Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuska

"Malamai lafiya kukazo kuka yimun tsaye bisa kai?"

"Yayya Basmah dama naga aikin kamar zaiyi maki yawa shine mun kazo mu tamaki" har ga Allah tana son surik'a mata aikin amma tasan halin Batool da tsarguwa beside ita bata son raini don haka ta fuske tace

"To ban gayyace kuba kufice kubani wuri bana son sa ido" dariya Batool tayi had'e da cewa Billy

"Kinga abunda nake fad'a maki, ai yanzu saiki wuce muje ko?" Ta k'arasa maganar had'e da dafa kafad'un Billy zasu fita, batare data juyo ba ta d'ago mata hannu tabaya tana fad'in

"Byeee..the great cooker" wani irin tuk'uk'i da takaicine suka tasowa Basmah kamar tayi ihu tace sudawo amma ko kad'an bazata iya hakan ba, tsaki ta d'anyi tare da gallamata harara "Asauka lpy" takusa minti biyar a zaune tana tunanin ta inda zata fara gashi 8:00am har takusa, tukwanen ta shiga bud'awa d'aya bayan d'aya taga gaba d'aya ruwan da tasa sun tafasa har sunfara k'onewa, nan hankalinta ya sake tashi tashiga bud'e kitchen cavinage tana neman abunda zata zuba masu, can taci karo da busashen kifin da Ummi ke amfani dashi idan zatayi miyar tuwo irin k'ananun kifin nan da akecewa crayfish sai dai wud'annan ba laifi don ba k'anana bane sosai , lumshe idanuwa tayi had'e da cewa "Alhmdulillahi" da sauri taciro kifin, ko wankewa bata tsaya yiba ta rutatashi a d'ayar tukunya sannan ta d'auko tattasanta da albasa mai uban yawa ta yankasu manya manya tazuba aciki, magunan data gani Jere acikin wasu bowl masu marfi tabud'e kowane tasaka k'waya d'aya "bari inbarsu haka kada suyi yawa" tafad'a tana k'ok'arin goge hannuwanta arigarta, dubawa tayi taga idan akwai curry da tyme ai kuwa cikin Sa'a taga dakakkin spices d'in da mom ke amfani dasu kowane ajiye, da sauri tad'ibi curry da tyme da tafarnuwa tazuba can tasake hango dakakkar daudawa tazuba kai tsabar nuna gwanewar Basmah hadda kdakakken kanumfari tasaka, kamar ance ta duba gefenta daga k'asa taga gyad'a cikin wani d'an bokiti k'arami tun jiya ummi ta jik'ata bayan sallar magrib saboda tajik'a sosai ya zamana yau blanding d'inta kad'ai za'ayi. Da sauri Basmah tarufe tukunyar ferfesun kifinta ta d'auko jik'akkar gyad'ar ta tsameta sannan ta zube cikin tukunya ta biyu da ruwan ta ke tafarfasa tarufe, fridge ta bud'e ta d'auko ruwan da zata sha don cikinta yafara neman abunda za'a saka masa saita hango gansarar kunun gyero da Ummi ke kunu da ita, d'au kowa tayi tad'ibi kusan rabinta tazuba a cikin tukunyar data zuba gyad'arta a hankali tasa ludayi tana motsawa nan take yayi kabri saboda yawan gansarar ammafa yayi k'olallai sosai ga kuma k'olallan gyad'a sun fito b'aro b'aro. Murmushi tayi had'e da sauke tukunyar ta aje gefe tayi wata irin ajiyar zuciya tace

"Kunun gyad'a!, dama ashe sauk'i ne dashi, ko kad'a bayada wata wahala" Juyowa tayi gefenta ta d'auko k'aton flaks d'in data gani ajiye cikin kayan jere tajuye kunun aciki sannan ta koma ga fik'ar doya, ganin lokaci na k'urewa yasa ta ajiye fik'ar doyar ta tashi tabud'e tukunyar ferfesun kifinta, "yawwa nasan dai ya nina haka yanzu bari na kwasheshi duk da dai akwai ruwa acikinsa ai zaifi dad'i ana d'an d'ebowa da ruwan da kifin anaci" kula mai kyau ta d'auko tazube farfesun aciki sannan ta d'auko bowls d'in miya da spoons ta d'orasu duka akan k'aton trey, hannu tasa tagoge zufan daya taran mata agoshi sannan ta d'auka tanufi wajen dining table dasu, jeresu tayi tsaf abun gwanin ban sha'awa kai kad'auka abun arzik'ine aciki sannan ta d'auki treyn takoma kitchen dashi, flaks d'in data zube kunun gyad'arta ta d'auko tare da tea cups suma takai ta ajiye akan dining,

