Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai balle ya kaita asibiti, wayarsa yasa Batool taje takarb'o masa wajen yaya mahmud pilot saboda Haba d'ayansu basuyi bacci ba zaune suje suna firar bankwana saboda gobe zasu koma borno shida Umma, tana zuwa karb'o wayar yake tambayarta ko lafiya nan tasanar dashi yayya Basmah ce batajin dad'i hakan yasa shima yabiyo bayanta suka dawo tare kuka takeyi sosai yana rarrashinta gaba d'aya yarud'e yarasa ta ina zaifara da wannan matsalar don dagashi sai Batool suka san halin da Basmah keciki akan soyayyar d'ana uwansu da baisanma tanayi ba, suna shigowa yakarb'i wayarsa yakira faraaha saida tayi ringing sau kusan biyar ta tsinke saboda baccin da takeyi kafin can yasake kiranta.

Cikin magagin bacci ta d'auki wayar had'e da sawa akunnenta, yanajin muryar all I have d'inta kuma da alama cikin tashin hankali yake tamik'e zaune da sauri a tsakiyar gadon. "All I have lafiya?"

"Lafiya klw faraaha don Allah kitaimaka kiyo mun text d'in magungunan ciwon zuciya masu kyau yanzunnan Basmah ce balafiya yace zuciyarta keciwo gashi dare yayi ballantana nakaita asibiti"

"Subhanallahi ita kuwa meyajawo mata wannan matsalar da k'ananun ahekaraunta?"

"Abeg faraaha wannan balokacin yin tambaya neba da amsarta ina jiranki yanzun kituromun"

"Ok" tafad'a tare da tsinke wayar tarubuta masa magunan da sauri ta tura masa, message na shigowa ya rik'o hannun Batool yamik'e tsaye tare da zaunar da ita inda ya tashi ya d'ora mata Basmah ajikinta yace

"Batool kikula da ita kina tofa mata addu'o'i bari naje nasamo mata wud'annan maganukkan" ficewa yayi pilot nabiye dashi suka nufi bakin gate,

"Dan uwa inazakaje awannan tsohon daren" mahmud pilot yafad'a yana kallonsa,

"Baka ganin 'yar uwata batada lafiya ne, kome tsananin dare aidole nafita nanemo mata magani"

"To mezai hana mu d'auki mota mukaita asibiti ai ina ganin zaifi ko?" Jiyowa yayi ya kallesa kafin yace

"Babu buk'atar haka d'an uwa domin banaso su dady susan abunda kefaruwa har sutashi daga bacci, kaga muntayar masu da hankali akan matsalar da zamu iya solving d'inta, idanu zaka iya fita acan bakin titi zanje akwai wani chemist anan innemo mata magani" ganin mahmud naneman jefo masa wata tambayar lokacinsa nak'ara b'aci yasa tayiwa maigadi knocking yace yabud'e masa k'ofa zai fita....




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

.👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____59💎


Da sauri malam habu yataso yabud'e k'ofar d'akinsa don dama ba bacci yake yiba zaune yake yana jiran kota kwana, yana ganinsa yace

"Ranka ya dad'e ko lafiya?"

"Lpy klw malam habu bud'e mun k'ofa" yaya mahmud yafada yana k'ok'arin maido kallonsa ga mahmud pilot daya d'oro hannunsa akan kafad'ar sa, e

"'Dan uwa kada kafita, kabari mud'auko mota mukaita asibiti i think dis is the solution"

"Noo..k'ara tasamu taimakon gaggawa tunda abunda sauk'i inyaso idan baiyiba da safe sai muje asibitin" yana gama fad'ar haka malan habu nabud'e k'ofa, bai jira yaji amsar da zai basa ba yabar wajen, hakan yasa shima yabi bayansa duk dako ba hakan yasoba amma bayada zab'in daya wuce yabi bayan nasa. Malan habu yaso bin bayansu shima amma mahmud ya dakatar dashi akan yazauna bakin aikinsa tunda yaga su biyune in sha Allah babu abunda zai samesu har suje su dawo, dole Mlm habu ya hakura bakinsa d'auke da adduar Allah yakaresu zuciyarsa nayaba k'ok'arin yaya mahmud akan kulawa da soyayya da yake yiwa 'yan uwansa, komai yataso akansu zakaji yana fad'in 'YAN UWANA NE cike da shauk'i da soyayyayaw da zai tabbataar maka da muhimmancin da suke dashi aransa,

