Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga k'arshe haushi da takaicin yarufesu a tunaninsu fushi yakeyi dasu don sun nema masa aure, baccin gata suka yimasa,

Tuni Billy tayi bankwana da 'yan makarantarsu zainab har da kukanta haka ma husnah randa zata wuce yini tayi tana kuka, oh Billy ba kunya kowata wahala dady baisha da itaba wajen zancen ajiye karatunta ta amince cikin sauk'i abun nema yasamu, Wanda hakanne yasake tabbatarwa da dady irin soyayya da k'aunar da takeyiwa d'an uwanta wanda sai yanzu yafahimci cewa ko lokacin da tahak'ura da aurensa k'arfin soyayyar 'yar uwarta ce data rinjayi tasa yasa ta iya jurewa da hak'urewa bawai don bata sonsa.

Saboda yanda Umma taji haushin kashe masu wayar da yayi yasa takira Billy tace kada ta tab'a nunawa Mahmud cewa shizata aura koya kirata, kawai tafita batunsa inya iso yaga kowaye amaryarsa, ko kad'an itaka kam Billy wannan plan beyi mata ba, amma saboda Umma dole tayi hak'uri dama itama yabata haushi kiransa da kullum take famanyi baya d'aga waya, nan take ta amince da abunda Umma tace.

Mom kuwa ita tashige gaba wajen hidimar bikin dama Ummi nacan na fama da nonuwanta dake ciwo saboda yayen da tayi don haka takoma gefe tana kallonsu iya nata abunda yazama dole tayi amatsayinta na uwar d'iya, duk da mom gaba d'aya hidimar ta tuno mata da abubuwan da suka faru da dama alokacin bukinsu yaya Mahmud amma haka tajure ta manta da komai tayi imani da Allah yabata Basmah kuma shiya karb'i abissa.

Ana saura sati d'aya d'aurin aure Mahmud yaje yasiyo sabuwar waya yasaka layinsa aciki don har 'yar rama sai da yayi saboda tunanin auren da ummanshi ke son yimasa daga k'arshe ya yanke shawarar zai lallab'a Umma tayi hak'uri idan yaje hutu daga nan sai ya d'aukikke 'yarsa sudawowarsu kuma bazai komaba sai sadda yasan anbuk'aci ganinsa, to alokacin yasan babu wanda zai takurasa da zancen auren, wannan dalili yasa yayi tunanin sayen wata wayar yabud'e layinsa.

Kamar da wasa umma na zaune sun gama waya da alhaji akan ya canzawa Mahmud gida saboda yanda taga gaba d'aya wancan yafita ransa saboda rashin matarsa tace bari tagwada kiransa taji ko zata shiga, ai kuwa cikin sa'a bugu biyu tayi taji tafara ringing, Mahmud da gama searching d'in wayar kenan yaga Kiran Umma yashigo, gabansa ne yafad'i yayi saurin tsinke kiran yana faman jero addu'o'i kafin yakirata.

Saida takusa tsinkewa sannan tad'aga tare da cewa

"Agaisheka my son, ubangiji Allah dai yayi maka albarka kuma yarabaka da wahala, yanzu Mahmud mukake kashewa waya don muntirsasaka kayi aure? Wai shine har zaka d'auki fushi damu?" Jikinsa ne yayi sanyi cikin girmamawa yace

"Kuyi hak'uri Umma nayi kuskure, kuma lalacewa wayata tayi wlh ba kasheta nayiba, Umma dole inyi maki biyayya amma kibari har sai nadawo sai muyi magana, idanma so kikeyi inje har gidansu wacce kika zab'amun da kaina innemo aurenta duk da nasan bana sonta wlh zanje"

"Dalla rufemun baki wani zakayiwa dad'in baki, ai tunda abunnaka yazama tsiya munriga mungama yin komai idan kaga dama kada kadawo, wlh kahad'u da b'acin raina, satinnan maizuwa za'a kawo maka mata don haka yarage naka, ita wacce ma kake zancen aure zatayi itama satinnan da wanda ranta keso yanzu kaga kai saika tabbata a gauronka tunda bakasan ciwon kankaba " sannan takashe wayarta.

