Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma saboda kar wani tunani yazo masu arai yasa tarik'o hannun Batool data mik'e tana batun iskosa tasamu itama tamik'e tsaye, tare suka isa wajen kowacensu tajawo kujera ta zauna, juyawa Batool tayi tana k'walawa twiny d'inta kira, ita kuma Basmah ta noce kai k'asa tanaji tamkar zuciyarta zata fito saboda tsananin soyayyarsa dake fizgarta, wani irin ciwo zuciyar tafara yimata amma saita daure tace

"Yaya kozaka bari sister ta wakilceni tunda banida lpy" d'ago kai yayi yana kallon Billy data nufo wajen saboda kiran da taji twiny d'inta tayi mata rik'e da apple tanaci, murmushi yayi sannan yace

"Karki damu yanzun nan zamu gama, dukkaninku 'YAN UWANA NE, don haka kowace tanada matsayin da babu wacce ke iya wakiltarta acikinku" hannun Billy Batool tarik'o da niyar zaunar da ita akan kujerar dake kusa da ita tace

"Twiny ina zuwa akwai aikin da zan k'arasawa ummi a kitchen, so kusha firarku ta 'yan uwa kafin in dawo" tana gama fad'ar haka takoma kitchen abunta shi kuma ya fiddo wayoyi da layoyan daya siyo guda uku ya janje kwalin Samsung galaxy agefe had'e da layin da akayi wa register da sunansa, phantom d'in guda biyu ya mik'awa Basmah d'aya sannan yaba Batool d'aya had'e da layoyan yace "ga tsarabarku dana manta ban kawo maku ba da mukazo" sannan ya ajiye qatuwar ledar kayan cosmetic d'in daya sawo masu itama yace "ga wannan ku k'ara da ita kuda twiny d'inki, yaya is srry fd let tsaraba" yafad'a yana kallon Batool, cikeda farinciki suka bud'e baki suna yimasa godiya especially Batool da bata tab'a rik'a wayaba, don dady cewa yayi basu isa rik'a taba, Basmah ma dake da ita ada ab'oye mom tasaya mata ita wai saboda abokananta nayi mata dariya wai batada waya,



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____63💎


Kallonsu kawai yakeyi yana dariyar yanda suke nuna jin dad'i da tsantsar farincikinsu akan kyautar da yayi masu, d'ago kai Basmah tayi had'e da cewa

"Yaya anya hidimar nan batayi yawa ba?" "Dame kuma Basmah?" yafad'a yana kallonta

Sadda kanta k'asa tayi tace "Mungode sosai yaya Allah yabar zumunci kuma yakareku da dukkanin abink'i" saida ya lumshe idanuwansa fuskarsa d'auke da murmushi sannan yace

"Shiiii...kidena godiya ku 'YAN UWANA NE, don na kyautata maku basai kun godemun, fatana Allah ya kawo maku miji nagari da zai kula daku yanda yakamata koda yake naga rawar kan Batool tayi yawan da bazata bari sai auntynta ta tsaida miji ba sannan ita ta tsayar da alama aure takeso" yafad'a cikin zolaya yana kallon Batool, dariya tayi kafin tabashi amsa dace

"Kaji yaya da wata magana ai duk rawar kaina bankaina k'anwataba ita data kawo mana miji har cikin gida suna tsula soyayya ko kunyar iyaye basaji" zaro idanuwa yayi kafin ya jefeta da simpack d'in dake hannunsa yana fad'in "iyyeee ya tabbata yarinyar nan aure kike so, yayan kike ga yawa magana haka?" Kaucewa tayi tare da d'aukar kwalin wayarta tamik'e tabar wajen tana dariya, karo tayi da yaya Mahmud zai shigowa wayarsa lak'e akunne suna waya da faraaharsa, kallo d'aya yayi mata ya had'e girar sama data k'asa sannan yaciro wayar yamik'a mata yana fad'in

"Ke nifa gayennan naki yafara takurani, always feel a little jealous idan naji muryarsa acikin wayar matata" karb'a tayi had'e da barin palourn tana nuna masa kwalin wayar da mahmud pilot ya siyamata tana nuna masa yabud'a yagani irin nima nayi tawa d'innan, mere baki yayi tare da jujjuya kwalin wayar sannan yanufi inda su Basmah da Mahmud pilot kezaune yana fad'in

