Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigowa makarantar nan mutum na bibiyata ya kasa k'yaleni"

"To yazakiyi!? shifa babban malamine, narok'eki don Allah da kitsaya ki sauraresa, bari inje canteen injiraki" husnah tawuce tana waigenta.

Ganin ta tsaya ba tare data motsa daga inda takeba yasa malam jika yafito cikin motar, mutumne mai matuk'ar kamala a idanuwa duk dako d'alibai nayi masa kallon mugu marar mutunci, kallonta yayi tun daga sama har k'asa kafin yace

"Bilkisu Bashar maifulawa ko?" D'ago kanta tayi itama ta kallesa kamar yanda yayi mata kafin tace

"Yes my name"

"Kin burgeni gaskiya, Ina son mace marar tsoro"

"Ni kuma ko kad'an baka yimunba don natsani namiji mai naci"

"Da gaske?"

"Da dawasa?" Murmushi yayi don shikam gaba d'aya son yarinyar yakeyi da gaske kuma a shirye yake yayi komai akanta

"Bilkisu, sunana alhaji lawan amma amfi kirana da malam jika, ni malamine anan makarantar, bana d'agawa kowane d'alibi dake wasa da karatunsa, kuma Ina quntatawa d'aliban da duk suke nuna su wata tsiyane acikin wannan makarantar, wannan dalilinne yasa sukayi mani lak'ani da mugu kuma macuci, inada mata d'aya da yara uku, tun ranar da kikazo makarantar nan naji Ina sonki kuma nayaba da hankalinki, sosai nayi sha'awar aurenki a matsayin matata tabiyu idan kin amince nayi alk'awarin zan kula dake har iya k'arshen rayuwata, wannan dalilin kawai yasa nake bibiyarki amma kikak'i saurarona"

"Kayi hak'uri, nafahimceka kuma nagode da soyayyar ka, amma zuciyata bata muradin wani atare da ita, tana buk'atar hutu sosai don haka kayi hak'uri" tana gama fad'ar haka tarab'a ta gefensa tawuce abunta.

Yajima wajen atsaye cike da mamakinta kafin yace "Hmm! Muje zuwa in sha Allah sai na mallake ki amatsayin matata"...






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Gaisuwa tare da fatar alkhairi agareku *Nana Hauwa'u, Aisha abubakar* and also once agains to you *Jaanatusanikaka* a gaskiya inajin dad'in yanda kuke comment littafinnan cikin fahimta tare da fad'in ra'ayoyinku akai abun nak'ara mani k'warin guiwa sosai especially you jaanatu sai nakeji tamakar debating ne mukeyi akan abu d'aya da ke kike supporting ni kuma nake opposing, nakanji nishad'i sosai akan hakan, ngd sosai ina fatar Allah yakai amincinsa agareku aduk inda kuke kuma yabarmu tare๐Ÿค๐Ÿป_

๐Ÿ’ŽPage_____95๐Ÿ’Ž


Gaba d'aya wunin ranar yini Billy tayi ranta ab'ace, koda suka koma hostel haka zainab tasata agaba tana tambayarta ko lafiya taga gaba d'aya yau bata cikin walwala,

"Babu komai 'yar uwa am just borring da wancan malamin kenema ya takurawa rayuwata, yasani tunowa da memories d'in da nake neman shafewa arayuwata?"

"Wa kenan 'yar uwa?" Zainab tafad'a tana k'ok'arin d'ora tukunyarta saman d'an k'aramin gas d'in dake can gefen d'akin nasu, tsaki Billy tayi kafin tace

"Wa kuwa Inba malam jika ba, wai harda wani yana son in zama matarsa ta biyu, kijifa!, Ashe yana da mata yake zaman b'ata lokacinsa wajen bibiyata instead of yaje ya bata kulawa" dariya zainab tayi had'e da cewa

"Maza kenan, ai indai sune sunfi da haka, kedai kawai kiyi addu'a kuma kiyi abunda yakawoki dt's all"

Tsaye take ta rakosa abakin bakin mota tana hawaye, kallonta yayi bayan yabud'e motar ya shiga had'e da cewa

"Basmah don Allah kidena kukan nan haka!, Bana son kina shiga damuwa ko kad'an, pls badon niba ko don albarkacin abunda ke cikinnan naki kiyi hak'uri, in kin lura na shanye hutun dana d'auka wajen aiki amma saboda rashin lafiyarki na sake komawa na d'auki excuse wajen kuma aka bani, yau gashi almost one week fa kenan da k'arewarsa ban koma ba, ko kinfiso akoreni indawo gida in zauna" Saida tagoge hawayen idonta sannan tace