Cikin tsiwa Batool tashigo kitchen d'in tana fad'in "wai har yanzu yayya Basmah baki gama had'a breakfast d'innan ba, nifa yunwa nakeji wlh"

"To munafuka ai nagama, yam balls d'in kad'ai ya rage" fridge ta bud'e ta d'auko garar ruwa har zata rufe sai ta hango kifi aciki, kuma tasan Billy tace hadda ferfesun kifi za'ayi

"Yayya Basmah kikace kingama? Hadda ferfesun kifin duka kinyi"

"Eh mana" tace batare da kalli inda Batool take ba, "Amma naga ai ga ki..."

"Abeg don Allah get out kar kisa nayi confusing abunda nake sonyi" Basmah tafad'a had'e da had'a hannuwanta kamar yanda indiyawa keyi, "ok! No wahala am out" itama tafad'a tare da d'aga kafad'unta tabar wurin,


Ummi ce tafito cikin doguwar rigarta royal blue anyimata k'awa da Cristal stone, rigar tayi mata matuk'ar kyau sosai saboda yanda ta d'an kama jikinta, pink vail ne ta d'auro akanta abun ba'a cewa komai don indai kyaune tayishi sosai, "Bilkisu..Bilkisu.." ta kwala mata kira tana gyara zaman agogon dake sanye ga tsintsiyar hannunta,

"Na'am Ummi ganinan zuwa"

"Haba what is the time now ace har yanzu baki gama had'a breakfast ba, kinaso yunwa takamamun yarana ne" cike da mamaki take kallon Billy dake fitowa cikin d'akinsu gashi tanajin motsi cikin kitchen,

"Ummi gani" saida takalleta irin kallon nan mai d'auke da alamar tambaya sannan tace

"Motsin waye nakeji a kitchen?"

"Yayya basmah ce"

"Ok kingama had'a komai ne?"

"Ummi yau bani nake had'in breakfast ba yayya Basmah ce keyi" gaban Ummi ne yafad'i don rashin sanin mezata isko, kitchen d'in tanufa ta isko Basmah nazuba doyar data fera acikin tukunya, kallonta tayi sannan tayi murmushi had'e da dafa kafad'arta,

"Sannu da k'ok'ari Basmah dama kece a kitchen d'in, ai tund'azu nazata Bilkisu ce, agaisheke Allah yayi maki albarka, yanzun kin kammala ko akwai abunda yarage"

"Eh yam bolls d'inne kad'ai ya rage shima yanzunnan zan k'arasa"

"A'a jeki kiyi wanka nina k'arasa tunda kin gama mai wuyar kinji ko? Wani irin dad'ine ya rufeta don tund'azu tunanin yanda zatayisa kawai takeyi, azuciyarta kuwa cewa tayi ashe dai ko Ummi tasan aikin nada wahala, murmushi tayi sannan ta wuce d'aki ita kuma Ummi ta k'aro wutar gas d'in saboda doyar tayi saurin nina batare da tabi takan abunda Basmah tahad'a ba taci gaba da aikinta,

Cikin mintunan da basufi sha biyar ba Ummi tagama had'a yam ball d'inta takawo kan dining da tund'azu kowa ya hallara itakad'ai ake jira, cikin soyayya da yaba shigar datayi dady yace

"Weldone madam, yau kam anso asa mumakara"

"Am sorry dadyn yara, weldone yau ai na basmaty ne saboda ita ta shirya breakfast ida k'arasa mata kad'ai nayi, beside laifin ma duka na Bilkisu, sun shige d'aki sun barta ita kad'ai da aiki aidole tawahala sosai"

"Kai Ummi itafa Bilkisun da kike bari ita kad'ai tayi kuma naga akan lokaci take gamawa, ita dai d'in ce laziness" Mahmud ne yafad'i haka yana kallon Basmah data wani fuske ita ala dole yau ayaba mata da aikin datayi,

"What ever dai yakamata ace sunfito sun kamamata koba haka ba dadyn su" saida dady yayi murmushi sannan ya kalli Basmah yace

"Weldon Basmah 'yar gidan dady, yanzu dai a ajiye wannan zance afara zubomun ferfesun kifin in new test and aroma na 'yatah"