"Zaki gane yarinya" kujerar dake gefensa yaja ya zauna had'e da cewa

"Sannun ku d'an uwa, Basmah yajikin?" 'Dago kanta da tund'azu yake ak'asa tayi tana kallon yaya Mahmud tace

"Naji sauk'i yaya, barka da shigowa"

"Yawwa, kije mom naki ranki" yafad'a ganin yanda take zaune awajen takure da alama tana cikin damuwa, sosai taji dad'in hakan da yace tayi saurin mik'ewa zatabar wajen taji muryar Mahmud pilot nafad'in

"Basmah dawo kizauna dama akwai maganar da naso nayi da d'an uwa akanki kafin muwuce gobe don banajin dad'in yanayin da kike ciki yanzu, gaba d'aya kin canza daga Basmar dana sani agidannan zuwa wata Basmar daban, so tunda dai gaki gamu ina so kisaki jiki mu 'yan uwanki ne najini kifad'a mana meyake damunki" gabanta ne yayi rass rass jin kalaman dake fitowa daga bakin wanda take tunanin kamar bai damu da halin da take cikiba kafin tajuyo da k'arfi tana kallonsa,

"Yes akwai abunda kedamunki 'yar uwa, koda kin b'oye hakan to yanayin walwalarki shizai bayyana halin da kike ciki koba haka ba d'an uwa" kallon yaya Mahmud da damuwarsa tabayyana k'arara afili tayi sannan ta kallesa tace

"Ni babu abunda yake damuna, duk wannan yanayin da nake ciki jarabtuwa da ciwone ya jawomun haka amma ina warkewa zan koma normal" wata maganar Mahmud pilot ya yunk'ura zaiyi yaya Mahmud ya dafa kafad'arsa had'e da girgiza masa kai,

"Haba d'an uwa to meye zumuncin idan bazamu iya fuskantar damuwar 'yan uwanmu mumagance taba, let her answer d question natabbata tanada damuwa, idan tafad'a sai muyi mata maganinta idan kuma tafi k'arfin mu saimu fad'awa iyayenmu su magance mata ita, haba kadubi yanda takoma sai kace ba Basmah ba" cike da takaici Basmah ke kallon idanuwansa yanda yake zabgar fad'a da kuwa ace zata fad'a masa damuwarta ta tabbata shikansa zai shiga damuwar da zata rusa gaba d'aya farincikinsu, fashewa tayi da kuka tabar wajen aguje, binta yayi da kallo yayi har tafita kana ya kalli yaya Mahmud yace

"Kaga niko, kaga abunda nake fad'a maka ko? Idan har babu damuwa aranta taya za'ayi daga tambaya tafita tana kuka"

"Relax d'an uwa bazamu iya fahimtar matsalarta yanzu ba saboda situation d'in da take ciki, mubita a sannu zata fad'a, kuma i promised koma meyake damunta zanyi settling d'insa in sha Allah, karka damu kajiko!" Yaya Mahmud yafad'a tasigar rarrashinsa saboda ganin yanda yanuna damuwarsa k'irik'iri, ji yake inama ace bainuna soyayyar da yake yiwa qanwarsu Billy afiliba, tabbas da dakansa zai zauna ya fayyace masa damuwar 'yar uwarsa, amma yanzu dole sanin matsalar Basmah taga gari kunnuwansa, bubbuga kafad'arsa yayi sannan yamik'e yabar palourn yana fita ya tarar da Batool lak'e ajikin corridor sai zuba soyayyarsu sukeyi ita da dr Allah awaya. Harara ya 'balla mata sannan yawuce part d'in mom cike da damuwa afuskarsa, kai tsaye d'akin au Basmah yashiga ya taradda ita kwance tana kuka, jin tayi andafa kafad'arta tare da zaunawa gefen gadon, k'amshin turarensa ya tabbatar mata da cewa yayanta ne, hakan yasa tad'ago da sauri tafad'a jikinsa tanaci gaba da kukan,

"Nashiga uku yaya don Allah kad'aukeni daga gidan nan kada zuciya ta tunzurani na aikata abunda zai cuci rayuwata data 'yan uwana, ahalin yanzu kowane lokaci raunina da gazawata zasu bayyana batare da sanina ba, pls yaya..."

