Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusanceki to tabbas babu wata macce da zai koma kallo a matsayin macce aduniya idan ba keba" sake d'auko wata gumba tayi cike da k'aramin d'an bokiti fari irin wanda ake saka turarukkan wuta aciki ta mik'awa mom tace

"Ita kuma wannan gaba d'aya zaki dame kishanyeta, da kanki zaki bani bayanin kyautar da zaki karb'a a wurinsa don duk abunda kikace ya baki to wlh sai ya mallaka makishi"

Zaro idanuwa tayi had'e da cewa "kai dagaske kikeyi?"

"Sosai kuwa kigwada kigani"

"To amma ni k'awata har yanzu banji kintab'o abunda nafi buk'ata ba, matarnan fa tazamo mani tamkar ciwon ido"

"Kash matsalata dake Hussaina gaggawa, ai kifara mallakar mijin tayanda duk wani tuggu da makirci da zaki had'a mata zai yadda dashi"

"Nifa nafison ayita tak'are, bana son ganinta gaba d'aya agidan" dafa kafad'arta tayi tana dariya

"Kai k'awata wai wannan tsana da kike yimata dame tayi kama? Ki kwantar da hankalinki abu komai a sannu kada garin gaggawa k'aik'ayi yi koma kan mashek'iya, abunda yakamata yanzu kiyi shine kisan yanda zaki jawo hankalin mijinki kibashi hak'uri in yakama har kuka kiyi masa ya maisheki d'akin ki hakan zai taimaka mana wajen yin aikinmu yanda ya kamata, amma kina nan azaune gida bana tunanin aikinmu zai yuyu kin fahimta" Shiru mom tayi tna nazarin magani ganunta sannan tace

"To shikenan, yanzu kitashi ki watsa ruwa kafin hajia ta k'wallo maki kira"

Basmah kuwa Ummi na shiga d'aki ta kira wata k'awarta awaya, suna gama magana tafita abunta batare da kowa ya sani ba,

A b'angaren Ummi kuwa bayan ta kammala abincin rana ita da 'yan biyunta wato Batool da Billy ta umurcesu dasu tafi part d'in mom su dubo mata Basmah idan tana can don tunda tagama yimata fad'a tabarta afalo zaune bata sake ganin taba ta d'auka tana d'akinsu kwance amma ga mamakinta koda taduba d'akin bata gane taba gashi har k'arfe biyu ta wuce, tafe suke suna firar breakfast d'in Basmah suna dariya har suka iso part d'in mom nan ma bata ciki saboda part d'inma akulle yake ba kowa aciki nan suka shiga dudduba ta tako ina gefe gefen gidan basu ganeta ba, wajen Ummi suka koma suka fad'a mata bata can, nan take hankalinta yatashi tafita tana duba ko ina a compound d'in gidan ba Basmah ba labarinta, innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta dinga fad'a in tayi nan tayi can, wajen maigadi tanufa tana tambayarsa shin ko yaga fitar Basmah, shiru yayi ya kalli yanda hankalin Ummi ya tashi, cike da tausayinta yace

"Tuba nake uwar d'akina banso nafad'a makiba saboda har kud'i aka bani na toshiyar baki, amma ganin yanda kika tada hankalinki zan fad'a maki gaskiya, d'azu ina anan zaune saiga wata k'awarta tazo ita da wani acikin mota, basu cemun k'alaba ni kuma ban cemasu ba naga ta fiddo wayarta tayi kira, ba'a jima ba saiga Basmah tafito, shine har ta shiga motar sai tafito ta mik'o mani d'ari biyar tace ko antambayeni naga lokacin data fita ince a'a ya k'are maganar had'e da nunawa Ummi d'ari biyar d'in, ki gafarceni hajia nasan konayi yunk'urin hanata walak'anci zata yimani shiyasa nayi shiru, hawayene suka zubo a idanuwanta da sauri tasa hannu ta shafo bakinta daya kasa furta komai sannan tajuya takoma cikin gida, wayarta tajawo takira Mahmud cike da damuwa tafad'a masa halin da ake ciki, saida ya kwantar mata da hankali sannan ya kashe wayar.

