Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kike ciki har zuwa lokacin da za'a kammala bukinnan, amma idan wannan ciwon yak'i kwanta maki har zuwa lokacin to tabbas da kaina zanje insanar da dadynku kuma zan nuna wannan sonkan nawa tahanyar durk'usawa koda agaban 'yar uwar kune data hak'ura tabarmaki Mahmud don bazan iya jurewa in rasaki ba" tak'are maganar cikin kukan dake nuna irin tsantsar soyayya da tausayin 'yar tata da takeji.

Ko kad'an yaya Mahmud da Batool basuyi na'am da shawarar da mom tayanke ba, wanda hakan yasa yaya Mahmud cewa

"Mom wannan fa bashine mafitaba kawai.." Katsesa mom tayi tahanyar d'aga masa hannu tare da d'ago kai tana kallonsu tace

"Indai nice mahaifiyarku banyafe kuje kufad'i wannan maganarba ga kowa saboda yin hakan tamkar kun muzanta 'yar uwar kune" murmushi Basmah tayi jin abunda mom tafad'a tare da qudurtawa aranta dayardar Allah har akanmala bukin bazata koma yarda tabayyanawa kowa halinda take ciki ba koda sud'in ne, nan take tarufe idanuwanta kamar tayi bacci mom na shafa gashin kanta ahankali,

Tsabar yanda ransu tab'aci akan abunda mom tafad'a yasa daga yaya Mahmud d'in har Batool suka fice daga cikin d'akin, kallonsa Batool tayi had'e da cewa

"Yaya kaji dai abunda mom tafad'a yanzu meye shawara?"

"Babu!, kawai abunda yafi mubita da addu'a Allah yasawak'e kuma yarabata da wahala"

Gaba d'aya Basmah da Batool da Billy da kuma yaya Mahmud daren basuyi bacci ba, it dai Basmah ciwon da take cikine ya hanata, Billy kuma rad'ad'i da zafin hukunci data yankewa kanta ne ya hanata sukuma su Batool tunanin makomar 'yar uwarsu akan halin da take cikine yahanasu bacci.

Soboda kukan da Billy keyi har saida ya sakar mata zazzab'i tashi tayi tajawo first aid d'in dake cikin wardrobe tab'allo PCM tasha sannan tashiga toilet tayo arwala, sallah takeyi amma har lokacin hawaye basudena saukowa daga cikin idanuwan taba har aka kusan kiran sallar asuba, addu'a tayi sosai mai tsayi tare da fawwalawa Allah dukkanin al'amurranta, har aka kira sallar asuba tananan zaune akan abun sallah, tashi tayi tayi raka'atanil fijir sannan taci gaba da addu'o'inta kafin atayar da sallah, tana gama sallar asuba tad'auko azkar d'inta taci gaba da karantawa har rana tafito, toilet tashiga tayo wanka sannan tafito tayi tsaye gaban madubi tana kallon yanda idanuwanta suka kumbura, gaba d'aya ko iya bud'esu batayi sosai, wasu hawayene suka ziraro mata a fuska ta koma gefen gado tazauna tare dasa hannuwanta tadafe kanta tanaci gaba da kukan, wata zuciya ce tace mata,

"To yanzu meye abun kuka tunda ke kika zab'awa kanki rabuwa da farincikinki, yazama dole kema kiyiwa 'yar uwarki sadaukarwa da halaccin da tayi maki wajen danne soyayyarta, wanda badon kunnuwanki sunji komai ba da tak'wammacewa tarasa ranta saboda kisamu farinciki" nan take ta tuna da jinin data sharo jiya ad'akin ummi ajikin tissue, tabbas yanzu tasamu amsar cewa wannan jinin na Basmah ne don ita takwana ad'akin kuma tasamu dalilin fitar jinin atare da ita.

