Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shagwab'a had'e da rungumesa cike da tsantsar so irin na d'an uwa da 'yar uwa.

"Allah yaya bana son sunan nan da kake yimun dariya yake bani wai Billy Japanis Inani inasu wajen kyawun duk da dai ance suma ba wani kyau ne dasu ba"

"Hhhhh lallai Billy ai japanis nada kyawu shi yasa ma na iya had'a kyawunki dasu sbd yanda kike Kama dasu...ni kam na san sai nayi yanga wajen aurar dake don ked'in kyakkyawa ce" kallon ummi yayi da tun d'azu itama take kallonsa tana mamakin yanda Allah ya fiddashi na musamman acikin 'yan uwansa sannan yace.

"Ai ina ganin garin yawon shak'atawar da Ummi sukaje ita da daddy aka samo cikinki acan agarinsu shi yasa kikayo kama dasu"

Murmushi Ummi tayi tare da shafa kansa.

"A gaida babanah Allah yayi maka albarka, yanda kake kula da farin cikin mu ko mahaifinka iya yanda zai yi kenan, indae mom d'in kace ni bana ganin laifinta tunda nice babba dole nayi hak'uri da duk abunda zata yi agidan nan dama shi babba a duk inda yake dole ya kasance mai hak'uri don da shine na k'asan sa zasuyi koyi, but plz kaima karage fushin nan naka yanzu da anbarka sae kajiwa batool ciwo saboda ta tab'a maka 'yar uwa kai mai 'yar uwa ko?"

"Amma Ummi ai laifin tane bata da Kunya wlh"

"To kade rage fushin zuciyan nan kaji babanah"

"shikenan Ummi Allah ya bani ikon ragewar, Ummi bari naje ga kiran sallah can naji anfara yi a masallatai" muryar bilal dake can gefe kwance yajiyo yana fad'ar

"Yaya nima zan bika nayi sallah" hannu mahmud yasa ya d'ago bilal daga kwance yana cewa,

"Yawwa my lil broth taso muje Daga nan in mun dawo mubiya insai maka sweet zaka sha ko?"

"Wayyo yaya nima zansha kasiyo mani har da chaculate"

"Baza'a siyo dake ba kinyi girma da yawa"

"Ummi kin deji bilal ko? Ina ruwansa ai ba dashi nake ba saina kamashi zan dokesa Ummi kice nazama babbar banza bacin shike fara jana"

Billy tak'ara she maganar cikin shagwab'a tana neman kamo hannun bilal dake sauri mahmud yaja baya yana dariya ita kuma Ummi tarike hannunta cikin dariyar yanda 'yar shekara sha hud'u ke neman yin fad'a da d'an shekara uku tace,

"Haba Bilkisu ai da gaskiyar bilal wai bacin sweet d'in a had'o maki da chaculate, yo ai kece chaculate d'in"

Bubbuga k'afa Billy ta shiga yi tana neman yin kuka ganin yanda Ummi tayi siding bilal kuma ga yaya mahmud nayi mata dariya da sauri ya ajiye bilal cikin zolayarta donta huce yana fadin,

"jid'a ajikina nafasa d'aukar ka, a hannu zan jaka mutafi tunda kake tsokanar aunty Billy, k'yalesa my sister ba chaculate kad'ai zan siyo maki ba hadda duniya bisa tsinkenta (lol pop)"

Wani irin tsallen jin fad'in tayi da yasa bilal tsorata ya b'uya abayan mahmud yazata akansa Billy tayo ta dukesa,

"Thank you yaya" Ta fad'a tare da rugawa tayi d'akinta tana Murmushin jin dad'i,

Shikuwa sake d'aukar bilal yayi suka bar part d'in, girgiza kai Ummi tayi tana dariyar shirme da quruciya irin na 'yar tata sannan itama tawuce bedroom d'inta don yin sallah.

'Dauke da bilal mahmud ya nufi part d'in momynsa yana basa labarin yanda suka yiwa mom b'arna, Ashe bassam ne ya taka gefen gadon mom suna wasa shida batool garin ta kamasa ya fad'owa madubin mom shinefa kwalaben humrorinta da turarukka suka fashe shi kuwa bilal na ganin haka yaje ya ta yasu d'auke wud'an da suke kwashewa da basu fashe ba sai ga mom shine da tana fad'a sukace ai bilal ne yafasa kwalaben.