"Meye haka kike fad'a Basmah, shin ashe bazaki zamo cikin bayi masu yadda da qaddarar da Allah ya tsaro akansuba, bazaki so ki cinye wannan jarabawar da Allah yayi makiba acikin sauk'i sai kin fitini rayuwarki da yawa, haba Basmah kefa musulmace da kikayi ik'irarin zakiyi imani da kowace irin qaddara mai kyau da marar kyau, ki k'arfafa zuciyarki sosai nasan zaki iya, bana son ganin wannan kukan naki yana sakani jin nazamo mafi raunin yaya ga qannensa"

'Dago fuskarta tayi tasa hannuwa tana goge hawayen idanuwanta tace "kayi hak'uri yaya nadena kukan, nayi imani da wannan qaddarar da ubangijina ya jarabceni da ita, daga yau zan aro k'uwwa nasaka azuciyata, kuma zance gaba da addu'o'i da nafilfili kamar yanda nasaba akan Allah yasamu juriya da hak'urin da zancanye jarabawata, in sha Allah bazani koma zudda hawayena akan soyayyar yaya Mahmud pilot koda hakan na nufin zamowar ajalinane" rik'e fuskarta yayi yana kallonta yace

"Kinyi alk'awari?" Hawaye nazubo mata had'e da dariya duk cikin lokaci guda ta jinjina kai tace

"K'warai kuwa yaya kodon farincikinka" had'e goshinsa yayi da nata shima hawaye nazubo masa,

"Allah yayi maki musanya da wanda yafisa zama alkhairi sister, wlh ina matuk'ar jin tausayinki, so dafine kuma yanada zafi sosai, banida yanda zanyine domin ke da Billy duka 'YAN UWANA NE shiyasa kikaga nazubawa sarautar Allah idanuwa"

"Nasani yaya, nasani karka damu nima nabarwa Allah ya zartar da duk tsarin da shine mafi k'ololuwar alkhairi akanmu"

A b'angaren Batool kuwa Soyayya kam yau sun shata kamar ba gobe don sai da yaya Mahmud yagaji yaje ya anshi wayarsa yana jininin baisan mesuke fad'aba acikin waya fiye da mintuna arba'in, cike da kunya Batool tabasa hak'uri tare da barin wajen tana jin wani fresh air nashigarta ahankali. 'D'akinsa ya wuce ita kuma ta koma part d'in Ummi, zaune ta isko Mahmud pilot shikad'ai yana latsar wayarsa, murmushi tayimasa had'e da cewa

"Sannu da hutawa yaya" batare da yad'ago kansa ba yace

"Yawwa Batool sannu kema da soyewa" hannunta tamik'a takwashi kwalayen wayoyin daya siyo masu tare da ledar cosmetic d'in tanufi bedroom d'in Ummi, har takusan shigewa ya d'ago kansa yace

"Batool kituromun Bilkisu pls" kad'a kai kawai tayi sannan ta shige abunta, kayan tashiga nunnunawa su Ummi cikin jindad'i da yaba kyautar suka dinga sanya masa albarka suna masu yimasu addu'a da fatar Allah yabar masu zumuncinsu har abada. Kayan ta d'auka had'e da kallon Billy da shigowarta kenan takawowa su Umma fruitslad d'in data gama had'owa mai sanyi tace

"Twiny wai kije yaya Mahmud nakiranki" sannan tajuya zata fita, d'ago kai Billy tayi daga duk'en da take tace "twiny wanne daga cikinsu" murmushi tasakar mata had'e da cewa "pilot" kana tafice tana kaiwa bakin k'ofar fita tace masa "yaya tana zuwa"

"Thanks" yafad'a atak'aice ita kuma tawuce abunta.Billy kuwa saida tagyara kitchen d'in tsaf sannan tad'ebo had'in fruitslad d'in da tayi a bowl tanufo wajensa bakinta d'auke da sallama, can k'asan mak'oshi ya amsa sallamar yaci gaba da latsar wayarta batare daya kalli inda takeba, tafi minti biyu atsaye ita bata zaunaba kuma bata tafiba sannan yad'ago kansa yana fad'in "ai saiki zauna ko" saboda yanda ranta yab'aci tajawo kujera da k'arfi ta zauna had'e da d'aure fuska tana wasa da d'an yatsanta bayan ta ajiye bowl d'in da spoon agabansa, sanin halinta da yayi don yasan taji haushi yasa ya had'e hannuwansa yana fad'in

"Am sorry my noor" kauda kanta gefe tayi shikuma sai yarik'e kunnuwansa yana cewa

