Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwaranya a fuskarsa, ahankali yafurta "why Billy?.. Meyasa kika yimun haka?"

Jin abunda yace yas basmah kuwa da tuni tafarka daga baccin daya d'auketa saboda hawayensa da suka d'igomata a fuska, tayi saurin sake runtse idanuwanta tana fad'a aranta cewa "Kayafemun yaya duk laifina ne yajanyo haka" har suka isa garin borno misalin k'arfe 10:30pm nadare babu wanda yakoma cewa komai, gaba d'aya kowanensu da abunda yake kitsawa cikin ransa da kuma zuciyarsa dan gane da auren nasu, wanda za'a kira da auren qaddara ko kuma auren d'ibar fushi, kai tsaye yaya Mahmud pilot yacewa wanda ketuk'asu ya wuce dasu asibiti, yayinda yakira dadynsa yace su zasu iya wucewa gida shizai tsaya asibiti aduba 'yar uwarsa.

"To shikenan my son Allah ya sawak'e, sai kun iso" gaba d'aya alhajinsa yaba sauran motocin umurni suwuce can gida kai tsaye kafin su iso, don shima binsu zaiyi zuwa asibitin,

A wata 'yar madaidaiciyar asibiti da aka rubutawa _HAIFA SPECIALIST HOSPITAL_ wacce take mallakin garince a k'ark'ashin gwamnatin jahar suka shiga motar dady na biye dasu abaya, sunayin parking yad'an bubbuga gefen fuskarta kad'an da yake tuni takoma baccin nata dake cike da damuwa, ahankali tabud'e idanuwanta sannan tamik'e daga ka cinyarsa da take kwance cike da jin kunya,

"Sorry yaya nagajiyar dakai ko?" Tafad'a kanta ak'asa,

"Bakomai" yafad'a had'e da bud'e gambun motar yafito ya zagaya tabaya ya bud'e mata gambun gefenta had'e da mik'a mata hannu, kallon ginin wajen tafarayi d'aya bayan d'aya saboda yanda taga tsarin irn na asibitotane yasa tab'ata fuska kamar zatayi kuka,

"Fito mana" taji yana fad'a tare da sake mik'o mata hannunsa, hannunta tamik'a masa yarik'o sannan tafiddo da k'afafuwanta daga cikin motar da suka d'an kumburo saboda yanayin zaman da tasha, ahankali take takawa yana rik'e da hannunta, rufe gambun motar yayi sannan suka shiga daga ciki, nan take suka samu tarba tamusamman daga wajen nurses d'in dake wajen tare da tanadar masu inda zasu zauna kafin agama had'a folder d'inta a sadasu da babban likitan da zai dubata.


Suna zaune kiran Ummansa yashigo awayarsa, agajiye ya d'aga wayar had'e da cewa

"Hello ummanah"

"My son kun iso kuwa?" hannu yasa yana d'an mummurza goshinsa a hankali kafin yace

"Afuwan Ummanah, mantawa nayi ban kirakiba nasanar dake, bamu dad'e da isowa ba, halan bak'inku basu iso ba" muryar mutanen da yajiyo acan cikin wayar suna sallama yatabbatar masa da yanzu suka isa. Cikin farinciki Umma dake amsa sallamarsu tace

"Alhamdulillah gasunan sun iso yanzu kai kana ina danaji kace bak'ina basu iso ba?"

"Ina nan asibiti nida dady za'a duba Basmah don koda muka taso batada lafiya"

"Allah sarki ai dole yarinya tayi ciwo ace cikin rana d'aya and'aura mata aure bada sanin taba kuma aurenma da wanda k'anwarta zata aura"

"Umma mubar wannan zance koma meye Allah yakyauta, ana gama dubata zamu iso gida insha Allah"

"To shikenan Allah yak'ara mana lafiya, ka gaisheta"

"zataji in sha Allahyafad'a had'e da kashe wayar yana kallon fuskarta data jingina kanta idanuwanta arufe, gaba d'aya ta canza daga Basmahr da yasani takumbure saboda kukan da tayi"

Sosai tabashi tausayi don yasan biyayya kawai tayi ta auresa badon yana zab'in rantaba, hannunta yakamo yarik'e yana mai rayawa azuciyarsa cewa duk daba ita yake soba kuma babu k'aunarta aransa yayi alk'awarin zai bata kulawa tare da sauke duka hak'k'ok'anta dasuka rataya akansa amatsayinta na k'anwarsa kuma 'yar uwarsa.

