Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lipstick d'in data shafa a lab'b'anta sannan ya d'ago idanuwansa arine yace

"Gashi nabiya afad'amun" wata irin kunyace tarufeta da tasata yunk'urin mik'ewa daga kan cinyarsa da take zaune yayi saurin rik'eta, kanta naduk'e tace

"Bilkisu" a hankali ya saki hannunta, zuciyarsa nabugawa jin sunan data anbata, shiru yayi na mintota kafin ya d'ago kansa ya kalleta

"Shi kike so? Kuma ya yimaki?" Kad'a kanta tayi had'e da cewa

"Eh"

"Shikenan Allah ya albarkaci rayuwarta kuma yaraya mana ita"

"Amin ya Allah" tafad'a tare da bud'e wardrobe taciro masa wata shadda sabuwa dark pink sai k'yalli takeyi, taimaka masa tayi yasa sannan ta d'auko masa takalminsa da hula mai k'ube ta daidaita zamanta akansa, agogonsa na rolex dake kan madubi ta d'auko ta saka masa sannan ta d'auko turare ta feshe masa jikinsa dashi, hannunsa tarik'a ta kaishi agaban madubi tana murmushi, kallon kansa yayi yaga yanda yayi matuk'ar kyau, juyowa yayi shima yana murmushin tare da rungumota ajikinsa sosai yayi kissing d'inta a forehead yace

"Nagode sosai oum little, Allah yayi maki albarka"

"Amin yaya" tafad'a tana d'an turo bakinta gaba kafin tace "Ai dai ba sunan 'yata little ba"

Dariya yayi had'e da jamata hanci kad'an sannan yace

"Basmaty ba kunya, agabana kike cewa 'yarki?"

"Eh mana zan iya fad'ama agaban kowa, yanda nake sonta ko kaina banaso haka infact dia baby is my everything, she mean alot to me and I proudly to have her in my life" Saida tayi murmushi sannnan taci gaba da cewa "Bilkisu kenan baiwar Allah, my sister my dota" tak'arasa maganar had'e da d'okarta tayi kissing d'inta, bata ankara ba sai dai ganin hasken camera tayi ya d'aukesu, d'ago kai tayi da niyar yimasa magana ya sake d'aukarsu wani sannan yadawo kusa da ita ya maido camerar agaba ya d'aukesu gaba d'aya fiye da sau biyar, karb'ar babyn yayi ya ajiye gefe sannan ya jawota ajikinsa yayi masu wani su biyu kad'ai, wani murmushine yabayyana a fuskarta wanda zai iya fassara maka irin farincikin dake tattare da ita.

Sallamar da suka jiyo a palour tasa yayi saurin kad'a wayarsa a aljihu, ya d'auki little yafito, harararsa Umma tayi tana fad'in,

"Ai nazata baka shirya bane in sab'a maka don nasan 'yata batada matsala" karb'ar little tayi a hannunsa sannan tawuce tana fad'in

"Ku ake jira kufito rana tasoma yi"

Tsaye ya iskota tana juye tsakiyar d'akin tana kuka, tanajin muryarsa tayi saurin goge hawayenta tare da yafo mayafinta akai,

"Basmaty fito muje ko? Umma tace mukad'ai ake jira" sannan yajuya tana biye dashi, har takai bakin k'ofa tadawo da sauri tare da bud'e wardrobe ta hankad'a tsakiyar kayansa ta ajiye wani abu sannan tayi saurin ficewa d'akin tana goge hawayen idanuwanta.

