Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'ololuwar cutuwa agareni wacce jureta abune mai wahala da nake tunanin bazai yuyu ba don bana buk'atar hakan amma kafin na yanke hukunci ina so inji meye ra'ayin ke hajia Aisha da kuma 'ya'yanah akai" shiru yayi na kusan minti biyu kafin yaci gaba da cewa

"Hajia Hussaina ta nemi da araba wajen zama saboda bazata iya jurewa cin fuska da munafurcin da ake yimata agidan nan ba don haka me kun kace akan wannan buk'ata tata"

"Alhaji indai ta b'angare nane wlh banida ja duk hukuncin daka qudurta aranka zan bishi matuk'ar zai sama maka farin ciki" tana rufe baki basmah tace

"Bawani mudai munyarda araba wurin zama saboda musamu natsuwa muda mom d'in mu, ana takura mana a gidan nan don haka mu bana buk'atar zama dasu"

"Haba yayya Basmah kada kice haka mufa 'yan uwan junane, kar mubari son zuciya da kuma sharrin shaid'an ya b'ata mana zumunci"

"Dady fita batun Billy wlh Allah mudai muna amince, tsabar munafuncine ya hana sununa amincewarsu suma" cewar Batool dake zaune kusa da small mom tana taunar cingam.

Tunda ake zancen nan Mahmud baice komai ba sai da yaji fitsarar k'annen tasa na nema ta wuce gona da iri, cikin damuwa yace

"Dady ni kwata kwata bana goyon bayan wannan shawarar domin hanyace ta wargaza zumuncinmu, yakamata ace mom tafad'i abubuwan da akeyi agidan nan da bataso sai anemi hanyar gyarasu bawani ace lokaci d'aya araba wajen za.."

Kukan mom ne da yaji ya hanasa k'arasa maganar sa tana cewa

"Shikenan Aisha kin cuceni, Allah ya isa tsakanina dake tunda kika juyamun k'wak'walwar yaro, alhaji dubi yanda yaron nan kejuyawa muradina baya saboda yaci gaba da ganina cikin bak'in ciki da b'acin rai, yazab'i wacce batasan zafin saba akaina dama ni nasan bazaka tab'a canzawa ba matuk'ar muna wuri d'aya da wannan munafukar" tanuna Ummi dake zaune tana kallon ikon Allah, daga yaro yafad'i gaskiya shikenan sai abu ya juye akanta, a hankali tace "Allah ya sawak'e"

Cikin zafin rai dady yace

"Rufemun baki kafin na sab'a maki, wannan wane irin abun kunyane kikeyi agaban 'ya'yanki, kina jifar 'yar uwarki da munanan kalamai donki cimata zarafi" ai kamar jira takeyi tafara zuba masu balbalin bala'i wanda hakan yasa Mahmud ya sallami k'annensa daga d'akin shi kuma yadawo yana lallashin dad d'insa daya dena biyewa mom, kallon Ummi dady yayi had'e da yimata umurnin itama ta tafiyarta ya sallameta, ta gefen mom tabi zata wuce ta fizgota da k'arfi


"Munafuka wlh babu inda zakoje har sai ankai k'arshen matsalar nan, bana buk'atar zama dake don haka dolene murabu" murmushin takaici Ummi ta saki tare da kallon ta tun daga sama har k'asa

"Hajia Hussaina ki tabbata kinyi na farko kuma kinyi na k'arshe, kada ki kuskura hannunki ya sake ya k'ara tab'a jikina, zaginki, k'azafin ki da sauran miyagun kalamanki basukai ga baki matsayin da zan tanka maki ba amma ranar da duk kuskurenki ya aikeki da sake tab'a jikina, ranar zaki samu matsayi aguna da zaisa in canza maki kama" hannu mom tad'aga da niyar marin Ummi dady yayi saurin rik'eta tana d'ago fuska ya d'auketa mari, zai mayar mata da na biyu Mahmud ya rik'e masa hannu hawaye na zubowa daga cikin idanuwansa

"Kayi hak'uri dady, uwa nada matuk'ar muhimmancin da akwai zafi a daketa agaban 'ya'yanta, dady ba momy kad'ai ba ni kaina ina buk'atar araba wajen zama saboda farincikin mahaifiyata, Ummi kifahimci buk'atar mom idan har kin duba musulunci ma ya amince da haka sai idan lalurar rashin wani zaman ta gitta kad'ai ya bada damar azauna waje d'aya"

"Mahmud wlh ni banida matsala tunda nima aurena akeyi duk hukuncin da dadynka ya yanke daidai ne, ni bance abijirewa buk'atar mahaifiyar kaba!" Jirine ya d'ibi dady dake tsaye Mahmud yayi saurin zaunar dashi akan kujera, ita kuwa mom tunda tasha mari bata sake cewa k'anzil ba.

