Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwarsa na cikin wannan halin, amma yazaiyi da tsarin Allah yana fata akoda yaushe shima Allah ya gyara masu halayen mom d'insu, saida Ummi ta tabbatar ya k'oshi sannan tace yaje part d'insa yayi wanka sai ya d'an kwanta ya huta kafin akira sallar magrib duk da tasan kwancin beda fa'ida amma k'ara yasamu rest of mine ko kad'anne,

Har zaifita yadawo yana kallon Basmah cike da tausayinta aransa yanaji inama yanada ikon cirewa Basmah zuciyarta marar tunani ya sakamata wata wacce zata lurar da tunaninta akan dai dai,

Allah sarki wato shi d'an uwa daban yake komai lalacewarsa za'a so shi, juyowa yayi ya kalli su Billy yace

"Sis kada wanda yayi mata magana idan tafarko kuma kada kushiga sha'aninta kowa yasa mata ido kuyi har kar gabanku, hakan zaisa tafahimci kuskuren data aikata" suka amsa masa da to jikinsu duk a sanyaye,

"Ummi nagode" yafad'a lokacin da yake k'ok'arin barin falon, lumshe idanuwanta tayi alamar bakomai sannan ya wuce ita kuma tayi zaune tana tayiwa su Batool nasiha akan ko meye duniya da kuma rud'anin dake cikinta. Sallamar su papi ce ta maido da hankulansu abakin k'ofar, bayan gabaki d'ayansu sun amsa sallamar Batool ta tashi taje ta bud'e k'ofar don tabbatar da muryar wud'an da suka jiyo, tana bud'ewa taga hajia kaka da papi a tsaye cikin farinciki ta rungumeta tana fad'in

"Oyoyo babyn papi" tana dariya, gaba d'aya suma dariyar sukayi papi ya d'aga sandar,

"Cikata kada ki b'allata ja'irar yarinya" Batool na dariya tashigo dasu daga ciki tana fad'in

"Oh ni d'iyar Ummi wannan tsofon nagano bakada buri irin kaga kana dukana da wannan k'afar taka da ta uku, Billy zoki tayani mu karb'eta sai muga yanda zaiyi tafiya balle har ya iya dukan mutane da ita" murmushi Ummi data k'araso wajen da sauri tana yimasu sannu da zuwa tayi jin bakantar da take yimasu had'e da yimasu iso acan gefen wasu kujerun na musamman dake k'arshen falon, cikin girmamawa ta duk'a tana gaishesu

"Hajia ina wuni, sannunku da zuwa, ya hanya?"

"Lafiya lau Aishatu uwar muminai, ya gida duk lpy kuke?"

"Lafiya lau alhmdulillah" Ummi tafad'a tare da juyowa inda papi yake zaune ta russuna kai kad'an

"Sannu papi da k'ok'ari, ina wuni, anzo lafiya?"

Cikin sakin fuska da nuna tsantsar soyayyar da yakeji akanta yace

"Lafiya lau 'yatah, alhmdulillah, ya naki k'ok'arin?' Ubangiji Allah yayi maki albarka, ga yara nan duk sun canza masha Allah aci gaba da hak'uri dasu wata rana sai labari in sha Allah" ita dai Ummi batace komai ba sai murmushi da takeyi kanta nak'asa a sunkuye, Billy da Batool ne suka iso wajen hannuwansu d'auke da treys d'in abinci da abunsha, Billy tafara gaishesu sannan Batool itama suka k'ara gaisawa, ruwa suka tsiyayo masu a cup suka mik'a masu cikin ladabi da girmamawa, bayan sun karb'a sun sha, hajia kaka takalli Ummi