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Billy aure zatayi dama shiyasa tak'i d'aga wayarsa? Tabbas idan hakane taci amanar k'auna kuma sai Allah yakamata, amma taya zai yuyu yabari wani ya aure masa farincikinsa bayan ya d'aukarwa Basmah alk'awarin zai kawota amatsayin matarsa kuam burin ransa da zata iya kula masu da 'yarsu" yafad'a tare da lalubo lambarta awayarsa,

Billy dake zaune ita da Batool tana tuyar wainar fulawa ita kuma Batool tana kallon pics a wayarta taji wayar tana ruri, ABBAN MY BABY..da tagani arubuce jikin screen d'in nayawo yasa tamik'awa Billy wayar tana fad'in

"Allah sarki yaya Mahmud, walh tausayi yake bani" k'in d'aga wayar da Billy tayi har ta tsinke yasa Batool taci gaba da cewa

"Allah twiny bakida kirki, ai wannan ma mugunta ne, ita kuma Umma Allah tafiye tayarwa da rayuwa hankali, ko tsoro batayi yashiga wani halin" zataci gaba da maganar Billy ta aza yatsanta abaki alamar tayi shiru saboda kiran sa daya sake shigowa, cike da farincikin dake tabbatarwa Mahmud da cewa hankalinta kwance yake bata cikin damuwa kamarsa tace

"Hello yaya Ina wuni?"

Rufe idanuwa yayi cike da takaici kafin yace

"Menene gaskiyar abunda naji ana fad'a" cikin b'acin rai, zaro idanuwa Billy tayi kafin ta had'iye wasu yawu da k'yar tace

"Name fa?" Jin yayi tazo masa da tambayar cikin rene, yana wani irin huci yamik'e cikin b'acin rai da k'arfi yace

"Karki maidani sakarai Bilkisu, kada kisa nakasa controlling kaina bisa renin hankali irin naki, nizaki yaudara, nizaki ciwa amana saboda bakida tausayi, gaba d'aya baki damu daniba saboda tsananin sonkai irin naki kin manta da soyayya da k'aunar da nake yimaki gaba d'aya, koda yaushe burinki insha wahalar rayuwa bayan kinsan cewa my life is incomplete with out you" lowering voice d'insa yayi sannan yaci gaba da cewa "Bilkisu kesani Ina sonki sosai, qaddarace tashiga tsakanina dake har muka nisanta da juna amma shine kuma qaddara tasake bamu dama zakije ki auri wani bayanni, kuma har kina farinciki da hakan"

Amaimakon ranta yab'aci da kalaman da yake yimata saima murmushi take famanyi jin yanda har yanzu wannan soyayyar da yake yimata bata canzaba, ahankali cikin muryar da duk abunsa dole ta tank'wasa b'acin ransa tace

"Haba yaya, meye abun b'acin rai anan bayan kaima auren zakayi, ni inaga kamar lokaci yayi daya dace muhutar da kanmu musama zukatanmu natsuwa tunda kowanenmu aure zai yi, pls kai yayanane kamanta da komai karik'eni ababban matsayi na 'yar uwarka domin yafi muhimmanci akan wancan matsayin, zaka rabu dani wataran idan Ina matarka amma amatsayin k'aunarka bazamu tab"a rabuwaba har abada zamu rayu nahar abada amatsayin 'yan uwa batare da munrabeba..." Tsabar takaicin kalamanta baisan lokacinda ya kashe wayarba tare da blocking d'in no. Zaune yayi yana tunanin inda kalamanta suka sama gaba, wato inya fahimta dai da gaskene auren zatayi, kuma taciresa aransa bata sonsa, fad'awa yayi kan gadon fuskarsa na kallon cielyn idanuwansa arufe yace

"Am sorry Basmah, bazan iya cika maki burinki ba saboda 'yar uwarki tadena sona"

Itakam dariya tayi tare daci gaba da tuyar wainar fulawarta duk da k'asan zuciyarta bataji dad'in haka ba, duka Batool ta kaimata abaya tare da cewa

"Wlh Allah bakyau abunda kikayi, banda Umma ce tatsara hakan Allah dasaina fad'a masa gaskiya"

"Hh ai Umma tace surprise me take son yimasa"

"Jacan don Allah surprise ko suffering, Allah yasa yaya Mahmud yakirasa yafad'a masa"

"Ba Amin ba wlh, ai k'ara yasan ba'a samun mai gadon zinari cikin sauk'i" haka dai sukaci gaba da firarsu har dare Batool nak'ara enlighten d'inta akan rayuwar aure,

