Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyautar littafin ga wacce kukaga sunanta Asama๐Ÿ‘†๐Ÿป don haka banida sauran ikon da zan iya kyautar da wani yanki daga ciki sai idan ita taga damar yin hakan, but idan muhimmancinka agareni yakai mak'ura nakan mik'o sak'on gaisuwa tamusamman agareka, saboda haka kusani yau gaisuwar takuce GHOST READER'S na littafin 'YAN UWANA NE! Ina fatar alkhairin Allah yakai gareku aduk inda kuke, duk da cewa bakwayin comment balle godiya kunada matuk'ar muhimmanci agareni domin ko kad'an rashin yin hakan baya damuna๐Ÿ˜ƒ, lada nake neman samu tahanyar ilmantarwa da fad'akarwa kuma natabbata idan kunkaranta zan samu gwargwadon abubuwa masu kyau da kuka tsinta aciki kuma kukayi aiki dasu don haka jinjina agareku tare da fatar kowacenku na cikin k'oshin lafiya, Billy s fari na sonku over๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜_

๐Ÿ’ŽPage_____34๐Ÿ’Ž


Tunda dady yad'auko mom yake kallon tsantsar kyau da kuma kwarjini da tayi masa, tuk'i yakeyi amma duk bayan sakon biyar sai yajuyo yana kallonta, da mom talura da haka sai tasaki murmushi tana fad'a acikin zuciyarta cewa tabbasa hak'ata gab take data cinma ruwa, ai wajen kagani alhajina wani shagalin ma sai aiki ya kankama, hannunsa taji ya d'ora akan nata dake saman cinyarta yana d'an mammatsawa ahankali, lumshe idanuwa tayi kafin taji muryarsa ta dakan mata dodon kunnuwa.

"Ranki yadad'e wannan murmushin fa?, kinga yanda kikayi kyau kuwa?"

"Hmm anya wannan maganar dagaske kakeyi?"

"Sosai ma kuwa" yafad'a yana d'an matso da jininsa ga starring mota" wani irin murmushi tayi da yabayyanar da hak'oranta da yasa lokaci guda dady ya danne burkin mota yana fad'in "Ma sha Allah, irin wanna murmushin zai iyasa na saki titi batare dana ankaraba, a gaskiya bazan iya jurewa ganin kina yinsa awajeba don duk namijin daya gansa toya matuk'ar cutar da zuciyata ya k'arasa maganar cikin yimata rad'a akunne" ai nan take mom taji wani abu yarr acikin jikinta, soyayyar dady mai tsanani tak'ara nink'aya acikin zuciyarta, ji takeyi tabbas bazata iya jurar had'a alhajinta da kowace irin macce ba, wani kuzari tasamu azuciyarta naganin cewa duk yanda zatayi takori Aisha agidanta sai tayi don tabbatarwa kanta da cewa shi natane ita kad'ai kuma ita kad'aice wacce zai dinga yiwa irin wud'annan kalaman. K'arar 'yan yatsunsa daya murza taji a fuskarta yana fad'in,

"What? Mekike tunani kobaki yarda bane?"

"A'a nayarda mana kawai shakku nakeyi akan anya inada matsayin da zakayi irin wannan kishi akaina kuwa" murmushi yayi daidai lokacin da yakaryo layin gidansa tare da juyowa yana kallonta,

"Tabbas yau zan cire maki wannan shakkun, natabbata haka zai fahimtar dake zunzurutun son da nakeyi maki yakai matsayin da zanyi kishin da nakeyi maki fiye da tunani"

"Allah yasa haka" tafad'a daidai lokacin da yake k'ok'arin tura kan motarsa cikin gidan nasu da maigadi ya wangame masa gate yana kwasar gaisuwa, yana ganin mom da sauri yaja baya tare da d'ora hannuwa akai yana fad'in

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'unn, shikenan annobar gidan nan tadawo, wayyo 'yar dimirmiyar yarinya Bilkisu da Bilal natausaya maku kuma nima na tausayawa kaina don wallahi natabbatar wannan karon bak'in halinta zai iyasa inkasa tura gate agidannan saidai gate d'in yaturani, bayan tafiyarki banida matsala da kowa, inci mai kyau insha maikyau, babu tsawa balle zagi ko harara, alhaji badon kar ince wani abuba da nace wallahi Allah bakasona da alkhairi, Haba wannan wace iriyar musibace?" Ya k'are maganar yana goge guntayen hawayen da suka fito masa a idanuwa, zai sake sakin wata maganar kenan yaji muryar dady yana k'wallo masa kira, dagudu ya isa wajen lokacin dady na k'ok'arin bud'ewa mom gambu tafito, juyawa yayi da sauri yana fad'a cikin muryar da shi kad'ai ke iya jinta.

