Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin daren akasa na zamani sannan aka hau sanya tiles, saida dady ya tabbatar ya ajiye komai da masu aikin zasu buk'ata kafin safe lokacin har karfe d'aya na dare ya wuce sannan yayi sallama da 'yan uwansa da sai faman godiya da sanya masa albarka sukeyi har sun rik'osa mota zai tafi sai yakalli alhaji kabiru yace "yaya ko zaka bani 'ya'yanah Zainab da Amina k'anwarta suje sutaya 'yan uwansu shire shire tunda dama Basmah abun yayi mata yawa gashi batada cikakkiyar"

"Why not d'an uwa? Bukar shiga ka kirawosu, Allah dai yasa basuyi bacciba" alhaji kabiru yafad'a yana kallon d'an uwan nasa,

Aikuwa yana shiga ya tadda Zainab zaune tasa iyayen nata agaba tana basu labarin yanda bukin ya k'ayatar da kuma diramar da sukayi da Batool akan tace taje ta tsare mata meamah kada tafita sai gashi tayi mata k'asa ko sama tana tayi mata mota da jinini akan haka sunata dariya, kallonta yayi had'e da cewa

"To suda baki abun magana, kitaso baffanki zai wuce daku can gidansa saboda kutaya 'yan uwanku shire shire, ki tado da Amina tare zakuje" turo baki Zainab tayi had'e da mik'ewa tana bubbuga k'afa "Baba gaskiya bazanje da itaba, bafa sa'anmu bace kawai muje tayita yimana rashin kunya"

"Ikon Allah to yanzu ya kike so ayi tunda baffanku yace kuje ku biyu?"

"Nidai baba tunda tayi bacci ak'yaleta don Allah ai gobe zandawo" har zai koma cewa wani abu matar alhaji kabiru wacce yake kira da yaya tace

"Haba alhaji, inzai yuyu ak'yaleta ita tunda bacci takeyi kuma kariga da kasan indai aka cemaka Zainab da Amina ne basa jituwa waje d'aya tamkar annabi da kafito suke, kasan mabiyi da mabiyi yanda suke kullum cikin fad'a" kasancewar akwai girmamawa tsakaninsa da ita kawai sai dai ya girgiza kai yana kallon mahaifiyarsu dake zaune gefenta batare da tace komai ba yace "Allah ya shirya yaya ai duk laifin wannan ne data saka masu idanuwa, jeki kisanyo hijab d'inki yana jiranki dare na k'arayi" yana gama fad'ar haka yawuce fuskarsa d'auke da d'an b'acin rai, bayan kamar minti biyar sai gata tafito saye da hijab d'inta ta sagalo jikkarta data jefa kayanta kala d'aya da 'yan kayan kwalliyarta da brush d'inta aciki. Saida safe sukayi sannan dady yatada motarsa suka bar anguwar.

Part d'in Ummi yanufa da ita saboda ranar ita keda girki kuma koba don hakaba itace uwar gida shiyasa yakaita can, lokacin Basmah da Batool suma duk sunacan part d'in wajen Billy suna ciccire kayan da zasuje dinner dasu, sosai sunji dad'in ganinta inbanda Batool data galla mata harara tana fad'in

"Wlh d'azun kin bani haushi sosai sister, wai keda nace kitsaremun yarinyar nan kika barta tab'ace maki saidai na hango maki mace na faman lek'amun fuskar miji tana nunosa da yatsa ita da wata, da alama ma, wani mugun target take son had'a mun don ranar na tata mata tsiya akansa ga waya"

"Kai Batool! Yanzu wannan jininin bazai k'are haka ba?, wlh Indai magaji kawai kiyi hak'uri wannan d'an banzan kishin naki haka har ina" Zainab tafad'a had'e da collar da jikkar hannunta baisan gado, dariya sukasa gaba d'ayansu har Batool "yo ina zan yarda, Allah kike d'innan bazan yarda dake ba indai akan dr. nane" dariya suka sake sakawa tare daci gaba da firarsu ta 'yan uwa,

Jin yanda surutunsu yafara son ya dameta yasa Basmah mik'e had'e da yimasu sai da safe ta shige d'akin Ummi abunta tayi kwance, ga zahiri bacci takeyi amma abad'ini idanuwanta biyu tana sauraren firar da sukeyi sama sama har itama Batool tayi bacci tadena jin muryarta saita Billy da Zainab, tana jinsu lokacin da Zainab kefad'awa Billy yanda basu ga maciji da 'yar uwarta Amina basa shan innuwa d'aya Billy tace mata