"Shikenan hajia Hussaina kinyi nasarar raba mani gida, kije na amince kizab'i d'aya daga cikin gidajena ki koma, Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" wasu zafafan hawayene suka zubo a kumatun Mahmud don har ga Allah baiji dad'in rabasa da 'yan uwansa da mom tayi ba, kawae ya zab'i hakane don samun farincikin iyayensa ko ba komai shi kansa dady yasamu farin ciki.

Nan kowanensu yafita yanajin wani irin sabon yanayi acikin zuciyarsa, daidai inda kowacensu zata nufi part d'inta sukaci karo da Batool itada Billy suna fad'a ga Bassam can agefe ya haye Bilal yanata faman dukansa shi kuma yana kuka Basmah kuwa ta koma gefe sai fad'in take

"Yawwa Batool sauya mata kama, banza dubi yanda Bassam ke lallasa Bilal amma ke kin tsaya wasa, wlh kika bari billy ta jibgeki kin zama samna. Tana rufe baki Allah yaba Billy sa'a ta d'aga Batool sama ta nane (mayar) k'asa.

Da gudu mom dake farincikin cin zalinsu Bilal da 'ya'yanta keyi ta nufi wurin yayin da itama Ummi ta nufi inda Bassam ke dukar mata yaro don kai masa d'auki.













Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____12πŸ’Ž


Saida ta d'auke Bassam dake saman jikinsa yana duka kafin ta d'agosa yana kuka, lallashin tashiga yi had'e da kakka b'e masa jiki, a hankali tad'ago kanta tana kallon Bassam dake faman nishi sai kace wanda yayi wasan tsere,

"Bassam don me zaka yiwa d'an uwanka wannan duka, baka ganin kafishi girma, ko kana son kaga yaji ciwo ne, haba! Kudinga tausayin da k'asa gareku don Allah"

Hannunsa Basmah tazo taja tana qunquni k'asa k'asa ita marar kunya, girgiza kai Ummi tayi tare da cewa

"Allah ya shirya manaku" hannu tasa ta d'auki Bilal dake kuka sannan tajuyo da niyar barin wajen, juyowar da zatayi taji Billy tasaki wata irin muguwar k'arar data sa both ya Mahmud da dady fitowa aguje saboda tashin hankali, kwance suka hango Billy a some kanta na zubar da jini a sanadiyar hankad'eta gefe da mom tayi lokacin da ta iskota bisa jikin Batool tana duka shine tafad'a akan d'aya daga cikin kujerun dake harabar gidan da yake irin na stones ne sai kanta ya bugu, speechless mom tazama takasa karasawa wajen wasu zafafan hawaye na zubo mata a idanu yayinda Mahmud ya d'auki Billy idanunsa ko gani basayi tsabar takaici shima hawayen ne ke zubar masa, bakin gate ya nufa da nufin samun abun hawa sai ga dady yafito da mota suka nufi asibiti, sosai jini ya zuba akan Billy don haka aka nemi a k'ara mata jini, nan take Mahmud yaje aka aunasa jininsu yazo d'aya, dafarko dady yaso a ibi jininsa kasan cewar Mahmud bai dad'e da tashi ciwo ba amma shi yak'i amincewa da haka, sai da likitoci suka tabbatarwa da dady babu wata matsala don and'ebi jininsa tunda ya samu sauk'i sannan hankalinsa ya kwanta, dady na ganin komai ya daidaita a asibiti ya d'auki motarsa ya kama hanyar gida, yana isa ko parking mai kyau bai yiba ya nufi part d'in mom, yana shiga ya taradda ita tana kallon wani season film (king of the heart) hankalinta kwance tamkar bata aikata komai ba, yaran tane kad'ai suka d'an shiga damuwar abun da yafaru don dukkanin su zaune suke kamar ruwa ya cisu, cikin kakkausar muryar da mom batasan dady da ita ba taji yace