Hannu tasa tagoge hawayen ahankali tafurta

"Ya hayyu ya qayyum birahmatika astagisu, aslihli sha'ani kulluhu wala takilni ila nafsi d'ar fata ain,laa'ilaaha illa antassubhanka inni kunta minazzalimin, Allah ina tawassali da girman zumunci da kuma kyakkyawar manufar dake cikin zuciyata, ya Allah Kabani hak'uri da juriya rashin yaya mahmud, Allah ka sanya alkhairi acikin kasantuwarsa shida 'yar uwata, Allah Kabani dangana kuma ka tausayawa 'yar uwata mahaifinmu ya amince mata tasamu farincikinta" kuka maik'arfine ya sake kuccemata tafad'a akan gado tana auruttai masu kama da sabbatu "kayafe mun yayana, ina matuk'ar sonka, ina sonka sosai sonda bazan koma yiwa wani d'a namiji shiba aduniya, amma dole nahakura dakai domin ina son 'yar uwata fiye da soyayyar da nakeyiwa ni kaina, zan barkane kawai don ceto rayuwarta, badon hakaba da tare zamu rayu kuma atare zamu mutu",

A hakane har bacci mai nauyi yasoma d'aukarta saboda rashin baccin da bata samu tayiba jiya, cikin baccin ne tayi mafarkin wai gata zaune cikin taron mutane d'auke da wani abu ahannunta da batasan ko meyeba tanata kuka, nan taga ana k'ok'arin fitowa da makara d'auke da gawa, tasowa tayi tana son taje taga ko gawar waye sai aka rik'eta aka hanata zuwa wajen, kuka takeyi sosai lokacin da mutane ke k'ok'arin fita da gawar tana don Allah abarta taje amma aka hanata, wani iskane mai k'arfi yataso had'e da d'age tabarmar da aka rufe gawar da mayafi, kawai sai taga fuskar 'yar uwarta yayya Basmah aciki kwance tana murmushi, fad'uwar da tayi zaune ne tare da k'ank'ame abunda ke hannunta tasaki wani irin kuka mai sauti yasata farkowa daga baccin da takeyi afirgice wanda yayi daidai da shigowar Ummi ad'akin, da gudu ta taso had'e da rungumeta tana kuka "Ummi ni bazanyi aurennan ba nafasa, don Allah Ummi kifad'awa dady bazan auri yaya Mahmud ba" murmushi Ummi tayi da fitowarta kenan daga part d'in dady bayan tafito wanka yanata tsokanarta akan Billy zata tafi gidan mijinta tabarta shikuma zata samo masa wacce zata cire mata kewarta, atunaninta duk jimamin barinta da zatayine yasa take wud'annan maganganun amma saitaji yanayin rik'on da tayi mata da kukan da takeyi yafi k'arfin ace kawai narabuwa da itane, d'agota tayi da sauri had'e da kallon fuskarta data kumbura tashiga bubbuga kumatunta cikin tacin hankali tana fad'in

"Bilkisu, Bilkisu, lafiyarki kuwa? Ke wai meyake damunkine, bazaki bud'e baki kiyimun maganar da zan fahimta bane?" Cikin shesshekar kuka tace

"Ummi bana son aurennan, don Allah kada ad'auramunshi, bana buk'ata Ummi" wani irin jirine ummi taji ya d'ibeta ganin da gaske da gaske billy ke wannan maganar wanda yasa nan take ta d'auketa da zafafan maroran da saida tafad'i k'asa, cikin b'acin rai Ummi takalleta had'e da cewa "idan mafarkine kikeyi Bilkisu to maza kifarka kafin ranki yab'aci kamar yanda kika b'atamun nawa" sannan tajuya cike da b'acin rai zata bar d'akin, da sauri Billy tarik'o k'afafuwanta had'e da cewa

"Wayyo Ummi nah wlh ba mafarki nakeyi ba, afarke nake Ummi kuma da gaske nakeyi bana son aurennan, saboda koda anyimunshi bazan tab'a samun farinciki ba"

Juyowa tayi tana kallonta had'e da cewa "innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Bilkisu anya ko ba aljanu suka shigeki ba, taya za'ayi ace gobe aurenki wai kice kin fasa, to kibari idan aka d'aura auren aka kaiki kimutu kinji ko? Shashashar yarinya kawai" tafice abunta cike da jin haushin 'yar tata.