"Ayya srry lil broth me yasa kaki fad'awa mom gaskiya...." dai dai nan suka iso k'ofar shiga d'akin mom kafin ya basa amsa, tirjiya bilal ya fara yi saboda tsoron mom ba yaso ya shiga d'akin, ajiye shi a k'asa mahmud yayi tare da rik'o hannunsa suka shiga d'akin, cikin d'ari d'ari bilal ke shiga yana rirrik'e mahmud tare da b'uya a bayan sa abun har yaso ya bawa mahmud dariya.

Zaune ya hango mom d'insa tana gyaran kayansu bassam dake kan gado an baje kamar wani d'an k'aramin boutique, kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai alamun haushinsa takeji marairaice fuska yayi tare da kneeldown agabanta yana fad'in.

"Na tuba my mom kiyafe mini indai akan na doki batool kike fushi dani barina kirata tunda belt d'in na hannunta saita rama"

Saboda son da take yi masa yasa ba zata iya jurewa ba ta d'ago kanta karaf suka yi ido biyu da bilal dake tsaye abayansa a tsawace tace.

"Uwar me ka dawo kayi a d'akin nan ko kazo ka karasa fasa sauran ne?" had'e da banka masa wata irin muguwar harara "maza ka ficemin a d'aki ja'irin yaro"

Tsabar rud'ewar da bilal yayi tasa ya saki mahmud da gudu ya nufi wajen madubin yana kuka kafin mom ta sake sakar masa wata irin tsawa yabaro wurin aguje sannan yana mean k'ofar da zai fita, dafe kai mahmud yayi yana kallon momynsa yana so yayi dariyar abun Amma ba dama,

"Mom kiyi hakuri don Allah ni bana so in dinga ganinki cikin irin wannan yana yin plz"

"Ai kuwa ka dinga ganina Kenan matuk'ar baza kafita harkar wud'annan can matsiyatan ba, ina yanzu saeda kajeka lallaso su sannan ka shigo d'akin nan har kake cewa bakaso kaganeni cikin wannan yanayin"

"Pls srry mom kinga har za'a tada sallah banje masallaci ba"

"To ai sae kayi sallarka agida Allah zai karb'a"

"Subhanallah mom kinsan illar dake cikin rasa jam'i ga baligin namiji Kuwa? ai babbar asarace dake kai Mutum ga dana sani, Bari in tafi ina bassam yake ne?"

"To sarkin malamai ai sae ka dubashi a guarding Ina ga yana can yana wasa shida batool"

Girgiza kai yayi yana mamakin halin mom indai mahaifinsu baya gida ba zata tab'a damuwa da tasa k'annensa suyi sallah ba, Gashi yanzu salloli ake yi amma su suna can suna wasa kuma ko ajikinta,

"Allah ya kyauta" ya fad'a afili kafin ya bar d'akin mom na fad'in.

"To kuma me aka yi kake kiran Allah ya kyauta"

"Ba komai mom" yace ba tare da ya juyo ba.

Yana fitowa yaci karo da bilal gefen d'akin yana jiransa Ashe duk tsoratar da yayi be tafi ba, Murmushi mahmud yayi yace

"Bilal kayo sallarka? "

"A'a yaya kai nake jira"

"Agaida takwaran ladanin annabi kayi dai-dai muje ko...?!"

_The more u coment the more updates u will getπŸ€·πŸ»β€β™€ ina godiya da ruwan addu'o'in da kukayi Mani, tabbas natabbata cewa koda yaushe masoyana na man atare daniπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»alhamdulillah kun matukar sanyani farinciki in my previous update da nayi nagode sosai Allah yabar k'auna🀝🏻_ LUV YOU ALL MAH FAN'S❀













Mr's huss@in✍🏻

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NANE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT STORY AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____3πŸ’Ž


Suna fitowa sukaci karo da Bassam aguje Batool ta biyo shi yana kwasar dariya, ganin yaya mahmud yasa suka shiga taitayinsu cike da fargabar kar yayi masu wani abun, wata uwar harara ya watsawa Batool had'e da cewa.

"Ke ko? Hmm! zaki zo hannuna ne, wato ana sallah ke kuma kintsaya yin shashanci da k'anenki don rashin sanin ciwon kai ko?, zaki wuce kiyi sallah ne ko saina makeki awurin nan?"