A garin k.d kuwa shirye shirye akeyi sosai na isowarsu, musamman dady yasa aka sake gyra asalin d'akinau ita da Basmah aka chanza sababbin kayan d'aki akasa wasu ga d'an gadon jarirai da sauran kayan kula da yara abun gwanin ban sha'awa, gida yacika da 'yan uwa da abokanan arzik'i sosai gasu aunty faraaha da Batool duk sun iso, ga family d'insu alhaji bukar da kabiru dasu baba k'arami duk sun iso tarbonsu kai kace ranar ake suna, saboda tunda tayi aure kusan shekara bata samu tazo ganin gidaba, shiyasa kowa yake mararin ganinta,

Basu iso ba sai misalin k'arfe sha d'aya na rana saboda matsalar da aka samu acan filin jirgin kafin su taso amma alhamdulillah sun iso lafiya,

Murna kam ba'a magana awajen mom haka Batool da Billy kamar zasu canye little da tunda suka iso suka kamata suka rik'e, Batool ce ta kalli Billy tace

"Twiny Allah yarinyar nan duk dake take kama" murmushi Billy tayi had'e da cewa

"a'a twiny aikam dai da abbanta take kama ba niba",

Shi kuma dady da yaga yarinyar cewa yayi da baba k'arami take kama, ai kuwa duk akasa dariya a palourn, kallon babyn baba k'arami yayi had'e karb'arta yace

"wannan yarinya duk wanda yasan bababnta, yana ganinta yasan dashi take kama bani ba, indai kamfen ne kukeyi mata to kuma dena don bazanyi da mai fuskar 'yan china ba" sake kwashewa da dariya akayi kafin alhaji bukar da Umma suce

"To ai jiya iyau, duk abunda yayi ka shi yayi Mahmud kuma shi yayi Bilkisu, don haka dai kaga zancen duk d'ayane angulu ta koma komawa gidanta na tsamiya"

"Ahh to indai hakane jinina mai k'arfine gashi har yafara kaiwa ga jikoki"

Nan dai akayita farinciki da murnar sake had'uwarsu akaro na biyu bayan aurensu, kuma kowa yayi farinciki jin sunan da suka rad'awa 'yarsu, Billy kam harda kukan dad'i tayi jin cewa ita 'yar uwarta tayiwa takwara,

Kasancewar yau su Umma zasu koma yasa dady yanemi keb'ewa da alhaji mahaifin Mahmud da kuma 'yar uwarsa yayi masu godiya sosai bisa kulawa da suka bawa Basmah cikin so da qauna, ga kayan da sukazo dasu har akwatuna set biyu na baby guda na Basmah guda, sai yaga kamar hidimar tayi yawa, nan suma suka nuna masa cewa ai komai sukayiwa Basmah 'yar suce kuma hidima dole suyi tunda suna farinciki da kyautar da Allah yayiwa d'an nasu,

Ahaka dai suka rabu kowa cikin farinciki da k'aunar juna.

Ana gobe suna 'yan uwan Mahmud nawajen mahaifinsa suka iso garin tare dashi, tarba ta musamman akayi masu bayan angyara masu part d'in da yaya Mahmud yabari, duk wani abun da zasu buk'ata antanadar masu,

Bukine na musamman aka had'a don har hall aka kama musamman don gabatar da walima, tunda sassafe aka fara shire shiren suna,tsayawa fad'ar irin kyawon da Basmah tayi ita da baby b'annar lokacine, sunsha kyau sosai kamar ba gobe, Batool ma tunda sassafe ta iso ita da aunty faraaha da mu'azzam d'inta da yayi wayau sosai,

Mamy ma ta iso da ita su mom ke duk hidimar daya kamata, papi da Hajia kaka ma suma sun iso sai hidima ake guda narwa,

Duk irin yanayin da Ummi kejin kanta aciki haka tadaure akayita 'yan aikace aikace da ita, mom na tsokanarta wai taje ta huta karta haihu abakin murhu, itadai Ummi dariya tayi kafin tace

"Ba ruwanki ko baisan murhu zai haihu, biki namu nida 'yatah dole ingwadi uwar d'iya nake"

"Ai kuwa mungani amma dai ai aje ahuta" dariya Ummi tayi had'e da cewa

"Aifa sai kiyi, badai so kike ace ganican kwance ba? Kice anyi uwa kwance d'iya kwance? To da yardar Allah hakanne bazaki gani ba"

Gaba d'aya dariya akasa wajen kowa fuskarsa d'auke da farinciki da sha'awar su mom yanda suke zaunensu lafiya.

