Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace

"Alhaji bari naje gida nacanzo kayana, naga ashe duk sun lalace, ga wannan idan anfito da ita aka tambayeku takardar shedar biyan kud'in aikin saika basu, insha Allah bazan jimaba zandawo" fashewa da kuka alhaji yayi kamar ransa zai fita yana rok'on dr. Ahmad ya yafe masa bisa zamowarsa na sanadiyar rasa mahaifinsa har yana rik'e k'afafuwansa, ja dabaya yayi had'e da sa hannuwansa ya d'agosa yana fad'in "haba alhaji sau nawa zance maka komai yawuce babu komai kamanta"

"Wlh bazan iya tsaida kaina daga rok'onka ba saboda kunyar alkhairin daka ramamani da sharrin da nayimaka, don Allah kayafe mani Ahmad"

"Shikenan alhaji naji kuma nayafe maka, kaje kamatsa kusa kaida iyalinka kafin afiddo maku da jaririn kuma karok'i Allah yasa ayi nasarar ceton uwar da abunda ke cikinta"

"To Ahmad nagode nagode Allah yajik'an mahaifinka kuma ya gafarta masa"

"Amin alhaji bari naje nadawo"

Yana fitowa asibiti saiga kiran Batool yashigo awayarsa, rejecting yayi sannan yayi calling nata back daidai lokacin daya tare maimashin yahau sannan yace

"Hell my amarya to be"

"Na'am my dr. Ya kake ya k'ok'ari?"

"Alhamdulillah hop kina lafiya?"

"Sosai kuwa don gani a asibiti nakawo wata mata zata haihu har nabata jinina gora biyu amatsayin jahadi, kaga kuwa ina lafiya klw my dr." Murmushi yayi don yatabbata sister faraahace takirata tafad'a mata abunda yafaru sannan yace

"Faraaha ko?" Saida tayi dariyar da sautinta yadakar masa zuciya sannan tace

"A'a aunty faraaha dai, Weldone my ango gaskiya kaid'in namusammanne kamar yanda nafad'a maka, naji dad'i sosai da kazamo mai taimako natabbata kaida ahalinka bazamu tab'a tozarta ba aduniya in sha Allah, dama just call u to appreciate and telling I love u so much my man, always proud of you my ango and lucky to have you milkheart" tana gama fad'ar haka takatse wayar cike dajin kunya tana dariya, ciro wayar yayi akunnensa yana kallon screen d'inta yayi murmushi tare da cewa "I luv you too my fatima, ked'in tamusammance kema"

Muryar maimashin d'in yaji yana cewa "Ranka yadad'e halan sabon aurene kayi kuma budurwa ko, nima cikin shekarar nan nakeso nasamo 'yar yarinya ko ak'auyene tadinga suburbud'omun kalamai irin haka inyita nishad'i abuna" duk da miskilancin dr.Ahmad da rashin son maganarsa saida abun yabashi dariya, kafad'un mai mashin d'in yad'aga had'e da cewa

"Kai malam k'asimu, bana son munafucci da sauraren abunda ba'a kasa da kaiba, maza nik'a kaini anguwar g.r.a nasamu nafita wannan shigar"

"Hhhh ai yallab'ai balane sunana ba k'asimu ba"

"What ever dai sunanka karik'e matarka gam inaga zaifi maka"

Dr Ahmad baijima da fitowa ba sai gashi anfitowa da alhaji Tukur da jariri anan nad'e cikin d'an kwalin matar anmik'a masu da sauri alhaji yakarb'a yana kallon jaririn yace "masha Allah dr. ansauka ko?" Cikin damuwa dr yace

"Alhamdulillah anyi nasarar ciro yaron d'and'ane amma saidai kuyi hak'uri ita uwar Allah yakarb'i abussa" baya baya alhaji yayi da kad'an yafad'i yana fad'in "innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, Allah sarki jamila shikenan kitafi kinbarmu , duk k'ok'arin da yaronnan yayi don ganin rayuwarki tatsira dake da jaririnnan ashe Allah yayi ke bazaki tashiba," rik'osa matansa sukayi suka zaunar dashi suma suna kuka tare da fad'in alkhairinta suna cewa sun yafemata, sosai alhaji yarik'e jaririn yana kallonsa jawur dashi amma ba uwa tatafi tabarshi, matsowa dr yayi had'e da bubbuga kafad'arsa yace

