Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunanta kafin tajuyo ta amsa mata tana kallonta "Batool lafiya?"

"Lafiya klw mom, dama bak'one akayi yana palour zaune dadyne yaturo sa"

"Ok kije ina zuwa" juyowa tayi tadawo parloun tana kallonsa tare da yimasa murmushi shima yamayar mata yana kallon k'wayar cikin idanuwanta had'e da murza hannayensa waje d'aya, mom nashirin saukowa daga kan gadon saiga kiran dady yashigo awayarta, tana d'agawa tagaishesa cikin girmamawa, bayan ya amsa sund'an tab'a firar soyayya kamarta minti biyu yake sanar da ita zancen dr.Ahmad da abunda yakawoshi na neman auren 'yarsu, daga k'arshe yace tafara zuwa sugaisa da yaron saita iskoshi part d'insa su tattauna maganar, sosai mom taji dad'i aranta sukayi sallama da dady sannan ta ajiye wayar cike da fatan Allah yasa yaron d'an babban gidane wanda yad'ara Mahmud pilot komai.

Ita kuma Batool kitchen tashiga ta d'auko ruwa da lemon exotic ta azo akan tray had'e da d'oro glass cup akai tayo cikin parloun, a gabansa ta ajiye tabud'e gorar ruwan ta tsiyaya a cup ta mik'a masa tana fad'in "Bisimillah dr." Murmushi ya sakar mata sannan yamik'o hannu yakarb'i cup d'in hannunta "Nagode gimbiyata, Allah ya nuna mun ranar da nine zanyi maki haka" yana rufe baki saiga mom tashigo parloun fuskata ba yabo ba fallasa, da sauri ya ajiye cup d'in ita kuma tanemi kujera tazauna tana kallon mom k'asa k'asa cike da fargaba, saida tazauna sannan ya d'an zamikke akan kujera had'e da duk'awa yana gaisheda ita, tunda ta shigo takallesa ta tuno da fuskarsa ranar da yaje asibiti ganin Mahmud pilot, kallonsa tayi daga sama har k'asa kafin tace

"Daga ina?" Saboda gaba d'aya tun ranar data fara ganinsa bai yimata kuma ace wai shine keson 'yarta, Batool najin wannan tambayar da mom tajefo masa amadadin ta amsa gaisuwar da yayi mata gabanta yafad'i, muryar Basmah da fitowarta kenan taji abunda mom d'insu keshirinyi tace

"Laaa..dr Ahmad yau kaine agidanmu? Sannunda zuwa" tak'araso cikin parloun tana yimasa murmushi, duk'ar da kansa yayi don dama har ga Allah baisan ta ina zaifara bawa mom amsartaba, zaunawa gefen mom tayi tana dariya tare da rik'o hannunta tace "Mom wannan shine dr. Ahmad cikakken likita kuma k'wararre a 'b'angaren gyaran k'ashi wato orthopedic doctor, shine yakula da Batool ranar da k'afarta naciwo muka kaita asibiti" dakatar da ita mom tayi cikin b'acin rai tahanyar d'aga mata hannun had'e da cewa

"Kibarshi yayi bayani da kansa mana ko bayada bakine?" Cikin i'iniyar muryar da baisan yanada itaba yace

"Ayi hak'uri mom, kamar yanda dai tayi bayani ni sunanan.." Shima katsesa tayi tahanyar cewa "Bana buk'atar jin wannan yanzu "fad'amun waye mahaifinka kuma meye sana'arsa a wannan garin" rik'o hannun Basmah Batool tayi kamar zatayi kuka jin abunda mom keahirinyi, girgiza mata kai tayi alamun tayi hak'uri, bud'e baki dr.Ahmad yayi zaiyi magana saiga yaya Mahmud yashigo parloun, gaida mom yafarayi sannan yajuyo ya mik'a masa hannu suka gaisa,