"No..no at all"

"Yawwa to kokefa, kinga kiyi zamanki wajen Ummah nasan zata kula dake fiyema da yanda zanyi kinji"

"Shikenan yaya, Allah yatsare hanya kuma ya saukeka lpy, nida little d'inka zamuyi kewarka sosai" tafad'a tana shafa d'an tummy plat d'inta da har yanzu bai fara fitowa ba,

"Nima zanyi kewarku, pls ki kula mana da little d'inmu kuma kidinga cin abinci sosai kinji ko?"

"In sha Allah yaya" fitowa yayi had'e da jawota ajikinsa, da sauri tafara k'ok'arin jaye jikinta daga rik'on da yayi mata tare da duba gefe gefen da suke tsaye tana fad'in

"Pls yaya cikani kada Ummah ko alhaji sufito su ganmu ahaka"

"Kibarni mana ko d'iminki dana little inji kafin natafi, kin fiye raki da yawa Basmah, badon haka ba dana d'aukeki mun koma gida," zaro idanuwa tayi kafin tace

"Gida kuma yaya? Mezamuyi acan kai dake kan hanya?"

"Basmah kema kinsani dole inada buk'atarki, tausayin halin da kike ciki kesa bana son damunki, shiyasa kikaga tun ranar har yanzu ban sake kusantar kiba, don Allah kibani dama Basmah ko sau d'aya ne?" Sosai tausayinsa ya kamata, ita kanta tasan yanada matuk'ar hak'uri, kimanin watansu biyu kenan da aure amma sau d'aya suka tab'a had'a shimfid'a har aka samu abunda ke cikinta kuma duk yana hak'urine saboda rashin lafiyarta, amma ya zatayi ita kanta idan tace bata buqatarsa tayi k'arya kawai tana daurewane don ita kad'ai tasan yanayin da ranar tashiga tana tsoron sake faruwar haka shiyasa itama take nesa nesa dashi, jin tayi shiru yasa ya rik'o hannunta yana murmushi yace

"Kada kidamu kinji, dama da wasa nake yimaki, amma promise me ranar dana dawo zaki bari ingaisa da my little?" Rufe fuskarta tayi had'e da cewa

"Am sorry yaya, in sha Allah yanda duk kake so hakan za'ayi, Allah dai ya dawo dakai lpy"

"Amin ya Allah Basmah" yafad'a tare da kissing d'in goshinta sannan ya koma cikin motar ya tayar ya wuce yana yimata bye bye horn,

Tuni itama faraaha da dr Ahmad sunjima da komawa bakin aikinsu tun bayan aurensu da sati biyu, inda faraaha itama ke d'auke da cikinta d'an kimanin wata biyu da sati uku, a b'an garen Batool kuwa har yanzu batada komai, kuma hakan bai dameta ba da ita har Ahmad d'inta, soyayyace mai k'arfi da k'aunar junansu da kuma kulawa ta musamman suke yiwa juna, ga muhib d'in mamy shima yak'ara wayau da girma sosai kamar bashiba don ba kad'an madarar da yake sha takarb'esa ba, kamarsa kuwa da mahaifiyarsa sai dad'a fitowa takeyi, watansa hud'u kenan amma har ya iya zama yana koyon rarrafe,

Jaddi kam hankalinsa ya kwanta, kullum cikin farinciki da jin dad'in yanayin kwanciyar da jikanyarsa keciki yake, wasu lokuta da dama idan yazo wajen papi yakan biya yadubo lafiyarta wanda hakanne ya tabbatar masa da tana cikin kwanciyar hankali, gashi tayi kyau sosai kuma tayi k'iba saboda yaron cikin dake jikinta, ko kad'an bata wani shan wahala wajen renon cikin don wataran har mantawa take dashi ajikinta saboda lafiyarsa, ga kula da tausayawa da take samu wajen yaya Mahmud abun ko magana ba'ayi,