"Pls noori yaya is so sorry" juyowa tayi taturo baki cikin shagwab'a tace

"Shikenan, amma kada akoma domin zuciyar Billy bata son walak'anci"

"Angama ranki shidad'e baza'a sakeba, me kuma kika kawowa mijin naki?" Yafad'a yana bud'e bowl d'in data ajiye masa agabansa, d'an harararsa tayi kafin tace "abunda matar tasan mijin nata naso ne" ahankali yafara sha yana lumsar idanuwa saboda ba k'arya tabbas shi d'in masoyin fruitslad d'inne sosai, saida ya shanye tas sannan yature bowl d'in gefe yace

"Alhamdulillah matar gaskiya nagode, Allah yayi maki albarka"

"Amin yaya, ya shire shiren tafiya? Gobe kuma sai borno state ko?"

"Eh idan Allah ya yarda kuma ina zuwa da sayi d'aya su alhaji zasu zo nemamun aurenki da duk abunda yakamata, in the next 3month wannan had'in fruit d'in saidai kiyimunshi agidana"

"Hmm, kadaiji yaya nifa bazanyi aure ba har sai anyiwa yayuna don sune manya" d'aure fuska yayi had'e da k'walalo idanuwa awaje yace

"What? Ai baki isaba, idanma mafarki kikeyi kifarka don wlh bazan koma wajen aikiba saida matata" dariya tadinga yimasa tana fad'in "kai yaya wannan rawar k'afa kuma har ina gaskiya wannan tsarin beyi ba"

"Haka kikace" yafad'a cikin b'ata rai, da sauri tace "a'a yallab'ai wasa nakeyi" dariya yayi sannan ya d'auko wayar daya siyo mata ya saka mata layi had'e da mik'a mata sannan yace

"Ungo wannan Kiyi chaji sosai kuma don Allah inaso takasance tare dake akoda yaushe" kallonsa tayi cike da mamakin tsadar wayar daya mik'omata amatsayin tata, zatayi magana kenan yace

"Shiiii...bana son jin komai daga bakinki koda kuwa godiya ce" speechless tazama kafin tace

"Shikenan amma ayimun izinin bada tukuici idan an amince" "bana buk'atar tukuici matuk'ar bana harafi hud'u bane ko takwas"

"Shikenan kayiwa kanka, dama cewa zanyi ina k'aunarka amatsayin tukuicinka, kuma kagashi haruffa sha d'ayane amma ba matsala tunda kahutar dani" dariya yayi tare da cewa

"A haka ma ai nagode tunda anfad'a duk dako ba'a matsayin tukuici bane"



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Gaisuwar yau tamusammance zuwa gareku Auntynah da kuma takwarata *BILKN JML AND ZAINAB MUHAMMAD🌹* ina mai yimaku fatan alkhairin Allah yakai agareku a duk inda kuke bisa soyayya da k'aunarku ga wannan littafi na 'YAN UWANA NE, maganar gaskiya kud'in na dabanne kuma bazantab'a mantawa da kyawawan addu'o'inku agareni ba, ngd ngd ngd sosai, Allah ya albarkaci rayuwarki data dukkanin ahalinku kuma yasanya aljannah itace tabbataccen wajen zama agareku, I do really appreciate ur always care, LUVS U FILLAH_😘

💎Page_____64💎


To shikenan tunda haka kace "narok'i Allah daya k'aro maka tarin arzik'i mai yawa da kwanciyar hankali acikin dukkanin al'amurranka,

"Amin ya Allah matar" tashi yayi ya zagayo har inda take zaune yai neildown agabanta yana kallon cikin idanuwanta yace