Cikin sigar shagwab'a Batool ta fara bubbuga K'afafuwan ta,

"Ni yaya Mahmud ba yanzu zanyi ba sai.... "

Kafin ta rufe baki Mahmud yayo kanta fuska a d'aure, tana ganin haka takwasa aguje ta shige wajen small mom tana qunquni had'e da tura baki shi kuma yaja hannun Bassam suka d'auro arwala a famfon dake cikin guading d'in sannan suka nufi masallaci. koda sukaje har an kusa sallame sallah saura raka'a d'aya, haka Mahmud yabi jam'in bayan an sallame ya tashi ya cika sauran taka'o'in da yarasa sannan ya baro masallacin hannuwansa rik'e da Bassam da Bilal yana koya masu addu'ar da ake yi idan anfito daga cikin masallaci...,

_"Bismil-lah wassalatu wassalamu ala rasoolil-lah, allahumma innee as-aluka min fadlik, allahumma iaasimnee minash-shayta nir-rajeem."_

Yana yi suna mai-maitawa har suka isa wurin wani mai shago dake saida sweets dasu biscuit, d'ari biyar ya mik'awa mai Shagon yace ya had'o masa biscuits da sweet amma yayi masa Leda leda kowanne na d'ari har guda biyar. Bacin angama had'a masa ya sake mik'a masa naira d'ari yace ya bashi chaculate da lolipop, cike da jin dad'in cinikin Mai shagon ya had'o masa ya mik'a masa yana dariya wannan karon hadda gyara yasa masa yana fad'in,

"An gaida malam Mahmud shalelen alhaji kaga farin saurayi mai farar aniya, ranka ya dad'e yayi k'arko yayan Billy jepenese godiya nake yi"

Dariya Mahmud yayi don inda sabo ya saba da halin mai shagon duk lokacin da zaizo siyayya shagon mutumin sai yayi mashi wannan banbad'ancin kallonsa yayi kafin yace.

"Uh'umm..malam shehu kwalelanka akan sunan nan dan idan sister Billy taji wannan suna yana fitowa a bakin ka, ina tabbatar maka daga ranar ta dena son kayan shagon nan naka kuma zan dena siya saboda dama saboda ita nake saya"

Yana gama fad'ar haka ya mik'awa Bassam da Bilal kowanen su leda d'aya tare da yiwa malam shehu mai shago sai anjima, Murmushi ya sake yi wanda ya k'ara fiddo masa da tsantsar kyawon da Allah yayi masa ganin yanda malam shehu yasa hannu biyu-biyu ya toshe bakinsa tare da turo idanuwansa waje saboda jin abinda ya fad'a, hannuwan su Bilal yaja suka nufi gida suna shiga yaci karo da Basmah k'anwarsa dake bimasa ta rako qawayenta earpiece lik'e a kunnenta ko d'an kwali batada shi balle mayafi kuma a haka take shirin fita har wajen gate, qawayenma nata kowanen su babu shigar kirki ajikinsu kaida ka gani su kasan k'awayen ban zane, tsuke fuska yayi tare da sakin hannuwan su Bilal..

"Oyah! Maza kushiga ciki gani nan shigowa"

Suka bar wajen aguje hannuwansu rik'e da ledar sweet d'in daya siya masu,

Basmah na ganin haka gabanta ya fad'i don ta riga da tasan kwanan zancen, amma saboda kafuwa da k'arfin hali irin nata sai ta basar tare dayin kamar bata ganesa ba, cikin fad'uwar gaba tace da qawayenta.

"khady, shapsy bye-bye sai mun had'u gobe ko?"

Tana k'ok'arin fita. Wata muguwar damk'a ya yiwa gashin kanta da ta sakawa ribon d'in acuci maza tare da jawota baya,

"Ke wace irin wawuyace zaki fita a haka? Bakya ganin ko wud'annan dak'ik'an qawayen naki da basa iya sanya suturar k'warai ajikinsu sun d'an yafo abunda yarufe masu kansu, shine ke zaki fita haka"

Sai alokacin khady da shapsy suka juyo suna kallonsa cike da son yi masa rashin mutunci saboda jin abunda ya fad'a akan su, tsantsar kwarjininsa yasa a maimakon suyi masa masifa sai gashi sun tsinci kansu da gaishe sa.