Ummi na bud'e kular ferfesu gabanta yafad'i saboda k'amshin kanunfari daya fara dukan hancinta, bata tsorata ba saida taga d'iyan k'anan kifi nayawo asaman ruwan ferfesun, k'walo idanuwa Ummi tayi ta juyo tana kallon Basmah, murmushi basmah tayi irin wow d'in nan tazata Ummi zatace, kallon dady tayi sannan ta kalli Mahmud, wani farincikine ya mamaye zuciyar har tana fad'a aranta yau ba reni tsakaninta da yaya Mahmud saboda yanda taga Ummi na kallonsu ta tabbatar sak'one take isar masu na yanda taga had'uwar ferfesun.

Bassam ne dake kusa da Ummi ya lek'a kular da ferfesun keciki shima ya k'walo idanuwa awaje

"Kai..! Dady kaga yanda grasshoppers (fara ko fari) suka mutu acikin ferfesun, gaskiya ni bazanci ba gasunan duk suntaso sama, Bilal zoka gani"

Rufe kular Ummi tayi tana d'an murmushin yak'e sannan tajawo flaks d'in kunu, cup ta d'auka tana zubowa ahankali aikuwa k'olallan da yayi dana gyad'a suka dinga fad'awa acikin cup d'in da wani yafad'o saida kunun yayi tsalle yafad'awa Ummi a fuska, rufe kunun tayi ta d'auki plates ta zubawa kowa yam ball d'in cikin zuciyarta kuwa b'acin raine kwance ace wai k'atuwar budurwa irin Basmah bata iya girki ba, batare da tace k'anzil ba tajawo hannun Basmah tayi kitchen da ita, suna shiga takai mata d'an rank'washi akai tace

"Wannan wace iriyar kwamacala ce kika had'a Basmah? Idan baki iyaba meya kaiki yi? Ina kika tab'a ganin anyi ferfesun crayfish" turo baki Basmah tayi hawaye na neman zubo mata a idanuwa ita kuma Ummi ta kunna gas had'e da d'ora ruwan zafi akai tana cigaba da yimata fad'a cikin b'acin rai,

"Kamata yayi ace tunda baki iyaba kin yimun magana sai narik'a maki muyi tare kiga yanda akeyi, ko kuma kitambayi Bilkisu tasan duk yanda akeyin komai sai tafad'a maki, yanzu dakin natsu yanda ya kamata ko kin tambaya baga kifinan acikin fridge ba, yakamata mirage wannan girman kai naki da shashanci kinatsu ki koyi girki domin gidan wani zakije, babu namijin da zai iya tolerating wannan noisens da kikayi, at least kodon kizama isassar mace awurin mijinki yakamata ace kin iya abubuwan da suka shafi rayuwar ki data zaman gidan auren ki amma ke kenan kullum cikin bak'in rai da sauraren wak'e wak'en banza a earpiece tare da rashin kunya, to kicanza wannan ba rayuwa bace kuma ba tarbiya mai kyau bace da zata zaunar dake d'akin ki idan Allah ya gwadamana,

Ruwan zafin natafasa Ummi ta d'auko sauran gansarar data rage tana girgiza kai tazuba mata ruwa ta d'auraye sannan ta dama wani kunun amma shi wannan normal kunun gyerone,

Tana juyewa ta kashe gas d'in sannan takoma inda su dady ke zaune d'auke da kunun ita kuma tayi zaunenta kitchen tana sharb'ar kuka, cup's ta d'auka tazubawa kowa tare da sugar sannan ta maido da kallonta ga dady dake cin yam ball d'insa hankali kwance

"Am sorry dadyn yara kayi manage da wannan kunun, wud'annan bazasu ciwu ba" murmushi yayi sannan ya karb'i cup d'in kunun data mik'o masa, a hankali yake sipping saboda zafin da yake dashi har yasha fiye da rabi sannan ya ajiye,

"Thank you rabba'atul bait, am going saboda nayi latti sosai" Allah ya kiyaye gaba d'aya suka yimasa ita kuma Ummi tarakasa har bakin mota sannan tayi masa addu'ar Allah ya kiyaye hanya kuma yasa adawo lpy, hugging nata yayi tare da yimata light kiss a forehead d'inta yana fad'in