"Sannu da k'ok'ari Aisha, ashe abunda yafaru da Bilkisu kenan shine ba'a fad'a mana ba sai jiya dasu mommodu (Mahmoud) sukaje yake fad'a mana, ashe abun har saida aka kwantar da ita asibiti?, to don Allah kiyi hak'uri, d'ane inka haifesa baka haifi halin saba, inba don shashanci irin nataba banga dalilin shiga sha'anin yaraba wai har ace tajima d'aya ciwo, wlh ko kad'an bamuji dad'i ba kuma munyi mata fad'a sosai ai ba'a haka d'an uwa da d'an uwa sai Allah ba'a shiga tsakani, yanzu dubesu atare gwanin ban sha'awa har sun manta da abunda yafaru a tsakaninsu kai kace tagwayeni, shin idan da kunya intaga yanda suke yanzu ai tajita, to don Allah kiyi hak'uri, Allah kashiryeku baki d'aya kuma yayi maku albarka kuma Allah yaganar da ita damu baki d'ai" duk suka amsa da amin, shima dai papi haka yayita ba Ummi hak'uri ita har kunya tafara kamata,

"Don Allah papi kudena wlh babu komai ai 'yar tace itama, don haka tafaru bakomai dama Allah yatsaro haka zata faru gareta koda kuwa a hannuna ne"

Rungumo Billy papi yayi ajikinsa yana kallonta

"Amaryata sannu kinji? meyasa bakiyi mun wayaba nazo jinya?"

Kallon hajiya kaka dake murmushi tayi tace "saboda nasan bazaka jurewa rabuwa da babyn nan takaba shiyasa nahutar da kai" dariya sukayi gaba d'ayansu har Batool nafad'in

"Ai kuwa dai my sister kin huta don nasan yana zuwa jinya itama hajia kaka zata biyo bayansa, kinga daga nan amaimakon yayi jinyarki sai yakoma kiwon babynsa don duk abunda aka kawo maki ita zai bawa tacinye" hajia kaka dake faman dariya tace

"Oho dai ku kuka sani, tunda kuncinye abunku ba zancen ayi mani gori" Ummi na murmushi tabar wajen cike da sha'awar rayuwar su papi, cikin zuciyarta kuwa addu'a takeyi Allah yasa ta tsufa lafiya cikin soyayyar juna itada mijinta, k'ofar d'akin dady taturo yana zaune shida su Bilal da Bassam dake faman k'ilbasa shikuma yana kallonsu yana dariya, murmushi tayi sannan ta k'arasa cikin d'akin tace dasu

"Oya Bassam, Bilal kuje gasu papinku can sunzo" ko kafin tarufe baki har sun bar d'akin aguje, suna shiga Bilal ya rungume hajia kaka shikuma Bassam papi, cike da sha'awar yanda suka gansu tubarkallah masha Allah hajia kaka tafad'a tana kallon Bilal dake gaisheta

"Lpy lau mai gidana takobin daga kana lpy?" Dariya Bilal yayi had'e da cewa

"Lpy klw, papi mai sanda ina wuni?" adai dai nan sai ga Mahmud da tund'azu ya hango tsayawar motarsu lokacin da yafito wanka yashigo d'akin jikinsa duk ba k'wari, murmushi yayi tare da duk'awa ya gaishesu cikin natsuwa had'e da mik'awa papi hannu sukayi musabiha, nanfa suka kacame da fira abun gwanin ban sha'awa,

Allah sarki uwa da d'a sai Allah lokacin sai da mom tafad'owa hajia kaka cikin rai tanajin wani irin abu makamancin rashin jin dad'in ganin 'yar tata awurin, koba komai zata so ace izuwa yanzu dady yayi hak'uri tadawo cikin 'ya 'yanta duk da babu abunda suka rasa awajen Ummi kusan ma inta fahimta kamar yaran sunfi natsuwa yanzu akan da,

Sosai Mahmud ya fahimci yanayin da hajia kaka tashiga ciki, murmushi yayi had'e da dafa cinyarta da yake gaba d'ayansu zaune suke ak'asa su kuma akan kujeru yace

"Ran hajia kaka yadad'e yayi k'arko, babyn papi mekike tunani?"

