfer, amma faruwar haka yasa yaji gaba d'aya baya buk'atar yaci gaba da zama annan shiyasa ya amince da komawarsa.

Bayan sati d'aya ya gama shire-shiren komawarsa yaje har k.d yagano little d'insa da tad'anyi wayau sosai gashi tayi k'iba saboda yanda nonon Ummi yakarb'eta. Hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba kuma yasamu natsuwa sosai aransa, rik'eta yayi ga hannu yasata agaba yanata faman yimata suruttan daba fahimta take yiba har yagaji sannan yamaida ita wajen Ummi yayi masu bankwana yawuce, saida yabiya ta mak'abartar da aka rufe Basmah yayi tsaye yana kallo, jiyake kamar Basmahrsa zata dawo, addu'a yayi mata sannan yabar wajen yana hawaye, Billy ma tuni takoma makaranta yayinda ko sau d'aya tunani da kewar 'yan uwanta basu tab'a barin taba, kullum cikin waya take da Batool idan bata kirata ba to ita zata kirata, akoda yaushe jisukeyi tamakar suma mutuwar zata rabasu shiyasa basa iyayin fiye da awa uku batare da sunji muryoyin junan suba.

A b'angaren malam jika kuwa ya kasa ya tsare yasa Billy agaba har saida tafara saurarensa duk dako ba sonsa takeyi ba,

Babu ranar da zatazo ta shud'e batare da yaya Mahmud yayiwa Basmah sadaka ba da niyar Allah yakai ladan agareta, hakama Batool duk ranakun alhamis da juma'a cikin yimata sadaka take, musamman dady ya gina rijiya da sunanta matsayin sadaqatujjariya agareta, a gaskiya tsayawar fad'ar yanda wannan family suke k'aunar junansu b'ata lokacine domin azahirine Basmah tarasu amma abad'ini ita rayyayyace atare dasu don akoda yaushe addu'o'insu da sadakokinsu natare da ita.

Mahmud kuwa tunda yakoma India kimanin shekara d'aya kenan bai dawoba saidai tawaya, sau da yawa idan yanaso yaga little d'insa saidai ya kira Mom ko Ummi ta vedio call anuna masa ita don da ita har little Basmah sun wayau sosai sun iya tafiya, idan kagansu zakayi tunanin cewa tagwayene, wanda da duk yasan tashin Basmah da Billy lokacin da suna k'anana babu abunda ya banban tasu dasu little. Mom kuwa bazaka iya tantancewa tsakanin little Billy da little Basmah kowa tafi so, kowace jinta takeyi har tsakiyar ranta ga wata soyayya mai tsanani da shak'uwa a tsakaninta dasu, duk wata kicaniyarsu da renonsu ita keyi, inka ganesu wajen Ummi to tabbas vaccine zasuyi ko kuma zasu sha nono ne, haka ma Umma takan d'an zo can baka rasaba taduba jikanyar tata sannan takoma wani lokaci ma tare suke zuwa da alhaji shima ya dubata,

Ganin gaba d'aya Mahmud baya maganar aure gabansa gashi har ana shirin yaye little Billy yasa Umma takira dady awaya, bayan sun gaisa tace

"Dama yaya maganar d'an kace, kaga tunda Allah yakarb'i Basmah har yanzu ya kasa samun natsuwar da zai komayin batun wani auren, gashi yanzu ana batun yaye su little kaga akwai buk'atar ace yasamu wacce zata kular masa da ita, bawai don bani iya rik'eta a hannuna ba amma nafi sha'awar ace tana hannun ubanta ko ita yadinga kallah yaji sanyi aransa, shine nace idan Bilkisu bata tsayar da miji ba, mezai hana amayar da wannan alak'a da zumuncin da tun farko akaso yi da ita, tunda dama tana sonsa kuma shima yana sonta rabon wannan yarinyar da aka haifa ya hana aurensu"

