Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina Bilal muso juna karka yadda kabarni, dady kace ta tashi nima bana so tabarni" dafa kansa dady yayi had'e da cewa

"Bazata barka ba kuna atare in sha Allah" ahankali Ummi ke shafa kan Bilkisu tana tofa mata addu'ar samun sauk'in rad'ad'in ciwo

_BISMILLAHI ARK'IK', WALLAHU YASHFIK, MIN KULLI DA'IN MAUDU'I, WAMIN KULLI AINI AU ANI HATIM ALLAHU YASFIK, ALLAHUMMA RABBAN NAS, ASHFI BIL BA'AS, WASHFI ANTASH SHAFI'I LAA SHIFAA'A ILLA SHIFAA'UKA, SHIFA'ALLAHU LAA YUGADIRUSSAK'AMA, AS'ALALLAHUL AZHIM, RABBIL ARSHIL AZHIM AN YASH FIKA/KI_

Sosai Ummi ke maimaita wannan addu'ar tana tofamata, cikin Ikon Allah sai gashi tafara bud'e idanuwanta ahankali,

"Ummi" ta furta ahankali, murmushi Ummi tayi sannan tace

"Sannu Bilkisu, Allah yabaki lpy" maida idanuwanta tayi ta rufe sannan ta sake bud'e su ahankali hawaye na zubowa daga ciki, k'ok'arin tashi tayi da sauri ta koma had'e da dafe kanta dake d'aure da bandage,

"Washhh..."

"Yi a hankali" Ummi tafad'a tana k'ok'arin gyara mata kwancinta, d'ayan hannunta ta mik'awa Bilal tana yimasa alama da kai da yazo, hannunsa dady ya saki

Da gudu ya k'ara wajen ta "sannu Aunty Billy, bazaki barni ba ko?" A hankali ta d'aga masa kai hawaye na zubar mata,

"Eyyee..alhmdulillah my lil sis ta farfad'o" idanunta ta d'ago tana kallon Mahmud dake a bakin k'ofar d'akin yana murmushi, k'arasowa yayi daga ciki tare da jaye Bilal dake rik'e da hannunta

"Jaye daga nan autan Ummi inga lil sis d'ina" kallon dady yayi cikin farincikin ganin 'yar uwarsa ta tashi yace



















Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____15πŸ’Ž


Dady yaushe tafarka ne? Gaskiya am so happy "yanzun bada jimawa ba" dady yafad'a yana d'an Sosa k'eyar kansa, sai a lokacin yake jin ba dad'i bisa abunda yafaru tsakaninsa da mom saboda gaba d'aya sai yaji kunyar yaronsa yake ji, ganin yanayin da dady ya shiga ya sashi saurin juyar da fuskarsa yana murmushi don dama yariga da yasan ko waye mahaifinsa, Sam shi ba mutumne mai taurin rai ba yana da matuk'ar sanyin hali fiye da tunani, duk da baisan meke ransa ba yafahimci cewa izuwa yanzu har yafara jin ba dad'i akan abun da yafaru, murmushi ya sakeyi wanda har sai da kyawawan hak'oransa suka bayyana had'e da shafa gefen fuskar Billy yana fad'in "sannu ko my lil", murmushin itama ta mayar masa tare da nuna masa gorar jinin da ake k'ara mata dake batun k'arewa, d'ago kansa yai yaga kad'an yarage jinin ya ida shigewa sannan yafita domin ya kirawo likita, bayan kamar minti biyu sai gashi ya dawo tare da wata nurse a bayansa. Sai da tacire mata gorar jinin dake lak'e a hannunta ta tambaye ta shin ko akwai inda keyi mata ciwo yanzu tace a'a sannan ta juyo cikin natsuwa tana gaishe dasu Ummi dake zaune, cikin 'yar siririyar muryarta da tayi daidai da tsarin jikinta ta maido kallonta ga Mahmud tana fad'in

"Za'a iya nemo abinci a bata taci"

"OK nurse mungode" batare da tace masa komai ba tajuya tabar wajen tana murmushi, daidai k'ofar fita taci karo da dr kamal yaturo gambun k'ofar d'akin zai shigowa, sunkuyar da kanta tayi cikin girmamawa tana gaishesa,

"Lpy klw faraaha, ya aiki?"