"Amin ya rabbhi, Allah yayi maki albarka" tace "amin" yana shiga motar ya tayar had'e da zuge glass d'in dake gefenta ya duk'o da kansa yana fad'in

"Ki kula mani da kanki sosai rabba'atul bait, luv you more than how word can say it"

"Luv you too dadyn yara" tafad'a cike da jin kunya shikuma yaja motarsa yana dariya kasancewar drivern sa yayi tafiya k'auyensu shiyasa yanzu shike driving kansa zuwa office wata rana kuma Mahmud ne ke kaisa,

Yana fita saiga wata motar ta kunno kai ta shigo cikin harabar gidan tayi parking, har zata juya sai ta hango babbar aminiyarta hajia maijidda tare da wata k'awarsu hajia fareeda nafitowa daga cikin motar, farincikine ya rufeta lokacin da suka iso inda take tsaye tana murmushi, Rungume su tayi cikin soyayya da shak'uwar da zata nuna maka cewa aminantane na rai da rai tun suna 'yan k'anana, manyan matane masuji da kansu daka kallesu zaka tabbatar wayewar ilimin addini data boko sun ratsasu, bayan sunyi breaking hugging d'in da suka yiwa juna suka mik'amata hannuwansu dake d'auke da zobbunan zinari suna fad'in

"Assalamu alaikum hajia Aisha" cikin farincikin ganinsu ta amsa masu tare da rik'o hannunsu tana fad'in

"Mushiga daga ciki...."

_Yau ake yinta ga aunty maijidda ga Basmah delicious, to asha dad'i lpy duk da kince baki amshi gayyataba amma rabo ya rantse sai maishi inji malam bahaushe..lol๐Ÿ˜ƒ_
















Mr's huss@inโœ

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____23๐Ÿ’Ž


Da sauri suka dakatar da ita, "a'a hajia Aisha akan hanya muke zamuje legas ne wajen d'auko kayayyakin mu sai hanya tabiyo damu ta wajen gidanki shine mukaga bai kamata muwuce batare da mun kawo maki ziyara ba,

"Kai amma naji dad'i sosai wlh, yau sha rabo? Gaskiya duk da haka yakamata ace kun shigo daga ciki ko ruwane kusha ko?"

"Kiyi hak'uri hajia Aisha sauri mukeyi next time idan munzo zamu yimaki wuni" duk da bahakan tasoba cikin murmushi tace "shikenan na fahimceku dama 'yan kasuwa haka suke basada lokacin kansu" dariya sukayi had'e da tafewa "yo kinga laifinmu? Kema ai bayadda bamuyi dake akan ki shigo adama dake ba kikak'i"

"Ai very soon zaku jini but not now? Lokaci nazuwa" dariya sukayi gaba d'ayansu tare da komawa cikin mota ita kuma Ummi ta koma cikin gida had'e da cewa ina zuwa kud'an jirani pls

Bayan minti biyu sai gata tadawo rik'e da 'yan matsakaitan ledoji guda uku a hannunta, d'aya snacks ne masu yawa da takeyi tana ajewa saboda irin bak'in dake zuwa unexpected ta biyun kuma drinks ne aciki sai kuma ta ukkun turarukkane masu k'amshi da tsada, gambun motarsu na baya tabud'e ta ajiye ledojin sannan tadawo wajen da hajia maijidda kezaune a sit d'in driver tace

"To matafiya ina godiya da wannan ziyara taku, Allah ya tsare hanya" juyawa tayi takalli ledojin data ajiye masu sannan tasake juyo tana kallonta

"Amin ya Allah hajia Aisha ke kullum bakya gajiya da yimana hidima"

"Haba nothing much fa? Ai yiwa kaine"

Daga haka sukayi ban kwana da ita zuciyoyinsu na masu yabon kirki da kuma kyawawan halayen Aisha,

Ummi nakomawa cikin gida tanufi kitchen aduk tsawon lokacin nan Basmah na nan zaune tana kuka a inda tabarta taye Ummi tayi cike da mamaki sannan tasa hannu ta rik'o hannun Basmah ta mik'ar da ita tsaye ahankali take janta har suka isa dining table, hannunta ta saki tajawo kujera, ta sake rik'o hannunta ta zaunar da ita akai, plate d'aya ta d'auko ta ajiye a gabanta tabud'e ferfesun kifin tazuba mata sannan ta sake d'auko cup shima ta cikasa da kunun ta ajiye mata, da sauri Basmah ta d'ago kai tana kallon Ummi dake tsaye akanta tayi folding hannayenta tana kallonta, murmushi tayimata had'e da lumshe idanuwanta tana nuna mata plate d'in dake gabanta

