Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke fad'a,wani farinciki ne ya mamaye masa zuciya ganin yanda Billynsa ke cikin jin dad'i da walwala, baisan lokacin daya shafo sumar kansaba tare da sakin wani k'ayataccen murmushin daya bayyanar masa da gaba d'a hak'oransa, ahankali yafurta "I luv u so much Billy nah!" Aransa kuma yatabbatar wa kansa da cewa komai zaifaru yau sai ya gabatar da soyayyarsa agareta, Billy kuwa bata fahimci komai ba cikin maganganun da Basmah tayi ba kuma itama ta fahimci hakan,

d'ago kai Basmah tayi daniyar yin wata magana ta hangosa a tsaye aji tagar d'akinsu hangosa a tsaye daidai lokacin da yake shafa kansa yana murmushi, kallon Billy da batasan abunda kefaruba tayi tasake maida kallonta agaresa ta tabbatar ita yake kallo, wasu zafafan hawayene suka zubo mata agefen ido tayi saurin gogewa, "junior taso muje mu gaida su Ummi duk yau sau d'aya naje gunsu" tafad'a tana k'ok'arin danne damuwarta. "Bye sisters sai kun shiga"

"Ok yayya gamunan zuwa" nan tabarsu tawuce part d'in Ummi, tana shiga yaya Mahmud nafitowa, kallo d'aya yayi mata ya tabbatar tana cikin damuwa, hannunta ya jawo suka rab'e gefen d'aki ya d'ago kai yana kallonta sannan yace

"Basmah kirage sa damuwa aranki, kisa azuciyarki duk abunda zai zamo naka Allah yariga daya rubutashi acikin k'undin littafinka kuma komai rintsi komai wuya sai yazamo mallakinka kinji ko?"

"Eh yaya" tafad'a atak'aice don idan tace zatayi wata doguwar magana to tabbas kuka zaici k'arfinta kuma bata buk'atar haka ayanzu, wucewa yayi itama ta k'arasa shiga palourn Ummi, tare ta taddasu ita da Umma zaune suna firar kyawon motocin da dady ya basu tare da Allah yasanya alkhairi kuma yak'aro bud'i, gaishesu tayi cikin natsuwa sannan tanufi d'akin Billy, Bayan sun amsa Umma tayi mata nuni da tazo ta zauna a inda suke, wani irin nauyi tajiya don bata sama zama cikin manya ba idan suna zaune, cike dajin kunya tak'araso wajen Umma tarik'o hannunta tana fad'in

"Oh ni hafsatu wai 'yatah ina zakije da wannan kunyar, kisaki jikinki nima mahaifiyar kice kinjiko? Haka zani kaiki d'a kinki kina b'oyon fuska Basmah"

"kinga kibarta haka ake son 'ya mace takasance da kunya ko agidan mijinta domin adoce ga duk 'ya macen da tasan kanta" ummi tafad'a tana kallon fuskarta cike da alamar tambaya don taga Basmah d'in ta canja cikin kwana biyu hadda d'an fad'awa tayi. "Basmah meke damunkine?

Shiru tayi kafin tace

"Babu komai Ummi"

"Anya Basmah?"

"Allah kuwa babu komai" shikenan Allah yasa haka d'inne. Basmah bata jima da barin wajen ba itama Batool tanufi part d'insu rik'e da ciki tana cewa Billy

"Twiny my stomach ina zuwa?" Ita dai Billy zaunenta tayi saboda bata son bin Batool mom tab'ato mata rai, haka kuma ganin Ummi da Umma a falo zaune suna fira yasa takasa walwala a part din nasu, shiru tayi tana faman karanta wasik'ar jaki kawai taji an rik'o hannunta, d'aga kai tayi da niyar magana amma yakasa bata damar yin hakan, jan hannunta da yayi yasata mik'ewa tabishi bud'e da baki tana binsa da kallo, can gefe bayan part d'in dady daba kowa ke iya ganin suba ya nufa da ita, dama tuntuni wannan damarce da zaiganta ita kad'ai yake jira shiyasa yana samu bai tsaya wata wata ba yanufi wajenta, suna isa yasaki hannunta sannan yayi folding hannuwansa akan k'irjinsa yakafeta da idanuwa yana kallon fuskarta data matse alamun b'acin rai, k'asa tayi da kanta tanajin haushin rik'o hannunta da yayi don ita tunda take babu wanda yatab'a rik'e hannunta inba yayan taba, jin yayi shiru baice komai ba yasa tajuya zatabar wajen, da sauri yasha gabanta cikin wata iriyar kasalalliyar murya yace

"Ina kuma zakije?" Tsayawa tayi batare data amsa masa ba, amma zuciyarta nabuga mata da sauri da sauri saboda tsananin b'acin rai, jitake yau daba d'an uwanta bane yaya Mahmud data shayar dashi mamaki, ahankali yafara magana cikin taushin muryar da bazaka tab'a cewa yaya Mahmud pilot bane...






