Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai faru don haka dole nima nayi abunda kebisa tsarin da Allah yayo.ni zan wuce, amma idan o.c ya rufeni dafad'a to Allah kai zance kasani kula maka da wata patient"

"Ai ba za'ayi haka ba, muje nataka maki"

"A'a nahutar dakai wannan ai hurumin all I have ne" tana gama fad'ar haka tafice abunta shikuma yaci gaba da aikinsa.

Mom kuwa tun ranar da umman borno tazo take jiran jin sakamakon k'ullin data yiwa Ummi awurin dady amma taji shiru gashi tun daga ranar taga dady yad'an sauya mata, yau tak'uduri niyar zata yimasa magana akan dalilin wannan sauyi daya yimata, bayan yadawo daga wajen aikinsa dama ak'a'idarsa inya dawo yakan shiga part d'in kowaccensu yaduba halin da take ciki ita da yaranta, yana shiga ko gaisawa basuyiba tana faman d'ad'd'aure fuska da hurar hanta tace

"Wlh nagaji da wannan walak'anci da tozarcin da akeyimun acikin gidannan, azalinceni in fad'a maka kuma ka kasa d'aukar kowane mataki akai, kuma tsabar cuta a shirya makircin da zaka dinga d'ad'd'auke mani kai, haba alhaji ai wannan ba adalci bane" tafashe da kuka kamar wadda aka cutawa kamar yanda tace. Murmushin takaici dady yayi kafin yajawo hannunta ya zaunar da ita gefen gadon da yake zaune, rarrashinta yadingayi yana bata hak'uri har saida yaga tayi shiru sannan yak'walawa Basmah kira,

Cikin girmamawa Basmah ta amsa ta taho, abakin k'ofar d'akin tatsaya tayi sallamah, dady yabata izinin shigowa, gaidashi tayi sannan tace

"Gani dady" saida ya kalli idanuwan mom da kamar ba ita bace tagama kuka yanzu sannan ya d'aure fuska sosai yana kallon Basmah.

"Basmah so nake intambayeki shin wai umminku tazo duba momynku dake ranar da bakwada lafiya ko kuwa?, don ni abunne yaban mamaki saboda ranar banga alamun tazoba, sai umminku kefad'amun wai tazo shine nace bari dai inkira 'yatah intambayeta don intabbatar da hakan, shin da gaskene tazo?" D'ago kai Basmah tayi suka had'a ido da dady tace

"Laaa...eh wlh dady tazo ita da sister da safe lokacin ma ina d'aki ina rarrashin Batool dake kuka, naji sallamarsu, ina zuwa na tarar dasu abakin k'ofa, nace su shigo, shine da ummi taji kukan Batool take tambayata dama nida Batool ne ba lafiya taji kamar kace nida mom, to nan nake sanar da ita mom d'in daice Batool daga bayane itama tajimu, nan naje nakirawo mom suka gaisa har ummi na lallashin Batool data dawo itama nan falo, saidai bata wani jima ba tayi mana Allah yak'ara sauk'i suka tafi ko mom?" Tak'arashe maganar had'e da kallon gefen da mom take zaune tun d'azu tana faman k'yak'yaftawa Basmah idanuwa akan tayi shiru amma bata masan tanayi ba, don bilhakki Basmah tazata fad'a dady zaiyiwa Ummi shiyasa ta tak'ark'are tana koro masa bayani, ikon Allah kenan, idan kazamo mai maida alamurranka ga ubangiji to kana zaunenka Allah zai dinga yimaka fighting da kansa ga duk wanda keda niyar cutarka, kana nan zunenka ana cinno maka wuta sai wani yayita ingije maka ita batare da sanin kaba, da gangan dady yayiwa Basmah wannan tambayar saboda ya nunawa mom kuskurnta idan zata gyara. Dady na murmushi ya kalli mom yace

"Tabbas kinyi gaskiya Momyn yara, saidai yanzu da 'yatah tayimun bayani nafi samun gamsuwa, hak'ik'a kin burgeni da kika kasance mai yiwa 'yar uwarki shedu nak'warai, Allah ya shirya kuma yaci gaba da ganarwa" Basmah ta amsa da amin sannan dady yace zata iya tafiya sannan taje takirawo masa yaya Mahmud da kuma Mahmud pilot.