"Sorry yanzu kushirya zuwa anjima za'a baku gawar"

Dr Ahmad kuwa yana zuwa gida yafad'a toilet yayo wanka sosai sannan yafito yana labartawa mamy abunda kefaruwa da alhaji Tukur wanda garin taimakon matarsa ne yab'ato kayansa da jini, sosai mamy ta tausaya masa tare da fatar Allah yasa ayi nasarar wajen aikin, kud'in hannunta yace tabashi ya ida cikashe kud'in alhaji daya tab'a akayiwa matarsa aiki sannan yaci abincin agurguje, yana gamawa yayiwa mamy sallama sannan yakoma asibitin, yana shigowa yaci karo da sister faraaha zata fita idanuwanta jawur da alamar tayi kuka, nan take sanar dashi rasuwar matar alhaji Tukur cikin tausayi da shaida masa tabar jariri yana can ahannunsu rungume gwanin ban tausayi, sosai dr Ahmad ya girgiza da rasuwar matar duk da bai santaba had'e da nema mata ga farar Allah, sallama sukayi da faraaha sannan ya k'arasa wajen alhajin, tasowa yayi tare da mik'a masa jaririn yana kuka yace

"Ahmad kaga ikon Allah ko? Yakarb'i ajiyar daya bamu ya sake bamu kyautar wata ya Allah kaba wannan yaro dangana"

Tunda dr Ahmad ya d'ora idanuwansa afuskar jaririn yaji k'aunar yaron tashiga ransa sosai kuma yaji tausayin maraicin uwa da zaiyi arayuwarsa.

Cikin k'ank'anen lokaci aka basu gawar suka tafi da ita akayimata wanka aka suturceta tare da kaita gidanta na gaskiya duk tare da dr Ahmad, bayan kwana uku dr.Ahmad yakawo mamy tayiwa alhaji Tukur gaisuwa sannan ya d'auko kud'insa da yake biyar mahaifinshi dubu d'ari uku da hamsin yabashi tare da cewa

"Alhaji ga kud'in da kake biyar Abbanah don Allah kayi hak'urin rashin samunsu da bakayi ba akan lokaci, ubangiji Allah yajik'ansu duka kuma ya gafarta masu, kuku alhaji Tukur yafashe dashi had'e da cewa

"Don Allah Ahmad kuyafemun, bazan karb'i kud'innan ba ko kad'an duba da halacci da kuma taimakon da kayimun, haba Ahmad ai da nazama butulu"

"A'a alhaji ai hak'k'in kane kuma wlh duk taimakon danayi maka nayine don Allah badon komai ba saboda haka kakarb'i abunka nasan bazaka rasa abunyi dasu ba" k'in karb'a alhaji yayi saida mak'wabcinsa daya bashi aron wani d'aki agidansa shida iyalansa yasa baki sannan yakarb'a koshi saidai dr.Ahmad ya ajiye masa kud'in ak'asa gabansa, kan alhaji duk'e ak'asa yana kuka yadinga yiwa mamy godiya tare dasawa dr Ahmad albarka sosai sannan sukayi maau sallama suka wuce batare daya d'ago kai sunk'ara had'a ido da mamy ba saboda kunya, har sunkai k'ofar fita ya dakatar dasu tahanyar cewa

"Ahmad don Allah kujirani ina zuwa" cikin gida yashiga jaririn na hannun uwar gidansa ya karb'esa, wajensu mamy yanufo tare da durk'usawa agabanta ya mik'a mata jaririn.

"Wannan d'ankine na bakishi duniya da lahira, Allah da mala'ikunsa sune sheda akan haka sai kuma wud'annan bayin Allah dake zagaye dani, banaso kirenesa amatsayin kyautar da nabaku, ina so kirenesane a matsayin d'anki dake kika haifi abunki ina fatar wannan zai zamo kyautatawar da zan iya yimaku aduniya bisa rabaku da farincikinku da nayi, sannan tun ranar da aka haifesa narad'a masa suna Bashar, amma idan kunso zaku iya canza masa da wanda kuke so" karbar yaron mamy tayi jikinta har yana tsima saboda soyayya da wata irin k'aunarsa da taji tana ratsata, idanunta nahawaye takalli alhaji Tukur tace...








