Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakira Batool yafad'a mata cewa satinnan za'azo kawo lefenta amma don Allah tayi hak'uri da abunda tagani aciki saboda bayada halin da zaiyi mata fiye da haka amma yayi mata alk'awarin bayan aurensu idan Allah ya hore masa ko duk sati take buk'atar ya d'unka mata sutura tare da canjin kayayyakin kwalliya da gyaran jiki to zai yimata" murmushi tayi sannan tace

"Hatta gaskiyarka ta musammance my angel, karka wani damar da kanka akan haka, ni kai nake so ba wani abun hannunka ba, wlh koda cewa kayi bakada halin yin lefe bazan damuba saboda nasan kai d'in mai kwatantawane daidai gwargwadon k'arfinka kuma natabbata idan nashigo zakayi mun idan Allah yahore mana, don haka kadenama wannan tunanin, nagode sosai da k'ok'arinka Allah yak'ara bud'i da d'aukaka" speechless dr Ahmad ya zama don bak'aramin burgesa ta sakeyiba, tabbas yau yamusanta zancen mutane dake cewa 'ya'yan masu kud'i basu fiye tarbiya ba kuma sunfiye son abun duniya shiyasa basa auren talaka sai masu kud'i irinsu, yau gashi 'yar mai kud'i tayi masa halacci da karamcin dako 'yar talaka kamarsa bazata iya amincewa tayi masa ba,

"Helloo.." Batool tafad'a jin yanda yayi shiru batare da yace komai ba, hakan yasa yayi murmushi had'e da cewa "Hello my angel, so sorry kinji nayi shiru, tsantsar halacci da karamcin da kika yimunne ya haifar da haka, ina rok'on kada Allah ya amshi rayuwata har sai nafaranta zuciyarki fiye da tunaninki, fatima saina sanyaki alfahari acikin mata 'yan uwanki tare da yimasu zarrah da yardar Allah"

"To amin my angel Allah yacika mana dukkanin burinmu na alkhairi" bayan yagama waya da ita yakalli mamy da shigowarta kenan rik'e da wasu atamfuna guda uku a hannu wud'anda guda biyun zasukai kimanin dubu hud'u da d'ari biyar d'ayar kuma dubu bakwai irinta ta cikin kwalinnnan mai golden yace "Mamy ajinkirta kai lefennan har zuwa wani sati zanyi k'ok'ari inga sunkai koda kala ashirin ne saboda wlh yarinyar taburgeni sosai kinji kinji yanda mukayi da ita yafad'awa mom yana mamakin yanda halin Batool d'insa yasha banban dana sauran 'ya'yan masu kud'in yanzu" murmushi mamy tayi had'e da cewa

"Yawwa ko kaifa, ai tunyaushe nace kak'ok'arta ka k'aro kala biyar sucike ashirin amma kace a'a ai yanzu kaga karamcin 'yatah yasa kunya zata sakaka dole kayi, Allah dai yayiwa yarinyar nan albarka yasa har tak'are rayuwarta bazata d'auki kud'i umrun ayimun na, ungo wannan ka k'ara dasu inyaso kaga kala biyu kad'ai yarage kak'aro" tafad'a had'e da mik'a masa atamfunan dake hannunta, bud'e baki yayi yana kallonta kafin yace

"Mamynah a ina kika samu wud'annan kuma?"

"A'a badaga agareni bane, d'azu baffanka yakawosu inji 'yan uwanka yace kak'ara alefe, sannan ga dubu biyar shima yace kaci hak'uri dasu" mik'a mata atamfunan yayi had'e da cewa

"Haba mamy shine kuma kika karb'a, ai idan ban basuba bai kamata ace na ansar masu ba, kawai kima ida masu nagode, in sha Allah anjima zan kirasu inyi masu godiya sosai"

"A'a kada kayi haka, ai laa yaruddul khaira illashahaid'an, duk arzik'in mutum zaiji dad'i idan hidimarsa ta tashi 'yan uwansa suka yimasa koda kuwa yafi k'arfin abun, ka karb'a mana don natabbata bazasuji dad'iba idan aka mayar masu dasu"

"Allah sarki 'yan uwana wlh sunyi k'ok'ari sosai Allah ya saka masu da alkhairi, to ke mamy ki d'auki guda biyu sai asaka d'ayar aciki inyaso kud'in sai kiyi d'inki dasu ko?" murmushi tayi sannan tace