Bayan kamar minti biyar aka kira sunanta ya rik'ata suka shiga cikin office d'in tayiwa dr bayanin yanda takeji da abunda ke damunta wanda anan take yafahimci matsalarta, magunguna ya rubuta mata yace tasha na tsawon sati d'aya amma gobe tadawo akwai gwaje gwajen da za'ayi mata don yafahimci kamar akwai matsala, godiya Mahmoud pilot da dadynsa suka yimasa sannan suka nufi hanyar gida,

Cikin so da k'auna family d'insu Mahmoud suka tarbeta, soyayyar da har saida tabata mamaki, hawaye suka zubo mata a idanuwa tunawa da batasan ko wane hali 'yar uwarta Billy da itace yakamata ace ta tsinci kanta cikin wannan ahali mai matuk'ar karamci da soyaya take cikiba.

Jawota Umma tayi ajikinta tana fad'in "'yar gidan dady kisaki jikinki mana, meye abun takura kanki keda gidansu gaki ga Ummanki keyi" kallon Mahmoud tayi daya zube kan kujera saboda tsananin gajiyar da yayi tace

"Son sannu da hanya ko?, ya jikin Basmah d'in injin da sauk'i"

"Eh Umma amma doctor yace gobe mukoma akwai wasu 'yan gwaje gwaje da za'ayi mata" yafad'a had'e da tashi zaune yana kallon mom data wani sanya Basmah ajikinta, imagining yayi inama ace Billyn sace da tuni shima yaje ya nanik'eta, murmushi yayi yana murza tafunan hannunsa kafin yace

"Umma bari inje in watso ruwa, inajin gajiya sosai"

"Ai kuwa gajiya dole son, kaje kafito zuwa lokacin itama tad'an watso sai kuci abinci tasha magani ko? tafad'a had'e dasa hannu ta d'ago fuskar Basmah, dakanta tarik'a Basmah takaita cikin d'akinta sannan tashiga toilet tahad'o mata ruwan wanka masu zafi tace ta shiga tawatso,

'Dakin alhaji tashiga kafin tafito tayi masa sannu da zuwa, sannan shima tahad'o masa ruwan wanka, bayan yafito yana kimtsawa tace

"Alhaji dama nace ko zakayi magana da yaronnanne yabar Basmah hannunmu har nan da kwana biyu idan tasamu sauk'i naga har yanzu kamar tanajin jiki, kasan halin yaran zamani ba'a iya masu kada inyi masa magana yaga kamar wani abun ko yak'iyamun amma idan kaine kayi masa magana natabbata zai barta"

"A'a hajiya wannan ba huruminmu bane, shiya ke da iko da matarsa don haka don Allah ki kauda idanuwanki akansu kibashi matarsa sutafi" yafad'a yana zura doguwar jalabiyarsa ajiki,

Haka kuwa akayi misalin k'arfe sha d'aya da rabi bayan sun kammala cin abinci duk da kad'an Basmah ta tsakura, alhaji da Umma suka d'auketa cikin mota da kansu suka kaita har cikin gidanta tare da yimata addu'ar Allah yazaunar dasu lafiya kuma yabasu zuria mai albarka sannan suka fito suka koma gida, daidai lokacin sukaci karo da mahmud yafito yana kullikke d'akinsa dake nan cikin gidan alhaji yakirawosa had'e da cewa "Son kayi maza kaje gidanka iyalin ka nacan munbaro ita kad'ai, ubangiji Allah ya albarkaceku"

