Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zugi da rad'ad'in ciwon zuciya daya uzzura mata, koda safiya ta waye ta matuk'ar jigata amma cikin ikon Allah jinin ya tsaya ya dena zuba, a firgice Batool ta tashi da asuba jin yanda 'yar uwarta ke fidda wani nishi da k'arfi dake nuna tana kokuwa da lumfashinta dake neman yafi k'arfinta, rik'ota tayi tana jijjigata da k'arfi tana fad'in

"Yayya Basmah meke faruwa dake ne, pls kiyimun magana mana yayya mike damunki?"

Da k'yar tabud'e idanuwanta had'e dayi mata murmushi tana nuna mata saiti zuciyarta, ai da sauri ta ajiyeta tamik'e da nufin zuwa takirawo mom, rik'o hannunta tayi a hankali tafurta "kada ki kirawomun kowa inba yaya ba kinji?" Sannan tasaketa, da gudu Batool tafita part d'in lokacin ita kuma mom na toilet tana arwala da niyar tana gama sallah zataje tadubo yanda takwanta da jiki, gab da takai d'akin yaya Mahmud taci karo dashi zaije masallaci, cikin muryar kuka tace

"Yaya kazo yayya batada lafiya sosai kuma tace kai kad'ai take son gani" jin haka ya tabbatar masa da matsalar ciwon tane yatashi shiyasa bata buk'aci ganin kowa ba saishi, d'akinsa yakoma ya d'auko keys d'in motarsa arud'e don yau kome zai faru saidai yafaru amma dole yakaita asibiti ko bata so, saida yafiddo motar sannan yawuce part d'in lokacin mom na sallah, yana shiga dama yace Batool tagyarata yasamu tana saka mata hijabi, rik'ota sukayi suka fito da ita ko wanensu yanayi yana kallon fuskarta ganin tana dad'a k'ara jinjiki yasa ya d'agata sama ya d'auketa da gudu Batool tak'arasa tabud'e gambun motar nabaya tana share k'wallar idanunta, yana sata ita tashiga ta d'ago kanta tare da azawa bisa cinyoyinta tana yimata sannu, horn yaya Mahmud yayi maigadi yabud'e masa gate yafice aguje, daidai lokacin dady ya dawo daga masallaci rik'e da hannuwansu Bassam don yau shima a part d'in Ummi ya kwana wajen Bilal yabi motar da kallo cike da mamaki don dama zuciyarsa d'auke take da tambayoyi akan rashin ganin yaya Mahmud masallaci wajen sallah.




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: ๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar alkhairin Allah da amincinsa sutabbata agareku da ahalinku bisa jajircewarku da nuna k'aunarku ga wannan littafi *Anushbee moh'd, Jaanatusanikaka, Zeezubyr mytamah, Meenert marke, Hijjah yaks, Aunty rash Kaura, mardiyambawa, Mamana'ima1994, Zainab garba faruk, Halimatu Mr's H, HAUWA a Auwal sarina, Sumayya busum, Khadija tukur, Nana Hauwa'u, Surayya Awwal, Zahra, Oum aslam, Zainab madugu, Aunty Rukky, Hadiza jauro, Hajia Ruky, Oum sulym, Haulatu sabi* kai gaskiya kunada yawan gaske da bazan iya lissafoku gaba d'aya ba acikin wannan page ba, ngde ngde sosai bisa k'arfafamun guiwa da kukeyi, ina rok'on Allah da yasa kufi k'arfin duk abunda yafi k'arfin ku aduniya kuma ya faranta maku dukkanin zuciyoyinku yabaku aljannah da rahamarsa๐Ÿ‘๐Ÿป *ME LUVS YOU FILLAH*๐Ÿ˜โค_


๐Ÿ’ŽPage_____73๐Ÿ’Ž


Da sauri dady yak'arasa cikin gida kai tsaye ya wuce part d'in mom, yana shiga ya tadda ita tana k'ok'arin shigewa cikin d'akin su Basmah ya dakatar da ita tahanyar cewa

"Ina yaranah, meke faruwa dasu ne?" yafad'a batare daya kalli inda take tsayeba don har lokacin babu wata jituwa tsakaninsu, kafin mom tace wani abu saiga wayar yaya Mahmud da tsabar gudun da yayi akan titi har yakai bakin k'ofar shiga gate d'in asibiti yakira dady, kallonta ta yayi sannan yajuya had'e da d'aga wayar, "My son ina kajene da uwar safiyarnan, lpya dai injin" yafad'a cikin kausasa murya.