Murmushi tayi masa sannan takalli papi da tund'azu shima ita yake kallo ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa sannan sukaci gaba da firarsu, sai alokacin papi ya lura da Basmah bata wurin, kallonsa ya maido wajen Mahmoud yace

"Kai dakata wai inama bak'auyar matata take ne, tunda muka shigo ko wulgawarta bangani ba ko bata nanne" sai alokacin itama hajia kaka ta ahamo da tunda suka shigo bata ganta ba, amma kamar ta lura da mutum kwance a falo kan kujera, Ummi dake k'ok'arin shigowa dady na biye da ita abayanta tanajin papi na tambayar ina Basmah, gaban yafad'i saboda rashin sanin amsar da zata fito daga bakinsa gashi gaba d'aya ko zancen b'atanta bata sanarwa da dady ba balle halin da take ciki saboda bai dad'e da dawowa ba sai tabari sai zuwa anjima tafad'a masa, da sauri tak'arasa wajen tana murmushi, amma ina har Mahmud yafara fad'in

"Gatacan kwance papi..."

"Eh wlh papi yanzunnan muka samu bacci ya d'an d'auketa, tun safe take fama da matsanancin ciwon kai amma alhmdulillah tasamu sauk'i" Mahmud yaji Ummi tayi saurin katsesa lokacin data k'araso wajen, kallonta yayi cike da mamaki don shi so yayi yafad'a masu abunda yafaru ita kuma ummi tayi kamar bata gane saba. Durk'usawa dady yayi cikin girmamawa yana gaisheda su papi sukuma yaran gaba d'aya suka tashi suka bar falon,

"Ashha injin da sauk'i? ai da antada ita tunda marece ya gabato, kuma kunsan vaccin bashida kyau alokacin" hajia kaka tafad'a tana kallon Ummi shi kuma papi yace "Allah ya sawake" hakan yasa Ummi ta tashi taje ta rik'o Basmah ahankali hannunta akan kafad'arta ta maida ita d'akinsu batare datayi k'ok'arin tashe taba saboda rashin sanin yanayin da zata tashi aciki,

Nan shi kuma papi da hajia kaka dake matuk'ar jin kunyar dady suka shiga bashi hak'uri akan abubuwan da suka faru tare da nuna masa rashin jin dad'insu, sosai shima dady yaji kunyar abunda yafaru tsakaninshi da mom d'in don koba komai yanda iyayenta suke da matuk'ar mutunci da yanda suke darajjashi amatsayinsa na surikinsu yaci ace yahak'ura mom tadawo d'akinta.

Saida su papi sukayi sallar magrib sannan suka koma gida, suna yaba kirki da mutunci irin na hajia Aisha data had'osu da sabulayye da turarukka masu tsananin tsada bayan tabasu shadda da atamfa masu kyau sunata sanya mata albarka. Koda zasu tafi still Basmah bacci takeyi da suka sake tambayar ta sai Ummi tace masu ai ta tashi, harma tayi sallar magrib tana gama wane baccin ya sake d'aukarta, k'ilan saboda maganin data shane, hajia kaka taso ta fahimci wani abu amma saita basar tace "Allah yabata lpy" suka amsa da "amin"

Mom kuwa suna dawowa har ta kammala girkinta tayi sallah ita kuma hajia kilishi tana kwancenta akan gado,

"Tashi muje gasu papi can sun dawo"

Afalo suka tarar dasu zaune akan kujeru suna firar kyawon halin Ummi, gaishesu sukayi tare da yimasu barka da dawowa sannan mom tace

"Papi wai ina kuka jene haka kuka dad'e?" cikin basarwa dady dake k'ok'arin mik'e yashiga d'aki yace

"Daga gidan mijinki muke" cikin jin haushi mom tace

"Kai papi me kuma kukaje yi acan bacin kunsan bani ciki asalima 'yar taku da don ta zakuje kun barota agida, ai wannan saiku saimun reni wlh, haba papi meyasa kuka yimun haka, gaskiya banji dad'i ba"

