Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine kikayi zamanki batare da kunje munyi takin dinner ba" langab'e kanta tayi ta d'ora akan kafad'ar yayya Basmah dake zaune gefenta cikin muryar baccin da bai ida sakintaba tace


"Kinganta ko yayya Basmah?" tana turo d'an k'aramin bakinta, shafo gefen fuskarta dake saman kafad'arta tayi da hannu sannan tace "k'yaleta sweety je kiwanko bakinki muci abinci kinji ko, ina Bilal ne?"

"Yana wajen ummi k'ilan yayi bacci" tafad'a tare da mik'ewa tashiga toilet cikin sigar tsokana Batool nakira mata baby jepanise, murmushi tayi batare data tankata ba,

Anatse sukecin abincin har suka kammala, sabuwar firar rayuwarsu tabaya suka d'auko sunata dariya, mafi yawancin firar tsakanin Batool da Billy akeyinta Basmah nacan gefe abunta. Yaya Mahmud ne yashigo part d'in jin yanda suke k'yak'yata dariya, "kai sisters wannan irin dariya haka dare fa yayi" nan Ummi tashigo tace

"Kabarsu babana tund'azu nake son yimasu magana hankalina ne yad'auku, kuduba agogo kugani quarter to 1:00am fa amma kunata faman d'aga murya" jin haka yasa Batool da Basmah mik'ewa suna kallon Ummi.

"Ummi sai da safe" sosai Ummi taji ba dad'i ganin ba'anan zasu kwanaba amma yazatayi tunda suma suna buk'atar mahaifiyarsu akusa dasu, d'an murmushi tayi tare da fad'in

"Allah yatashemu lpy, kutabbatar kinyi arwala da addu'a kafin ku kwanta" "to ummi" sukace had'e da hugging nata sannan suka fita.

Tun abu na wasa wasa tsakanin mom da dady har yazama gaske domin kuwa mom takashe masa jiki da duk wani salon d'aukar hankali da jan ra'ayi, ganin abun na neman wuce wuri gashi basusan lokacin da yaran nasu zasu iya dawowa su riskarsu ba aciki yasa dady yayi k'ok'arin daidaita natsuwarsa, ahankali yake rad'awa mom magana akunne.

"We should stop all this Momyn yara kada su iskomu, bari naje na watsa ruwa, ina jiranki" sakinta yayi tare da nufar part d'insa cikin wata iriyar kasala, mom kuwa gaba d'aya labari yafara canza mata don jitake kamar ana mintsilarta tare da fizgarta ak'asanta, sosai take jin buk'atar mijinta atare da ita, d'aki tashige jikinta narawa ta d'auki abubuwan da take buk'ata sannan tanufi part d'in dady batare da tajira dawowar yaranta ba.

Su Basmah nafitowa part d'in ummi sukaga shigar mom part d'in dady.

Da sauri suka k'arasa part d'insu, Batool tace

"Yayya yazamuyi, intafi yanzu" cikin miskilanci tace

"A'a Batool wlh ganomu mom zatayi kawai mubada minti biyar, amma duk sai nakejin badad'i hakan da zamuyi wlh ina son mom, it been long time fa bata cikin gidan nan"

"Ohhh my God yayya kimanta da wannan, muyi abunda ya kamata, wlh yayya idan mom ta kwana part d'in dady akwai matsala, zata cutu, ummi ma zata cutu, mafi munin abu sa 'yan uwanmu zasu cutu, kitunafa 'YAN UWANMU NE, Idan bazaki iyaba to nidai 'YAN UWANA NE, yazama dole inkula da duk abun da zai cutar dasu, kinga tafiyata u should know what to do idan sukazo, bata jira amsar da Basmah zata bataba tafice d'akin aguje.

Mom da tuni jikinta yafara tsuma jira kad'ai takeyi taji tabbacin cikar burinta sai kawai suka jiyo an banko k'ofar falon k'asa da k'arfi,

"Wayyo dady mom kufito yayya Basmah zata mutu, dadyyy..." Gaba d'ayansu tashi sukayi cikin firgicewa tare da gyara jikinsu, bil-hakk'i Batool tak'ak'aro kukan k'arya tanaci gaba da takowa bisa matattakalan sama da zasu sadata da d'akin dady dake can sama, cikin kukan taci gaba da cewa

"Dady don Allah kuzo kada in rasa 'yar uwata...yayya Basmah zata iya mutuwa gatacen tana bille bille"

Tana kawowa step d'in k'arshe taci karo dasu sun fito, cikin rashin kuzari dady yace "meke faruwa da itane Batool?"