"Lafiya klw dady gamunan asibiti munkawo Basmah" hankalin dady atashe yace

"What wrong with her? Ko ciwonne yatasammata"

"Eh dady amma da sauk'i" ai dady bai tsaya jin mezai ida fad'aba ya katse wayar sannan ya juya zai fita, biyo bayansa mom tayi yayi saurin dakatar da ita tahanyar d'aga mata hannu batare daya juyo ba sannan yawuce yabar part d'in cikin sauri, akan kujera mom tafad'i zaune hawaye nazubowa daga idanuwanta, Bassam ne yamatso wajen shida Bilal suna tambayar

"Mom meyafaru kike kuka" kallo d'aya tayi masu ta d'auke kai had'e da cewa "yayya d'inku ce ba lafiya, kuje kuyi mata addua" had'e da mik'ewa tabar wajen, shi kuma dady part d'insa yanufa ya d'auko key d'in motarsa ya wuce asibiti n.

Koda suka isa asibitin lumfashin Basmah yayi k'asa sosai da gudu nurses suka karb'eta zuwa emergency don ceto rayuwarta, cikin gaggawa aka saka mata oxygen sannan aka fara bata emergency care, Batool kuwa tunda suka shigo take kuka saida yaya Mahmud ya jawota ajiki ya rungume yana fad'in

"Kidena kukannan haka Batool all what she want now is our du'ah kinji" wanda shimad'in k'arfin haline yayi bawai don bayajin damuwar hakanne azuciyar saba, sai da yaga tadena kukan sannan ya d'ago kanta yace

"Kinyi sallah?" Tagirgiza masa kai had'e dasa hannu tagoge hawayen da suka jik'e mata fuska

"Ok muje fanfo muyo arwala muyi sallah kinga rana nasoma fitowa kada lalurinta yawuce" tare suka nufi wajen fanfon sukayo arwala sannan yaje wajen motarsa yabud'e ya d'auko mata darduma yabata shikuma yayi masallacin dake can farkon shigowa cikin asibitin, but shida Batool sunyi addua'a sosai akan Allah yaba 'yar uwarsu lafiya, koda yagama sallar zaune yayi yana sake rok'on Allah akan ya walwale wannan matsalar dake tsakanin 'yan uwansa wacce duk inda akayi tunanin b'ullo mata don walwale matsalar d'aya to d'ayan zai iya shiga matsala yakawo hanya mafi sauk'i da kowanensu zai samu natsuwar zuciya. Yana fitowa masallacin motar dady nayin parking, da sauri ya k'arasa wajen yabud'ewa dady gambun motar,

"Sannu da zuwa dady antashi lafiya?"

"Lafiya klw son yajikin ita Basmah d'in"

"Da sauk'i dady amma har yanzu likitan daya shiga dubata basu fitoba!" Shiru dady yayi kamar mai tunanin wani abun fuskarsa d'auke da da damuwa kafin ya lak'amo kafad'arsa sufara tafiya yana fad'in

"Son amatsayina na uba narasa gano meye matsalar data haifarwa 'yatah fad'awa cikin wannan damuwar, amma kai da kake yayanta wanda yafi samun kusanci da ita sosai akaina mekake tunanin yajefata cikin wannan matsalar?"

Har ga Allah ciwon Basmah yakai matakin daya kamata yabayyanawa kowa dalilin daya jawo matashi koza'a iya samo mata wata mafitar amma baya tunanin cewa zai iya fad'a domin yadad'e da fahimtar yanda billy ke matuk'ar son Mahmud fiyema da yanda Basmah ke sonsa kuma shi Billy yafurtawa soyayyar sa wacce har taso jefasa amakamancin halin da ita Basmah keciki yanzu, d'aya b'angaren zuciyar sane yace masa kawai yafad'a tabbas Billy zata iya hak'ura tabarwa Basmah shi kodon halin data ganeta aciki, "Noo..dukansu 'YAN UWANA NE!" Ya fad'a abayyane da k'arfi wanda har saida yasa dady yaji,kallonsa dady yayi cike da alamar tambaya abakinsa sannan yace

"Dukansu 'yan uwan kane sukayi me to" sai alokacin yafahimci zancen zucinsa yafito fili da sauri yace

"Ina nufin dukansu 'yan uwana ne ba Basmah ce kad'ai ba kuma inada kusanci dasu" girgiza kai dady yayi sannan yace

"Eh to shine ai nace kasancewar kanada kusanci dasu nake so kafad'amun meyake damun 'yar uwarka?, meya jefata acikin wannan damuwar?"