Ana gama sallar azahar aka kwasa sai wajen walimar da dady ya shirya masu, saida kowa ya hallara sannan maijego Basmah da Mahmud suka shigo,

Sanye take cikin wata rantsattsiyar shadda mai tsananin kyau da tsada royal blue anyi mata aiki pink da gyalenta shima pink shima sai takalmi, shi kuma gaba d'aya royal blue ce don banko sukayi hular kansa kad'aice pink irin wacce ake lank'wasawar nan gefe (yoruba style) sunyi matuk'ar kyau sosai bayansu kuma Batool da Billy ne sun takikke masu baya cikin ado na musamman da burgewa, billy ce tarik'o little itama tasha doguwar rigarta ta 'yan kanti pink colour ansa mata baby band akai royal blue abun gwanin ban sha'awa,

Cikin farinciki da natsuwa akayi walimar har aka k'are, kyautukka kuwa maijego da 'yarta sunsha wajen abokanan dady babu adadi,

Kallo d'aya Billy tayi masu ta d'auke kai saboda yanda sukayi matuk'ar kyau sai taji wani abun nason motsa mata azuciya, murmushi n qarfin hali tayi tare da korar shed'an tana fad'in "qadarallahu wama sha'a fa'ala" sannan tabar wajen tanufi wajen tarbon bak'i dake isowa, anci ansha antaya little Billy murnar isowarta duniya, hotuna kuwa duk inda kajuya camerorine ana vedioting da d'aukar hoto, tsabar farinci both Basmah da Mahmoud bakinsu kasa rufuwa yayi,

Dr Ahmad ma da abokinsa Khalid sun samu hallarar walimar inda yayi bud'i tare da fatar Allah ya nuna masa shima da teemarsa sun rik'a babynsu ahannu,

Zuwa k'arfe hud'u aka kammala waleemar bayan anraba kayan buki masu d'auke da hoton baby da aka rubutawa THANKS FOR ENJOYING WITH US IN OUR BABY NAMING CEREMONY BILKISU MAHMUD (little Billy), sannan kowa ya watse ya nufi gida.

Agajiye Basmah da baby suka isa gida saboda hayaniya da zirga zirgar da suka sha fama da ita.

Da daddare bayan tayo wanka itama little anyi mata wanka tahaye kan gado saiga yaya Mahmoud ya shigo

"Sannu amaryar jego, yau kunsha hidima" yafad'a yana k'ok'arin zama kan gadon, murmushi tayi masa tana daga kwance, kafin tace "Yawwa angon k'arni, ai hidimar tamuce duka, ya gajiya?"

"Alhamdulillah ya k'arfin jikinki?"

"Naji sauk'i sosai ko dambe zan iyayi"

"Ah lallai kice komai normal, to bari inzo infad'a maki wata magana" yafad'a tare da hayewa kan gadon yayi mata rumfa, juyawa tayi yanda fuskarta na kallon tasa had'e da jawosa tayi kissing d'in lips d'insa sannan tace

"Go ahead in abun kunya zakayi a gidan sarakai ni am not afraid of anything"

"Haba! Meyasa?"

"Saboda nasan mutuwa zanyi" da sauri ya d'agata had'e da fad'awa gefenta cikin tashin hankali yace

"Meye kike fad'a haka Basmah, kina so kishiga hurumin Allah ne? Sanin lokacin mutuwar mutum a hannun Allah yake kuma gaibine don me zaki ce haka?"