"Wayyo alhaji, walh kana cikin matsalar jarabtuwa da wannan muguwar mata" juyowa yayi tare da cewa gani alhaji batare da yakalli inda mom takeba,

"Yawwa kafiddowa hajia kayanta ka kaimata aciki" dady yafad'a tare da wucewa gaba mom nabiye dashi abaya, sai alokacin maigadi yakalli mom yace

"Sannu da dawowa" wata uwar harara ta watsa masa batare da tace komai ba tawuce abunta.


Ita dai ummi tunda dady yadawo bayan la'asar take lura da yanayinsa duk da yana k'ok'arin b'oye mata nuna damu warsa akan dawowar mom amma dole saida yadinga yin wasu abubuwan dashi kansa baisan sun bayyana ba, saboda miji da mata sai Allah duk yanda basajin dad'in zama da juna aduk lokacin da suka nisanta da juna nawani tsawon lokaci to tabbas idan zasu had'u sai kaga suna d'oki da mararin had'uwa da juna, ummi naganin hakan tayi murmushi tare da danne kishin dake k'ok'arin motsamata ta hanyar addu'a

" _Rabbhi a'uzu bika min hamazatish shayad'in, wa a'uzu bika rabbhi anyahdurun_" ita tayita maimaitawa cikin ikon Allah taji komai ya lafa mata azuciya. Bayan sallar isha'i daya fito zai tafi d'auko mom ita tarakosa da kanta har bakin mota tana gyara masa zaman hular kansa had'e da yimasa fatan Allah ya kiyaye kuma adawo lpy batare da tasake jin komai aranta ba.lokacin da tadawo paloun ta tarar da yaran gaba d'aya zaune itama tazauna acikinsu suna ta fira, nan tafara surko nasiha da wa'azi acikin firar tana nuna masu muhimmancin rik'e 'yan uwantaka da zumunta tare da nuna masu illar dake k'unshe cikin b'atawa iyaye rai da nemawa junansu duk abunda suke so akansu, jajircewa bisa kaifin takobin gaskiya tare da juriya da kuma hak'uri, sosai nasihar takama zukatansu suna sake yiwa Allah godiya daya basu Ummi acikin rayuwarsu kuma a matsayi na uwa, mahmud da yashigo lokacin da Ummi ke k'ark'are nasihar, yace

"Laaah..gaskiya banyar daba ummi anyimun wayau asako baya, ko so kikeyi 'yan uwana sufini k'aruwa da baiwar da Allah yabaki" murmushi ummi tayi lokacin da yake k'ok'arin zaunawa agabanta tare da nad'e k'afafuwansa yana kallonta "A'a babanah saidai in son kai zakayi amma nasan bazasu fikaba don kai kake da baiwar da Allah yasa 'yarka ta gadoka, babu zancen asako baya domin kai kadad'e da kiyaye wannan karatun harma da aikatashi" bud'e baki yayi zaiyi magana ummi ta katsesa ta hanyar cigaba da cewa

"Maza ka tasa k'annenka agaba suje su d'orawa mom d'inku abincin duk da kasan tafiso natabbata suna gab da isowa" haka kuwa akayi batare da sunyi mata mu suba suka nufi part d'in mom hadda Bilkisu da zuciyarta ke cike da fargabar dawowar mom d'in har sun fita ummi takira Basmah tabata turarukkan da suka sawo masu d'azu bayan taraba ta d'auki nata.