"Ban saniba dady amma dai nafi tunanin kawai ciwone Allah ya jarabceta dashi" daidai lokacin suka iso bakin d'akin da aka shiga da Basmah wanda saida likitocin sukayi da gaske sannan suka samu dai daita lumfashinta ajikinta, cikin k'ank'anen lokaci suka gama gano matsalarta da ciwon zuciyar dake damunta, bayan sunyi mata dukkanin abunda ya kamatane har an maisheta awani gefen da zataci gaba da samun kulawa dr.n yafito yana cire hand glove d'in dake hannunsa, da sauri su dady suka k'araso wajensa suna tambayar ya jikin Basmah d'in" cire glass d'in idanuwansa yayi kafin yace

"She's now ok. In sha Allah but ko kunsan tana d'auke da ciwon zuciya" kamar dady da yaya Mahmud sun had'a baki atare sukace "Eh dr meyake farune" cikin b'acin rai likitan yabud'e baki zaiyi magana aka kira dady awaya, jawo wayar yayi had'e da duba wa yaga kiran mom ne, har zai tsinke kiran sai kuma mom tabashi tausayi yatuna cewa UWA DA 'DA fa sai Allah yatabbata yanzu tanacan cikin damuwar rashin sanin halin da 'yar tata keciki kuma k'in d'aga warsa zai k'ara jefata ciki damuwa don haka sai yayi excusing kansa ga dr.n yakoma gefe had'e da d'aga wayar, hakan ba k'aramin dad'i yayiwa yaya Mahmud da gabansa kecikin fad'uwar kada likita yasanar da dady cewa damuwace da tunani suka haifarwa da Basmah wannan ciwo wanda yasan dole dady zaitasata agaba sai tafad'a masa abunda ya jefata cikin tunani da damuwa, ganin haka yasa likitan yace to idan sungama su samesa a office d'insa had'e sannan yabar wajen, nuni dady yayiwa yaya Mahmud da hannu akan yabi bayansa kafin yazo, suna shiga dr. Yacire glass d'in idonsa yace

"Anya kuna sane da illar da ciwon nan yayiwa yarinyarku da baku hanzarta kawota asibiti ba sai yanzu da har yacita ya cinye"

Gyara zamansa yaya Mahmud yayi had'e da cewa likitan "pls dr. Duk da bamuda masaniya akan ciwon yakai haka tabbas munyi kuskure amma don Allah kafad'amun awane irin hali take yanzu?" Nisawa dr yayi sannan ya kallesa had'e da cewa

"Am srry to say matuk'ar bakuyi k'ok'arin bincikarta kuka san kome take buk'ataba akayi mata to tabbas idan har zuciyarta tasake bugawa akaro na biyu babu tantama akan cewa zaku iya rasata matuk'ar baku d'auki matakin gaggawa ba alokacin da hakan yafaru wanda bama fatarma yasake faruwa" cikin tashin hankali yaya Mahmud yace

"Ban fatimata ba dr, kayimun bayani dalla dallah yanda zangane"

"Eh to ina nufin yanzu dai zuciyarta ce tabuga akaro nafarko wanda tsananin ciwon da takeyi matane da tunanin data tsanantawa zuciyarta ya haifar mata da hakan har yajawo tafara bleeding jini ta hancinta"

"What?" Yaya Mahmud yafad'a had'e da mik'ewa tsaye cikin tashin hankali, zaunar dashi dr yayi tare da cewa