Basmah kuwa duk da tanajin jiki haka tatashi tazage suka fara shire shiren walimar da za'ayi yau, ko kad'an bata bari gazawarta tabayyana afili don d'ai kar mom tafahimta harta aiwatar da abunda tace, Batool ma gaba d'aya yau babu walwala atattare da ita saboda rashin sanin madafar 'yar uwarta akan sharad'in mom, don duk b'oyon da Basmah keyi tana kalle da ita da kuma yanayin da take ciki,

Ganin kuka bazai amfana mata komai ba dole tayi abunda keyuyuwa don gaba d'aya mafarkin da tayi yaga tsoratata akan cewa tabbas Basmah zata iya rasa rayuwarta idan har tayi saken da igiyar aure tashiga tsakaninta da yayanta gobe, tashi tayi tasaka kayanta don dama towel kad'aine d'aure ajikinta tare da nufar part d'in dady tana maijin kowane hali da matsala zata fuskanta bazata tab'a auren yaya Mahmud ba bacin 'yar uwarta tafita buk'atarsa.

Da sallama tashiga parloun fuskarta ba yabo ba fallasa duk da kana kallonta zaka gane cewa tayi kuka kuma ba d'an kad'anba saboda yanda idanuwanta da fuskarta suka kukkumbura, cikin sa'a tasamu dady yana k'asa ya sauko don bai dad'e da gama breakfast ba yana waya da Mahmud pilot akan yazo yana son ganinsa akan zai tambayesa idan an d'aura aure gobe asabar zasu wuce da amaryarau ko sai banda gobe safiyar lahadi, shigowa tayi ta zauna gabansa wani b'angare na zuciyarta cike da tsoron rashin sanin abunda dady zai yimata idan tafad'a masa abunda ketafe da ita, yana gama wayar yakalleta fuskarsa d'auke da murmushi yace

"Auntyn Bilal injin dai ko lafiya naga fuskarki takumbura haka, Kaddai ince har kinfara kukan rabuwa da ummin taki tun yau" Shiru tayi kanta na duk'e ak'asa kafin tad'ago tana kallonsa idanuwanta na hawaye tace

"Dady kayafemun don Allah" tak'arasa maganar tare da had'a hannuwanta wuri d'aya, shima jiyayi hawayen sun cika masa idanuwa saboda tausayinta don shi atunaninsa saboda rabuwar da zatayi dasu ne, gashi za'a d'auketa tayi nisa dasu sosai, hannuwanta yarik'e had'e da cewa

"Aini baki tab'a sab'amun ba duk iya zamanki dani tun kina k'aramarki don haka kidena neman yafuwata saboda keda 'yan uwanki nadad'e da yafe maku duk wani abu da ku kayimun" cikin kuka tace

"Nasani dady shiyasa yau nake rok'on ka saboda akaro nafarko zansab'a maka da girmana, dady don Allah ina neman alfarma agareka amatsayina na k'aramar 'yarka daka tausayamun ka amshi k'orafin da nazo dashi agareka zuciyata cike da sarai da kuma yak'ini akan cewa zaka amsa mun" jikin dadyne yayi sanyi tare da d'an matsowa gaba daga zaunen da yake akan kujerar yace

"Bilkisu meke faruwane?, kin sanyani aduhu, maza ki gaggauta fad'amun k'orafinki ashirye nake dana karb'a makishi matuk'ar zakiyi farinciki"

"Kayimun alk'awari dady" tafad'a tare da mik'o masa hannu, cikin mamaki yabita da idanuwa yana kallo cike da tunanin wannan wane irin k'orafine da har saita nemi yayi mata alk'awarin cewa zai karb'ar matashi yamik'a hannunsa had'e da d'ora sa akan nata yace