"Abokina idan kungama gaisawa da mom ana jiranka awaje, i think emergency call ne daga hospital" yatsa Batool tasa tagoge hawayen da suka zobo a idanuwa had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya, duk'ar dakai dr. Ahmad yayi sannan ya d'ago yana kallon mom yace

"Sunana Ahmad Bashar mai fulawa kuma ni cikakken haifaffen wannan jaharne, nai karatuna na boko dana arabiya daidai gwargwado kuma yanzu haka ni jami'in lafiyane a asibitin Jidda specialist hospital, muna zaunene a anguwar g.r.a nida mahaifiyata, mahaifina kuma bakowa bane face k'aramin d'an kasuwa mai matsakaicin k'arfi dabai rasa rufin asirin ciyarda iyalansa ba kuma Allah yayi masa rasuwa kimanin watanni biyar da suka wuce, bamuda kud'i amma munada d'inbin soyayya wacce da ita nazo nan don neman amincewarku na auri 'yarku, ina son fatima kuma ina son na aureta, natabbata koban bata komai ba aduniya zan bata soyayya da farinciki nahar abada" yana gama fad'ar haka yamik'e tsaye tare da cewa

"Kiyi hak'uri mom idan nab'ata maki rai acikin amsar tambayar dana baki da kika yimun, nizan tafi" sannan yajuya yabar wajen zuciyarsa cunkushe da damuwa, tashi Batool tayi zatabi bayansa mom ta dakatar da ita

"Karki kuskura kibar palourn nan idan ba b'acin rai kike so yabiyo bayanki ba, kimanta dashi don keba sa'ar sabace ni bazan bari 'yata ta auri mai jinin mai saida fulawa ba wanda yamutu a sanadiyar bashi, tsaye cak dr. Ahmad daya kai bakin k'ofar fita yayi tare da juyowa yakalli mom sannan ya kalli Batool dake hawaye yayi murmushi tare da ficewarsa, fad'a mom tadinga yiwa Batool sosai akan wai taje tayo mata kwashe kwashen d'an gidan maifulawa da mahaifinsa bai barmasa gadon komai ba saina bashi tabuga mata warning akan karta kuru tasake kulasa saboda tadad'e da jin tarihin mahaifinsa agari bazata yarda tahad'a jininta da matsiyaci kamar saba bedroom d'inta tashige tanaci gaba da banbami da kumfar baki, tana shigewa da sauri tafice tabi bayansa ita kuma Batool tazube k'asa tana kuka had'e da maimaita "innalillahi wa inna ilaihirraji'un"

Yana k'ok'arin ficewa daga gate ne bayan yaya Mahmud yayita bashi hak'uri Basmah ta cimmasa "docter" tafad'a tana k'ok'arin dai daita tsayuwarsa, juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ba walwala, duk'ar da kanta tayi k'asa kafin tad'ago kanta tace

"Don Allah kayi hak'uri da abunda mom tayi maka nida 'yan uwana duka bamuji dad'in hakan ba ko kad'an" "babu komai yayya Basmah dama haka rayuwa tagada wani lokacin farinciki wani lokacin bak'in ciki wani lokacinma atare suke zomaka da farinciki da kuma bak'in ciki kamar dai yanda suka zomun yanzu atare, karku damu kinji"

"Kayi hak'uri don Allah kar hakan tashafi soyayyar da 'yar uwata keyimaka domin natabbata bazata juri rasakaba saboda tana matuk'ar sonka sosai" tsayuwarsa yagyara yana murmushin da saida hak'oransa suka bayyana yace

"Haba yayya kima dena wannan tunanin domin ni wannan abun bazai sa naja da bayaba, fatimafa itace rouhina, zuciyata da kuma gangar jikina taya za'ayi narabu da ita akan wannan d'an k'an k'ananen abun, ashirye nake dana bada dukkanin farincikin rayuwata matuk'ar hakan zaisa na mallaki fatimatah" dariya Basmah tayi jin yanda ya ajiye kalmar sunan fatimah saika rantse yafi kowa iya fad'ar sunan sannan tace