Kallonsu yayi tun daga sama har k'asa tare da yatsine fuska yace

"Idan har zaku dinga irin wannan shigar banzar a matsayinku na 'ya'yan musulmi to kar in k'ara ganin k'afarku ta tako da sunan zuwa gidan nan, Infact idan ma ba zaku iya sauya irin muguwar shigannan ba kar nasake ganinku da qanwata if not i will make sure dt nasa kowacen ku tayi nadamar saninta."

k'arasa maganar yayi had'e da nuna Basmah da d'an yatsansa, har lokacin hannun sa rik'e yake da acucinta, cikin tsawa yace dasu.

"Get out now..."

Kallon Basmah suka yi da tuni idanuwanta sunyi jajir suna neman kawo k'walla saboda azabar da takeji, Kafin yace wani abun ya kaiga sake daka masu tsawar da tasa jikinsu na rawa suka bar gidan ba tare da sun yi mata maganar da suka tashi yi mata ba ita kuma yaja k'eyar kanta har cikin gida yana zuba mata masifar karya sake ganin kanta ba d'an kwali balle tayi tunanin fita haka!,

Basmah najin muryar small mom ta saki wani irin azababben kukan da yasa mom k'arasowa wajen aguje tana sallallami cikin sauri ta rik'o Basmah daya hankad'e can gefe yana cigaba da yi mata fad'a, kallonsa mom tayi a hasale tace.

"Amma Kai anyi mugun yaro anan, kai kenan kullum cikin cin zalin yaran nan ko tausayin su baka yi"

"Mom sune suke yin abubuwan da basu kamata ba wallahi duk da 'YAN UWANA NE SU banajin dad'in d'abi'un da suke yi, don Allah mom dubeta, a haka fa take shirin fita cikin gidan nan kanta babu d'an kwali sai kace ba d'iyar musulmai ba, ko Bilkisu da take k'anwar ta bata yin irin wud'annan mugayen d'abi'u sai su, to wlh kwanan nan idan basu dena ba jikinsu zai gaya masu"

Yana gama fad'ar haka yasa kai yabar part d'in ransa a b'ace,

"Eyyeeee...! lallai Mahmud wuyanka ya isa yanka, 'yan uwan naka kake cewa suna mugayen d'abi'u har kake cewa wata ta fisu? to ka canza wasu 'yan uwan mana tunda kanada wacce tafisu kyawawan d'abi'un, Jimun fitinannen yaro zaibi duk ya takurawa yarana, yi shiru ki k'yalesa zai dawo ya sameni idan ma turosa aka yi zanyi maganinsa, maza kishare hawayenki"

Mom ta fad'a tare da rad'awa Basmah wata magana akunne.

Hararar mom Basmah tayi had'e da langab'e kanta tace

"Da gaske?"

"Ha'a Basmah zan maki k'arya ne?"

"Yeee sai mom! Shi yasa nake masifar sonki"

Aguje Basmah ta wuce d'akinta kai tsaye ta nufi wardrobe d'in kayanta, tana bud'ewa taga wasu had'add'in kaya jins da t-shart har kala uku da mom tasiya mata, tsalle tayi had'e da yin ihu sannan taciro wayarta..

"Hello khady"

"Inaji basmah me kuma zaki fad'a mana bayan agabanki brother naki yaci mana mutunci amma kika kasa cewa komai"

"Haba khady Wlh yaya Mahmud matsalarshi ya wace da ita, ni bakiga wak'i'ar daya sani bane? wlh har yanzu kaina ciwo yakemun, abeg kimanta kawai kinji qawata"

"Hmm! Shikenan ammafa banji dad'in abinda yayi mana ba, don har nace keda ganina sai baba ya gani"

"Hhhhh matsoraciya"

"Naji d'in irin wannan red-face da yaya Mahmud yayi ai dole na tsorata, ammanfa ba k'arya basma yayan nan naki ya had'u ba kad'an basu don yafiki kyau sosae"

"mtsss manta kawai, naji yafini kinsan me?"