"Enough hajia Hussaina, nace enough is enough, basai kin kashe mani 'yaba zan gane bakya son jinina, ba sai kin nuna cewa Bilkisu ba 'yarki bace zan gane bakya da asara idan tamutu, Allah yasani ina matuk'ar son 'ya'yana gabaki d'ayan su, bazan iya jurewa cutuwar d'aya daga cikin suba matuk'ar ina raye, nayita k'ok'arin tausar zuciyata wajen ganin banyi abunda zaisa yaranki suji ba dad'i aransu amma ke kin kasa fahimtar haka har saida kika kaini bango, saboda haka kitafi gidan ku bana buk'atar ganin ki agidan nan, kin fita raina tun lokacin da ida nuwana sukaga yanda kika illata mani yarinya, kika raba tsakanin d'aya da biyu don haka kibar gidan nan kafin indawo, sannan karki kuskura kibar gidan nan da yaro ko d'aya"

"Kasha k'arya, wlh tunda kakoreni cikin gidanka to kamar ka kori yaran kane, ai 'ya'ya nane ba ubanda ya haifa mani su don haka ba ubanda ya isa ya hanani tafiya da abuna da kuma ke cewa naraba d'aya biyu to ina naga d'ayan balle narabata biyu, babu wanda baisan cewa Aisha bata haihuwa ba , amma tsabar muna furci tunda taga inayi shine taje ta samo wud'ancan shegun aka k'ak'a ba maka, da yake kai kuma anriga an wanke an baka ka tara kai ka amsa shine kake nema ka mai dasu d'aya da 'ya'yanka to hakan bazata sab'uba wallahi"

"Tir Hussaina! tir da halinki, karki kuskura kisake sheganta mani yara, maza ki fice mun daga gida Allah ya shiryeki"

"Mtsss aikin banza, ance..." Kafin ta rufe baki dady ya shak'e mata wuya had'e da matseta ajikin bango idanunsa sunyi jawur tamkar garwashi,

"Ki maimata abunda kike son fad'a in kin cika, am tired of ur stupidity" da gudu yaran suka fito d'akunansu jin kakarin da mom d'insu keyi suna bawa dady hak'uri amma yak'i sakinta, ganin haka yasa Basmah tarik'e k'afafunsa tana kuka,


"Don Allah dady kayi hak'uri, ka saketa dady zafa ta mutu" sai da yaji gaba d'ayansu sun fashe da kuka sannan ya jefar da mom gefe yabar d'akin ransa a b'ace yana mai da na sanin aurenta, da sauri suka nufi kanta Batool ta d'ebo ruwa suka bata, dak'yar take shan ruwan sannan ta koma takwanta,

"Mom kitashi kitafi, wlh bakiga yanda fuskar dady tayi ba kada ya dawo ya iskoki, kitafi mu zamu biyoki daga baya" Basmah ce kefad'ar haka cikin kuka, saida mom tad'an dawo hayyacinta sannan tafara had'a kayanta tana jin wutar tsanar Aisha tare da yaranta na dad'a ruruwa acikin zuciyarta.


Ummi kuwa tunda abun yafaru tashige d'aki tana kuka, ko kad'an bata zaci tsanar da mom keyi mata ba takai ga har ta iya cutar mata da yara ta hanyar zubar masu da jini, ga Bilal a gefenta shima sai faman kuka yakeyi wai

"Ummi ina aunty Billy, meya faru da itane?, Ummi akaini wajen ta" Jawosa tayi ajikinta ta rungume hawayen ta na d'iga akan fuskarsa,

"Kayi hak'uri, auntynka na asibiti ba tada lafiya"

"Me yasameta Ummi? Itama 'YAN UWA NA NE suka yimata duka? Ummi ni basu jimin ciwo ba, sune suka jimata ko kuma mom ce? Ummi me yasa basa son mune?"