"Amin alhaji" yafad'a tare dayi masu saida safe sannan yad'auko motarsa yabar gidan, wajen masu kaji ya tsaya yasai k'waya biyu tare da gorar fresh lemon da gorar swan water sannan yak'arasa gidansa,

Saida ya kukkulle ko ina bakinsa d'auke da addu'a sannan yashigo cikin d'akin tana kwance ya ajiye ledojin akan bedside, wardrobe ya bud'e yaciro sallaya ya shimfid'a tare da cewa

"Basmah kije kiyo arwala kinji ko?" Ahankali tabud'e baki tace inada arwala, rik'ata yayi ta tashi sukayi sallah raka'a biyu sau biyu sannan ya sallame, addu'o'i yayi masu sosai masu tsayi tare da rok'on Allah yabasu ikon sauke hakkokan juna dake tsakaninsu, bayan sun kammala yajawo ledojin yabud'e naman tare da tura mata agabanta yace taci, girgiza masa kai tayi alamun tak'oshi yace

"A'a Basmah kada kihad'a yunwa da k'arya waje d'aya don naga kocan bawani abinci kika ciba, kinsha maganinki ko?"

"Eh Umma tabani nasha"

"Yawwa kici wannan ko kad'anne kinji ko? Yaya baya son kafuwa" tare da d'ebo naman yakai mata abakinta, dole haka tadaure tadinga ci yana bata har saida takauda kanta sannan yamik'a mata gorar fresh lemon d'in tasha kad'an, gorar ruwa ya sake bata takarb'a suma takurb'a 'yan kad'an abakinta sannan ta ajiya. Kan gado takoma takwanta shikuma yakwashe sauran naman da lemunan yakai kitchen sannan yashiga toilet yayo arwala, yana fitowa yaja mata bargo ya lullub'eta sannan shima yahau gadon ya kwanta yana karanto addu'o'in bacci dana neman tsari daga shed'anun aljannu, saboda yanda yagaji kafin kaceme tuni bacci ya d'aukesa yayinda ita kuma inbanda tunanin 'yar uwarta tana hawaye babu abunda takeyi, tashi tayi taje tad'auko wayarta cikin jikkarta tahannu takoma parlour takira Billy dake zaune tana fira dasu Zainab, bugu uku tayi ba'a d'agaba saiga na hud'u sannan Billy talura da wayarta dake haake tad'aga had'e da cewa

"Hello Yayya lafiya bakiyi bacci ba" murmushi Basmah tayi kafin tace

"Taya zan iya bacci bayan k'anwarta batayi ba"

"Laa fira nakeyi dasu Zainab da Amina gamunan atare, ya gajiyar tafiya kun isa lafiya"

"Lafiya klw sisto"

"Masha Allah, ya k'arfin jiki? Gaskiya yayya akwai gajiya kije ki kwanta dare nayi nima yanzu zamu kwanta kinji?"

"Bilkisu" Basmah tafad'a cikin rawar murya, Billy dake sauraronta taji gabanta yafad'i don a iya tarihin rayuwarta bazata iya cewa ga ranar da ta tab'ajin takira sunanta kai tsayeba sai yau, ahankali tafurta "Na'am yayya lafiya?" had'e da mik'ewa itama tabar inda take zaune ita dasu Zainab takoma can palour wajen dining area tazauna.

"Kiyi hak'uri 'yar uwa bisa rushe farin cikinki da nasa kikayi don kisakani cikin farinciki, Nashiga damuwa sosai akan hakan da kika aikata, naji kunya dana kasa zamowa nice wacce zanyi sadaukarwar da kikayimun akaina, narasa gane wane irin sonkai nayi wajen tauye zuciyarki bacin nasan cewa tawa batada wani dogon amfani da zatayi aduniya, don Allah kiyafemun 'yar uwata ina matuk'ar jin zafin haka araina"

"Mekike fad'a haka 'yar uwa nifa..."