Lambar Basmah ya shiga lalubowa ajerin contact d'insa had'e da danna mata kira, Basmah naganin kiransa amma tak'i d'agawa har sau uku, ganin haka yasa yafita batun kiran yaja motarsa da yake yana wajen abokansa yabar wajen aguje cikin matsananciyar damuwa.

Ita kuwa Basmah dake zaune bisa wata katifa ita da suby k'awarta tayi dariya tana nuna mata gaban wayarta kafin tace

"Kinganshi ko? Sai wani faman kirana yake don ya takuramun, gaba d'aya gidan sun tsaneni, mom d'inmu kad'ai ke sona yanzu kuma bata gidan dadynah ma baidamu dani ba agabansa za'ayi tayi mani fad'a akan d'an k'aramin laifi idan nayi amma bazayace komai ba, hatta k'anwata dake bimun tagujeni taya kike zaton zansamu farinciki agidan?" Murmushi suby tayi sannan tace " ki kwantar da hankalinki anan zaki samu farinciki kawai abunda nake so dake kiyarda dani"

"Taya zan yarda dake suby bacin bakida maganin matsalolina" wata kwalba suby tafiddo ta mik'awa Basmah

"Karb'i wannan kisha da kinsha shi zakiji gaba d'aya matsalolin ki suntafi koba haka ba bab's" tak'are zancen tana kallon saura yin dake gefe yana zuk'ar shisha" cikin maye Bab's yace

"Tabbas haka yake suby, idan kuma bata buk'atar sa, to tasha wannan don yafi k'arfi sosai" ya mik'o mata wata kwalbar dake ajiye acikin kwalaben da suka daza agabansu.

Karb'a Basmah tayi tana yatsina fuska

"Meye wannan Bab's"

"Hhhh Basmah Basmah kenan, wannan shi ake kira da sabuwar duniya kawai kisha zaki tabbatar da abunda nake nufi" har tad'aga kwalbar zata sha saiga kiran Ummi ya shigo a wayarta, bataso d'aga wayar ba amma saboda tanason yiwa Ummi fitsara tad'aga

"To kuma meye? Ko fad'anne kika kirani kik'ara yimun" da wuri Ummi tagoge hawayen daya zubo mata a idanu'

"A'a Basmah, kiyi hak'uri kidawo gida, ina kika shigane, kuma waye ya d'aukeki amota?"

"Meye damuwarki aciki, kawai ki ajiye waya"


"Basmah kiji tsoron Allah a duk inda kike kidawo gida, kada kiruguza rayuwarki abanza, kib'ata tarihinki na har abada" tuni kalaman Ummi suka tunzura Basmah ta d'aga kwalbar dake hannunta tashanye abunda keciki tas sannan ta bubbuga kanta da hannu tace

"Kikace me? To koma mezai faru ai rayuwatace babu abunda ya shafeki aciki don haka sai anjima" Ummi kuwa tanajin zata katse wayar takama fad'in "hello hello Basmah, Basmah" amma ina tuni takashe wayar tana kallon suby tace

"Kinji 'yar rainin wayon matar nan ko?"

"Kawai ki manta da ita Basmah yanzune zaki samu farincikinki da 'yancin kanki" saida tayi dariya sannan taci gaba dacewa welcome to the new world"









Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Ina kuke 'yan group d'in *HOME OF NOVELS* gaisuwa ta musamman zuwa agareku saboda muhimmancin da kuke dashi agareni bazan tab'a iya misaltashiba, tabbas kuna sakani nishad'i tare da k'aramun k'warin guiwa aduk lokacin da naga kuna comment idan nayi update, wannan dalilin ne yasa bazan iya wuce wannan page d'in ba har sai na isar da jinjina had'e da fatar alkhairi agareku, especially you people UMMIE, ZULAIHA SAMINU ELJIBRIL, MALKALFRED966 da kuma OUM RUQAYYAT, nagode nagode sosai Allah ya faranta maku zuciyoyinku fduniya da kuma lahira, *luv you all to the square of infinity*πŸ’‹β€_


πŸ’ŽPage_____25πŸ’Ž


Daga nan fa Bab's da suby suka dinga mik'awa Basmah kayayyakin dake sa maye kala kala tana sha wai don duk su sama mata farincikin da take tsammanin tarasa acikin agidansu,