"Bansani ba dady nima dai naji tana fad'in cikinta, dady muje ataimaketa wlh bana so narasa 'yar uwata"

"Subhanallahi ko ciwon jiyane yadawo mata" tsaye Batool tayi tanaci gaba da matsar hawaye alokaci guda kuma tana kallon mom dake safa da marwa saboda yanayin da take jin kanta aciki, juyowa tayi tare da cewa Batool "kije wurinta gamunan zuwa yanzu" aikuwa tafashe da kuka tana haba mom ni mezan iya yimata plz tanajin jiki sosai fa, kasawa tayi ta tsare har saida ta tasa dady agaba batare data jira ganin ko mom zata biyosu ba.

Suna fita mom ta'aza hannu akai, nashiga uku ni husaina ya zanyi da wannan alamari, Batool da kinsan bala'in da nake ciki da baki katseman hanzari ba , k'afafuwa tashiga matsa kafin itama tabiyo bayansu, ganin yanda bala'in yayi mata yawa yasa tadinga rarrafowa akan step d'in har tasamu tasauko "wayyoni Hussaina meke shirin faruwa da nine?" tafad'a tare da nufar part d'inta cikin wani hali mai wuyar fassarawa.

Koda dady ya shigo ya tarar da Basmah kwance k'asa tsakar falo tana kuka, tana ganinsa tarirrik'e shi "dady kataimakeni cikina" rungumeta yayi yana fad'in

"Sannu Basmah bari muje asibiti" wata irin k'ara tasaki da tasa mom dake k'ok'arin shigowa firgicewa da gudu mom tak'arasa wajen

"Basmah, Basmah.. Me kikaje kikacine, wayyoni Allah naboni, Allah ya isarmun? Amaimakon tayi ta Basmah dake cikin wani hali sai faman nanik'ar jikin dady takeyi ko zataji suk'in abunda takeji, ganin babu wani sauk'i yasa tatashi tana zagayar falo tana buga ciyoyinta sai kuma ta mammak'e jiki kamar irin tanajin fitsarin nan sosai surutai ta dingayi wud'an da azahiri kamar don yanayin da 'yarta take ciki yasata yin hakan amma abad'ini da kanta take akan yanayin da take ciki,

"Shikenan tawa tak'are, Allah kawomun d'auki kafin narasa raina, yanzu me zanyi, menene mafita, wash, wayyo Allah na yi hoho"

"Hussaina meye haka, kidena wud'annan maganganun mana meye fa'idarsu" fashewa da kuka mom tayi tare dafad'uwa zaune dab'al tace

"Alhaji kabarni in fad'a, idan kuma bakaso infad'ane kazo muje ciki mana, wlh zan iya mutuwa" cike da mamaki da rashin fahimtar maganganun ta dady yace

"Anya kanki d'aya"

"Wlh Allah indai zanci gaba da ganin wannan yanayin ahaka kaina zai koma uku bama d'aya ba" mom tafad'a tana cije baki tare da share hawaye kamar k'aramar yarinya, itadai Basmah da Batool nagefe suna kallon alajabi ga mom d'insu da hankalin dady yadawo kansu sai suci gaba da kukan ita kuma Basmah na juye juye tana wayyo cikina, tashi mom tayi tajawo Basmah ajikinta tana cewa "Basmaty kiyiwa Allah kitashi, narok'eki kiwarke da wannan ciwo, ganinki da nakeyi ahaka na daidai da bugawar zuciyata don nima zan iya mutuwa, ganin Basmah nak'ara birgima yasa mom cigaba da bubbuga fuskarta, Basmah kijure ai ciwon ciki shahada yake sawa kinji ko 'yata tashi mana.


Ganin azaba da masifar wannan magani sunyi mata yawa yasa tayanke shawarar yin aljanun k'arya ko itama tarage zafi.