"A'a Basmah sai kin fad'a"

"Akwai chilling! Mom ta had'o min wasu had'addun kaya shine nace yaushe ne birthday din qawar nan taki sai mukece raini dasu"

"Haba bab da gaske? Wow kice akwai corrumboling"

"Yes woo....dama kala uku ne kinga sai na d'auki d'aya na baku sauran"

"Ok..shikenan Zanyi checking up naji ko yaushe ne I will call you back "

"Shikenan bye-bye sai najiki" daga haka tayi hanging wayar sannan tafad'a kan gado tana rera 'yan wak'ok'i cikin jin dad'in kyautar da mom tayi mata,

Kai tsaye Mahmud ya wuce falon Ummi bakinsa d'auke da sallame yanemi wuri ya zauna, ganin babu kowa a falon sai k'amshin girlie dake tashi ya tabbatar masa da cewa suna kitchen, jin muryarsa tasa Ummi ta fito hannunta rik'e da cup d'in ruwa ta mik'a masa

"Babanah an dawo masallacin?"

"Eh Ummi me kike dafawa naji falon ya gauraye da k'amshi" Mahmud yafad'a tare da karb'ar cup d'in ruwan, dariya Ummi tayi sannan tace

"Kai babanah wane k'amshi kuma, Bilkisu ce ke dafuwar indomi" tana rufe baki sai ga Billy ta shigo falon d'auke da plate d'in indomien a hannu Bilal biye da ita yana kuka tana fad'in

"Yaro k'ara volume indai indomien nan ce bazaka cita ba"

Dariya Mahmud yayi had'e da girgiza kai

"Billy!.Billy!!..baki da dama wato ya k'ara volume d'in kukan ba zaki basa ba ko?..Toh nima bari chaculate d'ina ya sha zamansa ba zan baki ba"

"Sorry yaya gashi na ajiye, Bilal zo muci" Har Bilal ya fara kokarin zaunawa ta jaye plate d'in tace "To kaje ka wanko hannunta ko malam"

Zaune shima mahmud yayi tare dasa hannunsa sukaci indomien yana yaba k'ok'arin Billy data iya girki haka.

"Lallai idan daddy ya dawo zance ya yiwa Billy aure tunda ta iya girki"

"Hmm Allah dai ya tsare wanda zae aureta a haka da shan jagwalgwalo, ai kaima daurewa kad'ai kayi don tana ta hannun damarka nasan da bazaka iya ciba" Bilal ne yake fad'i yana d'ago kai yana sud'ar hannu yace

"Hiynnmmm... su aunty Billy Japanese an iya dafa indomi"

Dariya suka kwashe da ita har ummi na rik'e ciki

"Wato indomien tayi dad'i Bilal?, ashe kaima karage iya fad'an Billy jepenese d'innan?" cike da k'warewa Billy ta d'aga hannu zata doke sa yaya mahmud yayi saurin rik'eta yana dariya

"Bafa shi ya fad'a haka ba malam..."

Sai kuma yayi shiru tare da jawo ledar sweet da biscuit d'in da ya siyo mata ya mik'a mata har ya turo baki zatayi k'orafin chaculate d'inta taga ya mik'a mata had'e da lolipop, cikin jin dad'i tayi masa godiya tare da cewa

"yaya ina nasu aunty Basmah da batool? "

Nuna mata nasu yayi tare da mik'ewa yana cewa ummi.....





















Mr's huss@in✍🏻

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NANE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____4πŸ’Ž


Ummi sai anjima, wai yaushe daddy zai dawone?, d'azu nayita trying number sa but it's switch up!,

"Babanah kenan! yanzu nake cewa bari na tambayeka naji ko kunyi waya da Alhaji yafad'a maka ranar da zai dawo,ni kaina nata kiran wayarsa a kashe, Ashe kaima baka samesa ba"

"Eh wlh...Allah dai ya dawo mana dashi lpy, Ummi bari intafi ina so ind'an fita wajen sulaiman"

"Amin babanah, to adawo lpy ka gaidashi inkaje"


"Yaya Mahmud inzo muje wurin su yayya batool muyi hawasa"

"Eh taso mutafi, Bilal kaima zakaje?"

"A'a ya'ya ni bazan jeba mom zata koroni"

Cike da jin kunyar hali irin na mom Mahmud yasosa qeyar kansa tare da cewa

"To bari naturo maka Bassam kuyi wasa ko?"