Tunda ummi tagama waya da ita tafad'a akan kujera zaune hannunta na rik'e da wayar yayin da idanuwanta suka kasa dena zubar da k'wallan bak'inciki da takaicin rashin sanin halin da Basmah tajefa kanta aciki, haka Mahmud ya gaji da yawace yawacen nemanta ya dawo gida ya tarar da ita cikin wannan halin, har ya k'araso gabanta ya duk'a had'e dasa hannayensa akan hannunta dake rik'e da wayar bata san yana wajen ba sai lokacin da taji ya rumk'e hannun nata sosai sannan ta farga dashi awajen, hannunta d'aya ta d'aura akan hannayensa dake kan nasa had'e da kallonsa cikin muryar kuka tace

"Basmah..!" da sauri ya lumshe idanuwansa yace "ki k'yaleta Ummi, duniyace ta isheta wando da riga hadda mayafi, rayuwar da tazab'awa kanta kenan babu yanda zamuyi da ita sai addua, babu inda banjeba cikin gidajen 'yan uwa da wasu k'awayenta dana sani amma ban sameta ba, abun takaicima ko wayata tak'i ta d'aga saboda d'ai tasan mezai faru idan ta d'aga" yak'arasa maganar shima hawaye nafita daga idonsa.

"Bazai yuyu a k'yale taba, itafa 'ya macece dake buk'atar killacewa, wallahi zaifi ace aure aka yimata da a k'yaleta cikin wannan rayuwar sam hakan bai dace ba Babanah kayi tunani mana"

"To Ummi yanzu me za'ayi?, tunda bamu ganeta ba"

"Sake komawa zakayi ko Allah zaisa ka ganta"

"A ina kuma awane wajen, natabbata bata area nan, amma bari na sake komawa" tashi yayi yafita yana gogur idanuwansa da sukayi masa jawur saboda tsananin b'acin rai da yake ciki, har yakai bakin k'ofar fita Ummi takira sunansa,

"Babanah ka kula da kanka sosai" gyad'a mata kai kad'ai ya iyayi sannan yafita,

Tunda hajia kilishi ta d'ora mom akan hanyar salo da yaudarar da zata bijirowa dady da ita don ya maisheta d'akinta tafara shire shiren yanda zatayi yanzu haka kusan minti biyar kenan tana kiran wayarsa amma yak'i d'agawa, hakan ba k'aramin b'ata mata rai yayiba cikin takaici tajefar da wayar tana maseefa

"Lalle mutumennan yamatuk'ar walak'antani, yanzu nike kiransa yak'i d'agamun waya, wlh duk randa yashigo hannuna sai nasa yayi nadamar wannan abun da yayimun" dariya hajia kilishi dake zaune a gefen gado tana buga game da wayarta tayi ba tare da tad'ago kan taba tace

"Saifa kin kai zuciyarki nesa yanzu don da alama uwar gidansa ta cikashe masa duk wani gurbi da kika kasa cikashewa acikin gidansa, mezai hana ki gwada tura masa text message, natabbata zai gani kuma zai karanta, ki kula banda rawar kai ko kuma kushe masa mata acikin alamurranki ai kingane ko?" Sai da mom tad'an bata rai tare da gallawa kilishi harara sannan tajawo wayar, message tafara rubuta masa kamar haka cikin zafi da k'unar zuciya

_Alhaji natabbata kana ganin kirana ka kak'i ka d'auka saboda yanzu banice agaban kaba, to koma dai meye yakamata kasaurareni kona minti d'aya ne saboda kasan ko meye dalilin da yasa nakiraka, alhaji kenan inaso kasani fa har abada babu wacce zata iya maye maka gurbina matuk'ar ina raye saboda nice uwar 'ya'yanka wacce tafara baka farincikin da aka kasa baka na tsawon shekaru don haka kuwa kasan ban cancanci walak'antawa daga gareka ba, idan kayi tunani ina jiran kiranka domin mu magantu_ tana gama rubutawa ta tura masa had'e da jefar da wayar ta dafe kanta da duka hannayenta.

"Wlh alhaji na neman sa in zubar da matsayina agunsa" kallonta hajia kilishi tayi sannan tasake maida hankalinta ga game d'in da takeyi tana fad'in

"Abune da yazame maki dole kiyi inhar kina so kikoma d'akinki don cikar burinki to dole kisauke wannan girman kan da jijji dakan da kike yimasa",

"Shikenan! He most to pay fo all this wlh" k'arar shigowar message a wayarta taji da saurin ta d'auko wayar tana duba amsar da dady yaturo mata,

" _Hmmm kice har yanzu da sauran zama kenan!_"

Da k'arfi mom tace "what?", kingani ko ai duk ke kika jamun wannan rainin, anfad'a masa cewa gidan namu isata yayi ne?"