"Tab..gaskiya kinyi kuskure Zainab ai kamata yayi kijawota ajiki ya zamana itace babbar k'awarki kuma abokiyar sirrinki da zaku iya warwarewa kanku duk wasu k'ananonin matsaloli kafin suje kunnen Iyayen ku, Zainab su 'yan uwa fa da kike gani rahamane, matuk'ar zakuso junanku son gaskiya na tsakani da Allah to wlh babu abunda ke iya shiga tsakaninku balle ya rabaku, bari in fad'a maki wani abu kiji wlh soyayyar da nake yiwa 'yan uwana zan iya sadaukar da komai nawa aduniya akansu hatta rayuwata zan iya bayarwa a matsayin fansa agaresu matuk'ar zaauyi farinciki, idan kika cire iyaye aduniya babu wasu dake biyowa abayansu wajen cancanta ga soyayya da kuma kyautatawa kamar 'yan uwa, don haka kidena kyarar 'yar uwarki hakan zai iya cusa tsana atsakaninku, kimanta da zancen da mutane keyi wai mabiyi da mabiyi basa zaman lafiya, kawai kiso 'yar uwarki zakiganki cikin farinciki marar misaltuwa domin ni shedace akan haka" nan take jikin zainab yayi sanyi ta jinjina soyayyar dake tsakanin Billy da 'yan uwanta duk da kasancewar ba uwarsu d'aya ba amma saboda uba daya zama d'aya har tana ik'irarin zata iya sadaukar da komai nata ciki har da rayuwarta muddin zasuyi farinciki, shin anya hakan na iya yuyuwa afad'in duniyarnan kuwa? Nan take itama tayi alk'awarin itama daga yau zatayi koyi da wannan halin don tabbatarwa da 'yar uwarta cewa itama tana k'aunarta"

Murmushi Basmah tayi had'e da cewa "Allah sarki 'yar uwata muma muna sonki irin soyayyar da kike yimana kuma koda zan rasa rayuwata zanyi k'ok'ari in tabbatar da wannan soyayyar agareki" daganan dai gaba d'ayansu bacci yayi awon gaba dasu basu farkaba sai da safe saboda yanda sukayi dare suna fira.

Kasancewar har kace ta masu abun duniya da kuma inda kud'i suka zauna yasa koda safiya tawaye angama saka tiles da silin anyi fentin ko ina sai k'yalli da k'amshin sabun taka ke tashi, sosai su alhaji kabiru da bukar suka jinjinawa ma'aikatan don gaba d'aya gidan yakoma sabo tamkar bashi ba, koda Amina tafarka da safe ta tambayi ina 'yar uwarta don dama ita lafiyayyace bata cika son fitinaba kawai halin Zainab d'inne da cikaciki shiyasa takebiye mata sai babarsu tafad'a mata cewa tana can gidansu baffansu bata wani damuwa ba saima cewa tayi "Allah raka taki goma" amma duk da haka tad'anji kewarta kad'an aranta.

K'arfe goma nayi na safe yaya Mahmud ya azazzali su Billy akan suyi sauri su shirya faraaha nacan najiransu zai kaisu wajen k'unshi, adole yasa suka shisshirya aguguje bayan sun gaida iyayinsu, mom naganin Zainab taganeta don kamarta d'aya da mahaifiyarta wacce aminiyar tace kafin subaro can gidan, cikin sakin fuska ta tambayeta ya iyayenta suke duk dai suna lafiya ta amsa mata da lafiyarsu lau don dama tuni dady yasanar dasu sun dai daita shida 'yan uwansa shiyasa da ita har ummi basuyi mamakin ganinta ba, horn d'in motar yaya Mahmud da suka jiyo yasasu mik'ewa da sauri suka fita da sauri suna yima mom sai sun dawo,

Dady kuwa da shima lokacin zai fita yana ganinsu yace

"Yaran dady sai ina kuma?"

"Wajen k'unshi zamuje dady" Basmah tafad'a cikin sanyin murya, kallonta yayi da kyau ganin yanda tarame kuma tad'anyi duhu kad'an yasa yakirata.