"Ai baza'ayi hakaba, kabarmata abunta tunda ita akaba, nikam Alhamdulillah inada suturata sabbi ajiye fiye da kala uku ko kamanta wancan watanma kayoman sabbin d'unkuna kuma ban saba"

"Kai mamynah don Allah kirink'a sawa"

"Naji amma ungo wannan Allah bazan d'auka ba duka" tafad'a had'e da mik'a masa kud'in dake hannunta tana d'aure fuska don kar yasamu damar sake yimata gardama, dole ya amsa tare da kiran baffa yayi masu godiya sosai had'e da fatar Allah yabar zumunci"

Yau saura sati biyu aurensu faraaha da yaya Mahmud, dr.Ahmad da Batool, Mahmud pilot da Billy, takowane b'angare shire shire akeyi na musamman don kowane family auren 'ya'yansa nafari akeyi dole suyi rawar gani acikin bukin, tuni aka kawo lefen Billy akwatuna goma sha biyu wato set biyu kowane akwati biyar da kit, kayane kamar k'azanta don musamman dady yaturawa Umma kud'i taje har dubai tahad'o lefunan yaran nasu guda biyu 'yan gaban goshi wato Mahmud da Mahmud kowa Saiti d'aya d'aya yayinda shikuma alhajinsu Mahmud pilot yaturawa kowannensu dubu d'ari uku uku a account yace idan ankawo kayan sai suduba suga abubuwan da babu suk'ara dasu, hakan yasa basuyi shawara da kowaba suka d'auki hanyar kwatano sukaje suka sake had'o wasu akwatunan na kayan da suke buk'atar ganin matan nasu dasu wud'anda mafi yawancinsu k'ananan kayane da dogayen riguna dana bacci kala kala koda suka kawosu gida sosai Umma tayita fad'a dasu akan ai riyar da almubazzarancin yayi yawa amma saboda alhaji ya d'aure masu gindi yace idan bata dena surutu da mitar hakaba wlh sai yak'ara maau wasu kud'in yace suje suk'ara had'o wasu, hakan yasa dole ta tsuke bakinta don tasan kad'an daga cikin aikinsa kenan" hakama ankai lefen Batool kuma ankarb'esu cikin girmamawa tare da yabawa don kayane masu kyau da tsadar gaske saidai ace 'yan kad'an ba yawa, sosai Batool tayi farinciki tare da jinjinawa k'ok'arin gogan nata batare data maida hankali ko k'yashi da kishi akan tulin yawan na 'yar uwar taba, Basmah kuwa tuni ta d'auko wayar da Mahmud pilot yasiya mata wacce sai lokacin tafara amfani da ita tana d'aukar akwatunan hoto tana posting a WhatsApp da sauran wuraren media tana turawa tare da pics d'in 'yan uwanta ana tayata murnah, gaskiya ba k'arya akwatunan Batool sunsha comment saboda tsabar kyawonsu don meamah k'anwar fareeda 'ya'yan abokin dady har ta private tabiyo yayya Basmah tana tambayarta wai tabata lambar dr Ahmad tanaso ta tambayesa nawa yasai akwatunan kuma a ina yasiyasu, dariya Basmah tayi had'e da kiran Batool tanuna mata abunda meamah tace, aikuwa nan take Batool tayi copying nomber meamah awayarta takirata tare da buga mata warning akan koda mafarki kada tasake cewa zata nemi lambar mijinta idan akwatunan takeso to tabari bayan aureta zatazo har gida takawomatasu kyauta amma ahiren d'inta data koma cewa tana son lambarsa balle takirasa sannan takashe wayar tana huci, kallonta Basmah tayi tana dariya tace

"Oh ni jikanyar papi, Batool ina zakije da wannan uban kishi haka, ko kin manta yanda dady yake da abbansu meamah ne" cikin jin haushi tace

"Ni inama ruwana, amma ai duk laifinsane kowama yace yaje yasiyo irin wud'annan akwatunan gashi suna nema su jazamun tsiya" turo idanuwa awaje Basmah tayi tace "Too..ikon Allah, bari ni namatsa gefe kada kikaimun naushi nima akan nad'ora hotonsu a media na jazamaki" dariya Batool tayi tare da rungumeta tace "Inaa...ai yayyatah bata laifi awurina duk abunda tayi daidai ne"