"Ke dalla rufemun baki, shashasha to munjene mubada hak'urin shashancin da kika tafkawa abokiyar zaman ki ga yarinyar ta, kewai sai yaushe zaki hankali ne?, shikenan saboda bakya nan bazamuje ba? Duk da d'inbin rashin mutunci da kika aikata" Shikam papi juyowa kawai yayi ya kalleta had'e da girgiza kai sannan ya wuce abinsa batare dayace mata uffan ba,

Cikin fushi mom tabar wajen tana fad'in,

"Wlh nidai hajia baku kyautamun ba, yanzu gashi kun jamun gori ko nakoma gidan Aisha tace mijina baya sona sai da iyayena suka rok'amun ya maisheni" Baki abud'e hajia kaka ke kallonta kafin tace












Mr's huss@in✍

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____28💎


Tafd'i jam Hussaina ashe bakyada hankali, mu kike cewa haka? To shikenan munje d'in, kizo ki dokemu, wannan rashin mutunci har ina, fad'a hajia kaka tadinga yimata ita kuma jin bazata iya tsayawa ta saurara ba yasa tawuce abunta tabar hajia kilishi nan tanata faman bata hak'uri, jin fad'an yak'i ci yak'i canyewa yasa papi fitowa daga cikin d'akin yadawo ya zauna kusa da ita, kallonsa tayi idanuwanta cike tab da k'walla tana fad'in

"Don Allah kaji abunda take fad'a sai kace itace ta haifemu" ta k'arasa maganar tana nuna hanyar da mom tawuce da hannu hajia kilishi na ganin haka itama tabar falon,


Rungumeta yayi ajikinsa yanajin kamar ya kamo mom yayita duka saboda yanda tasa ran babynsa ya b'aci,

"Kiyi shiru haka baby, d'ago fuskarki ki kalleni sai kija numfashinki sosai sannan kifitar dashi ahankali kinji ko?" kamar yanda papi yace tayi haka tayi sai ga hawayen da take nefan fitowarsu tund'azu suka mak'ale sun fito, cike da tausayinta yadinga shafa kanta data d'ora akafad'arsa ahankali sannan yaci gaba da cewa

"Babynah kiyi shirunki, bana son kina yawan fad'a da ita tunda batada hankali, abunda yafi kawai shine muyi mata addua Allah ya shiryeeta, kinsan halina idan nabiye mata sai inyi abunda zandawo ina nadama da kaina, shiyasa kikaga na k'yale ba tare dana tanka taba"

"Nifa nafara tsorata da halinta alhaji, yarinya sai kace akanta shed'an yake zaune, bata tab'a yin abunda zai faranta zuciyar wani sai dai tata, wannan irin son kai da me yayi kama?"

"Muyi addu'a Allah ya canza mata halayya insha Allah zata dena"

"Allah yasa, amma wannan abubuwan ta sunfara wuce wuri" haka papi ya zauna yanata lallashi da lurar da babynsa yanda zasu dinga hak'uri da halin 'yar tasu har akayi kiran isha'i, papi bai fita masallaci ba da yayo arwala saboda har antayar da sallah sai ya jagoranci hajia kaka sukayi abussu tare.

Shikuwa dady bayan su papi sun wuce d'akinsu Bilkisu ya shiga don yadubo halin da Basmah ke ciki jin cewar da yaji anyi batada lafiya, sosai yake kallonta daya shiga shima kamar yana son gano wani abun amma da yake bacci takeyi bai fahimci komai ba yakoma part d'insa yana fad'in

"Allah yasawak'e" bayan yayiwa Ummi umurni data biyoshi yana son magana da ita.