"Shikenan dr. Nagode Allah yatabbatar maku da alkhairinsa"

"Amin yayya yanaga kina dariya don nace fatimatah ko bazaki bani qanwar takiba ne"

"Rufamun asiri dr.karka jamun naje asibiti ak'i dubani, ai indai Batool ce nabaka gaba d'aya gangar jikinta da rouhinta kai kad'ai nake jira kazo ka d'auki aburka" murmushi yayi sannan yace

"Shikenan yayya godiya nake sai anjima ni zanwuce"

"To agaida mana da mamynmu sosai" farincikine yarufe dr. Don yana mugun son duniya yaji ana karrama mamynsa da girmata "in aha Allah zataji" yafad'a tare da ficewarsa aransa yanaji komai rintsi komai wuya bazai tab'a rabuwa da Batool d'insaba...


_Manage pls kutarbene anjima in sha Allah_




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Ina kuke iyayen K'warai iyayen kirki, kumatso kusa domin gaisuwar yau takuce ku kad'ai, nagaisheku durum durum tare da fatar alkhairi agareku manya iyayen yaran gobe *Mmn Sss, Mmn Adnan, Mmn muhad, Mmn hanan, Mmn taufiq, Mmn Usman, Maman fatima and Ummi, Maman Ahmad and fatima da kuma oum Imaan* ina matuk'ar jin dad'in yanda kuke bibiyar wannan littafi, ngd ngd ngd sosai ubangiji Allah yabaku aljannah da rahamarsa kuma ya albarkaci yaranku👏🏻 ina so kusani ni Billy s fari ina alfahari daku akoda yaushe_😍

💎Page_____66💎


Koda ya isa gida bai sanar da mamynsa labarin matsalar daya samu awajen mahaifiyar Batool ba illama dad'a bata labarin karamci da halacci da mahaifinta ke dashi, sosai mamy tanuna masa farincikinta saidai idan yalura da ita kamar akwai abunda kedamunta.

Kusa da ita yadawo had'e da rik'o hannunta yace "Mamynah meyake damunki naga bahaka natafi nabarki ba kuma koda mukayi waya banji alamun kina cikin wannan damuwar da nake gani atattare dake ba?" Fashewa da kuka tayi tace "Yau antunomun da rasuwar mahaifin kane, naso yana raye yagani kuma yaji abunda ya dad'e yana addu'a taganin ansamu zaman soyayya da lafiya tsakanina da 'yan uwansa amma abun yacutara, sai gashi yau da baya raye Allah yakarb'i addu'arsa kuma hakan tafaru" hannu tasa ta d'ago hab'arsa tana goge hawayen idanuwanta taci gaba da cewa "Yau baffanka wato yayan mahaifinka sunzo harcikin gidannan lokacin bandad'e da gama waya d'a kaiba suna kuka tare da nadamar abunda suka yimana nida mahaifinka, sun zubar da hawaye sosai suna rok'ona dana yafe masu abubuwan da sukayimun suntuba sunyarda da kuskurensu, kuma dama canni banrik'esu araina ba nace duka nayafe masu abunda na sani dama wanda bansani ba, sunjima suna jiran dawowarka kaima surok'eka kayafe masu, anan nake sanar dasu cewa kana wajen nemo auren surukarsu, sunji dad'i sosai kafin sutafi akan cewa jibi zasu dawo saboda kiran da akayi masu daga gida ana bid'arsu da gaggawa, wannan abun shiya janyomun tunawa da mahaifinka har yasa damuwar ta taushe farincikin wannan labari dana so yimaka albishir dashi", Rungumeta yayi sosai shima yana hawaye yace

"Alhamdulillah mamy naji dad'i sosai nima zan shiga cikin 'yan uwana, ubangiji Allah yajik'an Abba yagafarta masa"

"Amin ya Allah, ya kabaro 'yatah lafiya take?"