"Bilkisu har ga Allah bana son intafi nabarki, gani nakeyi tamkar zaki bawa wani k'ofar da zai iya fuskantarki yace yana sonki, kuma idan hakan yafaru tabbas zan iya rasa raina, Bilkisu inajin sonki ako wane fitar lumfashina ba adadi, tayanda bazan iya cigaba da rayuwaba idan babushi azuciyata, dena sonki atare dani tamkar tsayawar lumfashina ne, kiyarda dani kuma ki amince mani kikula mani da kanki idan natafi, nabaki amanar ajiyar zuciyarki da ruhinki dkm gangar jikinki, don Allah kikula mani dasu har ranar da zandawo gareki" yak'arasa maganar idonsa cike tab da k'walla, gefen d'akin dasu Ummi ke ciki sannan tajuyo takalla da sauri tana fad'in "wai meye haka kakeyi yaya tafiyafa ba mutuwaba, kuma natabbata maki cewa duk duniya banida burin rayuwa da kowane d'a namiji amatsayin miji inba kaiba, to meye nayin wud'annan maganganu haka agabana ko baka yarda dani bane" girgiza mata kai yayi hawayen da suka cika masa idanuwa nak'ok'arin fitowa yace "Nayarda dake Bilkisu amma tsoro nakeji kada wanda yafini iya dubarar sace zuciya yayi ido dake yanemi raba soyayyarmu, wlh bazan iya jurar hakan ba ko kad'an" jitayi tamkar tarungumesa saboda yanda yabata tausayi, dama haka yake matuk'ar sonta da yawa shiyasa baya iya hurar b'acin ranta, tabbas tayarda shid'in masoyine na musamman kuma tayi alk'awarin rik'e masa kanta shikad'ai batare data bari ya jigata akan sonta ba, itama hawayenne suka zubo mata tana kallonsa cike da k'auna tace "ka kwantar da hankalinka ni d'in takace kuma mallakinka domin kaf aduniyarnan kai kad'aine Allah yayiwa baiwa da dubarun da zasu iya sace zuciyata, kasa aranka ni takace kuma kai nawane da yardar Allah, ko kamanta akullum ina fad'a maka cewa tare zamu rayu kuma tare zamu mutu kuma a k'ark'ashin inuwa d'aya"

Hannunsa yasa yagoge hawayen da suka zubo masa had'e da cewa "Dagaske kikeyi?" Saida tayi murmushi sannan ta d'aga masa kai had'e da cewa "sosai kuwa"

"Kinyi alk'awari?" Yafad'a yana nunata da d'an yatsa yana murmushi

"Tabbas insha Allah" tafad'a tana dariya hawaye kwance a fuskarta, zoben yaciro daga aljihunsa yabud'e 'ya jikkar da yake ciki ya ciro k'onk'on tare da bud'ewa yaciro zoben, d'ago kansa yayi yana kallon fuskarta yace "idan kin tabbatar da haka, to kikarb'i wannan zoben amatsayin shedar alk'awarin da mukayi tsakanin ni dake" had'e da mik'o mata zoben dake hannunsa, kallon zoben tayi dake walk'iya a hannunsa saboda hasken k'wan lantarkin daya bugesa tace

"What a nice...really luv it yayanah" hannunta tamik'a masa yasaka mata tana dariya, cike da farinciki yaturo zoben zuwa d'an yatsanta nakusa da k'arami da sauri tajuya hannun zoben yafad'a a tsakiyar tafin hannunta, d'auka tayi tasaka a yatsanta tana kallon hannun nata, sosai zoben yayi mata cicciccif kuma yama hannun nata kyau, d'ago kai tayi tana kallonsa had'e da d'an murza zoben ahankali tace

"Thank you yayanah it was so amazing and excited, luv you so much" tare da kissing zoben, rufe idanuwansa yayi yana murmushi tare da bubbuga saiti zuciyarsa yace "luv you uncountable my Noor"

"To ataimaka mun atashi kar Ummi tafito ta d'auka punishment ne nasa yaronta, kajamun rigima" dariya yayi sannan ya mik'e tare da jawo kujerar dake kusa gareta yajuyo da ita tana facing d'inta sannan yazauna. Sunjima suna firar bankwana da jimamin rabuwa da juna tamkar karsu rabu, haka itama Umma da Ummi firar sukeyi ta bankwana, d'aga kai Ummi tayi takalli agogo taga past 12:00 sannan taci gaba da firar amma hankalinta gaba d'aya nakan 'yarta hakan yasa tamik'e tanufi kitchen da zimmar d'auko ruwa a fridge, bayan ta d'auko takashe wutar kitchen sannan ta kuma kashe tafalon yarage saura tagefen dining area inda suke zaune sannan tashige d'akin, hakan ya ankarar da Billy abunda mahaifiyarta kenufi tamik'e da sauri tana cemasa

"Gudnigth yayanah my milkheart" d'aga mata hannu yayi shima yana fad'in

"Sweet dream nourii!"