"K'warai kuwa idan har baku sani ba to tabbas hakan yafaru da ita, wanda zuciya nabugawane sau uku acikin rayuwar d'an adam wanda idan har akayi sakacin data buga akaro na uku babu abunda zai hana arasa rayuwar mutum inba ikon Allah ba, shiyasa muka fad'a maku don ku hanzarta nemo mata abunda take buk'ata saboda tarabu da wannan tunanin" sosai yayita na yaya Mahmud shawarwari tayanda zasu iya shawo kanta barta fad'a masu damuwarta sai amagance mata ita cikin lokaci sannan sukayi sallama bayan yaya mahmud yayi masa godiya sosai, dady kuwa yana d'aga wayar mom tafashe masa da kuka tace

"Pls alhaji do fevour for me inzo inga halin da 'yata take ciki wlh tunda kuka tafi nakasa samun natsuwa da kwanciyar hankali, ina so insan awane hali take ciki, alhaji bana so narasa rayuwata kona rasa basmah har saina gamsar dasu cewa nima uwace tagari atare dasu akaro na biyu"

Sosai tabashi tausayi kuma yau ya gamu cewa tayi nadama ashirye take data gyara dukkanin kurakuranta, a hankali yafurta mata "kiyi hak'uri tasamu sauk'i sosai yanzu haka dr. Suna can tare da yayanta kuma natabbatar yayi masa bayani akan taji sauk'i don haka kikwantar da hankalinki basai kinzoba kinji ko?"

"Shikenan alhaji tunda haka kace Allah yabata lafiya"

"Amin" yace tare d'aci gaba da rarrashinta yana kwantar mata da hankali wanda hakan yasa tad'an samu natsuwa kad'an aranta duk da jikinta nabata cewa 'yar tata nacikin matsala, suna gama wayar yanufi office d'in dr, har zai shiga kuma saiga kiran Ummi da tund'azu take trying nombers ana cemata busy ya shigo, d'agawa yayi had'e da cewa

"Hello rabba'atul bait" ai bata tsaya amsa masa ba cikin tashin hankali tace

"Abu Bilal meyake damun Basmah, yanzu su Bassam suka shigo suna fad'amun cewa anyi asibiti da ita injin dai da sauk'i?" Tak'are maganar kamar zatayi kuka,

"Ki kwantar da hankalinki insha Allah da sauk'i yan zuma wajen likitan zanshiga" "Allah yak'ara sauk'i don Allah idan kafito kakiramu don muji yajikin nata hankalinmu ya kwanta"

"To shikenan, ina Bilkisu"

"Gatacan tayi wajen momynsu tana kuka jin ance 'yar uwata bata lafiya har anyi asibiti da ita"

"To Allah yasawak'e, ai kuka bayayi tadai yimata addua" yafad'a tare da kashe wayar yana k'ok'arin shiga office d'in, karo sukayi da yaya Mahmud dake fitowa fuskarsa cike da damuwa, yan ganin dady yasaki murmushin k'arfin hali tare da cewa

"Dady har kagama"

"Eh me dr.n yafad'a maka, ko mushiga daga ciki sai yak'ara yimani bayani ko?"

"A'a dady ai yace alhamdulillah jikin nata da sauk'i amma gaskiya anyi sakacin kawota asibiti da wuri har ciwon yad'an tsananta mata but yanzu alhamdulillah komai ya daidaita"

"Masha Allah to akwai abunda yace kedamunta ne?" Saida yaya Mahmud yad'an juyar da fuskarsa gefe yagoge hawayen da suka zubo masa sannan cikin nuna jarumtarsa tayanda da cewa but Basmah da Bilkisu duka 'yan uwansa ne baya son ya zamo silar mutuwar kowacensu don d'aya tasamu farinciki, yana sonsu kuma bai isa ya canzawa duk wacce Allah yatsa rowa qaddarar ta agaretaba yace..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: ๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____74๐Ÿ’Ž


Eh dady, dr yace kasancewar ciwon yana iya wuce mata haka to dolene akula sosai da yanayin walwalarta da kuma farinciki sannan adena barinta tana zama ita kad'ai don kaucewa shigarta cikin tunani da da damuwar da suke haifar da tashin ciwon nata, amma in son samune abinciketa ko akwai abunda takeso aranta wanda rashin samunsa shiya haifar mata da wannan matsalar"

"Ikon Allah, amma ai da dad'ewa nataba tambayarta cewa ko akwai abunda take buk'atane aranta kuma ta tabbatar mani da cewa babu komai kuma kai shedane akan haka" dady yafad'a cikin mamaki da al'ajabi.