"Ya isa haka! nafad'a maka cewa ba tada lafiya ne, kayi hak'uri yanzu zamuje wajen ta kaji"

Mik'ewa Ummi tayi ta d'auko mayafinta, hannun Bilal ta rik'e suka nufi kofar fita saiga dady ya shigo, ganin yanayin da yake ciki yasa ta koma ta cire mayafinta, fridge ta bud'e ta d'auko ruwa masu sanyi a gora ta tsiyaya masa ga cup ta mik'a masa, kasa karb'a yayi yana kallon yanda idanunta suka rine saboda kukan da tayi, Bilal ta tura bedroom sannan takai ruwan abakinsa, a hankali yake shan ruwan yana kallon idanuwanta dake k'ok'arin sake kawo ruwa, bayan ta janye ruwan abakinsa, cikin sanyin murya yace


"Kiyi hak'uri rabba'atul bai..." Kafin ya iyar ta rufe masa baki,

"Ba komai dama Allah ya tsaro yau jinin Bilkisu sai ya fita saboda haka muyi hak'uri mu rungumi wannan qaddara Allah ya tsare gaba, saidai naji ba dad'i naji zafi sosai araina" rungumeta yayi tana kuka yana cigaba da bata hak'uri

"Nayi kuskure sosai arayuwata rabba'atul baiti! Wannan duk ni najawo dana kasa tantance wace irin mata yakamata in d'auko gidana gashi yanzu..."


"Shhh...kadena fad'ar haka, ya jikin ita Bilkisu?"

"Da sauk'i amma tarasa jini saida aka d'ibi na yayanta aka saka mata, yanzu haka bacci takeyi"

"Haba alhaji! Saboda me za'a d'ibar masa jini bacin kasan bashida lpy so kakeyi ayi biyu babu ne?" Muryar Mahmud tajiyo daga bakin k'ofa yana fad'in

"Saboda ni yayan tane kuma au 'YAN UWA NA NE!...."


















Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____13πŸ’Ž


Da sauri dady ya nufi inda yake

"My son ya akayi kabaro asibitin? Bilkisun ta farfad'o ne?"

"A'a dady har yanzu, bacci nabaro tanayi shine nadawo in karb'i kayayyakin da za'a iya buk'ata don gaskiya dr kamal yace sai ta kwana biyu anga yada jikin nata yayi kafin su bata sallama saboda da alamu tana d'an jin jiki"

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, Allah yasa bawani abunne ya faru da ita ba" Ummi ce tafad'i haka tana mai dafe hannun kujerar dake gefenta saboda jirin da taji yana shirin d'ibarta"

"Ki kwantar da hankalinki Ummi babu abunda zai sami lil sis in sha Allah, suna so ne sai an yimata scanning d'in k'wak'walwar ta anga buguwar da tayi bata haifar mata da wata matsala ba shiyasa zasu d'an rik'emu na kwana biyu"

"Shi kenan kaje ka watsa ruwa kafin nan ta shish shirya kayan"

"A'a dady babu buk'atar hakan yanzu nasan gab take data tashi, Ummi kije ki had'a mani kayan bari inje indawo"

"To Babanah sannu kaji, Allah yayi maka albarka"

"Amin Ummi"

Nan yafita yabar dady zaune akan kujera ya dafe da kansa da alamu har yanzu yana cikin b'acin ran abunda ya faru.

Part d'in mom ya nufa yaci karo dasu Basmah abakin k'ofa d'auke da akwatuna guda biyu biye a bayan mom, wani irin kallo mai d'auke da alamar tambaya ya watsa masu da sauri suka ja baya tare da sakin akwatunan, kai mom ta d'ago cikin b'acin rai tana kallonsa tun daga sama har k'asa

"Dallah matsa kabani wuri in wuce, lpy zaka shigo ka tsoratamun yara haka"

"Yi hak'uri mom amma ina zaki jene?" Ba tare data kallesa ba tace

"Kaje katambayi mahaifinka" sannan taci gaba da tafiyarta, da sauri yasha gabanta

"Don Allah karki tafi mom, ya kike so muyi idan kin tafi, ko kina so ne murasa gatar da muke da ita agareki, ko kad'an bazamu juri rashin kiba, don Allah mom kiyi hak'uri" cigaba da tafiyarta tayi tana fad'in