Tana fita shima dady yamik'e tsaye had'e da kallon mom yana fad'in

"shin yanzu zaki iya fad'amun tsakanin ke da ita waye aka cutar kuma waye wanda aka zalinta waye aka shiryawa makirci acikinku, sannan kuma inaso kifad'amun tsakanin ke da ita waya cancanci ayiwa abunda kika lissafo ana yimaki agidannan?" yana gama fad'ar haka yafice abunsa batare da jin wani d'ar azuciyar saba.

Kwance yake akan gado sai faman juye juye yakeyi yana buga tsaki don gaba d'aya wayar da yaya Mahmud keyi da faraaha sake tsananta masa ciwon dake zuciyarsa takeyi, kimanin kwana biyu kenan baisa Billy a idanuwansa ba wanda hakan ke matuk'ar cin zuciyarsa fiye da tunani, ji yake bazai iya rayuwa idan babu billy atare dashi ba kuma shi yanzu yagama yanke shawarar aurenta zaiyi don bazai zauna da damuwa aransaba amma taya hakan zai faru bayan yakasa fuskantarta ido da ido yafad'a mata sirrin dake ransaba, gashi yanzu tunda tafara tsanar alak'ar dake tsakaninsu saboda gwatsileta da yake yawanyi yasa tadena yadda suhad'a hanya da ita, mezai yi yanzu ya gyara wannan kuskure taya za'ayi ya fahimtar da ita tsagwaron k'aunarta dake ransa kuma azuciyarsa tuntana 'yar k'ank'anuwa, rashin samun amsarsa yasa zuciyarsa tafara yimasa zafi yana fitar da wani nishi da k'arfi da k'arfi kamar wanda za'a zarewa rayuwa. Tsananin ciwon da yakeji ne yahaifar masa da fashewa da kuka yana juye juye, afirgice yaya Mahmud ya katsiye wayar da yakeyi yayo kansa yana fad'in

"'Dan uwa, meyake faruwa da kaine?, fad'amun meke damunka d'an uwa" dak'yar Mahmud pilot yabud'e baki yana hawaye yace

"Bazan rayu inbabu keba 'yar uwata, ina matuk'ar sonki, amma duk hanyar da zanbi tafahimceni takasa, kullum gani take kamar tsarguwar tace nakeyi hakan yasa taharamta mani ganinta gaba d'aya, d'an uwa sonta ajinina yake don Allah kataimaka ka fahimtar da ita" wani irin farincikine yarufe yaya Mahmud sanin cewa 'yar uwarsa Basmah kad'aice kenuna tana sonsa kuma yatabbatar da ita yake nufi amma don yaji da bakinsa yafad'a ya tallofo kansa had'e da d'orawa ak'irjinsa yana goge masa hawaye.

"'Dan uwa ban fahimceka ba wai wace yarinyar ce kake nufin ta jefaka acikin wannan hali fad'amun ko wacece nayima alk'awari zansa tasoka koda hakan zaisa narasa farinciki atare dani"

"Broth 'yar uwa tace ba..." Kasa iyarwa yayi had'e da rik'e hannun yaya Mahmud sosai saboda wani irin tari daya taso masa ba k'ak'k'aftawa.....







*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Ban manta dakuba qawayen k'warai, abokanan kirki, akowane lumfashi da zanyi kuna nan mak'ale acikin zuciyata❤ gaisuwa mai tarin yawa da fatar alkhairi agareku, *SA'ADATU SHEHU BUNGUDU, SARATU ADAMU, ZAINAB 'DAN MALAM, MOM HAFSAT BARUMI, FARIDA MOH'D GUSAU, MARYAM BELLO, SADIYA M LADAN, RUK'AYYA BELLO KARIKKAI, ASMA'U UMAR GUSAU, ZARA'U MOH'D MARADUN* ina matuk'ar alfaharin zamowarku atare dani Allah yaraya maku zuria kuma ya sanya masu albarka, ina so kusani BIL-SAN KAURA takuce kuma tana sonku irin sosai d'innan💋🤝🏻_