Da daddare suka kaita gida itada Dr Ahmad saboda yanzu arzik'i yafara bud'uwa har yasai mota kuma gininsa na k'aton gidan da yakeyi nacan yafara azawa a anguwar maitama,

Shawarar da Umma taba Alhaji ita yabi don wani d'aya daga cikin gidansa dake opposite dasu yasa aka gyarawa Mahmud, dady kuwa bai dubi kayan Basmah dake can ba yasa aka zubawa Billy nata wasu kala daban sabon design kamar yanda yayiwa 'yan uwanta, kodasu baba k'arami suka nuna masa cewa kamata yayi ace tunda na Basmah basuyi komaiba abarmatasu tazaunesu cewa yayi a'a ai hakan bai halattaba domin kayanta hak'k'in magadan tane, sannan itama Billy tanada hakki dashi don haka kamar yanda yayiwa 'yan uwanta itama dole yayi mata,

Billy dai cewa tayi babu wani program da zatayi inba walima ba, haka akai ko ranar juma'a akayi walima taji da gani, sosai Billy tayi kuka ita da Batool tunawa da 'yar uwarsu Basmah saboda kusan malaman da sukayi wa'azi a waccan walimar aurensu na farko sune suka sakeyi a wannan, bayan an kammala aka raba manya manyan jikkuna da aka rubutawa HAPPY MARRIEGE LIFE BILKISU AND MAHMUD PILOT, wacce ak'asawa cutecy Little's Billy & Basmah, babu komai aciki illa kayan motsa baki kala kala da drinks da naman kaji dasu snacks ga take away d'insu friedrice da tasha kayan lambu kai komaidai Masha Allah Masha Allah

Musamman dady yayi booking d'in jirgin da zaikai amarya da wud'anda sukazo d'aukarta da masu kaita don tak'aita nisan tafiya da Basu wuce mutum takwas ba, had'i da ita da mom goma, 'yan uwan Ummi uku dana dady uku, sai faraaha da Batool sannan mom da amarya wanda idan aka qidanya kud'in jirgin da dady zai biya bakomai bane acikin dukiyar da Allah yayi masa,

Da misalin k'arfe 1:00pm aka d'aura auren Mahmud pilot da Bilkisu Bashar maifunitures bisa sadaki dubu d'ari lak'adan ba ajalanba, indaana gama d'aurin aure yaya Mahmud ya damk'a matasu a hannunta. Tuni yaya Mahmud yabi 'ya d'aurin aure suka wuce don yace shi bazaibi mataba kuma dole dashi za'aje kai 'yar uwarsa rabin ransa wanda hakan yasa yabi 'yan d'aurin are saboda jirgin da za'a shiga kai Billy bazai tashi ba sai k'arfe 5:00pm namarece,

Billy kam yau idanu sun raina fata, duk d'oki da farincikin da takeyi zata auri masoyinta saida yakau saboda kukan data sharb'a, momce da kanta tarik'ata takaita wajensu dady da yannensa dake part d'insa lokacin da za'atafi suka yimata nasiha sosai tare da adduar Allah ya tamata rik'on 'yar 'yaruwarta data barmata amana sannan aka wuce da ita part d'in Ummi dake zaune tare da wasu 'yan uwanta tana rungume dasu little, nan suma suka yimata nasiha mai ratsa jiki wacce tasa kukan nata yak'ara tsananta, hannunta Ummi tarik'o sannan ta damk'a mata little Billy a hannunta tace

"Bilkisu ga amanar marainiyar Allah nan a hannunki, kece uwarta yanzu kuma gatanta, shin amatsayina na mahaifiyarki wane irin tabbaci zaki bani bisa tarbiyar dana yimaki akanta" cikin shesshekar kuka Billy tace

"Ummi zankula da ita bisa gaskiya da amana kuma zan bata tarbiya bisa tsoron Allah batare dana cutar da itaba har izuwa k'arshen rayuwata." kukane yaci k'arfin Billy takasa cigaba da magana, ita kanta Ummi hawaye takeyi kafin tayi k'arfin halin cewa

"Alhamdulillah, ya isa haka, ahaka kad'ai kika tsaya kuma kika tabbatar da abunda kika fad'a natabbata Bilkisu zatayi rayuwa maikyau kuma 'yar uwarki zatayi alfahari dake kuma nima zaki sani farinciki, tashi kuje cikin amincin Allah, ubangiji Allah yayi maki albarka kuma yabaki ikon rik'e wannan amana, yabaki zuri'a masu albarka" tana rufe baki ta tashi tashige d'aki tana kukan rabuwa da 'yar tata, duk wud'anda ke d'akin suma saida suka zubar da hawaye saboda tausayi, mom ma tayi kuka sosai kaman ba gobe sannan aka fita da ita zuwa gidan mijinta, dama tuni yaya Mahmud yawuce da kayan little Billy don haka Batool ta d'aukota yayin da faraaha ta d'auko little Basmah don gida tabar mu'azzam wajen Ummi da take shima anjima da yayesa tun yanada shekara d'aya da wata hud'u saboda shigar cikin da faraaha yasamu na biyu.