"Bismillah, yimaza kici kar yunwa ta tab'a munke" idanunta na hawaye tace

"Ummi ni bazan iyaba"

Su batool dake zaune afalo tare da yaya mahmud suka dinga yimata dariya, cikin b'acin rai Ummi tajuyo

"Gaba d'ayanku kub'acemun da gani ko ranku ya b'aci, Babana kaje ka shirya akwai inda nake son aikinka" suna fita tajawo kujerar dake kusa da Basmah ta zauna, kallonta tayi had'e da d'ora hannunta akan nata dake saman table d'in ta rumk'e sannan tace

"Basmah banyi maki fad'a saboda bana sonki ba balle kizauna kina kuka har na kusan minti 30, nayi makine saboda kuskuren da kika aikata, ba lallene kiyarda da abunda zanfad'a ba shiyasa na zaunar dake kici abincin da hannunkine ya sarrafashi kiji yanda yake kozaki yarda da cewa kuskurenne yajawo nayi maki fad'an"

"Ni nayarda nayi kuskure amma ni banason fad'a, saboda mom d'ina bata saba yimani shiba ko kad'an" shiru mom tayi tana kallon yanda take fad'a mata wannan maganar ido da ido kafin can ta sake wani dogon numfashi tace

"Shikenan Basmah bakyason fad'a ko? Naji bazan sake yimaki ba, tabbas bazan sake yimaki fad'a agidan nan ba, to amma ke kuma yazame maki dole kinatsu kibi duk wasu k'a'idojin dana shimfid'a maki ba tare da rashin kunya ba, if not kuma bazan dena yimaki fad'aba ta k'arasa maganar had'e da mik'ewa tabar falon zuciyarta na rad'ad'i, har ga Allah bataso faruwar haka tsakaninta da itaba, amma ya zatayi idan har bazata jurewa ganin Billy acikin yanayi irin wannan ba to don me zata k'yale Basmah acikin wannan halin, koba komai amana take agareta kuma dole Allah zai tambayeta akan amanar daya bata, 'yar mijin tace hakk'ine akanta takula da tarbiyarta koda mahaifiyar ta nanan balle kuma da batanan.

Tana wucewa Basmah tagoge hawayenta

"Wallahi babu wanda ya isa yasa inbi k'a'idojinshi tunda bashi ya haifeni ba kuma indai rashin kunyace yanzu aka fara ganinta"

Tunda sassafe mom ta tashi cikin wani irin farin ciki tana jiran isowar 'yar uwarta kuma aminiyarta wato hajiya kilishi, sosai su papi sukayi mamakin yanda take fara'a saboda tunda tadawo gidan cikin bak'in rai take amma sai gashi yau takasa zaune takasa tsaye saboda tsabar farinciki, kallon hajia kaka papi yayi yace

"Baby anya yau lpy 'yarki ke wannan farincikin, shin kodai addu'ar muce takarb'u"

"Ga alama domin yau tunda safe na lura da yanayin da take ciki na farinciki, Allah yasa sauyawar mummunan halintane zuwa kyakkyawa zai bayyana"

"Amin ya Allah" juyowa papi yayi yana kallon mom dake tsaye abakin window tana jiran isowar hajia kilishi karaf suka had'a ido dashi

"Zonan usain", saida tasake kallon windown sannan taje gabansu ta zauna"

"Gani papi"

"Dama cewa nayi lpy kike wannan zagaye zagaye cikin farinciki?, ko alhaji ne ketafe" cikin farinciki tace

"Lahhh...papi na manta bangaya maku ba, ai jiya mukayi waya da 'yar uwata kilishi tace yau tana nan isowa harma tace ingaisheku sosai" cike da farinciki daya bayyana d'auke a fuskokinsu sukace

"Shine baki fad'aba sai yanzu, eh lalle dole zakiyi farinciki yaushe rabo?, Allah ya kawota lpy kotasa kidena wannan shashanci kikoma gidan mijinki ki rungumi 'ya'yanki" sanin yanda take da ita yasa suka dena mamakin farincikin da takeyi.