"Alhmdulillah"

"Dama kece on duty today"

"Yes sir,"

"OK, very good naji dad'in haka don dama ina tunanin acikinku wanda zanba foler patient d'ina a kula mani da ita before indawo saboda d'azun aka kirani zamu tafi wurin seminar na tsawon two days, to tunda kece on duty nasan no trouble zaki kula fiye da yanda zan buk'ata kiyimun" ya k'arasa maganar had'e da rufe k'ofar suna tafiya yana cigaba da yimata bayani har suka iso wajen gadon, hannu ya mik'awa dady suka gaisa yana kallon fuskar Billy da tayi wani irin haske sosai, tafin hannunta ya duba sannan yasa hannu fad'an bud'a cikin k'asan idanuwanta kad'an don ya tabbatar da jinin ya isa yanda suke buk'ata

"Yawwa 'yar gidan dady! Yanzu komai yayi daidai alhmdulillah, babu ciwon kai da jiri ko?"

"Eh dr. Amma ina jin zafi cikin kaina sosai"

"Eh dole zakiji haka saboda anyi maki d'unki a inda kikaji rauni amma insha Allah shima zai dena" nurse d'in yafara gabatar masu cikin nuna k'warewarta da sanin yakamata ga aikinta...

"Alhaji wannan d'aya daga cikin jajirtaccin ma'aikatanmu ce mai suna faraaha, duk da Bilkisu tasamu sauk'i bazaku samu sallama yauba har sai nan da kwana biyu anyi mata scanning akanta an tabbatar babu wata matsalar data shiga acan ciki, don haka duk abunda ya kamata ayi mata anyi photon shi kad'ai ake jira da kuma dawowar k'arfin jikinta, yanzu zan mik'a folder d'inta a hannun sister faraha zataci gaba da kula da ita saboda kiran gaggawa da nasamu yau d'innan akan zamuje wajen seminar, na yarda da k'warewar faraaha sosai ina fatan bazaku samu damuwa ba, faraaha ina so kibawa patient d'ina kula yanda ya kamata domin su d'in tamkar 'YAN UWANA NE"

"Shikenan dr. In sha Allah zanyi" sai da ya sake yiwa Billy checkup da kyau ya tabbatar babu wata matsala sannan yayi sallama da dady ita kuma faraaha ta koma bakin aikinta, hannun bilal dady ya rik'o suka fito shida dr. suna k'ara tattaunawa akan yadda abun yafaru, acan cikin d'akin kuwa wayar ummice tayi k'ara da sauri ta d'auka ganin lambar wacce takira had'e da barin d'akin shikuma Mahmud ya koma inda Billy ke kwance yana tambayarta ko me zataci,

"Bana son komai Yaya"

"Ai kuwa kinsha k'arya dolene kifad'i abincin da za'a nemo maki kici"

"A'a Yaya ni bazanci ba"

"Zancen kike so lil sis, idan baki fad'a ba zanje inkawo maki duk abunda na samu kuma dole zakicisa in kuma kink'i inyi maki d'ure"

"A'a to zan fad'a, kasiyomun chaculate" zaro ido yayi cike da mamaki,

"Lallai Billy kin renani da yawa, chaculate d'in ne abinci?" K'efta idanuwanta tafarayi alamar zatayi kuka, goshinsa ya dafe

"Oh! Sorry shikenan ina zuwa bari naje nakawo maki, enough ki kwanta kihuta kinji ko? kai ta d'aga masa had'e da rufe idanuwanta"