*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____71💎


Alhaji taya zakayi tunanin bamu d'an d'anka alhalin kana cike da alhini da rad'ad'in rashin mahaifiyarsa, sai nake tunanin idan kayi hakan kewar zata zame maka biyu, karik'e yaronka mu azuciyarmu babu komai har ga Allah munyafe maka duk abunda yafaru koba komai muma Allah zai iya dubonmu da idanuwan rahama ya yafemana wasu laifukan da muka aikata masa.

"K'warai kuwa alhaji kabarshi ya zauna cikin 'yan uwansa kada kasa muje dashi yayi rayuwa cikin kad'aicin daba wa balle k'ane" dr Ahmad yafad'a yana kallon jaririn daya dad'e da shiga ransa, wasu hawayenne suka sake zubowa alhaji Tukur a idanuwa yace

"Bazan tilas taku karb'ar saba, amma Allah shine sheda akan da zuciya d'aya nabakushi kuma inda son samu kada ku tab'a nuna masa cewa shi ba d'an gidanku bane, kada kutab'a fad'a masa cewa nine mahaifinsa don zuwa gobe zanyi nesa daku zan koma k'auye da iyalina na nemi wata sana'ar da zata iya rik'emu don natabbata dole banki su zauni gidana amatsayin bashin kud'insu dana karb'a koda zan tsira da wani abun acikin gidan bazai wuce suturunmu ba, don haka don Allah da girmansa ku karb'i yaronnan nabakushi duniya da lahira" mamy zatace wani abu Dr Ahmad ya hanata ya kalli alhaji Tukur yace

"Shikenan alhaji Mungode da wannan kyautar kuma bazamu tab'a mantawa da wannan alkhairin daka yimana ba, akaro nafarko kenan da wani ya saka mamynah zamowa uwa bayan tahaifeni kuma a lokacin da take da tabbacin cewa har iya k'arshen rayuwarta bazata koma samun d'a aduniya ba bacin ni da Allah yabata sai gashi kabata wani d'an da zata kalla taji sanyi, nikuma kabani k'ane wanda zan iya bugun k'irji innunawa duniya cewa nima inada d'an uwa, gashi kayiwa mahaifina takwara wanda hak'ik'a hakan bakad'an ya sakamu farincikiba mungode mungode sosai Allah yaraya shi kuma ya sanya mashi albarka" dariya alhaji yayi mai had'e da kuka sannan ya rungumesa yana fad'in

"Nagode ahmad da wannan karamci naka ina rok'on Allah daya yimaka albarka kuma yakare rayuwarka aduk inda kake"

"Amin ya Allah alhaji, kace dai Allah yayi mana albarka kuma yakare rayumarmu aduk inda muke ko kamanta cewa yanzu bani kad'ai nake ba inada d'an uwa" yak'are maganar had'e da d'ora hannunsa bisa kan jaririn, murmushi alhaji yayi tare da goge hawayen idonsa yana kallon mamy da itama hawayen takeyi tsabar farinciki daya lullub'eta na samun damar zamowa uwa akaro nabiyu, rungume jaririn tayi ajikinta sosai tare da had'e hannayenta waje d'aya tana yimasa godiya, duk wanda ke wurin ya jinjina alamarin tare da yabawa abunda alhaji yayi koba komai anaso musulmi ya kasance yanabin mummunan aikin da yayi da kyakkyawa.

Wasu 'Yan uwan alhaji da mutanen gari kuwa sunyita yin k'orafi akan wai alhaji ya sayar da d'an sane saboda halin da yake ciki wasu kuma suce bazai iya kula da 'ya'yan bane sunyi masa yawa tunda ya tsiyace yanzu shiyasa yabayar da kyautar d'ansa, kai maganganu dai iri iri amma yayi kamar baisan ana yiba ya toshe kunnuwansa saboda shi yasan don Allah yayi da kuma kyautatawa ga mutanen da sukayi masa ramakon alkhairi da sharrin da yayi masu, kwana biyu da faruwar haka aka saida gidan alhaji da abun duk dake ciki a daidai farashin kud'in daya ranta, k'arin dubu saba'in kawai ne aka samu akai, nan banki tacire kud'inta dana dillalan da suka had'o mutane wajen yi gwanjon gidan sannan aka mik'a masa dubu arba'in amatsayin canjinsa daya rage, hannu biyu yasa yakarb'a yana hawaye tare da tattaro kayansu nasawa shida iyalinsa sukayi sallama da mutanen anguwa sannan suka kama hanyar komawa k'auye, ko kad'an baiyi tunanin neman dr Ahmad ba balle yaje gidan saboda acewarsa iya abubuwan alkhairin daya yimasa sun isa hakanan, bayaso yaje yimasa bankwana kuma yanemi k'ara had'asa da wani alkhairin da zai sashi cigaba da zubar da hawaye da danasanin abunda yayi masa har abada, Shikuwa dr Ahmad ko daya sake komawa anguwar yatarar har alhaji Tukur yawuce, gashi bayada nombarsa kuma baisan k'auyen daya koma ba kuma daya tambayi dattijan anguwar suma cemasa sukayi bai sanar dasu ko a wane k'auyenne zai jeba, ko kad'an hakan bai yimasa dad'i araiba amma dole tasa ya hak'ura cike da fatar allah yasake had'a fuskokinsu da alkhairi,