"o'oh shima dukana yakeyi shi dasu yayya Basmah"

"Dukan ka kum..... " Ummi ce tayi saurin katseshi saboda ta yanke maganar

"Babana idan zaka dawo kabiyo mani da lemun tsami naga na guiding be nunaba kuma ina buk'atarsa anjima zanyi had'in bama"

"To Ummi" ya fad'a had'e da rik'o hannun Billy suka bar falon

Suna fita ummi tajawo Bilal ta rik'e masa kunne had'e da murd'ewa ta yanda zaiji zafi ta d'aure masa fuska sosai kamar ba ita ba

"Bilal mena fad'a maka? ban cemaka bana son yawan surutu da k'orafi ba? shine har kamanta kake nema ka d'auko mani fitina, kanaso yayanka yaje yata dukan maka 'yan uwane?" tasake murd'e kunnen har saida ya saki 'yar k'ara..


"Awwsh... A'a Ummi, nadena bazan k'ara ba..amma ai yayya Batool tace muba 'yan uwansu bane!"


"Itama mantawa TAYI shiyasa tafad'i haka Amma ku 'yan uwansu ne haka suma 'yan uwanka ne bakuda kamarsu aduniya kaji ko?"

"Eh Ummi kenan su 'YAN UWANA NE nida aunty billy?

"Sosae kuwa, saboda haka kar insakeji kana fad'awa wasu ko yayanka cewa sunyi maka kaza da kaza, kazamo mai hak'uri da rik'e sirrin 'yan uwanka!"

"To ummi" Murmushi tayi sannan ta sakar masa kunne had'e da cewa

"Good boy, Allah ya albarkaci rayuwarka kai da 'yan uwanka"

Suna shiga part d'in mom suka tarar da ita zaune cikin falo itada yaran gaba d'aya zaune suna kallo, Billy ce tafara shigowa bakinta d'auke da sallama amma babu wanda ya amsa saida suka jiyo muryar yaya mahmud a bayanta shima yayi sallamar sannan suka amsa atare kamar sun had'a baki, dariya Billy ta kwashe da ita saboda kai da kaji yanayin da suka amsa sallamar kasan atsorace suke, kallon d'aya ummi tayi mata mai had'e da tsana ta d'auke kai, rufe baki tayi tare da k'arasowa cikin falon tagaida mom, batare da mom ta kulata ba tace

"Lpy" koshi don taga Mahmud ba wurin ne kuma tasan halinsa yanzu sai ya cika mata kunne da zancen 'YAN UWANA NE se kace garesa farau 'yan uwa!..

kallon mom yayi kamar yasan metake tunani yayi murmushi had'e da girgiza kai sannan ya nemi guri a falon yazauna,

Atare k'annen nasa suka sake had'a baki suna gaishesa...saida yayi murmushi sannan ya amsa had'e da cewa

"Batool d'in mom zoki karb'a yana hararar Basmah data quro masa idanuwa tana jiran taga abunda zai ba Batool"

Mik'amata ledar sweet da biscuits din daya siyo masu yayi

"Kid'auki d'aya kiba waccan marar kunyar d'aya"

Godiya sukayi masa fuskokinsu d'auke da fara'a, mom kuwa da tunda suka shigo bata d'aure fuska batare data kula saba dashi har Billyn saboda haushin abunda yayiwa Basmah sai gashi ta saki fuska tana fad'in

"To ko kaifa amma ka zauna kullum cikin kyarar 'yan uwanka najini babu wata kyautatawa sai fifita wasu kakeyi akansu, koda yake ba laifinka bane anriga da anshanye mani kai kamar yanda aka yiwa babanka, me akeyi da zuriar Sammu da sihiri nikam... "

Katseta Mahmud yayi cikin raunin murya

"Haba mom! wai meye haka? Shikenan ni babu yanda zan rab'i mahaifiyata naji sanyi batare da naji tana fitar da kalaman da zasu b'ata mani rai akan 'yan uwana ba!?"

Kallon Bilkisu yayi da tuni kalaman mom suka tab'a zuciyarta amma sai tayi kamar batajin abunda suke fad'a maida kallonsa yayi ga mom dake taunar cingum tana fad'in

"To ai saika canza uwar dama nasan indai Aisha na raye bazan tab'a samun girmamawa awajenka ba sai ranar da tamutu"

A wannan karon kukane yaci k'arfin Bilkisu dama tuntuni idanunta cike suke tab da hawaye tabar d'akin aguje tanajin wata irin tsanar mom nasoma shiga zuciyarta, wai yanzu agabanta mom keyiwa mahaifiyarta fatan muyiwa.