"Lpy klw sunce agaisheki sosai da ita da yayarta"

"Allah sarki ina amsawa, ashe tanada yaya?"

"Eh mamy inkika ganta kamarsu d'aya da 'yarki d'an haske kawai ne ya banban tasu don kina ganinsu zaki zata sud'in 'yan biyune"

"Ikon Allah! To Allah ya albarkaci rayuwarsu"

"Amin mamynah ni kad'ai, dadyn tama yace inturo iyayena idan har da gaske nakeyi, to da nayi tunanin inje infad'owa su baba bala da liman suje tare da kayan nagani inaso amma yanzu nabar shawara ahannunki duk yanda kikace kuma kika ga yadace sai ayi"

"Karka damu idanma sud'in zasuje duk d'ayane sai asanar dasu tunda wuri amma da zaka iya hak'uri har zuwa jibi idan baffan naka yazo tunda yasan da maganar sai akira shi liman d'in sutafi tare kai kuma saika tanadi abubuwan daya kamata aje dasu kafin ranar tayi" Shiru yayi na d'an mintota kafin can yace "Shikenan mamy babu damuwa Allah yakai ranmu"

"Amin yaron Abba" tafad'a had'e da mik'ewa tabar d'akin, tana fita yacire safunan dake lak'e a k'afafuwansa tare da rigar jikinsa ya lak'e ajikin hanger yarage dagashi sai dogon wandon shaddar daya cire da singlet ya haye akan gadon tare da rufe idanuwansa ahankali yana tunano maganganun da mom tayi masa, duk dayaji zafinsu azuciyarsa hakan baisashi tsanartaba saboda kima da daraja da take da ita a idanuwansa koba komai takasance mahaifiya awurin yarinyar da yakeji tamkar jinin jikinsa don haka dole yamanta da abunda tayi masa, beside duk maganganun data fad'a gaskiyane babu k'age balle sharri aciki saidai ita cinfuska da walak'anci da rena arzik'in mutum ba abubane mai kyau kuma ko a musulunce Allah da manzonsa duka sunyi hani da hakan, yana cikin wannan dogon tunaninne yaji rurin k'arar wayarsa dake neman agaji acan cikin aljihun gaban rigarsa dake rataye, tashi yayi ya d'auko wayar ya d'aga kiran had'e da karawa akunnensa yana murmushi,

"Hello rabin raina ya kike" yafad'a tare da sake komawa kan gadon yakwanta fuskarsa na kallon silin, cikin muryarta maikama da tasha kuka sosai tace

"Lpy klw my angel hop ka isa gida lafiya?"

"Sosai kuwa swthrt gani kwance yanzu nagama tunanin mom d'inmu, pls don Allah kibata hak'uri bisa abunda yafaru d'azu, bana son wannan abun yashafi soyayyarmu ko kad'an"

"Insha Allah zanbata my angel, amma kaima kayi hak'uri bisa zafafan kalaman datayi agareka, ko kad'an banji dad'in faruwar haka kuma banzaci hakan zai faruba, am so srry for dt my angel" tafad'a hawaye nagangarowa daga gefen idanuwanta,

"commonnn..swthrt kar wannan abun ya dameki, ai ita uwa tanada matuk'ar muhimmancin da duk abunda tayi ga d'anta daidaine kuma tayine don tana sonsa, saidai awasu lokutan soyayyar kejawo asamu akasin da zaisa a aikata kuskure aciki bawai don a k'untata rayuwar 'ya'yaba, dani dake duka d'ayane don haka dole muyi hak'uri da duk wani kuskuren mom d'inmu kinji ko?"

