Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha Allah" sanan ya bar d'akin yana yimasa godiya. Kallon yanda suke soyayarsu Mahmud keyi cike da burgewa yanaji inama ace shima Billynsa zata bashi had'in kai haka da soyayyarsu tazama abun kwatance aduniya.

Dady kuwa yana komawa part d'in mom yanufa da yake ita keda girki, yana shiga yasameta zaune afalo tana kallon maimaicin wata drama da akeyi SAPNE SUHANE, kallo d'aya tayi masa takauda kai batare da tace masa komai ba, kusa da ita yasamu ya zauna agajiye yana fad'in

"Am sorry kinjini shiru, Mahmud ne ba lafiya, yanzu haka yana asibiti"

"Eh naji ga 'yarka tund'azu, tunda ni banida daraja da kima awurin ka zaka kirani kafad'amun" dafa goshi yayi kafin yace

"Ayya sorry ba haka bane, hankalina ne atashe shiyasa, ummansa kad'ai nakira wayarta"

"Oh ka kirasu kafad'a masu amma ni tunda ka maisheni daniyar ware shine ka kasa kira kafad'amun, Allah dai nasane da duk namijin dake banbanci tsakanin matansa" baki tabud'e dady ke kallon mom, meyayi anan na rashin adalci? Shifa 'yar uwarsa yakira sai akayi sa'ar wayar na a hannun ummi ta d'aga, shikenan sai yafasa yin maganar da zaiyi da ita don ba girkin tabane, saboda bayaso maganar tayi tsauri yasa yace da ita

"Kiyi hak'uri nayi kuskure, in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba, shikenan ko" yak'are maganar yana kallon fuskarta, da yake Allah yayiwa mom son girma nan take tasaki, breakfast tashiga kitchen tahad'o masa, bayan yaci yace tagyara zaije ya watso ruwa sai suje asibitin shima yaya Mahmud yadawo gida yayi breakfast. Basmah dake kwance zazzab'i ya rufeta ya k'walawa kira, jin muryar mahaifinta yasa ta tattaro sauran d'an k'arfin da take dashi tamik'e taje inda yake kiranta, batare da yakula da yanayin da take cikiba yace

"Kije kifad'awa 'yan uwanki kushirya Nazir driver ya ajiyeku asibiti kugano yayanku kafin muzo" ta amsa masa da "to dady" jikinta na rawar sanyi, Batool ta tura tafad'owa Billy sak'on dady sannan ta dawo ta taimaka mata itama ta shirya sannan suka nufi wajen Nazir driver ya ajiyesu asibitin, ita kuwa ummi koda yaya Mahmud yakirata yafad'a mata dady yace suyi zamansu kitchen tashiga ta had'a abincin daza suje dashi asibiti bayan ta sanar da Umma zancen rashin lafiyar Mahmud cikin hikima tayanda hankalinta bazai tashi ba, kuma Alhmdllh tafahimta cikin sauk'i tare da fatar Allah yabashi lafiya, suna zaune saiga dady yashigo da sauri suka taso suna tambayar yajikin Mahmud ya tabbatar masu daya samu sauk'i sosai don har ya farka kuma yana magana,

"Alhmdllh" suka fad'a atare had'e da fatar Allah yak'ara masa lafiya, cemasu yayi su zama cikin shiri inya fito zasuje asibiti sai sudubosa.

Tun acikin mota Billy kefaman jerowa Nazir driver tambayoyi wai ya jikin yaya mahmud? Yaji sauk'i?, ya farka, yana magana? Ko k'ak'a, murmushi yayi had'e da kallonta yace

"Kai 'yar gidan Ummi, wud'annan tambayoyin anya basuyimun yawa ba, to wace zanfara amsawa aciki?"

"Duka" tafad'a atak'aice cikin d'auki da zak'uwar ganinsa,

"To 'yar gidan dady alhamdulillah yaji sauk'i sosai" Basmah kuwa tunda tashiga motar ta jingina ajikin kujerar baya ta rufe idanuwanta batace uffan ba har suka iso asibitin, duk da Billy na d'okin ganin masoyinta hakan bai hana tajira fitowa 'yan uwanta daga cikin motar ba jiri ke d'ibar Basmah Batool na k'ok'arin rik'eta amma don kar a fahimci tana cikin wani yanayi ta dinga tureta tana k'wace jikinta, dole tak'yaleta takoma gefenta tana kallon yanda take takawa cikin k'arfin hali itama Billy ta tsaya ad'ayan gefennata suka san yata tsakiya har suka iso d'akin da aka kwantar dashi da taimakon Nazir driver shida yasan wajen.