"Nidai dady nasan akwai abunda ta tab'a yimun maganarsa lokacin da suka kammala secondary cewa tana so taci gaba da karatu to amma kasancewar ka nuna baka buk'atar haka kafiso sai kowacensu tayi aure sannan taci gaba da karatun idan mijinta ya amince shiyasa na dakatar da ita da zancen na nuna mata tayi hak'uri kawai tunda baka so, to ina tunanin k'ila tasa abun arantane sosai don tana yawan yimun zancen acewarta yana matuk'ar burgeta taga mace tayi karatu mai zurfi" har ga Allah yaya Mahmud baisan lokacin da yatsara wannan k'aryarba abaki har yafiddo da ita,

"Mtsss idan kuwa wannan ne dalilin ciwon ta dakai har ita kunzama shashashu, don me bazataje tayimun bayaniba tunda ni anawa tunanin duk sun amince da tsarina basa son cigaba da karatun kamar yanda bana so, aini ra'ayina nafad'a bawai cewa nayi dole haka za'ayiba"

Kallon fuskar dady yayi yaga yanda yagama yarda da maganar saboda yanda haushi da takaicin maganar yabayyana k'arara a fuskarsa "kayi hak'uri dady dani har su mun zata dokace ka gindaya shiyasa mukayi biyayya akan maganar" yafad'a tare da d'an sunkuyar da kai alamar ban hak'uri.

Billy kuwa tanajin maganar dasu Bassam kefad'awa Ummi akan rashin lafiyar Basmah tanufi part d'in aguje tana kuka, tana shiga ta tararda mom zaune tayi tagumi, agabanta taduk'a tana fad'in "Mom ina my twiny?, me yasamu yayya Basmah ne? Da gaske batada lafiya sosai injisu Bassam?" Kallo d'aya tayi mata had'e da mik'ewa tana fad'in

"Dama ana k'aryar ciwone Bilkisu? Idan baki yardaba kije d'akinsu kigani mana" sannan tabar wajen tana sharar hawayen idonta. Dagudu tafito itama tanufi d'akin habu mai gadi tana fad'in

"Habu, habu" da sauri yafito had'e da cewa "na'am shalelen yayanta lafiya?"

"Don Allah ina nazir driver?"

"Yanzunnan ya shigo amma yad'an d'auki buta ya zagaya"

"Don Allah kace yafito da mota zai kaini asibiti"

"Haba shalele ai dakinyi hak'uri har sudawo tunda kinga kosu hajiya suna nan ko kuwa" cikin wata irin murya da batasan tanada itaba tace

"Ina ruwanka da zuwana, 'YAN UWANA NE fa meya shafeka aciki, malam kawai kafad'a masa abunda nafad'a maka kafin nadawo" tana gama fad'ar haka tawuce, dafe baki yayi yana fad'in "ikon Allah jimun yarinya da tsiwa daga magana, meye abun fad'a anan da har take mani ik'irarin wai 'YAN UWANA NE" yak'are maganar yana kwaikwayon muryarta da yanda tafad'a, zura wuyansa yayi yana lek'en yanda take tafiya da sauri da sauri har tana had'awa da d'an gudu gudu tamkar zata taahi sama sannan yaci gaba da cewa "wai shalele shale kenan, tana dai son 'yan uwannan nata koya za'a kwashe ranar aurensu idan zasu rabu?"

Ba'afi minti biyar ba saiga nazir driver yafito nan ya sanar masa da sak'onta aikuwa cikin hanzari yajawo motar dayake kai su Bilal makaranta don dama makullenta kad'aine a hannunsa, yana gama parking sai gata tafito sanye da dogon hijabinta mai hannuwa ash colour har k'asa, bud'e motar kawai tayi tafad'a tare da cewa

"Asibiti zamuje" daga haka bata k'ara cewa komai shikuma ya tada motar suka bar gidan, har suka isa bata sake cewa komaiba, hango dady da yaya Mahmud da tayi a tsaye yasa tanufi wajen tare da gaishesu tana goge k'walla a idanuwanta, kallonta dady yayi tare da girgiza kai yace

"Bilkisu meye abun kuka, keda yakamata kiyiwa 'yar uwarki addu'a Allah yabata lafiya" duk'e kanta tayi k'asa tare da cewa