Ganin yanda hankalinsa ya tashi yasa ta jiyo kwancinta suna fiskantar juna sannan tace

"Am sorry abban bilqees kuma yayan bilqees, kasan dolene duk wata rayuwa ta d'and'ana mutuwa, shiyasa kaji nafad'i haka amma i beg of you koda namutu kada kutab'a mantawa dani acikin zuciyarka kuma kayafemun duk abunda nayi maka, ka kula da 'yarmu, ka kawo 'yar uwata tamaye mata gurbina sannan kada soyayyar da kake yimata tarufe maka idanuwa tasa kayi rauni wajen barin momynta yimata tarbiya"

Tashi yayi zaune yana kallonta had'e da cewa

"Wai meye kike fad'a haka, don Allah kidena wannan tunanin, inada tabbaci akan insha Allah zamu rayu tare da 'yarmu kuma muyi mata tarbiya atare har zuwa girmanta, kada ki aminta akan cewa ciwo mutuwane, hakan ba gaskiya bane"

Murmushi tayi had'e da aza hannunta agefen fuskarsa tana d'an shafawa ahankali shima ya d'ora hannun nasa akan nata yace

"Basmah! Believe me cuta ba mutuwa bace, sau nawa Allah yakarb'i lafiyayye yabar marar lafiya? Kiyarda cewa sai lokacin bawa yayi yake mutuwa tsananin ciwo bayasa mutuwa saidai awahala"

"Yaya i do believed, amma akwai kuskure da kuma raunin imani ga duk bawan da baya tunanin mutuwa arayuwarsa, laifine bawa yadinga tunanin cewa bai dace wata rayuwa ta mutuba saboda rayuwar ba'a hannunsa take ba, Allah yana karb'ar rayuwar bawa aduk lokacin da yaso kuma alokacin da yaga dacewar haka agaresa, yarda tare da yak'ini akan zuwan mutuwa akowane lokaci shikesa bawa barranta daga sab'on Allah, tunani da kuma sakankancewa akan cewa ai bai kamata wane ya mutuba saboda wani dalili shine shiga hurumin Allah, muyarda da ikon Allah da kuma tsarinsa akoda yaushe saimu samu barranta daga garesa, Allah baya barin wani don wani domin da kansa yacewa jabrilu ya fad'awa annabinmu cewa " _INNAKA MAYYITUM WA ANTUM MAYYITUUN_"

Duk inda ilahirin jikin Mahmud yake saida yayi sanyi jin kalaman dake fitowa abakin Basmah,

Jawota yayi ajikinsa ya rungumeta sosai yana fad'in "karki damu insha Allah bazaki mutu yanzu ba Basmaty"

Baibar d'akin ba sai wucewar k'arfe sha biyu nadare sannan sukayi sallama, bai jima da fitaba saiga Billy tashigo don dama tund'azu tazo part d'in, muryarsa da taji yasata komawa wajen mom suna fira kafin ya wuce, dama tun ranar da Basmah tadawo gida tare suke kwana, kwance ta iskota ta aza Billy saman cikinta, fad'awa tayi akan gadan tana fad'in

"Yayya barka da soyewa, gaskiya yau yaya yashiga hak'k'ina, tund'azu nakeji bacci yazo ya takurani"

"Kai sisto yayan naki? da bakinki kike fad'ar haka ko?, insha Allah saina fad'a masa" dariya Billy tayi tare da jawo d'an net d'in da akesa little Billy aciki ta ajiye a tsakiyarsu tagyara shimfid'ar ciki sannan tamik'a hannu zata d'auketa, k'ok'arin mik'ewa zaune da taga Basmah nayi yasa tafasa tare da jawo pillow zata kwanta don tazata nono zata bata sai taji takira sunanta,

"Na'am yayya" tafad'a had'e da tasowa tana kallonta, murmushi tayi mata had'e da d'ora mata little dake bacci saman jikinta sannan tace

"Sisto ki d'auka kece kika haifi little da cikinki, shin wace irin rayuwa zaki gina mata tun tasowarta har zuwa lokacin data girma"

"Kai yayya wannan wace irin tambayace haka a wannan tsohon dare?"

Rik'o hannunta tayi cikin hikima tace "ina so inkoya wani abu daga gareki nasan zan amfana, just answer me pls."