Suna shiga suka nufi wajen gadon duk su uku suna yimasa sannu ba tare da sun lura da faraaha dake can gefe tare da yaya Mahmud suna soyewa.

Tunda suka shigo idanuwansa na akan masoyiyarsa abur k'aunarsa wato Billy, ganin haka yasa Basmah tamatse hannun Batool dake rik'e da ita sosai alamun sud'an basu wuri, suna juyawa itama Billy tabiyosu, muryarsa suka jiyo yana fad'in

"Kin.ji.." Cikin i'ina kamar an matso maganar dole, gaba d'ayansu suka tsaya cak had'e da juyowa suna kallonsa in banda Basmah data runtse idanuwanta taci gaba da tafiya.

"Sorry Batool da Bilkisu nake" yafad'a idanuwansa na akanta..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Some are celebrating, dancing, singing, happy, drunk, their head is almost vibrate on their birthday date with out knowing dt they are just close to their graves, hope u will not be among them, u will be among those one's who said "ALHAMDULILLAH ya rabh, forgive my sin's and make ur holy home jannatul Firdausi be my final abode๐Ÿ‘๐Ÿป" *Happy birthday to you MRS. QUDIEDIE* may Allah forgive ur fast years and bless ur up coming years, wish u more qudie qudie in ur bank accaunt๐Ÿฅฐ๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜_

๐Ÿ’ŽPage_____54๐Ÿ’Ž


Wucewa Batool tayi ita kuma Billy tadawo inda yake kanta ak'asa zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, "Bilkisu!"

"Na'am" ta amsa kanta na daga k'asa,

"'Dago kanki ki kalleni" yafad'a, d'agowa tayi cike da jin kunyarsa amma takasa kallon k'wayar idanuwansa, "kinga yanda nakoma, meyasa zakiyi wasa da rayuwata, kina tsammanin kalaman duk dana yimaki bana gaskiya bane don in yaudare kine?, meye ribar Mahmud idan ya yaudari 'yar uwarsa kuma jininsa da yake matuk'ar k'auna, shin ko da gaske kikeyi bakya sona har cikin zuciyarki?" Kallon gefen dasu yaya Mahmud zuke zaune tayi ashe su har sun dad'e da ficewa daga d'akin don dama kunyarsuce tasa takasa tanka masa.

Girgiza kanta tayi sannan tace "Ko kad'an yaya niban furta bana sonka ba, amma tabbas zuciyata akwai wanda takeso kuma take k'auna tun ina 'yar k'ank'anuwata kuma bakowa bane wannan face kai," tak'are maganar had'e da d'agowa tana kallon cikin idanuwansa, lumshe idanun yayi had'e da cewa "Dagaske kikeyi Billynah kina sona?" Jinjina masa kai tayi itama had'e da lumshe idanuwanta,

"Why? Meyasa kika bani wahala baccin kinsan da kema kina k'aunata, ko bakya tsoron zaki iya rasani" dariya tayi sannan tace "saboda ingano daraja da girman son da kake yimun ne yasa nayi haka kuma nasan bazani tab'a rasa kaba insha Allah"

"Tabbas hakane! Domin indai ina raye ke mallakina ce kuma nima mallakinkine har abada"

"Amma shine kayi k'ok'arin jefani cikin halin ni 'yaso wajen illata kanka"

"Soyayyarki tajawo hakan, amma tunda naci gari hakan bazai sake faruwa ba"

Turo gambun k'ofar da akayi yasa gaba d'aya suka d'ago kanso don ganin ko waye, dadyne ya shigo mom nabiye dashi abaya dasu Ummi, Billy na ganin haka tabar wajen cike dajin kunyar Allah yasa basuji abunda tafad'a ba, kallo dady yabita dashi kafin ya maido kallonsa ga Mahmud cike da alamar tambaya. Sosa kansa yayi sannan ya gaishesu yana kallon ummansa dake fad'in.

"My soldier yajikin naka?" Dayake da haka take kiransa wasu lokutan "Alhamdulillah Umma naji sauk'i sosai hop dai baki tashi hankalinki ba ko?"