Mamy kuwa tuni taci gaba da renon yaronta Bashar da sukayiwa lak'ani da MUHIB wato abunso cikin tsantsar kulawa da soyayya, sosai taso tashayar dashi amma sai dr.Ahmad ya hanata, acewarsa tsutsa nada matuk'ar wahalarwa arayuwa kuma shi duk abunda zaisa tawahala baya sonsa ko kad'an, sannan ba'asan tsarin da Allah zaiyo tsakaninsu da shiba nan gaba don haka tayi hak'uri a d'ora daci gaba da bashi madarar insha Allah babu abunda zai samesa sai adinga had'a masa da ruwan zamzam da yardar Allah zai samu cikakkiyar lafiya da kuzari, dole haka mamy tahak'ura tabi shawarar d'an nata badon ranta yasoba.

A b'angaren Mahmud pilot kuwa saida su Umma da alhajinsa sukayi da gaske sannan yakoma abakin aikinsa don bazai yuyu ya zauna masu cikin gidaba har nan da wata biyu kafin aurensu, kullum cikin mita yake yiwa Billy akan wai da had'in bakinta aka kai auren har nan da wata biyu don bata sonsa ita kuma saidai tayita yimasa dariya tana fad'in babu ruwanta tsarinsu dadyne, ranar da kuwa yaji labarin cewa ai iyayen faraaha suka saka ranar auren nan da wata biyu shiyasa dady yasaka nasu suma ahaka saboda yanaso a had'e auren gaba d'aya lokaci guda, musamman yakira yaya Mahmud yata yimasa jininin wai sun cutar dashi don basu san meye cutar so ba da zafinta shiyasa akai fixing aurensu nan da 2mnth gashi yanzu sunja masa, haka dai shima yata yimasa fitina sai kace shine farahar ko iyayenta, shimadai d'in dariya yayi masa yace ka kwantar da hankali d'an uwa nan da 2month ai kamar gobene, tsabar takaicin yace masa wai nan da 2month kamar gobene yasa yakashe masa wayar yana cigaba da mita, Umma ko data shigo d'akin tund'azu tana sauraren fitinar da yakeyi zata kwashe kayan da yayi breakfast dasu dariya tayi cike da mamakin yanda duk kunyar d'an nata da yake da ita tacire akan soyayyar Bilkisu, mudai Allah ya nuna mana wannan rana koma huta da rigimarka son, tafad'a tare da ficewarta

Lambar Billy yakira bugu biyu ana ukun tad'aga had'e da cewa

"Hello mijin"

"Na'am matar ya kk, kina lafiya?"

"Lafiya klw yayana kaifa?"

"Not fine at all"

"A'a'a'ahh.... assha to fad'amun waya tab'a mun kai da safiyarnan"

"Waye banda yayanki, shine yab'atamun rai shida damammiyar waccan malamar asibitin tasa" saida tayi murmushi sannan tace

"Ayya d'an uwan naka da kansa yatab'amun kai?"

"Eh mana, shiyasa nakiraki ki sanyayamun zuciyata"

"To shikenan mijin kayi hak'uri, kaga dai acikinku babu wanda zan shigar wa don dukanku 'YAN UWANA NE, amma rufe idanuwanka kabud'e kunnuwanka sosai inturo maka da wani sak'on na musamman da zai dad'ad'a maka rai kaji yayana"

A hankali yarufe idanuwansa ya sake manna wayar akunnensa sosai had'e da cewa "to ina saurarenki matar"

Wayar takara abakinta tare da jan wani irin dogon kiss ta jefe masa direct acikin kunnensa had'e da cewa "I luv you yayanah" takashe wayar tana dariya.