Yaya Mahmud ne tafe cikin motarsa ya d'auko faraaha wajen aiki kawai saiga wasu macce da namiji aguje anbiyo ana jifarsu sun fad'o masa agaban mota wanda badon yayi k'ok'arin tada burki da sauriba da gaba d'ayansu ya bugesu, da sauri ya fito cikin motar yana ba mutanen da suka biyosu hak'uri duk sun jejjefesu sun jimasu ajiki, cikin girmamawa yaya Mahmud ya kalli wasu dattijai maza guda biyu yace

"Baba don Allah ina rok'onku a matsayina na d'a agareku da kuyi hak'uri kuyafe masu, duk da bansan laifin da suka aikata maku ba amma ina rok'onku da kuyi masu afuwa, watak'il hakan zaisa sugyara kuskurensu nan gaba" cikin b'acin rai d'aya daga tsofaffin yace

"Yaro kabarmu mu illata wud'annan karnukkan, sunjima suna shigowa anguwar nan suna d'ibar mana yara 'yan mata suna b'ata su da shaye shaye da sauran fasik'anci da sunan abota, don haka muka yanke shawarar cimaau mutunci da kuma kai k'arshen iakancinsu a anguwar nan" Shiru yaya Mahmoud yayi tunawa da yanda rayuwar k'awaye shima taso b'ata masa rayuwar 'yar uwa kafin yajuyo zai yima wud'an da aka biyo suma fad'a da nasiha, mezai gani qawar Basmace Suby da kuma saura yinta Babs, suna ganinsa suma jikinsu ya hau rawa don lokacin babu bid'ar da baiyi masu ba akan abunda suka yiwa 'yar uwarsa,

"Suby, Babs..dama har yanzu kuna cikin garinnan?" Cikin jin haushinsu da tsanarsu ya juyo yana kallon tsofaffin yace

"Shikenan baba duk abunda kukaga ya dace dasu zaku iya yimasu Allah yasawak'e" yakoma warsa cikin motarsa ya tayar ransa ab'ace, kallonsa faraaha tayi don duk abunda akeyi tanaji kafin tace

"All I have meyasa ka kasa taimakonsu bayan nasa zaka iya haka"

"My faraah wato nadad'e ina neman wud'ancan mutanen saboda su sukaso b'atawa Basmah rayuwa ada, badon Allah yakareba da tuni rayuwarta ta muzanta tasanadiyarsu, waccan da kika gani k'awartace, shikuma d'ayan saura yinta, wlh da alokacinne nahad'u dasu yanzu babu abunda zai hana inkakkaryasu kuma Inaa akullesu, don banga amfanin abunda suke aikatawa ba" duk wannan bayanin da yake yimata yna kallon yanda ake dukansu ta madubin motarsa, reverse yayi daidai lokacin da Basmah ta gama cemasa

"Kayi hak'uri mijina, tunda gashi kaga k'arshensu Allah yanuna maka, kabi alkhairi da mummuna don Allah kataimakesu kada kabarsu a hannun mutanen can don zasu iya kashesu lura da yanda duk jikinsu yayi jinajina amma sukak'i k'yalesu, kataimakesu hakan zaisa suma sugyara halayyarsu" dama tuni shima yaji tausayinsu kawai b'acin Raine ya rufe masa ido, saida yakai dazai wajen sannan ya sake tsaida motarsa yafito, hak'uri yayita ba mutanen kafin yasamu da k'yar su hak'ura su k'yalesu, bayan sun buga masu warning akan kada su sake ganinsu cikin anguwar basu ba yaransu, faraaha ce tafito ta rik'a suby shikuma yarik'a Babs suka sakasu cikin mota suka kaisu general hospital, kud'i yaya Mahmud yaciro ya mik'awa Babs dake jin jiki yace

"Ga wannan kubiya kud'in magani, ubangiji Allah ya shiryeku" cikin kuka suka dinga yimasa godiya, Suby tace "yaya Mahmud Mungode, daga yau bazamu sake aikata maka mancin wannan kuskuren ba, don Allah Kabani lambar Basmah in rok'eta itama tayafe mun" kwalo idanuwa waje yaya mahmud yayi kafin yace

"What? Lambar Basmah?, u're not serious, kije tayafe maki amma keda lambarta har abada, kuma ni don Allah nataimake ku don haka basai kinyimun godiya ba, kud'i canza rayuwarku don ita duniya batada tabbas" murmushi faraaha tayi domin komai na rayuwar mijin nata daban yake acikin mutane, hannunta yarik'o suna tafe tana kallonsa, ahankali tafurta masa "I luv you so much mijina"