Saida suka kammala girkin tsaf wanda fiye da rabinsa Bilkisu ce tayi dayake dafadukan makaronice da tasha kifi sosai da wake, sosai mom kesonta shiyasa yaya Mahmud yace sudafa mata ita sannan suka feshe ko ina da turarukkan masu matuk'ar k'amshi suka kunna A.C sai part d'in yakoma tamkar na wata sabuwar amarya. Zaunawarsu kenan sukajiyo tsayawar motar dady, da gudu Bilal da Bassam suka rugo suna fad'in "Dady oyoyo" ganin mom yasa Bilal tsayawa batare da yak'araso ba, juyawa yayi yakoma daga ciki yana fad'in

"Aunty Billy kifoto ga mom nan kada ta iskoki" jikinsa har rawa yakeyi, da sauri ya Mahmud ya d'aukosa yana fad'in ya kwantar da hankalinsa babu abunda zata yimasa, "duba kagani ga yayya Basmah, ga yayya Batool, ga aunty Billy itama a zaune duka bazamu bari mom tayi maka komai ba kaji ko?" Bilal da har lokacin jikinsa bai daina rawa ba ya kalli Batool yace

"Yayya kikaini toilet zanyi fitsari" ganin yanda yarud'e yasa gaba d'ayansu suka taru suna rarrahinsa cike da kulawa suna jin ba dad'i a zuciyarsu.

Mom ce tayi sallamah a daidai k'ofar paloun had'e da d'ago labule, Allah sarki uwa uwace komai mugun halinta, cikin jin dad'i gaba d'ayansu suka rugo aguje hadda yaya Mahmud suka rungumeta, ai kuwa kamar jira Bilal keyi yaruga aguje cikin toilet har fitsarin na kuccikke masa.

๐Ÿ‘๐Ÿป _sorry fd late update naje anguwane u should manage with dis_












*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____35๐Ÿ’Ž


Bayansa Billy tabi tasamu har fitsarin ya gama fitowo a wandonsa, tsarki tayimasa sannan tarik'o hannunsa suka fito tare, tsaye tayi tana kallon yanda mom kebin yaranta d'aya bayan d'aya tana rungumesu tare da yimasu sunbata agoshi tana kawowa kan ya Mahmud tace

"Kai kam kayi girma da yawa kabari har sai Allah ya nuna mana nakawo maka matar da zaka aura inyaso ta wakilceni" bubbuga k'afa ya shigayi tamkar k'aramin yaro kafin yace "A'a ni mom bazan yarda da wannan wayon ba" rungumeta yayi saurinyi tare da cewa "welcome back, we missed you so much mom, home with out you is like a field of war with out no body" cikin farinciki tadinga kallon yaranta d'aya bayan d'aya tanajin wani irin nishad'i nak'ara bayyana k'arara a fuskarta, "I luv you so much my kids and i missed you too, life with out u and ur father is like missing my whole life, my Allah bless you for ever mom lovers" gaba d'ayansu suka amsa da amin suna dariya tare da rungumeta atare. Billy dake gefe rik'e da d'an uwanta taji inama ace mom zata iya gwada masu ko kad'anne daga cikin irin wannan soyayyar da take nunawa tsakaninta da 'ya'yanta, tabbas ta tabbata babu wani sauran bak'in ciki ko damuwa dazata samu gurbi acikin gidan su, amma kash tasan inba ikon Allah ba wannan abune mai matuk'ar wuya agareta, cike da Sha'awa taci gaba da kallon yanayin da mom takasance ciki ita da 'ya'yanta kafin tafara yunk'urin takowa cikin tsoro da fargaba, ahankali ta k'araso wajen har lokacin hannunta narik'e dana Bilal wanda takun tafiyar suce tasa hankalinsu yadawo ga 'yar uwarsu, cikin jin kunyar abunda sukayi na mantawa dasu suka k'araso wajen gaba d'ayansu kamar sun had'a baki inbanda Bassam daya kame hannun mom tamkar za'a k'waceasa ita suna fad'in

"We are sorry sister" tare da rik'o hannunta suka k'araso wajen mom datayi sororo tana kallonsu, cikin i'inar murya Billy kefurta "san..nu. da zu.wa mom" har mom ta d'auke kai cikin d'aure fuska sai kuma ta tuna da wani abun, juyowa tayi tana murmushin da baikai cikiba ta rungumo Billy ajiki tare da rad'a mata akunne "maza kija k'anenki kubar nan kafin inbayyanar maku da sabon halina da baku sani ba, ina son naganni dagani sai jinina donnayi kewarsu" d'ago Billy da jikinta yafara rawa tayi cikin lokaci guda tana dariya "thank u dota" tafad'a tare da duk'owa tarik'a hab'ar Bilal dake faman ja da baya yana b'uya abayan 'yar uwarsa tace "kai yaron Ummi yau ba magana" sannan tawuce batare data kalli kowanensu ba, murmushi sukayi cikin jin dad'in ganin yanda mom d'insu takarb'i 'yan uwansu batare da tsangomaba. Murmushin itama Billy tayi tana k'ok'arin danne damuwar dake neman taso mata alokaci d'aya kuma hawaye na neman bayyana a idanuwanta, da sauri ta duk'ar da kanta tana fad'in