Bata kawo komai aran taba ta nufi inda yake tsaye, batare da yace mata komai ba ya zagaya yabud'e gaban mota wajen driver ya shiga tare da yimata nuni da itama tashiga, bayan tashiga ta zaune ya kalleta cikin yanayin d'aure fuska had'e da cewa

"Basmah!"

Kanta aduk'e ta amsa masa da "na'am dady"

"Meyake damunki?, Basmah nafara shiga damuwa akan yanayin da nake ganinki aciki, tabbas nasan ciwo jarabawa ne amma shi ciwon zuciya dole yana da dalili, nadad'e da fahimtar cewa duk da kince karatune da kike buk'ata shine silar damuwarki da akwai wani abun daban wanda ban sanshiba kike b'oye mun, Basmah nayi maki abunda kike so wanda yakamata ace tunda kin samesa ki koma normal ayanda kike da Basmah d'ita da nasani, Basmah nan da sati biyu zaki fara karatu to meye dalilin cigaba da wannan damuwar Ina tausayinki sosai saboda ganin 'yan uwanki zasu tafi subarki, shiyasa bana son takuraki har ace damuwarki ta bayyana acikin wannan lokacin, amma nabaki nan da sati d'aya kafin ki wuce makaranta, matuk'ar kika k'i fad'amun hak'ik'anin damuwarki ko kikak'i fad'awa mahaifiyarki to tabbas sai rayuwarki tab'aci don zan tabbatar namanta dake daga cikin jerin 'ya'yanah tunda banida daraja da kimar da zaki iya sanar dani damuwarki" wasu zafafan hawayene suka zubo mata afuska cikin yanayin damuwa tace

"Kayi hak'uri dady idan nab'ata maka rai, amma wannan damuwar tawa bakomaine silar taba face..." Saurin dakatar da ita yayi saboda sanin halinta, yanzune zatace akan karatune ko jarabawa ce daga Allah, shiyasa yayi mata hakan don yatabbata kalamansa zasuyi mata nauyi zuwa nan da sati d'ayan da zasu tirsasata fad'in hak'ik'anin damuwarta, ita kuma so tayi tafad'a masa gaskiya basai nan da sati d'ayanba don izuwa yanzu tafahimci cewa koda tafad'a ba abunda zai canza tunda kwana biyu ya rage d'aurin auren amma sai gashi kuma ya dakatar da ita.

"Kije amma kitabbata kinyi tunani kina jina?"

"Eh dady don Allah kayi hak'uri zan fad'a" tafad'a tana goge hawayen idanuwanta.

"Shikenan maza jeki sauna jiranki, Allah yayi maki albarka kuma ya yaye maki damuwarki" sosai addu'arsa tasa taji sanyi aranta kuma yafahimci bawai fushi yayi da itaba, d'ago kai tayi takallesa had'e da cewa "amin dady nagode" hakan kuma yasa tasake danne damuwarta afuska bata bari kowa yafahimci yanayin da take ciki ba duk da tana jin kalmar dady tak'arshe nayi mata yawo akunnuwa.

Kai tsaye gidansu faraaha yaya Mahmud ya wuce ya d'aukota suka nufi wani katafaren shago wajen wata kwararriyar mata dake gyaran jiki da k'unshi had'e da gyaran kai anrubuta *MAMAN ABULKHAIR SKINCARE, HENNAH AND HAIR DESIGNER* Ajikin shagon.

"Thanks" suka fad'a atare had'e da fitowa cikin motar, ita kuwa faraaha dake kujerar gaba kallonsa tayi had'e da cewa

"All I have, nifa nafara damuwa ganin wannan ramar da kayi, da son samune Allah kada ka koma zuwa ko ina sai ranar bukinmu idan nakawo munkai ad'aki"

"Kai my golden heart itafa hidimar 'yan uwan nawa da tamu wazai yimana"

"Kabarta mana sai asamu wani yayi"

"Tirk'ashi zan iya barin tamu wani yayi, amma banda ta 'yan uwana tunda ni kad'aine yayansu da zai iya tsaya masu abukinnan"

"Itama kabarta all I have kahuta ai ga yaya Mahmud pilot nan ko?"