💎Page_____45💎

Dady nafitowa yaci karo da Basmah zata shiga kitchen yace

"Bacewa nayi kije kikirawomun yayun kiba, mekuma ya tsaishekine? Maza kije kice susameni a falon umminku ina jiransu.cikin hanzari tanufi d'akin yaya Mahmud, wanda nan take sai taji gabanta nafad'uwa, bakin k'ofa tatsaya tare da rik'e handle d'in k'ofar da niyar yin sallama sai kuma tafasa jin kalaman dake tasowa daga d'akin, har ga Allah taji dad'i lokacin dataji Mahmud pilot ya ambaci cewa 'yar uwarshi ce yakeso wanda gaba d'aya tagama yarjewa zuciyarta cewa hak'ar tace ta cimma ruwa, jiki narawa tamatsu taji ya ambaci sunanta amma kash sai tarin da yakeyi ya hanasa iyarwa, hannayenta ta had'e waje d'aya kamar mai addua tana kallon sama yayinda zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, sai da tarin ya tsagaita masa sannan yabud'e baki ahankali yace

"'Yar uwa tace Balkisu, ina matuk'ar sonta fiye da komai d'an uwa, rasata tamkar rasa rayuwata ne!" Tsaye chak Basmah tayi jin abunda yaya Mahmud pilot yake fad'a wai 'yar uwarta Bilkisu yakeso! Wani irin kukane da bata san lokacin daya zomataba ta kucce dashi, hannu tasa tayi saurin to she bakinta tana bin jikin bango da take jingine dashi har takai k'asa, ta kusan minti biyar awurin duk'e tana kuka kafin da sauri ta tashi da guda tabar wajen tanufi cikin guarding tana kuka mai tsuma zuciya.

Yaya Mahmud kuwa gaban sane yayi wata irin muguwar fad'uwa wanda har sai da yasa kansa sarawa, innalillahi wa innalillahi wa'inna ilaihirrajiun yake fad'a acikin zuciyarsa, saida yayi dagaske sannan wani irin kuzari yazo masa tare da k'arfin halin cewa

"Enough d'an uwana, akan wannan zaka tashi hankalinka har kake nema kasa kanka cikin wani hali? Hala ka manta cewa kai d'an uwane, kuma dady namatuk'ar sonka fiye da tunani babu abunda zaka nema karasa indai a gidannan ne, pls don Allah kasa aranka tamkar Billy tazama taka, kawai kafara ba Allah zab'i sannan kanemi soyayyarta natabbata dady zai aura maka ita kaji ko?" Haka yadinga yimasa kalaman da zasu kwantar masa da hankali har saida yaga yazama normal.

Basmah kuwa kuka tayi sosai har saida kanta yasoma ciwo sannan taje ta wanko fuskarta ga fanfo amma duk da haka hawayen basu daina zubowa a idanuwan taba, komawa guarding d'in tayi tazauna tana tunano abubuwan da suka faru ranar da tajata suka tafi tabasa hak'uri wanda tun alokacin yakamata tagane cewa yana son Billy amma saboda yanda so ya rufe mata ido sai tadinga yaudarar kanta dacewa 'yan uwane shiyasa hakan kefaruwa. Rufe rabin fuskarta tayi da tafin hannuwanta idanuwanta na tsiyayar da hawaye tace "wa ufawwidu amri ilallah, ina matuk'ar sonka yaya Mahmud soyayyar da banida tabbaci akan zata fita azuciyata amma yazama dole zan hak'ura dakai koda hakan na nufin zan rasa rayuwata, bazan koma nuna maka soyayyar danake yimaka ba, zan jure zafin rashinka, zan sadaukar da farincikina agareku domin kud'in 'YAN UWANA NE!, shiko yaya Mahmud fitowa yayi shima yanajin wani bak'on yanayi atare dashi, yanaji aransa cewa yafi kowa shiga tsaka mai wuya saboda yanda yasan irin son da Basmah keyiwa Mahmud ba kad'an bane kuma zata iya shiga damuwa idan tasan da wannan maganar, kuma bayaso yarasata, sannan kuma gashi yanzu mahmud yanuna masa irin tsantsar son da yake yiwa Bilkisu wanda yatabbatar masa da rasata zai iyasa shima yarasa tasa rayuwar, kuma yaga hakan atattare dashi, goge hawayen da suka zubo masa a idanuwa yayi ahankali ya furta "ya Allah kawarware wannan matsala cikin sauk'i domin dukkaninsu 'YAN UWANA NE banaso narasa ko guda daga cikinsu" wayar sace tayi k'ara ya d'auko yana duba sunan wanda ke kiransa, ganin dadyne yasa yad'aga da sauri kafin ta tsinke had'e da daidaita muryarsa yace

"Hello dady barka da rana"

"Yawwa my son, tun d'azu naturo Basmah takira maniku kuma naga lokacin data wuce amma har yanzu banganku ba, lpy kuwa?" gaban Mahmud ne yafad'i cike da tsoron Allah yasa bata k'araso ba taji abunda ke faruwa cikin rawar murya yacewa dady

"Dady Bas.ma.h kuma!?"