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____50💎


Bilkisu! Shiru tayi batare data amsa masa, "Bilkisu" yasake fad'a yana mai kallon fuskarta dake kallon k'asa, d'ago kai tayi rai ab'ace ba tare da tace masa komai itama tana kallonsa.

"Wai meye na wannan ciccije fuska da kikeyi?, nidai nasan ba kalar tarbiyar da Ummi da daddy suka baki kenan ba ta wulak'anta d'an adam, d'an adam d'in ma kuma d'an uwanki" wasu yawu tahad'iye cike da takaici kafin itama tamayar masa amsa da

"Nima natabbata kaima ba irin tarbiyar dasu Umma suka baka kenan ba!, taya za'ayi ka kai hannunka katab'ani bayan kasan cewa yin hakan kuskurene kuma haramun bai halatta ba a addininmu" yanda take maganar ne ya tabbatar masa da cewa ranta ab'ace yake saboda rik'o hannunta da yayi hakan yasa ya rik'e kunnuwansa yana fad'in


"kiyi hak'uri tabbas nayi kuskure kuma hakan bazai sake faruwa ba" had'e da kallon idanuwanta, tajima batace komai ba kafin nan ta amsa masa da "Shikenan, ammafa ka kula yaya baniba da nake 'yar uwarka ko wace irin mace yin hakan agareta laifine kuma zunubine matuk'ar ba muharramar kabace" murmushi yayi had'e da cewa "insha Allah malama Billy, amma zanso inyi maki wata tambaya idan kin bani dama" nisawa tayi sannan tace to mukoma a guarding yaya don wlh bazan iya jurewa tsayuwa anan ba" bai so hakanba saboda wani dalili amma dole yabita suka koma can don bayada zab'in daya wuce yimata biyayya, zaunawa sukayi akan d'aya daga cikin kujerun dake wurin sannan tace

"Ina sauraren ka yaya Mahmud, Allah yasa nasani"

"Meyasa kwana biyu kika dinga wasan b'uya tsakaninmu?, meyasa kika canza ga yanda muke dake ada?, meyasa kika yanke shak'uwar dake tsakanina dake?, me yasa kikasa shamaki acikin kulawar da mukeba juna ada?" Dariya tayi had'e da cewa

"Tabd'i jam yaya! Wai duk kana nufin wud'annan tambayoyin dake kama da laifuka ni zan amsa su?"

"Sosai kuwa, tunda gashi da kanki kin fahimci cewa laifukane, kinga kuwa yazama dole ki amsa saboda ban san meyasa zaki aikata hakan gareni acikin lokaci d'ayaba"

"Saboda tsangwama, mugunta da kuma takurawar da katsiri yimani a wannan karon, shiyasa naga yadace inyi nesa dakai don kauce masu" tafad'a kai tsaye batare da shayi ko wani tsoro arantaba, hakan datayi yasa yaji yak'ara k'aunarta, d'ago kai yayi yana kallonta cikin wani irin so da k'auna yace

"Amma yakamata ace kin fahimceni dalilina nayin hakan, duk wannan abun da nakeyi ina yinsane saboda so da k'aunar da nake yimaki" 'yan k'ananan idanuwanta ta fiddo waje tana fad'in "kai yaya! Wane irin so da k'auna zasusa ka dinga yiwa k'anwarka haka? Gaskiya akwai alamar tambaya a wannan maganar taka?"