K'walalo idanuwa yayi waje had'e da cewa "Kai my golden 'YAN UWANA NE.." kafin ya ida suka k'yar da fad'in 'yan uwana nen atare tana dariya

"To d'an uwa ayimun afuwa, Allah yabar wannan soyayya taka da 'yan uwanka har a aljannah, akoda yaushe nakanji k'aunarka nak'ara nitso azuciyata saboda sanin darajar 'yan uwanka da kayi, natabbata nazab'awa 'ya'yana mahaifin da koba nida rai bazai tab'a bari kansu ya wareba ko au farrak'a a idanun duniya" tana gama fad'a tajuya da kanta zata fita cikin motar had'e da cewa "bye.. luv u, ka kula mani da kanka" saurin dakatar da ita yayi tare da fita cikin motar ya zagaya ta gefenta yabud'e mata gambun tafito,

"Thank you my mijin"
"Ur welcome my matar" yafad'a tare da karb'ar jikkar hannunta ya rataya akafad'arsa tare da rakata har cikin shagon tana tayi masa dariya, maman abulkhair yanemi gani tayi masa bill d'in kud'in da zai biya na gyaran amaren yace tundaga kai har k'afafu yana so tagyare masa su, su Batool ya nuna yace "wud'annan 'YAN UWANA NE, wannan kuma matata ce, don haka ina so duk kansu kiyi masu gyara na musamman" murmushi tayi had'e da cewa

"Yes sir, by six kadawo ka d'aukesu duka angama"

Da hannunsa yafara k'idanya awoyin da tabasa had'e da cewa

"You mean in the next 8hrs?"

"Confirm" tafad'a tana jaddada masa hakan da kai. Nan take yabiyata kud'in da tafad'a sannan yabar shagon, har yasa key zai bud'e gambun motar yakoma had'e da cemata

"Pls madam kada abarmunsu da yunwa" murmushi tayi cike dajin yaburgeta yanda yake matuk'ar son 'yan uwansa tace

"Ba damuwa sir, we here we don leave our customers with hunger, so never mind duk abunda suke buk'ata za'a basu suci in sha Allah, i assure you"

"Thank you madam" yafad'a tare da wucewa abunsa.

Dady kuwa yana fita yawuce shafi kai tsaye yasa aka koda masa kayan d'aki set uku gado, wardrobe da kujeru masu matsakaitan kud'i yasa aka nufi gidansu baba k'arami tare da wasu yaransa, nan take suna isa aka shiga gyaggyara kowane d'aki da kayan lokacin duk 'yan uwan nasa sunfita basa gida, saida yaga komai yafara kakkamta yanda yake so sannan shima yakoma shago, koda 'yan uwansa suka dawo matan gida suka taresu da maganar tunkafin sushiga sashen har da k'walla alhaji kabiru yayi nafarinciki alokaci guda kuma yana nadamar yanda suka cutar da d'an uwansu sai gashi yau yana rama masu wannan cutarwar da sukayi masa da alkhairi..





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____82💎


Bai tsaya jiran dawo warsa ba yad'au wayarsa yakirasa, dady naganin kiran nasa yayi rejecting sai yakirasa da kansa.

"Bashar wannan wace irin hidimace haka, bayan duk abubuwan da suka faru tsakaninmu yanzu kuma kana jifarmu da tarin alkhairai haka, kai da kake da hidimar aurar da 'ya'ya agabanka" alhaji kabiru yafad'a cikin raunin murya,

"Yaya kabar wannan maganar mana, ai komai yariga daya wuce, kufa 'YAN UWANA NE idan banyi makuba to wazanyiwa?"

"Duk da haka hidimar tayi maka yawa akai da bari kayi har sai bayan bukin yarannan tukuna" murmushi dady yayi don yafahimci meyake nufi, kuma shi Alhamdulillah cikin arzik'in da Allah yayi masa ko d'aya bisa kashi gomai bai kasheba tundaga hidimar 'ya'yansa har wannan, muryar alhaji kabiru yajiyo yana fad'in

"Mungode Allah yabar zumunci kuma ya albarkaci zuri'armu baki d'aya"

"Amin yaya, sai anjima idan nashigo, sai kuzama cikin shiri don yau ake dinner da daddare"

"To! Kuma dinner hardamu iyaye aciki?" Dariya dady yayi sannan yace

"Eh mana, baku kad'ai ba hadda manyan mutane daban daban insha Allah, yara k'anana kad'ai bazasu ba, amma daga 'yan shekara sha takwas abunda yayi sama are all invited"

"To masha Allah Allah yakaimu"