"Eh ko batazo bane?" d'ago kan da yaya Mahmud zaiyi yagoge zufan daya keto masa sai ya hango Basmah zaune cikin guarding ta tura kanta cikin cinyo yinta wanda hakan ya tabbatar masa da kuka takeyi. da sauri ya amsawa dady da

"Aa tazo dady gamunan zuwa" katse wayar yayi aransa yana fad'in shikenan tafaru tak'are don yanayin daya hangota aciki ya tabbatar masa da cewa taji komai, ahankali ya dinga takowa zuwa inda take zaune, gefenta yazauna tare da sa hannuwansa ya d'agota,

"Basmah lpy kuwa?"

Juyowa tayi tana k'ok'arin maida hawayen dake son zubo mata had'e da yin murmushi tace "lpy klw yaya Mahmud, dadyne ya aikoni inkiraku sai naji kaina yad'an sara mun shine nazauna anan har yakwanta sai intafi, amma tunda gaka nagani kafad'awa yaya Mahmud dady na neman ku yace kusameshi a part d'in Ummi, mik'ewa tayi tare da goge hawayen da suka zubo mata zata bar wajen"

hannunta ya rik'o "Basmah fad'amun gaskiya, shin ko wani abunne yafaru" girgiza masa kai tayi batare data juyoba hawayen naci gaba da zubo mata, "idan gaskiyane to kijuyo ki kalleni mana, fad'amun su hawayen da kikeyi na meye idan har babu abunda yafaru?" Juyowa tayi had'e da fad'owa kan jikinsa tana kuka "yaya am too late, ashe zuciyar yaya Mahmud tadad'e da zamowa mallakin k'anwata bansani, gashi nayi nisa sosai a soyayyar sa, yaya ya zanyi nafiddashi acikin tawa zuciyar?" Sosai 'yar uwarsa tabasa tausayi amma shikansa baisan amsar da zaibata ba, idan yace tacire Mahmud aranta baiyi mata adalci ba, idan kuma yace tabayyanar da soyayyarsa ga iyayensu shima baiyi masa adalciba tunda yafad'a masa wacce yake so, haka yabarta ajikinsa tayi kukanta mai isarta sannan ya d'agota, kallonsa tayi da rinannin idanuwanta da sukayi jawur duk shacin jini ya kwanta aciki saboda kasancewarsu manya, murmushi ya sakar mata had'e da sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Basmah kiyi hak'uri, bansan yanda zamuyi da wannan al-amari ba, amma inaso kisa azuciyarki Billy'yar uwar kice kuma duk wani ciganta nakine, kibarwa Allah dukkanin al-amurranki natabbata bazai tab'a bari ki wofantaba, be strong Basmah nasan zaki iya kinji ko?" Jijjiga masa kai tayi tana murmushi alokaci guda kuma hawaye nazubo mata "I will yaya, but fore sure ina matuk'ar sonsa, kuma bazan iya denawa ba amma zan tirsasa zuciyata tarage k'aunarsa don natabbata narasashi"

"Karkice haka Basmah _laa taqnad'u min rahmatillah_ Allah da kansa yace kada mud'eba k'auna daga rahamarsa, kuma yak'ara da cewa _faswabrun jamil_ wato hak'uri abune mai kyau, don haka kidaiyi hak'uri kuma kiyiwa addua kinji ko?"

"Zanyi in sha Allah yaya Mahmud, kaima katayani addua"

Da haka yata janta da labarai masu dad'i da kuma faranta zuciya har saida yaga tad'an saki abun sannan ya mik'e yana fad'in

"Yau kinsa nayiwa dady laifi, dole inazuwa infara da bashi hak'uri na rashin amsa kiransa da banyi ba cikin gaggawa" murmushi dai tayi masa sannan tawuce shi kuma yakoma d'aki ya sanar da Mahmud pilot kiran da dady keyi masa, jikinsa ba k'wari yarik'asa suka nufi part d'in Ummi, suna shiga dady zai fitowa Ummi ta rakosa rik'e da jakarsa da yadawo office don dama yau ita keda girki, gaishesu sukayi cikin girmamawa bayan sun amsa Ummi ta mik'awa yaya Mahmud jakar tana kallon dady daya zuba mata idanuwa ganin abunda take shirinyi tana dariya tace