"Ya Mahmud, yayya Basmah, twiny bari naje na sanyowa Bilal wando sai nadawo" batare da tajira mezasu cewa ba tayi saurin ficewa daga falon hawayen dake kokuwar fitowa a idanuwanta suka gangaro mata afuska, da gudu tabar part d'in tanufi d'an guarding d'in dake tsakanin part d'in mom, ummi da kuma dady.

Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun take fad'a tana kuka, Bilal ya rungumeta yace

"Aunty Billy kidena kuka ai muma muna da umminmu, mutafi muma tayi mana yanda mom tayiwa su yayya Basmah, kuma ni bazan koma wasa da ya Bassam ba tunda yak'yaleni don yaga mom d'insa, ALLAH yasa ma tasake komawa ko?"

Murmushi ne yakucce mata jin abunda Bilal kefad'a har lokacin tana kuka, rungumesa tayi na wani d'an lokaci sannan takunna fanfon dake can gefe ajikin d'akin ya Mahmud tawanke fuskarta. Juyowa tayi tana kallon Bilal "Bilal kada ka koma yin irin addu'ar da kayi d'azu, idan 'yan uwanmu sukaji baza suji dad'i ba kuma zasuyi fushi damu, kana son haka?" Girgiza kai yayi tace

"Good boy itama ummin muce kuma suna sonta yanda suke son umminmu don haka dolene muma musota kamar yanda muke son ummi kaji ko?"

"Eh amma ni nafison ummina akanta"

"Shikenan yanzu sai muje ko? Zaka fad'awa Ummi nayi kuka" girgiza kai yayi tare da langab'esa gefa sannan yace

"A'a bazan fad'a ba banaso ranta yab'aci"

"Good give me five" tafad'a bayan sun tafe tarik'o hannunsa suka nufi part d'insu suna wasa kamar babu abunda yafaru.

Dady kuwa part d'in Ummi ya wuce ya tarar da ita zaune tayi shiru tana tunanin yanda kuma zaman nasu zai kasance yanzu, jin sallamarsa yasa tafito daga duniyar tunani, murmushi tasakar masa tare da tasowa ta rungumesa.

"Sannu da dawo angon mom, hope kunzo lpy?" Shiru dady yayi yana tunanin wai ummi wacce irin macece da bazata tab'a barin damuwa ko b'acin rai suyi galaba akantaba. d'agota yayi tare da manna mata kiss a forehead yace

"Rabba'atul bait meyasa baki kishi a kaina ko kad'an?" Murmushi tayi bayan tasakesa had'e da juyowa tadawo kan kujera sai ga hawaye suna biyar kuncinta, cikin rikicewa da tashin hankali yak'araso wajenta tare da yin neal down agabanta cikin damuwa tare dayin nadamar abunda yafad'a yace

"Ki gafarceni oum Bilqees idan abunda nafad'ane yasa kika shiga cikin wannan hali, natuba rabba'atul bait, kiyi hakuri kiyafeni" runtse idanuwa tayi hawayen suka ida fitowa kwance a fuskarta,

"Abu Mahmud kanemi tsarin Allah da infara bayyana tsantsar kishin da nakeyi akanka, domin zai sanya adalcin da kake dashi a tsakanin nida matarka yayi rauni saboda tsoron kada karasani, kamanta sunan da nake dashi ne? AISHA fa akace, wlh dajin sunan zakasan cewa tanada matuk'ar kishi akan duk abunda take so, amma kuma Allah daya sanya kishin a kirjina sai yayi mani kyauta da ilimi da zai dinga jagoranci akaina, kayi hak'uri ina sonka kuma ina matuk'ar kishinka fiye da yanda kake tunani abu Mahmud"

Rungumeta yayi shima hawayen nazubo masa saboda tausayinta akan tsantsar hak'uri da kawaici da take dashi "sorry rabba'atul bait, u're the best among the betters wife in d world, am lucky to have u oum Bilqees"

"Me too, dadyn yara" suna ahakane su Billy suka shigo suna dariya, da gudu Bilal yarugo yana "oyoyo dady"

Dariya dady yayi tare da cewa "ka kuru my boy dana biyoka bashi, d'azu ina kallonka bakazo kayimun oyoyo ba sai dai Bassam yayimun" "sorry dady" yafad'a yana kallon Ummi dake dariya.