"Nayi maki Bilkisu, ina fatar Allah yasa incika maki wannan alk'awarin matuk'ar baifi k'arfina ba" murmushi tayi tare da goge hawayenta sannan tace

"Don Allah dady afasa d'aura aurena da yaya Mahmud, bana son in auresa ko kad'an bana buk'atar yin aure yanzu dady don Allah kataimaka mun kada ad'aura wanna aur..." Ai kafin tarufe baki taji saukar zafafan marora da batasan ta ina suke fitowa ba, da gudu Mahmud pilot daya dad'e a tsaye bakin k'ofar yana k'ok'arin shigowa saboda kiran da dady yayi masa sai yatarar da mummunar maganar data nemi tasakasa suma yak'araso cikin falon jin saukar maroran da dady kesakar mata yana nema ya rufeta da duka ya rik'esa tare da shiga tsakaninsu.

Jikin dady naciccira yake fad'in

"Dama ke shashashace ban sani ba? Nizaki zowa da wannan mummunar maganar da zatasa inzama mutumen banza? to wlh baki isaba, idan tarok'i akayi to k'aryarku tasha k'arya inkuma Wasu jinnune suka hau kanki to zanyi maki maganinsu, mutuniyar banza da wofi baki isa ki watsemun zumunci ba nida 'yar uwata data nuna mun soyayya fiye da kowa aduniya, wallahi da inb'ta ran 'yar uwata k'ara natabbata cikin k'unci da damuwa nahar abada akan rashin yimaki abunda kike so" kalmar k'arshe da yayi tak'arasa Billy k'warin guiwa akan cewa idan har dady yana tsoron b'atawa 'yar uwarsa rai haka to ita yafi cancanta ace taji tsoron rasa 'yar uwarta, tabbas zata jurewa kowane hukunci dady zai yimata kuma tad'au alk'awari bazata tab'a bayyana sirrin zuciyar 'yar uwar taba saboda hakan shizai sa Mahmud ya aminta da aurenta batare daya musguna mata ba bisa da ace yasan cewa itace silar da tasa tak'i amincewa data auresa.

Dak'yar Mahmud pilot ya zaunar dady had'e da d'auko ruwa a fridge yabashi yasha, sanan shi kuma yajuya inda Billy ke zauna tahad'a kai da guiwarta tanaci gaba da kuka, gabanta ya duk'usa cikin sanyin murya dake nuna yanayin damuwar da yake ciki yace

"Billytah" d'ago kai tayi da niyar kallon fuskarsa amma sai taji bazata iyaba "Billytah d'ago kai kifad'amun menayi maki kikace kinfasa aurena? narok'eki kifad'amun komeye ashirye nake dana rok'eki kiyafemun, Bilkisu kiyimun magana mana" yafad'a ijiyarsa d'aya nafidda k'walla, jin tak'i cewa komai sai kuka da takeyi yasa yaci gaba da cewa "karki manta ba sau d'aya ba ba sau biyu ba da bakinki kinsha fad'amun cewa atare zamu rayu kuma atare zamu mutu, har alk'awari kika d'aukar mun cewa tabbas zamu rayu tare dake kuma ak'ark'ashin inuwa d'aya, to meyasa yanzu kuma zaki karya" yafad'a cikin tsawa tare da jawo hannunta yana k'ok'arin cire zoben daya bata ranar da zasu koma barno.