Kai tsaye d'akinta tawuce don kunya bazata barta taje wajensu Ummi taba, tana shiga tayi arwala tayi sallar isha'i sannan tayi azkar d'in bacci takwanta, kwanciyarta tagyara tana kallon silin had'e da d'ago hannunta tana kallon zoben daya bata, kissing d'in zoben tayi tanajin wata irin zunzurutun k'aunar yayanta nabin dukkanin sassan jikinta izuwa yanzu tagama tabbatarwa kanta da zuciyarta itama bazata tab'a rayuwa idan babushi ba, juya kwancin nata tayi zuwa gefen hannunta nadama sannan tarufe idanuwanta ahankali tana tunano irin yanda yake nuna mata masifaffen son da yake yimata, da wannan tunanin tasamu bacci b'arawo yayi gaba da ita.

Bayan kamar minti biyar Ummi tamik'e saboda hankalinta baida natsuwa tanufi falon don ba tarbiyar mahmud pilot take tsoroba sharrin shaid'an daba ruwansa da tsakanin wa da k'anwa balle d'an uwa d'an uwa, ajiyar zuciya tayi ganin basu falon sannan tanufi d'akinta, globe d'in d'akin takunna ta hangota kwance akan gado lokacin bata dad'e da kwantawa ba, shigowa tayi tabud'e toilet tarufe sannan tasake tofe d'akin da addua takashe fitilar tarufe sannan takoma d'akinsu, murmushi Umma tayi don har ga Allah taji dad'in hakan da Ummi tayi kuma yasake tabbatar mata da tarbiyar data bawa 'yarta tare da alfaharin cewa itama zata tarbiyantar mata da nata jikokin idan Allah yanufa.

Da sassafe kowa yatashi da sanin komawarsu Umma yau don haka da sukayi sallar asuba babu wanda yakoma bacci, gaba d'aya dady umurni yayi masu dasu had'u part d'insa bayan kowa ya hallara dady yafara bud'e taron da addua sannan ya yimasu nasiha sosai akan girman zumunci kuma suyi koyi da k'anwarsa 'yar uwarsa dake biye dashi akoda yaushe don d'abbak'a zumuncinsu duk da cewa ba ita kad'aice 'yar uwarsa ba amma tarik'e sa hannu biyu. Yana kawowa nan yafashe da kuka tunawa da sauran 'yan uwansa da yayi kuma suna raye amma gaba sun gujesa bisa wani banzan dalili nasu amma ita tarik'esa hannu biyu, godiya yadinga yimata yana rok'on Allah yafarant zuciyarta kamar yanda ta faranta tasa, gaba d'aya yaran kallonsa sukeyi cike da mamaki jin cewa dadyn nasu nada wasu 'yan uwan bayan umma inbanda Ummi da mom da kuma umma da suka san da wannan matsalar tuntuni, ita kanta Umma kuka takeyi sosai tunawa da abubuwan da suka faru can baya bayan haihuwar yaya Mahmud wanda shine yazamo silar rabuwarsu da 'yan uwansu,daga k'arshe dady ya tsagaita kukansa sannan yakalli Mahmud yace

"7:00am tayi yakamata ace kun kama hanya saboda bana son tafiyar dare sai katashi ku hanzarta ko?" Godiya Umma itama tashiga yimasa akan alkhairin da yayi masu da kuma kyautar motar da yayiwa Mahmud pilot sannan tasanar dashi bayan sati d'aya idan sun koma iyayensa maza zasuzo zancen nema masa aurenki Bilkisu, yaso ya gardanta hakan saboda yafiso sai suma 'yan uwanta sun tsaida nasu mazan sai yahad'asu tare yayi masu aure amma don ya sanyata farinciki kamar yanda take sakashi yasa yayi murmushi had'e da cewa "Shikenan hafsatu ai kema 'yarkice duk yanda kikayi daidaine, ubangiji Allah yakaimu kuma ya sanya alkhairi" duk suka amsa da amin sannan aka watse taron,

kasancewar Umma tasanarda alhajinta cewa yayanta ya yima Mahmud kyautar mota yasa tunjiya yaturo drivernsa ta motar haya don yaja d'ayar motar da sukazo da ita, sunyi bankwana da kowa cikin so da k'auna sannan suka d'auki hanyar komawa borno cikin jimamin rabuwa da 'yan uwansu wanda Billy saida tashige d'aki tayi kukar rabuwa da milkheart d'inta.