_WAYE HAJIA KILISHI_

'Yace ga aminin papi kuma shak'ik'in abokinsa wanda yarasu tun tana k'arama, hakan ne yasa papi yanemi alfarmar mahaifiyar ta da kuma 'yan uwan mahaifinta da abashi ita tadawo hannunsa da zama tare da yimasu alk'awarin zai rik'eta amana tamkar 'yarsa, kasan cewar kowa yasan halin papi mutumen kirkine kuma ansanshi tare da mahaifinta yasa batare da wani dogon tunani ba aka bashi ita shikuma ya karb'eta hannu biyu ya had'ata da 'yarsa Hussaina, kasan cewar halinsu yazo d'aya sai sukayi matuk'ar shak'uwa da junansu ta yanda hatta baccima baya rabasu, suna son juna sosai kuma duk abunda zasuyi atare sukeyin abunsu batare da sun bari kowa ya sani ba, a tsawon rayuwarsu babu abunda ya tab'a rabasu sai aure wanda hakan ne ya sanyasu rabuwa da juna badon sun soba, amma duk da haka babu wanda ke iya zartar da wani abu agidanta batare da taimakon d'an uwansa ba, duk abinda d'aya zaiyi sai yanemi shawarar d'aya akai hakan yasa akoda yaushe suke mar
ari da d'okin ganin junansu, hajia kilishi tun tana k'aramarta fitinanniyar yarinyace ta iya makirci da tuggu kala-kala, sam bataso taga anzauna lpy arayuwarta kuma bata shakkun kowa akan duk abunda tasa agaba, hajia kaka kad'ai da papi take d'an shakkar yin abu a gabansu koshi don tasan taka mata burke zasuyi, agabansu tana nuna halayen kirki ko kad'an bazata tab'a yin abun asshaba, shiyasa suke matuk'ar ganin mutuncinta da kimarta fiye dana 'yarsu da suka haifa domin bakad'an take girmamasu ba, wannan shine tarihin hajia kilishi.

Tsayawar motar da sukaji yasa su yin shiru daga fad'a da nasihohin da suka fara yimata akan maganar abunda yafaru na gaskiya tsakaninta da dady da Mahmud yafad'a masu,

Cikin hanzari mom ta tashi tanufi bakin k'ofa don tarbota, tana fitowa cikin motar suka rungume juna cikin farinciki saida sukayi kusan minti uku ahaka kafin can hajiya kilishi ta d'ago had'e da rik'e hannun mom tana yimata wani kallo tun daga sama har k'asa


"Tafd'i jam qawata anya kece kuwa? Kinganki yanda kika rame kika lalace kamar bake ba, to wlh badon muryarki danaji ba aguje zan ingijeki in wuce abina"

Wani irin takaicine da bak'in ciki suka rufewa mom zuciya wanda d'acin kalamanta yasa hawayen ta zubowa batare data ankara ba, da sauri taja iska a hancinta tare da goge hawayenta

"Bari kawai 'yar uwa akwai labari" tak'are maganar tana kallon yanda jikin hajiya kilishi yayi wani irin haske da kyau gaba d'aya ta canza tayi fresh ga wata irin qiba data k'ara kamar ba itaba tana mamakin yanda tasamu wannan hutun ita dake auren mai mata uku itace ta hud'u kuma mijinta ko kad'an bai kamo ko rabin arzik'in dady ba, dariya tayi mata had'e da jujjuyawa ahankali tana fad'in "dubeni da kyau kigani babu abunda ke damuna yanzu saboda remote control d'in gidan alhaji dashi kansa yana hannuna sai yanda nayi dashi"

Baki bud'e mom ke kallonta tace

"Ke kina sha'aninki, muje daga ciki kihuta ki shafa mani ko meye sirrin"

Tafewa sukayi suna dariya har suka isa falo, adaidai bakin k'ofar shiga hajia kilishi tawani gyara mayafinta had'e da marairarice fuska kamar tak'warai tashiga bakinta d'auke da sallama, cike da ladabi ta isa inda su papi kezaune taduk'a har k'asa ta gaishesu sannan taje ta rungume hajia kaka tana fad'in

"Hajiya ta nayi kewarku dayawa"

"Allah sarki yarinyar kirki muma munyi kewarki, ya maigidan naki da abokanan zamanki duk lpy kuke ko?"

"Lpy klw hajia duk sunce agaishe daku sosai tare ma mukaso zuwa dasu to sai Allah bai nufaba saboda wasu dalilai amma sunce zasuzo suma sugaisheku insha Allah"

"Madallah! muna amsawa ya hanya ya hanya?"