"Cool k'awata" hajia kilishi tafad'a

"Mik'omun wayar naga mekika rubuta kuma wacce amsa kika samu da kika buga man wannan uwar tsawar acikin kunne"

Duk jahilcin hajia kilishi saida ta bud'e baki cike da mamakin kalaman da taga mom ta turawa dady, dafe goshinta tayi da tafin hannunta tana kallonta

"Ai kuwa da gaskiyarsa baki gaji da zaman gida ba, taya zaki tura masa wannan sak'o mai cike da isa da kuma izgilanci kuma kiyi tsammanin zai tsaya ya saurareki? Kash wlh so kike kib'ata mana tsari gaba d'aya, keda zaki yita lallashinsa da kalamai tausasa masu dad'i har kisamu ya saurareki amma shine zaki tura masa wannan shirmen? Cab...to wlh da sake indai baso kikeyi ki ida tsofewa agidan nan ba sukuma suna can suna bugun ingantacciyar rayuwarsu cikin soyayya ba"

"To yanzu ya kikeso nayi? nifa gaskiya bazan juri wannan sabon walak'anci nasa ba"

"Ai kuwa yazama dole kijure don cikar burinki idan kuma kin safe tun yanzu kin barwa Aisha shi sai intattara inawa inawa gobe inbar garin nan" da sauri takame hannunta

"Haba k'awata karki yimun haka, yanzu me kikeso ayi ko nace masa kuma?" shiru tayi ta kalleta ta kalli wayar sannan ta jefa mata ita ajiki,

"Maza kisake tura masa wani kuma kibasa hak'uri" jiki na rawa ta d'auki wayar don tana matuk'ar buk'atarta atare da ita domin batada wata madafa idan ba itaba, wani message d'in tafara rubutawa cikin jin haushin k'awar tata.

" _pls kayi hak'uri bahaka nake nufi ba, gaba d'aya narasa natsuwatace atare dani saboda rashinka akusa dani, nayi kewarka don Allah kayafe mani nayi nadamar abunda nayi kuma ashirye nake nagyara kuskurena_

Tana gama rubutawa ta mik'awa hajia kilishi wayar tana tuk'uburi domin taduba tagani idan yayi, murmushi tayi tana kallonta bayan tagama karan ce message d'in had'e da rubuta _I LUV YOU SO MUCH & AM MADLY MISSING YOU_ ak'asan rubutun sannan tayi sending message d'in wa dady tare da mik'a mata wayarta tace

"Shak'iyiya ana so ana kai kasuwa, to sai kijira amsa kigani yanzu"

A wannan karon kam dady dake zaune akan kujerar office d'insa yana duba wasu takardu tashi tsaye yayi cikin sauri kamar wanda aka tsikara da allura, lokacin daya gama karanta sak'onta, domin a iya saninsa tunda suke bata tab'a bashi hak'uri ba idan tayi masa laifi ba saidai yagaji da fushinsa sudawo su daidaita, amma sai gashi da kanta take basa hak'uri had'e da dad'ad'an kalamai, Allah sarki miji da mata sai Allah ko yanzu dady baisan badon karan kanta tayi hakan ba sai don ta cimma mummunan manufarta tare da taimakon k'awarta hajia kilishi" wani irin farinciki ya tsinci kansa aciki wanda ya haifar masa da nan take ya manta da kaidi da kuma makirci irin na mom, har zai kiranta sai kuma yafasa shima ya sake rubuta mayar mata da sak'on a takaice

_Da gaske kikeyi hajia Hussaina_

Tana karantawa tayi dariya tana cema hajia kilishi

"Kinga sokon har ya yadda, bari zakayi idan kazo hannu, dama indai wajen sanyin zuciya ne nasan babu kamar alhajina kuma ai inada tabbacin yana matuk'ar sona ransa ne yab'aci har yayimun haka" wani sak'on tasake tura masa

_Sosai kuwa alhajinah don Allah kasake bani dama zaka fahimci rashinka yasa na canza dukkanin halayyata nidai fatana kayafe mani kai da Auntynah_

A wannan karon cikin zumud'i dady yakira wayarta tana d'agawa tafashe da kukan makirci

"Kayafemun alhaji wlh nayi nadamar duk abunda nayi, nayi maka alk'awari zanbika zanbi aunty Aisha bazan sake yin abunda zai haifar da damuwa acikin gidan kaba" wani lumshe idanuwa dady yayi yanajin kukan nata har cikin ransa.