Wata irin k'ara mom tasaki tare da sakin Basmah gefe kan dady tayo dake k'ok'arin rik'eta suka fad'i k'asa aikuwa mom tasamu yanda takeso ta k'ank'amesa sunata birkid'a tsakar d'aki da sunan itama batada lafiya sai gumza takeyi, gaba d'aya burinta yanzu bai wuce tadena jin abunda takeji ajikinta ba, da zaran dady ya yunk'ura yatashi sai mom tajawosa sufad'i tare ganin haka yasa Billy ta rik'o Basmah tana kukan k'arya, " yayya Basmah sannu don Allah kitashi kinga har kinsa mom itama cikin wani hali"

Saida dady yayi da gaske yasamu ya kucce hannun mom ai kuwa da gudu yabar falon yacire makullin k'ofar yarufo d'akin tare da sa makulli tanan waje ya rufesu.

Da sauri Batool taja Basmah suka shige cikin d'aki suna dariyar mulmular da dady sukayi afalo, Batool takalli Basmah tace

"Yayya dama mom nada aljanune?" Bansani ba kije kitambayeta.

Dady kuwa da duk jikinsa keyi masa ciwo yanufi d'akin ya Mahmud, karo yayi dashi yasanyo riga birkice cikin tashin hankali yace

"Yawwa my son, ungo makullin nan kaje part d'in mom d'inka Basmah batada lafiya sanadiyar haka itama mom d'inka inaga aljanu sunshigeta sune suka tasar mata, amma sunada matuk'ar had'ari don masu kayarwane da mulmula, kabi ahankali kuma kafara saka karatu awayarka kafin kashiga, maza kaje ganinan dawowa zand'auko habbatussaudane da nake amfani da ita sai asamata...














*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____37πŸ’Ž


Kamar ya 'yar uwa tafad'a tana kai kallonta ga k'afar tata, duk'awa tayi arud'e had'e da tallafo k'afar, "Ayya Allah ya sawak'e banzata ciwon zaiyi haka ba, sorry, bari narik'aki kisamu kiyo arwala lokacin sallah na wucewa, sak'alo hannunta tayi awuyanta tana takawa ahankali, cikin k'arfin hali take taka k'afar tana hawaye har suka isa toilet d'in, da taimakon Basmah tayo arwalar sannan suka fito, sallarma azaune tayita saboda zugin da k'afar keyi mata. Tun tana daurewa har tafara kuka da gaske da gaske,

Ummi kuwa tana gama sallah ita da Billy suka nufi part d'in mom cike da fargabar yanayin da zasu isko, sallamar suce tsaida Basmah daga rarrashin da takeyiwa Batool dake faman kuka sharkat, da sauri ta tashi tanufi bakin k'ofar palourn da suke faman doka sallama, bud'ewa tayi tare da fad'in "Ummi kece a safiyar nan, ina kwana?" Murmushi tayi tare da jawota ajikinta "aidole ne tasa, tunjiya nadamu da sanin wane hali kike ciki, but alhmdllh naga kinji sauki" shiru tayi batare da tace komai ba wannan ne yaba Ummi damar jiyo kukan da Batool keyi, cikin rashin fahimta tare da neman k'arin bayani don tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyo mata tace

"Basmah kukan wa nakeji kaman na Batool?"

"Eh Ummi itane"

"Aww.dama itace ba lafiya naji kamar dadynku yace momyn kuce ba tada lafiya?"

"Eh itama mom batajin dad'i, daga bayani itama Batool taji ciwo ak'afa"

"Subhanallahi agarin yaya?" Ganin zancen na nema yayi tsayi yasa Basmah cewa

"Ummi kishigo daga ciki mana, sister shigo ko?" Tak'arasa fad'a tare rik'o hannun Billy, ko kad'an Ummi bataso shiga d'akin ba saboda sanin halin mom amma donkar Basmah taji ba dad'i kuma kamar tanuna less care yasa ta tsarkake zuciyarta ta shiga, mom kuwa adai dai lokacin da Ummi ke fad'in ta zata dady momce yake fad'in batada lafiya tafito daga toilet, maganar kad'ai ce tadaki kunnenta aikuwa taji kamar tafasa ihu, wato dady zuwa yayi yana tallarta awajen Ummi yana fad'a mata duk halin da take ciki, lallai dady yayi kuskure daya aikata hakan, tana wannan tunanin ne Basmah tashigo d'akin, gaisheta tayi tare da yimata ya jiki sannan tafad'a mata cewa Ummi na a palour tazo ganinta, amsawa mom tayi tare da tambayarta itama ya nata jikin?