"Amin yaya sai anjima" suna gamawa yakira wayar baba k'arami yace yaje yafad'awa iyalansu yaya zasu iya komawa sashensu yanzu ya mallaka maau duk abubuwan da sukaga ansaka acikin d'akunansu halak malak, kayansu kuma zasu iyaba duk wanda suke so

Misalin k'arfe biyar da rabi na yamma yaya Mahmud yayi parking motarsa bakin k'ofar shagon maman abulkhair, yana zuwa ba b'ata lokaci duk suka fito don dama tuni tagama gyaresu tsaf from head to toe, a tsammaninta ma gaba d'ayansu amarene har Basmah da Zainab shiyasa tafara da faraaha tana gama mata sai kawai tace Basmah ta shiga, wani irin mahaukacin gyaran jiki tayi mata wanda nan take yasa haskenta fitowa dama gata fara abun ba'a magana ita dai Basmah sai binta takeyi da kallo dama tuni Billy da Batool tasa k'wararrin yaranta suma sunfara gyarasu yanda idan kagani baka tab'a banbancewa da ita tayi saboda ita ta koyarwar dasu, atare tagama gyara Basmah dasu lokacin ana zanawa faraaha bijin, nan takirawo wata daga cikin yaranta tace tazauna tazanawa Basmah siffar saboda yanda tayarda da k'warewarta, sukuma su Batool wasu suka cigaba da yimasu suma sun matuk'ar k'warewa sosai, Zainab kuwa cewa tayi ita bataso gaba d'aya gobe zataje itada 'yar uwarta Amina wajen wata mata ayimasu lallen daga nan sai suje wajen saloon, babu yanda basuyi da itaba amma tak'i yarda sai da maman abulkhair tafito takalleta had'e da cewa "pls kizo agyaraki mana, zakiyi kyau sosai"

"A'a madam nagode, akwai 'yar uwata da zamuyi tare"

"Ha'a keba amarya bace?" Mmn abulkhair tafad'a tana yimata kallon mamaki, dariya Zainab tayi had'e da cewa

"A'a madam, ai wud'annan ne amare nida yayya Basmah 'yan rakiyane kawai" tak'are maganar tana nuna su faraaha dake jeri su uku waje guda"

"What of dis one" tanuna Basmah

"Banda ita"

"Mts. Ba gaskiya ba, look at her she's totally resemble with amare fa" d'ago kai Basmah tayi had'e da cewa

"Gaskiya nefa ai nafad'a maki tun can ciki kika k'yaleni"

"Ha! Banjiba, namanta gaba d'aya nayiwa yayanku totalin kud'in gyaranku da price d'in amare" guntun tsaki taja had'e da ba Basmah hak'uri sannan tarok'i Zainab data bari ayi mata ko gyaran kaine da lalle, saida faraaha tasa baki sannan ta amince aka yimata. Wani irin kallo yaya Mahmud yabisu dashi saboda yanda sukayi kyau sai yakasa tsakaninsu wa zai cewa yayi kyau, kallon Mman abulkhair dake murmushi yayi yace

"Thank you madam, they all look excellence" fad'a d'a murmushinta tayi tana maijin dad'in yabon daya yimata sannan taciro kud'in daya bata d'azu taki'rga daidai nata tabashi sauran had'e da cewa

"Here is ur balance, nazata duka amarene to ashe mutum uku kad'aine amaren, so gashi nacire kud'ina na mutum uku wannan chanjin kane"

"Oh madam amma naga kowanensu yayi kyau sosai especially my big sis kinsa takoma har tafi amaren ma" yafad'a tare da jan hancin Basmah yana dariya

"Bakomai sir let take it volunteer"

"Wow..madam we do really appreciate it gaskiya kibarsu kema Mungode sosai, muje ko sisters" yafad'a tare da juyawa yafice, godiya suma sukayi mata don gaskiya sun yaba da gwanewarta da kuma karamcinta har Batool nafad'an itakam tasamu wajen zuwa bayan tayi aure, hadda karb'ar no tayi, har bakin titi maman abulkhair tarakosu ita da yaranta tana fad'in "thank you, thank you sir for the patronage, Allah yabada zaman lafiya" saida taga sun wuce sannan takoma cikin shagonta tana mai farinciki da jin dad'in zuwansu don ba k'ananan kud'i tasamu ba"

Kai tsaye yawuce dasu shagon Hindu _Him's touch_ wajen kwalliya don dama yakirata yace tazauna abunta basai tazo nan gida ba saboda lokaci yak'ure idan ya d'aukosu zai kawosu nan shagonta sai tayi masu makeup d'in.