"Karki damu komai ya wuce, kiyi shiru bana son jin kukan nan naki yana azabtar da zuciyata" mom najin haka tasake fashewa da wani kukan dak'arfi har tanayi kamar tana sharar majina

"Kabarni inyi kuka mana, na zalinceka da yawa don Allah kayafeni" haka dady yayita rarrashin mom yana fad'a mata dad'ad'an kalamai har saida yaji muryarta ta daidaita sannan sukayi sallama

Kallon hajia kilishi data saki baki tana kallon ta cike da mamaki tayi ta sakar mata murmushi had'e da ajiye wayar akan gado tashige toilet abunta, saida tafito hajia kilishi ta iyayi mata magana,


"Hussaina dama shak'iyancinki da makircinki yakai haka shine har kike neman taimakona kina yimani kamar bakisan mekike yiba, to plan A yak'are tunda kun daidaita da mijinki nima gobe komawa zanyi yarage naki ki aikata plan B yanda yakamata inyaso idan kingama dashi saiki nemeni musan yanda zamu b'ullowa plan C.

Dariya mom tayi tana goge jikinta da towel tace

"kad'an kika gani, dama can fashiyar bak'i ke wahalsheni amma ana nunamun hanya shikenan anwuce wurin"

"Eh naga alama kuwa irin wannan makirci haka!"

Muryar hajia kaka suka jiyo tana doka sallama abakin k'ofar d'akin, bayan sun amsa mata ta shigo cikin shigarta irinta nagartaccin tsofaffi dake nuna shirin fitane tayi tace

"Muzamu fita nida papinku don Allah kuje kud'ora dinner kafin mudawo" da yake ba'a jima dayi sallar la'asar ba a lokacin,

Atare suka amsa da "adawo lpy hajia"







Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____26πŸ’Ž


Dady nagama waya da mom ya tattara takardu da laptop d'in dake gabansa yasa acikin jakar da yake zuwa office da ita dama lokacin tashinsa yayi, don haka batare da b'ata lokaciba yabar office d'in cikin farincikin dashi kansa bazai iya misal tashiba, yarasa dalilin da yasa duk irin rashin mutunci da mom keyi masa yakan tsinci kansa cikin farinciki aduk lokacin da yaji muryarta kuma yake samun tsananin damuwa da damuwarta.

Basmah kuwa ta shawu iya shawuwa, gaba d'aya halittarta ta canza kamar ba itaba, cikin awanni k'alilan tafita daga cikin hayyacinta takoma 'yar maye inbanda suruttai wud'an da basuda kai da ma'ana babu abunda takeyi har tagaji bacci ya soma d'aukarta, ganin hakanne yasa Bab's da suby suka d'aukota a mota sukazo da ita gida, koda suka iso anguwar su Basmah marece ya somayi don haka sai suka tsaya a farkon shigowa area su suka ajiyeta, cikin muryar dake nuna tatil suke suby tace

"Baassmah.... anan zamu ajiyeki fa..kitashi mana munzo layinku, ahh bazaki bud'e idanuwanki bane?..Allah mubazamu iya zuwa k'ofar gidanku ba saboda nasan dad d'inku ya dawo" cikin dak'ilalliyar muryar da bazaka iya fahimtar abunda take cewa ba ta lumshe birkitattun idanuwanta tace

"Indai ta dadyne mai sauk'i ne, kawai ni yayane banaason had'uwa dashi mugun kubcyne" gambun motar tafara bud'owa sannan ta sakko k'afarta a hankali tana faman tangad'i tayi kusan minti uku tana kokuwa da marfin motar sannan tasamu dak'yar ta turasa ya rufe da k'arfi, hannu ta d'agawa suby had'e da cewa,