Tafiya sukayi sosai kafin sukai babban titin da acanne suka sami wata babbar chemist kuma da alama akwai mutun aciki duk daba abud'e takeba, d'an k'wank'wasawa sukayi kusan sau uku kafin can suji muryar wani inyamuri yace

"Pls waye anan wurin"

"Am srry sir munzo sayen magani ne" abunka da inyamuri da son kud'i bai tsaya wata wata ba yabud'e, sunan maganin ya fad'a masa had'e da mik'a masa kud'in yakarb'a, maganin ya d'auko yamik'a masa yana fad'in

"Thank you sir" karb'a sukayi suka nufi gida cikin sauri suna shiga malam habu yamaida k'ofar ya kulle kamar yanda take, suna shiga part d'in kai tsaye suka shiga d'akin tananan kamar yanda suka barta har Batool d'in natayata kuka, maganin yayi shaking saboda na ruwane, sannan yabud'e yasa Batool ta d'agowa masa kanta yabata tasha dama har bayanin yanda za'a shasa Faraaha ta turo masa, bayan tasha Batool ta ajiyeta akan gado tashiga toilet shikuma yadawo gefen gadon wajen kanta yana shafawa ahankali tare da yimata sannu, Mahmud pilot dake tsaye bakin k'ofa shima k'arasowa yayi cikin d'akin yana jero mata sannu, da kai ta amsa masa had'e da rufe idanuwanta har ya gaji da tsayi yakoma parlour ya zauna shikuma yaya Mahmud nan yayi zaunensa har saida yaga bacci ya d'auketa sannan yamik'e yana kallon Batool dake can gefenta zaune idanuwanta sunyi jawur hadda d'an kumburowa sunyi kad'an saboda kukan datayi yace

"Kinemi wuri kikwanta kema kafin akira sallar asuba tunda itama baccin ya d'auketa kinji ko?"

Ahankali tad'an mirgina kad'an daga inda take zaune ta kwanta saiti kan Basmah fuskarta na kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tayi, da k'yar take fitar da lumfashinta don bakad'an taji jikiba, kallo yabita dashi yanajin wani irin tausayinta aransa, yanaji badon ita da Billy duka 'yan uwansa bane da yabayyana matsalar dake damunta ga iyayensu ko tadena shan wannan wahalar haka amma idan yayi hakan bak'aramin sonkai ya aikata ba, furzar da iskan yayi ahankali ta bakinsa had'e da cewa "Allahumma yassir wala ta'assir" sannan yafice daga d'akin, shima palourn yadawo yanemi waje ya zauna yana tunanin matsalar dake bibiyar rayuwarsa shida 'yar uwarsa ta b'angaren soyayya, kallon Mahmud yayi dake zaune ya dafa kafad'arsa had'e da cewa

"'Dan uwa kaje ka kwanta, tasamu sauk'i don har bacci ya d'auketa" sai da safe sukayi yawuce shikuma yayi kwancensa nan palourn batare da yadamu da komawa d'akin saba.

Kasancewar bai samu yin bacci sosai ba yasa da baccin ya d'aukesa har aka gama sallar asuba bai farkaba, sosai dady yayi makin rashin ganinsa masallaci shiyasa lokacin da suke dawowa ya tambayi yaya Mahmud pilot ina d'an uwansa yake abbai ganesa masallaci ba, nan yake sanar dashi abunda yafaru jiya k'ilan shiyasa baccin yayi masa nauyin shima badon dadyn yayi masa knocking ba kafin yatafi da bai samu sallar ba, "Ashsha" dady yafad'a tare da nufar part d'in yana fad'an meyasa basu taddo shiba. Suna shiga suka samesa palour yana sallah, ganin haka yasa dady yawuce d'akinsu Basmah shikuma Mahmud pilot yayi zamansa parlour wajen yaya Mahmud, koda yashiga yasamu Batool har ta sallame sallah da alama ita d'inma tamakara ita kuma Basmah na kwance kan gado, zauna wa dady yayi tare da shafa fuskarta ahankali yana tambayar Batool meke damunta, nan ta sanar dashi cewa ita dai bata saniba kawai dai taga tarik'e zuciyarta tana kuka tace ciwo take yimata, ajiyar zuciya dady dake kallonta ya sauke yana fad'in