Kasancewar ankira sallar magrib yasa suna shiga tace sushiga toilet suyo arwala suyi sallah kafin afara kwalliyar, haka kuwa akayi suna kammalawa tahau yimasu kwalliyar cikin gwanewa nan take cikin awa d'aya sai gashi tak'are masu duka su ukun, dama tuni yaya Mahmud yaje gida ya d'auko masu kayan da zasu saka wud'an da jiya suka fitar had'e da sakaau cikin akwati sannan yabiya yakarb'o na faraaha, yana kawowa ya juya yakoma gida don shima yayi shirinsa nazuwa wajen dinner. Yauma light make up Basmah tace Hindu tayi mata amma takafe kai da fata saida tasa tatsaya ta cancara mata kwalliya taji da fad'i wacce ko batafi amare ba sai dai suzo d'aya., sallar isha'i sukayi ta kawo masu abinci sukaci sannan tahau shiryasu cikin wasu arnayen dogayen riguna dasu kasha d'ige d'igen rose flowers ajiki suna ja har k'asa, gaba d'ayansu su uku komai iri d'ayane har zuwa takalmi kala kad'aice ta banbanta.

Faraaha aka fara shirya wa cikin rigarta pink colour flowers d'in dake jikinta da head sky blue, sai kuma Batool red colour d'in riga flowers and head ash colour sannan ita kuma Billy rigarta royal blue flowers da head kuma golden colour, nan take Hindu tafara watsa masu hotuna saboda yanda sukayi masifar kyau badai kamar Billy da zakaji kamar ka sace ta saboda d'an jikin dake gareta sai yazamana rigar tafi zaunawa ajikinta sosai,

Yayya Basmah kuwa street gown ce popul da tasa ajikinta wacce adaidai bayanta inda yakamata ayi tsaguwa sai telan ya zuba wata tattara dake ja har k'asa itama Hindu ta Nad'an mata head cilver saidai bayayi bud'ewar na amaren ba amma yayi maseefar yimata kyau abun sai wanda yagani, murmushi Basmah tayi ganin yanda itama tayi kyau, sai taji inama ace itama auren zatayi, fad'a d'a murmushinta tasakeyi had'e da fad'in "Alhamdulillah"

Saida suka kammala gyarawa da kusan minti ashirin saiga kiran yaya Mahmud ya shigo awayar Hindu, tana d'agawa ba abunda yace face

"Ya 'yan uwana hope dai dukansu kowa ya shirya"

"Eh angon faraaha ku kad'ai suke jira" tafad'a tana kallon faraaha dake faman kashe selfie da sister inlows d'inta, katse wayar yayi had'e da k'arasa saka agogon hannunsa yana kallon kansa amadibi, sosai yayi matuk'ar kyau cikin shaddarsa giznah da tasha d'unkin babbar riga sai wani maik'o maik'o da k'yalk'yali takeyi, feshe jikinsa yayi da turare sannan yanufi part d'in mom yanajin wani nisha d'i naratsa zuciyarsa, kallo d'aya mom tayi masa had'e da sakin murmushin da bata san lokacin daya kucce mataba tace

"Masha Allah my son kayi kyau sosai, to ina sauran 'ya'yan nawa banganesu ba"

"Yanzu zanje in d'aukosu Hindu tace sungyara"

"To masha Allah, Allah yasanya alkhairi kuma yasa ayi lafiya awatse lafiya ya amsa da "amin mom" sannan yafice,

Daidai shiga part d'in Ummi yaci karo da Mahmud pilot shima yafito cikin shirinsa na d'unkin babbar riga golden sai wani shek'i yakeyi saboda yanda kayan sukayi masa kyau abunka ga farar fata sai shida kayan suka kusa sadewa, murmushi yayi tare da kallonsa yace

"'Dan uwa kafayi kyau masha Allah, anya yau k'anwata zata ganeka kuwa?"

"Haba ai wlh nasan yanda tayi kyau rena wannan kwalliyar tawa zanyi idan naganta, abeg dady fa yakira yace kowa ya hallara wajen shigowar mu kad'ai ake jira"

"Ok to kodai muwuce gaba d'aya tacan idan mun d'aukesu"

"Eh ina ganin zaifi don dare yafarayi, nafi nakira dr inji idan ya shirya" yana rufe baki sai gashi yakirasa da kansa, d'auka yayi had'e da cewa

"Hello dr. Kana inane?"