"Shiiii...kidena b'oye mun haka 'yar uwata, natabbata cewa ranar duk kinji abunda kefaruwa, kuma nasan cewa kinga tissues masu jini dana manta nabasu ad'akin Ummi shiyasa kika aikata haka, nayi dana sanin faruwar haka don nazamo silar rushe farincikinki" Billy dake murmushi hawaye nafitar mata a idanuwa tace

"Shikenan yayya tunda kinriga kin san komai, ni nayi hakanne don bazan iya juriyar rasaki akan abunda nasan cewa idan nabar maki zaki iya cigaba da rayuwa ba, wlh ko kad'an tun farko bansan da soyayyar da kike yiwa yaya ba daban so shiba har nasakashi azuciyata ba, amma ko yanzu alhamdulillah tunda kin mallakesa amatsayin miji da ace sai bayan na auresa ne nasan da haka da bazan tab'a yafewa kaina ba, kimanta da komai yayya kuma kibar wannan magana atsakaninmu in sha Allah komai zai dai daita kedai kiyi farin ciki kinji ko 'yar uwatah" Shiru Basmah tayi tana mamakin yanda k'anwarta ta iya jure son yaya Mahmoud haka azuciyata har take da k'arfin halin iya furta irin wud'annan kalaman, amma ita takasa jurewa haka har tayi saken daya illatata kafin tace

"Dukkanin farincikin da ni'imar Allah sutabbata agareki, hak'ik'a kinyi abunda bakowa ke iyayinsaba aduniya, madallah da samun 'yar uwa irinki, ina rok'on Allah daya yalwata akhairansa agareki kuma ya haskaka maki dukkanin al'amurranki, kitayani addu'a kada Allah ya amshi rayuwata har sai nayi maki abunda zai sakaki farinciki har iya k'arshen rayuwarki"

"Karki damu yayya, saida safe ngd sosai" billy tafad'a tare da kashe wayar, zama tayi wajen na tsawon minti biyar tana tunane tunane aranta kafin tamik'e takoma d'akinta, inda ta tarar harsu Zainab sunyi bacci,

Ita kuwa Basmah tana gama waya da ita saiga kiran Batool yashigo, cikin sanyin murya ta d'aga tace "hello Batool"

"Na'am yayya ina wuni?, ya jiki?, kun isa lafiya"

"Lafiya klw sister, jiki Alhamdulillah da sauk'i"

"Masha Allah dama tun d'azu nake son nakiraki to bansamu time ba sai yanzu da aka watse"

"Ayya 'yar uwa to inashi dr.ne da kika iya bud'e baki haka ba kunya kina waya?"

"Yaje yarakki abokansa , shinefa nace bari inkiraki inji ya jikinki?"

"To naji sauk'i, kije ki kwanta saida safe kinji ko"

"To yayya ina kewarki sosai"

"Nima haka my sister" sannan takashe had'e da rungume wayar tana hawaye har bacci b'arawo yayi nasarar saceta.

Lambar Billy tayi k'ok'arin kira sai gashi tajiyo takun step d'in dr. Ahmad yana hawowa sama, da sauri ta maida wayar a jikkar dake gefenta sannan taja mayafi tarufe fuskarta, saida yayi kusan minti biyar tsaye abakin k'ofa yana kallonta sannan yak'araso ciki bakinsa d'auke da sallama, kan gadon ya hau tare da yaye mayafin daya rufe mata fuska yana fad'in

"Tsarki da dukkanin yabi sutabbata ga Allah daya mallaka mani fatimatah amatsayin matata, batare da k'arfina ko kuma dubarata ba, arrzik'ina ko kuma kyawona, ya Allah ina godiya akan haka"