"Ofcourse Bilkisu, wannan tambayar ce nakeso nabaki amsarta tun kafin kitambaya, Bilkisu tun kina 'yar k'ank'anuwarki ni kuma ban mallaki hankalina ba nake jin sonki araina kema sheda ce akan hakan don zakiji Umma nafad'i banida zancen dayafi naki agida kuma idan mukazo babu wacce nake kulawa sama dake acikin gidan nan duk dako kasancewar kinada 'yan uwa bake kad'ai kike ba, gaba d'aya zuciyata tagama amincewa da ki zamo mallakina kuma uwar 'ya'yana, haka kuma gangar jikina da ruhina keta zab'amun amatsayin abokiyar rayuwata, dukkanin wani tanadi da buri nawa aduniya inayinsane wake kad'ai, kiyarda dani don Allah Bilkisu hakan ne tabbacin wanzuwar farincikina nahar abada, natabbata ubangijina ya halicceni ne da sonki daga cikin jinin 'yan uwantakar dake tsakanina dake kinkoga babu yanda za'ayi sonki ya iya ficewa cikin zuciyata sai inhar jininki dake yawo acikin jinina da kuma jikina zai iya fita, ki amince dani zan d'aukaka darajarki acikin 'yan uwanki mata kuma zantabbatar dacewa duk inda kika shiga sai an hango tsantsar soyayya da kulawar da nake baki atare dake, Bilkisu inayi maki so mai tsanani tunkafin insan koni waye, yanzu kuma dana sani inajin soyayyarki na shiga sau dubu acikin kowane lumfashi d'aya na rayuwata da zanyi aduniya" tunda yafara magana take kallonsa cike da mamakin wai anya wicked yaya d'in nanne nata kuwa?, anya yaya mahmud d'in data sanine kefitar da wud'annan kalamai masu tsananin nauyi agareta batare da gittawar kowane irin shamaki atsakanin suba kodai mafarki takeyi? Lumshe idanuwanta tayi had'e da bud'esu akan nasa tana kallonsa "Yes Bilkisu! I mean all dis for u, ba mafarki kikeyi ba, dagaske ne ina sonki sosai kuma bazan tab'a iya rayuwa ba idan babu ke, bazan tab'a komawa cikakken mutum ba face har sai wannan awazar da aka cira daga jikina tadawo mazauninta, kuma natabbata kece wannan awazar aka halitta mani amatsayin mata wacce kasancewar ta atare dani zai tabbatar da zamowata cikakken mutum rayayye, jarumta da kuma kamalata bazasu cikaba har sai kin yarje mani nazamo zaka ran gwajin dabin da zai iyayin yak'i acikin zuciyarki, wlh Bilkisu matuk'ar kika barni zansha wuya koma inrasa rayuwata gaba d'aya, ban tab'a son wata mace azuciyata ba inba ummanah ba kuma inada yak'ini akan kece tak'arshe insha Allah" speechless tazama don gaba d'aya ya d'ad'd'aureta da kalamansa, babu wata k'ofa da bai k'onk'osaba acikin zuciyarta kuma tabbas idan taci gaba da saurarensa gaba d'ayansu bud'ewa zasuyi, mik'ewa tayi da zimmar barin wajen kafin yayi galaba akanta yayi saurin zube gwuiwowinsa agabanta kamar zaiyi kuka,

"Kar kiyimun haka Bilkisu, kar kisa raina k'una da kuma cikin tunani don Allah kicemun wani abu kada kitafi kibarni da ciwo cikin raina"

"Meye haka kakeyi yaya? Shin baka gudun wani yazo ya ganka ahaka, don Allah karufan asiri katashi"

"Bilkisu, bazan tab'a tashi anan gurinba har sai kinsanar dani makomar soyayyata, bazan damu da duk wanda zai riskeni a hakaba koda kuwa Iyayen mune don Allah kikarb'i tayin soyayyata Bilkisu kada in rasa raina" lokaci d'aya taji wani irin tausayinsa ya mamaye mata zuciya, har ga Allah idan tace bata son yaya Mahmud tayi k'arya domin itama tun tana k'arama take dakon soyayyarsa saboda irin kulawar da yake bata, amma kuma wane irin tabbaci take dashi akan maganganun daya fad'a balle tayi saurin nuna masa tata soyayyar ba har sai tagwadashi ta tabbatar da shima yana sonta, kallonsa tayi tace

"Bazan b'oye makaba yaya Mahmud, nima gaskiya akwai wanda zuciyata keso tun ina k'an k'anuwa kuma shima yana sona, don haka kayi hak'uri muci gaba da zumuncinmu yanda muka saba" wani irin juyawa yaji kansa yayi hawaye suka zubo masa a idanuwa,