"To abu Bilal ga 'ya'yanan sun hutar dani da wannan rakiyar, bari nakoma wajen k'anwata" murmushi sukayi had'e da karb'ar jakar suka bar wajen. Speechless dady yazama yana kallon yanda take dariya, ya nunata da makullin motar dake hannunsa shima yana dariyar yace

"Ke koh!" "Afuwan dadyn yara Allah kad'aici ba dad'i shikenan ni dad'i miji saina barta itakad'ai azaune"

"Shine kuma ni za'a sakani zaman kad'aici bacin ansan bayada dad'i, shikenan kije amma ina tabbatar maki da duk bayan sakon d'aya sai nazo acikin tunaninki tayanda firar ma bazata yimaki dad'i ba sai kinzo inda nake"

"Hmmm to shikenan, ai natabbata nikuma 'ya'yana bazasu bari hakan tafaruba tunda suna tare dakai bazasu bari kad'aici ya ziyarto kaba"

"Haka kike tunani oum Bilqees amma ko mutanen duniya zasu zo suzauna atare dani matuk'ar bakya kusa dani to bazasuyi tasirin da zaisa kad'aici ya kasa ziyar toniba, kije abunki amma wannan qanwar taki ta matuk'ar takurani da yawa"

"Nagode abu Mahmud, shiyasa nake sonka da yawa" tafad'a tare da juyawa tabar wajen sannan shima yawuce abunsa zuciyarsa nak'ara jin soyayyar matarsa kuma uwar gidansa.

Zaunawa dady yayi akan kujera, sukuma suka zauna k'asa suka k'ara gaishesa, yaya Mahmud yabashi hak'uri akan rashin zuwansu da wuri, "bakomai" dady ya amsa masu dashi atak'aice tare da sanya masu albarka sannan ya kalli Mahmud pilot yace

"Kaine babba kuma akanka zanfara, yakamata ace izuwa yanzu ka fiddo da matar da zaka aura don iya rufin asiri Allah yayi maka shi, ka kammala karatu kanada gidansa nakanka gashi kuma kanada aikinyi shin to mekake jira da bazakayi aure ba? Ko so kakeyi sai kagama tsofewa sannan zakayi auren? don haka ina shawartarka daka taimakawa kanka kazamo cikakken namiji bawai tazuru ba kaji ko?" Eh Mahmud ya amsa masa dashi yayinda zuciyarsa ke ingizasa daya fad'awa dady cewa Billy yake so wata kuma zuciyar na hanasa akan yabari har sai yasamu soyayyarta sannan yafad'a masa. Juyowa dady yayi ga yaya Mahmud yace

"Kai kuma magana biyu nakeda ita dakai tafarko shawarace kaima tabiyu kuma umurnine!" Gaban yaya Mahmud ne yayi wani irin fad'uwa na rashin sanin wane umurnine dady keshirin bashi, muryar dady ce yaji yaci gaba da cewa "a matsayina na mahaifinka ina baka shawara daka ajiye kula da shagona na furniture's da kakeyi ka koma makaranta ka had'o master's d'inka ta fannin business in yaso kana dawowa saika fara neman aiki daga nan sai batun aure sannan kuma sai inbud'a maka naka shagon da zaka dinga kula dashi ranakun dabaka aiki, sauran ranaku kuma sai azuba maka yaran da zasu kula maka dashi, sai abu nabiyu ina so kaje gidan aminina alhaji Usman akwai yarinyarsa da mukayi maganar had'aku aure Fareeda idan tayi maka shikenan sai asa rana inka gamo karatu sai ayi auren, don yanzu SS1 take a makarantar secondary, ga d'an uwanka nan anjima sai yaraka ka" Wani irin zufane ya ketowa Mahmud ya k'walalo idanuwa awaje yana kallon dady yace

"Dady wa kace? faraaha ko Fareeda?"...














*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____46💎


Yaushe nafara wasa dakai my son Fareeda nacema ko har yanzu bakaji bane, durk'usawa yaya Mahmud yayi agabansa yana fad'in,

"Tuba nake dadynah amma inaso kabani dama inyi magana idan ka amince" "go ahead" dady yafad'a yana mai gyara zamansa akan kujera.