Shiru dady yayi yana nazarin maganarta kafin yace

"Hakane maganarki hafsatu amma wani hanzari ba gudu ba, shin munada tabbaci akan cewa har yanzu suna k'aunar junansu? Kada azo ayi maganar auren kuma d'aya daga cikinsu ya bijiro da wani abu daban sannan kinga ita Bilkisu yanzu haka tana makaranta kinsan karatu takeyi na medicine kuma shekara bakwaine zatayi kafin tak'are gashi sai yanzu suka shiga shekara tabiyu, kina ganin anya zasu dai daita kuwa don kinga idan akace ak'ire mata karatu inaga kamar ba'a yimata adalciba indai ba ita tabuk'aci haka ba"

"Gaskiyane yaya, ni banida haufi ko shakku akan har yanzu suna k'aunar junansu kuma bana tantama akan cewa a wannan karon wata matsala zata iya bijirowa, maganar karatunta kuma yaya tunda batayi nisa ba idan ta amince zata iya hak'ura suyi aurensu inyaso sai yasama mata gurbin karatu acan india tunda shekara biyar zaiyo kaga yayi d'aya yanzu saura hud'u, kafin sudawo natabbata takammala karatunta acan ko kuwa?"

"To bantari lumfashin kiba koma meye yanzu mufara tuntub'arsu muji ra'ayinsu, idan sun amince kinga babu wata matsala kome annan zasu kai k'arshe tsakaninsu"

"Shikenan yaya Allah yatabbatar mana da abunda yafi zama alkhairi kuma yagafartama Basmah da kulluhin musulmi baki d'aya" murmushi dady yayi saboda yanda tafahimcesa kafin yace

"Amin ya Allah hafsatu manga shiyasa nake jinki araina, kinada fahimta sosai, na tabbata da kece gurbin muzammil fushi zakiyi kiga kamar bani so ink'ara had'a jini dake don narasa Basmah"

"Haba yaya ai babu wannan tunani araina kwata kwata, koda Bilkisu tasake k'in amincewa da auren Mahmud akaro na biyu babu abunda zaisa nayi fushi don nasan babu mai auren matar daba tasaba, balle ina fatar Allah yasa ta amince don nasan shi har yanzu yana k'aunarta, kuma kaga ita kad'aice zata auresa munsamu natsuwa da kwanciyar hankali akan tabbacin tarbiyar little da kuma kula da ita, shiyasa nayi kwad'ayin hakan"

"Hakane hafsatu Allah yasa mudace"

"Amin ya Allah yaya sai anjima"

Suna gama waya da dady takira lambar Mahmud, lokacin yana kwance yana tunanin yanda gaba d'aya Billy tasharesa tafita lamarinsa ko tunawa dashi batayi balle yasamu kira daga wajenta, watakilma tuntuni tasamu wani wanda yashafe mata soyayyarsa azuciya sai ga kiran Ummansa yashigo, hannu yamik'a ya d'auko wayar tare dayin rejecting call d'in sannan shi yayi calling d'inta back saboda anfi sauk'in cin kud'i.

"Hello Ummana, barka da safiya?" Cike dajin dad'in muryarsa da taji tace

"Yawwa my son, kana lafiya?"

"Lafiya klw Umma yasu little?"

"Aikuwa lafiya lau take itama shekaranjiya nadawo dubata na isko har ana batun yayeta"

"Kai Ummi yanzu harsu little sun isa yaye? don Allah Umma kice Ummi tabarsu ko shekara d'aya su k'ara" zaro idanuwa Ummi tayi waje had'e da cewa

"Sannunka shugaban 'yan wauta, yanzufa ana maganar shekararsu d'aya da wata shida aduniya kake zancen ak'ara shekara ko don bakai ake tsutsa ba, kuma banda shirme irin naka waya fad'a maka cewa anayin fiye da shekara biyu ana shayar da yaro?" d'an yatsina fuska yayi had'e da sosa k'eyar kansa kafin yace

"To Umma don Allah abarsu ko shekara biyunne suyi, wlh tausayin little nakeji sosai"