"Taya hakan zata faru bacin koda yaushe ina saka idanuwa akanki kuma natabbata babu wani dayake zuwa wajenki, kada kiyi wasa da rayuwata Billy don yanzu haka zuciyata gab take da bugawa" d'aure fuska tayi had'e da cewa

"Koma meye dai nafad'a maka, kawai kayi hak'uri ni inada wanda nake so" da sauri tabar wajen ganin yanda hawaye kezubar masa gudun kada yayi nasarar karya mata zuciya,

Tana kaiwa bakin k'ofar shiga part d'insu taci karo da Basmah dake tsaye tund'azu da tazo fitowa tahango yanda wanda takeso ke durk'ushe agaban k'aunarta yana baran soyayya, hakan yasa takoma da baya tayi tsaye saboda bazata iya komawa cikiba tasha kukanta sosai, tana niyar fitowa wajenne sukaci karo da Billy. Murmushi tayi mata had'e da kauda fuskarta saboda kada taga halin da take ciki, "yayya Basmah su Ummi na palour" tafad'a had'e da waigawa tana kallon inda yake duk'e har lokacin bai tashiba"

"A'a sun shiga kitchen" ta amsa mata atak'aice tare da barin wajen tana sharar k'walla.

Kwance take tana waya da all i have d'inta taji muryar jaddi na k'walo mata kira, "faraaha, faraaha.. Wai kina inane nake faman kiranki kikayimun shiru" yafad'a yana turo k'ofar d'akinta, da sauri ta b'oye wayar tana fik'ifik'i da idanuwa, jin anyi shiru yasa shi kuma tab'an garen sa yafara kiran

"Hello, hello" danne wayar tayi sosai har saida ta mutu gaba d'aya tare da mik'ewa zaune tana kallon jaddi dake k'ok'arin zaunawa agefen katifar "malamar asibiti, me kikeyi haka da kika kasa amsa kirana"

"Bakomai jaddi ina d'an duba wani abune to banjiba saida kishigo" zamansa ya gyara daidai yana kallonta yace

"Faraaha, ina ranar nace dake ina son yin magana dake idan kindawo wajen aiki amma shine da kika dawo baki tuntub'eni ba, gashi har yau anyi kwanaki da yin maganar" dafe goshi tayi da tafin hannunta had'e da cewa

"Yaa salam, wlh na shafa'a gaba d'aya, kwatakwata namanta da wannan maganar, kayi hak'uri jaddi banyi hakan da ganganba kodon in b'ata rankaba, amma yanzu gani gaka, kafad'i duk maganar da kake son fad'a mani ina saurarenka mijina" shafa kanta yayi yanajin tausayin jikanyar tasa data taso cikin hali na maraicin uwa da uba, ahankali yabud'e baki yana fad'in

"Kimanta da wannan tsohon mijin naki dake gab da shigewa kuahewarsa kiyi tunanin samun wani mijin mai nagarta da kuma kamala wanda zaiyi maki soyayya fiye da wacce nayi maki, yabaki kulawa fiye da wacce nabaki kinji jikata" rik'o hannunsa tayi tana d'an murzawa ahankali tace

"Jaddi baza'a tab'a samun wannan mutum ba aduniya domin kaine uwa da ubana, kamaye gurbin duhuna da haske alokacin da narasa mahaifana, kabani kulawar da tahanani zubar da hawaye taya kake tunanin akwai wanda zaifika awurina, don Allah kadena fad'ar haka jaddi karkasa nakasa yafewa kaina" murmushi jaddi yayi sannan yace

"Idan kina tunanin baza'a samuba to kibani dama ingabatar maki da zab'in danayo maki natabbata zaki fahimci akwai wanda zai yimaki wud'annan abubuwan daidai da yanda nayi maki koma fiye da hakan"

"Jaddi ni bana buk'atar hakan domin inada wanda nake tunanin zai kwatanta bani irin kular da kabani koda d'aya bisa goma ne" sosai yaji badad'i aransa amma sai yace

"Faraaha nariga nayi magana da aminina akan d'an wurinsa zaizo kuga juna, amma tunda bakya buk'atar hakan mezai hana ki amince yazo ku gaisa kinga daga nan zansan abunda zanfad'awa aminin nawa"

"Jaddi kayimun uzuri amma da zaku dakatar da zuwansa zanfi jin dad'i"

"Yin hakan tamkar watsawa aminina k'asa a idanuwane bayan nina buk'aci hakan amma tunda bakya buk'ata shikenan zance masa ya dakatar dashi har sai naje munyi magana" hakan datayi kuma sai taji badad'i aranta, aranta kuma jitake tamkar tacutar da masoyinta idan takeb'anta dawani amatsayin wai yana sonta, kuka tafashe dashi tare da fad'awa jikin jaddi dake k'ok'arin mik'ewa jikinsa duk ba k'wari tace

"Kayi hak'uri jaddi ina son mahmud sosai kuma nayi masa alk'awarin zan auresa amma idan kana buk'atar in saurari zab'in ka zanyi hakan don faranta maka......