A b'angaren mom kuwa tayi abu ya shamata kai, don tsabar kishinta tunda ta isa gida takasa samun natsuwa babu abunda take ayyanawa aranta sai hango dady da Ummi suna buga sabuwar soyayya ga wata irin kula ta musamman da yake bata da 'ya'yanta ita kuma nata 'ya'yan sun wofantar mata dasu hatta bacci idan takwanta kyakkyawan murmushi take hango dady yana yiwa Ummi abu mafi munin data tsana taga yayi mata, da zaran taga haka cikin bacci a firgice take tashi kuma baccin da bazata koma ba kenan, yau kwana d'aya kenan da komawarta gidansu amma dady bai tab'a yunk'urin nemanta koda awayane haka yasa Basmah dole ta koma asibiti wajen jinyar Bilkisu sukuma Batool da Bassam yasa suka kwashe kayansu suka koma part d'in Ummi, duk abunda uwa keyiwa 'ya yiwa 'ya'yanta Ummi nayiwa su Bassam daidai gwargwado duk da ba k'aramin hak'uri takeyi da yanayin tarbiyar tasu, kullum tana kalle da Batool in lokacin sallah yayi bata tashi tayi haka safe ko rana gaba d'aya bata iya gaishesu ga rashin kunya kala-kala da take yimata agidan, dafarko Ummi na hak'uri amma ganin abun yayi worst yasa tazaunar da Batool tayi mata fad'a sosai sannan ta nuna mata matuk'ar bata gyara ba to tabbas sai ta sab'amata, hakan yasa Batool tashiga taitayinta amman kullum cikin kuka take wai Ummi na takura mata, shi kuwa Bassam bawata matsala da yakeba ta inba cutar Bilal da yake yiba, har mamakin kalolin k'etar da yakeyi take koda yake kullum cikin kallon wrestling yake shiyasa, Basmah kuwa zuwan asibitin kad'ai take amma babu wata jinya da takeyi, hatta abinci bazata iya zubawa Billy taci ba saida tagaji tazuba ma kanta ko kuma idan Yaya Mahmud yazo yazuba mata duk da ba wani ci sosai takeyi ba, kullum basmah na kwance akan caution d'in dake d'akin rik'e da waya tana latsa tana tamnar cingum, sallah ma sama sama take yinta takomawarta kwance tana cigaba da latsar waya tana dariya, saboda yawan dariyar da takeyi yau sai da sister faraaha tayi mata magana akan tadena tana damun marasa lafiya amma tsabar rashin kirki irin na Basmah ta zauna ta zagaeta tass tare da buga mata warning akan karta sake shiga gonarta, tun alokacin taji ta tsani faraaha, duk abunda takeyi babu wanda ke iya da katar da ita inba Yaya Mahmud ba shikad'ai ne ko muryarsa taji zata shiga taitayinta, gashi yau tun safe bai samu lek'owa asibitin ba, shigowar sister faraaha d'akin yakai sau goma duk don tasamu ta gansa amma hakan ya gagara, tun ranar da idanun sister faraaha suka sauka akan fuskar Mahmud taji ya matuk'ar kwanta mata arai, duk abunda yayi na matuk'ar burgeta wannan dalilin ne yasa idan ta kammala duba lpyr patient d'inta sai tadawo d'akin suyita fira da Billy, baza tabar d'akin ba sai lokacin da taga shigowarsa, cike da jin dad'i da fara'a sun gaisa da juna tanajin wani irin shauk'in soyayyarsa na fisgarta sannan zatabar d'akin, maganar gaskiya faraaha tafad'awa son Mahmud son da bazata iya misil tashiba, turo k'ofar tayi bakinta d'auke da sallama tashigo tana kallon Bilkisu cikin fara'ah tace

"Sisto kishirya anjima zamuje wajen scanning kinji ko"

"Eh Aunty faraaha" har ta juya zata fita sai kuma tajuyo

"Yawwa sisto nace har yanzu yayanki bai zoba? Injin dai ko lpy?" Kafin billy ta bata amsa taji Basmah taja wani ubantsaki

"Mtssss..munsan komai anji haushi wlh ace ina macce in kwarewa namiji har ina zuwa neman sa tirr, wai sunan malamar asibiti kenan to kota soyayya?" Kokad'an faraaha bayani mamakin kalaman dake fitowa daga bakin Basmah ba domin tasan ko zata girmeta kad'anne, ga yanda yanayinta ke canzawa idan ta ganeta ta tabbata duk cikakkiyar budurwa irinta zatasan halin da take ciki akansa, don haka itama sai tayi murmushi cikin natsuwa tana kallonta tun daga sama har k'asa sannan ahankali itama taja nata tsukin.

"Mssss..Aikin banza harara cikin duhu, ai shi malam bahaushe yace iya ruwa fidda kai" tana rufe baki sai ga Yaya Mahmud ya iso tare dasu Bilal da bassam da kuma batool ta rik'o kulolin abinci wajen, daga ciki ta shige ta sakar masu hanyar da zasu shigo daga ciki, suna shigowa tajuya zata fita batare da tace masa komai ba Bilal ya rugo ya rik'eta yana fad'in

"Oyoyo aunty faraaha" cikin sakin fuska ba sosai ba itama tace "oyoyo aunty Bilal kana lpy?"