"Haba mom meye haka wai yanzu babu damar Bilkisu ta shigo cikin 'yan uwanta tazauna sai ansata kuka? Kitunafa ba ita yakamata ace kina yiwa wud'annan abubuwan ba, Wallahi Allah mom bakya kyautawa" Cikin takaici yabar falon kamar zai tashi sama, mom takalli Basmah da Batool suka bushe da dariya tace

Indai akan waccan munafukar matar ce dake neman rabaku da d'an uwanku gab nake da yimasa iyaka akanta


"Wayyo mom har yayya Billy tabani tausayi" cewar Bassam

Tangad'o k'eyarsa Basmah tayi dad'i duka, itama Batool takaina masa ran k'washi akai tace

"Samnan yaro zauna garin tausayinta kaima ahad'a da kai a asirce kamar yanda akayiwa yaya mahmud yafi sonsu akanmu"

"Gud girl shiyasa kike burgeni batool"

"Ai Wlh mom kinmun dai dai, ita munafuka tazo tayi mana zaune don tsabar gulma da lek'en asiri"

Basmah ce tayi saurin cewa

"Hmmmm..mom wama yasani ko Ummi ce ke turota shak'ar sirrin mu"

"Tabbas Basmah kinyi gaskiya, inko hakane sai natabbatar nasa Aisha nadamar daga ita har 'ya'yan nata"

Billy na fitowa part d'in mom ta hango bilal rik'e da ball d'insa yana bugawa, cikin gudu-gudu tanufi wurinsa had'e da rungumesa tana kuka,

"Aunty Billy me akayi maki kike kuka"

"Bilal mun shiga uku 'yan uwanmu basa son mu, mommy ta tsanemu..."
da sauri Bilal ya rufewa Billy baki

"Aunty Billy kiyi shiru kuma kidena fad'a kar ammie tajiki zata murd'e maki kunne nima haka tayimun d'azu"

"Bilal me kake tunani akansu da yasa suke yimana haka"

Shiru Bilal yayi kamar wani babban mutum yana tunani kafin ya kalli billy yace

"'YAN UWANA NE! haka Ummi tace"

Dariyar yaya Mahmud suka jiyo da tund'azu yake tsaye bayansu yana sauraren abunda suke fad'a, d'ago kan da zatayi suka had'a ido dashi, murmushi yayi tare dasa hannu ya goge mata hawayen dake zubowa daga idanuwanta.

"Am srry my Japanese sister, abunda Bilal yafad'a shiya kamata ace kema kina tunawa aranki, mu daku 'yan uwan junane, muyi hak'uri da halayen juna da sannu komai zai wuce, karki d'auki zancen mom azuciyarki har yazo yadameki kinji ko?"

Shiru Billy tayi tana tunanin kalamansa har Lokacin hawaye basu dena zubowa a fuskar taba..

"Haba Billy Japanese" yafad'a had'e da jan hab'ar bakinta kafin ya rufe baki shima bilal yakai bakinsa a kunnenta ya hura mata iska sosai dama d'abi'ar da yake yimata kenan inyana son tsokanarta sai bata sakar ba ya hura mata iska a kunne suyita fad'a don yasani bata so, aikuwa yana ganin ta zabura ya ruga aguje guading yana dariya bayansa tabi itama tana fad'in

"Allah yau sai kagane tunda kiyimun wannan abun, Kama tsaya in kamaka don ko Ummi taji saita rik'e munkai tunda tace ka dena tsokanarta" ganin yana bata wahala yasa Mahmud ya zagayo tacan gefa ya rik'e matashi...ihu bilal yafara had'e da dariya yana zille zillen tserewa amma ina saida Billy ta riskesa, hannu tad'aga da niyar dukansu taji Mahmud ya rungumesu suduka yana fad'in

"We're srry aunty Billy luv you much" batasan lokacin da itama ta saki dariya ba had'e da cewa

"Luv u too brother, always proud of you yaya"

Da haka Ummi ta iskosu wajen saboda ihun bilal da taji mai had'e da dariya, salati ta rafka tana tafa hannuwa


"Fitar kenan anan babana?, dama kana wurin atsaye suke tafka wannan uban rashin ji, ka kama ka biye masu fisabilillah kamar bakada abunyi?"

Kafin yace wani abu

Please Login or Register in order to submit comment