"Eh my angel nagode sosai daka zamo mai yiwa mahaifiyata uzuri da kuma fahimtarta, don Allah kak'ara hak'uri nasan da sannu zata fahimceka"

"Karkiji komai nafad'a maki ko kin manta matsayinkine awajena?" Murmushi tayi sannan tace

"Bazan mantaba saboda nasan my angel namusamman ne"

"Dagaske kikeyi hayaty ni d'in na musamman ne?" Yafad'a tare da mirginawa yajawo pillown dake ajiye can gefe ya rungume yana murmushi

"Sosai kuwa my angel, saboda arayuwata bantab'a ganin mutumen da Allah yayiwa baiwa mai tarin yawa kamarka ba" lumshe idanuwansa yayi had'e da cewa

"Kifad'amun wace irin baiwa nake da ita wacce tasani zamowa namusamman awurinki nikuwa nayi maki alk'awari zanbaki tukuici mafi soyuwa azuciyarki"

"Shikenan bari nafad'a kodon wannan feeling da kake dashi yasake samun gurbin zama fiye da yanda kake dashi don nasan hakan zaisa 'yanmata suk'ara nisanta kansu dakai"

"Ki hanzarta fad'a kada kisa inyi azarb'ab'in baki tukuici tunkafin naji abunda kikeson fad'a, 'yar dariya tayi kafin ta juya kwanciyarta zuwa kife hab'arta na akan pillow sannan tace

"Ahmad! Suna mai matuk'ar daraja da Allah ya ambata acikin alqur'ani, kasantuwar wannan suna atare dakai yasa Allah yayi maka ni'ima da baiwar hak'uri, fad'ar gaskiya, kwarjini, cikakkiyar siga, fikrah tare da iya magana, kyakkyawar zuciya, sanyayyan murmushi, girmama iyaye, tarin ilimi, sanin yakamata sannan abu mafi girma da yasa nake matuk'ar k'aunarka shine rama kyakkywa da mummuna"

"Kai.ka.kai..hayatie kaffa kisa nafad'o akan gadon tsabar farinciki, mamy ta'aza mani dariya"

"Kasan Allah nama manta wasu my angel, amma duk wud'annan abubuwan suna cikin baiwar da Allah yayi maka"

"Hayatie mezan baki amatsayin tukuici domin wanda natanadar maki nida kaina na tabbatar yayi kad'an, amma inaso kisani ina yimaki so irin wanda romeo beyiwa Juliet ba haka kuma majnunnin laila baiyiwa kaima shiba"

"My angel kenan! Ai nadad'e da sanin hakan domin soyayyar ka agareni fili take azahiri ba b'oyayyiyaba abunda kawai nakeso shine, duk lokacin daka fita wata takalleka to kace mata ni nace antsayarmun dakai amatsayin mijin da zan aura sannan katsole mata idanuwa tayanda bazata sake iya kallonkaba" tak'arasa maganar tana dariya, k'walo idanuwa yayi awaje kamar zasu fad'o k'asa shima d'in yana dariya

"Ki rufan asiri hayaty kada kisa akirani da mijin makafi don natabbata hukunci da iyayensu zasuyi mun baiwuce na saina auresu" da haka sukaci gaba da firarsu cikin so da k'auna tamkar babu wani abun daya faru d'azun.

Yaya Mahmud kuwa tuni ya sanarwa da papi cewa zab'insa itace zab'in daya yimasa don haka jaddi da papi sukayita murna tare dasa albarka koda maganar taje kunnen dady cewa yayi babu matsala don dama ita fareeda d'iyar amininsa tuni mahaifina yasanar dashi cewa mahaifiyar yarinyar da yarinyar duka basu yarda da zancen cewa ahad'asu su biyu ya auraba wanda jin hakan bak'aramin dad'i yayiwa yaya Mahmud ba, nan take dady da amininsa sukaje suka nemowa yaya Mahmud auren faraaha wajen jaddi da k'annen mahaifinta bisa jagorancin papi, kuma alhamdulillah ankarb'esu cikin mutunci da girmamawa tare da karramawa, sosai dady yaji dad'in samun sarakanai nak'warai da yaronsa yayi wanda saida farincikin da yake ciki ya bayyana k'arara afuskarsa.