"Ciwon zuciya kuma?, Allah ya sawak'e dole idan safiya ta ida wayewa muje asibiti kenan!" Basmah da alokacin tafarko tana bud'e idanuwa a hankali taji abunda yafad'a ta tattaro k'arfinta gaba d'aya tamik'e zaune tana fad'in "a'a dady basai munjeba nasha magani kuma naji sauk'i sosai" k'ura mata idanuwa yayi tare da mik'a hannunsa ya d'auko maganin da yaya mahmud yasawo jiya dake ajiye akan bedside wardrobe yana duba sunannsa, d'ago kai yayi yana kallonta kafin yace

"Basmah meye dalilin wannan ciwon nak?, a wud'annan shekarun da kike dasu bai kamata ace kinada ciwon zuciya ba"

"Dady daga Allah ne shike jarabtar bawa da ciwo aduk sadda yaso komai girman sa ko k'ank'antarsa kuma batare da yana da damuwar komai ba, dady kamanta shi ciwon zuciya hatta jarirai akwai wud'anda ake samunsu dashi lokacin da aka haifesu?" Shiru yayi yana nazarin kalamanta kafin yarik'o hannunta yace

"To meyasa bakyason kije asibitine" yayi maganar cikin damuwa da nuna kulawa sosai ganin haka yasa tak'ak'aro murmushi a fuskarta sannan tace

"Saboda alhamdulillah dady naji sauk'i sosai da taimakon yaya mahmud" rik'e hannunsa tayi tana dariya sannan taci gaba da cewa "dady kayiwa Allah godiya daya baka yaya Mahmud amatsayin d'a kuma magaji natabbata zai kula damu acikin kowane hali batare da yabari kashiga damuwaba" duk wud'annan abubuwan da takeyi cikin Mugun k'arfin haline don kada hankalin kowa ya tashi kuma batason aje asibiti har likita yanemi fayyace sirrin da take b'oyewa tarusa farincikin 'yan uwanta amma ita kad'ai tasan yanda takeji da kuma halin da take ciki sai Allahnta. Hannunsa yasa yajawo kanta ya d'ora asaman kafad'arsa yana fad'in

"Tabbas nasan Allah ke kawo ciwo gabawansa kuma nayi imani da hakan amma idan akwai abunda yake damunki kifad'amun ko dukiyata zata k'are duka matuk'ar bazaki cutu ko wani ya cutuba akansa nayi maki alk'awarin zaniyi makiahi kinji ko?" Wasu zafafan hawayene suka zubomata a fuska tayi saurin gogewa had'e da cewa

"Dady kayi mana komai aduniya baka barmu da matsalar kome ba, hatta yayan da zai iya kula damu kamar yanda kake yimana kabamu, to meye zai kuma dameni aduniya?, addu'arka kad'ai nake buk'ata nida 'yan uwana akan Allah yabamu ikon yimaka biyayya da kuma faranta maka kamar yanda kayimana har iya k'arshen rayuwarmu"

"Nasani Basmah ko bana duniya yayan ku zai kula daku fiyema da yanda nakeyi, addua kuma akoda yaushe ina yimaku, amma ina tsoron ko akwai wani sakaci danayi har wata damuwa tayi kuskuren isowa acikin rayuwarki shiyasa nafad'i haka amma tunda babu matsala alhamdulillah Allah yak'ara maki lafiya"

"Amin dady bari inje inyi sallah" tamik'e da k'yar har tana shirin fad'uwa wajen saukowa daga kan gadon, Batool ce tayi saurin rik'eta had'e da cewa

"Kiyi ahankali yayya kinsan jikinki baiyi k'wari ba" rik'ata tayi ta sauko kan gadon tarakata har toilet shikuma dady yana kallonsu cike dajin dad'in yanda suke ba 'yan uwansu kulawa, saida yaga fitowarsu sannan yabar d'akin ya koma parlour inda su yaya mahmud ke zaune, zaunawa yayi akan kujera mai zaman mutun d'aya yaya mahmud yataso a inda yake zaune yana gaida dadyn, sun jima suna tattaunawa akan matsalar ciwon Basmah tare da tunanin abunda yajawo matashi amma ko kad'an yaya Mahmud bai bari yabada wata alama da zata nuna cewa wai don tana son Mahmud pilot bane daga k'arshe dai dady yayarda cewa ciwon Basmah daga Allah ne kuma yana fatar Allah yabata lpy.