Da sauri tak'wace hannunta tare da cewa

"Saboda bazan tab'a samun farinciki ba idan na aureka, pls don Allah kabarni bana son auren nan yanzu ko kad'an" matsowa yayi dafa da ita kamar zai rungumota sannan yakama kunnuwansa idonsa na hawaye, zuciyarsa nayi masa wani irin k'una da rad'ad'i

"Pls Billy kiyi hak'uri, idan wani abu nayi maki na amince kiyimun hukunci amma don Allah kada kibarni, ko kad'an bana son wannan kalmar rabuwa da kike furtawa atsakaninmu, kiyi hak'uri billy kituna da cewa munyiwa juna alk'awari akan tare zamu rayu tar..." ganin zai iya cin galabar zuciyarta har ya sauya mata quduri yasa tayi saurin katsesa tare da turesa da k'arfi tana fad'in

"Bazai yuyuba yaya don ahalin yanzu bazan iya auren kaba, don Allah kayi hak'uri ka d'auki wanna kalmar atare zamu rayu kuma atare zamu mutu amatsayinmu na 'yan uwa kawai amma bada aure ba"

Dady da tund'azu yake saurarensu yanaji tamkar yakamo Mahmud d'in dake faman rarrashinta da ita dake bashi haushi yayita duka yanufo wajen da sauri cikin fushi da b'acin rai zai rufeta da duka saboda yanda yaji ta katsawa Mahmud d'in tsawa tare da turesa,

Da sauri Mahmud pilot ya dakatar dashi had'e da cewa

"A'a dady kabarta, nahak'ura bazan aure taba tunda har tanaji cewa bazata samu farinciki dani ba, na amince murayu amatsayin 'yan uwa ni da ita" juyowa yayi tare dasa hannu yagoge hawayen da suka zubo masa a idanuwa yana kallonta sannan cikin sanyin murya yace

"Zanbarki Billy, zanbarki kiyi farinciki akaro nabiyu kin sake wasa da zuciyata, karki damu nafahimci duka laifina ne dana tirsasaki akan soyayyata, amma ina so kifad'amun da bakinki cewa bakya sona kuma kin tsaneni hakan zai tabbatar mun da cewa da gaske kikeyi bazaki iya aurena ba"

Wani irin kuka mai tsima rai takeyi wanda duk wanda yasan meye soyayya da yanda akeji akanta zai iya fahimtar cewa ko kad'an babu komai azuciyarta face tsantsar soyayyar yayanta kafin tad'ago kanta idanuwanta acikin nasa tace

"Wlh yaya dagaske nakeyi bazan iya auren kaba, kawai ka hak'ura dani" ai kafin Mahmud yace wani abu yaga dady yaciro wayar socket yafara bugun Billy da ita yana fad'in "wlh baki isaba sai kin auresa idanko ba hakaba sai dai kibarmun gida, su alhaji kabiru ne shida 'yan uwansa da shigowarsu kenan suka isa wajen da sauri suka rik'esa shi kuma baba k'arami ya d'auketa k'asa ransa ab'ace don duk yafisu zuciya yace

"Yaya wannan wane irin muzgunawane zaka jima yarinyarka ana gobe d'aurin aure kuma agaban mijin da zai aureta"

"Muzammil don Allah kubarni inkoya wa yarinyar nan hankali, agabana take wulak'antamun d'a, take fad'a masa kalaman da zasu cutar dashi sai kace ita kad'aice mace aduniya" nan dai suka zazzauna suka rarrashi dady tare da bin ba'asin abunda kefaruwa, take dady yazayyane maau komai a-z har yanda sukayi da Mahmud d'in agabansa, iya girgiza sunyita jin abunda dady yafad'a cike da mamaki suna faman jinjina kai, ita kuma inbanda addu'a da fatar Allah yasa sugoyi bayanta babu abunda takeyi duk kuwa da tsamin da jikinta keyi, alhaji bukarne yayi k'arfin halin kirawota ya zaunar da ita a k'asa tsakankanin k'afafuwansa dana baba k'arami sannan yace Mahmud yaje ya zauna tsakanin dady da alhaji kabiru saiti da ita. Cikin natsuwa yadafa kanta had'e da cewa

"Bilkisu karkiji komai ni mahaifin kine, kuma zanyi maki adalci matuk'ar kinada hujja mai k'arfi akan cewa bazaki auri d'an uwanki Mahmud ba, don haka saki jikinki kifad'amun meye dalilinki.