Sun kusan minti biyar zaune a falonsa batare da kowanensu yace uffanba, azahiri dukkaninsu kallon makekiyar TV dake jikin bangon d'akin sukeyi amma abad'ini ba haka abun yakeba kowane da abunda yake tunani aransa, gyaran murya dady yayi wacce ita tamaido da Ummi aduniyar tunanin data shiga, ahankali tajuyo tana kallon fuskarsa da haryanzu take kan TV yana kallo...murmusawa tayi kad'an sannan gaba d'aya tajuyo jikinta tana kallonsa, shima hakan yayi bayan ya tsaida kallon da sukeyi waje d'aya, hannayenta biyu yarik'o da hannuwansa yana kallonta yace

"Rabba'atul bait, inaso insanar dake shawarar da nayanke akan maganar da mukayi dake yau da asuba, sai dai bansan yanda zaki kalli abun ba ina fatar zaki yiwa abun kyakkyawar fahimta" d'an muskutawa yayi ya gyara zamansa sannan yaci gaba da cewa

"D'azu hajia Hussaina takirani tana bani hak'uri akan abunda yafaru kuma har tayi alk'awarin cewa idan tadawo zata baki hak'uri akan abunda yafaru sannan zakuyi zaman lafiya kamar yanda nake buk'ata, tabbas nafahimci tayi nadama don haka nake son bayan sallar isha'i zanbi bayan su papi inje inyo bikonta, naso ace idan har zata dawo to awani gida cikin gidajena zata tare amma saboda wani dalili nafiso kuyi hak'uri kuci gaba da zamanku atare hakan zaifimun dad'i, to amma ke mekike gani akan haka?" Murmushi Ummi tayi wanda zai tabbatar maka da cewa har cikin zuciyarta tayi farinciki da abokiyar zamanta zata dawo d'akinta sannan tace

"Alhmdulillah dadyn yara, Allah yak'ara maka hak'urin zama damu, kuma kayi daidai da kayanke shawarar zuwa ka dawo da matarka, d'azu bakaji irin kunya da nauyin su papi da suka rufeni ba, gaskiya naji dad'in haka Allah ya zaunar damu lpy kuma ya yafe mana laifukan da muka aikata, saidai wani hanzari ba gudu ba, mezai hana ka tambayeta idan tanada ra'ayin dawowa nan gidan tunda tanuna tanada buk'atar arabamu tunfarko sai kaji ko me zatace akan haka" kwanto da kanta yayi ak'irjinsa sannan yace

"Karki damu da wannan rabba'atul bait ni ra'ayinki shine nawa kuma na tabbata shine nata don haka feel free kifad'amun abunda yakamata kinji ko?"

"Shikenan dadyn yara tunda haka kace to nima ra'ayinka shine nawa"

Cike da jin dad'in amsar data bashi yazagaye bayanta da hannuwansa had'e da manna mata kiss agoshi

"Allah yayi maki albarka rabba'atul bait, ngd da zamowarki always by my side" dariya tayi tana k'ara shigewa jikinsa "wannan abune da yazama dole akaina don haka babu buk'atar godiya" sosai sukayi tighting d'in juna suna jin bazasu iya rayuwa ba idan basa tare.


Ana gama sallar isha'i dady yanufi gidan papi tare da rakkiyar amininsa alhaji Usman, suna isa maigadi yabud'e masu gate suka shiga, bayan sun fito cikin mota da gudu maigadin yak'araso yana gaishesu kasancewar yasan dady kuma duk sadda yazo gidan sai yayi masa alkhairi mai tsoka, bayan sun amsa dady yace yaje ya sanarwa da papi zuwansa, sosai papi yayi mamakin zuwan surikin nasa saboda basu dad'e da baro gidan ba, "Allah dai yasa lafiya" hajia kaka tafad'a tare da mik'ewa tashige d'aki, umurni papi yayi masu da su shigo ciki, bayan sun shigo sun zauna suka gaisheda papi sannan dady ya gabatar da dalilin zuwansu, sai da papi ya kira hajia kaka ya sanar da ita sannan yasa takira masa mom.