*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____51💎


Karki damu, nafahimceki, zanje inyiwa alhaji bayani, kiyi shiru bana son kukanki kinji ko?

"Don Allah jaddi kayafemun idan nab'ata maka rai, na amince da zab'inka agareni koda hakan na nufin zanrabu da nawa zab'in har abada" d'ago kanta yayi daga jikinsa yace

"Had'uwarki dashi bayana nufin zaki auresa bane har sai inkun daidaita tsakaninku, saboda haka ki kwantar da hankalinki ni farincikin ki nake so, matuk'ar nagartar wanda kikeso takai ina tabbatar maki da bazaki rasashiba da yardar Allah" hakan daya fad'a sai yakwantar mata da hankali sosai tarungumesa tare dasa hannuwa tana goge hawayen dake kwance akan fuskarta, "nagode jaddi, Allah ya tsawaita mani rayuwarka, ina matuk'ar sonka sosai"

"Nima ina sonki jikata Allah yajik'an mahaifanki ya gafarta masu"

"Amin" ta amsa masa dashi tana k'ara kwantar da kanta ajikinsa.

A b'angaren Mahmud kuwa sau kusan goma yana sake kiran numberta but switch up sai yayi tunanin matsalar chajine don haka ya tashi ya fad'a toilet, wanka yayi ya d'auro arwalar bacci ya koma kan gado ya kwanta zuciyarsa cike da kewar abun k'aunarsa har bacci ya d'aukesa, can cikin dare misalin k'arfe uku da kwata nishin d'an uwansa ya farkar dashi, zazzab'ine sosai ajikinsa sai rawar sanyi yakeyi ga jikinsa yayi zafi sosai, cikin hanzari yaya Mahmud yatashi zaune yana dafa goshinsa,

"'Dan uwa meyake damunka bakada lpy ne?" Tsananin yanda zazzabin yayi masa zafi yasa yakasa amsa masa, rik'o hannunsa yai yanaso yayi masa magana amma yakasa sai hawaye ke gangarowa daga cikin idanuwansa, ganin rawar sanyin da yakeyi tayi yawa yasa yaya Mahmud ya yaye bargon dake lullub'e ajikinsa yak'ara rufa masa ajiki, sauka kan gadon yayi yabud'e wardrobe d'in kayansa yaciro first aid box aciki, yamutsa box d'in ya shigayi yaciro pcm (paracetamol) cikin magungunan dake zube aciki sannan ya maida first aid d'in, fridge ya bud'e ya d'auka gorar ruwa marar sanyi sosai yadawo gefen gadon wajen kansa ya zauna ya kwand'aro maganin ahannunsa. Tallafo kansa yayi har lokacin jikinsa na rawar sanyi ya tura masa maganin abak'i, k'in karb'a yai yazame kansa zai koma ya kwanta yaya Mahmud yace

"Haba d'an uwa kadaure kayi taken pcm d'innan before asuba tunda yana treating fever, jikinka yayi zafi sosai da alama itace takamaka" bai jira cewarsa ba ya sake d'ago kansa saida yayi dagaske sannan yasamu ya tura masa maganin cikin baki saboda yanda hak'oransa ke bugun junansu, da sauri ya d'auko ruwan gorar yabud'e batare daya tsaya zubawa a cup ba ya d'ora masa bakin gorar, saida yaga yasha ruwan sosai sannan ya d'auke gorar abakinsa, maishesa yayi kwance tare da hanasa bargon zuwa wuyansa sannan yakoma inda yake kwance, kasa komawa baccin yayi saboda yanayin da yaga d'an uwan nasa keciki, hakan yasa ya d'auro arwala yafara nafilfili kafin asuba tayi,