Murmushi yayi tare da manna wayar saiti zuciyarsa yakoma kan gadon yayi kwance yana fad'in

"Yarinyar nan kasheni zatayi da salon soyayyarta, innayi wasa lumfashina gagarar fita zaiyi aduk lokacin dana tunata" d'ago wayar yayi ya k'urawa hotonsu dake a fuskar wayar suna dariya yayi kissing d'inta tare da fad'in "I love u too my noor"

Basmah dake kwance gefenta tayi dariyar k'arfin hali tace

"Allah Billy kinzare yanzu ko kunyata bakyaji ko?"

Rufe idanuwanta tayi da tafin hannuwanta tare da cewa "kai yayya to ai laifin yayankine shine ya b'atani" murmushi Basmah tayi sannan tace

"A'a sister baruwan yayanmu kedai ke neman b'atasa da soyayya" juyowa batool dake lunkar kaya tayi had'e da cewa "hmmm yayya kenan kawi bakisan halin yayannan namu bane, mugun d'an soyayyane kamar shahrukan, wlh duk shi ya lalata my twiny da wannan soyayyar har tazama lamba d'aya itama" tak'arasa maganar tana zungure Billy ga kai, da haka sukayita firarsu Basmah na zolayarta tanata faman dariya ita kuma Batool nashigar mata, soyayyace mai tsananin gaske tsakanin wud'annan 'yan uwa guda uku da basa k'aunar ganin b'acin ran junansu, akoda yaushe bakin kowane d'aya daga cikinsu baya gajiya da fad'in cewa 'YAN UWANA NE!

A 'yan kwanakin nan gaba d'aya Basmah tadena jin dad'in jikinta, kullum cikin ciwon kai da jiri take ga ciwon zuciyar na yawan tasar mata akai akai gashi bukin 'yan uwan nata sai k'aratowa yakeyi don yanzu saura sati biyar, iya k'ok'ari da juriya tanayi wajen b'oye halin da take ciki wanda hakan yajawo hankalin mom akanta, yau tana kwance saiga mom tashigo d'akin, kallo d'aya tayi mata tashiga tashin hankali da sauri tak'arasa wajen tare da rik'e hannuwanta cikin damuwa tace

"Basmah injin bajikinne ya tasar maki ba" cije baki Basmah tayi tana k'ok'arin tashi mom tadakatar da ita "Aa Basmah koma ki kwanta, amma don Allah kifad'amun meyake damunki, kullum kece cikin ciwon kai da jiri ga wannan ciwon zuciyar naki yak'i kwantawa kuma idan akace aje asibiti kice bakya zuwa to wai menene hakan kedamunki"

"Mom babu komai, kawai ciwone kad'ai keda muna kuma zansamu sauk'i in sha Allah kiyimun addua zanwarke da yardar Allah mom"

"Haba Basmah to idan ciwone donme da bazaki bari aje asibiti ba"

"Mom banaso muje akwantar dani, gashi bukin 'yan uwana namatsowa inaso ayi komai dani shiyasa"

"Amma Basmah nifa mahaifiyar kice bai kamata kib'oyemun komai narayuwarki ba, don Allah kifad'amun idan da akwai wani abun da bansani ba" duk'owa tayi kusa da fuskarta had'e da dafa goshinta tana shafa gefen fuskarta "Basmah kodai tunani kike akan 'yan uwanki zasuyi aure subarki a gida" "A'a mom" tafad'a had'e da girgiza kanta lokaci guda hawaye nazubo mata,

"To meye Basmah?"

"Babu komai mom, kicire wannan tunanin aranki aishi aure lokacine dashi kuma nayi imani cewa duk lokacin da nawa yazo zanyi, kuma don 'yan uwana zasuyi aure su barni mezaisa nadamar da kaina bacin nasan Allah yana zab'a wa kowane bawa abunda yafi zama alkhairine akansa, kawai kiyarda dani ciwona jarabawa ce daga Allah kuma kiyimun addua Allah ya yaye manishi"

"Shikenan Basmah tunda haka kika fad'a Allah yazab'a maki kema miji nagari kuma yabaki lafiya"