"Dady ina yayya d'in, ince dai jikin nata da sauk'i"

"Eh da sauk'i" kije ga 'yar uwarki can ina ganin sai zuwa anjima zasu bari ashiga yana nuna mata inda Batool kezaune ta sunkuyar da kanta k'asa tana tunanin halinda 'yar uwarta ke ciki akan abunda zai matuk'ar yimata wahalar mallaka tunda yanzu bai fiye wata d'aya ayi aurensu ba, balle ayi tunanin wata hanyar da ko Allah zaisa Billy tasan da wannan matsalar ta hak'ura tabar matashi,

Wajenta tanufa daidai lokacin da shikuma nazir ya k'araso wajen yana gaishe dasu dady cikin girmamawa, hannu dady yamik'a masa sukayi sallama sannan yaya Mahmud shima yabashi suka sake gaisawa daga nan yayi masu ya Basmah da jiki,

Alhamdulillah jikin Basmah yayi sauk'i sosai kuma koda dady ya tambayeta meke damunta kai tsaye kamar tasan abunda yaya Mahmud yafad'a masa kenan tace don Allah so take dady ya amince taci gaba da karatu tayi hakan ne amatsayin kare kanta daga amsar da zata basa sai akaci karo da maganar tazo d'ai da dalilin da yaya Mahmud yabasa nacewa shine silar ciwon nata atunaninsa, hakan yasa dady yak'ara amincewa da zancen, wanda anan take ya amince mata akan cewa zata koma karatu da zaran tak'ara samun lafiya, sosai taji dad'in haka aranta wanda take fatar Allah yasa hakan yazamo shine mafi k'ololuwar alkhairi agareta, bayan kwana biyu aka sallamesu bayan dr yaja mata kunne sosai akan tadena yawan tunani kuma tak'i yaye duk wani abu da zaib'ata mata rai ko yasa tashiga cikin damuwa, sannan dole ta k'auracewa duk wani abu daya had'a da maik'o ko yaji ko tsami ko kuma abu mai zafi don gujewa ciwon nata tashi haka kuma ya gargad'eta akan ta tsare shan magani bisa k'a'idar yanda aka batashi akoda yaushe kuma idan taji alamun ciwon nata nason tashi to agaggauta zuwa da ita asibiti don shawo kansa da gaggawa.

Yanzu kam alhamdulillah no more any tension ko damuwa aran Basmah don tana yak'ar zuciyarta sosai wajen ganin tadena bijiro mata da soyayyar Mahmud pilot, tazama 'yargata ga kowa agidan hatta dady haka kurum zaisa akirawo masa ita yamik'a mata jarida yace tadinga karanta masa don d'ai yatabbatar yayi keeping d'inta busy tayanda damuwa bazata ziyarto taba, haka mom tasata takeyi agaba su shiga kitchen tare tana koya mata girki kala kala suna firarsu ta uwa da d'a cikin jindad'i suna dariya duk don ta tabbatar da cewa tasamu farinciki, Ummi ko ba'a magana don tasa mata k'a'ida matuk'ar safiya da marece sukayi to dole tazo ta had'a masu takarar haddace azkar d'in safiya da marece ita dasu Billy zasu dinga musaffarta kullum kafin ayi aurensu tace duk wanda yafi iyawa zatayi masa kyauta ta musamman duk da tasan Billy tadad'e da haddacesu amma saita yimata gargad'i da itama tazama 'yar koyo atare dasu saboda Basmah tazamo cikin farinciki , yaya Mahmud ma ba'a barshi abayaba don matuk'ar baya komai haka zai d'aukosu da mota yafita zagaya gari dasu ana fira ana dariya wani zubin da gangan zai dinga jansu Batool da rigima yace Basmah tadawo gaba yakoya mata mota ammasu bazai koya masuba suje can mazansu sukoya masu aikuwa tayita yimasu dariya, yauma tafe suke ana dariyar Billy tab'atawa Batool fuska da ice cream yaya Mahmud yayi parking gefen titi, fitowa yayi tare da zagayawa yana kallon Basmah dake gaba zaune ta gefensa had'e da bud'e gambun motar yace

"Fito sister ki koma can gaba inda nataso yau ke zakiyi driving d'inmu har gida" ahankali tabud'e baki tace