Shiru Billy tayi kafin tace

"Zan gina mata rayuwa bisa turbar tsoron Allah da sanin hakk'ok'ansa akanta domin hakan zaisa nima tasan hakkokana da suke akanta, zanyi hak'uri da kurakuranta kafin tagirma amma zanyimata hukunci bisa isgilancinta idan tagirma, zan bata kulawa kuma najata ajinina shixaisa tasan muhimmancina sannan zanyi mata tarbiya ingantacciya tayanda zata zamo mai alfahari dani da kuma yimani addu'a idan bana raye daga k'arshe kuma zan nuna mata so bisa horo da turbar hak'uri da juriya acikin al'amurranta"

"Alhamdulillah" Basmah tafad'a tare da cewa

"Bilkisu ina so kisaka aranki cewa little 'yarki ce ta duniya da lahira, kuma kinada iko akanta ko ina araye ko bana raye nabaki amanarta kuma ina fatar zaki kula da ita bisa wud'ancan tsari da buruka da kike dasu"

Billy kam ko kad'an bata kawo komai arantaba tace

"Yayya kenan ai indai baso kike kiraba d'aya biyu ba, babu batun kibani amanarta domin kuwa zan iya kula da ita fiye da tsammaninki, tunda nima 'yatah ce koba haka ba?"

"Hakane sistonah afuwan kinji Billy uwar Billy" dariya tayi tare da sanya little cikin net d'inta sannan takoma ta kwanta abunta. Basmah kuwa daren kwana tayi zaune tana kallon little cike da tausayinta saboda tanajinta awani yanayi da bazata iya fassara shiba, ba abunda takeji azuciyarta irin maraicin uwa da little zata tashi dashi amma awani b'angare na zuciyarta idan tatuna cewa 'yar uwarta zata kula mata da ita kuma zata tashi a hannun nagartaccin mutane irin family d'insu sai taji ta samu natsuwa sosai, ana haka misalin biyu da rabi na dare little ta tashi tafara k'ananun kuka, k'ok'arin bata nono tayi amma tak'i karb'a sai kuka takeyi, tun tanayi ahankali har tafara d'aga murya, tashi tayi tagoyata tana jijjigata amma tak'iyin shiru, momce tashigo dai dailokacin da Billy itama tafarka saboda kukan yarinyar daya tadasu, karb'arta tayi tana jijjigata tare da cewa Basmah

"Kin bata nono"

"Eh amma tak'i karb'a" jijjigata akayitayi amma tak'iyin shiru, wani irin kuka Basmah tafashe dashi tare da duk'ewa gaban mom tana fad'in

"Mom dama haka kikasha wahalar renonmu tare da kula da rayuwarmu har muka girma bayan wahalar d'aukar ciki data haihuwa da kika sha amma duk kika jure rana d'aya baki tab'a nuna gazawa damu ba kullum burinki musamu farinciki da ingantacciyar rayuwa? Mom da wane abu zamu saka maki dashi? a gaskiya na jinjina maki kuma Ina alfaharin zamowarki mahaifiya agareni, mom don Allah kiyafemun duk wata wahala da kika sha tawa da kuma b'acin ran dana saki arayuwa"

Haka kurum mom taji jikinta yayi sanyi, wani b'angaren zuciyarta ne yabata ai saboda fitinar da little keyimata da 'yan matsalolin reno data fara fuskanta yasata furta wud'annan kalaman, kallonta tayi cikin yanayin bacci dake fuskarta bai saketa ba tanaci gaba da girgiza little tace

"Basmah kenan ai indai renone haka yake sai ka kai zuciya nesa, ai yarinyar nanma batada wata rigima don tunda kukazo bantab'a jin kukan taba, yauma dai inaga da akwai abunda kedamunta" baki ta'aza saiti saman cibiyarta ta busa cikin da d'an k'arfi ko cikin natane ke ciwo amma taji kukan bai canza ba, ya tsunta biyu tasa tana daddanna mata kunnenta amma shima taji kukan nata ya gagara canzawa,

Billy ce ta matso takarb'eta hannun mom tare da d'orata saman kafad'arta tana d'an jijjigata ahankali sai gashi tayi shiru, inda Basmah take zaune k'asan k'afafuwan mom tajeta aza mata ita ahankali had'e da cewa

"Yayya karbeta kibata nono kigani ko zata karb'a" cikin sa'a kuwa tana bata takarb'a tanasha har bacci ya sake d'aukarta.