"Alhmdllh mom naji sauk'i Batool dai ce kefaman kuka k'afarta ta e, da sauri mom ta tashi daga ita sai towel d'aure ajikinta wanda iyakarsa giuwarta tanufi d'akin su Batool, a palour taci karo da ita zaune ak'asa ta d'ora kanta ajikin Ummi dake zaune akan kujera har lokacin tana kuka, burki mom taja kafin ta maida kallonta ga k'afar Batool data kumbure sannan ta kalli Ummi dake shafa kanta ahankali, cikin takaici tayi saurin komawa d'aki ta sanyo doguwar riga tadawo falon, ita dai Basmah biye take da mom tana kallon ikon Allah, shin wai koda gaskene aljanu sunfara shafar mom d'insu? Batasha mamaki ba saida ta hango mom tana sakarwa Ummi wani shu'umin murmushi kamar ba itaba, cikin natsuwa suka shiga gaisawa da Ummi dake yimata yajiki tare da jajanta abunda yafaru da Batool d'in, hakama Billy itama gaisheta tayi tayimata yajiki sannan tajuya tana rarrashin twiny d'inta dake kuka.

Azahiri babu wani abun da mom ta nunawa ummi na Allah ya waddai amma abad'ini wani takaicine da bak'in cikin ganin fuskar Ummi kwance acikin k'asan zuciyarta kecinta. Ba kad'an Ummi tayi farincikin ganin canji daga wajen mom ba wanda har saida fuskarta ta bayyana hakan,

Allah yak'ara sauk'i Ummi tayi masu sannan tafice zuwa part d'inta, wani irin mugun kallon tsana tabita dashi wanda Billy kad'aice ta lura da hakan koshi don tajuyone tana yiwa Batool Allah yabida lpy, girgiza kai tayi bayan sufita aranta tace

"Mom kin zama zulwajahaini, meyasa koda yaushe take sakawa mutum yarda da ita agabansa amma tabisa da k'ulli tana cutar dashi abayan idonsa...hmmm ya Allah kashiryar da mom tagano gaskiya" tak'arasa zancen zucin daidai lokacin data turo k'ofar d'akin yaya Mahmud. Kwance yake shi dasu Bilal akan gado suna bacci dama tunda suka dawo sallah da asuba dady ya wuce part d'insa sukuma sukabi yaya Mahmud d'akinsa. Tilawar azkar sukayi kafin rana tafito sannan suka koma suka kwanta do kowanensu akwai bacci kwance a idonsa. Knocking ta shigayi da d'an k'arfin kafin tace

"Wakeup yaya" tafad'a da k'arfi cikin yanayin damuwa,

"Pls katashi mana, wlh k'afar my twiny ta kumbure sosai sai kuka takeyi"













*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_ina mai baku hak'uri bisa rashin samun update d'ina jiya hakan yafarune bisa rashin lpy data d'an bijiro mani, haka kuma idan zaku lura mun samu doublecating na page 37 don haka kar wannan ya rud'aku yanzu zamuci gaba daga page 38 yazamana kenan munsamu page biyu masu numbering iri d'aya, hop kun fahimta?, thanks all_🀝🏻


πŸ’ŽPage_____38πŸ’Ž


Tashi yayi had'e da dafe kansa yana kallon Bassam da Bilal dake gefensa sannan ya maida kallonsa gareta, "shikenan kije ganin zuwa kinji ko?" k'in yarda tayi tatafi saboda yanda taga yana k'ok'arin komawa ya kwanta da alama dai baccin bai ishesaba "pls Broth don Allah katashi muje, sosai fa take kuka" adole tasa yatashi yafad'a toilet, ganin haka yasa takoma part d'in mom wajen 'yar uwarta, tana shiga tasamu mom na zaune akusa da Batool d'in tana faman rarrashinta, hakan yasa Billy takasa k'arasawa wajen ta tsayawarta daga bakin k'ofa tana yiwa 'yar uwarta sannu, wata irin harara mom ke jefota da ita wacce tasata saurin noce kai k'asa ba tare da tasani ba. Basmah kuwa dake kitchen tana k'ok'arin had'a breakfast don yanzu ba laifi tad'an iya k'ananun girki da basuda wahala kamar ance tafito tahango Billy ajikin k'ofa tsaye, kallon mom tayi kafin tanufi wajenta tana fad'in "laahh...sister ashe baki wuce ba, mekikeyi anan shigo daga ciki mana" tak'arasa maganar had'e da rik'o hannunta, jawota tayi amma taga tak'i shigowa sai ma kallon mom da takeyi, ganin haka yasa tajawota da d'an k'arfi tana cewa

"Wai meye haka sister, kishigo mana, kina nufin mom d'ai zata zauna zaman jinyar twiny d'inki ba dake ba?"