"Lpy klw Ummi tace agaisheki da k'ok'ari" duk'owa tayi daidai tsawonsa taja hancinsa

"Yawwa Ummi kace mata nagode" wani tsakin Basmah tasake ja acan k'ark'ashin mak'oshi yanda Mahmud bazaiji ba tace

"Munafuka" ko kallonta faraaha batayi ba taja hannun Bilal zasu fita, da sauri Mahmud dake k'ok'arin mik'ewa Billy ledar ice cream da chocolate daya siyo mata yana fad'in lil sis ya jiki ya juyo yana kallon faraaha da zata fita

"Malamar asibiti yau ba magana ne?" Batare data juyo ba cikin 'yar siririyar muryarta tace

"Naga ko 'yar k'anwata Basmah data gaisheka bakaji ba balle ka amsa mata shiyasa nima nahutar da kaina" faraaha nasane da ko sallamar da sukayi bata amsa ba balle ta gaishesa tayi hakanne don ta nunawa Basmah kuskurenta kafin ta rufe baki taji tana fad'in

"Eh.eh.Yaya inata magana bakaji ba, ina wuni?" Wani irin mugun kallo ya watsa mata had'e da cewa

"Munafuka yaushe ki kayi mani magana keda inji ko sallama kasa amsawa kikayi kina can kina latsar waya, keda aka kawo jinyar marar lpy kin koma shashanci idan bakiyi hattara ba saina karb'e wayar nabawa mai gadin asibitin nan stupid"

Murmushi faraaha tayi tana kallon Basmah dake kallonta rai ab'ace ta kashe mata ijiya d'aya tare da jan Bilal suka fita, shi kuwa Mahmud bayan faraaha dake tafiya yabi da kallo cike da jin dad'in ganinta"

Batool kuwa kallon Billy tayi tace





















Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____16πŸ’Ž


Ke Billy wai meye tsakanin waccan nurse d'in ne da Yaya, 'yar dariya tayi tana kallon Basmah dake tsaye abinta har lokacin zuciyarta na tuk'uk'i akan fad'an da faraaha taja akayi mata, da hannu tanuna Basmah tare da maido kallonta ga Batool daidai kunnenta ta rad'a mata.

"Bansan komai ba kije kitambayi yayya Basmah don naga alamar ita tafahimci ko meye ko kuma intambayar maki yaya yabaki amsar da kansa.." Da sauri ta zaro idanuwa waje had'e da sakar mata rank'washi akai tana nunata da hannu,

"Ke rufe baki so kike ya b'abb'allani nima abani gado a asibitin nan?, kawai manta dashi idan tayi tsami zamuji" tana rufe baki taji an rik'e mata d'ayan kunnen da k'arfi tamkar zai cire ashe duk abunda suke fad'a akunnensa yana jinsu,

"Bari nafad'a maki tunda so kikeyi kiji magulmaciya"

"Awshhh..Yaya cikani don Allah wlh da zafi" sake rik'e kunnen yai sosai ta yanda zafin zai d'ara wanda taji daga farko,

"Pls am sorry Yaya" sakinta yayi tare da mak'alo wuyanta a k'ark'ashin kafad'arsa yana dariya

"Kura ga tsoro ga ban tsoro, to ya kika ganta kuwa tayi?" Turo baki tayi hannunta d'aya na saman kunnenta dake yimata rad'ad'i.

"Gaskiya batayi ba, mace sai kace muciya" tana rufe baki kafin yayi k'ok'arin d'aukar wani action ta zille masa tabar d'akin aguje tana dariyar k'eta don tasan tayine kawai don ta k'waga masa akan abinda yayi mata, dariyar shima yayi had'e da shafa kansa, hatta Billy da Basmah dake faman kumburar fuska saida sukayi dariyar yanda ta zunduma da gudu, juyowa Basmah tayi donta koma mazauninta taga Bassam rik'e da wayarta sai faman game yakeyi, ak'ufule tayo kansa shi kuma ya yadda wayar ya ruga abayan Mahmud ya b'uya, jawo hannunsa yayi yace

"Zo gashi narik'e maki" ai kuwa ko kunya bata jiba tayo kansa cikin b'acin rai da nufin kai masa duka, da sauri Mahmud ya rik'e hannunta yana dariya

"Kai Basmah yanzu saiki dukesa akan ya tab'a maki waya ke ko kunya bakiji ba"

"To don me zai tab'amun, game fa yakemun kuma banida enough charji"