Shiru tayi tare da d'ago idanuwanta tana kallon Mahmud da shima ya tsureta da idanuwa kafin tace

"Baffa tun ranar da Mahmud yace yana sona nafad'a masa gaskiya inada wanda nake so, bayan haka tunda yasanar da dady yana sona zai aureni ba'a tab'a kirana akaji shin nima na amince ina sonsa zan auresa a matsayina na 'ya, sannan kafin infurta cewa bazan auresa ba saida narok'i dady akan inada k'orafi kuma da kansa yayimun alk'awarin zai karb'a sai abu nak'arshe na amincene zan auresa saboda ceto rayuwarsa lokacin da likitoci sukace yakusa kamuwa da ciwon zuciya matuk'ar ba'ayi masa abunda yake soba, sanin haka yasa danaje asibiti yarok'eni nayi sauri amincewa don kada yafad'a cikin wani hali amatsayinsa na d'an uwana yanzu kuma baffa nafahimci bazan samu farinciki ba idan na auresa shiyasa nazo da k'ok'on barana da tunda yanzu yasamu lafiya kawai yahak'ura" runtse idanuwa Mahmud yayi hawaye suka ziraro masa afuska don yasan duka gaskiya tafad'a amma shiyasan tana matuk'ar sonsa sosai don koyanzu yaga haka cikin idanuwanta dole akwai abunda yasa tace bazata auresa ba, dole sai indai shiga tsakaninsu akayi amma haka kurum ya tabbata Billynsa bazata k'isaba duk da cewa tayi masa abubuwan daya kamata idan har shi yanada zuciya yahak'ura da ita.

Ajiyar zuciya alhaji bukar yayi had'e da cewa "to kunji hujjojinta da dalilanta duk da Wasu basuda amfani amma akwai wud'anda dolene aduba mata koba hakaba yaya" yafad'a yana kallon alhaji kabiru da gaba d'aya kansa ya kwance, nan yatambayi both dady da yaya Mahmud cewa shin abunda tafad'a gaskiyane haka yake, duk suka tabbatar masa da eh, hakane, amma dady yace shi wud'annan hujjojin bazasu sa yajanye zancen aurnba saidai idan ankaita ta mutu, ganin rigima ta kabre tsakaninsu baba k'arami da dady sunce baza'a fasa aurenba shikuma alhaji kabiru da bukar sunce dole ahak'ura don gudun lalacewar zumuncin su tunda bataso yasa Mahmud yace

"Dady, baffa don Allah abari wannan rigima haka, tunda batason auren shikenan, Allah yayi mana zab'in dukkanin abunda yafi zama alkhairi"

Sosai ya burgesu kuma dama shi dady tuni wata shawara tazo masa saboda baya son suci gaba da musu da yayunsa har azo wani sab'anin yasake rabashi dasu kamar yanda na mahaifiyarta yasa suka rabu na tsawo lokaci, bayan duk sunyi shiru dady yakalli 'yan uwansa had'e da cewa

"Shikenan na amince, amma baza'a fasa d'aura aure da Mahmud gobe ba, Alhamdulillah da Allah yasa ba Bilkisu kad'ai nahaifa aduniya ba, ina so amatsayinku na 'yan uwana kusheda cewa naba d'ana auren 'yarku Basmah wato babbar 'yatah kuma ina fatar b'acin rai bazaisa Mahmud kawatsamun k'asa a idanuwaba kamar yanda 'yar uwarka tayi" Alhamdulillah wannan abu yayi sukace gaba d'aya tare da kallon Mahmud, "kaji abunda mahaifinka yafad'a, shin mekace?"