Mahmud kuwa bai baro India ba sai ranar d'aurin aure tunda asuba, shima d'in saboda Alhaji ne daya kirasa yayi masa fad'a sosai tare da nuna masa b'acin ransa sannan yabaro k'asar don data tashi za'a biyewa bazai dawoba sai wani sati,

Kai taye jirginsu na isa gidan Umma Suka nufa da ita, inda farinciki yasa tarasa Ina zatasa kanta, murna da farinciki tayi sosai harda 'yan hawayenta kafin tayimata nasiha da samata albarka, tare da ita aka kai Billy har cikin gidanta dake kallon nasu, mom nata tsokanarta tace

Ita kam babu wata sarakkuta tsakaninta dasu, ita gwaggoce kuma uwar d'iya don haka bawata kunya da zataji,

Sai misalin k'arfe 8:30pm nadare Mahmud ya iso gida tare da rakiyar wani abokinsa daya sauka wajensa tunk'arfe hud'u na marece amma yak'i shigowa garin sai yanzu, lokacin yaya Mahmud yafita shida faraaharsa da little Basmah zagaya gari, ita kuma Batool tana can tareda Billy don cewa tayi tsoro takeji bazata iya zama ita kad'aiba, kasancewar bak'i na part d'in da aka saukesu yasa Mahmud wucewa kai tsaye d'akin mahaifinsa don tun amota sukayi waya, koda yashiga Umma naciki taje kaimasa abinci fuskarnan tasa ko walwala babu, cikin farinciki Suka tarbesa tare da yimasa sannu da zuwa, ganin fuskarsa babu walwala yasa Suka zaunar dashi sunata bashi hak'uri da lallashinsa, Umma da kanta ta dinga bashi abinci abaki tana bashi magana har saida taga ya saki ransa sannan tace yaje ya watso ruwa sai yazo yagaida bak'i,

Haka kuwa akayi d'akinsa ya wuce ya watso ruwa, sannan yaje ya gaida bak'in da akace lokacin mom tashiga toilet 'yan uwan dady kuwa dama yasansu baiyi mamakin ganinsu ba tuda 'yan uwane yazata bukin nasa sukazo, na Ummi kuma bai wayesu ba, abokinsa yabi suka sake fita inda yanata yimasa Sheri wai ango ango, suna tashi su yaya Mahmud nadawowa, koda yasamu labarin cewa d'an uwansa ya iso cewa yayi a k'yalesa gone zasu had'u kafin suwuce don yagaji bacci yakeji,

Batool na ganin goma tayi ta tattara inata inata tayi wajen mom gida yarage Billy kad'aice aciki,

Saida goma da rabi tawuce Billy taji motsin shigowarsa shida abokinsa da sauri taja mayafin fuskarta tarufe, tsaye yayi bakin k'ofa tare da mere baki yana kallonta kafin shureim yayi k'ok'arin shigowa dashi da k'arfi, muryar Junior suka jiyo a palour hannunsa d'auke da wani tray daya sha soyayyin kaji da sukasha source anyi rapin d'insu da wata leda mai kyalkyali sai had'ad'd'en fruithsalad mai sanyin gaske daya sha madara da zuma acikin wani bowl Umma da taji tsayawar motarsu tace yakawo, shureim ne yaje yakarb'o yakawo ya ajiye masu saman madubi sannan yayi masu saida safe, guntun tsaki yaja tare da bin bayansa ya rufo gidan, har zai shiga yaji ankira wayarsa Yana dubawa yaga ashe Batool ce,

Cike da gajiya ya d'aga had'e da cewa

"Hello sister" murya k'asa k'asa tace

"Na'am yaya Mahmud, andawo lpy?"