"No..bazan iyaba yaya"

"Zaki iya just try ita yaufa six days kenan kina koya, beside ai gani agefenki ko?" Juyawa tayi tana kallonsu Billy da suka k'walalo idanuwa suna saurarensu takwashe da dariya saboda yanda suka sandare waje d'aya cike da tsoro sai kace sak'ago tace

"Hi guys, better tight your belts yau zakuga gwanewar sabon hannu a drivern" sannan tafito shikuma ya zauna wajen yana dariya, zagayawa tayi itama tazauna driver seat tare da lak'a belt d'in motar ajiki sannan tasa key had'e da take break d'in motar ahankali suka fara tafiya sannan tasaki ta danna wutar motar suka cigaba da tafiya kasancewar motar authormatic ce, ahikuma yaya mahmud yad'an dafe mata starring motar yana saita mata tafiyar had'e da yimata bayani, rungume juna Billy da Batool sukayi suna 'yar k'ara saboda tsoro, juyowa yayi yakallesu tare da fashewa da dariya yana fad'in "kai meye haka kuma?"

'Dago kai Batool tayi TNA kallonsa bayan ta mak'ale ijiya d'aya tace

"Yaya tsautsayin amarci, don Allah ka karb'i motarnan" murmushi Basmah data maida hankalinta sosai akan tuk'in tayi tare dakai speed d'in motar 40 aikuwa suka sake k'ank'ame juna suna ihu, kallon Basmah dake murmushin mugunta yayi had'e da cewa

"A'a d'alibata d'an d'age k'afarki kad'an ga giyar motarnan, nimafa an gone ina tsoron tsautsayin angwancinnan koba haka ba Batool?" Dariya sukayi gaba d'ayansu wanda daidai lokacin Basmah ta tashi bugun wani mai napep da sauri yaya Mahmud yarik'o starring suka kauce masa gabansa nafad'uwa, lek'owa mai napep d'in yayi da kansa cikin masifa yana fad'in

"Dallah gafara malan wa ka d'aukone haka kake neman ture mutane don rainin hankali" dariya Basmah tayi daidai lokacin da suka wuce sa tace "yi hak'uri malan 'YAN UWANA NE" tsaki mutumen yayi ganin macece had'e da cewa "learner kawai" sannan ya wuce, cikin natsuwa taci gaba da tuk'a motar ahankali tare da taimakon yaya Mahmud har suka iso gida, tanayin parking su Billy suka fito da sauri kamar sun had'a baki atare sukace "learner kawai" sannan sukabar wajen da sauri da sauri suna dariya don karta kamasu, dariya itama tayi sannan tajuya tana kallon yaya mahmud tace

"Thank you broth for keeping me happy always nida 'yan uwana we always give thanks to Allah for giving us a wanderful elder brother like you"

"Me too proudly to have an amazing sister like you" yafad'a yana murmushi. Tun abakin k'ofa suka faraba mom labarin driving d'in Basmah yau tayi murmushi don tasan yaya Mahmud yayi hakan ne don kauda damuwa atattare da ita, tabbas tana yiwa Allah godiya daya albarkaceta da samun d'a kamarsa da kullum burina bai wuce yafaranta ran iyayensa da kuma 'yan uwansa ba..


_A special thanks to you my dear sister *shamma halliru* thanks fd called jxakillahu bikhair๐Ÿ’‹โค_





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: ๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Is a great and bless to meet some one special who knows your value, love u and respect you any time and any moment, I will not forget to extend my gratitude to you my honour sister from a wanderful mother *YA HAJJA* (mom ihsan), wan't you to know am always remember and loving u in my holly heart, thanks be to God for having u in my life, i wish u many more ALLAH'S khair in ur life, ur billy is always care and luv u muchโค๐Ÿ‘๐Ÿป_

๐Ÿ’ŽPage_____76๐Ÿ’Ž


Ko kad'an dr. baiyi abunda bayada zarafi ba. Kuma baici bashi ba saboda tsoron abubuwan da suka faru ga rayuwar mahaifinsa da kuma ta mahaifin Muhib don haka yayi alk'awarin da izinin Allah bazaiyi abunda yafi k'arfin saba wanda hakan yasa

Please Login or Register in order to submit comment