"Ja'ira kin koma baccin bacinmu kin hanamu ko?" Mom tafad'a tana zungureta tare da tashi ta koma d'akinta, murmushi sukayi kafin Billy ta karb'eta had'e da cewa

"Yayya da alama bakiyi bacci ba tun d'azu,kawota kije kikwanta bari nagoyata" tashi Basmah tayi cikin rashin k'warin jiki ta'azawa Billy ita abaya sannan taje tayo arwalar bacci tahaye gado abinta ta kwanta, addu'o'in bacci tayi sannan tarufe idanuwanta.

Tunda asuba yaya Mahmud ya shigo part d'in saboda kukan little da yakeji, rashin baccin da basuyi ba jiya yasa baccin nasu yayi nauyi sosai suka kasa jin kukan little, a bakin k'ofa ya tsaya yayi knocking had'e da cewa

"Basmah, Basmah kitashi ki kama yarinyar nantana kuka, wannan wane irin nauyin baccine haka?" Yana gama fad'ar haka yajuya ya wuce masallaci, knocking d'in da yayi yasa Billy ta tashi taga little rungume ajikin Basmah sai kuka takeyi fuskarta tayi jajir da alama tajima tana kukan, d'aukarta tayi sannan ta shiga bubbuga hannun Basmah tana fad'in "yayya, yayya kitashi tun d'azu little sai faman kuka takeyi kibata nono" ganin tayi ko kad'an Basmah bata motsaba balle ta tashi, hakan yasa tayi tunanin k'ila saboda bata samu tayi bacci sosai bane shiyasa takasa farkawa, fita tayi da little dake hannunta tana kuka tayi d'akin mom da ita, koda tashiga ta tarar tana sallah don itama bubbuga k'ofar da Mahmud yayine ya tayar da ita, jijjigata taci gaba dayi kafin tagama sallar, tana gamawa tamik'a mata ita had'e da cewa "mom karb'e insamu inyi sallah, nayi tada yayya bata tashiba may be baccin yayi mata nauyi don jiya batayi bacci da wuriba"

"A'a to kuma shine saiki k'yaleta yarinya nafaman kuka bazaki tasheta tabata nono ba" mom tafad'a tare da karb'ar little tana cigaba da cewa

"Bilkisu Allah dai yasa lafiya kike wannan kuka haka da kike faman yi tunjiya" had'e da mik'ewa tabar d'akin d'auke da ita a hannu, dady ne ya shigo shida Mahmud dasu Bassam dawowarsu masallaci kenan saboda kukan da takeyi yasa sukayo part d'in,

"Ke amaryata lafiya yau kika tashemu tunda asuba da kuka, inaita Basmah d'in take data barta tanata faman wannan kukan" dady yafad'a yana k'ok'arin karb'arta ahannun mom, shidai Mahmud ji yake kamar yaje yajawo Basmah saboda kukan da yarinyar keyi amma kunya bazata barshiba, d'akin mom tawuce tare da nufar inda Basmah take kwance, tada ita tayitayi amma taga bata motsaba, cikin tsoro da yanayin da taga Basmar keciki tad'aga hannunta gabanta nafad'uwa, ganin hannun tayi yayi luuu.k'asa ya koma, cikin firgita tace