Yau sati d'aya da komawarsu Mahmud pilot borno kuma yaune mahaifinsa da k'annensa suka sanar da zuwansu, hakan yasa gidan suka tashi da shire shiren tarbar bak'i na musamman, wata hotel dady yasa akayo odar kalolin abinci da namomi kala kala, ga lemunan kwali dana goruna da aka tanada suma banda snacks da fresh lemons da suma akayo oda awajen k'wararrun Baker's kai abun sai wanda yagani, kiran dr.Ahmad daya shigo wayar dady yanzu yasa aka sake yowar wani sabon had'i na musamman duk don tarbar sarakanan nashi don dama tun kwana biyu da suka wuce dr.Ahmad yaje har office d'in dady ya sanar masa da zancen zuwan iyayensa amma sai ya dakatar dashi akan yayi hak'uri yabari sai bayan wasu kwana biyun auzo kenan ranar da iyayen Mahmud pilot suma zasu zo, yayi hakanne saboda abun yazo masu cikin sauk'i to shine dr. Ahmad d'in yakirasa akan zuwa bayan azahar iyayen nasa nanan isowa. Yaufa idan kaga fuskar dady da Ummi zaka d'auka ranar auren yaran nasune tazo sab'anin mom dahar yanzu tak'i sauka akan dokinta nabata son auren Batool da dr.Ahmad, duk nasiha da lurarwar daya kamata dady da yaya Mahmud da Basmah sunyi mata amma fir tak'i tasauko itadai kawai bata sonsa, dady kuwa da ransa yab'aci kai tsaye yace mata kotana so ko bataso sai ya aurawa 'yarsa wanda takeso donshi natsuwa da hankalin yaron sunyi masa,

Yaya Mahmud ma cike yake da farinciki yau za'azo neman auren k'annensa wanda shi dady ya wakilta a matsayin wakeelin 'yan uwansa, mahmud ikon allah yaro kenan mai hankalin manya da kuma dattako, farinciki sosai yakeyi duk da ak'asan zuciyarsa tausayin k'anwarsa Basmah ke kwance aciki, jiyake inama ace duka su akunne haka zai faru agaresu da yafi kowa farinciki, ita kuwa hankalinta kwance tariga ta dangana tabarwa Allah komai saidai idan ciwon yatasar mata tashige toilet ko can part d'in dady tayita fama har Allah ya kwantar mata dashi, izuwa yanzu ciwon yayi mata tsanani don bata bari kowa yasan halin da take ciki balle akaita asibiti ashawo kanta duk data d'an rame babu wanda yakula da hakan kasancewar dama can batada wani jiki sosai shiyasa aka kasa fahimtar hakan saidai duhu da tayi kuma shima ba sosai ba.

Alhamdulillah duka family's d'in biyu sun iso lafiya tsayawa fad'ar yanda abu yakasance b'ata lokacinne, domin takowa ne b'angare suntaka rawar gani da kuma ban mamaki wajen kayan nagani ina so da suka kawo especially dr Ahmad da mom keyiwa kallon matsiyaci d'an mai saida fulawa sai gashi yayi abunda ko wani maikud'in bazai iya ba.














*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Bazai yuyu na manta da d'inbin soyayya da k'aunar da kuke yiwa wannan littafi, hakan yasa nake mik'o gaisuwata tare da fatan alkhairin Allah yakai agareku aduk inda kuke my sisters *Haifa💋, Jidda alk'ali, Ni'ima barhama, Asma'ul husnah💏, Kubrah, Shamma halliru, Oum Suhaima, Ummeeteey, Sara2zamfara, Balqias, Hawwabilyer, Chamsiya, Salmah shafi'u salis, Hauwa isa Ibrahim, Maman ummi, Sumaya sifawa, Jamila abdullahi garba, khadija tukur* a gaskiya kunada matuk'ar yawan da idan nace zan tsaya lissafoku gaba d'aya page d'innan bazai isheniba, amma ina masoya wannan littafi na 'yan uwana ne, wud'anda na ambata dama wud'anda ban ambaci sunan suba su sani cewa kune hasken fitilar dake yadamun acikin rubutuna kuma ina alfahari daku a duk inda kuke, ina rok'on Allah yafaranta dukkanin zuciyoyinku kuma yabaku aljannah firdausi da rahamarsa👏🏻, ngd ngd ngd sosai da zallar k'aunarku Allah yabar zumunci_🤝🏻