"Oh sorry!...bazai k'ara ba ko? mahmud ya fad'a yana kallonsa, kad'a masa kai yayi yace

"Eh Yaya"

"To kinji yace ya dena saboda haka tunda gani nazo kije gida kigyara idan dady da Ummi zasu zo sai kudawo tare muje gaida mom" hakan da yace ba k'aramin dad'i yayi mata ba, nan take cikin farinciki tahau har had'a kayanta, wayarta da ear piece da kuma charger tad'auko tasaka a cikin 'yar mini hand bag d'inta dake gefenta sannan tabar d'akin ba tare data kalli ko inda Billy ke zaune ba balle tasa ran zata cemata wani abun.

Bayan tafita yayi murmushi yace 'YAN UWANA kenan ko wannenku da kalar tasa rayuwar ya Allah kasa muso juna.

"Amin" yaji Billy tafad'a tana k'ok'arin tura chaculate d'in data kwand'are acikin baki, gefenta ya zauna akan gadon yace

"Billy ya jikin naki?"

"Alhmdulillah naji sauk'i Yaya, wai sai yaushe zasu bamu sallama wlh ni nagaji da kwancin gadon nan"

"Ai kuwa hak'uri zakiyi har sai lokacin da aka yimaki scanning result ya nuna ba wata matsala sannan, gashi har yanzu basusa date d'in yin scanning d'in ba kinga kuwa indan zama yanzu kika fara"

"Kai Yaya hadda wani yanzu nafara zama don bakaso ka dena ganin aunty faraaha ko?, to thank good ance bayan sallar la'asar za'ayi scanning d'in" mintsili ya kaimata a kumatu had'e da cewa

"Kema biyewa Batool zakiyi ko? Nifa babu wani abu tsakanina da faraaha, the way yanda ta gwane ga aikin tane da kuma kulawar da take baki yanda ya kamata shiyasa kikaga nadamu da ita"

"Dagaske Yaya ba sonta kake yiba?"

"Eh mana baki yarda bane?"

"No..amma meyasa kacewa Batool..." Kafin ta iyar yace

"Common.. da wasafa nakeyi, sincirely ni babu wani tsarin soyayya ko aure agabana, faraaha kuwa burgeni ne kad'ai alamurranta keyi amma babu soyayyar ta aziciyata"

Sun jima da ita tana nuna masa irin alkhairan da faraaha take tartare dasu zaifi dacewa ace ya mallaketa amatsayin masoyiyarsa amma fir Mahmud ya nuna mata shi ba sonta yakeyi ba, abunda ya matuk'ar d'aure mata kai shine yanda yake matuk'ar farinciki idan suka had'u da ita da irin kallon da yake yimata amma wai yace shi ba sonta yakeyi ba kawai burgesa takeyi, yatsunsa ya murza akan fuskar ta har saida sukayi k'ara, firgigit Billy tafarka daga duniyar tunanin data lula, girarsa ya d'aga kafin yace

"What?"

"Nothing Yaya just dt ina mamaki ne"

"Believe me lil sis dama kindena"

Sai gab da sallar la'asar su Ummi suka shigo cikin asibitin tare da Basmah, kai tsaye dady ya nufi wajen faraaha don bincikar cigaban da aka samu game da lafiyar 'yarsa ita kuma Ummi da Basmah suka wuce room d'in da suke jinyar Billy, cikin girmamawa dady daya isko faraaha zaune dasu Bilal da Bassam tamik'e tana gaishesa, sun d'auki kusan mintuna biyar tana yimasa cikakken bayani daga k'arshe tafad'a masa cewa yau d'innan za'aje da ita wajen scanning da zaran anyi sallar la'asar, godiya yayi mata sosai tare da sanya mata albarka sannan ya nufi d'akin, Billy na ganinsa ta washe baki cikin farinciki tace

"Dady sannu da zuwa" cikin fara'a shima ya amsa mata da "yawwa Bilkisu ya jikin naki"

"Alhmdulillah dady naji sauk'i sallama kad'ai nake jira" Ummi ya kalla cikin sigar tsokana yace

"Umminsu mekike bawa Japanese d'innan tawa naga tak'ara haske da k'iba dubi fa yanda idanuwanta suka k'ara shigewa" gaba d'aya d'akin aka hau dariya banda Basmah data koma gefe tana kallon duk abunda ke faruwa da gefen idanuwanta, wata irin muguwar harara ta aikawa Billy dake faman yiwa dady kukan shagwab'a wai yadena fad'a yasa suna yimata dariya had'e da cewa