Juyowa yayi tare da rufe idanuwansa yabud'e sannan yace

"I luv you too"

Kai tsaye gidan papi suka sauka yana zaune shida babynsa a palour suka shigo bakunan su d'auke da sallama, har k'asa faraaha ta duk'a ta gaishesu kafin tawuce ta zauna saiti k'asan k'afafuwan hajia kaka, shi kuma yaya Mahmud hannu ya mik'awa papi suka gaisa sannan yagaida hajia kaka ya wuce kitchen yana fad'in "Babyn papi me kika dafa yau in samoma tawa babyn don da alama yunwa takeji"

"Kai dallah ja can no nagaji da faman yimaku girki inkaji haushi ka auro wata tunda wannan aiki takeyi?" Hajia kaka tafad'a cikin raha da ban dariya

"Oh'oh hajia kaka rufamun asiri, duka duka ni nawane da zaki kiramun ink'aro aure, naga dai wasuma sarakunane amma mata d'aya kedasu balle ni"

Dariya papi yayi kafin yace "bakayi k'arya ba, amma nima can inada wata matar, rud'in duniya ya d'ibeta, tagujeni tunda na ajiye masu sarautarsu, badon haka ba ai nida kake gani nan saidai ka kirani mijin mace hud'u harda k'wark'wara" ita dai faraaha kanta naduk'e ak'asa ta kasa cewa komai Saida hajia kaka ta dafa kanta tace "'yar tsohuwa uwar d'and'ana mezakici akawo maki, don wancan mijin naki d'an banzar surutunsa bazai bari yaje ya kawo maki abunda zakici ba" d'ago kai faraaha tayi tana murmushi had'e da cewa.

"Indai tsufane nabar maki hajia kaka, saboda nalura so kikeyi da k'arfi da yaji sai kinsa mijina ya dena yayina kamar yanda ya dena naki"

"Aw..haka kikace?, Shikenan gamu gani indai mommodu ne" daidai lokacin yaya Mahmud ya iso wajen hannunsa d'auke da plate da dambun masara yasha zogale aciki ya zauna gabanta had'e da cewa

"Baby zaki iya cin wannan?" Faraaha da har yawunta sun tsinke da sauri ta d'aga masa kai tare da karb'ar plate d'in a hannunsa tafara ci,

Ko kad'an bata takura kanta agabansu domin sun bata fuskar da zata iya kallonsu suma amatsayin jaddi d'inta.

Tasowa Mahmud yayi had'e da zaunawa tsakanin papi da babynsa sannan yace

"Papi na tambayeka?"

"Allah yasa nasani malam mahmudu"

"Wai ya akayi kadawo nan garin da zama bacin mom tafad'a mun cewa ku 'yan asalin garin kanone a wata k'aramar hukuma da kaike sarautar garin"

"Tab ai wannan labarine mai tsawo amma bari nabaka kad'an daga ciki, sarautar da kaji mom d'inka tace nayi, sarau tace mai had'ari wacce na gajeta awajen mahaifina shi kuma ya gada awajen nashi mahaifin, kasancewar munada yawa awajen mahaifinmu yasa sai kujerar tazama abun rigima atsakaninmu wacce daga k'arshe ni Allah ya mallakawa ita, rigingimu da fitintinun da sukayi yawa ga tsaface tsaface da surk'ulle da akeyi duk akan kujerar ana neman salwantar mun da rayuwata data iyalina yasa bayan waau ahekaru da naga abun yayi yawa nayanke shawarar ajiye mulkin sarautar don gaba d'aya 'yan uwana sun kasa yimun mubaya'a, babu abunda ke gabansu irin sukauda rayuwata adoron duniya don su samu su mallaki wannan kujerar, Wanda adalilin hakan matata ta biyu tace ita bazata iya da abun kunya ba indai saina ajiye sarautar nan dole inbata takardarta, ni kuma alokacin babu abunda ke gabana illa inceci rayuwata data iyalina saboda matsaloli da jefe jefen da akeyomun, don ma Allah ya taimaka ina kula da ibadodina yanda ya kamata tare da addu'o'in tsari shiyasa basuyi nasara akaina ba, nan take narubuta takarda zuwa ga babbar masarauta cewa na ajiye mulkina bisa wasu dalilai nadaban don haka abama wani, ita kuma dama Allah bai bamu k'aruwa a tsakaninmu ba saboda yanda ta fitineni sai na sawwak'e mata sannan da taimakon aminina wato mahaifin dadynka wanda shine silar had'a dadyn naku tare da mom d'inku nadawo nan garin nayi zamana nida babynah wannan shine tak'aitaccen dalili da kuma tarihin ajiye sarautata, bana son fitina kuma bana son inyi duk wani abu da zaisa inyi shirka da Allah shiyasa nayi haka, kuma alhamdulillah wannan rayuwar da nake ciki tafimun rayuwar mulkin sarautar da nayi"