💎Page_____67💎


Sanadiyar maganganun da mom tayi masa yasa yaci burin nuna mata cewa ba tarin dukiyane arzik'i ba, kyakkyawar zuciyar iyayi dakai shine arzik'i, don kuwa shima yaya taka rawar ganin dta zarce fiye da wacce iyayen Mahmud pilot sukayi sosai, kwalayen lemun exotic katam biyar sai kuma na hollandia suma katam biyar sai biscuit shima kala kala har kwali goma masu matuk'ar tsada ga kwalayen cingums da mintuna kowane kwali goma ga chaculate chaculate kwali biyar, ga dabino kusan tiya goma had'e da k'aton kwali da aka zubo sabulayye da turarukka masu kyau da tsada. Ba dady kad'ai ba hatta yaya Mahmud yayi mamakin kayan da dr Ahmad yakawo, duk da itama Billy Mahmud yazubo kaya sosai saidai gaba d'aya tsari da had'uwa da burgewar kayan dr. Ahmad sun tsallake tunani godiya su dady sukayi sosai tare da d'inbin alkhairin tukuici da yayima kowane ahalin iri d'aya batare da banbantawa ba bayan ya gabatar da kowannensu da matsayinsu, suma d'unki dad'i K'warai dagaske inda anan iyayen Mahmud pilot suka bijiro da suna son ayanka masu sadaki zasu biya had'e dasa rana saboda yanda Mahmud pilot yatsare mahaifinsa da rigimar shi bazai koma wajen aikiba saida matarsa, dady yaga gaggawar hakan sosai amma saboda karamci 'yar uwarsa agaresa yasa yaji bazai iya girgiza masu ba don haka yaba yaya Mahmud dama daya yanka masu sadaki, Shiru yaya Mahmud yayi don shima d'in baiso hakanba yaso abari har nan dawani lokaci zuwa sannan itama 'yar uwarsu Basmah tatsayar da miji sai ayi masu komai atare,

"My son kai muke sauraro kabar mutane azaune, mekake tunanin?" Sai alokacin yabud'e baki yace

"Dady idan sun amince kowace sadakinta za'a biya naira dubu hamsin" kallon dady qanen mahaifin Mahmud pilot yayi had'e dayin murmushi yaciro dubu d'ari biyu yace

"Ga wannan dubi d'ari biyune amatsayin sadakin 'yarmu domin tafi k'arfin hamsin awajen mu" sudai iyayen dr.Ahmad dama basuzo da shirin biyan sadakiba don haka baffansa yafita waje ya kirasa awaya yasheda masa cewa tofah har sadaki anyanka kuma gashi su basuzo da wannan shirinba amma ita 'yar uwar tata har iyayenta sun amince kuma sunbiya dama su suka d'auko maganar, wani irin farincikine ya lullub'e dr lokacin yana duba wata marar lafiya yamik'e tsaye had'e da cewa

"Baffa kuma ku amince ko nawane zanbiya, saiku sheda masu cewa zaku sake dawo ku kawo sadakin daga baya saboda yanzu ba'a shirya kukeba, ni kuma dama k'arshen watannan nakeso naciro kud'in da nake tariya a account saboda wata lalura dake gabana sai acira akai masu"

"To shikenan ahmadu kayi hak'uri ni yakamata nayi maka wannan amma gashi saboda alfahari da sonzuciyata yasa arzik'in nawa da nake tink'aho dashi yak'are banida hanyar da zan iya yimaka d'ana abunda zaisa yayi alfahari dani amatsayin wan mahaifinsa" baffa yafad'a yana kuka.