"Munafuka" Billy kam da batama san tanayi ba ta kalleta tace

"Wlh Allah dady yayya Basmah tafini k'iba, d'ibeta fa" gaba d'aya kowa ya juyo yana kallonta, indai k'ibace ba wanda bai yitaba agidan nan sai ni Mahmud yafad'a yana dariya, hannu Ummi tasa akuncinta tana shafawa ahankali fuskarta d'auke da murmushi

"Babanah aikai da wuya idan zakayi k'iba don kai gaba d'aya jikinka sak irin na abbatine" wato mahaifin dady Allah ya jik'an rai, hannunsa shima ya d'ora akan nata yarike

"Ummi aikuwa ni bana son irin jikin tsohon nan na fulanin rugga, nafison inyi irin jikin dadynah.." Kafin ya rufe baki dady yad'an rank'washesa akai

"Ai anriga angama, ja'irin yaro" haka dai suka yita firarsu cikin farinciki da walwala a lokacinne da dady yafahimci irin k'ibar da kowannensu sukayi, wani irin farinciki ne ya rufesa duk da cewa yana kewar mom amatsayin sa na mijinta hakan baisa kwanciyar hankalin data bayyana agidansa tab'oyu ba, sunanan zaune aka kira sallar la'asar dady da yaransa suka nufi masallaci yayin da Ummi da 'yan matanta suka shiga toilet d'in dake nan cikin d'akin sukayo arwala don gabatar da sallah, bayan duka sun sallame su Billy da Batool suka gaida Ummi ita kuma Basmah takoma gefe abunta tazauna, da gudu Bilal da Bassam suka rugo suka fad'a jikin Ummi dake zaune a inda ta ida sallah, suma d'in gaisheta sukayi Bilal na fad'in Ummi muda Yaya zamuje wajen Small mom zakije? Kafin tabashi amsa sai ga Mahmud yashigo shima har k'asa ya duk'a ya gaida Ummi had'e da cewa

"Ummi zamuje wajen mom, idan faraaha tazo tafiya da lil sis wajen scanning saiki rakata, dady ya riga da yafita shida abokinsa yanzu?"

"Shikenan Babanah babu damuwa zaku iya tafiya, kugaisheda mom d'in taku sosai" 'Dan tsaki Basmah tayi

"Yaya nidai ina waje zan jiraku bazan iya zama ina saukar maganganun da basu kai ciki ba" a hasale Mahmud yayi kanta cikin b'acin rai da nufin falla mata marora Ummi ta dakatar dashi,

"K'yaleta Babanah! Babu komai Allah ya shiryeta" juyowa tayi ta kalli Ummi sannan ta bud'e d'akin tafita cikin b'acin rai. Shi kansa baisan lokacin da yakaiwa bangon d'akin naushi ba saboda yanda zuciyarsa ke tafarfasa, tsabar yanda launin idanunsa suka canza zuwa jajaye zaka d'auka barkono aka watsa masa aciki, baisan meyasa Basmah bata shakkar kowa ba, yazama dole ya taka mata burki takowace hanya, matuk'ar halinta yamik'e haka zata matuk'ar shan wahala arayuwa shi kuma abunda baya fata kenan, wurin Ummi ya dawo yana bata hak'uri bisa abunda Basmah tayi mata, shafa gashin kansa tayi had'e da cewa

"Kamanta Babanah ita yarinya ce, maza katashi kutafi marece nayi ko acan zasu kwana"

"A'a Ummi gaisheta kad'ai dady ya amince muje muyi"

Akan hanya ne Batool ta kalli Basmah

"Yayyah Basmah" basmah dake rufe da idanu ear piec lik'e akunnenta d'aya tace

"Meye?"