Faraaha kam ba'a magana murna da farinciki agunta basa misiltuwa kasancewar yau sati biyu yarage ta mallaki ruhinta kuma abun k'aunarta, ga wani irin gyara da kulawa da take samu awajen k'anwar mahaifinta Gwaggo fareeda wacce tun daga Maiduguri ta d'auko wacce zata kula da ita, tuni tad'au hutu ita da dr.Ahmad sai shire shiren hidar bukinsu kawai sukeyi, ranar da aka kawo lefenta kuwa da ita har jaddi saida sukayi kukan dad'i, acikin ransu sunaji inama mahaifanta da kakarta zasu dawo duniya suga irin gata da d'aukar da Allah yayiwa 'yar marainiyar da suka bari aduniya, sosai takira yaya Mahmud da daddare tana godiya tare da yimasa addu'a akan wannan hidimar da yayi duk dako tasan ba komai bace acikin arzik'in da mahaifinsa yake dashi.


Kasancewar bukin nak'ara gabatowa yasa yaya Mahmud yaciro kud'in sadakin Billy da Batool ya mik'a masu a hannunsu sannan yaciro dubu hamsin d'in da dady yaba mom ranar amatsayin sadakin Batool daya cemasa yabiyawa dr.Ahmad d'in, wanda daga baya kuma dr yaturo iyayensa suka kawo nasa sadakin kuma yakarb'a duk da yasan dady yabiya masa, amma yayi hakanne saboda yanuna cewa k'anwarsa nada matsayin da za'aci sadakinta agumin mijinta bawai mahaifinta ba saboda tayi k'ima da daraja agun mijinta, har asibiti ya isko dr.Ahmad kafin yad'au hutu ya kaimasa tare da yimasa bayani amma sai yab'oye dalilin dayasa dadynsa yayi hakan yace yazata ga lokacin bayadasu saboda yanda aka yanka sadakin k'urarren wuri batare da shawartarsuba ko ajira su nemi hakanba, shiyasa yau yakawo masa abunsa tunda hak'k'in sane shi kuma sadakin daya bayar yamallakawa mai abu abunta.

Sosai dr.Ahmad yaji dad'in hakan don dama aransa yaci alwashin shizai biya sadakin matar da zai aura da halak d'insa saboda samun nagartattun 'ya'ya da zuriar da aka gino da tsantsar halaliya, ya yiwa yaya Mahmud godiya sosai bisa taimakonsa da yayi yacika wannan burin nasa, sannan yak'ara ganin kima da girma da kuma darajar dady a idanuwansa, baiso yakarb'i kud'in ba amma dole yaya Mahmud ya tirsasasa yakarb'a akan cewa kowata hidima ai bazai rasayi dasu ba, nan dai suka cigaba da tattauna akan yanda tsarin bukin zai kasance yana fad'a masa da shawarar da suka yanke shida Mahmud pilot.

Dady kuwa tuni ya samama Basmah gurbin karatu a ABU zaria under medicine, next 3week ma zata fara zuwa in sha Allah bayan bukinsu Billy da satai d'aya, saida ya kammala cukucukun bid'ar cigaban karatun Basmah sannan ya maido da hankalinsa ga batun auren 'ya'yan nasa, musamman ranar yazo da wani littafi na hotunan k'ayataccin gadaje da sauran kayan d'aki na musamman da alfarma yasa yaya Mahmud ya kirasu ummi dasu Basmah, basu littafin yayi yace su zab'a masu gadajen da za'a saka masu agidajensu, gaba d'ayansu murmushi sukayi suka taru waje d'aya suna duba littafin, ganin haka yasa Ummi yin dariya tare da kallon dady tace

"Gaba d'aya yarannan naka sun matsu subarmu, dubi yanda ko kunya basaji suka rufar mana akai ana duba kayan aurensu" saida yayi murmushi sannan yace "To yazamuyi ai zamani ne yakawo haka, ni kaina nalura kaman basajin kewar rabuwa damu" yafad'a cikin sigar ban dariya da marairaice murya, gaba d'aya sukasa dariya inbanda mom da dudduba littafin kawai takeyi batare da tace uffan ba, noce kai su Billy sukayi ala tilas sunji kunya, dady ya kalli mom cikin sigar zolaya yace