Har ga Allah yaso yamanta da zancen aure nan kusa gaba d'aya arayuwarsa amma bazai iya musawa dady ba, kuma dole yanunawa Bilkisu cewa ba ita kad'aice mace ba aduniya kuma don yarasata bazai mutuba, kuma bazai fasa son wataba azuciyars duk dako ba haka bane yasa yace

"Dady, baffa, Basmah da Bilkisu duka 'YAN UWANA NE, kuma duka ina sonsu ina k'aunarau tunda jininane, don haka na amince zan auri Basmah ina fatar Allah yasanya alkhairi tsakanin nida ita, dama wani baya tab'a auren matar wani" yak'are maganar had'e da mik'ewa yabar d'akin idonsa nazubar da hawaye, runtse idanuwanta tayi itama hawayen suka zubomata tayi murmushi mai had'e da kuka tare da cewa amin sannan tabi bayansa, gaba d'aya iyayen nasu nata saka mashi albarka,

Nan su alhaji bukar suka sake ba dady hak'uri tare da mik'a masa kud'i dubu hamsin da biyar da suka had'a masa amatsayin gudun mawarasu agaresa duk da cewa sunsan yafi k'arfinsu wanda dama shiya kawosu gidan suka isko wannan bak'on alamari da Allah yasa aka warwaresa cikin sauk'i, kud'in baba k'arami yabashi tare da cewa

"Yaya ga wannan tsayawa bak'i ruwa gobe, kayi hak'uri dasu kasan yanayin yanda yake"

Karb'a dady yayi cikin jin dad'i da farinciki duk da yana cikin damuwa don nunawa 'yan uwansa cewa lallai suma suntaimaka masa duk dako yasan cewa yanada d'unkin ba lunkin wud'annan kud'in, godiya yadinga yimasu sosai sannan yaciro wayarsa tare da cemasu yakamata akira Umman borno don asanar da ita halin da ake ciki nafasa auren Mahmud da Bilkisu wanda gobe za'ayi sa da mahmud da Basmah, nan take suka amince da hakan bayan sun sheda masa itama suntura mata da dubu ashirin da biyar ta account taba bak'i ruwa amatsayin tasu gudun mawa..



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Thanks for your beautiful comment, am so happy yanda naga kuna comment saboda yanda page d'in jiya yatab'aku, u people surprise me harda wud'anda bana tsammanin suna karanta littafinnan yau naga comment d'insu😅 thanks to my takwara Billy yau kin zak'ulomun ghost reader's d'ina💃🏼🤣, I luv you so much guzs jazakumullahu bikhairan🤝🏻Allah yak'aramaku k'arfin idanuwa da sabbin wayoyi na kamfanin iPhone🍏 *STAY BLESS FOR EVER MY FAN'S*_

💎Page_____85💎


Nan take duk suka amince dady yakira Umma bugu d'aya tad'auka cikin yanayin da zai tabbatar maka da irin tsantsar farincikin da take ciki had'e da cewa,

"Assalamu alaikum yayana ina kwana?, barka da wuni"

"Lapiya klw hafsatu nah kina lafiya"

"Alhamdulillah ya hidama da taron bak'i"

"Masha Allah muma nan komai Alhamdulillah, gamu zaune tare da 'yan uwana"

"To kagaida mani dasu, naga sak'o nagode sosai Allah yasaka da alkhairi kuma yabar zumuncinmu"

"Amin ya Allah" dady yafad'a tare da yin shiru, hak'ik'anin gaskiya wani irin nauyi yakeji tayanda zai fuskanci 'yar uwarsa da wannan maganar kuma ko kad'an baya son taji zancen abakin kowa inba shiba, don gudun kada tayiwa abun mummunar fahimata, gaba d'aya 'yan uwansa zuba masa idanuwa sukayi suna jiran suji yanda zata kaya tsakaninsa da 'yar uwar tasu.