Mom nashiga d'aki taciro waya takira hajia kilishi, ringing biyu tayi ta d'auka "hello amarya agidan alhaji miye lbari"

"Daidai wlh qawata ya kika isa kin isa lfy dai ko?"

"Lafiya k'alau keni shafamun naji injin dai baki mantaba"

"Hhh bari kawai qawata kinga yanda alhajina ya rikice, hmm wlh shi kansa idan yazo hannu yau sai yagane bayada wayau, ita kuma waccan banzar dazaran yau munkeb'e da alhaji wlh k'aryarta tak'are don da ita har yaranta saina gasa masu aya ahannu kafin na salwantar da rayuwarsu" Batool ce dake lab'e tund'azu da tazo shigowa tacewa mom tazo taci abinci taci karo da kalaman da ke fita daga bakin mahaifiyarta tayi saurin rufe baki tana hawaye fuskarta d'auke da mamaki tadinga ja da baya har tabar wajen ta nufi d'akinsu cikin tashin hankali, ita kuwa mom hankali kwance tadinga wayarta da hajia kilishi tana cigaba da d'orata akan muguwar hanya.

Batool nashiga d'akinsu tafad'a jikin Basmah tana cewa "yayya Basmah munshiga ukku wlh mom bata canzaba ko kad'an, har yanzu zuciyarta nanan cike da tsanar Ummi da 'yan uwanmu, nan ta zayyanawa Basmah duk abunda taji mom nafad'i awaya, sosai hankalin basmah itama yatashi,


Kasancewar Basmah tafita shekaru yasa tafahimci cewa har sai matuk'ar dadynsu ya samu keb'ewa da mom hakan zai iya faruwa don haka yazama dole sudakatar da faruwar hakan, d'ago Batool tayi tace

"kiyi shiru 'yar uwa bazamu tab'a bari hakan yafaru ba, zamu dakatar da mom don kautar da ita daga bala'i alokaci d'aya kuma don mutaimaki Ummi da 'yan uwanmu daga cutuwa" hannu tasa tagoge hawayen idonta kafin tace

"Taya yayya Basmah?"

"Yawwa aikinsan jiya dasu papi sukazo ummi tace masu banida lpyne nayi fama da ciwon ciki ko? Kuma dady yasan da haka, don haka da zaran munga mom tatafi part d'in dady zanfad'i ak'asa nadinga murje murje ina kuka, ke kuma saiki ruga ki kirawota, haka zandinga kuka sosai har safe tayanda hankalinta dana dady zai tashi, kinga daga nan dole mom zata dawo takula dani tsorona d'aya kada bacci ya kawomun ziyara " rungumeta Batool tayi tana fad'in

"Wow..nice idear yayya, Allah kasa kada yaya mahmud ya kwafsa mana tunda baisan abunda ke faruwa ba, kinsan zai iya cewa zai kula dake ko kuma yakai ki asibiti"

"To amin in sha Allah hakan ma bazai faruba, idan kuma yace zai kaini asibitn to wlh rirrik'e mom zanyi in tayi mata kuka ina neman gafararta kinga kuwa bazata yardaba k'afarta k'afata za'aje asibitin" dariya sukayi tare da tafewa cikin farincikin samun mafita da sukayi......
















*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Gaisuwa ta musamma tare da fatan alkhairi agareki *UMMIE* dake group d'in rano online novel, inajin dad'in yanda kike bibiyar littafin 'YAN UWANA NE, thank you sister am really appreciate, another greatng from Ummi ur name sake to you, tace kici gaba da k'arfafa mata hakan zaisa tayi nasara, keda ita abu d'aya ne don haka zaku cinma buri kuma tanayinki over๐Ÿคญ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿคฃ_


๐Ÿ’ŽPage_____36๐Ÿ’Ž


Mom nagama waya tafad'a toilet tayo wanka, simple make up tayi ta saka wata doguwar riga marar nauyi lemon green ta yaga k'aton black vail asama shima dai d'in marar nauyi tayi kyau sosai, fitowa tayi don jiran tsammanin kira daga dady, jin motsin fitowarta yasa suma su Batool fitowa, fuskarsu d'auke da fara'a sukace "mom sannu da fitowa, ur favorite food is ready"

"Wow are u serious?"