"To uwar amare 'yar kurma, ai sai kiba yaran suduba abunsu da kansu tunda dai naga alamar bazaku zab'ar masuba kunfiso kuyita kallo kallo da littafin, ashema da gaskiyarsu da sukazo duba abunsu kuka tsiri tsarguwarsu har kukaja na tamaku" yak'are maganar yana kallon Ummi tare da jefeta da throw pillow, mik'a masu littafin mom tayi suka k'i karb'a waisu alatilas kunya sukeji, Basmah na dariya tace

"Allah dady PDP kawai kuka so yimun, a matsayina na babbar yaya aini yadace inzab'a masu tunda 'YAN UWANA NE amma shine aka shareni wato tunda badani za'ayi ba ko?, shikenan ai nima idan lokacin nawa yazo Allah dakaina zanzab'a bazan bari kowa yazab'a mun ba ko mom d'ina" tafad'a tare da lak'ame mom tana dariya, sai alokacin mom tayi magana tace

"K'yalesu Basmahty ranar gari namu baruwanmu da wata kara tunda muma ank'i yimana"

Nan take dady yaji jikinsa yayi sanyi yafahimci lallai bai kyautaba don gaba d'aya hankalinsa yatafi gasu Billy da Batool suda zasuyi auren, kallon Basmah da har lokacin hannayenta na lak'ame awuyan mom dake zaune akan kujera ita kuma ta zauna akan hannun kujerar tana kallonsa yayi tare dasa hannuwansa yarik'e kunnuwansa yana fad'in

"Dady is sorry my dota, kada kiyi fushi kinji ko?"

"A'a bazanyi fushi da dadynah ba ko kad'an" hannu ya mik'a mata tadawo inda yake yace

"Yawwa my dota, u too I have something special for you but before jeki kikarbo littafin kinuna mun kayan da kikeso azuba ma 'yan uwanki kinji ko?"

Karb'a tayi tashiga dudduba littafin page by page, saida tayi kusan minti goma tana dubawa tare da sake dubawa dakyau sannan tazab'o wasu had'ad'd'un kayan masu d'an karen kyau da tsada ta nunawa dady yace

"Gud my dota, lalle kin iya zab'e domin wud'annan kayan sune latest design dis year kuma sunada matuk'ar tsada don kwalliyar jikinsu ma akwai surkin zinari aciki kuma jibi in sha Allah kayan zasu fara isowa nigeria kuma dama mune first da muka fara tura kud'in da za'a turo mana dasu, don haka ana d'aukowa kai tsaye za'a wuce dasu gidan kowacensu tare da masu had'insu in sha Allah" zaro idanuwa gaba d'ayansu sukayi cike da mamaki wai kayan d'aki za'a yiwa k'awa da ruwan zinari aciki, karb'ar littafin sukayi suna k'ara duba kyawon kayan tare da yiwa dady godiya da fatar Allah yak'ara masa bud'i, farinciki kuwa agun Basmah kai kace da ita za'a sakawa kayan kallon dady tayi tace

"Dady tabbas nida 'YAN UWANA NE kad'ai mukafi kowa samun nagartaccen mahaifi aduniya, muna matuk'ar alfahari dakai arayuwarmu don kagama mana komai" suma su Batool godiya suka yimasa yayi murmushi irin na manya dake nuna jin dad'i aransa sannan yace

"Allah yayi maku albarka, dukkanin farincikina yana wanzuwane bisa soyayyar da kuke yiwa junanku, natabbata zan iya bugun k'irji ince nine wanda zai amshi kofi idan aka saka gasar wud'anne 'yan uwane suke son 'yan uwansu fiye da son da sukeyiwa kansu aduniya, ko yanzu nabar duniya Alhamdulillah banida haufi akanku, ubangiji Allah yak'ara had'e mai kanku tare da soyayyar junanku"

"Amin" sukace atare hadda yaya Mahmud daya shigo yanzu bakinsa d'auke da sallama...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____75💎