"Haba baffa miye haka kakeyi, aikoda kana dashi nafi farinciki ace ni nabiya sadakin matata dakaina akan abiyamun, kuma koyanzu baffa ina mai alfahari dakai cewa a matsayinka na wan mahaifina kaje kanemomun aure da kanka, kadena wannan tunanin kajiko baffa"

Saida yagoge hawayensa da hannu sannan yace "shikenan Ahmadu Allah yayi maka albarka"

Acan cikin d'aki kuwa yaya Mahmud cewa yayi bazasu karb'i dubu d'ari biyuba amatsayin sadakin Billy saboda idan kud'i zasu saka to tabbas sadakin nata sai yafi dubu d'ari biyu amma albarkar abu tafi yawansa kuma albarkar Allah suke nema aciki don haka subada dubu hamsin d'in sun isa, dady dake gefe zaune abunsa yayi murmushi tare da godewa Allah daya yimasa ni'imar d'a kamar Mahmud har ya iya zaunawa yayi wakilcin auren k'annensa da yakamata ace 'yan uwansane sukayi, bud'e baki k'anen mahaifin mahmud pilot yayi zaiyi magana dady ya dakatar dashi tahanyar murmushi yana fad'in

"A'a alhaji mubarshi ahaka, ai yagama magana tunda yace albarkar Allah ake nema kawai muyi fatan Allah yanuna mana lokaci kuma yasanya masu albarka"

Adole auka cire dubu hamsin d'in suka mik'owa yaya mahmud yakarb'a suna fad'in

"To alhamdulillah Mungode sosai Allah yatabbatar mana da alkhairinsa." Kowa ya amsa da "amin"

Shikuma baffa tab'angaren sa bayani yayi masu kamar yanda dr.Ahmad yace yayi kuma sun amince da hakan, nandai shima dady yarok'esu dasuyi hankuri zancen sarana har sai yayi shawara da iyayen yaran mata da kuma 'yan uwansa in sha Allah zai nemesu ya sanar dasu a duk lokacin da suka kai k'arshe,

Bahaka suka soba amma tilas sukayi hak'uri saboda duba da irin shima karamcin da yayi masu daga nan baffa ya jagoranci taron yayi masu addu'ar watse taro sannan kowanensu yakama hanya da kyakkyawan labari zuwa ga ahalinsa bisa karamci irin na Allah Bashar mai furnitures.

Bayan sun wucene dady yasa yaya mahmud yakira masa Ummi da mom, kusan atare suka shigo mom sai faman wani d'ad'd'aure fuska takeyi ita kuma ummi fuskarta d'auke da farinciki taje kusa dashi ta zauna tana fad'in "mun amsa kira ranka ya dad'e Baban amare harma da angwaye duka anya wannan rana bazamu rubutata a qundin tarihiba irin wannan k'yalli da annurin da fuskarka kefitarwa, yau sainaga siga da kamalar da Allah yayi maka tak'ara bayyana ka k'ara kwarjini sosai fiye da ko yaushe" tak'arasa maganar cike da tsokana, dariya yaya Mahmud yayi shikuma dady yashiga gyaggyara babbar rigarsa yana d'aga allon kafad'unsa wanda hakan yasa mom data nemi waje can nesa dasu tazauna batasan lokacin da murmushi ya kucce mataba, tabbas yau ba k'arya suma maigidan nasu yayi matuk'ar kyau sosai masha Allah, kallon Ummi yayi sannan ya juya yana kallon mom itama irin kallon nan da ake cewa ya kuka ganni, kauda kai gefe tayi duk dako tasan ya wanku sosai amma saboda takaici dake cinta naganin kayan nagani inason yaransu

Please Login or Register in order to submit comment