"Ai sai kaje ita waccan daka fifita akaina ta maye maka gurbina, tabaka gatar da duk kake buk'ata, ammafa ina so kasani yazama dole ka kula da k'annenka kuma kayi masu duk abunda suke so tamkar inanan" cikin muryar kuka yake binta yana cewa

"Kiyi hakuri mom, babu wanda zai iya bamu gatar da takai taki, kefa uwace ita kuma uwa tanada matuk'ar karamci da tausayawa ga 'ya'yanta, inada tabbaci akan babu wacce takaiki ko tafiki awurinmu, don..." Da sauri ta katsesa had'e da d'aga masa hannu

"Ya isa haka..ka kula da 'yan uwanka shine kad'ai abunda zan fad'a maka idan kuma suma kazab'i wasu 'yan uwan akansu basai kayi hakan ba" saurin tarar gabanta ya sakeyi yana hawaye tare da rik'o Bassam dake gefensa

"Mom ki dubesa ki gani yana matuk'ar buk'atar ki a kusa da shi ko ba don muba kiyi hak'uri ki koma don sa, bana son kina fad'in wud'annan maganganun domin babu wanda zai iya maye mana gurbinki aduniya" sosai mom kejin tausayinsa azuciyarta, har ga Allah tana matuk'ar son sa fiye da sauran 'ya'yanta shiyasa duk lokacin da taga hankalinsa ya karkata a wajen Ummi da yaranta takeji tamkar anrabata dashi kallonsa tayi cike da kulawa

"My son!, ai shi mahaifinku bai san da haka ba saboda haka kamar yanda ya buk'aci in tafi in bar masa gidansa, to zan tafi in yaso ita wacce ya zab'a yasa tamaye maku gurbina" Runtse idanuwansa yayi, sauran hawayen dake lak'e a idanuwansa suna bin layi a fuskarsa, duk daya san cewa komai yafaru laifin mom d'in sane hakan bai hanasa jin d'aci acikin zuciyar saba, sosai yakejin ba dad'i akan hukuncin da mahaifin nasa yayi, hannayensa yasa ya goge hawayen dake kwance akan fuskarsa tare da kallon mom, kafin yace wani abun yaji muryar batool data hango dady na fitowa daga part d'in Ummi shida ita nacewa

"Ya..ya. Yaya don Allah kabar mom ta tafi ga dady can yafito karya sameta anan, zai iya yimata fiye da abunda yayi mata d'azun" akwatunan hannuwansu ya karb'a yana fad'in

"Shikenan maza ku shiga daga ciki, mom zo mutafi ko?" Gaba d'ayansu suka rungumeta yayinda itako hankalinta nakan dady da Ummi dake tsaye wajen motar da dady ke hawa aranta tana ayyana irin ja'izar (musibar) da zata saka Ummi da duk wani nata aciki, muryar Mahmud ta katse mata tunani dataji yana fad'in "mom mutafi"

Bud'e mata d'aya daga cikin motocin da key d'inta ke hannunsa yayi ta shiga sannan ya zuba akwatunan a bayan boot, wajen su dady ya nufa batare da ya kalli inda yake ba yace

"Ummi don Allah kuwuce keda dady ya ajiyeki asibitin akwai inda zanje yanzun amma idan nadawo zan sameku acan"

"Shikenan Babanah amma ina mom d'inka zata jene?" Murmushin karfin hali yayi yana kallon yanda dady ya juya bayan sa jin abunda Ummi tafad'a, tabbas yau mom takaisa bango, cikin sanyin murya yace

"Kayi hak'uri" sannan ya nufi motar da mom keciki ya tayar suka fita"

A gaban dady Ummi takoma tana kallon fuskarsa, hannunta tasa ta d'ago fuskar had'e da cewa

"Dadyn yara meka aikata" batare da amsa mata ba ya bud'e gaban gambun motarsa yace

"Shiga muje"

"Ka am samun tambayata mana, ashe bazamu kasan ce masu yadda da k'addara ba, Allah yariga daya tsaro hakan tafaru don me zakayi hakan, kenan idan nima da nake mahaifiyarta tsotsayi yasa hakan tafaru sai kace sai ka hukun tani"

"Ba haka bane, ki kwantar da hankalinki kinsan kowaye ni, bazanyi abunda ba daidai ba, kawai kishiga mota kinji rabba'atul bait?" ya k'arasa maganar yana k'ok'arin dafa kafad'arta, cikin rashin jin dad'i ta d'aga masa hannu.