"Ko d'aya, ai nasan shi ciwo ba mutuwa neba, amma kuma nashiga damuwa akan abunda likita yafad'a" d'an zaro idanuwa yayi "Umma me likita yace akaina?" Sai alokacin hawayen da takasayi tun lokacin da dady keyi masu bayani cikin mota akan abunda likita yace suka samu damar zubo mata cikin kuka tace "yanzu kai yaron nan meka rasa arayuwarka da zaka zauna kayita tunanetunane har ciwon zuciya na neman kamaka, kuma kasan bazan juri rashinkaba amma kake nema ka hallaka kanka" jawota ummi tayi ajiki tana rarrashi tare da yiwa Mahmud d'in fad'a akan yadena yin hakan idan wani abun yakeso k'ara yafad'a daya zauna da damuwa cikin ransa, "ya isa haka koma meye abari yasamu lpy in munje gida naji komeye kedamunsa, son koma ka kwanta, Allah yak'ara sauk'i" dady yafad'a tare da mik'ewa, murmushi mom tayi azuciyarta tana watsawa Ummi wani kallo "kyasan abunda yake so lokacin da yafurta yana son 'yarki tilo da kike tunk'aho da ita aka aura masa yabar garin da ita" azahiri kuma cewa tayi

"Sannu Mahmud Allah yak'ara sauk'i amma ka bayyana kome kake buk'ata gidan kune kuma za'a baka kaji ko" d'aga mata kai yayi tare da kallon ummansa "kiyi hak'uri ummanah kiyafemun, in sha Allah bazan sake ba" d'an bubbuga kafad'arsa dady yai had'e da cewa "Good dt's my son, ni zanwuce office sai nadawo, ku kuma inkun gama sai Mahmud ya ajiyeku gida tunda ga k'annensa nan" yana gama fad'ar haka yanufi k'ofar fita, Bayansa mom tabi ba kunya ba tsoron Allah tana fad'in "ni yanzu zankoma muje ka sai ka ajiyeni kawuce ko?, tsayawa yayi had'e da juyowa yana kallonta "Banida wannan lokaci saboda nariga da nayi latti" yafad'a tare da ficewarsa, nan take taji duk ta muzanta da abunda yayi mata, juyowa tayi tana kallon gefensu amma sai taga gaba d'aya hankalinsu baya kanta ta Mahmud sukai, duk da ko suna jin abunda yafaru amma sai basu kula kantaba, hakan yasa takasa komawa wajen adole tafice tabar d'akin tana fita tahango su Basmah zaune ita da Batool da kuma Billy, wajen tanufa tana tambayarsu ina Nazir driver yayi ya maidata gida suka fad'a mata cewa tare suka fita da dady shi kuma yaya Mahmud baya wajen yana can yana soyewarsa da faraaharsa don ko isowarsu bai gani ba, a dole yasa takoma cikin d'akin taja kujera can gefe dasu ta zauna tana lallatsar wayarta saboda tacire mata kewa, kallonta Umma tayi ta mere baki cike da jin haushinta yayinda Ummi ko gefen da take bata kula dashi ba balle ita,

Mom na barin wajen sai gasu yaya Mahmud sun dawo saboda faraaha nason tawuce geda, murmushi tayi masu tare da cewa

"Sister's am going" Batool tayi saurin cewa

"Laa aunty faraaha gasu mom can sunzo fa, bazakije ku gaisaba"

"Kai wlh kunya nakeji Batool, amma zanzo har gida in gaishesu"

"Ai kuwa baki isaba, dole kije ku gaisa" Mahmud yafad'a lokacin da yake k'ok'arin shafa kansa yana kallonta,