"Hello yaya yanaji ka kirani kuma kayi shiru, injin dai ko lafiya ko?" yaji Umma tafad'a cike da zak'uwar jin dalilin da yasa ya kirata,

"Eh lafiya klaw saidai wata 'yar matsalace nake nema kibani shawara akanta"

"To yaya Allah ya azamu akan daidai" ajiyar zuciya yayi tare da fitar da wani irin iska mai zafi ga bakinsa da kuma hancinta sannan yace

"Hafsatu tsakanin Bilkisu da Basmah wa kikafi so aranki" dariya tayi kafin tace

"Kai yaya wannan wace iriyar tambaya ce kayimun? Ai ina da Basmah da Bilkisu duka 'ya'yan kane kai ka haifesu ni kuma kai d'an uwanane don haka gaba d'ayansu ina sonsu kuma so maitsanani tunda jinina ne!"

"Kintabbata?"

"Sosai kuwa yaya wai meye na wannan tambaya, nifa kasani aduhu?" Saida dady ya runtse idanuwansa, sannan yafara kwararowa Umma bayanin abunda ke faruwa da kuma hukuncin daya yanke namayewa mahmud pilot gurbin auren Bilkisu da Basmah sosai Umma taji maganar tamkar saukar Aradu cikin kanta, cikin rud'ewa tafara tambayar halin da d'anta keciki saboda irin son da tasan yana yiwa 'yar uwar tasa Bilkisu,

"Ki kwantar da hankalinki, lafiyarsa klw, karki tab'a tunanin cewa Bilkisu shi tacutar, wlh koka d'an bata cutar dashiba kamar yanda tacutar dani domin har inmutu bazan manta da wannan abun da yarinyar nan tayimun ba, kiyi hak'uri hafsatu banyi hakan bane don b'ata ransa ba nayine saboda kada ayi auren matsalolinta sutaba mana zumuncinmmu" danne rad'ad'i da zafin da takeji azuciyarta tayi had'e da cewa

"Shikenan yaya bakomai ai dukansu 'ya'yana ne, ubangiji Allah yasa hakan shiyafi zama alkhairi"

"Amin hafsatu ngd" bai kashe wayar ba duk saida yaba 'yan uwansa wayar suka tayasa bata hak'uri tare da nuna mata cewa matar mutum kabarinsa don haka kada wannan abun yasa taji badad'i har 'yan buki sufahimci damuwarta. Cikin ikon Allah kuma taji duk b'acin ranta fiye da rabi yakau saidai d'an kad'an da yazama dole tajisa aranta, sallama sukayi tare da kashe wayar sannan takira yaya Mahmud dake tsaye Billy nak'ara basa hak'uri cikin dakewa duk da yanda takejin tausayin kansu amma tacije tanuna masa cewa k'addarace tarabasu amma badon bata sonsa bane, murmushi yayi had'e da kallonta yana k'ok'arin jawo wayarsa dake ruri yace

"You are so funny Bilkisu, kina sona, amma bazaki iya aure naba? to meye wannan"

"Jarabawa yaya, kawai kayarda cewa dama Allah ya tsaro zamuyi soyayyane ak'ark'ashin jarabawarmu amma bazamuyi aure ba"

"Ko?, to ai shikenan" yafad'a tare da kara wayarsa akunne yabar wajen yana fad'in "hello ummanah" ajiyar zuciya tasauke jin yanda muryarsa tafito awayar tamkar baya cikin damuwa wanda har saida tayi tunanin kodai wasa yayanta keyi mata, don gayanda tasan son d'inta na k'aunar Billy bata tunanin rabuwarsa da ita tazamo abu mai sauk'i awurin sa, muryar sace da taji yasake cewa

"Ummanah are you there" tasa da sauri itama ta amsa masa da cewa

"Yes my son, ya kk? Kana lafiya? shin da gaskene abunda dadynku yakirani yana fad'amun yanzu?" Ta jefo masa wud'annan tambayoyin ajere cikin lokaci d'aya kamar zatayi kuka, murmushin da baikai ciki ba yayi tare da kallon gefen da Billy ketsaye a inda yabarta har lokacin ko motsawa

Please Login or Register in order to submit comment