Part d'in Ummi yanufa yasanar masu da halin da Basmah keciki, sun matuk'ar tausaya mata sannan ya fice zuwa nasa part d'in, Billy kuwa tun kafin yagama fad'a masu tabar wajen tanufi part d'in mom cikin sauri fuskarta d'auke da damuwa, tuna abunda yafaru ranar da taje ganinta ita da mom da basa da lafiya yasa Ummi datayi saurin mik'ewa da zimmar zuwa ganota takoma tazauna, kallon Umma tayi dake tsaye itama don da atare suka mik'e zasu tafi idanuwanta nahawaye don har ga allah ta tausayawa Basmah sosai tace

"Ummansu kigaishemun da Basmaty Allah yabata lpy kuma ya yaye mata wannan lalurar"

Dady kuwa na isa part d'insa ya kalli mom dake cire bedsheet d'in dake kan gado tana shimfid'a wani ya kira sunanta had'e da mik'a mata hannu alamar tazo, murmushi tayi masa tare da ida gyara gadon sannan tazo inda yake tazauna tare da gaishesa, rik'o hannunta yayi yana d'an murzawa ahankali yana kallon fuskarta kafin yace

"Kintashi lafiya Momyn mahmud?"

"Lpy klw" tafad'a tana duk'ar da kanta k'asa don baitab'a kiranta da wannan sunanba sai yasa taji kunyarsa

"madallah amaryar dady kar dai kice kunyar wannan suna kikeji?" dariya tayi batare data amsa masa ba don indai salon soyayyane dady yakai k'arshe awajen bazata iya ja dashi ba, muryarsa tajiyo yaci gaba da cewa

"To ki ajiye kunyarnan agefe kije ki dubomun 'yatah Basmah batajin dad'i, ashe jiya da daddare gaba d'aya basuyi bacci ita da 'yan uwanta muna nan bamu san abunda kefaruwa ba, a gaskiya ina tunanin zanfara biyar kowacenku part d'inta saboda kula da yaranmu domin wannan nisanta kanmu da mukayi dasu don inganta tarbiyarsu zai iya cutar mana dasu, don ma Allah yasa yayan nasu na kusa aida muntarar da abunda bama so yau da safe" gaban mom ne yayi saurin fad'uwa jin 'yar tata ba lafiya had'e da mik'ewa cikin firgita, saurin rik'o hannunta yayi yace

"Relax ai yayanta natare da ita kuma alhamdulillah tasamu sauk'i, kitafi ahankali karkije idanuwanki surufe kijiwa kanki wajen sauka k'asa kinji ko?" d'aga masa kai tayi tanaji kamar ta k'wace hannunta daga rik'on daya yimata saboda yanda tamatsu taje taga halin da 'yar tata keciki, yana sakin hannunta tabar d'akin, da sauri da sauri take saukowa daga upstairs d'in sannan tanufi part d'inta, tana kawowa zata shiga part d'inta sukaci karo da Billy, wata uwar harara ta zabga mata itako Billy yi tayi tamkar bata ganeta ba tashige abunta, d'akin 'yan uwanta tanufa kai tsaye mom nabiye abayanta tana shiga tayi kan Basmah dake kwance kamar zatayi kuka "Yayya Basmah yajiki? Ashe bakyada lafiya, wayyo yayyatah sannu kinji" tafad'a tana d'ora hannunta akan fuskarta, itama Basmah hannunta ta d'ora akan nata tana murmushi "my sister naji sauk'i wannan irin rud'ewa haka da kikayi har ina, ni kwantar da hankalinki am ok kinji ko?, inasu Ummi lafiya suke"

"Lafiya klw, yayya dole in rud'e mana 'yar uwata balafiya tun jiya banjiba sai yanzu, bana son ganinku cikin halin ciwo ko damuwa wlh sai inji tamkar in maidosu akaina, ina sonku 'YAN UWANA NE ku dabanida tamkarku aduniya ina..." ai kafin tarufe baki taji andamk'o hannunta had'e da fizgota lokaci d'aya anjayeta daga kan gadon, tana d'agowa sukayi ido biyu da mom ta b'alla mata harara, "wannan wace irin takura ce yarinya ba lafiya kinzo kintasata agaba sai surutu kike yimata sai kace aku...mtsss dalla jaye kibani waje ai wannan dak'ik'anci ne" jayewa gefe tayi ita kuma ta zauna gefen gadon ta d'ago Basmah tarungume ajikinta tana yimata sannu, daga Batool har Basmah saida ransu yab'aci akan abunda mom tayiwa 'yar uwarsu, hawayene suka zubowa Basmah lokacin dataga Billy nak'ok'arin fita idanuwanta cike da k'walla ta kalli mom tace

"Meyasa mom?"