"Mukamaaa gobe" daga nan suka tada motar sukabar layin aguje, wanda duk mai hankalin da yaga yanda ake tuk'in motar dole ya kauce don yasan ba lafiyayyune acikiba, kasancewar riga da sket ne a jikinta na atampa d'inkin yad'an kamata sai takasa tafiya yanda yakamata saboda yanayin tangad'in da takeyi hatta mayafinta kasa rufowa tayi saidai ta rik'osa ahannu, tafiya takeyi tana had'a hanya basu jima da wucewa ba sai ga motar yaya Mahmud ta kunno kai,da farko horn yafarayi don gaba d'aya b'acin ran da yake ciki ya hanasa gano ko waye agabansa, iya abunda yasani shine akwai mutum a gabanai, yayi minti biyar yana yimata horn amma ko kad'an hankalinta bai tashiba kuma bata razana ba kai kace titin na gidan sune, hakan ba k'aramin dad'a masa b'acin rai yayi ba akan wanda yake ciki, afusace yafito cikin motar da niyar sauke mata ruwan fitina amma abunda idanuwansa suka gane masa yasashi razana yaja baya da sauri yana nunata da d'an yatsa saboda duk wanda yaga yanayin da take ciki kobai san taba sai yagane abuge take, balle shida take k'anwarsa, Basmah na ganinsa ta turo idanuwa awaje tare da watsa hannuwanta gefe tace

"Shikenan ai najawa kaina, kawai kayi hak'uri" ta k'arashe maganar had'e da nufatosa, idanuwansa na hawaye ya duba gefe gefensa yaga babu kowa a layin saboda quite area ce irin ta masu kud'i babu ruwan kowa da kowa kuma da wuya kaga gittawar mutum awaje, cikin sauri ya rungumota ajikinsa had'e da nufar inda motarsa take, turesa shigayi cikin yanayin muryarta na irin mashaya tace

"A'aa...kada ka yimun wayo, idan zaka dokeni kadokeni anan idan kuma bazaka dokan ba kawai ka k'yaleni zan k'arasa da k'afafuwana" kallon k'afafuwqn nata yayi yaga ko takalma bata dasu hannu yasa ya sake goge hawayen da suka zubo masa yace,

"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, wannan wace irin musiba ce" dariya tayi had'e d'ora yatsanta akan lab'b'ansa,

"Shiiiii....musibace ko?" Tana waige waige ganin zata b'ata masa lokaci yasa yaja hannunta da k'arfi ya turata cikin mota sannan ya tayar suka nufi gida,

Yana shiga ya hango motar dady ya dawo don haka kai tsaye ya sake rik'ota ajikinsa ya shigo part d'in Ummi da ita, akan kujera ya ajiyeta, Billy ce tafara shigowa sannan Batool suna ganinta suka k'araso wajen aguje suka rungumota suna kuka, da alama abunda tasha yanada k'arfi sosai ko kuma batada k'arfin jinine saboda har yanzu bai sake taba, k'urawa Billy idaniwanta dake lumshe tayi kamar mai son gano wani abun sannan ta maido kallonta ga Batool dake tambayar sa cikin kuka,

"Yaya me yasami yayya Basmah!" Goge hawayen sa yayi batare daya bata amsaba saima cemata da yayi,

"Ina Ummi take" Billy ce ta amsa masa itama cikin kuka

"Tana part d'in dady"

"Ok Batool kije ki kirasa, ke kuma Billy jeki kid'auko mun gwangon peak milk da man zaitun" a hankali suka mayarda kanta akujera sannan suka tashi, kamar antsinkili Basmah ta rik'o hannuwansu su biyu da sauri tana fad'in

"Kudawo ba inda zakuje ku 'YAN UWANA NE!" kafin subud'e baki suyi magana sukaga tafad'o masu luuu ajiki, kallon Billy Batool tayi itama ta kalleta, atare suka d'ago fuskarta sai sukaga ashe vaccine ya ziyartota. Kallon ya Mahmud dake dafe da kansa sukayi,

"Yaya..." Alama yayi masu da hannu gefen kujera

"Ku kwantar da ita"