"Alhmdulillah papi, ashe ita kuma Hussaina abunda yafaru kenan?"

"To kindai gani, abunda tun k'urciya ba'ayiba sai yanzu" papi ne yafad'i haka yana kallon mom dake gefe tsaye

"To papi k'addarorine Allah yatsare gaba"

"Amin, kidai yimata fad'a inzataji, yakamata ace takoya daga gareki yanda kike zaune lpy da abokanan zaman ki, amma ita ace ko yaushe gatanan cikin zargi da son zuciya tahana abokiyarta zama lpy kuma tafitini kanta" Kallonta tayi sannan tace

"Allah dai yakyauta papi, abubuwan ne babu dad'inji gaskiya"

"Tashi kije daga ciki ki nemi ruwa kiwatsa sannan kici abinci kihuta kinji ko? Allah yayi maki albarka yajikan mahaifinki" hajia kaka tafid'i haka itama tana k'ok'arin tashi

Suna shiga d'aki mom takai mata duka da wasa, tace

"Ke kam bakida kirki, bazaki dena k'aryannan takiba ko? Hadda wani zancen da atare zakuzo da duka kishiyoyinki don d'ai neman suna agurin papi ni kuma kijamun zagi ko?" saida tayi dariya sosai sannan tace

"Eh mana, bagashi har papi ya yarda ba, halinshi dai nanan yanda yake be chanza ba, gaskiya akwai gyara cikin rayuwar shi, ace wai da kanshi ke fad'ar wai kin takurawa kishiyarki, cab ashe da zaiga yanda nake da nawa kishiyoyin wlh sai ya tsaneni don kokad'an dasu har 'ya 'yansu babu maijin sanyina bugu da k'ari ko wanda ya ajiye su wlh indai ina kusa basu isa suji sanyin shiba, ke nifa nan zan iyayin komai don inga nike taka bani ake takawa ba"

"Hmmm barka da arzik'i aini kam k'asa nake war was ana takani dani har yarana sai yanda akayi damu"

"Hhhh ki kwantar da hankalinki nesa tazo kusa yanzu ke zaki taka duk wanda kikeso don nazo maki da maganin matsalar ki"

"Da gaske 'yar uwa?"

"Sosai kuwa kedai kawo kunnenki kiji...


















Mr's huss@inโœ

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Jinjina had'e da gaisuwa ta musamman ga dukkanin members d'in *MUSHA KARATU NA..YBK GROUP* hak'ik'a zuciyata na alfahari da kasan cewata atare daku domin kud'in mutane ne masu tsananin karamci da halaccin dake samar da nishad'i atare da ita, fatana Allah ya tsarkake dukkanin gabb'anku ya kuma albarkaci ahalinku, ina so kusani cewa aduk bugun zuciya d'aya nawa d'auke yake da miliyoyin k'aunar ku fisabilillahiโค๐Ÿ’˜_


๐Ÿ’ŽPage_____24๐Ÿ’Ž


Zaro idanuwa mom tayi tana mai kallon hajia kilishi sannan ta kwashe da dariya

"Ke 'yar uwa da gaske kikeyi?"

"Hmmm kina wasa wallahi ba itaba hatta shi kansa sai ya zame maki tamkar raqumi da akala, kedai kawai kisha kuruminki, kina zaunenki zakiga aiki da cikawa ba boka ba malam"

"Haka nake so domin naci alwashin salwantar da rayuwar Aisha da zuri'arta saboda na tsaneta fiye da yanda natsani shed'an"

"Hhhh kai k'awata shed'an fa kikace!" hajia kilishi tafad'a had'e da jefa cingum abakinta tana tauna, hannunta tasaka acikin jakarta tafiddo wata 'yar k'aramar kwalba kamar ta turare tamik'awa mom "ungo wannan ruwane aciki da basu wuce 3 drop ba amma sunada tsananin k'arfi, zakiyi amfani dasu kamar sau uku bayan sallar isha'i, zaki samu kad'a kid'an dangalo ruwan kad'an sai kiyi inserting acikin jikinki har na tsawon kwana uku amma ki tabbatar ranar alhajinki zai kusanceki, azahiri wannan kayan ni'imar matane ga duk wanda ya gani amma abad'ini sirrin mallakane mai k'arfi, ina tabbatar maki da cewa matuk'ar kikayi amfani dasu kuma alhajinki ya

Please Login or Register in order to submit comment