Jinjina kai yaya Mahmud yayi had'e da cewa "Allah kasa ingadoka papi wajen gujewa rud'in duniya da kuma taka tsantsan da rayuwar cikinta, kuma Allah yasa in gado ka da wannan halin na rik'o da addininka papi"

"Mahmud ai kayo gado fiye ma dani, Allah dai yayi maku albarka" gaba d'aya suka amsa da amin har da hajia kaka da wannan labarin yasata tunowa da wasu abubuwa da suka faru ta share k'wallan da suka zubo mata ga idanuwa, Basu bar gidan ba har sai bayan sallar magrib sannan suka tafi cike da shauk'in k'aunar kakannin nasu, ba komai kesa yaya Mahmud son zuwa gidan nasu papi ba tare da faraaha illa don su koyi wasu abubuwa masu ma'ana akan zamantakewar rayuwar auratayya domin suma suyi koyi dasu har zuwa k'arshen rayuwarsu

"Bilkisu, Bilkisu!" Billy taji ana faman kiran sunanta a bayanta, lokacin tana k'ok'arin shiga lecture 10am-12am, sanin ko muryar waye yasa tabasar tare da cigaba da tafiyarta, da sauri malam jika yaci gabanta yana fad'in

"Haba Bilkisu tah! Don me zaki wofantar danibayan kinsan ni d'in mai k'aunar kine" sanin idan ta tsaya yimasa musu zai iya jawo mata asarar wannan lecture yasa tace

"Kayi hak'uri mlam yanzu inada lecture, idan nafito sai muyi magana" bata jira mezai ceba da sauri tana had'awa da d'an gudu gudu tabar wajen.

Shikuwa Mahmud pilot tunda yakoma bakin aiki bayada aikin daya wuce tunanin Billy, wani zubin sai ya gama zai koma jin hauahin kansa tuna cewa ita bata damu dashi ba tunda har ta iya rabuwa dashi batare da tunanin komai ba, don haka dole shima ya manta da ita ya rungumi wacce Allah yabashi amatsayin mata, Yana yawan kira akai akai don yaji lafiyar Basmah da kuma little d'insa haka kuma Ummah nakula da ita yanda ya kamata, yau kimanin watansa hud'u kenan da tafiya amma ko sau d'aya baiyi tunanin dawowa ba, gashi har cikin Basmah yamik'a wata shida, sosai cikin yayi mata kyau kuma babu wata matsala da taka facing akansa, ummah ce da kanta kekaita asibiti a ranakun awo kuma sudawo tare, babu abunda ke damunta don tana samun kulawa yanda ya kamata kuma tanajin muryar masoyinta fiye da sau uku arana don haka hankalinta ke kwance kuma tanata renon cikinta.

Ranar da cikin Basmah ya cika wata bakwai aranar kamfanin da yake aiki suka turasa a branch d'insu dake k'asar India kuma sai yayo wata biyu kafin yadawo, ko kad'an baiso haka ba, don yaso ace yakoma gaban iyalinsa ya taimaka mata wajen renon cikin amma duk hanyar da zaibi koda kwana biyu abarsa yaje yayi sunk'i bari, sosai ransa yab'aci har saida su Ummah da alhajinsa suka yita rarrashinsa akan yayi hak'uri yaje sannan ya amince koshi Saida Basmah ta tabbatar masa da yaje babu wata matsala in sha Allah don motsi kad'an idan tayi su umma nakula da ita kuma bayan haka ai watan da zai dawo shine watan haihuwarta don haka ya kwantar da hankalinta zai iskota lafiya ita da little d'insa, sai alokacin yasamu natsuwar yin tafiyar amma yasa aransa bazai cike wata biyu acan ba zai dawowarsa don yafiso Basmah tahaihu Yana nan.