"Yeh! Suka fad'a tare da yimata iso akan dining table"

Dady kuwa bayan su Bilkisu sun shige d'aki, kallon ummi yayi yace

"Rabba'atul bait yunwa nakeji, zansamu abani abinci inci?"

"Gaskiya bazaka samuba tunda ga amaryarka can tadawo kuma yara sun shirya maku abunda zakuci, don haka katashi kaje tanacan tana jiranka karka shiga hakk'kinta" shiru dady yayi cike da jin kunyar yanda zai mik'e yafita, sosa k'eyar kansa yai tare da shafo kansa yarasa mezai cemat, can yasamu wasu kalmomin da basuda tushe suka fito abakinsa "Rabba'atul bait yau abun hadda kora da kuma horon yunwa" dariya ummi tayi cikin d'an basarwa tace

"Ko kad'an babu maganar horo anan don natabbata 'yar uwata shirye take data baka tarbo na musamman tare da cika maka ciki yanda ya kamata, kaga kuwa maganar Aisha tayi maka horo kamanta da ita" shiru dady yai ya zubawa Ummi idanuwa yana kallo, shi baice k'anzil ba kuma bai tashi ba, ganin haka yasa Ummi zuwa wajensa ta kamo hannuwansa ta mik'ar dashi,

"Katafi mana dare nayi" zaiyi magana tayi saurin d'ora d'an yatsanta akan bakinsa.. "Shiiiiii...ya kamata kayi abunda ke daidai kajiko?" Tafad'a rik'e da fuskarsa sannan tayi masa kiss agefen kuncinsa, galala yayi yanajin wata irin qaunarta na fisgarsa, hannunsa yaji takamo tanufi hanyar fita dashi sai da suka kai bakin k'ofar sannan tasaki hannunsa tarik'e gambun k'ofar tana fad'in,

"Saida safe abu Bilal" bayada zab'in daya wuce illa rungumeta da yai "I luv u so much rabba'atul bait, kayi daddad'an bacci tare da kular mani da kanki"

"Yanda kace hakan za'ayi da yaddar Allah matuk'ar zaisa kayi farinciki" kiss yai mata a forehead ta lumshe idanuwa sannan tayi breaking hug d'in takoma daga ciki tarufo k'ofar zuciyarta cike da tsantsar soyayyar mijinta, yajima a wurin tsaye kafin yanufi part d'insa yana cewa "Allah yayi maki albarka yakare aduk wani motsi da zakiyi rabba'atul bait, there will be no me with out u Aa'ishhh." Ikon Allah da yawan maza kanyi sabbatu akan hanya saboda rashin da cewa da mata nak'warai, amma akaro nafarko danaga mijin dake tafe yana sabbatu saboda soyayya, kulawa tare da kirkin matarsa.

Yana shiga kai tsaye ya wuce bedroom d'insa ya cire kayan jikinsa sannan ya fad'a toilet ya watso ruwa, kasancewar har 12 takusa yi yasa ya zuba jallabiyarsa seagreen sannan ya feffeshe jikinsa da turare, wayarsa yajawo da niyar kiran mom sai kuma yaji sha'awar saukowa ya iskota part d'inta, tasowa yayi yana zuba k'amshi a hankali yake saukowa akan matattakalar zuwa babban falon dake k'asa sannan yafito had'e da rufo k'ofar, part d'in mom yanufa amma a zuciyarsa tunanin Ummi kenema yahanasa sukuni.

Mom da zaunawarta keda wuya ita da yaranta akan dining suna bud'a mata yummy d'in da suka had'a mata tace

"Wow...daji wannan food special ne can't wait to eat my fav delicious" tafad'a tana mik'a hannu zata d'auko plate, muryar dady da shigowarsa kenan taji yana fad'ar.