"Pls All I have wlh kunya nakeji, don Allah kabari zanzo har gida ingaishesu kaji my luv?" Tafad'a had'e da marairaice masa fuska, wayar tace tashiga ruru ta d'auko had'e da duba mai kiran taga ashe dr.Ahmad ne, har zata mayar da wayar aljihu saboda a 'yan kwanakkin nan ya matsamata da kira waishi gaskiya yagaji da zaman jiran amsar fatima yanaso tabashi address d'in gidansu yaje suyita ido da ido don ba k'aramar wahala yake shaba sai taga yaya mahmud ya k'ureta da idanuwa, saboda ta fidda kanta daga tuhumar da yake k'ok'arin yimata yasa tayi saurin maido wayar had'e da d'agawa, "Hello dr. Good morning" jin muryarta yasa dr. Ahmad ya mik'awa mamy wayar yana fad'in "mamynah amsa kirok'amun ita ta had'ani da fatima tunda ni nayi k'ank'anta da tayimun wannan alfarmar" zaro idanuwa waje faraaha tayi don tanajin duk abunda yake fad'a cike da mamakin yanda taji ya shagwab'ewa mamyn tasa murya yana magana, muryar mamynce ta katse mata tunani lokacin data daki dodon kunnenta "Assalamu alaikum 'yatah" mamy tafad'a cikin dariyar wannan rigima da Ahmad ya azamata yau akan fatimarsa.

"Wa'alaikissalam mamy ina kwana" tafad'a kamar yanda taji yakira mahaifiya tasa, "Lafiya klw 'yata ya aiki?"

"Alhmdllh mamy ya gida kowa lafiya?" Kallonsa mamy tayi yanda ya k'ura mata idanuwa yana son jin mezata fad'a tayi dariya sannan tace

"Alhamdulillah duk lafiya klw muke, yaron Abba daine yatashi da rigimar son ganin fatimarsa, nace 'yatah koda akwai wata matsalane da tasa kika hanasa addreahin gidansu yarinya" babu wata matsala mamy tunda yayan yarinyar ke sonta itama" suka jiyo muryar dr.Ahmad yana fad'a, sosai faraaha tayi dariya kafin tace

"Mamy sannu da k'ok'ari, dama haka dr. Yake?"

"Hmmm ai yafi haka 'yatah, kad'an ma kikaji, don Allah indai babu damuwa kitaimaka masa da address d'innan ko ma huta dani har ke"

"Shikenan mamy dama don kada nayi katsalandan ga alamarin yasa nabari har saina nema masa izinin yin haka awajen yayanta amma tunda yamatsa mamy bashi wayar muyi magana ko kyahuta da rigimarsa"

"To nagode 'yatah Allah yayi maki albarka kuma yajik'an mahaifa kinji"

"To mamynmu ngd ssai" wayar mamy tamik'a masa had'e da mik'ewa tanaci gaba da gyaran d'akin da takeyi, yana karb'a yace

"Hmm ai kinga yanzu kodon albarkacin mamy kyafad'amun, wato da'in bakisan zafin so ba shiyasa kike jamun rai haka amma bakomai nagd"

"Tuba nakeyi dr ayimun afuwa, tunda dai azarb'ab'inka na nema yayi yawa to kamaza ka hanzarta kazo inanan cikin asibiti tare da fatimarka ankawo wani yayanta ba lafiya" tafad'a tana kallon Batool, gaban batool ne yafad'i don ko shakka babu tasan dr Ahmad ne d'an muskutawa tayi daga zaunen da take tana kyakkyafta idanuwa kamar marar gaskiya, shikuwa yana jin haka yayi wani irin dirowa daga kan gadon cike da farinciki yana fad'in.

"Are you serious sister faraaha?"

Dariya tayi masa had'e da cewa ofcourse, kayi sauri don wucewa zanyi yanzu "nooo..pls bani minti goma ganinan isowa" bai jira me zataceba ya kashe wayar had'e da rungume mamy yana dariya sannan ya saketa yanufi wajen kayansa dake tsare cikin 'yar k'aramar wardrobe d'in da mamy tagama gyarawa yanzu yana fad'in mamy zo kizab'amun kayan da zansa inje in had'u da fatimatah,

"A'a da wuri haka? Ahmadidinah"

"Eh mamy tana asibiti yanzu haka yayantane ba lafiya"

"Ashsha Allah yabashi lafiya" mamy tafad'a had'e da matsowa inda yake tsaye duk ya rud'e yarasa kayan da zai zab'a yasa, d'ai d'ai yadinga ciro kayan yana watsowa kan gado mamy na tsaye tana kallonsa har saida ya kwashe kayan gaba d'aya. Dariya mamy tayi sannan tazo ta d'ago wata sky blue d'in shadda data sha aikin blue d'in zare amma mai light tayi kyau sosai tamik'a masa had'e da cewa