"Alhaji, alhaji" da k'arfi" da sauri alhaji ya shiga cikin d'akin rik'e da little Mahmud na biye dashi Yana fad'in "lafiya momyn yara?" cikin rikicewa mom tace "Alhaji Basmah bata motsi.." ai kamar karta rufe baki Mahmud ya hau gadon tare da rungumota ajikinsa yana fad'in "Basmah, Basmah, oum little, Basmaty" Yana d'an bubbuga fuskarta amma ina.. Billy ce data shigo d'akin lokacin bayan ta ida kammala sallarta a d'akin mom dady ya mik'a mata little sannan shima yamatsa wajen gadon jikinsa amace, hannunsa ya kara a hancinta, ya aza yatsunsa biyu a jijiyar hannunta, sannan ya sake aza yatsunsa akan jijiyar wuyanta,

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun," yafad'a har sau uku kafin yace

"Allah yayi mata rasuwa" daidai lokacin Ummi itama tashigo tana takawa da k'yar don dama jiya tanajin kukan yarinyar saboda itama batayi baccin ba a zaune takwana, wata irin k'ara Mahmud yayi tare da k'ank'ame Basmah ajikinsa yana kuka Yana fad'in

"No..kada kitafi kibarni Basmah, kin sani tare zamu rayu mukula da 'yarmu don allah kada kitafi kibarni"

Mom kuwa mutuwar tsaye tayi tana hawayen itama innalillahi wa inna ilaihirrajiun kawai take maimaitawa,

Cikin k'arfin hali dady ya mik'e zai fita kawai yaga Billy dake rik'e da little tayi suuuuu.. tafad'i k'asa asume, da sauri Ummi tarik'o little d'in tana cije baki tayi k'asa zaune rungume da ita idanuwanta na tsiyayar da hawaye, shikuma dady kan Billy yayi tare da bud'e fridge ya d'auko ruwa ya yayyafa mata sannan tafarfad'o, kuka takeyi sosai tare da nufar gadon tana fad'in.

"Yayya kada kitafi kibarmu, ni Batool da kuma yaya duk munada buk'atarki ga little itama tanada buk'atarki sosai, yaya don Allah kace yayya ta tashi" haka Billy tayita sabbatu tana kuka hakama shima Mahmud Saida dady yayi da gaske sannan ya b'anb'are gawarta ajikinsa, ya kwantar da ita had'e da lullub'eta sannan yafita dashi,

Yaya Mahmud dady yakira sannan ya papi da Dr. Ahmad ya sanar dasu halin da ake ciki, gaba d'ayansu babu wanda yafad'awa matarsa halin da akeciki kawai cewa sukayi su shirya zasuje wani waje,

Nan take kafin safe mutuwar Basmah ta mamaye ko ina, duk wanda yaji sai jikinsa ya mutu tare da shiga tashin hankali, sosai jimamin mutuwarta ya ratsa zukatan mutane da yawa tunawa da ganinta da sukayi jiya.

Batool kam kasa k'arasawa tayi da k'afafuwanta lokacin da suka wucikke k'ofar gidan cike da mutane ana yimata gaisuwa saida Dr Ahmad yarik'ota k'afuwanta narawa, dagudu ta kwace hannunta tafad'a cikin d'akinsu, kwance tahango gawar Basmah anlullub'eta ga Billy zaune sai sabbatu takeyi, k'arasowa tayi jiri na d'ibarta tabud'e Basmah dake kwance fuskarta sai annuri take fitarwa zaka d'auka murmushi takeyi, da sauri taja baya tana k'ok'arin fad'uwa yaya Mahmud ya tarota, d'ago kai tayi takallesa tqna nuna gawar Basmah had'e da cewa

"Yaya bata mutuba, don Allah katasheta" tana kuka sosai, rungumeta yayi shima yana kuka yakasa cewa komai.