"Shikenan ya isa, amma kadubi yanayin da Babanah ya shiga, ashe bai cancanci yasamu farinciki daga gareka ba, ita uwa fa uwa ce duk yanda take d'anta bazai tab'a jurewa ganin ta cikin b'acin rai ba, don Allah kasake tunani"

"Rabba'atul bait kenan! Ai kema uwace ya akeyi kike jurewa damuwar da akae saka yaranki dake kanki aciki, ya kamata ak'alla ko sau d'ayane innuna mata kuskuren da take aikatawa, ina so mugudu tare kuma mutsira tare don haka dole tasan tayi kuskure beside wlh ba abunda ya faru akan Bilkisu yasa nace ta tafi ba, ta matuk'ar yin gangancine cikin kalaman da tayi mani wannan dalilin yasa nayi mata wannan hukunci" jin yanda yayi rantsuwa yasa jikinta yayi sanyi, tashiga cikin motar had'e da cewa

"Allah ya sawak'e"

A b'angaren mom kuwa ta madibi Mahmud ke kallonta kafin yace

"Mom ina zan kaiki?"

"Gidan mahaifina mana"

"A'a mom kituna koma da daraja irin ta papi, anya kina ganin zuwanki bazai tab'a masa kima ba, yakamata ace izuwa yanzu kinfitar da duk wani abu da kikeji aranki gameda Ummi, yanzu meye dad'in wannan abu da yafaru tsakaninki da dady agaban yara? Abunda tun kuna da k'uruciya bai tab'a faruwa ba sai yanzu da kuka manyanta"

"Tabbas kuma wannan abun ba abunda ya k'ara mani illa tsana da k'iyayyar matar ubanka, saboda adalilinta komai ya faru, wlh wlh matuk'ar inada rayuwa saina salwantar da rayuwar Aisha zuriarta" da k'arfi ya taka burki yana fad'in

"Wa'iya zubillahi meye haka kike fad'a mom?"







Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____14πŸ’Ž


Wani irin sarawa yaji kansa yayi saboda munin maganar da yaji mom d'insa tayi, dafe kan nasa yai na kusan minti biyar kafin can muryar ta dake faman masifa tadawo dashi duniyar tunanin daya shiga.

"Nifa nagaji da wannan zaman motar in zaka kaini inda nafad'a maka ka kaini idan kuma ba zakaje ba sai infita in hau napep, kabi duk kawani b'ata rai sai kace karasa wani naka"

"Mom kiji tsoron Allah kidena fad'an mugayen maganganu akan Ummi, wlh Ummi mutuniyar kirki ce batada wata mummunar manufa akanki"

"To ubana yimun wa'azi!, bari kaji tunkan ahaifeka nake zaune da ita, shin kasan ko saunawa ta salwantar mani da 'ya'ya?, don haka in kasake shiga maganganu na sai ranka ya b'aci"

"Ya salam! Mom duk duniya fa idan tataru bazata iya cutar dakai komai ba sai abunda Allah ya nufa akanka, ina da tabbaci akan Ummi bazata iya salwantar da yaranki ba Allah ne yayi cewa su ba rayayyu bane kuma wannan bazai zamo hujja agareki ba kice zaki salwantar da tata rayuwarta data zuriarta, yin hakan kuskure ne agareki" tsananin b'acin ran abunda yake fad'a yasa ta fita cikin motar had'e da bugo gambun motar da k'arfi, napep tafara k'ok'arin tara tana sabbatu

"Ya zama dole in d'au mataki akanki Aisha, yama za'ayi ace d'ana dana haifa ke k'ok'arin juyamun tunani akanki, inaaa doleni kisan cewa kinyi k'ok'arin shiga gonata" da sauri ya qaraso wajen cikin girmamawa yace

"Kiyi hak'uri mom, idan bakyaso in koma magana shikenan nayi shiru amma kiyi hak'uri ki koma cikin mota lokaci na qurewa" sai da yayi ta mata magiya kafin ya samu ta koma cikin motar tana huci kamar damisa.