"Karb'i wannan kaje kasa" karb'a yayi don dama bai dad'e da fitowa wankaba ya shiga toilet ya sanyo, yana fitowa mamy tamik'a masa wata hula mai k'ube kalar blue gaba d'aya sai d'an touch na sky blue aciki kad'an, karb'a yayi ya daidaita zamanta akansa yana kallon madubi "eyyeee ashe dai mamynah nason 'yar nan tata tak'yasa idan taga yaronta" turare mai k'amshin gaske na kamfanin oud ya d'auka ya feshe jikinsa, sannan ya sagala agogon hannunsa, d'an k'aramin glass d'insa da yake amfani dashi ya d'auko zai sawa mamy ta karb'a "kaje mata amatsayin ka na Ahmad batare da wani k'yale k'yaleba da zai d'aukar mata hankali sai yafi" black cover shoe's d'insa ya jawo tare da kakkab'esu duk da basa da wata datti yana sake gogewa da wani d'an k'aramin towel dake ajiye akan madubin sannan yasaka, kiran faraahane ya sake shigowa a wayarsa daidai lokacin daya d'ago daga sa takalumman nasa, d'auka yayi da sauri had'e da rungume mamy yana fad'in "mamynah natafi" sannan yace da faraaha "am sorry sister on my way" yafice mamy nasaka masa albarka had'e da fatar nasarar samo zuciyar fatimarsa...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____55๐Ÿ’Ž


Tsaye yake abakin titi yana jiran abun hawa saiga wani abokinsa khalid yana k'ok'arin karyo kan motarsa zuwa gidansu, yana hangosa tsaye ya juyar da kan motar kamar zai bugesa, da sauri yad'an ja baya had'e da d'ago hannu cikin b'acin rai, ganin motar Khalid abokinsa yasashi ajiye hannun tare da nufar wajensa, dariyar shak'iyanci Khalid yashiga yimasa had'e da yin parking gefe yafito cikin motar yana mik'a masa hannu suka tafe "dr.dr wannan irin kwalliya haka kamar wani sabon ango, sai ina" uffan dr. Ahmad baice masa ba baya ga gaisawar da sukayi, motar yanufa kawai yabud'e gidan gaba yazauna yana duba agogon hannunsa, ganin haka yasa Khalid shima ya koma ciki ya tayar da motar, sai da suka hau ka titi ya kallesa.

"Dr wai ina zuwane inata magana ka k'yaleni?" Saida ya sake duba agogon hannunsa kafin yace

"Pls kataka motarnan don Allah"

"Intaka mota zuwa ina? Kaifa wani lokacin d'an walak'ancine!"

"Naji dai komai zakace nayarda, asibiti zaka ajiyeni emergency ake jirana!"

"Mtssss.." Khalid yayi tsaki had'e da k'ara speed d'in motar, cikin minti biyar sai gashi sun iso asibitin, kallonsa dr Ahmad yayi had'e da cewa.

"Thank you Khalid, zaka jiranine don naga alamar da akwai magana a bakinka?" harararsa yai tare da tada motar yana fad'in "Ai kuma baka isaba tunda ba drivern ka nakeba" dariya ya sakar masa har kyawawan hak'oransa na bayyana sannan yace

"Ok, muyi waya anjima" baice masa komai ba yajuyar dakan motar yabar asibitin cike da mamakin halin abokin nasa, duk dako tun suna yara suke tare ba sabon bane a wajensa.


Wayarsa yaciro yakira sister faraaha, bugun d'aya ta d'auka tana fad'in "Allah ka kuru, yanzun nake cewa bari natafi abuna sai nabaka lambar all I hv idan kashigo sai kuyi waya"

"To tunda gani nashigo yanzu ina zannufa don ganinki"

"Ina kallonka tun lokacin da kuka shigo, gamunan emergency" d'aga kansa yayi ya hangota tsaye ita da Mahmud. Sai wasu 'yan mata su uku agefe wanda yake kyautata zaton fatimarsa nacikinsu, tsinke wayar yayi sannan ya nufi inda suke fuskarsa cike da annuri, gabansa ne yafad'i lokacin daya kusa k'arasowa wajen ganin 'yan matan su biyu kamar su d'aya hasken fata kawai ya d'an banban tasu, kasa gano wacece fatimarsa daga ciki yayi kasancewar gani d'aya yayi mata, kuma bai wani tantanceta sosai ba, ita kanta Batool tana ganinsa taji gabanta yafad'i don tabbas ta gane dr. Ahmad d'in,