"Anya kuwa anyi missing dady da aka manta dashi har ana zancen cin abinci batare dashi ba?, Basmah kuna ganin momynku ko?" Dariya sukayi sannan suka kalli mom data tsayar da hannun cak ita bata d'auko plate d'in ba, ita bata ajiye hannun ba tana sauraren abunda yake cewa, ganin duk suna kallonta yasa tayi saurin ajiye hannun itama tana dariya ta bud'e hannuwan had'e da d'aga kafad'u tana kallon dady daya k'araso wajen shima ita yake kallo tace "what to say?", d'aya daga cikin kujeru suka jawo mada ya zauna ya juyo ya kalli Basmah dake tsaye a gefenshi nadama yace

"My dota, ya jikin?"

"Da sauk'i dady" tafad'a tana maijin dad'in wannan tambayar, juyowa yayi ga Batool data gama zuzzuba masa abincin a plate shida mom tana k'ok'arin rufe warmer d'in yace

"Thank you dota, ina yayanku da Bassam ne?"

Yana rufe baki sai gasu sun shigo ya mahmud har yaiwa Bassam wanka ya shiryasa cikin shirin kayan bacci, k'arasowa yai had'e da gaida Iyayen nasa cikin jin dad'in ganin su atare, kujerar dake gefen dady Bassam yahaye "Nima yayya azubomun nawa inci bacci nakeji" zuba masa Batool tayi sannan ta d'auki plate ta zuba wani aciki mai yawa sosai, kallon ya Mahmud tayi tace

"Ya Mahmud, kaje kaci abincin ko" sannan tayiwa Basmah nuni da sutafi, har sun kai tsakar falon rik'e da abincin data rufo da wani plate asama kamar dady da mom sun had'a baki sukaji sunce,

"Ina zakuje kuma?" cak suka tsaya lokacin ya Mahmud nak'ok'arin zaunawa bisa kujerar dake kusa da dad yana facing d'in Bassam yayinda ta mom ke facing d'in ta dad,

"Wajen 'YAN UWANMU" suka fad'a babu alamun tsoro a fuskarsu" mom najin haka nan take ta k'ware da abincin dake neman wucewa abakinta, da sauri dad ya bulbulo ruwan dake ajiye a gorar faro gefensa a cup ya mik'a mata yana fad'in "sorry" kallon juna su Basmah sukayi yayin da Mahmud yace dasu

"Dan Allah kuwuce" don kar mom tasamu damar hanasu shi kuma dady dama cin abincinsa yaci gaba dayi don har ga Allah maganar tayi masa dad'i shiyasa baibi takanta ba, b'ata rai mom tayi amma da tatuna shirinta sai tace

"No ai da kunje kunce suzo nan sai kuci ko gaba d'ayanku, ai laifin kune da run farko kuka k'i kirawosu anan kuci abincin?" 'Dagowa dady yayi da mamaki, lallai mom ta canza dakanta take cewa akirawo su Bilqees suzo nan suci abinci, koda mom taji shiru saita juyo dama taba falon baya saidai ganin falon wayam tayi ashe sun dad'e da tafiyarsu tun lokacin da ya Mahmud yace su wuce. Dole yasa ta hak'ura badon ranta yasoba, Mahmud nagama cin abincinsa yayi masu sai da safe shi kuma Bassam tuni har bacci ya d'aukesa ko gama cin abincin beyi ba, d'aukar sa mom tayi takai d'akinsu ta kwantar dashi batare da ko addu'a ta tsaya tayi masa ba don gaba d'aya hankalinta na akan dady, sosai take jin maganin yafara aiki ajikinta don jitake kamar ana mitsilarta acan k'asanta, tana fitowa tawani fara fari da idanuwa tana jujjuya jiki, nan take dady shauk'i yad'ibesa, hannu ya mik'a mata alamar ta iso garesa a hankali tafara takowa tana wata kwarkwasa da tasa tatafi da hankalin dady gaba d'aya, mazauni yayi mata akan cinyarsa yana faman shinshinar jikinta saboda k'amshin turaren dake tashi,

Batool kuwa suna shiga sun samu har Billy tafara bacci mom kuwa tana d'akinta tana tilawar Qur'ani, haka yasa basu katseta ba. Dukan da bazai cutar da Billy ba Batool takai mata acinya, da sauri Billy ta tashi tana murzar idanuwanta, wata irin harara Batool ta balla mata tana fad'in

"Lallai twiny bakida kirki, daga kizo kisakawa Bilal wando

Please Login or Register in order to submit comment