"Srry dota yajikin naki?"

"Naji sauk'i tafad'a" tare da kauda kanta gefe ita kuma Batool da sauri tarik'o hannun Billy tana dariya "laa kinga halin mom idan yayya Basmah batada lafiya duk sai tabi tarud'e tayita fad'a da mutane tamkar mu muka azo mata ciwon, shiyasa nake k'orafi kullum akan tafi son yayya Basmah dani, zo muhau tacan gefe karta had'a mana da duka" tajata suka hau kan gadon acan gefe dayake k'aton gadone irin family d'innan, murmushi Billy tayi tana goge hawayen da suka zubo mata don ba kad'an irin wannan wayon da twiny d'inta tayiba yabata dariya wai duk don tafaranta mata tahanata jin haushin abunda mom tayi mata ba, hakan yasa itama tadanne zuciyarta don tayi masu yanda sukeso wato gusar da damuwarta tace

"Ayya mom Kiyi hak'uri in sha Allah yayya zata warke, nida twiny kuma zamukai k'ara wajen dady tunda aka fifita yayya akan my twiny ko twiny?" Tak'are maganar tana kallon Batool, "k'warai kuwa my twiny haka za'ayi dole mom ta amsa quarry a wajen dady" gaba d'ayansu dariya sukayi hadda Basmah dake rungume ajikinta tace

"Kinjisu ko mom, ashe tare nake da 'yan partyn adawa ban saniba?" Rungume ta tayi sosai taci gaba da cewa "Momynah ink'ara sona sosai kinji?" Mom data b'ata rai bata san lokacin da dariya ta kucce mataba, wato ita zasu linkewa don farincikin 'yar uwarsu, murmushi tayi tare da hugging back d'in Basmah tace

"Zan kuwa soki sosai akan kowa tunda ke nafara gani", d'ago kai tayi had'e da cewa

"Mom shifa yaya mahmud d'inka?" Saida ta d'aure fuska sannan tace "nabarwa dadynku da matarsa" ko kad'an wannan dasu har Billy bai tab'a ransuba saima cewa da sukayi kamar sun had'a baki "aikuwa sun gode" suna dariya sallamar Umma da suka jiyo a parlour tasasu tsagaita dariyar tare da amsawa tana shigowa cikin d'akin mom tajanye Basmah daga jikinta tamik'e tabar d'akin batare da takalli ko inda Umma takeba, takowa bakin gadon tayi tana kallon Basmah da gaba d'aya tad'an zurma yace "'yatah sannu ya jikin naki?" Saida ta gaisheta sannan ta amsa mata da cewa jiki da sauk'i, bakin gadon Umma tazauna tana kallonsu Batool dake gaisheta tace "lafiya klw 'yan tagwayen Ummi, kuna nan kuna jinyar auntynku ko?"

"Eh Umma"

"To masha Allah, Allah yayi maku albarka, kurik'e junanku sosai kuma kowannenku yaso d'an uwansa fiye da yanda yake son kansa hakan zai k'ara maku dank'on zumunci kunji ko?" Haka ta dinga yimasu nasiha sosai don tana matuk'ar k'aunar 'ya'yan d'an uwan nata aranta, tajima d'akin kafin tayi masu sallama don zuwa anjima zasu wuce borno idan maigidanta dubai amince da suk'ara kwana biyu ba, saboda tayi tunanin barin tafiyar sai jibi saboda wani dalili tana jiran feedback daga wajensa.