"Dady kai mahaifinane kuma nasan bazaka tab'a zab'amun abunda zai cutar dani ba kaine ka tarbiyantar dani yanda zanyi kyakkyawar mu'amala acikin mutane kuma nake koyi da kai wajen d'abi'u masu kyau tare da cika alk'awari, dady akwai yarinyar da nakeso kuma mukayi alk'awarin aure da ita, idan kace inbarta inbi zanb'inka to zan barta koda hakan nanufin zansaukane bisa tarbiyar daka bani da koyin da nakeyi dakai wajen cika alkawari don tabbatar dana farantamaka" shiru dady yayi yana kallonsa da nazarin kalamansa daki daki kafin yace

"Shikenan my son nafahimceka, kuma na amince kaci gaba da neman yarinyar amma inaso kasani kai mijin mace hud'u ne zan samu alhaji Usman nafad'a masa abunda kafad'amun idan har jin hakan baisa ya jaye muradinsa akankaba to ina tabbatar maka da cewa nima bazan watsa masa k'asa a idanuwa ba saidai kahad'asu su biyun ka aura ka fahimta." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke dake nuna kalaman sunyi masa nauyi azuciya ya koma zaune daga duk'en da yake had'e da cewa

"Amma dady ni bana sha'awar ajiye mata biyu, bazan iya zama da suba ko kad'an!"

"Haka zakayi hak'uri sai dai kayi addu'ar Allah yasa alhaji Usman yajaye qudurinsa wannan kad'ai zai hanaka auren mata biyu but idan ba haka ba dole ka hak'ura kahad'a da ita Fareedar!"

Mahmud pilot da kansa ke duk'e k'asa yana tunanin ta hanyar da zai soma maganin tasa matsalar kafin dady yace shi mata hud'u zai aura ya d'ago kansa yana kallon fuskar yaya Mahmud data koma kalar tausayi baisan lokacin da dariya ta kucce masa ba, kallonsa dady yayi yace "zanzo takan kane!, idan har baka fitar da matar da zaka auraba kaima zannemo maka auren yayar Fareeda yama sunan da suke kiranta dashi? yawwa Meamah! Itace daidai kai saboda this year zatayi graduating SSCE d'inta" Dariyar da yaya Mahmud baisan da zuwan taba shima ta kuccemasa yana nuna Mahmud pilot daya kumbure fuska da hannu, dariya shima dady yayi yana kallonsa, murya can k'asa k'asa yake fad'in "ni Bawata meamah wlh sai Billy" ko kad'an dady baiji abunda ya fad'aba saboda bakin sane kad'ai yaga yana motsi, shikuwa yaya Mahmud da har yau baidena dariyar ba kallonsa yayi yace

"Ah abu yayi d'an uwa Allah yasanya alkhairi" had'e da mik'amasa hannu, buge hannun yayi ya mik'ewarsa zai fita dady dake dariyarsu yace "koma kazauna ai ban sallameku ba ko?" makullan mota guda biyu ya mik'amasa, "Gashi kazab'i d'aya kaba d'an uwanka d'aya, yau aka kawomun tallarsu guda biyu iri d'aya k'irar BMW amma different colours ne, golden da kuma ash sai kuje kamfanin al-ikhlas kuce agwada maku manager wurin zai nuna maku motocin saiku d'auka" tunda dady yafara magana suka saki baki suna jujjuya makullan motar cike da mamakin irin wannan kyauta daya yimasu tabazata, godiya suka yimasa sosai suna zuba masa addu'o'in neman tsarin Allah daga abun k'i tare da fatar samun tsawon rayuwarsa cikin amincin Allah, murmushi dady yayi sannan yace

"Karku damu ubangiji Allah yayi maku albarka kuma kukula sosai kutsare mutuncinku da namu aduk inda kuke"

"In sha Allah dady" da haka yasallamesu fuskokinsu d'auke da tsantsar farinciki shi kuma ya haura sama domin ya huta.

Suna fitowa yaya Mahmud ya kalli Mahmud pilot cike da tsokana yace

"Ahh lallai angon meamah tazo a Sa'a, sabuwar amarya sabuwar mota, daga yin zancenta saimu samu kyautar dank'areriyar mota haka, gaskiya inatayaka murna d'an uwa to inata daka aureta, ahhhh..mukam wlh mun amince dady yaje yayi magana da gani zata shigo da farar k'afa, kai masha Allah congrat" tsabar takaici baisan lokacin daya ja wani dogon naushi zai kai masaba da sauri ya kauce tare da barin wajen yana yimasa dariya.