Ganin d'ayar zaune agefe kamar bata motsi da yai ita kuma sai faman nonnoce kai da mutsumutsu takeyi tana neman yanda za'ayi tasamu tabar wajen yasa zuciyarsa cinko masa ita amatsayin fatimarsa saboda yanda kunya da tsoron abunda ya had'ata dashi ranar suka hanata natsuwa, murmushi yayi lokacin daya iso idanuwansa na akanta sannan ya mik'awa yaya Mahmud hannu suka gaisa cikin girmamawa, kallon Mahmud faraaha tayi bayan sun sake gaisawa da dr. Ahmad had'e da cewa,

"All I have wannan shine dr Ahmad d'in da kaji muna waya dashi, anan asibitin yake aiki ab'an garen k'ashi, sunansa dr. Ahmad Bashar, k'wararren likitane da yasan aikinsa sosai kuma shine nayi maka bayani akan yaga sister Batool ranar da kuka kawota batada lafiya yace yana sonta" juyowa tayi ga dr. Ahmad shima tace

"Dr. Here is my luv, husband to be in sha Allah, sunansa Mahmud kuma yayan fatimar da kake so" hannu ya mik'a masa fuskarsa d'auke da farinciki yace "Nice to meet you yaya Mahmud, ya mai jiki?"

"Me too dr. Ahmad" shima yafad'a fuskarsa d'auke da murmushi "mai jiki Alhmdllh yaji sauk'i, ya aiki?"

"Alhamdulillah, ko zan iya ganinsa?"

"Sosai kuwa muje mana, my golden hope kin bani permission?" Yafad'a yana kallon cikin idanuwanta, dole kunya tasa faraaha bin bayansu itama saboda tagaida su ummi da akace sunzo duk da bata so hakan ba, tambayarta da yayi ne yasa tafahimci hakan, suna wucewa Billy ta k'yafaci Batool tana nuna su da idanuwa "ke twiny wancan shine dr Ahmad d'inki ko?" Murmushi tayi mata had'e da kad'a mata kai cikin jin kunya, rungume Basmah Billy tayi wacce tuni ta lula duniyar tunani har saida ta d'an tsorata tana fad'in "Yayya kinga dr. twiny d'ina gaskiya he's so cute" tana dariya, murmushi Basmah tayi had'e da cewa "is he cute more than yaya Mahmud d'inki?"

"Inaa yayya! Akwai banbanci sosai don yayan mu is damn cute fiye dashi ko?" Dariya tayi mata batare da tace komai ba sannan ta maida kanta ga jikin k'arfen rumfar da suke ciki zaune, ita kuma Batool cewa tayi "tab da baki fad'a don za'a rubuta maki zunubin wannan sab'on, da wud'annan k'ananan idanuwa irin na Japanese zaifi dr kyau?" Turo baki tayi had'e da b'ata fuska "Yayya kinji twiny ko?"

"Manta da ita my sister fad'a kawai takeyi, amma tasan shid'in na daban ne" dad'i Billy taji harda yiwa Batool gwalo ita kuma takafeta da idanuwa tanajin tausayinta sosai aranta, tasani duk abunda takeyi k'arfin haline kawai take don farincikin 'yar uwarta.

Cike da kunya Ahmad yashiga d'akin saboda ganin su Ummi aciki wanda ko ba'a fad'a ba yasan sune iyayensu, cikin girmamawa ya gaidasu shida faraaha sannan yadawo ga Mahmud pilot ya mik'a masa hannu suka gaisa yana yimasa ya jiki, kallonsa yaya Mahmud yayi cikin zolaya yace

"To idan angirma asan angirma don kada afara ciwo iri d'aya da 'yan k'anne, wannan sunansa dr Ahmad" kallonsu ummi yayi da hankalinsu kecen suna maganarsu sannan ya matsa ga kunnensa yace "d'an uwa wannan fa surukin kane, shine keson Batool kuma anan asibitin yake aiki" kallon gefen da mom take zaune tana dannar waya Mahmud pilot yayi shima ya rad'a masa akunne