"A'a yayya Basmah ai nakira ya Mahmud yazo sai akaita asibiti, bari inje Ummi kejirana" sallamar da yaya Mahmud yayi ce taba Basmah k'warin guiwar ida shigowa palourn rik'e da hannunta, cikin girmamawa suka gaishesa shima ya gaida mom had'e da yimata yajiki.kai dubansa yayi ga k'afar Batool data kumbure lokaci d'aya kuma yana kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tayi, sosai tabashi tausayi alokaci daya kuma sai ya tsinci kansa da jin haushin kansa na zamowa silar faruwar haka agareta, da ace bai kirata ba da duk haka bata faruba, kitchen Basmah tashiga ta kawo masu breakfast d'in data had'a, ruwan tea ne masu kabri sunsha kayan k'amshi sai biredi da soyayyen k'wai. Bata wahalda kantaba da d'orasu bisan dining table ba, anan falo inda suke zaune ta shimfid'a darduma mai d'an girma sannan ta d'ora kayan akai, Mik'ewa Billy da tund'azu take tsarge da kallon da mom ke watsa mata tayi zata fita, saurin dakatar da ita yaya Mahmud yayi lokacin da take k'ok'arin bi tagabansa, hannnunta ya rik'o yana fad'in "my sis ina kuma zakije bayan ga breakfast ankawo?"

"Am.ehm..dama ina son tashi tund'azu, Ummi ke jirana muhad'a breakfast"

"Koma kizauna tariga taga abunta, kafin in shigo saida na biya, acanma su Bassam nabarosu suna karyawa" ji mom tayi kamar tawatsa ihu, wai yanzu ita shikenan duk wani tsari nata data shirya ya watse, wannan bala'i da meyayi kama, ada tana tunanin mahmud kad'ai Ummi ta rabata dashi amma yanzu talura gaba d'aya 'ya'yan nata so take tarabata dasu, ace d'anta data haifa da cikinta in safiya tawaye sai yafara zuwa yadubo Aisha ya gaisheta kafin yazo itama ya gaisheta, duk da yasan cewa takwana cikin rashin lpy, wlh haka bazata sab'uba bindiga aruwa dolene tasakar mata mara tayi fitsari, ganin har lokacin yana rik'e da hannunta tayi tsaye batare data juyoba yasa mom ta ida hasala, a d'an tsawace tace

"My son cikamata hannu ta tafi tunda ni ba uwarta bace, tsoro takeji taci abinci anan kada azuba mata abunda zai kasheta ko, wato tana tunanin bak'in asirce asircen da uwarta keyi dabin bokaye shi nakeyi, ka cikata nace kosai naci mutuncinka, kada Allah yasa taci ita tasani. A take Billy tafashe da kuka ta k'wace hannunta daga rik'on da yayi mata tabar part d'in aguje zuciyarta na k'una, rai ab'ace Mahmud ya juyo yana kallon mom, har zaiyi magana sai kuma yafasa saboda tunanin rashin lpyr datake ciki amma ya qudurta aransa koyaushene sai yanunawa mom wannan kuskuren datayi, dubon Basmah da Batool dayaga suma fuskokinsu sun canza akan abunda mom tayi yayi sannan yace

"Batool kufito muje inkaiki asibiti, ina jiran ku awaje!" daga haka bai k'ara cewa komai ba yabar paloun ransa ab'ace batare da ya karya ba. Haka itama Basmah tarik'a 'yar uwarta suka koma d'akinsu suka shiryo, suna fitowa mom takallesu "Aw..kuma fitar zakuyi baku karya ba"

"Idan mundawo zamuci, bana son k'afar nan taci gaba da kumbure mata" Basmah tafad'a tana cigaba da tafiya rik'e da Batool dake tafiya dakyar ko k'afar bata iya takawa" mere baki mom tayi kafin tace

"Mtsss...aikin banza ku kuka sani, kada Allah ma yasa kuci masu bak'ar zuciya, ai tunda natab'a waccan manyar dole kud'au fushi dani, wawayen yara kawai, kuje kawai ko bakwaso dai nice nan uwarku"

Suna jin kalamanta amma babu wacce tayi yunk'urin tsayawa balle suyi abunda take so.