Tun fushin da mom keyi har yanzu bata sauko ba sai faman kmbure fuska takeyi, hajia kaka naganin haka tayi tsaki had'e da kwab'a ta maida kallonta ga hajia kilishi,

"Kelishi dama mijin wannan saunarce yazo wajenta, amma naga alamar kamar ita batada buk'atar ganinsa, don haka kifad'a mata zanje na sanar da papinta cewa tace ya sallamesa bazata zoba" mom najin haka tasaki fuska tana kallon hajia kilishi dake kallonta itama tayi murmushin da baikai cikiba tace

"Haba hajia ai ganinan zuwa yanzu, yama za'ayi haka so kike papi ya cimun mutunci?" Sake kallonta mom tayi tare da kwab'a tabar d'akin ranta ab'ace duk da dai k'asan zuciyarta cike yake da farinciki, mom d'ince idan ba haka tayi mataba sai tafito tana faman kumbura masa fuska, cike da zolaya hajia kilishi tace

"Ja'ira anaso ana kai kasuwa, ai nazata fushinki bazai bari kije kigansaba"


"Hmmm ina zanyar da hajia tamaido mana da aiki baya, ai zanyi yak'i da zuciyata intirsasata yin abubuwan da bata so don cimma burin rayuwata" da sauri ta d'auki wani zumbulelen hijabi tasaka sannan ta feshe jikinta da turarukka masu k'amshin gaske, juyowa tayi had'e da cewa

"Sai nadawo k'awata"

Tunkan ta iso wajen tafara acting d'in marairaice fuska har ta iso falon, kallon dady tayi da tunda ta doso wajen yake kallonta yana so suhad'a ido, wani irin shu'umin murmushi ta sakar masa wanda ya sashi saurin lumshe idanuwansa tare da saukar dasu k'asa gudun kar yayi abun kunya agaban surukansa, gaishesa tayi cikin girmamawa ya amsa tare d'ago kansa yana sake kallonta, a wannan karon labarine ya canza tab'an garenta ganin yanda yayi fresh sosai hadda 'yar k'iba ya k'ara, tsananin kyawon da yayi mata yasa ta lumshe idanuwanta sannan tabud'esu ahankali ta saukar akansa, murmushi yayi mata yana k'ok'arin motsa bakinsa yaji, papi ya fara yimata bayanin abunda ketafe dasu, sannan ya d'ora dayi mata fad'a sosai har hajia kaka na tayashi, bayin sungama suka juyo ga dady da abakinsa suka yimasu nasiha sosai akan muhimmancin aure da kuma kula da hak'k'ok'an juna, sosai jikinsu dady yayi sanyi mom hadda k'ak'alo kukan munafucci tana neman yafuwar dady agabansu. Hakan datayi ya matuk'ar faranta zuciyoyin iyayen nata dama shi kanshi dady, umurni papi yayi mata da tajeta d'auko kayanta tabi mijinta, taso tayi masu musu akan haka saboda bata shiryaba ga kuma maganin da takeso tayi amfani dashi bata sakaba, amma saitayi shiru, har zata mik'e sai taji dady yace

"Papi inba damuwa ina rok'on alfarma idan bata gyaraba abari sai gobe sai inzo ind'auketa saboda kocan ba'a kimtse wajen yakeba sai nasa angyaggyara wajen"

"Shikenan alhaji amma ai da kunwuce tare tunda ga yara goben sai surik'a mata tagyara" ji mom tayi kamar ta watsa ihu ganin papi naneman wargaza mata shirin da takeyi....