_*Manage pls, yau unguwa natafi kuma nagaji sosai, luv u allπŸ’‹πŸ’‹*_












Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

*HAPPY JUM@T TO ALL MY FANS, MUCH LUV😍❀πŸ₯°*


πŸ’ŽPage_____27πŸ’Ž

A haka Ummi tashigo falon cikin rashin walwala bakinta d'auke da sallama, hango Basmah da tayi a hannunsu Billy suna k'ok'arin kwantar da ita yasa tak'araso wurin da sauri takarb'eta had'e da rungumota ajikinta ta zauna akan kujera, hannu tasa tana d'an bubbuga kumatunta ahankali tana kiran sunanta cikin tashin hankali,

"Basmah, Basmah, Basmah kibud'e idanuwanki mana, lpy kike? Wai meke faruwa dakene basmah bakyajina? Basmah!" tak'arasa maganar had'e da girgiza hab'ar bakinta tana kallon idanuwanta data bud'e a hankali sannan ta sake kullesu saboda baccin da yayi mata nauyi, a hankali ta kwantar da ita akan kujerar sannan tajuyo tana kallon Mahmud daya tsura masu ido, dafa kafad'arsa tayi

"Babanah a ina kaganta? Kuma me yasameta hakane?" hannunsa ya d'ora akan hannunta dake saman kafad'arsa yana k'ok'arin maida wasu hawayen dake son zubo masa yace

"Ummi akwai matsala!, Basmah tafara shaye shaye, duk inda nayi tsammanin ganinta ba'a can na ganeta ba, daidai farkon shigowa layin nan naganeta abuge tsakiyar titi tamkar wacce batada gata, gaba d'aya tafita hayyacinta ko takalmi babu ak'afafunta, Ummi Basmah ta d'auko hanyar da bazata b'ulle ba kuma natabbata miyagun k'awayen dana hanata mu'amala dasu suka d'ora ta akanta" d'ora kansa yayi akafad'ar Ummi dake k'ok'arin goge masa hawaye yaci gaba da cewa,

"Ummi ina matuk'ar son 'yan uwana bana son wani abu yafaru dasu, duk da mugun halin Basmah bana fatar rayuwarta ta d'ore a hakan domin suma 'YAN UWANA NE! don Allah kiyi wani abu akai Ummi" a hankali Ummi keshafar sumar kansa tana rarrashinsa,

"Kayi hak'uri Babanah, komai na duniya mai wuce wane kuma babu wanda ke kaucewa k'addararsa, banida iko akan Basmah amma zanyi iya k'ok'arin da zan iya akanta, tsangwama da fad'a ko duka bazasu canza taba, haka kuma nuna mata soyayyr da take buk'ata ba abunda zai jawo illa sake jefata a had'arin rayuwa, don haka ka kwantar da hankalinka kukan beda wata fa'ida muyi hak'uri kuma mukarb'i k'addara, natabbata da sannu idan ana yimata nasiha da addu'a zata canza kamar yanda muke buk'ata kaji ko?" Bata jira amsar da zai bata ba tayiwa Batool umurni data zubo masa abinci takawo masa, Billy dake gefenta zaune itama ta mik'e ta d'auko gorar ruwa da fresh Orange juice d'in da Ummi tahad'a aka saka a fridge yayi sanyi sosai sannan ta d'auko glass cup takawo ta aza akan center table d'in dake gefen kujerar da suke zaune tajawosa agabansu ta ajiye, lokacin itama Batool takawo abincin da tad'ebo a plate ta ajiye akai, kallonsa Ummi tayi had'e da cewa "yanzu kadaure kaci abinci idan ka k'are saika watso ruwa kaji ko Babanah?"

"Ummi bazan iyaba, gaba d'aya yunwar dake cikina tafice mun" b'ata fuska Ummi tayi tace

"Bazai yuyu ba so kakeyi rashin lafiya yataso makane?" Bata jira mezai ceba ta d'auko Firar ruwan ta'ud'e ta tsiyayo a cup takai masa abakinsa batare da yayi mata musu ba yafara shan ahankali yana kallonta, sai da cup d'in yayi rabi sannan tajaye masa ta mayar ta ajiye, hannunta ta wanko tare da d'auko plate d'in abincin ta yamutsa tana basa abincin abaki, ciyakeyi yana kallonta hawayen nasake zubo masa afuska, ji yake azuciyarsa inama itace mahaifiyarsu ya tabbata da yau ba'a wayi gari ba 'yar

Please Login or Register in order to submit comment