Murmushi tayi kanta na duk'e ak'asa had'e da cewa

"Alhamdulillah Allah daka fiddani tamusamman acikin 'yan uwana mata kuma ka azurtani da samun miji wanda shima yake na musamman acikin dukkanin fad'in mazajen dake duniya, Allah nagode maka kuma ina alfahari da hakan da kamun acikin rayuwata" cike da farincikin jin dad'in kalamanta yasa hannu ya tallabo hab'arta yana kallon fuskarta yace

"Fatima nine yafi dacewa nayi irin wannan godiya ga Allah kafin ke amma saboda yanda ubangijina ya suranta mani ke yasa daga kallo d'aya danayi maki na manta da wannan, ina sonki fatima so mai tsanani kitayani addu'a Allah yabani ikon kiyaye dukkanin hak'k'ok'anki akaina kuma yabamu ikon zaunawa lafiya da farantawa juna"

"Ka kwantar da hankalinka mijina in sha Allah zanyi maka biyayya iya k'arfina, kuma nayita alk'awarin zan faranta ranka tamkar yanda farin wata ke haska duniya amaren sha biyar gawata, zan kula dakai tamkar yanda uwa ke kula da d'anta sannan zan kasance mabiyi maka hidima fiye da yanda bawa keyiwa uban gidansa, fatana ka kasance mai afuwa, rangwame, yafuwa da kuma yimani uzuri aduk lokacin da nayi maka kuskure kona sab'a maka" murmushi yayi yana maijin sanyin kalamanta acikin zuciyarsa kafin yace

"In sha Allahu zaki sameni ayanda kike so koma fiye da haka, kitashi muyo arwala mu mik'a godiyarmu ga Allah daya cika mana burin ganin wannan ranar da muka dad'e muna fatar zuwanta"

Ba musu tajuyo tare da sauko da k'afafuwanta daga kan gadon ya mik'a mata hannu tarik'o had'e da sau kowa, mayafin dake kanta yacire mata sannan suka shiga toilet d'in atare sukayo arwala, suna fitowa ya shimfid'a masu sallaya suka gabatar da sallah raka'a biyu tare da yiwa Allah godiya daya nuna masu wannan rana, suna idarwa ya d'auko ledojin da abokanansa suka shigo masa dasu yabud'e leda yaciro gasashahen naman rago da yasha had'i mai kyau tare da k'atuwar gorar yoghurt, a hankali yafara ciyar da ita itama tana cidashi har suka k'oshi sannan yaje ya d'auko cup k'waya d'aya ya tsiyaya yoghurt d'in yabata tasha sosai har saida takusa shanye cikin cup d'in sannan tajaye kanta shi kuma ya shanye sauran daya rage, d'aukar sauran yayi ya saka a fridge sannan yashiga toilet ita kuma takoma kan gado takwanta abunta, kasancewar akwai gajiya atare da ita yasa kafin yafito tuni bacci yasoma d'aukarta, yana fitowa yad'an feshe jikinsa da turare sannan yahau gadon had'e da kashe fitilar d'akin, tanaji yanda yake k'ok'arin rage mata kayan dake jikinta amma duk da tsoron dake tare da ita haka takasa hanasa, cikin sigar rarrashi da kuma lallab'awa yaci nasarar maida Batool d'insa cikakkiyar macce, sosai ya jinjinawa Batool irin k'ok'ari da k'arfin hali da kuma juriyar da take dashi, wanda hakan bak'aramin k'aramai sonta da k'aunarta yayi ba azuciya, yanajin yanda taki fidda nishi ahankali tana hawaye dake nuna irin rad'ad'in da takeji, cikin dubara ya lallab'ata ya kimtsa mata jikinta sannan suka watso ruwa suka koma abunsu suka kwanta, jawota yayi ajiki ya rungumeta sosai yace

"Alhamdulillah, fatima ina sonki ina k'aunarki sosai, ubangiji Allah yayi maki albarka Allah ya d'aga daranarki tun anan duniya har izuwa aljannah" ahankali tafurta "amin"