"To shugaban 'yan iyayi, ni rufemun baki ba wannan ne yasa nakirawo kaba, to waye baya tausayin nata inba dai rashin kunya irin taku ta 'ya'yan zamani ba" murmushi yayi had'e da jinkunya yana d'an shafa kansa kamar yana gabanta yaji tace

"Wai kai har yanzu tunanin naka bai baka kafiddo da matar da zaka auraba?, gashi kasan dole ana yaye yarinyar nan maidota hannunsu ya kamata ayi tunda munada buk'atarta"

"Umma wazan aura tunda Bilkisu nasan yanzu bata sona, kuma ni agaskiya bazan iya jurar auro wataba tazo tana cutarmun da yarinya, inda ace Bilkisu zata amince ta aureni da nayi auren don ni har yanzu ina matuk'ar sonta sosai fiyema da wanda nakeyi mata ada, amma tayama zanyi tunanin haka bayan tashareni azuciyarta ko tunanina batayi balle takirani, koda yake ma taya za'ayi ta aureni yanzu wacce tun farkoma tak'i aurenba balle yanzu da zataga har inada 'ya" sosai Umma taji dad'in kalamansa kuma tasamu amsar tambayar da tayi niyar yimasa, amma saita sa aranta bari ayi masa bazata, don haka sai tak'i sanar dashi komai tace

"Allah yasawak'e, amma bazamu zauna dakai ba aure ba don tak'amar cewa Bilkisu bazata iya aurenki yanzuba wannan yarage naka, nagaji da kullum ina yimaka zance d'aya amma kak'i kayi abunda ya kamata, to nida kaina zan samo maka mata awannan karon wacce zata iya kula mani da kai da kuma 'yarka, bazan zauna zaman jiranka ba nafad'a maka" Umma tafad'a da d'an fad'a fad'a,

"Umma kiyi hak'uri amma wlh ni babu wacce zuciyata ke k'auna idan ba Billy ba, don Allah kada ki auro mun kowace yarinya don bazata samu kulawa awajena ba"

"Aw ni kake gayawa haka, to shikenan kabari idan na auro maka ita ka kasheta kaji ko?" Umma tafad'a tare da kashe wayarta alamun kamar tayi fushi, jefa wayar yayi bisa gado kafin yasa hannuwansa yarik'e kansa dasu, wasu hawayene suka ziraro masa a idanuwa kafin yace

"Shikenan ni rayuwata ahaka zata k'are burina bazai tab'a cikiba?, to wlh duk wacce tayi k'ok'arin shigowa rayuwata sai tayi nadama itama arayuwarta, idan nayi biyayya na kyautata awancan auren to awannan akasin haka za'a gani don wancanma saboda 'yar uwatace shiyasa na rungumi qaddarata har tayi nasara akaina, amma wannan karon zan yak'i qaddaratane har sai nayi nasara akanta" jawo wayarsa daya jefa kan gado yayi zuciyarsa nak'una ya lalubo lambar Billy batare da wani shayiba ya danna mata kira, sau uku tana ringing amma bata d'agaba lokacin tana class suna lecture, jiyayi kamar yafasa ihu zuciyarsa natafarfasa tare da sak'a masa cewa da gangan tak'i d'agawa saboda ta dena sonsa, lambar alhajinsa yakira kamar zaiyi kuka, ringing d'aya tayi ya d'aga had'e da cewa,

"Hello my son kagama fushin dani?"

"Am sorry alhaji, ai bazan iya fushi da kaiba, kawai nad'an shiga damuwa ne"

"Mahmud wannan wace irin rayuwace, kai kace da zaran anyi maka maganar aure saika shiga damuwa ko kayita faman fushi, shin haka kakeso ka k'are rayuwarka ba aure don matarka tarasu?, Allah fa yabaka ita, don me da bazaka hak'ura ba" haba ina ruwan zafi Mahmud yafad'a tunda Alhaji yatayar masa da maganar da sukayi shekaran jiya bayan shi so yakeyi ya taimaka masa yasa Umma tajaye qudurin da tayi na auro masa matar da bai sani ba kuma baya so, cikin damuwa yace