Alhamdulillah jikin Basmah yayi sauk'i sosai don tana samun kulawa takowane b'angare hatta Billy yau yini tayi ad'akin nasu duk da yanda mom ked'an takurata hakan baisa tayi zuciyar tafiyarta ba, haka babu yanda Mahmud pilot baiyi da itaba akan yanaso sud'an keb'e yayi missing d'inta amma fir tak'i amincewa daga k'arshema kwancenta tayi takwana anan, iya jin haushi Mahmud yaji haushinta don shikam da gaske he badly missing her, haka yakwana yanata faman tsuki duk da yaji dad'i da alhajinsa ya amince suk'ara kwana biyu amma bakad'an yasamu damuwar rashin keb'ewa da masoyiyar tasa ba, yayi maya takai sau tara part d'in da sunan ganin Basmah amma azahiri Billynsa yake zuwa gani da sun had'a ido yayi mata alama tazo saita mak'e masa kafad'a tana dariya har yagaji ya hak'ura don kansa,

Da safe haka yadinga ciccin magani waishi alatilas fushi yakeyi akan abunda tayi masa ko wanka yakasa tashi yayi, shikuwa yaya mahmud yana fitowa wanka ya kallesa had'e da cewa "d'an uwa pls don Allah kataimaka karakani wajen papi inkarb'o address d'in zab'innan tasa ko nasamu nahuta da wannan naci nasa haka" tsaki yayi masa had'e da cewa

"God forbid babu inda zanje, kaje kai kad'ai, k'asan halin danake ciki kuwa zakazo kadameni?" Idanuwa yaya mahmud ya zuba masa cike da mamaki don tunjiya yalura da garasan da k'anwarsa keyi, murmushi yayi had'e da cewa

"Allah yabaka hak'uri, kumburi ga doki sakkiya ga jaki? Kada kaje d'in ai yau gareka gobe ga d'an uwa" yana gama fad'an haka ya gyarawarsa tsaf batare daya sake kallon inda yakeba, motarsa ya d'auka yaje gidan papi yakarb'o address d'in gidan jaddi sannan yadawo gida, yadad'e zaune yana tunanin mummunar shigar da zaiyi yaje gidan jaddi don ganin yarinyar saboda tace bata sonsa. Murmushi yayi saboda wata mafitar daya samu cikin sauk'i nan take yaji hankalinsa ya kwanta, wayarsa yaciro yakira faraaharsa da bata dad's da gama kumbure fuskaba saboda fad'a mata da jaddi yayi tagyara yau zuwa la'asar bak'on daya fad'a mata zaizo cikin satinnan to zaizo yau, firarsu suka sha ta soyayya suka faranta zukatan junansu batare da kowanenau ya bayyana halin da yake cikiba, suna kammala wayar faraaha tayi kwance akan katifar dake d'akinta tarufe idanuwa tana tunanin mafita akan had'uwarta da zab'in jaddi, wata irin dariya ta kwashe da ita had'e da cewa "yes" sannan tamik'e zuwa tsakar gida taci gaba da aikace aikacenta tana rera 'yan wak'ok'inta hankali kwance don ita kad'ai tasan muguntar data shiryayi anjima,..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____60💎


Cike da mamaki jaddi ke kallonta saboda bata dad'e da barin wajenba tana kumbure kumbure akan yayi mata maganar zuwan bak'on nata, amma abun mamaki cikin mintota kad'an sai gashi tadawo masa cikin fara'a da jin dad'i, tunanin dalilinta nayin haka yafarayi ganin bayada amsa yasa yaci gaba dayin abunda ke gabansa batare daya damu da hakan ba,

Mahmud pilot kuwa yana fitowa daga d'akinsu yanufi part d'in Ummi cike da damuwa, Billy ya hango tana tahowa daga part d'in mom yayi saurin b'oyewa gefen k'ofar shiga palourn yana jiran isowarta, tana zuwa ya tare bakin k'ofar had'e da kafeta da idanuwa, murmushi tayi tarab'a ta gefensa zata wuce yasake tareta, dariya tayi had'e da folding hannuwanta akan k'irji ta jingina ajikin bangon dake rik'e da k'ofar tana kallonsa, shima hakan yayi ad'ayan b'angaren bangon yana faman ciccije fuska, sunfi k'arfin minti biyar ahaka batare da kowanensu yace uffan ba, ganin haka yasa tasake yunk'urawa da zimmar shigewarta yayi saurin nufowa inda take, ja tadingayi da baya shikuma yana matsowa har saida takoma jikin bangon, hannuwansa yasa ajikin bangon yayi mata rumfa yana binta da kallo kafin yace