"Kinsan me?" Tura kanta tayi acikin k'irjinsa batare da tace komai ba tana shak'ar k'amshin sabulun da sukayo wanka dashi mai matuk'ar k'amshin gaske, janyota ya sakeyi ajikinsa tare da yimata kiss a goshinta yana 'yar dariya mai sauti kafin yace

"Ana cewa sai idan miji ya d'agewa matarsa tafin k'afarsa sannan zata shiga aljannah, to ni ba tafin k'afata kad'ai nad'age makiba har da k'afar tawa da duka gangar jikina, ina mai rok'on Allah da yabaki aljannah da rahamarsa, nagode nagode maki sosai da kika faranta zuciyata da baki d'aya duka raina, nanma "amin" kad'ai ta iya amsa masa dashi, haka yadinga yimata addu'o'i kala kala har saida yaji bacci ya d'auketa sannan yagyara mata kwanciyarta ajikinsa yaja masu bargo.

Kusan motoci biyar suka isa k'ofar gidan yaya mahmud duka abokanan sane aciki da suka rakosa, suna isowa k'ofar shiga gidan ya dakatar dasu tare da karb'ar ledar dake hannunsu yace

"To friends gudnigth don gaskiya babu wanda zai shigarmun gida ya kallemun kwalliyar amarya, ko banzama namakara kuma idan kuka shiga sake b'ata mani lokaci saboda haka you guzs da bakwada aure saida safe, don Allah yafidda Mahmud acikinku"

Gaba d'aya dariya sukayi had'e da rik'e baki kafin suce

"Dakyau ango, ai indai amaryace muna zaune zamu ganta kuma watarana zata koro mana kai musake jonewa, kawai jeka malam munyi maka uzuri" da haka suka cigaba da dariya had'e da mimmik'a masa hannu sukayi sallama suka wuce sannan yarufe gidansa,

Wata irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya shigo palourn, kai tsaye ya wuce bedroom d'in daya tabbatar tana ciki, yana shiga yasameta kwance ta lullub'e fuskarta don tagaji da jiransa har bacci ya soma d'aukarta, ledojin dake hannunsa ya ajiye kan bedside tare da hawa kan gadon rungumota tabaya, saboda bataji lokacin daya shigoba yasa ta tashi fasa ihu da sauri yasa bakinsa acikin nata ya toshe, ganin shine yasa tayi saurin jaye bakinta tare da juya masa baya alamun tayi fushi, aikuwa yaya Mahmoud saida yayi da gaske sannan yasamu ya shawo kanta, hardasu rik'e kunnuwa wajen ban hak'uri sannan ta hak'ura, sun ciyar da juna cikin so da k'auna kafinnansu gabatar da duk abubuwan da musulunci ya tanada a tsabtace kuma a ilmance.

Tsayawa fad'ar irin farincikin da wud'annan ma'aurata suka shiga a wannan daren b'ata lokacine domin sun ahayar da juna zumar da bazasu tab'a mantawa ba, albarka kuwa ranar faraaha tashata babu adadi,

Wanda hakan yasa faraaha tayiwa Allah godiya sosai daya bata ikon kai mutuncinta agidan mijinta har yayi alfahari da hakan tare da sanya mata albarka....


_KUYIMUN AFUWA JINA SHIRU DA KUKAYI, BANAJIN DA'DINE, AMMA YANZU ALHAMDULILLAH NASAMU SAUKI, *LUV U ALL FILLAH💋❤*_




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Kai Alhamdulillah gaskiya masoyi dad'i garesa, nagode sosai da kulawarku agareni my fan's, hak'ik'a dukkanin addu'o'inku sun iso agareni kuma sunyi matuk'ar tasiri akaina domin Alhamdulillah nasamu sauk'i fiye da tsammaninku, godiya agareku mai yawa wud'anda suka kirani awaya da wud'anda suka turo mun text messages da masu biyoni private kai dama wud'anda suka turo addu'o'insu ta group tare da yimani ya jiki duka nagode sosai Allah yabar tare🤝🏻, you guzs are always made proud💃🏼💃🏼 thanks and jaxakumullahu bikhair👏🏻_