"Amin mom" Basmah tafad'a had'e da juyar da kanta gefe hawaye nazubar mata, akoda yaushe Batool na lure da halinda 'yar uwar tata keciki kuma tana zaunawa tayita lurar da ita illar b'oyon damuwar da take ciki, takan rok'eta akan don Allah tabari suje asibiti adubata abata maganin daya dace tasha amma tsabar k'arfin halin Basmah saita nuna mata itafa babu abunda kedamunta ciwonma yadena tasar mata gaba d'aya, shikuma yaya Mahmud yanzu baya zama tunda akasa ranar bikinsu cikin zirganiya yake yau baya nan gobe baya can wajen ganin ya had'a lefensa balle yasan halin da 'yar uwar tasa ke ciki, Ummi ma da kanta tazauna tayita bincikar Basmah meke damunta amma tak'i fad'a mata, maganarta dai d'ayace ciwone kawai Allah ya jarabceta dashi amma babu damuwar da take ranta, daga k'arshe dai kowa ya ta'allak'a abunda k'ilan kewa da damuwar d'auke 'yan uwanta da za'ayi abartane kesata wannan ciwon, ita kuma Basmah ba abunda ke hanata son zuwa asibiti illah kada likita yafayyace masu gaskiya matsalarta wanda tatabbata dole dady yanemi sanin dalili kuma hakanne bata fata don kozaka mutu bazata tab'a bayyana sirrin zuciyar taba kodon farincikin 'yan uwanta,

A lokacin da labarin halin da Basmah ke ciki yakai akunnen dady sa yayi aka kirawo masa ita, sosai ya canza mata fuska ganin yanda takoma don d'ai kawai tafad'a masa meke damunta amma tak'i fad'a sai cemasa takeyi ciwon zuciyane kad'ai da take fama dashi amma babu abunda kedamunta. Hakan yasa ran dady ya matuk'ar b'aci had'e da yimata fad'a donme zata d'auki ciwon da wasa haka bayan gashi yana nuna illar da yake yimata atare da ita kuma har tace wai bata son zuwa asibiti akan wani banzar dalilinta, to meta d'auki lafiyartane wato bukin 'yan uwanta kenan yafi lafiyarta,

Kuka take sosai kamar ranta zai fita saboda fad'an da dady keyimata tasan inda zai ajesa daga k'arshe, shikuwa ganin haka yasa yayi lowering voice d'insa cikin ransa yana tausaya mata naganin gashi itace babba amma za'a d'auraye k'annenta akai gidan miji wanda ko wannan kad'ai ya isa yazame mata damuwar da zata iya jefata cikin wannan halin, cike da tausayawa yashiga yimata nasiha dake nuni da tayi hak'uri shi aure lokacine insha Allah itama yana fatar nan kusa lokacin nata yazo, kallonta yayi tare da mik'a mata hannu alamar tazo, rik'a hannunsa tayi takoma k'asan kujerar da yake zaune kusa da k'afafuwansa ta zauna tare da d'ora kanta akan cinyoyinsa, shafa kanta yashigayi alamar rarrashi sannan yace

"Kiyi hak'uri Basmah Allah yazab'a maki kema miji nak'wari, yanzu kije ki kwanta gobe da safe in Allah yakai ranmu kafin nawuce wajen aiki saiki shirya muje asibiti kinji ko?" Gabanta ne yafad'i da sauri ta d'aga masa kai don batada zab'in daya wuce amsa masa saboda maimaitawar daya yimata, mik'ewa tayi had'e da cewa

"Saida safe dady"

"Allah yatashemu lafiya Basmah kuma Allah yayi maki albarka" ta amsa da amin tana k'ok'arin barin d'akin, da k'yar takawo d'akinsu kanta nawani irin mugun juya mata tashige toilet dama Batool na part d'in ummi wajen Billy, tana shiga ta fashe da kuka had'e da duk'ewa tatura kanta a tsakankanin cinainanta jitake tamkar ranta zaya bar jikinta saboda tsananin ciwon da takeji, zuciyarta cike da fargaba zancen zuwan asibiti da dady yace zasuyi gobe don ko kad'an bata buk'atar haka, jin tayi ana bubbuga gambun toilet d'in da k'arfi, mom ce tashigo saboda tana zaune afalo taga shigowarta amma ko lura da ita batayi ba balle tayi mata magana ta wuce abunta, ganin haka yasa ita kuma tabiyo bayanta don ganin ko lafiya, sake bubbuga gambun k'ofar tayi had'e da cewa