Mom kuwa tunda taji anfara zancen batun turowa auren Bilkisu gabanta yafad'i ganin cewa ganata yaran nan har guda biyu agabanta babu mashinshini kasancewar bata san da zance soyayyar dr Ahmad da Batool keyiba, sai taji wata irin damuwa da bak'in ciki sun rufeta lokaci d'aya har zazzabi na neman saukar mata, yau dai gida yayi tsit, tsakanin Billy da yaya Mahmud anrasa wanda yafi jin kewar Mahmud pilot atattare dashi haka itama Ummi yini tayi sukutum da kewar ami niyar tata wato Umma, hatta Bilal da Bassam sunyi kewar junior sosai don bini bini sai kaji suna cewa junior kaza junior kaza.

Dady kuwa yini yayi ad'aki yana rafkar kuka domin ahalin yanzu bayaji zai iya k'arsa rayuwarsa batare da 'yan uwansaba ahankali cikin kuka yake fad'in "why? Sufa 'YAN UWANA NE!, meyasa suka zab'in haka atsakaninmu, meyasa zasu gujemu akan abunda yashafi rayuwata nikad'ai, tabbas ku 'YAN UWANA NE! kuma ina matuk'ar sonku, duk da kunbarni kunnesanta kanku dani amma ina bibiye da dukkanin alamurranku kuma zanci gaba da bibiyarku bazan tab'a rabuwa da kuba.

Yau kwanansu Umma uku da komawa kuma yaune dr. Ahmad yaci alwashin gabatar da kansa awajen dady don sun gama magana da Batool akan zaizo ya gaida dady kuma yagabatar da kansa kasancewar tkullum yana mak'ale da ita awaya don tuni yaya Mahmud ya turawa faraaha lambar Batool yace tatura masa don yadena damunsu.

Haka tab'angaren Billy kullum cikin waya take da Mahmud pilot suna raya soyayyarsu tare da ingantata, Basmah ma tuni ta dangana da soyayyar Mahmud pilot duk da har yanzu abun nacin zuciyarta amma ko kad'an bata bari kowa yasan halin da take ciki, hatta Batool da yaya Mahmud tadena bari sufahimci tana cikin damuwa ita kad'ai ke shanye abutta idanma ciwonne yatasar mata bata bari kowa yagane part d'in dady take zuwa acan gefen corridor dake can saman upstairs taci kukanta har tagaji sannan idan yalafa mata tadawo, tana k'ok'arin sakin jikinta dayin walwala kamar yanda tasaba.

Dr. Ahmad yasamu nasarar ganin dady kuma ya gabatar masa da kansa amatsayin wanda ke neman izinin zuwa wajen 'yarsa da sunan aure idan ya amince, sosai dady yayi farinciki kuma yatarbesa hannu biyu, yatambayiesa ko waye mahaifinsa kuma yabashi lbr a-z akansa batare daya b'oye masa ba daga k'arshe dady yabashi izinin cigaba da neman auren Batool kuma ya amince daya turo iyayensa don ga bayanin daya yimasa akan kowaye mahaifinsa yasanshi kuma yasan mutumen kirkin shiyasa yayi saurin amince masa. Dr mahmud yaji dad'i sosai da karamci irin na dady don kasa hak'uri yayi har sai yakoma gida yaba mamy labari yakirata awaya lokacin daya baro wajen dady yana labarta masa irin karb'uwar daya samu daga wajen mahaifin Batool, taji dad'i sosai itama harda 'yan k'wallanta a idanuwa tanata yiwa Allah godiya dayasa surikin d'an nata bai zamo d'aya daga cikin masu kud'in dake walak'anta talaka bane kamar alhaji Tukur.

Bayan yagama waya da ita yakira Batool yasanar da ita yanda sukayi da dady cikin farinciki tana tayi masa dariya yace tafito gashi aharaba zaiwuce. Kaisa tafarayi yagaida Ummi kafin yawuce sannan bayan sunfito tace yazo suje yagaisa da mom...



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____65💎


A parlour tayi masa mazaunin sannan tawuce bedroom ta iske mom kwance duk abun duniya yasha mata kai, babu abunda yanzu ya dameta kuma ya tsaya mata arai irin yanda ace wai Bilkisu k'anwar k'anwar 'ya'yanta ake zancen tsayarwa da miji bayan ansan yayyunta nanan zaune kuma su ba'a tsayar masu da mijin auren ba, abakin k'ofar d'akin tatsaya had'e da cewa

"Mom" sau kusan takira

Please Login or Register in order to submit comment