'Daya daga cikin gidajen dady dake unguwar igala ya kaita, gida ne mai matuk'ar kyau da tsaruwa, kallon gidan mom tayi sannan ta maida kallonta ga Mahmud dake k'ok'arin bud'e marfin motar ya fita

"Kai a ina ne nan ka kawoni"

"Gidan dady ne daya gama ginawa las two month ago"

"To sai akayi me?"

"Eh to, dama na kawoki nanne kizauna kafin dady ya sauko daga fushin da yayi"

"Kutumar ubancan! Sai aka cemaka ni banida gidan iyaye, wlh Mahmud kashiga taitayinka"

"Don Allah mom kirufa mana asiri kizauna warki anan, nasan yanda dady yake da sanyin rai bazai wuce kwana d'aya ko biyu ba zai nemi ki koma, kinga daga nan ma sai ki dawo warki nan gaba d'aya tunda dama kin buk'aci araba maku gida ke da Ummi"

"Kaji na rantse maka bazan zauna a wannan gidan ba, wan can gidan dai nake da buk'ata tunda yafi girma kuma ni nake da 'ya'ya masu yawa, idan ma zaka kaini gidan ubana ka kaini don yafi maka"

"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, wannan wace irin sabuwar rigimar ce kike shirin d'au kowa mom?, kefa kika nemi araba maku gida ba zaki zauna da ita ba, to taya za'ayi kuma kice ita zata fita tabar maki gidan, don Allah mom kicire son kai da yawa"

"Aikin banza, dalla malam ni wuce muje, bazan zauna anan d'in ba"

Shiru yayi kafin ya tayar da motar cikin b'acin rai, da gudu yabar wajen yanajin tamkar ya kurma ihu,

"Eyyeee.. Lallai ka girma da yawa Mahmud, ai sai kayi maza ka kasheni tunda na fad'i son raina" ba tare daya kalli mom d'in ta saba ya rage gudun da yakeyi har suka isa gidan papi wato mahaifin mom.

Tunda suka fita ba wanda ya cewa wani k'anzil, murmushi dady yayi had'e da kallon Ummi data juyar da kanta gefen glass, hannunsa ya d'ora akan nata dake saman cinyarta yana d'an matsawa ahankali, juyowa tayi tana kallon fuskarsa dake fitar da wani annuri saboda murmushin da yakeyi, a hankali ta lumshe idanuwanta, juyar da kanta tasakeyi tana kallon yanda motoci ke wucewa d'aya bayan d'aya, a hankali tafara motsa bakinta lokacin da taji ya sake rumk'e mata hannu sosai

"Maganar gaskiya dadyn yara inajin ba dad'i araina, bana son ganin Babanah a yanayin da na ganesa hakan na matuk'ar tab'a mani zuciya sosai"

A daidai nan dady ya shigo da kan motarsa cikin asibitin, sai da ya daidai ta tsayuwar motarsa sannan ya kalli Ummi

"Rabba'atul bait mun iso" juyowa tayi fuskarta ba walwala

"Wlh bana jin dad'in wannan shurun naka, kanaji nake magana ka shareni"

"To ya kike so nace?, Kiyi hak'uri zamuyi magana anjima kinji ko?" Gad'a masa kai tayi sannan ta bud'e marfin gambun motar tafito, aminity ward ya nufa tana biye dashi har suka iso room 5 in da aka kwantar da Bilkisu... Kwance Ummi ta hango ta bisa gadon jinyar marasa lafiya har lokacin bacci takeyi hankali kwance duk da da zaran ka kalleta zaka gano tana jin jiki sosai,

Da gudu Bilal dake rik'e a hannun ummi ya nufi gadon, Aunty Billy, Aunty Billy kitashi, Aunty Billy me yasa mekine, dady ne ya rik'o hannunsa dake neman ya rik'o hannun Bilkisu,

"Zo nan autana, Auntyn ka bata lpy ne, kayi mata addua kaji" gyad'a kansa yayi had'e da cewa

"Allah yaba Aunty Billy lpy dady, kullum abunda take cemun shine

Please Login or Register in order to submit comment