"A gaskiya abunda kikayi d'azu baki kyautaba" har lokacin idanunta na arufe tace

"Meye kuma damuwarki tunda ba mom nayiwa ba"

Da k'arfi Mahmud yataka burkin mota cikin b'acin rai yace

"Fitarmun a mota kafin na k'irga uku" ko kallonsa batayi ba tabud'e gambun motar tafita abunta tana taunar cingam, ya dad'e kansa kwance a staring mota kafin ya tayar da motar suci gaba da tafiya,

"Yaya kayi hak'uri mukoma a d'aukota"

"K'yaleta Batool, tafiyar Rabin kilometer yarage ak'arasa, wannan shine punishment d'in da ya kamaceta, yanzu idan za'ace kifad'i halin Ummi miye matsalarta data cancanci nuna k'iyayya daga wajenmu, yakamata ace munbar matsalar su can atsakaninsu bawai murik'a saka kawunanmu aciki ba, inajin zafi da rad'ad'i idan naga matsaloli na faruwa acikin gidanmu, shin kin tab'ajin Billy tayiwa mom rashin kunya?, yazakiji aranki idan ki kaga ta aikata haka ga mahaifiyarki wacce ta haifeki, ya kamata ace izuwa yanzu dukkaninku kun canza Batool! ku 'YAN UWANA NE kuma suma su Billy 'YAN UWANA NE, ina so muso junanmu, mubar su mom da abinda ke a tsakaninsu muyita yimasu addu'a har zuwa ranar da suma zasu so junansu, amma kina kallo 'yar uwarki kullum shashancinta sai k'aruwa yakeyi,

"Kayi hak'uri Yaya nadad'e da fahimtar Ummi ada ina yimata kallon munafuka wacce bata son mu amma fad'an zaman nan danayi da ita sai nafahimci tamafi sonmu akan mom" jawo Bilal tayi ajikinta sannan taci gaba da cewa nafahimci su Bilal 'YAN UWANA NE kuma ina sonsu, zance gaba da lurar da yayya Basmah har zuwa lokacin da ak'idar da mom tasaka mana arai zata fita cikin zuciyarta" wasu zafafan hawaye ne suka fito masa a idanu saboda jin dad'in canzawar Batool, yatabbata da sannu matsalolin gidansu sunfara ragewa, saita madubinsa yayi suka had'a ido da ita ya sakar mata murmushi

"Nagode sosai da fahimtar ta 'yar uwa....















Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____17πŸ’Ž


Daidai k'ofar gidansu mom yayi parking motar Batool tafito aguje tana kiran mom, mom dake zaune bisa d'aya daga cikin kujerun dake falon mahaifinta ta d'ora kanta bisa kan kujerar idanuwanta arufe azahiri zaka d'auka bacci takeyi amma idanunta biyu kawai tashiga duniyar tunanin hanyar da zata d'auki fansar wannan zaman da Ummi tajawo tanayi agidansu, muryar 'yar tata da tajiyo yasata saurin bud'e idanuwanta ahankali tace

"Batool" tare da dubon k'ofar da tajiyo sautin muryar ta, hangota tayi aguje Mahmud na biye da ita hannayensa rik'e da Bassam da Bilal yana dariyar gudun da Batool keyi, tana isowa inda take suka rungume juna tamkar sun dad'e basu had'uba cikin farinciki mom ta d'ago ta tana kallon yanda ta canza, Batool na dariya ta sake rungumeta

"Nice mom, nayi matuk'ar kewarki da yawa" wasu hawayen dad'ine suka zubowa mom tace

"Nima haka 'yatah, ina auntynki ne?" Ganin Bassam yasa bata jira amsar da Batool zata bata ba tasa hannu ta d'aukesa had'e da cillasa sama tana fad'in

"Oyoyo autana" shafa kansa tayi tana dariya"Auta bakayi missing mom d'inka ba gaskiya, dubi yanda ka canza lallai aunty Basmah tana kula mani daku yanda ya kamata ko Yaya Mahmud zance?"

"A'a mom Ummi ce ba yayya Basmah ba ko Yaya Mahmud?" Yak'arasa maganar yana kallon gefen da suke tsaye shida Bilal, d'ago kan da mom tayi sukayi ido biyu da Bilal dake gefen Mahmud yayi saurin b'uya a bayansa, kallonta Mahmud yayi sannan ya jawo hannun Bilal dake bayansa ya durk'usa daidai tsawonsa tare da d'ora hannuwansa akan kafad'unsa,

"Bilal! kai bazakaje kayiwa mom oyoyo bane?, dubi yanda Bassam yaje yayi mata ta d'aukesa kai baka so ne ta d'aukeka?" kad'a masa kai yayi ahankali yaje saitin kunnensa yace

"Yaya inajin tsorone"

"Karkaji wani tsoro, ka saki jikinki ba abunda zatayi maka saboda haka

Please Login or Register in order to submit comment