Ab'angaren Billy ma hakance tafaru don kalaman Mahmud sun hanata bacci sai juye juye takeyi, duk yanda taso kauda tunanin agabanta saboda tasamu baccin ya d'auke ta hakan yacutara, tausayinsane ya kamata tuna yanayin data barshi d'azu aciki, ahankali ta shiga kunna bedside lamp d'in dake gefenta tana kashewa "Am so sorry yaya mahmud nima ina matuk'ar sonka fiye da tunaninka amma bazai yuyu in bayyana hakan agareka ba har sai natabbatar da k'arfin soyayyar da kake yimun, a wannan lokacinne zannuna maka irin girma da darajar da soyayyarka take dashi acikin zuciyata, kuma awannan lokacinne zan nuna maka so fiye da yanda kake tsammani" ganin baccin baida niyar d'aukarta yasa tamik'e had'e da shiga toilet ta d'auro arwala, salloli tafara tare da addu'ar Allah yazab'a masu alkhairi acikin soyayyar da suke yiwa junansu, tana a haka aka kira sallar asuba, saida tayi sallah had'e dayin azkar sannan takoma tad'an kwanta kafin hasken safiya yafito.


Yaya Mahmud kuwa ana gama sallar asuba ya taimakawa Mahmud pilot shima yayi sallah dayake balaifi jikin nasa yad'an saki duk da shi kad'ai yasan pain d'in da zuciyarsa keyi, komawa yayi zai kwanta yace

"'Dan uwa tashi ka canza kaya muje asibiti"

"Noo..thank you broth amma bana buk'atar asibiti tunda nasamu sauk'i"

"Are you serious?" Ya tambayesa yana kallon yanda yad'an fad'a kad'an saboda gaba d'aya jiya bai samu yin bacci ba.

"Ofcourse Alhmdllh nasamu sauk'i" jin hakan yasa yaya Mahmud ya shaye kan gado saboda baccin da yakeji a idanuwansa yana fad'in

"Allah yak'ara sauk'i" ya kwanta abunsa tare dajan bargon dake gefensa ya lullub'e

Kallonsa yayi yana mamakin yanda yasamu soyayyar sa cikin sauk'i abun nurse d'insa amma shikuma bugun farko soyayyar wacce yake k'auna nashirin hallaka rayuwarsa" Runtse idanuwansa yayi yafara tunano kalaman da Billynsa tafurta masa nan take yaji wani irin abu nataso masa azuciya, da sauri yabud'e idanuwansa yana fad'in "no...." da k'arfi wanda saida yasa yaya Mahmud da bacci yafara d'aukar sa ya zabura, kallonsa yayi yace

"Anya lafiya kake d'an uwa? Kodai intaso muje asibitin" yana k'ok'arin saukowa daga kan gadon, hannu ya d'aga masa yana dakatar dashi,

"A'a d'an uwa koma abunka ka kwanta, babu wata matsala in sha Allah, dole yaya Mahmud yahak'ura amma kasa komawa baccin yayi yadawo inda yake ya zauna yana tambayarsa abunda kedamunsa, babu yanda baiyi dashiba amma yak'i fad'amasa saboda bayason yaga yagaza wajen nemo soyayyarsa da kansa, haka yagaji da tambayarsa ya k'yalesa yana furta Allah yasawak'e, yana zaunene yaji kiran faraaharsa a waya yashigo domin kobai dubaba yasan kalar ringing d'in daya samata daban dana saura, tashi yayi yaje ya d'auko wayar tare da zaunawa gefen gadon yace

"Hello golden heart! Kintashi lafiya"

"Lafiya klw all i have" tafad'a cikin sanyin muryar da zata tabbatar maka da yanayin damuwar dake tattare da ita, tsaye yamik'e cikin tashin hankali yace

"My faraah! Meyake damunki naji muryarki haka, fad'amun meke faruwa dakene my golden heart"

"Pls ka kwantar da hankalinka babu komai, kawai ina son ganin kane, natashi da wata irin matsananciyar k'aunarka da kuma kewarka sosai" ajiyar zuciya ya sauke wacce har tanajiyo fitar askanta akunnuwanta, ahankali ya furta mata

"Alhamdulillah Allah nagode maka daka tayar da masoyiyata cikin aminci da kwanciyar hankali, karki samu matsala indai wannanne nesa takusa zuwa kusa domin very soon zanturo iyayena sunemamun aurenki agun jaddi, kinga daga lokacin no more missing me kuma kullum muna tare da juna nahar abada" jin kalamansa yasa damuwar da take k'ok'arin b'oye masa ta haifar mata da fashemasa da kuka" tana cewa