"Lpy klw, Ina mijinkine yabarki yin waya a wannan tsohon daren"

"Yaya don Allah ba wannan ba, kashiga d'aki surprise nanan anyi maka believe me, yanzu haka muna nan.." ai bata rufe baki ba yayi saurin shiga cikin bedroom d'in yana tunanin wani abu da zuciyarsa ke raya masa, bakin gadon ya isa had'e da yaye mayafin fuskar Billy, wa zai gani a cikin gidansa, a d'akinsa kuma amatsayin amaryarsa inba Billy ba, kenan hasashen da yakeyi yazama gaskiya? Tirk'ashi yafad'a abayyane tare da murza idanuwansa Yana kallonta, wani irin murmushi ta sakar masa da yasa yaji da zai iya mutuwa alokacin d'aya mutu, tuna kalaman data yimasa yasa sai kuma yabasar tare da kauda kai yana fad'in

"Meyasa kika aureni bayan kince bakya Sona"

"Bantab'a cewa bana sonka ba saidai ince bazanyi farinciki idanna aureka ba kuma shima sab.." dakatar da ita yayi ta hanyanr d'aga mata hannu don bayason jin dalilinta tunda ya dad'e da saninsa,

"Meyasa kika aureni yanzu?"

"Saboda kai kad'aine na mallakawa zuciyata, kuma kaine farincikina kuma hasken dake yimun jagora acikin tafiya aduniyar soyayya"

"Meyasa kika b'oyemun cewa ni zaki aura kikasa zuciyata takusa tarwatsewa"

"Saboda intabbatar maka da cewa komai rintsi komai wuya atare zamu rayu kuma atare zamu mutu, intabbatar maka da cewa kai kad'aine kake da mallakina da kuma duk abunda ketare dani"

"Bilkisu kin tabbata har yanzu kina Sona kuwa"

"Karok'i Allah yabamu aron lokaci da aryuwa da kanka zaka tabbatar da hakan"

Juyowa yayi yana kallonta had'e da cewa "akoda yaushe kece mai yin nasara akaina saboda hakurinki da juriyarki, kiyafemun bisa kausasan kalaman danayi agareki, tsantsar b'acin rai da kishin jin cewa wani zai mallakeki yasa na aikata haka"

"Konice iya abunda zanyi maka kenan koma fiye da haka, bazan iya auren waniba ba bacin soyayyarka da k'aunarka na cikin zuciyata idanko nayi hakan to natabbata kowaye gangar jikina kawai ya aura amma zuciya da rouhina gaba d'aya na wajenka" wata irin runguma ya kaimata had'e da cewa

"Ina sonki Bilkisu, Ina sonki sosai fiye da wandakike yimun"

Wayarsa yaciro ya yiwa Batool transfer d'in naira dubu hamsin sannan ya tura mata message kamar haka.

_Thank you sister ga goron albishir d'inki nan kici da hak'uri tabbas badon keba da zuciya ta d'ebeni daren yau natabka babbar asara wajen yiwa Allah godiya da wannan ni'imar daya yimun_

Karb'e wayar tayi ahanunsa da sauri tana karanta message d'in da taga yatura ga contact d'in Batool data gani aeubuce, murmushi tayi aranta tace Allah sarki my twiny kindai yi nasarar bayyana sirrin kafin yagani da kansa ahankali ta furta Ina sonku 'yan uwana, shima murmushin yayi tare da juyawa yayi sujudush shukur sannan ya d'ago ya kalleta yace

"Nima Ina sonki sosai 'yar uwata kuma matata"...



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

πŸ”š _*END*_πŸ”š

πŸ’ŽPage_____101πŸ’Ž


Lumshe idanuwanta tayi had'e da bud'ewa itama tace

"Nima Ina sonka yayana mijina" nan take yaji kamar ank'ara masa wani kuzari akan wanda yake dashi duk kuwa da gajiyar doguwar tafiyar da yayo,

Mik'ewa yayi yacire mata mayafin sannan yarik'o hannunta suka shiga toilet, da kansa ya kunna fanfo ya dinga d'ebo ruwan a hannunsa yana zuba mata tayi arwala saida ta kammala sannan shima yayi tasa suka fito suna yiwa junansu kallon so da k'auna, ganin yanda gaba d'aya yacanza alokaci d'aya yasa Billy ta noce kanta k'asa tana murmushi, tabbas arayuwa babu abunda yakai hak'uri dad'i, lokacin yinsane kawai keda wahala har mutum yaji tamkar kamar bazai tab'a fita cikin qunci da damuwa ba, yau gata ga masoyinta da farko tayi tsammanin cewa ya haramta gareta kenan har abada sai gashi Allah ya halasta matashi akaro na biyu, tana cikin wannan tunaninne taji yarik'o hannunta lokacin harya shimfid'a masu abun sallah,