💎Page_____89💎

Tunda sassafe mom ta tashi tahad'a breakfast d'inta mai rai da lafiya sannan tashiga toilet tawatso ruwa, shiryawa tayi cikin wata atamfarta mai golden doguwar riga d'unkin buba, rigar tayi matuk'ar yimata kyau sosai, sannan tawuce kitchen tad'oko wanda tashirya cikin wani madaidaicin kwando tanufo part d'in Ummi dashi, har zata shiga sai kuma taji wata irin kunya takamata, tunda take rayuwarta bata tab'a zuwa part d'in Ummi inbanda ranar da dady ya aikota, kuma koshi bata shiga ba abakin k'ofa tatsaya saboda maganganun da taji sunayi, koda kuwa rashin lafiyane Ummin keyi ko ita ko 'ya'yanta daidai da rana d'aya bata tab'a zuwa lek'osuba balle taje gaiaheta, amma shine yau saboda tana buk'atar taimakon wanda zata aika gidan d'anta shine hadda wani bugo uban sakko haka, girgiza kai tayi tare da juyawa zata koma don gaskiya kunya bazata barta ta iya zuwa ba, ji tayi Bilal da har ya shiryo cikin shirin kayansa na islamiya zaije wajen Bassam zasuje tahfiz yarik'o hannunta had'e da cewa

"Laah mom, kawo in rik'a maki kwandon, yeee Ummi, Ummi, fito ga mom tazo part d'inmu," ya k'arasa maganar yana tsalle had'e da k'ok'arin karb'ar kwandon saboda jin dad'i, yau yaga abunda bai tab'a gani ba koda wasa a gidan,

K'ok'arin rufe masa baki tayi had'e da jansa zasu wuce saiga ummi tafito itama taci adonta cikin wani lace mai k'yalli riga da sket, cike da mamaki tace

"Am Bilal lafiya kake k'wallamun kira haka?, kai da waye atare da kai" cike da farinciki yafara k'ok'arin jawo hannun mom yana so tajuyo don tuni yasamu fuskar da yafara sabawa da ita kuma tana kulawa dashi tamkar yanda take yiwa bassam shiyasa yasamu k'arfin halin yimata haka

"Ummi zo kiba mom yaya Bassam ce tazo kuma zata koma" yafad'a yana k'arasowa wajen rik'e da hannunta ita kuma tana biye dashi kanta duk'e ak'asa har suka iso wajen da Ummi ketsaye sake da baki kamar ruwa yacita tsabar mamaki,

Ahankali Ummi tace

"Bilal cikata mana haka akacema anayiwa manya idan safiya tawaye"

Da sauri ya sake hannun mom tare da noce kansa k'asa "yace mom good morning" sannan yabar wajen aguje yana tsallen jin dad'i da farinciki wai yau mom ce a part d'insu,

Cikin wata iriyar kunya da mom tarasa yanda zatayi da ita tace

"Yaya ina kwana?" Tsabar mamaki saida ummi taji wani irin jiri ya soma d'ibarta don atarihin rayuwarta in aka cire ranar da taje ganinta bazata iya tuna waau ranakun da magana ta tab'a had'ata da mom ba balle gaisuwa har takirata da yaya, Allah dai yasa lafiya, dakewa tayi kafin can tace

"La.fi.ya klw momyn yara, injin dai lafiya ko? bawani abun yaron nan yaje yayi maki ba, nasan halin Bilal da raahin ji sosai"

Girgiza kai mom tayi had'e da cewa "ko zan iya shigowa ciki?" Wannan karon kam ummi danne mamakinta tayi had'e da cewa