"Au! ashe kai k'aramin shak'iyine ai da katsaya na zubar dakai k'asa can ka k'arasa wajen wannan nurse d'in taka da kuke damun mutum da d'an banzan surutu"

Dr Ahmad dai yau kam jiyake yafi kowa farinciki saboda yasamu jin muryar masoyiyarsa, tun kafin ya isa gida yakira mamy yasanar da ita yanda sukayi da fatimar sa kuma tayi farinciki sosai tare da fatan Allah yasa ta amince da soyayyarsa, koda yatashi office seda ya tsaya kan hanya ya siyo kaji d'anyu guda biyar tare da kayan miya sannan ya sayi katam d'in lemun roba na coca-cola sanan ya isa gida, cike da fara'a mamy ta tarbesa ana fad'in

"A'ahh d'an gidan mamy yau me ka kawowa mamyn taka ne?" tak'arasa karb'ar kayan dake hannunsa, bud'ewa tayi taga naman kaji aciki ta d'ago kai tana kallonsa bayan fuskarta ta sauya zuwa kalar tausayi tace"haba Ahmad har yaushe zaka dena wahalda kanka haka, kace kai kullum sai ka takura kanka don ka faranta mani, nafad'a maka banida damuwa ga duk abunda zaka kawo mani komai rashin dad'insa, babban burina shine naga ka sauke nauyin hak'k'in mahaifinka dake kanka"

"Mamy ki kwantar da hankalinki, duk abunda nakeyi inayinsa ne bisa tsari, zancika maki burinki nan bada dad'ewa ba, ruhin Abbanah yana gab da samun salama fiye da wacce yake ciki, kiyi hak'uri kuma kici gaba dayimun addu'a domin itace makamin da nake yak'ar duk abunda zai tari gabana, kuma akoda yaushe farincikin ki shinake son gani shiyasa nakeyi maki duk abunda nasan kinaso, ko kinmanta da amanarki da Abbana yabani" goge 'yan hawayen da suka zubo mata agefen idanuwa tayi sannan tace

"To madallah nagode, yaron Abba, ubangiji Allah yayi maka albarka kuma yajik'an mahaifinka"

"Amin mamynah haka nakeso inji kin fad'a" d'aki ya wuce yarage kayan dake jikinsa sannan yadawo tsakar gidan yayi zaune yana kallon yanda take k'ok'arin gyara kayan daya shigo dasu, "mamynah kawo narik'a maki wani aikin"

"A'a kabarshi nagode Allah yayi albarka, ga abincin ka can akan fridge kaje ka d'auka kaci inka gama saika d'an samu waje ka kwanta kahuta, wannan aikin ai namatane" murmushi yayi yana tuni rayuwarsu tabaya.

_WAYE DR. AHMAD BASHAR_

'Dane tilo awurin mahaifinsa Alh bashar mai fulawa, mahaifinsa cikakken d'ankasuwane dake da k'aramin jarin saida fulawa, wanda ananne yasamo lak'anin da ake yimasa, yanada matarsa k'waya d'aya da ake kira mamy amma asalin sunanta Hauwa'u, macece mai tsananin kawaici da hak'uri kuma shima haka halinsa yake, wannan dalilinne yasa zaman nasu yayi dad'i fiye da tunani, tunda suke ba'a tab'ajin muryar d'ayansu da sunan fad'aba, suna matuk'ar son juna da kuma mutunta juna, aurensu da shekara uku Allah yabasu k'aruwar haihuwar d'ah namiji wanda yaci sunan Ahmad kuma ta dalilin haihuwar sane mamy tahad'u da lalura ga mahaifarta da bazata sake iya haihuwa ba, sosai mamy tayi kuka wanda saida ya tashi zamemata damuwa, Abba yadinga bata hak'uri data barwa Allah komai kuma surok'i wannan yaro daya basu yaraya masu shi kuma ya sanya masa albarka, dole mamy tahak'ura tafawwalawa Allah alamarinta sukaci gaba da renon yaronsu cikin kulawa, akoda yaushe ciwon dake damun mamy ga mahaifa yakan tashi akai akai amma bata bari Abba yasan da haka don sai yanuna yafita shiga damuwa, haka mamy tayita fama da ciwon har Ahmad ya girma, abunda mamy bata saniba shine barazana da k'alubalen da Abba ke

Please Login or Register in order to submit comment