"Me kike tunani kuma bayan Allah yariga daya mallaka makini gaba d'aya, kizo mumik'a godiyarmu agaresa saboda yacika mana burinmu nazamowa ma'aurata a k'ark'ashin inuwa d'aya" yafad'a tare da shiga gaba ya kabbarta sallah, raka'a biyu yayi masu a daddafe ya sallame sannan yajuyo had'e da d'auko chicken source d'in da Umma ta aiko masu dashi tare da fruithsalad, yage ledar yayi sanna ya jawota ajikinsa ya dinga bata tanaci itama tana basa, saida suka cikawa juna ciki sannan yaje kitchen ya d'auko spoon d'aya yana bata fruithsalad d'in abaki tanasha har saida tak'oshi

Kusan atare suka kwashe kayan kafin ta koma shiga toilet ta wanko bakinta, tana fitowa taga fitilar bedroom d'in akashe, gaban tane ya fad'i kafin jikinta ya soma rawa jin mahmud yarik'o hannunta, runtse idanuwa tayi yayinda shikuma ya d'auketa cak yadireta akan gado, wani irin shauk'i da k'aunarta yaji suna fizgarsa alokaci d'aya wanda nan take yafara aika mata da sak'wanni masu wuyar fassarawa, jin haka yasa kukan da tund'azu take k'ok'arin danne wa ya kucce mata, k'ok'arin yanda zata tsere masa tafarayi amma ina tuni yayi mata damk'ar da bazata iyaba, kuka takeyi sosai tun kafin komai ya kankama saboda yanda tasa tsoron abun aranta, ahankali taji ya rad'a mata akunnuwa,

"Pls noorul hayat" had'e da sakar mata kiss acikin kunnen, jikinta narawa yayi nasarar rabata da kayan jikinta yana faman fitar da wani nishi kamar zaki, jin yafara karanto addu'ar saduwa yasa Billy tayi saurin rintse idanuwanta, ai bata karasa rufewaba tasaki wata irin k'ara da tasa yayi saurin had'e bakinsa da nata,

Yau kam Mahmud yagano sirrin dake cikin auren so da kuma k'auna, don badon Billy ta nuna raggwanci da rakiba zai iya cewa har safiya tawaye yanada zarrar da zai iyaci gaba da kashe arna, gaba d'aya ji yake wata irin sabuwar yunwantar na taso masa duk kuwa da jimawar da yayi yana d'ebe k'ishirwar da yadad'e tana taso masa akanta, Billy kuwa suma kad'aine batayiba amma tasha matuk'ar wahala, tayi nadamar soyayya ba adadi idan haka take, tuncikin dare yake rarrashinta har asuba tayi tana kuka, bata bar kukan ba har saida taji ya sauka kan gadon ruwa masu zafi ya had'o had'e da zuwa ya ciccib'eta tana faman wutsil wutsil da k'afafuwa bai direta ko inaba sai bayin, taimaka mata yayi tagasa jikinta sannan ya dawo da ita, bud'e idanuwanta da suka kumbura tayi tare da turo baki cikin 'yar dasasshiyar muryarta da bata fita saboda kukan da tayi tace

"Ni ka ajiyeni into wanka" yanaji ana kiran sallah amma ina yakasa hak'ura har saida angulu ta komawa gidanta na tsamiya, duk da dai zafin yanzu bai kai nafarko ba haka bai hana Billy ta narke masaba tanata kuka, yayi rarrashi har ya gaji amma tak'iyin shiru, harara kuwa yashata babu adadi, wankan sa yaje yayo sannan ya fice zuwa masallaci, lokacin kuwa har angama dalla mutane sunwatse cikin masallaci sai d'aid'aiku, ai yana fita dak'yar Billy tasamu ta lallab'a tasama k'ofar key sannan tashiga toilet tagasa jikinta da sai faman rad'ad'i yake yimata sosai tayo wanka, bayan tafito ta jaye bedsheet d'in ta d'auko wani ta shimfid'a, sallah tayi had'e da karanta azkar sannan tahaye saman gado takwanta tana faman ajiyar zuciya, koda ya dawo yamurd'a k'ofar yajita da key, dariya ta bashi sosai aransa yace