Yana gama waya da ita sai yaji kawai yanada sha'awar Kiran Bilkisu, bai jira me zuciyarsa zata fad'a masa ba kawai ya dannawa lambar wayarta kira lokacin tana kwance tana tunanin bawa malam jika dama saboda yanda yabi yatakura rayuwarta kota samu tahuta. Ko kad'an batayi niyar taahi ta d'aga wayar ba saboda yanda take enjoying kwancin da tayi amma kamar antsikareta tamik'e tare da d'auko wayar dake jikin socket tana charji, ganin lambar wanda ke kiranta yasa gabanta fad'uwa, amma hakan bai hanata d'aga kiran cikin sauri ba kafin ya tsinke hannunta narawa ta kara akunne had'e da cewa..



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____96๐Ÿ’Ž


"H..he.hello" yanda yaji tafad'i hello d'in cikin i'ina shiya bashi dariya yace

"Hello 'yar uwa" ajiyar zuciya ta sauke kafin tace

"Yaya Ina wuni?"

"Lpy klw, Bilkisu kina lafiya?"

"Alhamdulillah, yaya ya yayyatah lfiya take"

"Lafiya klw, ya karatu?"

"Alhamdulillah, ya aiki?"

"To gashi babu dad'i, yau insha Allah zanbar k'asarnan sunturani a d'ayan branch d'insu dake k'asar India"

"Allah sarki to yayya fa?"

"Tana wajen Umma kafin nadawo"

"Allah yatsare kuma ya dawo mata da kai lafiya" murmushi yayi Yana mamakin yanda akoda yaushe k'arfin halinta da courage d'inta akansa ke k'aruwa, jin yayi shiru yasa tace

"Sai anjima yaya"

"Aw korar yayan akeyi?, Dama kwana biyu nace k'anwa ta manta da yayanta bari nakira tunda har ga tafiya ta gitto mugaisa kuma muyi bankwana"

"Ayya nagode yaya, stress d'in karatune sukayi mani yawa shiyasa, be side nasan yaya nafad'a maka cewa nace Ina gaisheka idan mukayi waya"

"Yes ofcourse, ana Kiran yayya amma banda yaya, abun banbancine kenan!"

"Noo. Bahaka ba, ai babu banbanci tsakaninku domin gaba d'anku 'YAN UWANA NE, so just keep dt word aside, just dt su su biyune kai kuma kai d'ayane, kaga at least akwai buk'atar kulawa dasu duk yanda strees yayi yawa, amma tunda nayi laifi kayi hak'uri" 'ya dariya yayi kafin yace

"Shikenan 'yar uwa, aikin kashe bakin maganar, ngd ssai sai anjima" dariyar itama tayi had'e da cewa

"Ehem, ngd yaya Allah yatsare hanya" sannan suka kashe wayoyinsu, itakam Billy har ga Allah babu wani abu da taji aranta sab'anin Mahmud da yaji wani irin farinciki, duk da dai bawani abu da yake tunani atare da ita ahalin yanzu, wayar yaya Mahmud yakira shima suka gaisa sannan yakira ta Batool, sosai yadinga tsokanarta wai taji tsoron Allah amarcin ya isa haka ta samo masu baby, tayita dariya tana fad'in sai sun gama shan bukin sunan yayya tukuna,

Ummi ma ciki ya mik'a don itama cikin wata na bakwai yake, babu inda take zuwa saboda kada aganeta da ciki, Batool kuwa randa tazo gida ta isko Ummi da ciki tsalle da ihu tayi tayi na farinciki Wanda nan take takirasu Basmah da Billy ta sanar dasu, suma can sunata farinciki da murna sunaji tamkar suyo tsuntsuwa sutaho gida, zungureta Ummi tayi had'e da cewa

"Allah ya shiryaki Batool, shikenan kinfad'a hankalinki ya kwanta ko?" Mom dake gefe tana tuyar wainar fulawa saboda da kwad'anta Ummi ta tashi yau tace

"Ah dama ai k'yaleki kad'ai nayi ban fad'a masu ba don nasan mai fayyace abun natafe ko yaushene, kinga wata bakwai Ina k'umshe da bakina amma cikin minti bakwai ta fayyace komai" hararar mom Ummi tayi had'e da cewa

"Waya sani halin d'a da mahaifi ko dama can kin b'ulguta mata zancen"

"To ai 'yar kice, idanma hakane sai inke kika shige d'aka kika fad'a mata"

"Wa? Allah yasatari buk'ui, aini Basmah ce 'yatah indai wannan ce mai guru gurun idanuwa kamar k'waruru nabar maki abukki kiyita fama, Ina zan iya da wannan iyayin na Fatima"

"To ai shikenan tunda haka kikace, kyaga mai kula maki da 'yar taki idan tadawo, muna kallonku uwa kwance d'iya kwance" mom tafad'a tana dariya, ita dai Batool sai kallonsu takeyi cike da sha'awar yanda rayuwar zamansu ta kasance gwanin ban sha'awa.