Mr's huss@in✍

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

*_ASSALAMU ALAIKUM, INA MAI MIK'O SAK'ONNIN GAISUWATA GA 'YAN UWANA WRITERS DA SUKA NUNA MUN KARAMCI DA HALACCI TARE DA KULAWA TAMUSAMMAN ALOKACIN DA NARASA MAHAIFINA😭 LOKACIN DA NAKE BUKATAR RARRASHI DA BAN MAGANA SAI GASHI SUNYI TURURUWA SOSAI WAJEN MIK'A TA'A ZIYARSU AGARENI HA'DI DA KYAWAWAN ADDU'O'I ZUWA GA RUHINSA😭, WASU SUN KIRANI AWAYA, WASU KUMA TEXT MESSAGE SUKA TURO, WASU KUMA TROUGH INBOX 'DINA NA WHATSAPP SUKA AJIYEMUN DA'DA'DAN KALAMANSU DA BAN HAKURI AKAN RASHIN DA NAYI, WANDA DUK DA INA CIKIN ALHINI HAKAN BAI HANANI YIN FARINCIKI AKAN KULAWAR DA SUKA BANI BA, SUKA NUNA MUN DAMUWATA DA RASHIN MAHAIFI DA NAYI SUMA TASUCE, NAGODE MAKU SOSAI 'YAN UWANA WRITERS, HAKIKA NARASA MAHAIFIN DAYA ZAMA JIGON RAYUWATA😭 WANDA SHIKA'DAINE KE RARRABE DAMUWATA DA FARINCIKINA BATARE DAYA TAMBAYENI BA "KIYI HAKURI BILKISU KINJI KO?" KODA YAUSHE ITACE KALMAR DA YAKE RARRASHINA DA ITA DON GUSAR DA DAMUWATA,😭 UBANGIJI ALLAH KA RAHAMSHEKA ABBIE,😭😭WANNAN KALMAR DA KAKE FA'DAMUN "KIYI HAKURI" BATA TSAYABA ABBIE SABODA GUSHEWARKA, NASAMU 'YAN UWAN DA SUKACI GABA DA NANATAMUN ITA BAYAN NA RASAKA "'YAN UWANA WRITTERS" KUMA ZANCI GABA DA AMFANI DA ITA HAR K'ARSHEN RAYUWATA ACIKIN DUKKANIN AL'AMURRANA,😢 BAN MANTA DAKU BA READERS KUMA KUNNUNA SOYAYYA DA KULAWA AGARENI SABODA YAWAN KIRAYE KIRAYEN DA NASAMU AGAREKU HAR SAI DA WAYATA TAYI SHUTDOWN AMMA HAKAN BAI HANA SAK'ONNIN DA KUKA TUROBA TURURUWAR SHIGOWA ALOKACIN DANA KUNNA WAYAR BA, A GROUPS DA PRIVATE DUKA NAYI RECEIVING CONDOLENCE NAKU, NAJI DA'DI SOSAI KUMA HAKAN YA QARA MANI KAUNARKU AKO WANE LUMFASHI NA RAYUWATA KUMA ADDU'O'IN DANAYI AGAREKU TSAKANINA NE DA UBANGIJINMU SHINE KA'DAI YASANI, KUN NUNA MUN SO DA K'AUNA INA FATAN ALLAH YA 'DAUKAKA KOWACE WRITER DAGA CIKINMU, READER'S KUMA ALLAH YA KARE MANA RAYUWARKU DATA AHALINKU YA BAMU ALJANNA DA RAHAMARSA, WU'DAN DA MAHAIFINSU KE RAYE ALLAH YA TSAWAITA MASU RAYUWARSU CIKIN AMINCINSA👏🏻 MUKUMA DA NAMU SUKA RASU ALLAH KAJIK'ANSU DA RAHAMA😭😭 ALLAHU AKBAR SUN RASU ALOKACIN DA MUKE TSANANIN SONSU YA ALLAH KA HA'DA FUSKOKINMU DA NASU A AL-JANNAH FIRDAUSI_*😢👏🏻