"Tab lallai ashe akwai aiki gabana" sannan ya juya yakoma warsa parlour saman 3seater yayi kwancensa aransa yana fad'in tabbas kowace mace da yanayin da Allah yayi mata, kuma tanada baiwar da Allah yayi mata daba kowace mace 'yar uwarta keda itaba, Billynsa kam tamusammance, amma tafiye raki, inda kenan Basmah tad'arata, don Basmah kam nada hak'uri da juriya da duk tsawon lokacin da zai d'auka bazata tab'a nuna masa gazawar taba, da haka bacci yayi awon gaba dashi,

Dashi har ita basu farkaba sai misalin k'arfe goma nasafe koshi muryar junior ce ta tadashi daya shigo falon rik'e da hannun little, da gudu ta k'araso wajensa cikin muryar gwarancinta tana fad'in

"Abba" murmushi yayi bayan yatashi zaune tare da d'aukarta ya aza saman cinyarsa yana fad'in

"Oyoyo my little, kintashi lafiya?" Hannunta tad'aga tana nuna junior d'ayan hannun na abaki tace

"Uncle"

"Me uncle yayi maki?" yafad'a yana kallonsa,

"A'a Yaya ummace tace muzo mugani idan kuntashi za'a kawo maku breakfast" junior yafad'a cikin inda inda,

"Ok jeka kayiwa auntynka nocking tabud'e" yana wucewa little ta fashe da kuka tana fad'in

"Ni janje, Abba"

Sauketa yayi da gudu tanufi k'ofar d'akin tana bubbugawa cikin sautin da ko junior dake kusa da ita ba lallaine yaji sosai ba, idan kuma ya bubbuga saita fashe da kuka, hakan yasa Mahmud yace yazo yawuce ya k'yaleta, ita kuma Billy dama tun d'azu tatashi tashiga toilet tayo wanka sannan tayi simple make up d'inta cikin wani material peach colour, tana jin surutunsu natashi sama sama amma saboda tsoro takasa bud'ewa saida taji irin rigimar da little keyi da junior sannan tataso tana takawa ahankali tabud'e k'ofar.

Little na ganinta taruga ta d'auketa tana fad'in "yayya" yanda taji su Bassam nafad'a

Rungumeta billy tayi ajikinta sosai tare da cewa

"Iyyeee little d'in Ummi ina kika tafi jiya kika barni?" Kissing d'in kumatunta billy tayi had'e da cewa "ur yayya missed you so much"

Dariya tayi tana wasa da d'an kunnen dake lak'e da kunnen nata, parloun Billy tanufa kanta sunkuye a k'asa ta zauna kujerar dake facing d'insa har lokacin kanta na k'asa aduk'e cikin jin kunya tace

"Ina kwana yaya?"

"Bazan amsaba don wannan gaisuwar batakai cikiba har sai kindawo nan akusa dani" duk da tanajin tsoro hakan bai hanata mik'ewaba taje kusa dashi ta zauna" hannu yasa yajawota ajikinsa tare da cewa

"Lafiya klw my fearfear noorul hayat"

Kallon Billy da har lokacin bata d'ago kanta ba little tayi sannan takalli abbanta tare da k'ok'arin turemasa hannu tana fad'in

"Bayyi tafamun yayya" d'ago kai Billy tayi ta kalli little sannan ta kallesa tabushe da dariya, dariya itama little tayi had'e da bud'e hannuwa tarungume Billy tana kallonsa cikin yarinta tace

"Yayya tace" mahmud daya zama speechless jin abunda little tafad'a yana ganin haka sai shima ya rungumo Billy ajikinsa tare da had'e girarsa yace

"Yayya tace"

"O'oh Abba yayya tace" tafad'a tana kukan shagwab'a dariya sukayi gaba d'aya ya mik'a hannu zai d'auketa ta lak'alk'ame wuyanta,

"Shikenan naji takice amma daga yau kada inkoma ji kinkirata da Yayya, sunanta mommah kinji ko, idan ko ba haka ba zata zama yayyata ba taki ba" yak'are maganar yan nunata da yatsa irin tabbatarwa da mutum abu,


Yanda take kallon sane ya tabbatar masa da cewa tafahimci meyake nufi don haka sai yace

"Fad'a naji

Please Login or Register in order to submit comment