Ayanzu kam Mahmud pilot ya gama yarda cewa Basmah itace qaddararsa kuma zab'in da Allah yayi masa don ya gada imaninsa, don haka yayi imani da haka saboda tuni ya samama Basmah wani gurbi acikin zuciyarsa wanda bai tab'a tsammani ba, tsaye take tana faman har had'a wasu 'ya kayayyakinta tare da 'yan kakkab'e kakkab'e saboda yau cikinta ya shigo wata na tara kwasam saiga kiransa ya shigo awayarta dake kan madubi ajiye, murmushi tayi kafin ta d'aga had'e da cewa

"Ranka ya dad'e Abban little, barka da rana?" Shima ta tasa b'angaren cewa yayi

"Tare dake oum little naki ya dad'e har yayi k'arko, ya kike da my little d'ina?"

"Lafiya klw yaya, gashinan duk ya isheni ya shamun kai da rashin ji tun cikin ciki, gaskiya wannan babynta kwata kwata bakai ya gadoba, kuma basu yaya da sister naba, don rashin zamansa kurum yayi yawa, inaga duk Batool ce zai gado da rashin ji"

"Kai Basmah da gaske kikeyi?"

"Sosai kuwa yaya, baranma idan baci abinci da wuri ba, zo kaga yanda yake faman halbina yana shure shure sai kace jetli, koda yake no wander yanada iyaye Japanese amma dai ni sisternah batada irin wannan karauniyar" dariya yayi kafin yace

"Basmah kinsan wani abu kuwa?"

"A'a yaya sai kafad'a" tace had'e da k'ok'arin zaunawa gefen gado tana fad'in

"Awwshh" da sauri ya mik'e daga kwancen da yake yana fad'in

"Basmah lpy kuwa?" lumshe idanuwanta tayi tare da d'an sakin murmushi kafin tace

"Kai yaya meye kuma abu razana anan? Lafiya klw fa nake, kawai girman cikinne yayi yawa shinefa zan zauna kaji nace haka" wata irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace

"Alhamdulillah, Basmah bana son abunda zai sameki ko kad'an keda little d'ina"

"Saboda me? Ai bawa baya wuce qaddara da kuma tsarin da Allah yayo masa"

"Nasan haka Basmah, amma inajin soyayyarku araina fiye da tunaninki, babban burina aduniya baifi inga Allah ya saukeki lafiya ba"

Karka damu yaya, in sha Allah lafiya klw zan haihu, kawai dai munyi missing d'inka sosai nida little"

"Iyyeee dama ashe k'anwa zatayi missing d'in yayanta hakan?" Murmushi tayi had'e da cewa

"Sosai kuwa Abban little munyi kewarka"

"To shikenan kuyi hak'uri very soon zandawo gareku in sha Allah,"

"Hop so yaya!"

"Yawwa Basmaty to me aka tanadarwa yaya kafin yazo?" Saida tayi daria kafin tace

"Babu komai face ni kaina, gangar jikina, zuciyata da kuma rouhina gaba d'aya"

"Ashe dai anaji da yayan nan"

"Sosai ma kuwa kawai yakasa ganewa ne, amma k'anwarsa na matuk'ar sonsa sosai, I luv you so much" tana gama fad'ar haka takashe wayar da sauri don tunda take bata tab'a furta masa makamanciyar irin wannan kalmar ba sai yau, shiyasa nauyi da kunyarsa sukasa ta kashe wayar. Hakan daya ji yasa ya ciro wayar a kunnensa tare da kallon screen d'in wayar ahankali yace

"Nasani Basmah ko baki fad'aba, amma fad'ar da kikayi ya tabbatar mun da cewa ked'in masoyiya tace da zanyi alfahari da ita" sake kiran wayarta yayi har sau biyu bata d'aga ba hakan yasa yayi dariya tare da cije leb'ensa na k'asa sannan ya shiga text messages d'insa

Please Login or Register in order to submit comment