"Alhaji ayi hak'uri in sha Allah ina dawowa komai zaizo k'arshe amma don Allah karok'amun Umma kada ta auro mun wacce bana so don Allah alhaji"

"Aw ashe shiyasa kakirani? Madallah da wannan hukunci data yanke aini yakamata tuntuni inyi wannan tunanin had'aka da wata amma koyanzu takwana gidan sauk'i, zan iya hana Ummanka ta hanu duk da zamanta kaifi d'aya amma bazanyi haka ba saboda hukunci data yanke yayi mun daidai, kuma wlh kaji na rantse maka nan da wata d'aya kadawo ko kuma in sab'a maka"

"Alhaji, alhaji.." Mahmud kefad'a amma yaji har ya kashe wayars, jefar da tasa yayi ak'asa cikin b'acin rai tayi d'ai d'ai kota kanta bebi ba ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa idanuwansa arufe yanajin kamar zuciyarsa zata fito.

Suna gama lecture da sauri Billy tafito, husnah nabiye da ita abaya tana tambayarta ko lafiya, k'ok'arin fiddo wayarta tayi daga cikin jakarta cikin fara'a da jin dad'i saboda tuntuni taci alwashin cewa matuk'ar Mahmud bai kirataba ko soyayyarsa zata kasheta bazata kirasa ba balle har tanuna masa cewa babu abunda ya canza azuciyarta game da k'aunar da takeyi masa ada kodon takula da d'iyar 'yar uwarta data bata amana, sai gashi yau yakirata har sau uku saboda malami dake cikin class ta kasa d'agawa, kallon husnah tayi bayan taciro wayar tana murmushi tace

"Husnah yayanah ne da nake baki labari yakirani my love is back to me again" batajira me husnah data bita da kallo tana dariya zatace ba tayi calling nasa back, amma kash har sau uku itama tana kira lambarsa akashe saboda yanda tayi d'aya d'aya ak'asa daya bugata, cike da damuwa tajuyo tana kallon husnah kafin tace

"Kinji kuma wayar tasa akashe, kodai soyayyarsa tasa yafara yimun gizo har awaya husnah" tak'are maganar had'e da mik'a mata wayar, karb'a tayi tareda duba jerin missed calls d'in dake cikin wayar sannan tad'ago kai tace

"Billy ba gizo bane, wlh shine yakira har sau uku, koba shi kika sakawa *Abban my baby*"

"Eh shine.." tafad'a tare da mik'a hannu zata karb'i wayar, ai kafin tarufe baki sai ganin mutum tayi yaci gabanta, cikin k'ufulewa da b'acin rai dake cikin zuciyarta ta d'ago kanta, malam jika tagane tsaye yana faman sakar mata murmushi, juyar da kanta gefe tayi tare da rab'asa zata wuce don bataso ta jid'ar masa damuwar da take ciki akansa, sake tare gabanta yayi yana fad'in

"Haba gimbiyata, ya zaki rab'ani kiwuce bayan kinsan kin fara saba mani da soyayyarki da kuma kulawa" wani iska billy taja a hancinta sannan tafurzsa awaje tare dasa hannu d'aya ta dafe k'ugunta dashi, husnah naganin haka tabar wajen aranta tace

"Tab..yau qawata zatayi tsiyar, malam jika yau kam zaka ji zafafan kalamai" ai bata gama tunanin da takeyi ba taji cikin b'acin rai Billy nafad'in