"Kai bakaga mom zaune bane hakan, kaida ita idan tajika" juyowa yayi yana kallon mom d'in tasa don har ga Allah yazata tare da dady suka koma saboda yanda yasan halinta basa shan innuwa d'aya dasu ummi, wajenta yanufa tare da cewa mom, d'ago kai tayi tana fad'in "aw sai yanzu ka ganni" don dama tund'azu da suka shigo tacika tayi fam ganin ko kallon gefen da take dashi har bak'in daya shigo dasu basuyi ba sai faman dudduk'e kai sukeyi suna gaidasu Ummi, nan take taji duk haushinsu ya mamaye zuciyarta, bata jira mezai ceba tamik'e tana hurar hanta, "kazo ka sauke ni gida don zaman ya ishe ni haka" kallon Mahmud tayi tare da yimasa Allah yak'ara sauk'i tana juyowa idanuwanta sukaci karo da faraaha dake tsaye suna fira da Ummi da take tambaya inasu Bilal da Bassam sarakunan rigima tana fad'amata rigimar da sukayi mata kafin su fito tana dariya, saboda ta shak'u dasu sosai lokacin da Ummi tayi jinyar Bilkisu, nan take mom taji tsanarta ta dirar mata azuciya wani irin mugun kallo tabita dashi wanda saida cikin yaya Mahmud ya murd'a, sosai jikinsa yayi sanyi yadawo wajen dr Ahmad yace "dr here is our mom kaje kugaisa" yana nuna mom dake k'ok'arin ficewa cike da tsanar yarinyar da bata tab'a ganiba akan taso wacce tafi tsana acikin zuciyarta wato Ummi. Da sauri dr Ahmad ya matsa wajen mom yana fad'in.."sannu mom ina wuni ya maijiki?" Ko tsayawa kallonsa batayi ba balle ta amsa gaisuwarta taci gaba da tafiyarta.

Shiru yayi yana tunanin ita kuma wannan meye matsayinta a family d'in duk da yaji suna kiranta da mom, ga alama dai ga iyayensu Batool can wud'anda ya gaisa dasu daga farko, to ita wannan wacece?

Shikuwa yaya Mahmud bin bayanta yayi don bayada zab'in da yawuce yin hakan, kai tsaye bakin mota tawuce, tana isa shima ya iso wajen, hannu yasa a aljihu yaciro keys d'in motar yabud'e had'e da zagayawa ya bud'e mata gambun baya ta shiga batare da tace uffan ba sannan shima yabud'e gefen driver ya shiga had'e da tada motar yaja sukabar asibitin, tunda suka fara tafiya babu wanda yace k'anzil sai da suka hau titi daidai, gyaran murya yayi kafin yace

"Tuba nakeyi mamynah bisa b'ata ranki da nayi har ga Allah bansan da zuwanku ba, kuma lokacin da nagasu Ummi zaune nazata tare kuka wuce da dad ko kad'an ban lura dake awajen ba, natuba kiyafemun kinji momynah?"

"Shikenan, dama ni ba dakai nake wannan fushin ba, da waccan figaggiyar yarinya mara d'a'a nakeyi, kina 'ya mace kiyi tsaye gaban maza kina dariya kuma cikin tsofaffin mata don rashin tarbiya, mtssss gaskiya wanda zai aureta yana cikin takaici, gaba d'aya tsarinta keyimun ba ko kad'an" tsabar razanar da yaya Mahmud yayi da jin kalaman mom d'in tasa baisan lokacin daya taka burki ba, juyowa yayi yana kallon yanda mom ta b'ata rai sai fad'a takeyi wata irin ajiyar zuciya yayi had'e da cewa

"Mom ai yanayin aikintane haka, itama nurse ce a asibitin dole ta sakarwa marasa lafiya tare da 'yan uwansa fuska hakan shi zai taimaka mata tayi achieving acikin aikinta"

"Koma meye hakan baiyiba gaba d'aya ni haushinta nakeji." Juyawa yayi yaci gaba da driving yana tunanin ganin faraaha da mom tayi tare da Ummi shi yayi causing wannan matsalar, "ya ilahiee" yafad'a had'e da dukan starring motar batare da yasan yayi hakan ba, muryar mom yaji tana fad'in "wai meye haka son, tukunama meyasa d'azu ka tsayar da motar nan"

"Bkomai mom kawai nayi mamakin abunda kika fad'a ne?"

"Kadena mamaki don har azuciya nakejin haushin abunnan, nidai bazan tab'a yarda ace d'ana ya auro mun irin waccan yarinyar ba!" Daga haka baice komai ba har yakai mom gida ya juyo ba abunda

Please Login or Register in order to submit comment