Billy ce takalli mom tace "mom kinsan wai me yayya Batool tafad'a don taga yayya Basmah tafara gudu da mota?" Fuskar mom ba yabo ba fallasa tace "A'a sai kinfad'a" tare da shigewa kitchen, d'aga murya Billy tayi tace "wai cewa tayi yayya tadena gudu da ita saboda tsautsayin.." Kafin ta ida Batool tarufe mata baki tana fad'in "kai twiny wlh kin fiye d'an banzan surutu" had'e da janta zuwa d'akinsu ita kuma tana kokuwar bud'e bakinta alatilas saita fad'a da k'yar tayi nasarar shigewa da ita d'akin suka fad'a kan gado atare, gaba d'aya sukayi dariya suna kallon junansu cike da farinciki "Hmmm Allah twiny bakida kirki yanzufa nabarki saiki fad'a ko?" Batool tafad'a tana kallonta,

"Sosai kuwa fad'a zanyi, bake marar kunya ba, tunda kika iya fad'a agaban yaya ai nasan zaki iya fad'a gaban kowa"

"Sai akace maki har da gaban iyaye zan iya fad'a"

"Ah yo mezai hanaki tunda yaya Ahmad ya maidaki tantagaryar marar kunya yanzu" mirginowa Batool tayi had'e da haye ruwan cikinta tana fad'in

"Wato bakyada ta ido ko?, bara nanuna maki yau nice yayarki don naga alamar idan bahaka nayiba mijin nawama renasa zakiyi" tana rufe baki saiga Basmah tashigo cikin d'akin had'e da juyawa tarufe k'ofar tare da saka mata key, suna ganin haka suka mik'e arazane don sunsan rashin kunyar da suka yo mata kafin su shigo, cire mayafinta tayi tajefa akan gado sannan tanufi inda suke fuskarta ad'aure sukuma sunaja da baya "pls yayya sorry we're never repeat it again" batare data kula da mesuke cewa ba taci gaba da matsosu sunaja baya har saida ta cimmasu, hannuwanta tad'aga kamar zata dokesu da sauri suka runtse idanuwansu, ji sukayi tajawosu ajikinta tarungume tana fad'in

"Kunzaci zan iya dukanku ne hala?, tayama za'ayi na doki amaren dady yaya Mahmud da dr Ahmad su d'aukomun sammace, beside kufa 'YAN UWANA NE da kullum nake alfaharin kasancewarsu atare dani" d'agosu tayi had'e da lakutar masu kumatu tana dariya tace "my fear sisters ina matuk'ar sonku sosai" hugging d'inta sukayi atare suma sukace "muna sonki fiye da haka our great aunt" tare dayin lamo ajikinta sunajin yanda zuciyoyinsu ke bugawa saboda tsantsar k'auna da yanda jinin 'yan uwantaka ke gudu ajikinsu.

A b'angaren dr Ahmad kuwa duk Wasu gyare gyare daya kamata yayi akan bukinnasu yayi don idan kaga yanda yagyara gidansu bazaka tab'a yarda cewa wannan d'an k'aramin gidanne da iyalan marigayi Bashar mai fulawa ke zaune ba, kasancewar ginin da yana matuk'ar cinye fili yasa da aka rushe gidan cikin yayi girman da yaba dr.Ahmad samun damar mai dashi d'an madai daicin upstairs mai d'an karen kyau hawa biyu, wanda gaba d'aya tsarin sa bazai tab'a wuce na zaman mace biyu ba, saboda k'asan d'aki d'aya ne ciki da falo sai toilet da wani d'an k'aramin kitchen anan cikin falon banda au babu wani fili da yarage ak'asan wanda yawuce taku biyar tsakaninsa da 'yar katangar da aka zagaye gidan dashi, sai kuma matattakalar da zata sadaka da sama wacce kana shiga zaka fara cin karone da k'aramin corridor da zai sadaka da wani d'akin shima ciki da palour sai kuma d'an k'aramin toilet da bazai wuce tsayuwar mutum biyu ba acan cikin bedroom, sai wata k'ofa da zata sadaka da bayan d'akunan wadda anan zakaga kitchen agefe da wani toilet can gefe suna kallon juna, anja wata doguwar katanga mai 'yan hude hude da aka katange wajen da ita tayanda na k'asa bazai iya hango wanda kesama ba kuma nasama bazai iya hango na k'asa sosai ba, gidan yayi matuk'ar kyau sosai don bak'aramin k'ok'ari dr yayi wajen gyaransaba. Ranar da aka gama gyaran gidan da dr.Ahmad yaje ya d'auko mamy ita da baby Muhib agidan liman don can takoma da zama da za'a fara gyaran ba k'aramin farinciki tayi ba harda kuka tanajin inama mahaifinsa naraye tare dasu wannan ranar tazo da farincikinta ya lunku sosai fiye da haka, albarka tadinga sawa dr.Ahmad tana mai nema masa tsarin Allah daga sharrin dukkanin mak'iya" share mata hawaye yayi tare da rungumeta yana fad'in "Mamynah kiyi hak'uri za'a kwaso tsofaffin kayanki adawo dasu nan k'asa zaki zauna keda Muhib atare damu don banaso kuyi nesa dani, in sha Allah nan gaba kema zan canza maki duka kayan d'akinki kafin Allah yabud'a mun inyi babban gidan da zamu zauna ba'a takure ba"