"Wait malam jika kake ko waye? lemme end it here, i don't bloody care who ever are you! don Allah kak'yaleni, kabarni haka kanajina ko? Haba! Kai wane irin mutumne fisabillillahi da bazaka fahimta ba? duk hanyar da zanbi inga cewa mun rabu lafiya batare dana cutar da kaiba nabi don karabu dani cikin sauk'i amma kak'i fahimta, kasan komeye dalili kuwa, saboda nasan zafin so da kuma illarsa, nasan yanayin da zuciya keshiga idan tana son abu takasa samunsa, bari nafad'a maka gaskiya wannan zuciyar tawa mutum d'aya na tanadawa ita aduniya," tak'arsa maganar tana nuna saiti zuciyarta sannan taci gaba da cewa "duk da ada inada tabbaci akan bazan tab'a samun saba saboda nisan da yayimun hakan baisa daidai da point d'aya na k'aunarsa yafita acikin zuciya taba shin kana tunanin cewa yanzu da nake da tabbacin zan samesa in Allah ya yarda sai kuma nacire k'aunarsa acikin zuciyata nasaka taka?, Malam jika zanfad'a maka gaskiya koka yarda ko karka yarda shi nake so kuma shine farincikina sai in kuma idan Allah yaso ya sake jarabtata akaro nabiyu shi zaisa naso wani bayan shi, kuma koshi inda tabbacin kawai gangar jikinace zata sosa idan har hakan tayuyu amma zuciyar Billy bazata tab'a son saba" ko kad'an bata damu da mutanen dake gefe gefensu sun zubo masu idanuwaba taduk'a gabansa tare da cewa

"Narok'eka da kayi hak'uri kabarni, kayi hak'uri ka gwada amsar wannan jarabawar da Allah yayi maka kamar yanda nima nayi, natabbata Allah zaiyi maka musanya da wacce tafini zama alkhairi"

Cikin b'acin rai malam jika yace

"Shikenan kitafi nabarki Billy, yazan da raina, da nad'auka kece rabin jikina, amma yanzu nayarda cewa yaudarata zuciyata keyi, duk da haka bazan manta dake ba dare ko da rana, Amma Ina rok'on Allah daya musanya mani da wata Bilkisu wacce tamallaki dukkanin halaye da kyawon sura irin taki, ngd da gaskiyar da kika fad'amun, Allah yacika maki burinki"

Mik'ewa tayi had'e da cewa "Amin ya Allah nima ngd" sannan tajuya tanufi inda husnah take can gefe atsaye suka wuce, shikuma yafi k'arfin minti biyar atsaye wajen kafin yajuya ransa a dagule ya shige motarsa yabar makarantar aguje ransa na suya, baki husnah tasaki tana kallon Billy da har yanzu fuskarta babu annuri ita kuma tayi kamar bata gane taba, yini ranar Billy tayi tana trying no Mahmud amma bata samesa ba, jitayi gaba d'aya ranar haushin kowa da komai ya isheta, komai baya yimata dad'i hakan yasa tahad'a kanta da guiwoyinta tanata kukan da batada merarrashinta akai,

Jin k'arar wayarta yasa tayi saurin d'ago kanta tare da jawo wayar dake saman pillow tad'aga batare data tsaya duba sunaba cike da fatar Allah yasa Mahmud d'inta ne, muryar dady tajiyo tadaki dodon kunnenta yana fad'in

"Bilkisu" da suri tasa hannu tagoge hawayen idonta tare da daidaita muryarta tace

"Na'am dady inawuni? Barka da marece, anwuni lafiya?"

"Yawwa Bilkisu lafiya klw, ya kike ya karatu?"

"Alhamdulillah dady, yasu little da su mom kowa lafiya?"

"Lafiya lau, Allah ya taimaka, akwai wata matsalane?"

"A'a dady babu ko kad'an?" Ta aje maganar tana k'ok'arin danne damuwarta

"Shikenan kiduba za'ayi maki aleart naturo maku duba arba'in keda 'yar uwarki zainab koda kunada wata matsalar kinji ko?"