"Gani bakin gate ko har kun wuce ne?"

"Haba yanzunnan muka gama shiryawa gamunan fitowa" ok dr Ahmad yafad'a tare da kashe wayar yana kallon Khalid abokinsa daya tuk'osa, madubin dake lak'e a saman motar yad'an gyarawa zama yana kallon fuskarsa ciki, sosai shima yayi kyau cikin shaddarsa gizna itama d'unkin babbar riga ash colour data matuk'ar karb'ar jikinsa, zaman hular kansa ya gyara tare da ciro d'an siririn glass d'in idonsa agaban aljihun motar ya saka,

Kallonsa Khalid yayi had'e dayin d'an guntun tsaki sannan yace "wai kai don Allah yanzu har wajen dinner ma sai kasaka glass d'innan? Ko gajiya bakayi kullum abu mak'ale afuskarka?" Murmushi dr yayi batare da yace masa komai ba saima fiddo wayarsa da yayi yana daddagalawa,

Ganin yayi banza dashi yasa shima ya sharesa har su yaya Mahmud suka iso wajen, fita sukayi sukaba juna hannuwa suka gaisa Mahmud pilot nata tsarguwar dr. Yana fad'in

"Kai ashe dr ba wankan k'ananan kaya kad'ai ka iyaba, ka kuwaga yanda kayi kyau cikin manyan kayannan, masha Allah ba'a magana dole yau kasa sister tarud'e" murmushi kawai dr yayi don shikam yana d'an jin nauyin yaya Mahmud shiyasa baifiye biye masaba idan yana wajen, abokanan yaya Mahmud ne suka k'araso wajen cikin wasu manyan motoci masu d'an karen kyau guda biyu da bak'a da kuma wata golden gaba d'ayansu k'irar marcadis, kallon dr yaya Mahmud yayi had'e da cewa

"Am srry dr. Zaku iya biyo bayanmu domin muje d'auko amaren daga can sai muwuce don dady yace mukad'ai ake jira"

"Badamu, Khalid tada mota ko?" Yafad'a yana kallonsa

Suna isa bakin k'ofar him's touch yaya Mahmud ya shiga ciki, ba'ayi minti biyu ba sai gashi ya fito amaren sun biyosa abaya, cikin bak'ar motar daya fito suka shiga gaba d'ayansu su uku, sannan yabud'ewa Basmah gaba tashiga, yace da sauri sadiq abokinsa dake tuk'a motar yashiga gaba amma yayi tafiya ahankali, cikin hanzari yace Zainab tabiyo bayansa suka nufi motar da dr keciki, ya kalli Khalid had'e da cewa

"Khalid zaka bamu angonnan sai kawuce mana da sister d'inmu pls.."

Haka kuwa akayi dr yafito Zainab tashiga azuciyata tana mijin haushin rashin amincewar da tayi suzo tare da Amina, gashi yanzu duk taji ta tsargu duk da babu wani wariya da aka nuna mata amma wannan mutumen da zata shiga motarsa ko kad'an baiyi mata ba saboda yanda taga khalid ya tsuret da idanuwa yana kallonta, adole dai tashiga tunda ba yanda zatayi shi kuma dr ahmad da yaya Mahmud suka shiga d'ayar motar dake bayan wacce amaren keciki dama Mahmud pilot shima yana cikinta nan take faruq abokin yaya mahmud da shine zai driving d'insu yayiwa sadeeq horn yatashi sannan yabi bayansa shima suna tafiya slowly shima Khalid daya d'auko Zainab yana biye dasu har suka isa babban hall d'in da yasha gyara tun daga waje, suna isa wasu securities d'in da aka zuba wajen tare da sojoji 'yan sanda da sauran wasu masu kaki da aka zuba wajen saboda tsaro ga manya manyan k'ososhin gwamnati da 'yan kasuwa dake wajen suka rufo had'e da bud'e masu gambunan motar, yaya Mahmud ne yafara fitowa daga cikin motarsu ya nufi inda aka bud'e gambun motar amaren yaba faraaha hannu tafito, sannan dr Ahmad shima yafito yaje shima yamik'awa Batool hannu tarik'o itama

Please Login or Register in order to submit comment