"Why not, Bisimillah" tare da bata hili tawuce tamkar kwai yafashe mata aciki, kwandon data baro can ajiye Ummi ta d'auko had'e da shigowa dashi ta ajiye a can saman floor d'in dining area sannan tadawo paloun ta zauna akan kujerar dake passing d'in wadda mom tazauna, nan dai kowanensu yayi shiru zuciyarsa nasak'a masa abubuwa, fitowar Billy dasu Zainab ce takatse shirun saboda gaishesu da sukayi, wanda su Zainab kad'ai Ummi ta amsawa amma banda Billy mom kad'ai ta amsa mata sannan suka fice zuwa part d'in dady don su gaishesa idanuwanta cike da k'walla. duk abunda kefaruwa tsakanin Billy da iyayen nata mom nalure dashi tun jiya kuma tasan duka akan abunda tayine wanda mom najin cewa tayine don 'yar uwarta amma saboda rashin hujjar da zata iya fuskantar iyayen nata da ita yasa tazuba ido tana jira tagani ko zata iya samun wani abun da zai tabbatar mata da zarginta sannan taje ta warware matsalar da kanta,

Bayan sunfita, mom takalli Ummi had'e da cewa

"Bansan ta ina zanfarawa da baki hak'uri bisa abubuwan da suka faru abaya tsakanina dake, amma ina so kidubi girman Allah da manzonsa yaya kiyafemun, nafahimci cewa ni kad'aice ke haukata akanki na ganinan cewa kota kowane hali saina cusgunawa rayuwarki, na b'ata maki rai kuma na cutar dake keda yaranki amma ke ba haka kike rik'e dani azuciya ba, wanda ayanzu ne nagano cewa matuk'ar ban rok'eki yafiya ba bisa wud'annan abubuwa dana yimaki ba hakkinki bazai tab'a bari in gama da duniya lafiya ba, ada babu sunan dana tsana kamar naki, ina matuk'ar jin haushinki keda yaranki amma ayanzu Allah shine sheda nabi d'i duk wud'annan abubuwan narasa azuciyata saboda kad'ai kyakkyawar zuciya da halacci da kike dasu, wanda ada son kaina da sharrin zuciya dana shaid'an suka hanani fahimtar haka, hak'ik'a nagano cewa ke alkhairice atare dani kuma kece hasken wannan gida, nagano hakanne saboda irin hak'urinki da juriya da kuma kauda kai uwa ubama maida alkhairi da cutarwar da aka yimaki" mom dake zaune kan kujera idanuwanta cike da k'walla tana faman mummurza tafin hannayenta waje d'aya ta d'ago kai tana kallon Ummi da duk jikinta yayi sanyi sannan taci gaba da cewa

"Wlh yaya nayi nadama don Allah kiyafemun, kuma kiyarda dani don na dad'e dayin tubar da babu kome acikinta, zan so ki amince dani kibani dama cikin sauran tafiyar damuke da ita tsakanin nida ke idan rayuwa tabarmu inyi k'ok'arin kamanta kyautata maki tare da gyara halayyata koda so d'ayane, watak'il zan samu ingoge mikin dana dad'e ina yimaki acikin zuciya koda kashi d'aya ne acikin d'ari, don inada tabbaci akan cewa ubangiji ya d'aukaki akaina tunda kika kasance cikin bayinsa masu hak'uri"

Tasowa Ummi tayi had'e da dawowa kusa ga kujerar da take zaune tarik'o hannuwan mom tare da cewa

"Daga yau babu wani zargi tsakanina dake nayafe maki dukkanin abunda kika yimun, ina rok'on shima ubangiji daya yafe maki gaba d'aya laifukanki damu baki d'aya" nan mom tasake cika da al'ajabin wace irin rayuwa ce Ummi keda ita, ace ta shekara kusan ashirin da wani abu tana cutar da ita amma cikin mintuna da basu fiye biyar ba gaba d'aya tayafe mata, gaskiya tayi kuskure tare da tabka asarar moruwar rayuwa

Please Login or Register in order to submit comment