"To dady mungode Allah yak'ara bud'i da d'aukaka kuma ya tsawaita mana rayuwarka cikin amincinsa" lumshe idanuwa yayi don yanajin dad'in wannan addu'ar da takeyi masa kafin yace

"Amin ya Allah bikisu Allah yayi maki albarka" ta amsa da "Amin" har zai kashe wayar da sauri tace

"Dady yasu Umma da yaya Mahmud? Kuna waya kuwa?" Murmushi yayi had'e da cewa

"Lafiya klw, yawwa dama nace yakamata idan kinsamu wanda kikeso kiturosa atsayar maki, saboda bazai yuyu nace sai kin kammala karatunki ba, shekara bakwai ba wasa ba, kuma nasan dak'yar idan zaki amince ki auri zab'in da kika kawo farko tunda da bakinki kikace bazaki samu farinciki idan kika auresa ba saboda bakya sonsa balle nasaran zaki mayewa takwararki gurbin yayarki, shiyasa ma nayi saurin da katar dashi daya nemi kawomun maganar?" Wani irin farincikine ya lullub'e Billy, kenan yayanta har yanzu shima yana sonta?, kenan wannan maganar tasa yakirata suyi d'azu shine har dady kenema ya maida hannun agogo baya, turo d'an bakinta tayi kafin tace

"Nifa dady babu wani wanda nake so, kuma da bakina ban tab'a furta cewa bana son d'an uwana ba, kawai dai nace.." sai kuma tayi shiru takasa k'arasawa, dariya dady yayi had'e da kashe wayarsa don yasamu amsarsa cikin tak'aitaccin lafuzzan da tayi k'wara biyu "Allah sarki, haka shi son gaskiya yake, baya tunanin komai kuma baya b'oyuwa aduk lokacin daya motsa, tana son sa amma bazata iya furtawa ba, zata auresa amma bazata fad'aba, tsarin da Allah yayo na sake had'uwarsu a inuwa d'aya yasa ya Allah ya amshi ran 'yar uwarsu, ikon Allah kenan babu yanda bayayi" dady yafad'a yana jinjina al'amarin,

Dariyar itama tayi had'e da rungume wayar, saiga zainab da bata jima da fitaba tabarta zaune wajen tana kuka tashigo, binta tayi da kallo had'e da cewa

"Tofah! Mai kuka kuma takoma dariya, fad'amun insha Aunty Billy" pillow Billy ta d'auko tajefeta dashi tana dariya had'e da saukowa kan gadon tace

"Kan munafiki baya gashi, wato d'azu baki tambayi meyasa nake kuka ba kika tafi kod'an rarrashinnan babu sai yanzu kiwani tsuromun idanuwa kina tambayar meyasani dariya to koma meye baza kijiba" tamitsile mata ciki tare da juyawa tafice tanufi d'akinsu husnah tan tsallen farinciki, b'ata rai zainab tayi tare da shafa inda tamitsile mata ciki kafin tace

"Yo waya kaini tambayar dalilin kukanki balle har nima kisakani kukan, kada Allah yasa kifad'i koma meye intayi tsami maji" sannan ta kakkab'e gadonta tahaye tare da jawo wayarta takira masoyinta Khalid abokin Dr.ahmad don tuni suma sun jone.

Bayan kwana biyu Umma takira dady tasanar masa yanda tayi da Mahmud, dariya yayi sosai kafin yace

"Yara kenan?, Ai kinji kinji yanda nayi da 'yar taki itama" nan ya labarta masa shima yanda sukayi da Billy sunata dariya daga k'arshe dai taba Alhaji mijinta waya sukayi magana da dady inda nan take suka tsaida maganar aurensu nan da wata d'aya idan Allah ya kaimu kenan lokacin da zai dawo, cikin sati biyu iyayensa suka sake dawowa Suka nema masa auren Billy wajensu Alhaji kabiru tare da sadaki, Mahmud kuwa nacan har zazzab'i yayi, bai koma bi takan wayarba shiyasa baisan abunda ake shiryawa ba, Batool da yaya Mahmud kuwa ba k'aramin farin ciki sukayi ba lokacin da sukaji wannan maganar, dangi da 'yan uwa kowa sai sama Billy albarka akeyi data amince zata auri Mahmud, Umma da alhaji ko sunyi nemansa har sungaji wayarsa akashe wanda

Please Login or Register in order to submit comment