"A hakama Ahmadi ai Alhamdulillah, amma nidai naso ace kuyi zamanku anan kaida matarka nikuma sai inzauna can gidan liman nida yarona"

"A'a mamy kinmanta me Abbana yace?, cewafa yayi yabani amanarki kada intab'a bari kizubar da hawayeba, to taya za'ayi ace ni ina nan amanar da aka bani kuma tana can, taya za'ayi insamu natsuwa da kuma kwanciyar hankali?, nifa nafisoma kizab'a idan saman kike so zaki iya zaunawarki acan hankali kwance mukuma muzauna anan ak'asa"

Aza hannunta tayi agefen fuskarsa had'e da cewa "Taya za'ayi in iya jurewa tattaka matattakalarnan zuwa sama akoda yaushe, nidai kubarni ak'asan nafi gane masa kodon saboda d'ana Muhib, kukuma da kuke sabon jini saiku zauna acan nasan bawata wahala da zakusha" dariya yayi tare da shafa kan Muhib dake hannunta yace

"Shikenan mamynah duk yanda kike so hakan za'ayi amma nikam nafara kishi da d'ank'anen nan nawa don naga kinfiji dashi yanzu akaina" kallon Muhib tayi tare da sake rungumesa tana murmushi sannan tace "To ai kai yariga da ka girma zaka iya kula da kanka shiyasa, shi kuwa fa?"

Dahaka suka koma tattaunawa akan zancen wud'anda zasuje kai lefensa da yake had'awa wanda kad'an ya rage ya ida kammalawa yanzu, duk da dai bawata k'arya yayi ba acik set d'in akwatuna ukune kawai da kit yayi don bayada zarafin yin fiye da haka, ammafa yayi kaya masu d'an karen kyau da tsada wanda duk wanda yagani dole ya jinjina ma k'ok'arinsa...





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____77💎


Tun ana saura sati d'aya Mahmud pilot yatattaro inashi inashi yabaro garin borno saboda shire shiren aurensa izuwa gidan daddy wato uncle d'insa kuma surukinsa, lokacin da zai tafi kuwa haka cousins d'insa suka dinga yimasa sheri suna tsokanarsa, wai d'an kwali yaja hula murmushi yai had'e da cewa "ai bahula kad'ai d'an kwalin ya jaba hadda gangar jikin mai hular da ruhinsa, dariya Umma ta'aza tana fad'in "Ai sai kuyi indai my son ne yanzu soyayyar 'yata ta makamce masa idanuwa tasa gaba d'aya ya fitsare k'afafuwansa bayaji baya gani har sai ranar da yaga mun mik'a masa matarsa ahannunsa" kunya ce ta kamasa ya shafa sumar kansa had'e da yiwa Umma bankwana sannan ya juya yana kallon 'yan uwan nasa tab'angaren mahaifinsa yace

"Komai dai zakuce naji saina ganku, kuma wlh duk wanda baije d'auko mun matata ba hmmm" yayi k'yacci tare da wucewarsa don dama tun safe yayi bankwana da alhajinsa. Tunda ya isa Basmah tafara wasan b'uya dashi, duk hanyar da zata had'asu tadena binta haka kuma ta lizimci zaman d'aki don karma tagansa balle har wani abun akansa ya sake bijiromata, kuma Alhamdulillah don har mantawa takeyi da yana cikin gidan sai dai abunda takasa ganewa shine yanda ciwon nata ke barazanar taso mata, kuma ta tabbatar da cewa babu wani tunani ko damuwa data ajiye aranta don tana k'ok'arin kauda komai idan yazo mata azuciya, hakan yasa ranar da za'a fara program d'in tunda safe ta tafi asibiti wajen dr. Dake kula da case d'inta ta sanar masa da halin da take ciki, scanning yasa aka yimata da sauran gwaje gwaje wanda anan take hankalinsa ya tashi lokacin da aka kawo masa sakamakon ya duba domin b'an garen zuciyar Basmah na hagu yasamu matsala sosai wanda har yahaifar da jijiyoyin dake harba jini zuwa sauran sassan jikinta suka samu rauni, kallonta yayi cike da tausayi yace