Daidai k'ofar fita sukaci karo da dady zai shigowa, gaisawa sukayi yana yimasu sannu dayake yaya Mahmud yafad'a masa zancen zuwa asibitin, yayi masu adawo lpy sannan yawuce daga ciki sukuma suka fito suna d'an waige waigen inda zasu hango yaya Mahmud d'in.

Lokacin da yafito shi kuma part d'in Ummi ya nufa saboda ya rarrashi 'yar uwarsa amma sai ya tarar bata can dady kad'ai ya isko suna gaisawa da ummi sai su Bassam dake game d'innan da ake had'a mota ko gida ko shape d'in wani abu da wasu pieces d'in abubuwa, duk inda yake tsammanin ganinta acikin gidan yaduba amma bai ganeta ba, tsaye yayi had'e da rufe bakinsa da hannu yana shafowa har zuwa hab'arsa, gaba d'aya yarasa dalilin da yasa mom d'insa keyiwa 'yar uwarsa haka, tunowa yayi da wurin da take yawan zama idan irin haka yafaru da ita, da d'an sauri sauri yanufi part d'in dady ya bud'e k'ofar saman upstairs d'in ya hangota kamar yanda yayi tsamnani ta kifa kanta saman cinyoyinta tana kuka. Ahankali ya k'arasa wajen ya nemi wuri akusa da ita ya zauna, saida yaji kukan yad'an tsagaita sannan yafara magana cikin muryar dake nuna lallashi da tausayinta "kiyi hak'uri! Tabbas nasan mom d'ina bata kyautatawa, amma inaso kisani kowane mutum da halinsa ake zama, sannan wannan abun da takeyi nasani wani gurb'ataccen tunani kesakata yin hakan, wlh nikaina natsani wasu abubuwan da takeyi, shin kiyi tunani dani dakeda mom dake dake da Ummi wayafi kamata yayi kuka?, ina so kifahimci cewa bake kad'ai hakan kefaruwa akankiba akwai dubbanninki dake da irin matsalarki wasun suma tafi taki, amma sukayi hak'uri sai abun yazama tarihi, kisani duk abun d'a yanaso yaga mahaifiyarsa cikin salihan bayi domin shine zai sakashi alfahari, idan kuma yaga mahaifiyarsa a akasin haka dolene yazamo maitakaici da b'acin rai, ina son mom kullum fatana Allah ya sauya mata wannan mummunan tunani izuwa kyakkyawa, to amatsayin ki na 'yar uwata kema haka yakamata kiyi bawai kinuna damuwarki akan kalamanta ba, tunda kinsan bahaka bane,

Kafad'unta ya dafa sannan yace

"Don Allah kiyi hak'uri kiyafewa mom d'ina ko don karamci da Allah yayi maki na samun nagartacciyar mahaifiya kamar Ummi" sosai kalamansa suka saka jikinta yayi sanyi, sai taji tabbas haka maganarsa take shiya kamata yayi kuka da jarabawar da Allah yayi masa na samun uwa mai tsananin zargi, zato, munana kyawawan abubuwa izuwa qazafi irin mom ba ita ba, nan da nan tausayinsa da kuma kanta na muzgunawar da take fuskanta daga wajen mahaifiyarsa ya kamata, d'ago kanta tayi suka had'a idanuwa ta sakar masa murmushin da yasa 'yan k'ananan idanuwanta k'ara shigewa saboda kukan da tayi tace

"Shikenan yaya babu komai na hak'ura" rungumeta yayi yana mayar mata da murmushin tare da cewa

"Thank you my sis, jazakillahu bikhair" yak'arasa fad'a yana d'an matse mata kumatu, sannan yace taje ta karya wajen ummi sai tazo sukai Batool asibiti, tare suka fito suna tafiya zuwa hanyar da zata rabu izuwa part d'in Ummi shi kuma ya wuce parking space ya fiddo da mota, hango su Basmah sukayi suma sun nufi wajen parking space d'in ya juyo yana kallonta

"Oyah maza kifito kije kiyi breakfast d'in sai mutafi"

"Nooo.bari kawai nashiryo idan mundawo nakarya" tafad'a had'e da d'an rugawa da gudu zuwa part d'insu.