💎Page_____29💎


Tun fitar dady daga gidan bayan sallar isha'i Ummi kefama da Basmah ta tashi amma ina baccinta takeyi hankali kwance, Billy da Batool dake gefe suna kallon yanda Ummi kefaman tarai rayota ajiki tana bubbuga gefen fuskarta ahankali tare da ambatar sunanta, kamar sun had'a baki sukace "Ummi kibarta idan ta tashi zamu kiraki", juyowa tayi fuskarta d'auke da damuwa tace " Anya kuwa kina tunanin lokacin da zata tashi bacci bai d'aukeku ba, kuna gani ko abinci bataci ba, ni ko lunch ma bana tunanin tayi, gaba d'aya babu komai acikin ta wanda ya danganci abinci" tak'arasa maganar kamar zatayi kuka, rufe bakinta keda wuya taji Basmah dake rungume ajikinta tana yunk'urin yin amai kafin ta d'agota tuni ta wanke mata jiki dashi, ko kad'an Ummi batayi k'ok'arin d'agata daga jikin taba saima k'ara rik'ota datayi sosai cike da tausayinta, da sauri su Billy suka nufo wajen suma fuskarsu babu walwala suna yimata sannu, saida tagama a man tsaf sannan Billy ta bud'e wardrobe taciro wani d'an madaidaicin towel Ummi takarb'a tafara gogewa Basmah bakinta ta ajiyeta gefe sannan itama ta goggoge jikin ta, kallon Batool tayi tace

"Kuzo kugyara 'Yar uwarku kafin nadawo" kallonta ta maido ga Basmah data matuk'ar jigata kafin nan tamik'e tafita tana tunanin rayuwar data saka kanta aciki,

Cikin tausayawa suka tada ita zaune, Batool taciro towel d'in wanka suka cire mata kayan jikinta da suka lalace, a gefen gado da take zaune Billy ta rik'eta ita kuma Batool ta shiga toilet tahad'o mata ruwan wanka masu d'an zafi da zata iya gasa jikinta, ita dai Basmah gaba d'aya sai taji tamuzanta acikin su duk laifin da ta aikata baisa suka tsaneta ba sai ma jawota ajiki da sukayi, kallonsu takeyi tanajin k'aunarsu cike azuciyarta, Rirrik'ota sukayi gefe gefe har cikin toilet d'in sannan suka fito, wajen suka fara gyarawa sannan suka fiddo mata doguwar rigar bacci cikin kayanta bayan sun feshe d'akin da turaren room freshners masu k'amshi,

Ummi ma tana Shiga d'akinta toilet tafad'a tayi wanka, k'aznin da jikinta bai daina yibane yasa takoma toilet d'in ta had'a turarukkan wanka masu ka'amshin gaske ta sake wanke jikinta dasu, sannan ta d'auko burner tajona ga wutar nepa tasa wani turaren itace mai k'amshi ta turare jikinta dashi, kasan cewar dare yayi yasa bata b'ata lokacinta dayin kwalliya ba, kayanta tasa bayan tashafa mai sannan tawuce kitchen ta tad'ora ruwan zafi cikin mintuna biyar suka tafasa tajuye a flaks wasu ta d'iba a cup ta had'ama Basmah tea mai kabrin gaske da yasa madarar sannan tazuba zuma aciki amaimakon sugar kasancewar ita zuma maganin ko wace irin cutace.

'Dakin tanufa hannunta d'auke da cup d'in saiga yaya Mahmud yashigo shida su Bassam da Bilal yana dariyar firar shirmen da suke tayimasa ahanya, sai da gaisheda Ummi daya lura fuskarta na d'auke da damuwa sannan ya juyo yana cewa su Bilal suwuce d'akinsu fuskar nan d'aure kamar ba shine yagama dariya ba, kallon Ummi yayi cikin damuwa da yanayin da yaganta yace


"Ummi lpy kuwa?," cup d'in hannunta yakarb'a kafin tabashi amsa yana mai k'ok'arin bin bayanta zuwa d'akin su Basmah data nufa, cikin sanyin murya take fad'a masa cewa

"Basmah tafarko amma amaine ya tayar da ita,kuma ba kad'an a man ya galabaitar da itaba, ina tunanin koza'a kira dr. Yazo yasamata drip don natabbata run breakfast d'in safe data tsakura har yanzu bataci komai ba, bana son wannan abun yacutar da ita ko kad'an" dai dai lokacin da suka shigo sukaci karo da Basmah dake fitowa daga cikin toilet d'in idanunta na zubar da hawaye

Please Login or Register in order to submit comment