"Am Basmah ina mahaifinki da yayarki?, ina son yin magana dasu ne" murmushi tayi kafin tace

"Dr. Lafiya injin?"

"Lpy klw inaso dai inhad'u da d'ayansu yanzu yanzu, ina ranar au suka kawoki ko? Kuma nafad'a masu duk abunda yakamata ayi wajen kula da lafiyarki"

"Eh dr. Duk abunda kafad'a anyisa koma ince anyi fiye da haka, magani kuwa inasha akan tsari kuma bisa k'a'ida kamar yanda kabuk'ata ko wani abunne yafaru" Shiru yayi yana kallon cikin idanuwanta kafin yace

"Basmah baki dena saka damuwa da tunane tunane aranki bane?" arud'e tace

"Ko kad'an dr. duka nadena babu komai araina yanzu, ina samun kula gun mom, dady, Ummi, yaya, 'yan uwana mata kai harma da 'yan k'annena basayin komai sai abunda nakeso, kuma duk abunda suka san zai faranta raina shi sukeyi, dr meyake faruwa dani ne kafad'amun domin a gaskiya bana buk'atar duk wani abun tashin hankali da zai ziyarci ahalina yanzu saboda farincikin da suke ciki na auren 'yan uwana bana fatar ya rushe, pls koma meye kafad'amun basai kagansuba, pls dr." Tafad'a kamar zatayi kuka ganin irin k'warin guiwar da take dashi yasa cikin sanin murya da sigar da zata kawo natsuwa atattare da ita ya fayyace mata matsalar da take ciki akan ciwon dake k'ok'arin mamaye gaba d'aya zuciyarta, ko kad'an batayi mamaki ba kuma bata tashi hankalinta ba don yariga da tasan yanda takejin yanayin jikinta dole hakan zai faru da ita, murmushi tayi had'e da kallonsa yanda fuskarsa ke d'auke da damuwa tace

"Shikenan dr.nagode, yanzu akwai wasu maganunnuka da zan iya cigaba dasha don kad'an yarage wud'ancan suk'are"

"Eh akwaisu amma before dt zaifi ace wani daga cikin relatives naki yasan da wannan matsalar"

"A'a dr don Allah nabar wannan magana, zasu sani amma not now, kaima ina rok'onka don Allah da girmansa kada kafitar da wannan maganar waje har sai bayan auren 'yan uwana, zanci gaba da shan magani kafin lokacin da za'agama hidimar nasan in sha Allah zan samu lafiya"

"Basmah kinafa cikin matsala bai kamata ace kin fifita wani ra'ayinki akan lafiyarki ba"

"Wai meye haka dr. Rayuwa da mutuwa duka ahannun allah suke, ni nayi imani akan bazan mutuba har sai lokacin da Allah yad'ibarmun yayi koda kuwa gaba d'aya zuciyata zata dena aiki natabbata idan lokacina baiyi ba dole zanci gaba da lumfashi, kadameni da dole asanar dasu matsalar da nake ciki, kafad'amun shin idan aka sanar dasu mezasu iya hana yafaru dani ko zasu iya canza wa'adin da Allah yad'ibomun ne aduniya?, idan kana tunanin fad'a masu zai amfanar dani to bari nafad'a maka cutar dani zaiyi fiye da wannan ciwon dake cikin zuciyata" tak'are maganar tana daddaga saiti zuciyarta cikin fushi had'e da b'acin rai, sosai dr ya tausaya mata don yanada tabbaci akan matsalarta tanada alak'a da rayuwar 'yan uwanta wanda yasa tak'wammace cewa tarasa ranta data rasa tasu rayuwar,

Please Login or Register in order to submit comment