Ummi kuwa tsabar firgita yasa tuni labari ya canza mata a inda take zaune rik'e da little saidai mom tajiyo tana wani irin nishi dake kama da naquda tana cije baki, da sauri mom tamik'e ta karb'i little hannunta tamik'awa Billy da itama yanayin da sukaji ummin ta shiga ya maido da hankalinsu wajen sannan tarik'ata ta wuce d'akinta da ita,

Kafin agama shirya gawar Basmah Ummi ta haifo 'yarta k'atuwa tubarkallah amma saboda yanayin da ake ciki babu wani annuri balle farinciki a fuskokinsu hatta Ummi, "Alhamdulillah" kad'ai tafurta bayan ta haihu saboda jimamin yanayin da take ciki,

Kan kace me, tuni rasuwar Basmah da haihuwar Ummi tawatsu agarin inda da misalin k'arfe shabiyu aka fita da gawar Basmah don a sallaceta zuwa gidanta na gaskiya, ana d'auko gawar Billy ta taso rik'e da little tana kuka, ana rirrik'eta nan ta sake fad'uwa asume akayi kanta aka shiga da ita cikin d'aki, Batool ma tamkar mutum mutum takoma ba um balle a'a, mom kuwa Allah yasa mata juriya da dangana banda addu'a da takeyi tana fad'in "Basmah nayafe maki, ubangiji Allah yakarb'i bak'uncinki, Allah ya albarkaci 'yarki ya yafe maki dukan zunubbanki"

"Har aka kai Basmah gidanta na gaskiya Billy bata farfad'o ba, hatta wud'anda sukazo jana'izar Basmah sun tausayawa Mahmoud da yaya mahmud, baranma da suka shigo cikin gida wajen gaisuwa duk wanda ya shigo sai yafita da hawaye saboda tausayin halin da wud'annan 'yan uwa suka shiga na rashin 'yar uwarsu,

Dady ma duk da yawan mutanen da sukazo wajen gaisuwa hakan bai hanasa shigewa d'akinsa ba yayi kuka sosai yana mai rok'a mata gafarar Allah tare da Allah yaraya mata abunda tabari, yana zaune Umman borno tashigo d'auke da jaririyar da Ummi ta haifa, gaisuwa suka yiwa juna sannan tamik'a masa jaririyar tana fad'in

"Yaya ga kyautar da Allah yayi maka, muyi hak'uri mu ajiye kuka gefe mugodewa Allah daya bamu kuma yakarb'a, kai 'ya'ya shida gareka aka karb'e maka d'aya, adaidai wannan lokacin akwai wanda d'aya ke garesa kuma aka karb'e masa shin ashe kai bazaka zamo cikin bayin Allah masu godiya ba?"

Karb'ar jaririyar yayi da gaba d'aya fuskarta tamkar ta Basmah lokacin da aka haifeta, murmushi yayi dake nuna iyakarsa bakin leb'ensa sannan yace

"Allah Akbar, Allahu Akbar, Allah kaine keda ikonka kaine mai jujjuya al'amurranka yanda kake so, nagode maka daka karb'ar mun 'ya kuma kabani wata adaidai lokacin, ya Allah ba wayona bane ni'imar kace da kuma baiwarka" kallon Umma yayi had'e da cewa

"Hafsatu dubi ikon Allah, gaba d'aya yarinyar nan da Basmah take kama" had'e da nuna mata fuskarta, goge hawaye Umma tayi da gefen mayafinta kafin tace

"Nagani yaya, rabon sai wannan tazo aduniya yasa waccan tatafi, ya Allah kayafewa Basmah" tak'are maganar tare da fashewa da kuka.

Hud'uba dady yayiwa jaririyar had'e da yimata hud'uba da sunan Basmah sannan ya mik'awa Umma ita

"Hafsatu afad'a masu cewa taci sunan yayarta Basmah" dady yafad'a yana goge hawayen idonsa.

"Allahu Akbar, Basmah ta tafi Basmah tadawo, ubangiji Allah ya rayata " Umma tafad'a tare da ficewa takoma cikin gida, mik'ewa dady yayi shima ya wanko fuskarsa sannan yakoma waje wajen amsar gaisuwa...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA

Please Login or Register in order to submit comment