"Basmah, Basmah maza kibud'e gambunnan kinajina ko?" Jin muryar mom d'inta yasa ta d'ago kanta tana goge hawayen da suka mik'e mata fuska don kar tagane halin da take ciki, hannunta takai ga hancinta jin wani abu nafitowa daga ciki mai sanyi tana duba hannunta taga jini da sauri tanufi wajen madubin dake saman sink d'in dake cikin toilet d'in taga ashe tabbas jinine ke zubowa daga hancinta...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____72💎


Shafo hancin ta sakeyi tare da duba hannunta data lakuto jinin, jitayi mom taturo k'ofar had'e da shigowa ciki, da sauri tabud'e fanfon dake jikin wajen tana wanke fuskarta tare da jinin dake zubar mata a hanci, muryar mom taji tana fad'in

"Aw ashe dama kinaji ina kiranki kibud'emun k'ofar shine kika k'yaleni?, me yasamekine naga kin wuto afirgice tamkar babu natsuwa ajikinki?"

Saida ta sake d'ibar ruwan ta wanke hancinta tana k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata har lokacin kanta na aduk'e batare data d'agoba sannan tace "kiyi hak'uri mom babu key ajikin k'ofar ne shiyasa kuma babu abunda yasameni kawai inajin matsuwane bari nafito"

Jin haka yasa mom cewa "to shikenan amma gaskiya banyarda dake ba, yimaza kifito ganinan ina jiranki" tana gama fad'ar haka tafice had'e da samun gefe ta tsaya tana jiran fitowarta,

Tana fita tarufe idanuwanta hawayen da tamak'ale tun d'azu cikin idanuwanta suka samu damar zubowa, ganin kukan na neman kucce mata yasa tasa hannu ta toshe bakinta da sauri, tafi minti biyar ahaka sai hawaye ke k'warara a idanuwanta kafin can taciro tissue tana goggoge jinin dake cigaba da fitowa daga hancinta, ganin yak'i tsayawa yasa taciri tissue ta toshe hancin da ita tasake bud'e fanfon ta d'auraye hannuwanta sannan tafito daga toilet d'in rabin fuskarta arufe da gefen hijab d'inta don kar mom talura da yanayin da take ciki, ta gefenta tarab'a tawuce ta haye saman gado takwanta har lokacin hijab d'in na akan fuskarat, ahankali ta furta "mom don Allah lullub'eni sanyi nakeji sosai" mom da tund'azu tabita da kallo ta matso wajen tare da jaye bedsheets d'in dake shimfid'e a k'ark'ashin k'afafuwanta ta lullub'amata ajiki tana fad'in

"Basmah ko ciwon nakine yatashi?"

"Eh mom amma da sauk'i" tafad'a tana tura kanta acikin bedsheet d'inta, karo nafarko kenan data fara amsa cewa ciwon tane kedamunta ga mahaifiyarta, dafata mom tayi had'e da cewa

"Subhanallahi inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, Basmah yanzu kina cikin wannan hali shine tund'azu bazaki fad'a mani ba don kawai bakyaso kije asibiti, wai meyasa kike wasa da rayuwarki haka?, kina so kije ki kashe kankine Basmah?"

"A'a mom, kiyi hak'uri idan nab'ata maki, ki kwantar da hankalinki dady yace gobe da safe zai kaini asibiti" Shiru mom tayi tazuba mata idanuwa tana mamakin irin wannan zurfin ciki da take dashi wanda ke nema yakaita ga rasa rayuwarta, ita kuwa daga haka bata sake cewa komai ba saima baccin k'arya data tsiriyi hadda minshari,

Da daddare ko kasa bacci tayi, dole ta tashi tayi zaune tsakiyar gado tana kallon Batool dake baccinta hankali kwance don koda tadawo part d'in Ummi ta tarar har Basmah d'in tayi bacci shiyasa bata tsaya wani abuba itama tabi lafiyar gado, tashi tayi ta d'oro arwala a toilet sannan tafara salloli tana mai mik'a dukkanin alamurranta ga Allah tare da rok'on Allah kada yasanya wannan ciwon nata yazamo silar rushewar farincikin 'yan uwanta idan sunje asibiti, tissue kuwa kusan k'waya d'aya ta b'ata kafin safe wajen k'ok'arin tsaida jinin dake zubomata a hanci donma Allah ya taimaketa jinin yadena zubowa sosai kad'an yake fitowa saidai

Please Login or Register in order to submit comment