"Kayafemun all i have, zan bawa wani damar zuwa ya ganeni da sunan maganar aure tsakaninmu bisa ra'ayi da kuma umurnin jaddi, bazan iya yimasa musuba amma natabbatar masa da cewa kaine zab'ina kuma wanda nake burin na aura" tak'arashe maganar tana sheshshekar kuka, wani irin juyi kan Mahmud ya fara yimasa da sauri yakoma ya koma bakin gadon ya zauna ya dafe kansa da hannu d'aya yanaji tamkar zuciyarsa zata b'alle ta fito saboda tsananin kishi, ya kusan minti uku a haka baice komai ba kafin can yace

"Hello kinaji"

"Eh ina jinka"

"Faraah! Kidena kuka duk abunda Allah ya tsaroga bawa sai yafaru to tabbas zai farud'in komai dubararsa da kuma wayonsa, rashin son b'ata maki rai da sakaki cikin damuwa shiya haifar da b'oye maki makamancin irin wannan damuwar da kike ciki, amma da yake ban isa canza duk abun da Allah yatsaro zai faru akaina ko akankiba sai yajuya samuwar b'acin ran agareki ta sanadin jaddi, kwana biyu da suka wuce dady yakirani ya sanar dani ya nemamun auren 'yar abokinsa, ana haka kuma saiga papi shimadai d'in abunda yafad'amun kenan!, naso nakiraki na sanar dake amma nakasa saboda gudun b'acin ranki" faraaha dake kwance tana kuka bata san lokacin data tashi zaune ba tana sharar hawayen dake zubowa daga idanuwant ba had'e da cewa "wai mekace!?, har mata biyu aka nema maka aurensu? Wannan wane irin sonkai ne haka, sufa sauran mazan ya ake so suyi daza'a tashi abaka har mata, kai kuma mekace masu papi" tak'arashe maganar cike da tsiwa abakinta, duk da yana cikin damuwa hakan bai hanasa yin dariyar da seda taji sautinta akunnen taba, cikin b'acin rai tace

"Au dariya ma kakeyi, wato kaji dad'i anbaka auren har mata biyu, ni kuma nakoma marar amfani awajenka ko,shikenan ngd" sanin cewa kishi ne yamotsa mata kuma yaji haushin abunda tafad'a masa shima yana so yarama ya sashi cewa

"Haba faraah! Meye abun damuwa da b'acin rai aciki, nariga nafad'awa papi da kuma dady ke nake so kuma sun amince da zab'ina kina shikenan kece uwar gidana ta gaban goshina ko kuwa" rintse idanuwanta tayi tanajin d'acin maganar da yayi azuciyarta, jin bazata iya jurar cigaba da waya da shiba yasa takashe wayar had'e da fashewa da kuka, aranta kuwa cewa take lallai ashe har akwai ranar da mahmud d'inta zai iya furta mata kalaman da zasu iya tarwatsa mata zuciya, kenan ita ke haukan kishin sa amma shi bayayin nata ko kad'an, kiransane yasake shigowa awayar tayi banza dashi har ta tsinke, dariya yayi kafin nan yasake kiranta amma tak'i d'agawa, saida ya kirata sau wajen takwas sannan ta d'auka had'e da cewa

"Mezai hana kakira sauran matan naka tunda uwar gida tak'i d'agawa?, ni nafarka daga baccin da nakeyi duk da banida mahaifin da zai samomin wani mijin da zan aura amatsayin zab'insa bayan nawa, zanyiwa jaddi magana yasake nemamun wasu mazan da yake tunanin sun dace dani duka suzo mu maganta har zuwa lokacin da zansamu daidaini kai kuma kaje ka k'arata da matan da aka zab'a maka" tak'arashe maganar tana k'ara sautin kukan da takeyi...sosai yaci mamakin maganganun ta masu cike da yarinta ga dariya na neman kucce masa amma ba halin yayi gudun kar ya b'allowa kansa ruwan da zasu had'iyeshe, gyaran murya yayi tare da danna dariyar dake nema taci k'arfinsa yace

"Relax my golden heart, ba hakan nake nufi ba....bayani yaci gaba dayi mata dalla dalla akan yanda sukayi da dady da kuma papi, amma duk da

Please Login or Register in order to submit comment