K'arasawa shikuma yayi inda suke ya bud'e masu motar suka shiga sannan shima ya shiga ya tayar da motar, saida yaba motar wuta na tsawon mintuna biyar sannan yayo reverse da ita ya tsaya, dai dai nan Billy ta iso tsaye tayi agaban motar batare data shi gaba, zuge glass d'in yayi ahankali yana kallonta,

"Billy Japanese ya akayine?, kizagayo mana kishigo" yafad'a yana dariya don yasan duk duniya ba abunda ta tsana kamar shiga gaban mota, ji take kamar idon kowa na akanta.

"A'a yaya ni gaskiya bana son gaba sai dai in squatting zamuyi abaya" tafad'a tana k'ok'arin bud'e gefen da Batool ke zaune, yana kallo har tabud'e ta zauna, Batool da Basmah suka sakar mata murmushi had'e da cewa "sisto we are sorry for what happened"

"Kai auntys nothing much fa" had'e da maido hankalinta garesa, "yaya muje ko?" "Ina!?, tab ai wlh bako Mahmud ba, sai kace wani drivern ku" kashe motar yayi gaba d'aya sannan yakoma jikin seat d'insa ya lumshe idanuwansa, turo baki Batool tayi had'e da cewa

"Allah duk don bakusan me nakejiba da baku tsaya wannan kace nace d'in ba, waike twiny meye laifin ma gaban mota da bakyason zamansa?"

"Tsoro kawai nakeji don bana son yawan kallo" tabata amsa atak'aice "mtsss...shikenan idan k'afar ta rub'e aka cire ai sai kuji dad'i" tafashe da kuka, duk abunda suke cewa yana jinsu murmushi kawai yakeyi abunsa don tabbas in d'ayansu bata dawo gaba ba, ba inda zaije dasu, sanin halinsa yasa Basmah tabud'e takoma agaban motar tana dariyar kukan da Batool kefamanyi, ada dai bata santa da shagwab'a ba amma d'an zaman nan da sukayi awajen Ummi duk takoya saboda kulawar da Ummi kebasu. Tayar da motar yayi suka fice maigadi na zuba masu kirari,

_Kaga babban yaya d'an gaban goshin alhaji, shalelen uwar d'akina, gaba salamun baya salamun 'yan ukun Ummi atafi lafiya adawo lafiya, gabanku alkhairi bayan ku alkhairi Allah dai yafidda mugu da duk wani mai mugun nufi acikinku_ maganar yak'arasa yana lowering voice d'insa gudun kada ya tonowa kansa bakin galma, abincinsa kuwa yak'are agidan, shigewa d'akinsa yayi yana cigaba da cewa "ato, aishi alkhairi dank'one kowa yayisa dole tafad'a don ko yaushene sai ya bayyana, amma nikam dole in iya bakina, ya na'iya da abunda yafi k'arfin wuta..."

Tunda taji muryarsa gabanta yafad'i abubuwan da suka faru jiya suka dinga dawo mata akai shikenan tasani yanzu kimarta da class d'inta da take tunk'aho dasu agabansa sun zube, abunda kuwa bata sani ba shine, gaba d'aya wannan tunanin baizo akan dady ba, shi kawai abunda ya d'auka aljanune suka shafeta, k'arasowa yayi tare da zaunawa kusa da ita

"Sannu Momyn yara ya jikin naki?"

"Alhamdulillah naji sauk'i" tafad'a kanta na ak'asa, duk'owa yayi yana kallonta sannan yace

"Kintabbata?" "Sosai kuwa" tabashi amsa had'e da yin murmushi, breakfast d'in dake gabanta ya shiga bubbud'ewa kafin yafara had'a tea d'in a cup yafara sha, kurb'awa yayi kad'an sannan ya maido kallonsa gareta "hope kinyi taking break d'in kema" girgiza masa kai tayi batare da tace komai ba, shi saima abun yabashi dariya wai yau mom ce dajin kunyarsa haka, anya kuwa ba wani salonne aljanun suka b'ullo mata dashi ba!. Cup d'in ya ajiye gefe ya sake d'aukan wani ya had'a tea mai kabri ya mik'a mata tare da zuba mata soyayyen k'wan ya ajiye agabanta sannan ya d'auki nashi tea d'in yaci gaba da sha, ahankali yata kanta da fira har tagano bai

Please Login or Register in order to submit comment