"Meyasa!?.meyasa kikayi haka? Billynah halama Bakya tausayina ne? Shin ko kinsan gaba d'aya jiya ban samu bacci ya d'auke niba ko kad'an saboda d'ai rashin jin zazzak'ar muryar nan taki?, shin kinsan kuwa irin halin da nashiga adaren jiya saboda rashin abincin zuciyata da kika saba bata amma kika hanata? Haba qanwata kinsanfa dad'ad'an kalamanki sune ke qarawa zuciyata nagartabda k'arfin iya rik'e gangar jikina, k'iris kad'an yarage jiya kisa inyi dying saboda kinbar zuciyata da yunwa har tayi raunin da bazata iya rik'eni ba, badon idanuwa da suka taimaka mataba wajen kusanto mata da wannan kyakkyawar fuskar takiba da bansan makoma taba adaren jiya" tunda yafara magana take kallon cikin idanuwansa har ya dasa aya, lumshe idanuwanta tayi had'e da cewa

"Dagaske kake?" K'ara matsowa yayi a kusa da ita sosai tayanda zata iya jiyo sautin bugawar zuciyarsa shima d'in yana kallon cikin idanuwanta yace "baki yarda bane 'yan mata?" Yanda tagansa very close da ita yasa gabanta yashiga bugawa da sauri da sauri, zillewa tayi ta gefensa a k'ark'ashin hannunsa tashige palourn da sauri, juyowa tayi tana murmushi tare da kad'a kanta tace.

"Sosai nayarda don nima hakanne tab'angarena, karka damu domin nid kai tagwayen junane, kasa aranka tare zamu rayu kuma tare zamu mutu in sha Allah" d'ago kai tayi takallesa daga can cikin palourn tayi dariya sannan tawuce zuciyarta cike da k'aunar yayan nata

Nan take Mahmud yaji wani irin farinciki marar misaltuwa yarufesa, aransa yanaji babu abunda zai rabasa da Billynsa inba mutuwa ba domin tagama tabbatarwa da zuciyarsa itama tana sonsa tana k'aunarsa kamar yanda shima yakeyi, Nan take yayanke shawarar suna komawa borno zai sanarda alhajinsa azo atsaida magana tare dasa rana don bazai koma wajen aikin saba har sai yagama mallakarta amatsayin matarsa.

Bayanta yabi shima ya shigo palourn ya tadda Bilal da Bassam suna homework da aka basu a makaranta da taimakon Ummi dake zaune tana nunnunamasu shikuma junior yana gefensu shima sai gwalaje yakeyi awani extra buk daya tsira rigima Ummi tabashi saboda tasamu yabarsu suyi home work d'in cikin kwanciyar hankali, bakinsa d'auke da sallama ya k'araso cikin palourn fuskarsa ba yabo ba fallasa ya gaida ita cikin natsuwa yana kallon k'annen nasa dake faman gaishesa suma, amsawa tayi had'e da tashi tabar wajen don itakam kunyarsa takeji yanzu abunka ga fulani, dariya Umma dake fitowa daga kitchen tayi tana tsokanarta "dama kindena jin wannan kunya don andad'e da dena yayin haka banda abunki ai Mahmud d'an d'an kine tunda ahannunki aka haifesa kuma ke kikayi yayensa fitsarinsa da kashinsa babu wanda bakiciba, to meye najin kunyarsa yanzu? Zaifi maki sauk'i ki ajiye sarakutar agefe kibarshi amatsayinsa na d'anki" murmushi d'ai Ummi tayi batare data tanka mata ba tawuce d'aki abunta ita kuma tana tayimata dariya, shikansa dariyar yakeyi jin yanda tabud'ewa Ummi wuta yace "Kai ummanah"

"Eh mana, nifa ba wata kunya kaida Bilkisu duka kallon 'ya'yana nake yimaku don kasani baka fitaba awajena"

Game girarsa ta sama data k'asa yayi yana kallon k'ofar d'akin Billy da itama tana can tana dariyar maganganun Umma yace

"Ummanah don Allah kidena fad'a kada taji tarenani" basar dashi tayi ta mik'awa su Bassam goldenmon da madarar data had'o masu a kofuna, saida tazauna sannan tarik'e hannunsa "Meya kawo maganar raini Mahmud indai ba tsanani tsakaninku, ai tausayawa da kulawa da juna cikin rayuwar auratayya ita kesa mata girmama mijinta, bawai girmansa ko d'aure fuskarsa ba ko fifikon matsayi ko kuma cutawa ba" hannunsa yasa ya rumk'e na Umma had'e da cewa "Ummana da wasa nakeyi taya zan iya nuna duk wud'annan abubuwan ga 'yar uwata, jinina kuma wacce

Please Login or Register in order to submit comment